Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kula da duk wani movement nata,
Ita wanan kawar nata da samu salwa ce ta sa a,hadasu asaudiyan don matar ta iya harka so sai,
Zata dinga samo mata kowani irin abu take bukata ,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story

Duk wani shiri da yakamata muyi mun kammala shi ko zuwan bakin namu kawai muke jira isowar su
Sai misalin magrib suka iso garin kasan cewar ba su sauka da wuri ba,
Mun, masu taro na mutunci yadda yakama ta, mu nu,na namu kulawan gare su so sai,,,
Don duk kusan wanda ke gidan a lokacin mun fito waje don taron su,
Jinda kowa yayi cewa mahaifiyar cikon sheriff ce bata da lafiya za,azo da ita,
Suna fitowa a mota nariga nasan cewa motar da almustapha ke ja itace za,a sata aciki don haka gurin motar na nufa,
Dan jin kadan ba,a bude motar ba, hakan yasa muma mukayi tsatsaye cirko cirko a wajen,
Gaban motar nanufa don inga ko may yasa mustaphan bai bude kofar ba,
Ina zuwa gurin na rike hannu motar kenan sai naga an bude gefen driver,
Maimakon inga mustapha ke jan motar sai naga Sheriff din mune yajawo motar dakanshi,
Jayewa nayi kadan don in bashi wuri ya fito, ina mai sannu da zuwa,
Yana mai ansa kuma hankalin shi naga ya bude gambon kofar motar tabaya da ke ta daidai saitin wurin zaman driver,
Wata yar matace wace bazan iya cewa taikai dadtijiwa ba take kokarin ta,fito daga cikin motar,
Gurin na isa da sauri na don in taimaka mata wanda hakan yai daidai da shima sheriff ya miko hannu shi don ya taimaka mata,
Batare da na damu da inbarshi ya taimaka mata ba nai azamar riko mata kafadar ta ta baya kandan
Sainaji tadan yi wani irin ajiyar zuciya, kadan tare da fadin Alhamdullahi ala kulli halin,
Ina rike da gefen kafadar , ta har zuwa dakin da sheriff yace mu gyara masu,
Wanda yafi dan girma da kayan alatu acikin shi, na nufa da ita
Sai sannu kowa ke mata,
Shiko sheriff tunda yaga nazo kamata sai yabar min ita don yasan cewa zan iya,,
Kuma ganin dayayi a hankali nake takawa da ita yasa hankalin shi ya kwanta,
Amma yana bin mu abaya a hankali shima,
Kujeran dake dakin na zaunar da ita sama a hankali,,
Sai a lokacin da naga ta zauna sanan ido yakai ga sauran abokan tafiyar na su,
Wani dan dattijo ne baki dogo aje dan gemu mai rabi fari da baki yarata wani dan jan kyale a wuyan shi
Dagani koba fada maka ba kasan cewa shiga ce irin ta shehunan mu na Nigeria,
Bayanshi kuma wani matashi shine, baki cikin shigar wandon jeans dawata riga baka anyi rubutu da wani abu kamar gold cikin manya haruffa,
An rubuta we are d leaders of tomorrow,,,,
sai wata yarinya wace zan iya cewa chuculate colour ce ita,
Tasa wani buje da rigar na less, ta sa hijab baki saman kanta, tana rike da jaka, baka again,
Ganin mara lafiyan ta zauna duk suna kanta suna mata sannu yasa ni fita dakin don in gabatar masu da dan abin sha kafin su zo cin abincin su,,
Daidai zan fita yar bakuwar budurwan tace min dan Allah ina son in dan kewaya pls
Saida nadan saurara da kyau nagane hausan nata,
Bayin da ke manne cikin dakin na nuna mata,
Koda nafito daga bayin don in fita zuwa, dauko masu drinks sai na samu,
Sheriff din mu ne, rusune gwaiwa bibiyu, akasa, gefen kan mahaifiyar tashi saitin kanta yana mata magana cikin tausayawa,
Shikuma dattijon ya saman kujera kusa da kafafun ta,
Drinks nakawo musu cikin tire, na aje masu a saman stol
Duk da cikin dare suka iso hakan bai hanani gabatar masu da abincin lafiyyae da muka hada masu
Tun misalin karfe biyar na marance, mukayi masu komai
Har ita mara lafiyan nida kaina na hada mata abincin ta,
Agabanta na hada mata abincin nata, wakene sai ganyen lansir da kore da nadan hada mata dashi naimata shi ruwa ruwa sai kaza danai mata gyara nadaban yadda nasan cewa zata dan iya ci,,
Alhamdullahi do gaskiya ta dan ci abincin sosai
Sunyi mamaki don sunce rabon da taci abinci maidan waya haka yadade,
Natsiyaya mata ruwan Apple da carrot, wanda na markada wuri daya sanan nadan tace mata shi,
Duk iyalin nata nagefe suna kallpn yadda nake fanam dawai niya da ita,
Cikin larabci sheriff yace min in kai wayan sauran dakunan su shi malam zaizauna da mama a wanan dakin ne nasan da toh,
Lokacin shima yafito daga dakin suma bakin ni suka biyo bayan yai masu bayanin cewa zan kaisu dakin cikin harshen Kanuri,,,,,
A falo sukayi kicibis da Nafisat wace dawo wanta ke nan daga wurin da taje,
Idonta yayi jawur kamar garwashi, sai wani dan rausayawa takeyi indan ba ka gane ba zakace she is normal,
Kallon mamaki yake mata don da jiyakeyi bawai ya gaskanta bane,
Don shi mutun ne mai afani da badili ba zahiri ba,
Zuwa tayi ta batun rugumay shi tana fadin habibi ,,
Yaushe ka iso,
Ai baka fada min cewa kana hanya ba,
Yanzunan nadan fita,
Jakar ta na hannuta da ke batun faduwa na karban mata zuwa daki,
Nadan yi saurin ce ma, sheriff din mu,wani daki zan kai wanan bakon saurayin,
Sai nuna min yayi da hannu batare da yayi magana ba,
Yandan bita gefenta yawuce zuwa sama, ranshi a bace,
Dakin da ke kusa da nawa nakai yar budurwan sai saurayin dake can hanayar fita daga falon,gidan,,
Na nu makowan su inda zai dinga yin komai agidan,

Daki ya shiga jikin shi a san yaye saboda tsanan bacin ran da yashiga donganin yadda nafisa ta koma,
Gashi inba idon shi ke mai gizo, ba yaga har rama tayi gashi ta danyi duhu ,ta yi baki ,,
Itace ta shigo dakin nashi cikin irin dauriya nan
na yan kwaya,
Tana fadin ya hanya ya mutanen, takama nuna sama da yatsan ta maganar nata yaki fito wa,
Toilet ya fada yabarta nan tana shirmay ta,
Alwala yadauro daniyar zuwa masallaci
Kwance yasamay ta saman gadon shi tana ta nasarin barcin ta hankalinta kwance,
Tsaki yaja cikin takaici, yafita yabar mata dakin,bata masan inda take ba,

Kafin in kwanta barci danaga shehi a falo tare da sheriff din mu,
Sai na koma wurin,
Ummi, na is,kete kwance tadan dun kule waje guda,
A C dake aiki naje direct nadan rage ma karfi,aiki,
Dago kai tayi tana min godiya,
Tambayar ta nayi ko akwai abinda take so kafin mu kwanta
Duk da tace a,a saida na koma naje na hada mata kayan tea na aje masu adakin sa masu kayan kamshi a dakin sai ruwan wanka da na hada mata,,
sanan nai masu saida safe nafito,
Ina fitowa muka hadu da sheriff a kofan dakin zai shiga shima yai masu saida safe,
Nadan rusunna na gaishe shi, hannu kawai yadan daga min kamar kulun, batare da ya ansa da baki ba,
Yana shiga yaga yadda na kara gyara masu ko ina ga kuma kayan tea da na hada masu saman wani dan stol
Dadi yaji so sai cikin zuciyar shi don baiyi tsan manin hakan ba sam,
Sai gashi yar karama dani nayi abinda yadace ace matar gidan ce tayi shi,
Washe gari sheriff yana dawo daga gurin sallah dakin da su yaghana suke ya nufa ya diba lafiyar ta, Alhamdullahi jikin yadan yi mata sauki sosai,
hakan ya da yagani yasa shi dan kwantar da hankalin shi,
Inda yace masu zai je ya shirya dom su je asibiti da wuri,
Muma,dai Washegari tunda safe muka tashi tunda munsan cewa munada baki agidan hakan yasamu hi samakon yin aiyukan mu,
Koda sheriff ya fito ya iske ko ina nagidan fes har abin karin kumallo mun hada ko,
Batare da bata lokaci ba shima ya ci nashi sama sama don hankali shi wurin kai Ummi asibiti,
Sam ban kawo cew dani za,a asibitin ba ,
Allah yatai make ni muna gama aiki na fada wanka nafito tsaf dani cikin shirgar dogurwar riga yau ja ce ajikina ba baka ba,
Tsaye nake inadan gyara wurin da na gama hada tea a kitchen ina son in kaiwa hajiyar mu,
Muryan mustapha naji yana cewa sheriff yana magana dani a falo,
Koda nafito na iske kusan kowa a tsaye har da yaghana da bata da lafiya,
Tsoro nadan ji don nadauka ko nayi laifi ne, kallo na yayi yana fadin mutafi ko,
Batare da nasan inda zamu ba nagyara dan daurin rolling dim kaina, narufe ko ina inda nasan cewa gashin kaina zai iya fitowa,
Nadan kali mahaifiyar nashi naganta cikin shiga na kamala,
Lafaya tasa duk ta rufe jikinta tsab baka ganin ko ina nata sai tafin kafarta dana hannu,kawai,,
Shima mijin nata yana saye da jallabiya fara kal da alamar yau yafara sata,
Sheriff din mu yadan kali dan saurayin yace mai Salim ka tsaya gida har mu dawo, tukun,,,
Ke kuma Amal da wanan ya nunani da hannu ku kama ummi kuzo muje,,,
Mota muka shiga sheriff da shehi ke gaban motar saini da yaghana da Amal ke bayan motar inda mukasa yaghanar tsakiyar mu,
A hankali yake tukin motar yana yi yana dan waigo mahaifiyar tashi don yaga yanayin ta,
Saida gaskiya ni kallon yana yawan damuna don duk ya waigo kafin ya kai indon shi ga ummi kamar yadda naji yakira yaghana din,
Sai idon mu ya hadu, sainake dan shiga tsarguwa saboda nice a gefen da ge facing din shi,
Dana hakan na yawa sai na maida idona gefen titi ina kallon jama,a daketa wulgawa da shaguno nin da suka cika kowani titi, nagarin makkah,
Sultan Abdulraham specialist hospital muka tsaya bakin get inda muka karbi pass din mu yasa kai ya shige cikin katon haraban asibitin,
Wuri yasa mu ya perker motar Amal ce tadan rikawa ummin hannu aiko tace don Allah ki sake min wanan duk tafiku iya lalabani,
Kallona sheriff yayi yana min magana kadan kadan indan rike ummin a hankali pls, na ansa mai da toh,,,
Har office din da zamu zauna ganin likita nakaita na zaunar da ita,
Ruwa tace muna tana so, don haka da sauri na nafita can wani shago bakin get na siyo muna ruwa roba biyu guda na zam,zam baida sanyi guda kuma mai sanyi na riko muna, shi,
Na iske sheriff tare da ita ina zuwa na balle bakin roban ruwan nayi bissimillah nabata tasha,
Bamuyi wani dadewa ba aka,kiramu kunsan su bakamar kasar Nigeria bace
likitoci ne na kowani fanni birjit sun fi ashirin ako wani fanni aiki ne kawai ba
Shehi da sheriff suka shiga da ummi sai aka bar mu nida Amala, zaune,
A, lokacin Amal tadan kaleni tace mim ita sunan ta Amla,
Saida nadan yi takaitacen murmushi san nan nace mata fadima,
Nakauda fuska na daa gare ta, batare da na kara mata magan ba,
Sundan jima kadan sai gasuvsun fito da ita saman wani dan keken asibiti mai kama dana guragu,
Wani dan matashin balarabe mai karfi yana tura kekenn
Mikewa mukayi tsaye lokaci guda cikin fargaba,
Da larabci sheriff ke min bayanin cewa zaije yadawo don za,akwantar da ummi ne sai an gano ko maye matsalar ta tukun,
Cikin rashin jin dadi maganar muka bi bayan su har zuwa dakin da za,a ajeta,
Dakine lafiyaye mai kyau komai akwai adakin kamar mutun yana gida,
A gaskiya ummi ta sha awo sosai don tun da aka kaita dakin muke ganin likita kala kala
Wanan group din suzo sutafi wasu su zo,,,
Nida sheriff ne masu zirga zirga don wani lokaci kafin yadawo anbada wani test din dole nice zanje in yi kafin yadawo,
Don haka duk mungaji,amma sam ban yarda na nuna cewa nagaji ba,
Abin mamaki har muna batun tafiya gbaigana u labarin matar sheriff a asibitin,
Har Amal ta kai ga tambayar shi ko lafiya bata gan, ta ba,,,
Ce ma Amal yayi bata jin dadi ne,
Sai a wanan lokacin natuna cewa banci komai ba fa yau, cikina ya soma ruri ,.
Ban ko gama wana tunanen ba wana na yai dan tsuwa alamar kira ya shigo min,,
Cikin dan sauri nadauki wayar da na aje gefena ina dan diba lambar,
Nakara wayan akune na ina mai ansa sallama,
Idanuna su kai kan sheriff, yakafe ni da ido da alamar yana son yasan wanene yakira ni awaya,
Jin da yayi ina kwatancen inda dakin da muke yasa shi barin kallo na,

ZEEE MAKAWA24/10/2017, 1:50:11 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,

Allah ya karama Annabi darajja da sahabban sa,,,
Jumma,atu mubarak yan uwa musulumai,,,

Almustaphane tare da bakon saurayin nan mai suna Salim suna dauke da kwandon abinci, da abinsha, a hannayen su,
Nina karbi basket din hannu almustapha, nakai inda zan aje na aje,,,
Ahankali nadawo inda nake tsaye, nadan tsaya muna kallon ledar ruwan da ake kara, wa Ummi,
Almustapha gefen da nake yazo ya tsaya gab dani, ,,,
Shima kallon ruwan da ake kara wa Ummin yake yi cikin tausayawa,
Dan juyowa yayi daidai saitina ya ce min Aisha na can yau tana fitina wai sai ankawo ta gurina,
Murmushi nayi nace mai tunda tazo aibantaba dadewa waje hakaba, batare dani ba
Yace yau kan Yumma tasha rigima sosai
Ina dan murmushi don tuna Aisha da irin rigimar ta,
Ina,dan juyo sai ko muka yi ido hudu da Sheriff din mu,
Dake tsaye daidai saitin inda muke,
Hannu shi cikin aljihu yadan jingina da gina kadan,
Ashe idon shi na inda muke muna magana da mustaphan
Wani irin harara Ya watsa min,
Tare da wani irin mugun kallo na zaki gane kuren ki,
,bansan lokacin da na sada kaina kasa ba,
Don kallon ya firgita ni sosai,
Tunda ni bansan abinda nayi mai ba, yai min wanan kallon na kishi ga hankalin ki, da ni,
Shiko Almustapha sai kara fada min yadda Aisha ke fitinar yakeyi,,,
Duk nadan daga kaina sai mun hada ido dashi daga inda yake tsaye suna magana da shehi,
Ganin da tayi mustaphan ba daina yimin kus,kus din da mukeyi zai yiba saboda bai lura da sheriff din ba da kallon da yake muna,
Don baya yaba ma sheriff din,,,,
Daurewa kawai nakeyi ina yar dariya kasa kasa,
Muryan , sherrif naji gab da mu yana ce min naje muci abinci da Amal a waje
Kafin in yi wani yunkurin tashi wurin saina ji muryan shehi yana cewa kamar ruwan baya tafiya ko,
Da sauri ya juya zuwa inda ummi take kwance don ganin robar kara ruwan
Sai kawai naji duk banjin dadi saina dan shiga halin damuwa,
Saboda ban iya fassara laifin da nayi ake min wanan kalon warning din,,
Abinda ya kawar minda damur dana dan shiga shine,
Farkawan da Ummi tayi daga barcin da takeyi sanadiyar dan taba mata hannu da akayi,
yasa nadan saki jikina da sauri na naje gurin ta ka,fin kowa ya isa ciki
Sauri ina mata sannu da jikinta, Ruwa tace zata sha saina dan daga kaina nakali inda yake ina fada ma sheriff din bukatar ta wanda dama idon shi naga mahaifiyar nashi,
Shima gurin gadon ya iso, yadan duka daidai saitin kan ta yace mata tayi hakkuri, Ruwa ake kara mata tabari indan ruwan ya kare sai abata, tasha ruwan shan,,,
Cikin sanyin gwiwa ya Mike ya na tafiya yana ce min cikin larabci koda ruwan yakare kada in bata ruwan tasha don akwai tests din da za,azo aimata dan anjima kadan,
Barcin ne yakara daukanta mai nauyi duk ina tsaye, akanta sai likitocine keta zuwa da dawo kanta, suna aune aune don su gane ko may ye matsalar ta
Amal tana gefe zaune ita da salim cikin damuwa ganin irin wahalar da mahaifiyar nasu keyi,,,
Muna nan zaune mukaji takon takalma tun daga nisa kwas kwas sai duk hankalin mu yakai ga kofar shigowar don gani ko waye,
A,she Nafisa ce tashigo asibitin da marance lip,,,, cikin shigar wando da riga irin na yan Pakistan, take,
Ta yafa mayafin kayan ta rufe kanta da shi,,,
Tana shigowa ko wani gaisuwar kirki bata yi wa koda shehi datagai dattijo ba cikin mu balle su Amal dake tsaye gefe
Direct wurin gadon da ummi take kwance ta nufa,
Tadan dibata tana tabe baki kamar mai jin wani, bashi ,bashi
Ta dan jin tsaye,muma ba wanda yako kulata,
Ko minti goma batayi ba da zuwa tace zata wuce,,,
Har takai kofa tajuyo tana min tabayar ina habibi cikin turan ci,,,
Da larabci nace mata yana can gurin ansan result din test din da akayi, wa ummi,
Yafuto ni tayi da hannu alamar in kai ta inda yake,
Ba musu na dan gyara na nufi hanyar zuwa lab, da ita,
Dan tafiya mukayi maidan nisa sanan muka isa gurin, da yake,
Zaune yake saman kujerun da aka tanadawa mutane,
Saidai kan shi yana duke, ba wai kalon jama,a yakeyi ba,
Dagani jira yakeyi yaji an kira shi, kawai,
Muryana da yaji cikin lokacin da bai yi tsamani ji, ba yasa shi dagawa da sauri,
Yana dagowa saida idon shi yabani tsoro
Saboda Idon shi yayi jajir kamar wanda yai kuka,
Nikan nasan cewa ma kukan yayi ,don ko dazu dana kai mai wani takarda da aka bamu na iske shi zaune cikin mota shidaya yana kuka,
Ganina dayayi yasa shi yadan wayance, don kada in san cewa kuka yakeyi,,
Tausayi yabani saboda mahaifiya ai ba wasa bace,
Don gani nima kusan kulun da tunane inna nake wace nake ganin kamar ban kara ganin ta a duniyar nan,
Gashi tunda naga makwabcin mu ban kara ganin wani dan garin mu ba,
Balle ma yanzu da ban bara ban talan gumama atiti kida alhazai sun zo balle inga idon sani,,,,

Yana dagowa kan shi yagan mu tare da nafisa aiko sai naga yakara tamke fuskan shi tam
Kamar wanda aka aiko mai da mugun labari,,,
Ita sam bata damu ba sai wani dan kokarin shige mai da take batun yi,,,
Nikan wucewa nayi don nakoma dakin da ummi ke kwance,
Don kada su bidi wani abu ban kusa,

Gida zamu koma don saboda asibiti majinyata basu kwana aciki,saidai mai jiya kawai da nurse's,
Saidai gaskiya shi shehi yace sam bazai koma ba zai tsaya asibitin, tare da ummi ne,,
Saida Sheriff yadan yi shige da fita aka bar shehin ya kwana, agurin nata,

Mu hudu ne a cikin motar a hanyar mu ta komawa gida
Sheriff ke jan motar duk da dare yayi sosai,amma baka gane wa saboda hasken da garin keda shi ko ina,
Zakaga duk hasken fitilo ne ya haske ko ina a garin jama,a kuma basu daukewa har galin Allah yawaye,
A hankali yake jan motar bakajin komai sai sanyin A C kawai dake ta aiki amotar , kirar Jeep baka, wulk,
Murya a raunane yadan juya gefen da salim yake ya na magana, dashi,,,
Yace, yanzu salim kun san cewa ummi batada lafiya kuka barta har ciwo yacita haka ba wanda ya kirani a waya, ya fada min,
Yanzu saboda Allah kunyi min adalci ke nan,
May ye amfanin samun da nayi a,duniya,
Har, da za,ace wai mahafiyata tana dauke da ciwon yunwa ulcer da hawan jini har yai mata mugun kamu, haka ban sani ba,
Amal ce ta katse mai maganar shi tace wlh yayan mu Kada kaga laifin mu
koda mun ce zamu fada ma sai ummi tace batayafe mu fada ma ba,
Wai kada mutayar ma da hankali, tunda kana iya kokarinka akan mu bai kamata mu dinga sama wasu wahala ba hakana,,
Wai zai zama kamar rokon ka muka yi ,
Salim ya karbe zancen da cewa ai ni koda yaushe nikan ce ma ummi sai na fada ma, tunda mutane zasu ga kamar cewa ka kasa kula da lalurar mu ne bawai daga ummin bane,,,
Ya ci gaba da fadin,,
Aiko wanan kiran da Shehi yai ma bada son ranta bane saida yaga ta rikice shine yadaga waya yakiraka,
Tsuki yayi yana mai kada kan shi cikin bacin rai,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment