Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai hakan yana da kyau don kinsan cewa fadima ai zaman amana take gare shi kin ga ai dole ya kulata,
Taciki abinci kala kala aplate tamiko min daga inda nake zaune a bakin gado na,
Kawai don tace min ance mata sai naci shiyasa nadan tsakuri abincin kadan,
Nace mata na koshi saidai fruit salad din duk munsha har Amal din,

Nasan cewa yanzu sheriff yana falon shi yana tura sakonne a system din shi,
Duk dare sai yayi wanan aiki in da duk yake
Hakan yabani damar fitowa don in kara bashi hakkuri kamar yadda Amal da maman Umar suka ce min
Dogon rigace ajiki tunda nafito wanka na sauya ta,
Sai plat shoe's ne akafa na shi ma baki mai photo yar kwakwa karama kamar buzubuzu haka,
Ganawa wautar na manta cewa da ba yanzu bane don haka ko mayafi ban dauka ba , tunda naga cewa ai a cikin gida ne kuma sheriff ne fa wanda yasan ni tun ina yar karamana,
A hankali na tako har inda yake zaune saidai ba sakon yake turawa ba shiru yayi yarike gefen habar shi da hannu guda da alamar tunane yake yi,
Jin motsin da yayi a bayan shi yasa yadago a hankali yadubi gurin da yaji motsin,
Sai mukayi idi biyu dashi, amma sai naga kwayar idon shi ya kada yayi ja sosa,
Da sauri batare da tunanen komai ba nace subbahanallah ,
Barci kakeji ne, nasa mu kaina da tambaryan shi,
Shiru nadan wani lokaci bai ansa min ba,
Saidai yadan girgiza min kai kawai,
Ikon Allah saikuma nakara cewa kana ciwon kai naga idon ka ja,
Murmushi yau sherie din yai min da alamar tambayar nawa ya bashi dariya
Yana mai kura min ido shi ja da suka rine yace, min,
Bawa ni ciwon kai illa keda keson ki tarwatsa min kwakawalwata, fadima har ke zaki fita kibar gida tun safe har dare baki dawo ba,
Cikin sauri nakai durkushe a kasa nace mai kayafe min dan Allah insha Allah bazan sake ba,
Da wata dakusarshiyar murya ya ansa min yace gaskiya baki kyauta min ba fadima,
Kaman zan yi kuka nakara cewa ya yi hakuri pls,
Kafin yai wani mafana sai mukaji muryan Aziza abayan mu tana cewa haba dai habibi,
Ai tunda har ta bada hakkuri takamata ka yafe mata hakana pls,
Tazo inda nake tsugune tadan dagoni tace mai haba dai ai koda laifin da tayi yafi haka yakamata kayi hakuri ,,
Kujeran dake gefen shi ta zainar da ni tana mai dan jan shi da hira irin ta masoya duk da na lura bai son ansa mata sai dai yace eh, ki uhum atakaice,
Saidai takan dan jefani cikin hiran nasu jefi jefi,
Hira sukeyi abin su, cikin kwanciyar hankali, a,takure nake a cikin su kamar wace a ka tsure,
Amal ce tafi daukan cup a kitchen tagan ni zaune acimin su,
Daman hanyar gudu nake bida,
Aiko ina ganin ta na mike ina mai yi masu saida safe ,
Aziza ce ke ce min kin gudu ke nan fadima baza ki zauna muyi fira ba ke nan,
Kada ki manta cewa gobe tunda safe nake son mi fita,
Kafin ta kai karshen zancen yatare da fadi ba inda zan fita kuma, tunda nafita yau,
Da mamaki take kallon shi tace mai ai guri. Gyaran kai kawai zamu tafi
Nidai ban san ya suka karasa ba na wuce nabar su, abina,
Washe gari ina son indan motsa jikina sai na fada kitchen wurin masu aiki tare mukai aikin da su
Najera komai a dinning table din falon ,kamar yadda nassba yi da kafin intafi school,
Lokacin da sheriff yadawo gida shida almustapha, direct sashen shi yanufa
Saida yan gyara jikin shi yarage yawan jayan dake jikin nadhi bayan ya watsa ruwa,
Sai yafito ,wurin abinci ya nufa don shi baya cin abin a waje ko ya ya kyau abu yake sai dai wanda aka girka agidan shi,
Don haka da yadawo yai wanka yadan kintsa kafin yai komai sai ya fara cin abinci tukun
Zaune suke da Aziza sai salim da ke tare dasu Amal tunda aziza tazo takaurace ma yawan zama falon sam,
Acewar ta wai aziza batai mata ma,
Wai ruwan yan duniya ke ga aziza,
Don hakane ma bata son irin yadda taga inayi da aziza din,
Cibin farko da yakai bakin shi sai ya tsaya cak ,
Duk wanda ke table din sai ya bishi da kallon mamaki komai yasa ya dakatar da cin abincin ,
Fadima ya furta a hankali Aziza ta ce fadima ya ce na,am sai tadan fara waigawa kozatagan ni afalon,
Ga mamakinta batagan ni saitace mai yafaru da ira,
Cikin murmushi yace mata ya akagi tashi kitchen ai muna girki,
Aziza tace kamar ya don ban fahinta ba sai yace mata, wana girkin nata ne,
Har suka kare cin abincin tana mamakin shi,
Wani irin shakuwane a tsakanin mu haka ace har da girki in nayi zai gane,
Dan murmushi tayi maikama da na mugunta,
Batayarda ba sai da taje kitchen din ta tambaya suka ce mata tabbas nice nayi girkin
Dakina ke ina kokarin jona waya a cikin chaji naci kam shin turan sheriff a dakina ko ban diba din ba shi,
Ya saye da jallabiya mai ruwa assh colour,
A bakin kofar dakin ya tsaya yana karewa dakin kallo kamar yau ya fara shigo,
Tambaya ya jefo min da ga inda nake tsaye,
Ya akayi nai,cooking yau agidan nan,
Cikin mamaki na dan kallo shi nace mai cinkin han kali
Kawai dai nayi ra,ayin yin hakane,
Saida yadan dade tsaye yana min wani irin kallo mai kama da kallon sha,awa, sai nai sauri nadan waiga in ko may yake kallo a jimina hakana,
Hakan da yagani sai yai saiuri ya juya yabar dakin,
Mamaki wanan sauyin na sheriff nake ji saidai gaskiya ban wo komai araina ba,
Sai kawai na shere zan ce,,,naci gaba da aikina
Waje muke kusan duk kn mu gidan muna shan iska ne saboda mudan shakata,

Salim na badminton shida sheriff a gefen can nisa da mu, kadan,
Wayan aziza yai kara dai dai lokacin da Amal ke shirin tashi zuwa cikin gida tadauko drink da ma nice zan tafi sai Amal tace min wai in bari ta,tafi don zata danyi wani abu acimi dama,
Hinduce mai kiran saina dan tashi cikin dabara nabar gurin don kada in takura masu,
Bayan sungaisa take tambayar ta ko tagama plans din datakeyi sai tace mata tana dai gab da gamawa,
Sundanyi hira kadan takashe eayan lokacin da taga Amal tafito daga cikin gida da tuen kayan drinks ,
Amal naganin ta kashe waya tace azuciyar wanan akwai kakar mata ganin da taimin zuwa yasa tajadhe eayan sherin da takeyi,
Fuska a sake take min zancen wai kawar tace bata da lafiya a dubai tana son kafin mu koma indan tafi in rakata indawo
Don yanzu idan tace ita kadai zata sheriff ba zai yarda ba,
Amal ta kalleni don ta ji mai zan ce sai taga na shiru bance komai ba, har muka tashi, dagurin shan iskan,
Adaki kamar Amal zataciyeni danya, saboda bacin ran da tanuna min,
Saida nabari ta gaba,
Cikin ruwan sanyi nace mata,
Amal nidake ba daya muke a gidan nan ba kituna cewa fa niyar aiki ce bai wata shakikiyar maigidan nake ba, kamar ki taimakone kawai Allah yaza mai yai min harkikaga ina zama ahaka daku,,
Shiru tayi tana nazarin magana na nace kin san cewa aziza mata sheriff ce kina ganin cewa zata sani abu ko tasao in mata abu in ce a,a,
Saboda haka kin ga dole in mata biyayya ke kina da damar dazakiyi mata komai don ke yar uwan mijintane,,Sabanin ni
Duk da haka kibi a hankali don wana yar duniya ce sosai,
Koda Aziza ta fada ma sheriff cewa tare zamu tafi, saida yai dan mamakin hakan
Irin shakuwar da yaga mun yi abin na dan bashi mamaki arayuwan shi,

An muna shirin komai na zuwa dubai nida Aziza Amal jitakwyi kamar ta kamani tai min dan karen duka,
Rabona da shiga jirgi tun lokacin da muka shigo kasar saidiya da yan uwa na sai gashi yau kwasan tafiya yakamani,
Hjy hindu wata iri garmakekiyar mace ce ga tsawo ga kiba, muryan ta irin dan shakakken nan ne,
Ana ta kain i gurare ina ta dauka photo kusan duk inda naje,
Saidai guri wani likta da ta, ce min in rakata,,
Likitan indiya ne yanata turanci kusan maganar shi sai naji kamar ai yashe fe ni sosai
Ama da muka fito sai take ce min doctor yace dazata samu yar matashi kama zai san dabar da yayi yataimaka masu
Saikawai tasa min kuka acikin motar wai ita yan inda zata samu wace zata taimaka mata ai mata dashen shi take naima,
Ita bakomai ba sheirriff take tausayi,
Har muka kawo gida ina tunane mai zurfi araina
Nace idan ban yarda bafa watace can za,a dauko ta taimaka watakila ba mai halin kware bace tazo ta haifa ai bala,i,
Tana falon zaune na samay ta zaune a hankali nakira sunan ta nace mata hjy insha Allah ni zan yarda intaimaka maki ai min wanan dashen
Jawoni tayi ajikinta tana murna da magana na da na fada mata harda kukan taba fayce majina
Sai godiya take zaga min wai ta gode da rufin asirin da zan mata,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
6⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,

Saida ta tabbatar da cewa komai ya kanmala ga duk wani shiri da suke aiwatar wa,
Acikin shewa suke ta hiran su tafawa kamar ea yanda akaiwa bushar da gafara,
Saida Hindu tadan kurbi drink din dake gaba tukun sanan ta aje cup din saman table ,
Takalli Aziza wace take kokarin zuba nata drink din a cup ,
Tace mata wlh Aziza ban ta dauka wanan maganar, zai zo muna a cikin sauki haka, ba,,,,
Itama din kurban drink tayi tana lunshe idon ta a hankali,
Saida ta kara kurbawa sanan ta,aje cup din gefe,
Tace hindu Allah kawai yatai make akan wanan yariyan don kinga bawai kwadai bane ko ko ne man guri ,a,a
Hakatake, kwai wai ita sarkin tausayi, da wauta, idan ba tsabar wawanci ba da rashin wayo
Ko a ina ta bajin cewa, an ana dashen ciki idan ya kosa acire amayar inda akeso,
Aikawai dana samu anyi mata wanan dashe gaskiya, ninafi kowa sa,a da murna arayuwana,
Sai kuma idan lokacin da take tsamani, za,a cire mata, cikin zuwa nawa yayi sai kuma in samu sabon dabara in bullo mata da shi ,,
Sukayi wani irin shewa suka taba a tsakanin su, don murna da farin ciki
Taci gaba da cewa kima da zaran ta haihu karbe dana zan yi batare bat lokaci
Nasan cewa kuma dole dai yaro yai bearing din sunan uban shi da nawa,,,
Hindu ta dan gyara zaman ta kadan tace, aina san cewa zaki iya yin koda fiye da hakane, mutumiyar
Tamika mata hannu suka tafa cikin shewa,

Doctor kamal ne zaune a office din shi da cikin asibitin sarki fahad,,,
Asibitin da ke a kan shifidaden titin, khalifas road's
Kujerar dayake sama tana dan juya shi a hankali,
Cikin dariya yake maganar shi a gaskiya Ahmad kana bani mamaki ace mutum ya zauna ya hali irin wanan kamar ba namiji ba
Shiko dai kana tsoron matan kane baka son ransu ya baci kake wanan rufa rufan da baida anfani,
Kadiba fa yau shekara kusan uku kenan da yin wanan auren naka,
In a lokacin kana ganin cewa yarinyar nan she is young yanzu fa da takai mallakin hannakilin ka,.
Sheriff dake kokarin mike wa da ga kujerar da yake zaune
Yake ce ma doctor kamal ni bansan ko may yasa kake yawan damuwa da wanan zancen ba,
Ina son kasan cewa ni ba saboda komai har na yarda a wanan lokacin aka daura wanan auren ba sai kawai don in tsirar da mutunci su daga wulakancin da ake shirin masu,
Saboda hakan kawai zan yi in masu gata su koma gida acikin mutunci,
Hmmm nifa tun wancan lokacin bawai nayarda da manufar ka bane,
Ai ba kai kadaine namiji da zai iya taimakawa ba ko,
Ina ga takaru nan yan uwasu da suke aure saboda kawai su zauna akasar sudan yi yadda suke so indan sun tashi tafiya sukashe auren kowa ya kama gaban sa,
Wasu kuma shikenan har abada su zauna atare,
To ni na fadama cewa don in tallafa wa wanan yarinyar yasa har na amince,
Doctor kamal din shima mike wa yayi daga kan kujera suna fuskantar juna su,
Cikin kashe ido yace ma sheriff Ahmad yan zufa ,
Duk a cikin taimakon ne hakan kamar yadda nagan ku a,wurin taron African youth development found,,
Baiyi mai magana ba har yakai bakin kofar fita office din sanan yadan waigo yana kallon doctor yana gyara kwalar riganshi,
Yace ban san abinda yasa kake sa kan ka ga abin da bai shafeka ba yan zu kamal,
Yabuga kofar daidai lokacin da doctor ke cewa zan zo har gida mu karasa zancen,yafadi yana dariya,,,,
Yana fitowa Yusuf ya bude mai mota ya shiga, suka fara hanya,
Yace ma Yusuf suwuce zuwa gida kawai, saida motar tazaunu a saman titin ne yakai kallon shi ga dogon agogon da yake tsaye a tsakiyar gari,
Wanda duk inda kake cikin garin makka zaka iya hango shi a tsaye,
Sai kuma ya dan lunshe idon shi a hankali gami da yin sanya,yaar ajiyar zuciya,
Tinyar tinyar abin yafara dawo mashi a rai kamar yanzu aka yi zan cen
A lokacin da matsi ya kai matsi ga duk wata takari dake zama a cikin kasar saudiya batare da lasisi ba,
Hjy Lailai ce tare da wani takaru na miji sukayi mai sallama a kofar gidan shi,
Cikin mamaki yake kallon su don yasan cewa baida wani halaka da su to may yakawo su gidan shi,
Bayan sun gaisa ne shiru yadan biyo baya sai shine yake ce masu ko daga ina suke,
Hjy ce ta tayi karfin halin fara magana don daga cikin su,
Ta ce mai sun zo gurin shi naiman taimako akan yaran takarin da ke aiki, agidan shi,
Shiru yayi kadan yana dan sauranta
Tace mai ansa mu wanda yaje yafada yan bagaladi cewa suna nan gidan shi,
Shine sukazo neman taimako akan cewa suna son ya taimaka ya rufa masu asiri don idan aka gane cewa su takari ne da gaskiya za,a iya yi masu mugun wulakanci don hakane ma tazo tare da wanan Alhj tanuna wanda suke tare,
Inda shikuma yadan gyara tsayin shi ya shiga yiwa sheriff bayani yadda abin yake cewa komai zai iya faru dasu,
A ,kakauce yace to may ye mafita aciki sai Alhj yace zaiyi kokari ya samo wanda za,a daura wa aure da mutun gudan su idan yaso koda za,azo sai a nuna wanan takardan kan cewa yan uwar su ne sukazo daga kasar su yin umrah bawai zama sukeyi ba,
Magana dai takai har Alhj na batun dukawa kasa akan sheriff yarufa masu asiri ya yarda akawo wani na miji adaura aure,
Sunbar wurin shi da niyar cewa zasu dawo tare da mijin bizan da zasu dauko ne,
Shine Almustapha yakara yi mai bayanin yadda abin yake sai yaga rashin dacewar hakan ,,,
Sai tunanen shi da na hjy laila yazo daya don hakane ya yarda akan cewa za,a daura mai aure da Fadima saboda yasan cewa yar karamace ni daga cikin mu
In yaso idan yagama shirin yarda zai taimaka ya maida mu gida Nigeria gaba dayan mu sai ya maishe mu,
Saikuma ya hasale min auren shi tunda dama, ba wai da sani na bane,
A massalaci aka daura auren bayan sallah jumma,
cikin din bin al umman musulumi da suka halarci sallah jumma,a na ranan,
Alhj umar mai takari sarkin takarin tsakiya da Shehi mijin mahaifiyar sheriff, sune suka zama uban amarya,
Inda Su doctor kamal su ka tsaya a bangaren ango,
Murmushi yakarayi saboda tuna abinda yafaru bayan dawowar su, daga wurin daurin auren,
Inda abokan shi suka sa shi agaba akan su na son su san kowacece wanan Amaryan,
Sai ce masu yayi su bari idan lokaci yayi na su sani zasu sani,,,
Auren yaba duk wani abokin Ahmad mamaki saboda basu da masaniyar hakan don sun san cewa bai ko zancen aure da su,
Sai mamaki sukeyi ko wace,ce amaryan da basu san labarinta ba,
Kudin sadakin da a kabayar a masallaci Alhj umar sarkin takari ya kawo ma sheriff yace yarike a hannu shi asamu abinda akayi ma amarya na samun karuwa, cigaban ta,
Sai yaba Shehi mijin mahaifiyar shi bayan yai mai bayani duk yadda maganar yake,.
Don adinga juyawa kudin kafin in girma ko in wuce Nigeria,
Saidai shi a lokacin har ga Allah taimakon mu yayi don gudun wulakanci,
Saidaga bayan auren ne aka gane ko waye kewa yan takari wanan sherin wurin hukumomin kasar na saudiya
Inda shima akasamu wasu suka tona mai asiri, akan harkan saida kwayoyi, dayakeyi,,,
Duk da auren na sheriff da fadima yana nan daran.
Sarkin takari yace abar shi saboda gaba zai mata amfani tunda tana cikin kasar har yanzu,,,
Saidai yanzu ne kuma gaskiya, yake dan ji wani abu agamay da fadimar wace ada banda tausayi ba abinda yarinyar ke bashi,,,
A hankali yai ajiyar zuciya don yasan cewa duk wanan abin fadimar bata da labari
Saboda kafin ta dawo yasamu damar daukan nauyin hajiya mai sharwali tare da sauran yaranta zuwa gida Nigeria tare da guzuri mai tsoka wanda zasu iya tallafawa kan su idan sun koma gida Nigeria
Wanan abin yai ma su dadi so sai inda hajiya ta roke shi alfarman rike mata amanan fadima yarinya mai kirki da mutunci,
Saboda tayi dana sanin zuwa yawon takarin da tayi don abin bai amfana ta da komai,
Yanzun haka yazo ganin doctor kamal kam yawan damuwar dake damun shi,
Inda doctor yagano abin dake damun sheriff har ya sako mai zancen auren shi,,,

Jirgin safiya muka biyo zuwa saudiya a,Riyadh muka sauka sai muka karasa garin makka kafin ayi sallah azuhur duk muna cikin garin makkah,
Dakina na wuce don indan huta saidai kuma zuciya na fam yake da zunlumi da tunanen abinda ke gabana,
Gashi kuma maganar siri ne ba bu damar in fada ma wani,
Duk da basan ko ya maganar dashen ciki yake ba nasan cewa abune mai girma,
Saidai inda nake jin saukin al,amarin shine kawai in ance indan yafara girma za,a cire ne amayar mata da abinta a cikin cikin ta
Wanan abin zan yi shine kawai don sheriff din mu mutun mai mutunci da sanin yakamata,
Koma maye ai dolene in sadakar da rayuwa na agare shi don in,taimaka mai kamar yadda shima din yataimaki rayuwa na ta fan,ni daban daban,
Tunda muka dawo daga wanan tafiyan Amal tagane cewa ina cikin damuwa, sosai tunda ba haka tasan nake ba,
Tunda ta tambaye ni nace mata ba komai tun lokacin tasan cewa bazata gane komai ba kawai ido tasa min,,,
Ita ko Aziza ba abinda ya damay sai farinciki kawai takeyi da an,nashuwar ta,
Aziza taima sheriff bayani cewa likitan ta yace nanda dn wani lokaci yanason ta koma tare dashi don zai dan gwada wani fasaha akasu tayadda ciki zai zauna mata,
Cikkn rashin yarda da maganar ta yace Aziza na fada maki cewa bani bukatar wanan plan din naki pls,
Nabarwa Allah al,amari na idan Allah yatashi bani haihuwa basai natafi wata uwar duniya ne ma har inda nake zaibani
Kisani cewa rabon mutun bai wuce shi, idan kikayi imani da tawakkali sai ubangiji maji rokon bawan shine sai ya karba muna addu,an mu,,,
Kuka tasa mai , maitsuma rai yadda yakasa daurewa har yabar mata dakin
Yafito waje,
Ga mamakin shi sai ga alamar innuwar mutun a cikin duhun daren,
A hankali yanufi gurin da ganin kowaye wajen zaune,,, fadima ce zaune cikin wanan duhun ta hada kafa da gwaiwa da alamar akwai abinda ke damun ta,
A hankali ya furta sunan ta cikin mamaki,
Sai na dago kaina nimadai din cikin mamakin may yafito da shi cikin wanan lokacin haka,
Tambaya yawatso min a gagauce, lafiya, may kikeyi haka anan cikin wanan lokacin,
Bakomai na iya furtawa, cikin dan karamin,sautin,
Gefen guda yasamu yadan zauna gab da inda nake,
Yadan kura min ido na dan wani lokaci,,
Can yace fadima har yanzu kina akan tunanen yan uwanki ne da suka tafi, kokuwa da akwai wani abinda ke damun ki ne azuciyan ki,,
Maimakon inyi magana sai kawai nadan girgiza mai kai alamar a,a,.
Kamar mai rada ya ce fadima baki da wanda yafini duk cikin

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment