Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na
Sallama nai wa matar ta waigo a hankali daidai lokacin tana ciniki da wani mutum mai son sayen hijjab agurin ta
Fadimar mama Sharwali,
Tamike tsaye,cikin sauri ta dafe kirjin ta tana dan kokarin waigen bayana kazata ga garan,
Cikin kidima da rudewa take ce min Umar da Aisha fadima suna ina don Allah,
Dama nasan cewa zasu samu taimako daga gurin ku insha Allah ,,,,
Sai kuma ta fashe da kuka, mai tsuma rai, ,,, ganin da nayi tana shirin tara muna mutane,
Yasa ni jawo hannu ta muka nufi, motar da mukazo da ita,
Muna bayan motar nida ita take ce min tunda aka kamata da kwana biyar aka wuce da ita kasar ghana can jirgi ya zube su,
Allah yasa tana da dan kudi ajikin ta shine tasamu tazo gida dashi, katsina,
Tana fadin wanan maganan sai zuciyana tatuno min da Rugaiyya na,
Nace ko tayi sa,a tasamu jirgin yan Nigeria ankaita gida,
Sai natuna cewa koma ina aka kaita insha Allah tana da wada,tacen kudi wanda zasu kaita, gida,,,,
Motar muna tsayawa umar ne yafara taron mu, ya inda flower's suke yana wasa
Tsaye yayi cikin mamamki yana kallon uwar don gani yakeyi kamar idon shi na gizo ne,
Zuwa yayi ya rungumay ta, tam yana cewa ummi ke ce ko kuwa ummi may yasa kika gudu kikabar mu ,
Tun yana surutu yana sambatu, har yagaji yai shiru yana sha shekar kuka,
Aisha kan fafir kin zuwa tayi wurin mahaifiyar nasu ba yadda ban yi da ita ba amma sam taki,
tace ita,sam bata zuwa, gurin uwar,,,,
Saida Sheriff yadawo nagabatar mai da ita tare da yaran nata
Inda nake zaune itama yarinyar anan take zaune duk falon yayi tsit kamar ba, kowa ciki,

Saida yandayi gyaran murya san nan ya fara magana, bayan sallama yai ma Allah godiya da ya nufe mu da ganin wanan ranan, mai albarka da anfani
Saida yai ma kowa dake wurin nasiha so sai mai kashe ma bawa jiki da kara imani a zuciyar mutum,,
Sanan yajuya inda duk muke zaune har ummi da su Yumma da hajiyan mu,
Yafara da tambayar ta yace itace ta haifi yaran kokuwa tace mai itace,
Yace to yanzu zata bar kasa saudiya da su ne ko kuwa zata kara zama acikin kasar ne kaman da,
Amatsayin yar takari, Saida tashere wani gumi da ya keto mata, tunkun sanan ta dan daga kai ta kalleshi,
Hannu bi,biyu ta daga tacewa don Allah yatai make ta ya ce,ci rayuwan su,
Idan tace zata koma bata da kudin jirkin daukar yaran,
Kuma idan taje dasu Nigeria za,ace yaran basu da uba ,
Nasan cewa ganin da naimata ta,tana kuka zai iya sani kukan nima,
Don haka dagawa na tsab rike da hannun Aisha muka shige ciki,
Ina tashi yabi inda nabi da kallo yasan abinda zanje yi ,, watau kuka ke nan,
Yace mata tadaina kuka zai taimaka yaba su sana,ar yi wanda zasu dan samu,
Amma fa su sanda cewa nada wani dan lokaci insha Allah zai taimaka masu kowa ya koma gida,
Kafin yabar kasan, kowan su yayi murna akayi godiya ,
Bayan an watse ummi tadinga samai albarka tana mai godiya,
Ina ciki ina kallon Aisha cikin tausayi don nasan cewa tabbas za,a raba mune da ita ne yau
Shiru shiru ina ciki ina jiran azo ace min in kawo Aisha zasu tafi sai naji shiru,
Jin shirun yai min yawa saina dan gyara mata kwaciyan ta a hankali na fito waje,
A hankali nake saukowa daga step din dagani na kasan banda wani kuzari ajikina,
Shiru naji wurin yayi ba motsin kowa, a wurin cikin mamaki nakarasa saukowa ,
Ganin ba kowa yasa wuce wa dakin ummi,
Don in gani ko may ke faruwa nida nabar falo tab da mutane , dazu sai gashi cikin yan mintina nafito banga kowa ba,,,
Ummi ce kawai adaki daganin ta ta idar da sallah nafila ne don dai lokacin sallah da sauran tsamu
Gefen kujerar dake dakin ta na,dan samu gefen hannun kujerar na zauna,
Inajiran ta shafa addu,an da na samay ta, tanayi,
Ina dan wasa da yatsun hannu na ina lankwasa su,suna ba dan kara wani dawani dan sauti,
Muryam Sheriff ne naji yai sallama dakin, zubur nayi na gyara zamana ,tukun a tsorace nadan waiwaya kofar shigowa dakin na ummi,
Barka da rana, nace mai cikin sanyayan murya,,,
Saida ya dan kalli gefen da nake zaune sai ya kauda kanshi
Wani, irin dan guntun murmushi ya makale, agefen fuskanshi , yace yawa,
Sai Yace min nazo ne in ma ummi ruwan hawayen da nafi kowa iya zubar wa, itama tagani ko,
Sigar da yai maganar sai yasa nadan sake jiki ga tsoratar danakeyi mai
Tun jiya ban son mu hadu dashi,
A hankali yatako yazo ya shiga dakin,,
Ta inda nake zaune dole zai wuce tagabana, yana sanye da farar T shirt an rubuta agaban rigan iam proud to b a Muslim, da jan kala, sai dogon wandon chunus da yasa mai kyau kalar ruwan toka,, Wani farin agogo ya makala na kamfanin D&G wato, Dolece & Gabbana, sai wasu fararen takalma masu daukan ido ruffafu, dasu, amma a kofa yacire takalman,
Yazo tagabana yawuce hancina kamar cikin kwalban turare na nutsa shi,
Don kamshi shikam sheriff Allah yabashi son kamshi sosai don har abin ya bi mai jiki,
Don ko wuri ya zauna yatashi kamshin bai barin wurin,
Danaga ya shigo saina dan mike da niyar in fita waje,
Cikin saurin yace min in zauna abina ba zama zaiyi ba sako ne yazo fada mata,
Kaita dago a hankali tana kalllon shi, saiyake ce mata Abban shi yai mai waya zasu iso nan da gobe insha Allah,
Adduan tadan katse cikin lokaci guda , tace sai in koma wancan gidan naka ke nan ko har subar gari,
Dan murmushi yayi wanda yakara mai kyaun fuska,
Yace koda sunkai su dari ne insha Allah inada inda zan aje su ummi, basai kin bar gidan ki ba,,
Idan baki so su ganki ne ,har su koma babu wanda zai ganki,daga cikin su,,
Tace aishi zannah dan uwa hauwa nane ka ga bazan ce ban kin ganin shi mu gaisa amma sheri irin na hjy mama nake ma gudu,
Saboda gwanace ta kware wurin kulla sheri
Nidai Inajin su nai tsit kamar ruwa ya cine,
Don nauyin da nake ji,
a dakin sai nakoma takure cikin su gashi ina son fita tun farko ya hanani,
Ya ce ummi ki kwantar da hankalin ki don mama a halin yanzu kinfi karfin duk wani sheri da zata iya yi maki yazama tarihi insha Allah
Ummi tace ai inaga halin nasu a jini yake don kusan itama wanan yarinyar ta wurinka ba inda tarage halin Aminar
Saidai kawai muce Allah ya gyara tunda kun riga kun gaurayu da su ko,
Yace amin a sanyaye ya dan satan kallon na inda nake zaune,,
Duk hiran da suke yi shida ummi kaina yana kasa ban daga ba don duk a tsawale nake, cikin su
Saboda ba maganar da za,ayi agabana bane,,,,,
Sai alokacin ma natuna da nafisa don tun wurin cin abincin sallah jiya ban kara ganin ta ba
Dakina na koma batare da na tambayi ummi maganar mahaifiyar su umar ba,
Amal ce ta fado min a raina don nasan cewa zanji komai da yafaru a wurinta, gamay da maman su umar din,,
Tana zaune saman gadon ta duk tai dadaya da kayan ta wai ta fara shirin tafiya makaranta ne, inji ta dariya nai mata nace ai akwai sauran time,
Da sallama na karasa shiga dakin nata, tana duke tana ta faman gyaran takardun ta,
Wani littafi mai hoton wasu ma,aurata nagani a gefen ta sai na jawo nadan fara diban hoton dake jikin bangon
Nace mata gaskiya sunyi kyau sosai wallahi,
Sai tadan,diba tace ai yan uwan mu ne wanan bashir kenan dan yayan ummin mune, ita kuma matar yar uwan su ummi ce ta haifeta,
Cikin littafin na bude na fara karatu, sai naga sunaye ne mutane da lambobin su birjit,
Batare da ta waigo ba Amal ta,ke ce min sunayen abokaina ne da mukayi karatu da su a bauchi,
Ina ta karantawa tana dan yi min bayanin wasu masu mahin manci, daga cikisu,
Har nakai ga wata Khadijat Abdullahi dogon daji,
Zubur na mike don jin sunan dogon dajin dayi,
Nace mata ita tasan dogon dajin ne bata waigo ba tace min a,a ita kawai a school suka hadu da ita Khadijat din amma yar kano ce,
Nace Anty,Amal tace ummm dataji kiran ba na wasa bane sai ta dan waigo ni,
Nace dongon daji fa sunan garin mu ke nan,wata wata kila, ita Khadijat din yar garin muce,
Don Allah ki taimaka min ki buga mata waya muji ko Allah yasa yar garin namu ne, ita din ne,
Nakara cewa don Allah Anty Amal ki taimaka min kikiramin ita,
Batare da ta waigo tace min to naji, amma sai kin kwashe min wa,yan,nan takardun kin mayar,
Babata lokaci natashi na kwashe duk kayan da ra baza saman gadon
Har abinda batace ba saida nayi mata adakin
Ya,mutsa fuska tayi tana fadin, ke nifa Khadijat ba wai muna wani shiri da ita bace,
Ko wanan lanbar ma ina karba ne tana gurin kada taji daban shiyasa nace abata,
Nakara cewa haba Amal tace o Amal ko nace anty Amal,
Tace min in kawo wayana takira ta,
Aikafin takira layin Khadijat din saida takira kusan mutum uku kafin takira tana fada masu cewa tana kasar saudiya,
Saida taga dama don kanta tai dialing din noban khadijat din
Yako shiga amma har wayan ya katse ba a dauka ba,
Kusan kira biyu mukayi ba,a daukan wayan,
Dole muka kyale amma raina a bace,
Washe gari tunda safeg
Ina saye da yar doguwar rigar danayi sallah da ita ajikina ban riga na shiga wanka ba tukun,,,,
kirana aka yi ta intercoms din daki na
Cikin sauri sauri na sauko batare da na canza kaya ba,
Ina zuwa nadinga jin wani iri kugi da huci a saman ,dakuna kamar wani irin halitta ne yashigo muna,
Kusan duk kowa yana tsaye ina zuwa sai nake tambaya ko may ke faruwa haka na ne,
Almustapha ne yace min in shiga dakin matar sheriff ne sautin ke fitowa gashi kuma Sheriff bai gida yatafi wurin judging tunda safe,
Ba bata lokaci na fada dakin, Nafisat ce kwance cikin wani irin hali ga. kwalaben sirup nan kusan kala biyar tayar a kasa gefen gadon ta,
Ina shiga na tallabo ta aiko sai kokarin sakewa takeyi kamar mara rai,
Saketa nayi da sauri na fito dakin nata cikin tashin hannankali,
Nace ma almustafa yasa adauko min zuma da madara da sauri,
Ana kawowa nayi dibara nabude bakinta na tura mata kusan cokali biyu na zuma,
Aiko yana shiga cikin ta tai wani irin yunkurin amai, saida kowa ya watse don sun dauka ko ta shake ni ne,
Sheriff ne tsaye da kayan games ajikin shi yana mamakin ihun da yake ji tun shigowar shi get,
Sai gashi kuma yaga kowa na batun gudu,
Cikin tashin hankali mustapha ke mai bayanin abinda ke faruwa,
Dasauri ya haura sama dakin nata koda ya shigo tana kwance sharbat da ita saman jikina,
Ga wani irin amai da take kwarawa,
Maman su Umar na tsaye daga kofa rike da goran zuma da na madara,
Cikin tashin hankali yake kallon ta yana tambayar may yasa may ta haka,
Ban kai ga bashi ansaba idon shi ya kai ga kwalaben kayan mayen da ke zube kasa gefen gadon ta,
Cikim tashin hankali ya fidda idon shi waje don mamakin
Wani aman ta kara zubowa mai wari,
Sainace wa maman Umar ta miko min goran madaran da ke hannu ta shima cikin hikima na dura mata shi Allah ya ban sa a,a ta sha sosai,
Sai wani irin amai ya zubu mata, sai kawai jikin ta ya sake ta
Duk sheriff ya rude yama rasa may zaiyi,
Ganin da yayi mata haka yasa yace mu kamota muje asibiti,
Nace mai idan mun kaita asibiti haka za,a tuhumay ka sosai kai ma,
Yagane may nake nufi shi yasa shi yin shiru don hukumar kasan saudiya indan sun fara binciken lamari sai sun gano harda abin da ba suyi niya bincike ba sai sun gano shi, ga mutum
Nafada mai cewa zata samu sauki sosai,insha Allah idan ta farfado saboda naga irin haka a makwabciyar gidan su hajiya laila ,
Dakin na gyara mata tasa sai abin kamshin daki da nasa don dakin ya rage warin da yakeyi,
Abinci naje kitchen nadafa mata maidan nauyi saboda nassn cewa tana fafadowa zata bidi abinci ne taci,
Sheriff duk mamakin wanan yarinyar ya kama shi ,, yace,kai yarinya karama da shegen wayo da dabara haka,
Ummi tashiga cikin wani irim yanayi na,damuwa,
Tayaya har Alhji zanna ya bari danshi ta auri wanan yarinyar da bata da tarbiya ko kadan,
Ita dai tasan cewa duk da Alhj zanna mutun ne shiru shiru,
To amma bai yadda da aikin assha a gidan shi
To ta yaya zai ma Ahamad wanan hadin haka,,
Sai misalin karfe ukun rana nafisat ta farka daga barci tana mai dan bude idon ta da yai mata nauyi sosai,
A hankali ta bude su gabadaya idon ta ya sauka kaina ina tsaye gefe guda,
Ina kallon ta,ta kara lunshi idon nata tayi kamar zata tasahi amma ta kasa, yun komai,,,,
Matsowa nayi kusa da ita ina mata sannu,
Ta yunkura ta tshi saikawai taji ai bata iyawa sam
Nagane nufin ta sai naje kusa da ita nadan tallafa ta ta bayan ta sai tayi kokarin hanani amma ganin da tayi bafa zata iya ba
Saita hakkuri da intaimaka mata din,
Saina kara riko saita dan dago daga kwance, nataimaka mata muka sa,uko daga saman gadon
Munkai tsakar dakJain's ga sheriff fuskan shi murtuk kamar bai taba yin dariya ba
Wani wa,wan kallo yai muna, nikan sai na noke kaina
Da taimako na nasamu taci abinci sosai tako shi,
Ganin da nayi sheriff yadawo dakin yasa ni fita waje
Sai a lokacin nasamu nadan gyara jikina tsab nafito shar dani,
Noban wayan yar dogon daji ya fado min a rai na tashi nadauki waya zuwa dakin Amal
Ina shiga tace min gaskiya fadima bansan cewa baki da zuciya ba sai yau wlh,
Nagane nufin, ta don haka, Kafin taci gaba sai nace mata kowa yataimaki wani Allah na taimakon shi, saboda Allah nayi saboda kuma Sheriff wanda hakan ba karamin rufin asirin shi bane
Cikin jin haushina takara kiran labar wayan amma sai bai shiga ba,
Haka na hakkura nakoma dakin nafisa nasamu ta kara yin barci
Dakina nadawo daniyar indan kwanta kafin anjima kadan
Barci mai nauyi yadauke ni sai gab da sallah magrib na farka
Nayi barcin kusan awa hudu,
Sallah nagabatar cikin sauri, sai nayo waje domin yuwa nake ji banci komai tunda safe dana danci kwai kadan ,,,
Saboda ina fara ci natuna da aman da nafisat tayi sai na kasa ci,
Ina fitowa falo saiko mukayi arba da hjy tsohuwa da Abba, sai
Da ihu naje nafada mata ajikin ta ina murna na manta da duk wa yanda ke falon zaune
Saida na natsu san nan naga wayanda suke tare, cikin ladabi nagaida kowan su nai masu sannu da zuwa
Abinci naga batar masu sai kuma masaukin da aka kai kowan su,
Fafir hajiya tsohuwa tace ita sai dakin ummi zata sauka ko kuma na Amal,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎




✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎🎁NASIBI WRITERS associations
🎁
🎁N🎁W🎁W

Almost true life story,,,

Washegari natashi tunda safe na hada masu break fast, yadda yaka mata tare da taimakon su yumma,
Saida kowa ya kamala,break din ya sanan aka dawo falo aka zau zauna,
Ina tsaye ina hada kayan da suka gama cin abinci da su sai naji Allah Alhaji lawa zanna yana cewa a kamalo mai kowa da yakamata a kira mai agidan,
Falon yai tsit kowa na jiran ana sauraren abinda za a ce masu,
Wani takarada Abban yafitar daga cikin aljihun jallabiyar shi,
Sai da,ya fara bude taro da addu,a tukun sannan ya, kallo kowa dake falon,
Hjy tsohuwa tana zaune kusa da ummi,
Salim da Amal su gefe guda suma zaune,
Sai Sheriff da nafisat dake zaune kusan wuri guda
Duk da ba karfin jikinta take ji ba daurewa kawai tayi tadan fito tana yatsinar fuska,

Alhaji zanna yace ubana mun zo ne wannan kasar don mu tatance wani takarda sako da aka tura wa hajiya acinkin kayan da aka kai mata sako daga nan,
Sai lokacin Sheriff ya dan daga kanshi yadan kali Abban da ke magana ,mamaki yakeyi don bai san kowa yaba da sako zuwa wurin hjy ba,
Jin falon yai shiru yasa Abban yace ma hajiya tsohuwa ,
Hajiya wane ya aika maki da sako,
Sai tace wanan yariyar mai kula da ku, tana dan waige ,waige ko zata gan ni,
Cikin mamaki sherrif yace fadima
Ta kware itace,
Ta aiko min da sakon wani magani dana taba saye na ciwon kafa da kuma na idanu,
Acikin sakon ta jefa wanan takardan
Ta nuna takardan da bakin ta daidai inda Abba ya aje takardan
Sheriff yace mai takarda ya kumsa Abba,
Sai Abban yace yanzu kuwa zaka ji,
Don inba zuwa nayi da hjy taga lafiyan ka kuma taji zancen daga bakin ka,ba ,ba,zata taba yarda cewa lafiya kake ba,
Saboda Abba yasan cewa kazafi akai wa nafisa a takarda don ba halinta ba ne
Asani shi diyan Aminin shi suna da tarbiya sosai,
Salim akasa yaje yakirani,
Lokacin ina nagama wanka ina gyara jikina kafin hjy tsohuwa tafito inda sukeyin mitin,
A cikin sauri da kuma shakku na isa falon gidan
Inda suke zazaune ana jiran in, iso,
Gefen kujera nasamu nadan labe cikin ladabi nakara gaida su,
Alh zanna ya kalle ni azuciyar shi yace kai mutun abin tsoro ne,
Ji wannan yariyar da ko yaushe nake ganin kirkin ta wai itace yau take wanan kullin sherin don kawai ta raba ma yara hannkula, su,
Ina gama gaishe su sai Abba yace min fadima "nace na,am Abba
Yace, ke ,ce kika aikawa hjy da sako nace eh yace harda takarda aciki
sai nayi dan shiru ina tunane. takardan may ke nan kuma,
Yace ke ce sai nace eh cikin rudewa,
Abba yace Alhamdullahi,
Yace Ahmad wani irin zama kakeyi da matar ka har yakai wanan yariyar taima hjy sako akan azo a ceci rayuwan ka kafin , nafisa ta halaka ka,
Zubur na mike ina nuna kai na nace la,la,la haram, haram bani bace,
Bantaba rubuta wasika ga kowaba zuwa Nigeria,
Tsawa Abban yadan daka min, yace bayan mun tambaye ki kin ce muna kece ki, aika,
Ina kuka wi,wi, ina sharban majina,
A hankali sheriff yadan daga yakalle ni cikin tausayi,
Saboda yasan cewa koda nice ma din ai ba karya nayi ba saidai kassh,
May yasa fadiman tai mai haka, saboda yasan cewa ko shi yakai karan nafisa gurin Abba abinda zai faru ke nan
Abba baison ace ga laifin ta sam,
Shiyasa yake hakkuri da komai taimai ,
Saidai fa gefe guda na zuciyar shi tana ce mai bani ce nayi wasikan ba , akwai dai, gaskiya,
Nafisa ce cikin karfin hali tana magana tace Abba bansan ko mai nayi wa wanan yariyar ba,
Ta hana ni shakat agidan mijina,
Idan nai magana yace min ita din amana take gareshi,
Hjy tsohuwa tace ke rufe muna baki zuriar yan sheri aiba don Allah kuka mamaye min jini na ba,
Ta Allah ba taku ba,
Abba na jin hajiyan shi sai yadan yi murmushi don yasan cewa bakin jinin Amina ce yashafi duk danginta,
Jin kukan danakeyi yai yawa yasa sherrif dinmu yin maga a wurin,
Yace, Abba ina takardan Abba yadauko takardan ya nuna mai yace gashi nan, daga nesa inda yake zaune,
Yace bani son kaga abinda aka rubuta don sheri ba kyau,
Saboda ni nasan cewa ko yaushe ne ma waya kana fada min lafiya lau kuke da matar ka,
Tashi yayi har inda Abba yake yace rubutun zan gani kawai bawai zan karanta bane,
Dan dagowa da takardan yai mai kadan,
Da sauri ya waiga gefen da Salim da Amal ke zaune yace cikin ku wake da wanan handwriting din,
Salim yadan waiga gefen da Amal take zaune yana dan kallonta cikin mamaki,
Yace

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment