Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasan da hakane tun lokacin auren shi da nafisat,
Wata rana da tasa buje darigar dinkin material sun dawo office da Almustapha a lokacin yako dinga mata masifa yace kada ta kara sa irin su a gidan shi,
Yace may amfanin kasa kayan da duk tsiraicinka zai baiyyana afili,
Wai da sunan yin wa maigida kwalliya alhalin bashi kadai ,aiwa adon dashi ba dole ne a fita waje wani yaga ni,
Muna tsaye gefe muna jin su nida Amal, alokacin,
Yaci gaba da fadin matar Abdull ghana da ta rasu kwanaki ana bidan zanin da za,a rufa gawan ta dashi duk cikin kkayan ta ba zani,
Ya ce may yafi wannan abin tashin hankali ace yar musulumai bahausa ba,a samu zani a cikin kayanta ba ai wanan yazama abin ku ya ga mutum tun a nan duniya,,
Ya ce shi dama bai kaunar yaga mace duk ta matse jikinta a waje koba,a cikin ma,za bane,
Jin wanan maganar tasu da, nasifit yasa hakan ya zauna min a rai tun wancan lokacin duk abinda zanyi bana sa dinkin da zai mugun matsemin jikina ,
Balle gidan mu da kusan mutane su na shiga bawai shi kadai maigidan ke shigowa ba,
Duk su salim da malam Basiru wanda yazu yake tare damu yana zama kamar dan uwana na jini sosai,
Don gaskiya munji dadin zuwan shi saboda akwaishi da kwa,zo ga rikon amana,
Ina sauri inj tafi gurin su, ummi indiba ko sun fara cin abinci saboda bana son su zauna basu ci komai ba,
Dai step na karshe ya bude kofar falon yashigo gida a lokacin,
Yana rataye da couth din shi a kafadar shi, almustapha da Basiru suna bayan shi dauke da takardu da briefcase din shi mai dauke da laptop din shi,
Tun daga nisa muka yi wa juna yar murmushin mai aikawa da sakonni, kala kala,
Inda nagane nufin shi kwaliya ta taimai kyau, nikuma na nuna mai cewa don shi nayi ai,
Sai yai wani ragwada kai alamar yagode fa,
Su Almustapha da Basiru dake bayan shi basu gane komai muke yi ba,a tsakanin mu,
Kayan da su Basiru suka dauko mai nai kokarin karba
Tare muka koma sama, dashi, muna bacewa wasu Almustapha ya rungumo ni zuwa jikin shi yana mai sun sunar ko ina ajikina a kaukauce,
Da kyat na iya sabulewa rikon da yai min ina mai gabatar mai da ruwan wanka,,
Kafin yafito na fitar mai da kayan da zai sa har da plat shoes da zai sa ya fito,
Ina cikin fesa turare sai naji wani irin abu ya taso min kamar zan yi amai,cikin sauri nabar dakin ,,
Sam ban dauki hakan komai ba aguri na, dakina ,nakoma nadan kara kallon mirrow dan indan kara burge maigida ,
Zaune na samay shi a falo yana jirana in zuba mai abinci ,
Kurrr idon shi akai kamar bai taba gani na ba,
Direct dining na nufa shima yataso a hankali zuwa bisa tebur din,
Kululin da ke jere saman tebur din nafara budewa, nadago kai na kalle shi dan inji may zai ci daga cikin abincin da nake budewa,
Daidai lokacin naji wani irin amai ya zo min duk yadda, na so in daure har in gama zuba mai, abin ya faskara,
Da sauri na toshe bakina na nufi, toilet, din dake cikin falo,
Amai nayi sosai har sai da naji jiki, da kyat na samu ya tsaya min, na bude famfo na wanke baki na da fuskana,
A hankali na dago da niyar in koma in cigaba da zuba mai abincin,
Ganin shi na tsaye kofar toilet din hannun shi harde, a saman kirjin shi,
Wani irin kallon tuhuma yake min .
Zuwa, nayi da niyar indan bi gefen shi, in wuce zuwa cikin falo ,,
Tambaya ya watso min may yasa may ki fatima,ina kokarin wucewa ya, kara jefo min tambayar,
A hankali na ce mai ba komai, nima bansan komay yasa may ni ba nai aman,
Hanya yabani nawuce cikin tuhuma yake kallo na har muka kai bakin dinning din,
Nai kokarin in kara zuba mai wani abinci, aiko saura kiris in amayo ma sheriff amai a jiki,
Mikewa yayi da sauri yazo inda nake duke ya rike ni
Duk wanda ke gidan saida yafito a lokacin saboda irin kakarin aman da nakeyi,.
Tunda yatsaya min yace mutafi asibiti, amna fafir nace bazan je ba tunda lafiya na kalau,
Yanzun ne kawai hakan ya samay ni daga jin kamshin abinci,
Wani kallon tuhuma su Ummi da Inna suke min a lokacin,
Inna ce tace mai wani asibiti zamu ai saidai kuma in Allah ya rabamu lafiya,
Sam ban fahinci may inna take nufi da hakan ba dani don haka dagani har sheriff muka hau sama,
Duk da barcin yamma ba dabi,ana bace yin hakan yasa yau sai gani nayi barci ,don wuya,
Barci mai nauyi nayi a lokacin dan bakara min jin jiki nayi ba,
Doctor kamal ne yazo gidan bayan sallah isha,i don ya dibani,
Amma sai ya gani ,zaune a falo tare da su mariya da su maman Umar munata labarin mu muna dariya,
Ganin su tare da docto yasa ni dan shan jinin jikina,
Duk kan su mamakin gani na lafiya sukayi cikon hokima muka wayance zancen batare da doctor yabani koda paracetamol ba,
Tun wanan ranan ban son jin warin girki musam man mai dauke da tafarnuwa,
Idan kuma dare yayi sai in kama jin high fever har kusan sallah asubah,
Yau kamar na wancan ranan ne ina cikin taimakon shi sai kuma ga amai
Mariya tana gurin yace dole sai muntafi asibiti sn diba ko may ke samuna haka,
Mariya tace Allah yabar muna yaya Sheriff, shin bakaji abinda inna ta fado na ba,
Cikina fa take cewa sai randa Allah yasa ta haihu zata daina hakan,
Aiko hankali mu mida sheriff yai wani mugun tashi da jin kalamin mariya,
Tambayar mariya yayi ko yaushe inna ta fadi hakan,
Sai ta kara nanata mai abinda inna ta fadi a ranan
Tsaye nake amma ban san lokacin da nakakai zaune ba nadafe kai na sai wasu hawaye ke biyo min a fuska suna silalowa kasa,
Shi ma sheriff zama yayi yadafe kanshi da hannu gida duk yarasa abin yi,
Mikewa yayi ya nufi inda ake aje makullaiyan motocin gidan,
Ya hau sama da sauri yadauko min Naifal dina yace intashi muje asibiti,
Ba musu na shirya muka kama hanya zuwa asibiti,
Diba guda likita yai min ya tabbatar min da cewa ina dauke da cikin wata biyu a jikina ,
Ido nazaro dan mamakin jin hakan danayi bani ba har shi saida ya kadu,
A firgice yacewa doctor muna da babies yan wata takwas fa,
Likita yai dan murmushi yace ba komai bane hakan kawai za,a rubuta muna magani da kuma irin abincin da zamu fara ba yaran,
Niduk bayanin da sukeyi kaina yana kasa ina ta sharban hawaye kawai,
A cikin mota duk yarasa abinda yake ciki saboda gaba daya na birkice mai yarasa gane kaina,
Yai lalashi na har yagaji banyi shiru ba,
Ido kwai ya samin zuciyar shi duk bai mai dadi, don shi gani yakeyi ai yaran zasu shiga matsala har yajawo masu matsala,
Nikuma nafarkon abin da nake tunane a zuciyana shine da,wani ido zan kalli su Ummi da Inna kai har ma da sauran mutane
Kai gaskiya da sake awanan zan cen namu dole asan abinyi kafin a,san cewa akwai ciki atare da ni,,,


Dan Allah kuyi hakuri da wanan pls ba yawa bana jin dadin jikina sam,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
9⃣7⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,


Jin zuciyar shi yakeyi kamar zata tsage mai gida biyu, saboda jin kukan da takeyi kamar ana mai yayafin ruwan zafi ne a jikin shi,
Burki yataka da karfi saida ta dan razana, don yadda ya taka birkin mutanen da ke gefen titin suka dinga kallon su,
Shiru yayi yasa ma min idon ina ta faman gumzar kuka, na,
Ganin yadda ya faka motar da karfi ga kuma mace aciki tana kuka yasa yan bagaladi zuwa inda motar take dan ganin abinda ke faruwa a cikin motar,
A hankali suka kwankwasa glass din motar dan na ciki su bude masu,
Katin shedan wurin aikin shi yadauko yafara nuna, masu cikin girmamawa , suke ce mai may ke faruwa ne haka yace,
Masu ba matsala su wuce kawai, abinsu sai yai godiya yai kick din motar shi, yadau hanya,
Muna shiga get din gida mu ya dan waigo inda nake yace, idan har ina son su Ummi su san abinda nake cikine inci gaba da kukan da nakeyi
Dole nadan saita kaina nashare hawaye da tmyai min jagab a fuska,
Cikin dakiya nadan daure na bude mota zuwa cikin gidan
Cikin sauri na haye matakalan hawa sama ina mai zub da hawaye ,
Shiga na da kamar min ti biyar naji anturo kofar dakin a hankali,
Shiru naji ba ai min magana ba ni kuma ban waiga inga ko waye ba,
Don ni a zato na sheriff ne wanda yanzu haushin shi nake ji don gani nakeyi shi yai min wayo har aka kai ga haka,
Muryan mariya na ji cikin wani yanayi tana fadin haba anty dan Allah ya kamata ki daina wanan kukan haka,
Sai a lokacin nadan waigo kadan , fresh milk ta miko min a cikin wani cup din tangaran maidan sanyi kadan,
Bamusu na karba don kusan shine abinci na yanzu,
Duk son da nakewa fresh milk din yau sai naji shi kamar wani guba nake sha ,
Ko rabi ban sha ba na aje a sidedrower dina na koma ina batun dunku lewa a saman gado,
Mariya tace wai anty fadima kin san may kike yi kuwa,haka,
Bafa cikin shege kikayi ba cikine mai uba kuma uban ba gajiyye ba wanda ko kun kai ku nawa ne zai iya kula da ku,
Anty ko dai ni dake kasa gare ki aibani wanan abin dan nasan cewa ba mai wuce kaddaran shi,
Balle wanan abin alfahari ne ai agare ki,
Da sauri na dan waigo ta dan jin abinda tace min,
Ta ce eh mana, shin ki ko san cewa a kauye duk da talaucin da muke yi har gasan haihuwa suke yi a haka nan,
Fuska na alamar mamakin maganar ta ya nuna ,karara,
Taci gaba da fadin a cikin wanan talaucin za suyi ta zuba diya waidan kada kishiya tafi su tara diya,
Shiko miji ko oho,ho,ho, wata ma da kyat ake samun dan akuyan da za ayanka mata,
Gashi ba wani wada,ttacen abinci da mace zata ci takara kuzari,
Hakan bai hana kafin kwana biyu kiji ana fadin ai wance ciki aggareta,
Kinga sun samu riba biyu kenan gashi sun raya sunnan, ma,aiki (S A W) ga kuma ribar kishi da suka samu, ace ai wance yanzu aurenta shekera kaza ne diyanta kuma kaza,,,,
Kafin taci gaba sheriff yashigo dakin dauke da ummibanan a hannun shi tana yar fitinar ta da alamar nono take so,
Cikin ido na yake kallo yaga ko zan karbi yarinyar ko kuma zanki karban ta ,
Ina karbanta na bude nono na mika mata tai wani irin ajiyar zuciya takama nonon
Sai faman aje zuciya take yi don jin dadi da alamar tadan dade tana kuka,
Mariya ya dan kalla sai kawai ya fahinci cewa aikintane hakan,
Gefen gado yadan zauna batare da kalle ni ba, ,yana fuskan tar kofar dakin,
A hankali ya ke magana yace min Fatima kiyi hakkuri dan Allah ki shayar da yaran nan har zuwa lokacin da ya kamata a cire su a nono,
Wani iri naji a cikin zuciya da yace haka dan ban san lokacin da tausayi kaina da na yaran ya kamani ba,
Wani sabon kuka na sa masu mariya dake shirin barin dakin ta waigo tana fdin Ya Salam,
Anty fadima wai ko lafiya kike da wanan abin da kike yi,
Shin kisan cewa Bintu ta haihu da wata uku ta samu wani ciki,
Duk da kuka nakeyi saida nadan waigo dan mamaki jin maganar yar kaunata mai dabiar manya mata,
Tace walle ko bata kumayi wani fitina ko shiga tashin hankali ba,
Iyaka dazata haihu uwar ta ,ta taho, tadauki yarinyar ta farko, anka barta da dan jaririn,
Takara she zance da cewa to balle ke ga Ummi da Inna damuwa mika damuwan ki banda ki cika ma yaya sheriff gida da yan diya,
Wani irin harara da bugu nakai mata ta mike tana dariyar keta,
Sheriff da ke jin mu ya kama muna dariya yana dan murmusawa,
Fitar ta keda wuya sheriff yadan matso kusa dani kadan yadan sau,sauta muryan shi yace min fatima, kafin yafadi wani magana,
Nai saurin toshe mai baki , na a,za kaina asaman kirjin shi, nakama kuka,
Rungumay ni yayi ya na dan shafa min kai alamar lalashi,

Na hana mariya da sheriff su fadawa su inna wanan zancen haka naci gaba da shayar da yara na nono cikin fargaba,
Sheriff kuma yana kokarin sayo masu duk wani magani da zai sa su karin kuzari
Ganin da nayi yaran basuyi komai ba yasa nadan fara sake jikina ,
Ga bukin Amal yana kawo lokaci don yan zu saura wata guda ga lissafin da naji su sheriff da Salim nayi,
Hakan yasa yanzu ban da wani time din zama gida sosai don muna shirin zuwa sudan can garin iyayyen Almustafa dan gyarawa Amal gidan ta na can,
Cikin dake jikina duk da yafara girma so sai bai hanna ni yin kuzarin aiyukan da yadace inyi ba,
Saida muka fara zuwa Nigeria tukun muka kwana uku, gurin shehi, sanan muka dunguma zuwa kasar sudan tare da yan rakiya daga dangin su Shehi mutum guda sai dangin ummi mutum guda
Abin mamaki saigashi ni a fanni na har mutum shida sheriff ya yarda in tafi dasu,
Salimat safiyya mariya Rugaiyta, matar Basiru, da hafsin mu,
Hafsi taiwa Ummi kumshi mai kyau irin na yan sokoto kafar yarinya yai radam yai kyau,
Mun isa lafiya, ankarbe cikin mutunci, a can muka samu kayan da sheriff yai oda a Dubai har sun iso ko don haka ba bata lokaci muka shiga gyaran gida don yin abinda yakai ,
Tun a cikin family su Almustapha naga mata da maza suna ta zuwa kallon ummina, da ke dauke hannu matar malam Bashir wace yanzu kusan duk kula da yaran ya koma hanninta,
Abinda sukeyi bai bani mamaki saida mukaje gurin wasan kamun ango da sukayi da yamman ana gobe zamu dawo Nigeria,
Naga an kewaye min yarinya anata kallon , cikin tashi hankali na isa gurin da suke a zaune a sasu a tsakiya sai kafan Ummibanan da yasha kushi ake kallo ana mamaki,
Tambayar su nayi a cikin larabci, harshen larabci ko may ke faruwa suka kewaye min yar diyata,
Sai ce min sukayi wai kumshi sukaga an mata shine suke mamaki,
Wai ita da batada miji may zai sa ai mata kumshi yar karama da ita haka,,,
Mamakin su kwarai nayi dan sai da sukace haka na tuna cewa larabawa basuyi wa diyan su mata kwalliya irin namu wai sai wacce keda miji zatayi irin hakan damu nan muke yi,
Nai masu bayani cewa mu haka al,adar mu take diya mace za,a iya mata duk wani kwalliya da macen aure zatayi
Saboda ta tashi da wanan tarbiyar na koyi da sunnar maaikin manzan Allah, SAW,,
Lokacin da naiwa yan uwa na bayani sai duk mamaki ya kama su su ma,
Salimat tace min ai lokacin da ta taba yiwa Asamu,u kum shi da taje massalaci da ita a madina wasu larabawan Egypt taruwa sukayi suna kallon ta,
Tace ai su haka akidar su take wai wa yaro zaiwa kwaliyar burgewa da har za,a bata lokacin yi mai kumshi haka,
Muka dawo Nigeria abin cikin jin dadi irin karramawar da dangin Almustapha sukayi muna akasar su,
Gidan buki yafara cika don yanzu aiki har yawa yake muna saboda dangin uban nin mu sun zo daga jimeta,,
Sungan mu mun gasu inda sukai min korafin rashin zuwa inda suke daban yi ba lokacin da na haihu,
Hakuri na basu dan ban da gaskiya duk da nasan cewa ba laifina bane barinane da ba,ayi ba shi yasa ban je ba,
Amma yanzu nai masu alkawarin cewa zan zo insha Allah kafin in koma saudiya,
Duk wani al,adar da akeyi na bukin aure anyi a wanan bukin na Amal don gaskiya yan uwa da abokan arziki sun zo tako ina don taya mu murna,
Nafisat ma tazo daga Abuja saidai bata kwana ba tace zata tafi maiduguri ta kwana acan,
Kuma ko can din wai ba,a gidan Abba ba,ina jin suna fada da sheriff a cikin waya yana ce mata aida bata zo ba hakan zaifi mai sauki,
Hjy mama ko sakon Allah sa alheri bata aiko wa Ummi ko sheriff da shi ba, har aka ci aka sude,
Yan uwan Almostapha sun yaba kwarai da irin karancin da akai masu da sukazo don kusan duk abinda sukai muna da mukaje hjy Umma tasa mukai masu ninkin banin kin,
A gaskiya abin ba,acewa komai a lokacin, a gurin wanan bukin yan uwan mu ke cewa wai a hada mariya aure da Salim
Ban boye ba na nuna masu cewa hakan bai yu,yuwa sam,
Saboda ko nasan cewa halin su ba zai hadu ba, za,a bata goma daya bai gyaru ba,
Sanan shi Salim nafi kowa sanin yanada budurwan, da suka dade tare tun muna karatu a madina,
Ana gobe za a wuce da amarya kasar sudan inda zasu dan kwana biyu kafin su wuce saudiya,
Muka wayi gari cikin tashin hankali,don duk mun hada kayan tafiyar mu duk da sheriff yace bazan koma Sudan, ba dan tafiyan yai min yawa, hakana,
Sai gashi mun wayigari cikin tashin hankali, anyi sallah Asuba, lafiya da hjy tsohuwa ,
Inda take zaune tana lazimi sai Allah ya karbi ranta agurin,
Ba wanda yasan da haka sai lokacin da wata jikanta tashigo gurin ta ansar kudin kosai da ake mata sadaka duk safiya,
Taimagana taju shiru tana kai hannunta taga ta fadi gefe,
Sai ta sa ihu kawai cikin tashin hankali, lokacin ina dama ma Abbazannah madara ya sha,
Naji wanan ihun tashin hankali, Sheriff wanda yafito wanka alokacin ya na tsane ruwa a,kan shi,
Jin ihun yasa shi saurin sa rigan shi yai waje cikin tashin hankali,
Dauko yaron nayi nima mukayo waje inda yarinyar keta tsala ihu tana nuna falon hjy tsohuwa da hannu,
Cikin sauri ya fada dakin hjy tana kwance yadda ta fadi har yanzu,
Da sauri ya isa gurinta yana jijigata koda yadaga hannunta yaga ya biyo shi sharkaf,
Salati ya, sa,a lokacin yana mai zubda hawaye,a ciki tashin hankali,
Ina kawowa naga sheriff duke a gaban hjy dake kwance, bashiri naja da baya cikin tashin hankali,
Wayan sheriff na dauko lambar Bashir nafara kira sai na Shehi,
Batare da bata lokaci ba saiga,su,cikin gidan hankali a tashe,
Duk wanda yazo sai ya tabbatar da cewa ai hjy tsohuwa lokaci yayi,
Shehi ne da kanshi ya kira wayar Abba dake maiduguri ya sheda mai abinda ake ciki,
Kafin wani lokaci gida yacika fam da yan uwa da abokan arziki,
Andan jinkinrta ma Abban su Sheriff dan yazo yaga gawar mahaifiyar nasu, shida wasu yan uwan su daga Maiduguri,
Kulli nafsin za,ikatin,mau, yau muna kallon cikin tashin hankali da kuma jimamay aka wuce da hhy tsohuwa makwancinta,
Dole aka jinkirta tafiya da Amal wace taci kukan rashin kaka na gari da sukayi,
Duk shekarun da nayi da sheriff wanan ne karo na biyu danaga yana zub da hawaye arayuwan shi,
Duk da nasan cewa bakaramin rashi yayi ba na mutuwar hjy,
Amma kuma hawayen danaga yanayi yasa nakara gaskanta mugun shakuwar da ke tsakanin shi da yar tsohuwar mai mutunci ga zumunci da sanin ya kamata,,
Abba zanna ya ce lalai dai a wuce da Amal washe gari tunda ko an tsaya ba wai dawowa hjy zatayi ba,
Amal na kuka muma muna kuka kamar bazamu kara haduwa ba aka wuce da ita,
Tare da yan rakiyan ta duk da Abba ya hana atafi da yawa daga nan,
Su hjy umma da Salimat suna cikin yan tafiya, tare da mariya na,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

[12/15, 9:59 PM] β€ͺ+234 808 968 1079‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
9⃣8⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,


Saida akai sadakan uku, sannan muka fara shirin komawa saudiya,
Inna kan tace atabau ita bazata koma tare da mu dama zaman can ya ishe ta
Tace ace mutum kulun yana zaune bai aikin komai saidai aimai duk abinda yake so,
Gaskiya bazata iya wanan rayuwar ba itakan,
Ganin cewa inna ta matsa yasa Shehi ya cewa sheriff yasa amaida ita gida,
Banji dadin hakan ba gaskiya naso ace Inna tai hakkuri mukoma har lokacin da zan haihu amma sam taki yarda,
Hakan yasa muka dan daga tafiyan mu dan mu kaita gida tukun,
Wanan karon nasamu taron arziki gurin mutanen garin dogon daji so sai
Da kaina natafi gidan maigari batare da sanin kowa ba ,
Nakai makukan matsalata dan ina son in koma tare mama maidakin shi,
Sam baiji dadin yadda inna taki yarda ta zauna da mu ba a can yace mata ai anbar wanan kunyar da take yi yanzu
Yanzu koda gidan yar

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment