Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanin inna ta nake cikin wanan halin.
Abayana naji ana ce min kiyi hakkuri fadima addu,a kadai zamuyi har Allah ya kawo muna saukin wanan rayuwar,,, Don Allah bai manta da mu ba yana sane da halin da, muke ciki watara sai lbr in munyi hakkuri
Tashi ki share hawayenki ki saki jiki ki koma kamar kowa kada ki sake saka kanki cikin wata sabuwar ukuba kinji
Rugaiyya ce ke min wanan maganar
Nace mata to, nabita da kallo har ta shiga cikin gida fito da kayan suyan kosai,
Murmushi nayi azuciyata naji tausanyin kan mu sosai naji kuma ina kaunar Rugaiyya har cikin zuciyata.
Saboda tun farkon zuwana tana nuna min kauna, tankar ni yar uwartace tajini.


Wanan ciwon danayi yasa hajiya sanin dadina sosai tagane inada rana sosai a,gurinta .
Saboda yawan kudin da take samu aduk safe, yanzu ya rage yawa sosai,,,,

A haka na daure nakarasa jin sauki a bakin shagon mu don tun ban iyawa ina bin bango har na daure na zama normal . Naci gaba da harkoki na kamar kowa,,,,,,,


🐎 ZEEE MAKAWA🐎 HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 16:52] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

HUGUMA GROUP
ALLAH YA DAUKAKA

Almost true life story


Hankalin inna ya tashi kware ganin, yanzu kusan wata uku ke nan Gajiye batazo garin su ba kuma babu lbr ta
Inna tai sallama gidan, Ramatu suka gaisa cikin mutunci , sai shiru yabiyo baya har wani dan lokaci

Inna,ce ta kauda shirun tace, shin wai Ramatu ya lbr Gajiye ne naji shiru tunda suka tafi , har yau bajin ko sakon gaisuwar su ba.

Ramatu sai da hanjin cikinta yakada itama don da farko batayi tunanen hakaba ,,,, saidaga baya da ta fada ma mijinta yadda akayi har Gajiye tawuce da fadima sai ya hauta da fada,,,,,,,,
Yace ashe dama da hadin bakinta aka cuci inna yar kulu,
Gashi gari yadauka saboda kwadai tabari Gajiye tawuce mata da diya birni, Ashe cutar ta akayi,
Yace ma Ramatu tazauna da shirin duk randa asirinsu yatonu yar kulu taso diyar ta wlh shi ba,dashi cikin wanan rikicin ba.
Tun lokacin hakalin Ramatu yake a tashe tana tunane ranan da yar kulu zata tambayi diyar ta.


Ramatu tai shiru kamhar ruwa ya cinye ta, nadan wani lokaci
Sai can ta nisa tace ,,, A,gaskiya yar kulu banda lbr Gajiye ,
Asalima dai wlh ban san garin da take zaune ba,,, saida naji kamar an ce kano take zuwa sarin kaya daga sokoto.

Inna da ke zaune saitaji wani jiri yana kwasan ta , Allah ya taimaka a zaune take da a tsaye ne da tafadi.
Cikin karfi hali inna tace ban fahice kiba fa Ramatu?.
Gaskiya maganar,ke nan yar kulu,
Gajiye ban iyace maki ga,garin,da take.
Nima yadda take zuwa ganin gida hakane yasa muka dan shaku,,, amma da tunda tai aure birni bawai nasan ina take da zama bane balle insan lbr ta.

Habadai Ramatu zancan kikeyi kawai,, kizo har gidana kusan sau biyu akan inbari Gajiye ta, tafi min da diya taga inda take amma sai kice min wai yau aike bakisan Gajiye ba haba dai,,,,


Tun inna da Ramatu suna rikici su biyu har takai makwabta sun fara shigowa saboda gane ma idon su.
Daga gidan Ramatu, gidan yayanta malam sale tanupa
Batare da bata lokaciba ta zayyana masa yadda sukayi da Ramatu.
Shiru yayi cikin tashi hankali yanisa yace
Hakika yar kulu harda laifina ,,,,,,,,Don kamata yayi dakika kawo min shawara in tsaya in bincika kafin in yanke hukunci

Cikin kuka inna tace ita,kan kaiconta da har takasa rikon yar mareniyar Allah da tabari har Gajiye ta cuce ta.
Tacigaba da fadin gajiye kin cuce ni da har kika yaudare ni nabaki yar diyata da sunan sati uku yau gashi har wata hudu ke nan,,,,

Malam sale yatafi gidan maigari yakai karan maganan,,,, kowa yayi mamakin wanan maganar
Maigari yace to ai shi anfada mashi cewa yar kulu ta tura diyar ta birni wurin neman kudi.
Bawai yadda malam sale ya fada mashi ba,,,,

Ramatu da inna duk suna zaune a zauren mai gari kaida ganin inna kasan tana cikin tashin hankali so sai
Bayan mai gari yayi gyaran murya wurin yayi tsit,,, sai yafara da addu,a tare da neman tsarin shedan.
Yar kulu muna son jin bayanin tafiyar diyar ki daga bakin ki, duk da yayan ki malam sale yazo yai muna bayani. Sai dai muna son ji daga gare ki.

Inna takawo bayanin tun farkon haduwar su da Gajiye da kuma Ramatu ,har yadda akayi ta wuce mata da diya da irin zargin da gari ake mata
Takare bayanin ta cikin kuka tana fadin ko yan uwana ban yarda na basu rikon diyana ba saboda gudun zuciya ,,,,
An bukaci Ramatu tayi bayanin abinda tasani , Ita ma Ramatu bata boye komai ba duk yadda sukayi da Gajiye saida tafada a zauren maigari.

Zauren yai shiru kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi. Maigari yai gyaran murya yace,,, Dake yar kulu da Ramatu duk Gajiye tai maku wayyo ta gwada maku wayewa,, amma ai gajiye mutumiyar banza ce.

Yanzu addu,a zamuyi ma yarinya Allah ya tsare muna ita duk inda take Allah kuma yadawo muna da ita gida lfy.
Zan tura abinciko min duk inda Gajiye take cikin kasar nan anemo muna ita tazo tai muna bayani da kanta.
Maigari yakara ba inna yar kulu hakuri yace ta kwantar da hankalinta Allah zai dawo mata da diyar ta lfy.
Yace kuma wanan yazama maku darasi arayuwan ku,,,,,,, Don yanzu ba,a yarda da mutun koda ko kasan shi ba,aba mutum amma kai tsaye haka,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 16:55] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈.
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
🔟
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Almost true life story

Hafsta Yusuf Ali
Mariya SB
Fatima Garba Teema luv
Fadila Lamido novels
Musha karatu group novel
Maman Fati group novel
Duk ina ma wanda ke cikin wa "yan nan,groups din fatan, Alheri Allah sada mu da alherin da ke cikin wanan wata mai albarka👏👏👏👏👏👏




Zaune muke a bakin shagon mu, anyi, ruwan sama,an,dauke , Kasan cewar lokacin ruwan sama, ne babu wani kasuwa da muke samu yanzu sosai. Saidai manejin kasuwa .

To amma fa hajiya ce maiganin hakan ,,,,,, mudai mun,san ana samu. Ciniki daidai gwargwado
Wata yar doguwar rigace ajikina dinkin yai min yawa rigar Mari ce da tagaji da ja tayar shine Rugaiyya ta ce indauka in wanke indinga sawa .
Tun lokacin da nazo hajiya bata taba yimin dinki ba,,,, yan kayana duk sun kode sunzama ragga,,
Amma wai haka take ce muna wai mu kaza mai ne,
Ko sabulun wanki a sace muke saye mudan wake kayan mu

Wani lokaci kuma masu sayen abincin mu sukan dan yi muna alheri jefi jefi,
Sai dai Rugaiyya ta ja min kunne cewa kada indinga wasa da maza,,,,, kuma ka in,yarda in naje gurin tallan kosai kada in shiga cikin gida in tsaya daga waje
Aiko alheri akai muna hajiya muke ba wai acewar ta tana tara muna ne idan zamu gida saita hada muna da kudin aikin mu.
Zaman danayi jira nakeyi agama gyara kayan miya inkai wurin markade.
Bayan angama gyarawa nace ma Sukaina tabani kudin nika , saitace ai atabau tabani kudi tundazu
Wasa wasa muka fara wanan rikicin har gurin hajiya muka tafi,,,
Sukaina tace ai tun kafin ta wanke tabani kudi
Hajiya tasa aka cajeni kaf ba,aga komai ba aguri na
Amma sai hajiya tashiga zagina tana fada inda take shiga banan take fita ba,,,, wai ai dama halina baida kyau shiyasa uwata ta kawo ni yawon duniya tun ina,,,,, yar karama dani , wai, min shegiya mai shegen ido kakafe,da fari kamar gonar madara gakinan kaman akalla ki kulun kina cimin abinci a,banza baki auki

Yau duk inda kika kaimin kudina wlh sai kin tono minsu angaya maki barikin banza nafito yi ,
Ta, daka min tsawa saida na firgita Munafuka ina magana kin kafeni da shegun idanun nan naki, fita kiban wuri,,,,,
Sim sim na fita ina sharban kuka,,,,, hakana na dauki nikar nadoshi manika ina hawaye.

Matar dake muna nika ba ba,haushiya bace bayerabiya .ce,,,,, Cikin hausan yarbawa take min magana
Yaron hajiya maynene ya , samay,ka,ka nayi kuka yau, na fada mata duk yadda akayi ,,, tace wlh don dai nice kawai zatayi kuma na bata tausayi amma, in,don hajiyace bazatayi ba, don hajiya bakyau,,,,,
Bayan nadawo daga nikan sai hajiya tace wai wa,ya,bani kudi nabiya kudin nikan,,, nace mata kyauta a,kaimun nikan .
Aiko hajiya tace karya nakeyi kudinta ne dama naso in mata sata ne,,, Ta samayni taimin dukan tsiya har saida bakina ya kun bura
Saida yamma muna tatara kaya,muna kaiwa a cikin shago sai ga kudin da Sukaina tace tabani angani kasan wani roba ta aje ashe ,,,,,,,,
Rugaiyya ranta ya baci ta,fisge kudin taje ta nuna ma hajiya ,,,
Borin kunya hajiya ta kamayi tana fadin shegu da ban yi mata haka ba da shikenan ashani abanza,,,,,,,,,,
Kafin safe bakina ya kumbura sindib saikace an aza min dutse akai nake jinsa, hakan yasa nake jin zazabi yana son kamani
Rugaiyya ce, takama kula dani, taña dan gasa min wurin da ruwa mai dan dumi, tasayo min kwayoyi ta ba ni tace in,hadiye .
Hakana wuni ranan ina dan jin zazabi ajiki na.
Saida hakan bai hani zuwa tallan safe da nasaba yi ba na kosai,,,,,,
Aikin shago ne kawai yan uwana suka taimaka min yi

A haka rayuwar tamu tadinga tafiya yau dadi gobe zafi.
Girma kuma na zo mun a hankali , duk bautan da mukeyi bai sa Hajiya ta dan tausaya muna ba sai dai kulun cikin kara sabon sana,a mukeyi
Ita dai tayi kudi by all means ,,,,,,
Idan naga yara za su makaranta sai intajin wani iri a,zuciya,ta. Sai dai duk da haka dan karatun da ke a kaina bai fita ba dan ina iya karanta wasikar hausa tsaf kuma zan iya ta turanci ita,ma saidai aimin dan gyara kadan

Na riga na hakkura da duk wani halin da zan tsinci kaina banda wata matsala yanzu a,rayuwana sai dai kawai na bidan ma hajiya kudi,
Gwargwado yanzu hajiya ta wadata damu har takan dan yaba mu,
Wani lokaci har da kyauta takan dan bamu kamar dari biyu biyu ko kuma ta siyo muna dan abin marmari mu ci
Wanan kuma yasamu asaline tun ranar da wata kawarta tazo shagon mu taba mu kyauta da zata tafi,,,,
Tun agabanta muka fara ba hajiya kudin, sai bakuwar tace aa ,habadai mai sharwali kibar masu abinsu mana wanan ai kyauta nabasu..
Mudai muka fita waje muka bar su a cikin suna magana,,,
To tun tafiyar bakuwar komai ya canza.
Abakin Sukaina mukeji wai ashe bakuwar taima hajiya wa,azi tace mata amana fa muke a,gurinta

Shine dalilin ganin canji da muka gani ga hajiya,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎. HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 17:05] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Godiya ga masoyiya kuma anty na HAFSAT YUSUF ALI

Almost true life story



Hajiya mai sharwali ta bunkasa sosai yanzu kusan duk maison cin abincin kware shagonta zai zo ,,,,,,,
Abincin mu gaskiya yana da dadi sosai , saboda duk wani kayan hadi muna zubawa acikin aikin mu.
Mukuma muna tsayawa tsakani da Allah muyi mata aiki babu kissa ko cutar wa,
Yumma da Rugaiyya sun sha fada min cewa hajiya itace , gatan mu a garin kano .
Saboda zamanta mukeyi nan, ba zaman wani ko wata ba.
Wanan maganan nasu yakara min kwarin gwiwa wajen yadda da hajiyan mu kamar yadda muke kiranta,,,
Karfe shadayan rana, idan kazo shagon mu zaka samu mun gama dafa abinci kala kala,
Mundan gyara jikin mu don kada masu sayen abincin mu suga kazantar mu,,,,,,,


Yau ma kamar kullun mun gama aiki muna zaune muna jiran masaya, abincin,mu su,zo
Wata ma,aikata dake kusa damu nan cikin tarauni suke ,,,,,,, Suke zuwa sayen abincin indan sun tashi break, fast.
Daidai lokacin da suke zuwa cin abincin bamu da lokaci kan mu,saboda aiki kayi yawa kowa da abinda zai, ce a,kawo mai, yaci,,,,,,,,

Daidai wanan lokacin da ko hajiya bata da lokacin kanta,,,,, Wata hadadiyar mota mai ruwan kalar kakin soja tazo ta faka bakin shagon mu.
Hankalin kowa dake wurin ya kai ga wanan motar kusan , minti goma ba,a bude motar ba.
Koda,kofar,motar ta bude, Karfar wata mace ce tafara fitowa da shi tawaje amma bata fito da jikinta ba,,,
Gashi kusan duk wanda ke wurin hankalin shi naga wacce zatafito cikin motar,,,,,

Wata matace baka yar doguwa kyakyawa girma yadan fara kamata kadan, ita ta,fito daga cikin motar mayafin ta a kafada sai dan jakar fos data rika a,hannunta,,,,,
Hajiya na gani matar ta mike tsaye tana fadin a,a,a ,,,,,,
Wanake gani kamar zinaro ,matar tai,wani far da ido taware hannaye tana fadin nice mai sharwali,,,,,,
Suka rugumay junnan su cikin farin ciki da an,nashuwa,,,
Nan hajiya ta umurce mu da mukawo wa bakuwa abinci, tana fa mubarshi,, amma hajiya na fadin mu kawo duk abinda ke gare ,,,,,
Mari tace tirkashi ,yau kan munyi bakuwa mai muhinmanci kenan ,tunda har hajiya tace mukawo duk abincin da muka girka kalala wa bakuwar.

Koda nashigo da turen ferfesun kayan ciki dana kifi danye nasamu hajiya da bakuwar ta sun baje ana yaushe rabo,,,,,,
Bakuwar ta cire gyalenta tanawani juyawa agaban hajiya ,, hajiya nafadin wai Zinaro kece haka don Allah
Zinaro tace yo mai yai min tsinanen zafi mai sharwali ,,,,, mayye duniya ,
Wai yaushe kika zo kasan madai,,,,,
Bakuwar tace aini ma abinda yabani mamaki kenan mai sharwali naga,kusan kowa da akai zamar harka a saudiya amma ke bangan kiba . sai na tambaya akace min aikina nan gidin murhu kina halaka kanki,,,,
Shin may ku,kazo yi ne a,kasar ?
A,a buki mukazo mana kinsan Alhajiji yai aure wancan satin,,,
Waye kuma Alhajiji Zinaro, ta kalli hajiya galala tace kina ko kasan ga mai sharwali
Au tana gyara kafadan riganta,
Tace shugaban yan daudu mana nakasa kinsan yayi aure daga saudiya shine mukazo kawo amarya,,,,,
Hajiya ta girgiza kai cikin daurewan kwakwalwa tace gaskiya ban san shiba.
Tace anya kuwa a garin nan ma kike kuwa ,,,, sarkin yan daudun nakasa zakice baki sani ba ,,,,
Hajiya tace yo nazama kifin rijiya yanzu ai
Bani zuwa ko ina daga wanan runfar sai gida aikin kenan.

Yo kin zo kano kin boye ana can a,nata harka a saudiya
Kai habadai yo aike ma dai kinga a,lama aiko
Eh aiko nagani.
Haba dai don Allah kizo kawai acigaba da harka dake, har wa"yanda basu kai ki ba sun take balle ke.

Haka muka dinga shigowa muna, mata sannu da zuwa ,muna fita .
Ke sharwali duk ke keda wanan harkan haka?
Harka kuma ina? Gasu nan mana,wa yan nan zukazukan yan matan haka ,, yo aike kice min kin take
Kika tafi dasu saudiya ai nabaki watan ni kadan kin take kenan har abada,,,,

A haka bakuwa Zinaro ta dinga zuga hajiya tana cusa mata ra,ayin fita da mu zuwa saudiya bidan kudi


🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 18:54] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣2⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎



Hajiyan mu takasa yin barcin kirki yau,,,, hiransu da hajiya Zinaro ke dawo mata a, rai.
Sai juyi take tayi tana jin muryan zinaro na fadin in kika tafi dasu saudiya aikin take,,,,,,
Nan da nan shedan ya rinjaye ta ,taji kawai zuwa saudiyan take da bukatar yi.
Ta,manta duk wanan baiwar na samu da Allah ubangiji yai mata nasa nan kano.
Kafin asamu mai,sa,ar kasuwa inda ake samun, ciniki irin nata sai an tona.
Allah Allah gari ya waye takeyi , don taje gidan Zinaro .

Kwatancen da Zinaro taimata na masaukin su shi tabi, batasha wani wuya ba wurin gane gidan
Cikin kankani lokaci ta isa dawanau inda gidan da zinaro take a,karshe wani layi.
Gidan ginan jan bulo ne sai kato,kofar baki karfe da ke manne da ginar,,,
Koda hajiya tai sallama wani dan saurayi fari dogo , yazo ya bude mata kofar ta shiga .

Ginan gidan gaskiya ba laifi komai ya hadu daidai da zamani ,,,,,, kujeru ne manya manya sai, kayan kallo dana kida saiti masu kyau.
Ga dinning table agefe guda,,,, sai wata kofa da zata sada ka da kitchen , shima kitchen din ya hadu sosai komai na bukatar zamani akwai a cikin kitchen din.
Wasu samari guda uku tagani acikin falon gidan suna game kowanin su dagashi sai wandon tree quater, da yar singilati.
Sukayi ma hajiya sannu da zuwa ,,,,, guda daga cikin su ya , shiga ciki fada ma zinaro bayan kamar minti biyar yafito.
Yace ance tashigo daga cikin uwar dakin.

Hajiya Zinaro zaune a gaban mirrow tana shafa mai dagani daga wanka tafito.
A ,a mai sharwali kece tafe da safen nan
Hajiya na washe baki tace wlh nice zinaro.
Tun shekaran jiya da kika tafi kin barni da tunane kala kala azuciyata.
Shine nace bari inzo don bansan lokacin da zaki koma ba.
Zinaro ta lakato mai da yatsanta tana shafa ma kafarta tace,,,, "eh gaskiya zan wani dadewa ba zan koma kinsan yanzu ba wani harka sosai a cikin makka kamu sukeyi don haka a jidda ko Riyadh,
Sunta dan jefa hiran wa yanda sukayi zama dasu alokacin da suka fara zuwa aikin TAKARI na farko,,,,
Zinaro na bata lbr ai wasu sun dawo gida wasu kuma suna can wasu kuma sun rasu dadewa.
Cikin samarin dake zaune falo guda ya shigo yana fadin hajiya yau sai mun sayo kayan miya agidan nan don wanda yarage baida yawa kuma sun fara lalacewa.
Tace kadauki ga kudi can kaje ka sayo abinda duk yadace asaya.
Bayan fitar saurayin hajiya tace wa " yanan yaran "yan uwanki ne ko
Dariya sosai hajiya tayi tace yan uwana na,bariki ba ,Da su nazo daga can
Saurayi nane da abokan shi,,, saurayi fa kikace to may ye aciki don nace saurayi nane.
Hajiya takura mata ido har dan wani lokaci tace kai haba Zinaro,,,wa " yanan yan yaran zakice wai samarin ki yo ai wanan, ma mun kusa haihuwar su, Idan ma bariki kike so ai sai ki samu daidai dake amma ba wa yan nan yara ba
Wani irin dariya zinaro ta kyalkyale dashi na shakiyan ci gami da aje roban man da take shafi gefe guda tana rufewa,,
Ta ce lalai mai sharwali baki akasan don ina ganin ma ko a kanon kauye kike. Ai wa yan nan yaran sufi manya dadin sha,ani don su idan kika basu kudi kadan sai su biya maki bukatar ki fiye da yadda kike tsamani,,, kallonta kawai mai sharwali ke yi,,,,,,,,
Ta shashantar da maganar ita dai hajiya duk al,ajabi ya kamata, mamaki takeyi da wanan irin hali na su zinaro,,,
Saida tagama shirin ta tsab suka fito falon inda zinaro ke ma hajiya tayin samarin ko akwai wanda yai

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment