Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata taja guda
Ai barikin nawa baikai can ba Zinaro inji hajiya
Taufa ashe har yanzu da sauranki maisharwali. Don ko kinga su nan ba karamin riba naci dasu ba zuwan mu wanan bukin,,,,,,


Zama akayi sosai da hajiya da zinaro taba hajiya shawarwarin abin da yakamata a,yi saboda tafiyar su saudiya.
Komai an,kan,mala game da tafiya duk wani hanya da za,a bi an yi,,,
Hajiya taba da kudade masu yawa saboda komai yatafi daidai
Aiko kafin hajiya zinaro tabar kasan komai ya zama daidai,,,,,,,,,

Lokacin tafiya kawai za,ajira yayi abar kasan zuwa sabuwar duniya

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 19:02] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣3⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Ina duk masoya novel dina fatan alheri , nagode kware da kulawan ku yan uwa

Anty Mariya SB Allah ya baki lfy



Tunda hajiya ta dawo daga gidan zinaro mukaga canji sosai a wurin ta, Sai fa,ra,a takeyi da kowa
Mudai namu idanu kawai tunda babu daman mu tambaye ta,,,,,,,
Ai yukan mu kawai mukeyi kamar yadda ya kamata ,,,,, saidai mun ga hajiya kamar tana cinikin gidanta da shagon ta dawasu...

Mukan ba matsalar mu bace iyaka naji Sukaina yar sa ido na fadin kila hajiya zata maidamu gidajen mu don tana gani zata koma makkah da zama ne.
Jin haka yasa na fara murnan zan koma gida very soon,
Zanje inga hafsat dina da dattijo dan kani na ,,,,, har nace sai in saya masu bread da lemo in kai masu ,,,, haka nadinga sake sake a zuciyata,,,

Wasu mutane sukazo su biyu wurin hajiyan mu sun dade da ita cikin shago,,,,,
Hajiya takira Yumma tace taje tafada muna kowa ya gyara jikin shi da,kyau za ,a dauki photo ne. Aiko muka shiga murna za muyi photo.
Ta,ba mu, wasu kaya masu kyau doga yen riguna tace kowa yasa,a photo dashi,
muna ta murna zamuyi photo ban kwana da juna tunda ance hajiya zata bar kasa ne.
Sam bamu kawo cewa damu za,a tafi ba,,,,,

Bayan mai photo yadauke mu ya wuce da kwana biyu hajiya ta turo wata mace tazo tai muna kitso da kunshi masu kyau
Munata murna muka fito shar da mu kamar wasu yan birni,,,,
Tundaga ranan da akai muna kitso bamu kara zuwa shago ba kuma ,,,,,
Kayan dadi muke ci a gida babu wani tsangwama da ake muna yanzu,,,,

Bayan kaman kwana hudu tsakani cikin dare muna hira a falon gidan mu
Sai hajiya ta fito ta zauna a gefen mu duk mukayi shiru,,,,
Waya take yi alokacin amma saboda ladabi sai duk mukayi tsit wurin.
Tana gama wayan takai dibanta gare mu ,,,,,,, lokacin tai wani dan gyaran murya sai duk muka kara maida hankalin mu gareta.

Tace duk ina son ku bani hankalin nan ku saurare ni da kyau ,
Mukayi shiru cikin ladabi, tafara magana,
Tace dukan ku, ku ,biyar, zamu bar kasan nan zuwa kasar makka gobe da asuba insha Allah
Nasaida gida na da wasu yan abubuwa nawa, saboda tafiyar mu,,, nasan cewa baza mu dade ba shiyasa ban fada ma kowa cikin yan uwan kuba saboda dazaran angama aikin hajji zamu dawo nan kano muci gaba da sana,ar mu,,,,,,
Naga ,su Sukaina duk suna ta,murna sai Antyna Rugaiya ce naga bata wani murna sosai kamar sauran.
Naga kowa ya shiga hada kayan shi,,, sai hajiya ta shigo dakin na mu da kanta,,,,,, Tace muna ba wasu kaya masu yawa zaku dauka ba kada ya wuce kala biyu kubar sauran idan mun dawo sai kuyi amfani dashi,,,,,
A , haka muka dan tsinci dan abinda muke so mukabar saura da niyar in mun,dawo mu kwashi abin mu zuwa gida,,,,,,,

Tunda asuba masu adaidaita suka zo suka kwashe mu zuwa filin jirgi
Hajiyar mu ce da wasu suke ta zirga zirga a wurin mudai muna gefe guda, muna jiran ,,, Yadda za,ayi damu
Barci nake ji inna hamma Rugaiyya ta ce in kwanta ajikinta kafin , hajiya mu,tazo daukan mu,,,
Ina cikin barci naji ana tashins natashi firgigit dani naga an bamu wasu kumshi kaya ance kowa ga nashi ,,,
Wai goro ne a ciki dasu kayan miya irin namu na nan kasar ,,, wasu kuma wai turamay zani ne a cikin kunshin da sukayan amfanin mata,,,

Barcin da bankara yi ba ke nan duk inda zamu don a auna mun je an muna komai da ya kamata ,,,,, Kuma cikin ikon Allah kowan mu ta samu tafiya saboda an hada mu da wasu mutane can da ban waidasu zamu.

Allah mai ikon shi yau ni FATIMA Mohammed Sani ,ce acikin jirgin sama zuwa makka ,,, wai a sanadin yar ga aiki yau kuma suna zai koma TAKARI,,,,,,,,



🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:06] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎



Yan uwa musulumai na, duniya ina muna murna da sallah Allah ya kara ma musulunci daraja da dauka
Allah ya rupa ma kowa asiri Ubangiji kataimaki dukkan al,umman musulmai ameen👏👏





(Dogon Daji)


A gaskiya kamar yadda mai gari yayi alkawarin cewa zai taima ,haka din ne kuwa don ya taimaka sosai wlh wurin neman Gajiye,,,
Yakuma fadi a masallacin jumma,a ataimaka ayiwa fadima addu,an Allah yadawo muna da ita lfy,

Aiko mutanen kauyen mu su kasa Gajiye gaba da tsina da Allah waddai da ita.
Wasu sukace ai tayima inna maganine kafin tadaukeni wasukuma suna fadin ai kwadai ne yakai inna badani ,,,, wani gefen kuma sunce ai anfada masu an,sayar dani ne wurin yan yankan kai don Gajiye har tayi arziki a birni ko.

Wanan maganganu sune suke kara tayar ma inna da hankali sosai ,,,, duk tabi ta ramay bata cikin hayacinta so sai yanzu,,
Yayana hafsat ma da ta,fita sai ta dawo gida da kukan ta,saboda gorin da ake mata acikin gari.
Inna kullun tana kai kukanta ga Allah ,, Allah ya tsare mata fadima,tar
duk inda take,,, tana kuma tuba da cin amanan mareniya da tayi

Ana cikin haka kawai saiga Gajiye wani mutumin kauyen mu ya gani a Abuja a kasuwan wuse,,,,,,,,
Bata ganshiba yayi ta binta har yaga gidan da take ya tambaya ko nan take akace mashi eh lalai a nan take zaune tana haya,,,
Ya aika gida cewa yaga Gajiye har ma gidan da take zaune ya bincika anfada mashi,,,
Cikin kwana biyu mutanen dogon daji suka zo wurin wanan mutumin

Da taimakon jami,an tsaro aka kamata ,,, tana ta fada tana fadin ita mai tayi daza,a zo har nan inda take zaune ai mata cin zarafi irin haka suka ce ai kawai tazo gida mai gari ne ke bidan ta.
Koda aka isa dogon daji da ita tana wani,wuri wuri da ido har aka kira inna yar kulu tazo kofar maigari,,,,,,

Maigari yayi gyaran murya ya bude taro da addua , da kuma yima mutanen shi ,nasiha na su ji tsoron Allah aduk lamarin su na duniya,,,,, su sa Allah agaba saboda zafin ne ma baya kawo samu,,,,,,

Bayan dogon jawabin mai gari yayi ,,,,, Sai duk jikin Gajiye yai sanyi.
Gaba daya an daureta da jijiyoyin jikin ta,,,,, Ko magana ta kasa yi sai gyara zama take yi.
Duk da sanyi da a,keyi ita zufa take yi kawai. Kafin mai gari yayi bayanin shi sai tace,,, A gaskiya mai gari nasan na cuci yar kulu,
Nai mata wayo na dauki yar diyar ta da sunan zuwa ganin gida wurina.
Gaskiyan al,amarin dai shine nakai yariyar kano wurin aiki ne ba wai sayar da ita nayi ba.
Wurin wata amiyata na,kaita ai,katau, a kano.
Kuma gaskiya anbani kudin aikinta na shekara na,cinye saboda hakane ma yasa ban dawo gida ba don gudun kada mu hadu da yar kulu .
Ta nakai nan duk sai wurin yadauki salati,,,,,,
Wasu ,suna tama Gajiye tir da Allah waddai da halin kwadai irin nata.
Saida mai gari yayi da gaske yasamu wurin yai shiru,,,,,,,,,
Aka natsu maigari yace ko Gajiye zata kai su malam sale da wasu mutum biyu inda Fadima take su dauko ta tace "eh zatakai su insha Allah
Saida gaskiya bata da kudin da zata biya hajiya mai,sharwali,
Maigari yace kada ta da,mu, shi,zai biya hajiya kudinta,,,,
Aka shirya yadda tafiyan zai kasance idan an,tashi.
Daga karshe Gajiye ta roki gafara inna yar kulu tana hawaye, tana rokon gafara,,,,,

Maigari ya hada masu tafiya zuwa kano wajen dauko fadima,,,
Tun karfe shidda na safe suka bar garin dogon daji zuwa kano,,,,,,,
Sun isa kano da karfe biyun rana ,,,,, saida sukaje sukaci abinci tukun kafin su wuce shagon hajiya,,,,,,
Koda sukaje shagon hajiya sai Gajiye taga wurin duk ya canza mata ,,,
Ta,isa wurin wata mace fara kakaura da tagani tana gyara wuta tai mata sallama
Matar ta ansa mata cikin hausanta da ala,mar harshen yare,,,,
Bayan sun , gaisa da matar, take tambayar hajiya mai,sharwali, mai wanan shagon
Sai matar tace gaskiya bata santa ba ma don ita sayen shagon tayi wurin dillalai,.
Aiko Gajiye ta daura hannu akai tafara kurma ihu tana fadin ta shiga uku ita Gajiye haihuwar mutum biyu ,,,,,
Ina mai sharwali ta, tafi da diyar mutane,,, ita dai wanan matar tace wlh bata sani ba don ita daga lagos tazo kano ta sai shago ita yar ghanace,,,,,
Gajiye sai ihu take kurmawa mutane nata kallonta ,,,,,,, a, haka mutane suka taru aka zagaye su don jin ba,asi.


Wakilin sarki yace aidama munsan karya kikeyi mutumiyar banza kawai kinzo ki sayar da yarinya kin gudu ki ce wai anan kika kawo ta,,,, Gajiye sai sharban kuka takeyi tana bidan agaji

Ana cikin haka saiga wani dan tsoho yazo yatambayi ba,asin abin da yafaru akagayamai komai yai shiru nawani dan lokaci.

Can yace gaskiya indai matar da yasani ne tana saida abinci a wanan shagon tasai da shago ta wuce saudiya dayaranta duka.
Yau kusan kwana uku ke,nan da tafiyanta. Kuma shago da gidan ta dashi akayi ciki su duk ta sayar tabar kasan,,,,,,,,,,,,,



🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:11] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDIRS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Hafsat Yusuf
MSS ILLYAS
Nerbilar
Mariya SB
Fatima Garba
Ina maku godiyan kulawa da ni da kuke na gode fatan alheri gare ku ko yaushe,,,,,,,,,

Almost true life story




(Labarin Fadima Takari)


Mun isa filin jirgin jidda lfy , muka bi layin bincike akai muna screening na shiga kasar da niyar zamu yi sati biyu muna ibada,,,,,,
Muna fitowa wajen sai, ga hajiya zinaro tare da wani bakin mutum sun zo daukar .
Tun a mota aka fara hiran harka zai yi kyau tunda babu wanda yasamu matsala daga cikin mu,,,,,,

Wani gida aka kai mu mukan sai kallo mukeyi munga larabawa da kuma yanayjn kasar tasu
Mundan zauna baifi minti goma ba aka dan bamu abinci bawai don mun koshi ba,,,,,, Rugaiyya ce tace min in,tashi muyi ramuwar sallah da bamuyi ba,,,,,

Muna cikin sallah sai ga hajiya Zinaro da wani sun shigo suna fadi, oya oya kowa takawo bizan ta za,a aje mata kafin mu koma don kada ya bace a hannu mu,
Jiki na rawa muka mika ma hajiya zinaro,,, sai kawai ta dawo ta gaban mu tace,,,,,
Ina son kowa ya saurare ni da kyau, tanu muna biza din tace kunga wanan , mukace eh tace to idan ba dashi ba bu batun komawa gida Nigeria sam,,,,
Saboda haka mun karbe na kowa cen ku ne sai kowan ku ya kawo muna kudin da muka biya masa aka hada wanan biza din kuma ya ba da ribi a sama,,,,,
Sanan zamu ba mutum abinshi ya koma gida ,,,,,,

Wani irin ihu naji Yumma tayi cikin kuka tana fadin don Allah hajiya kuyi hakuri ku maida mu gida don Allah kada ku bar mu anan
Ke rupe muna baki kinji inji katon mutumin da suke tare da Zinaro yace ma Yumma,,,,,,
Sauran ma kuka naga suna yi nidai ina tsaye ina kallon su ido wuri, wuri dani

Daga nan aka kwashe mu lokacin dare ya fara zuwa wani wuri madan nisa saman wani dutse gidan yake dan karami daganin ginan kasan na da ne,,,, kuma na tallakawa ne ,,,, muna fita motan hajiya Zinaro ta karbi kayan su goron da muka zo da shi tace ma hajiya sai ta dawo zataji yadda za,ayi,,,,,,,,,

Tunda hajiya Zinaro ta aje mu bata leko mu ba , ga yunwa ga matsi ya ishe mu,,,,,,
Hajiyan mu ta dan shiga damuwa rashin ganin dawo wan Zinaro,
Wacce ta tafi da dan kudin da hajiya ta kulla zamu je mu ja jari da shi,,,,
Wata makwabciyar gidan da muke Laila yar katsina itace ta dan tai maka muna da abin da zamu ci,,,,,,
Data,ga la,lai zinaro ba zata dawo ba kuma da alama ta yaudari hajiyan mu ne,,,,,, Sai hajiya Lai,la bata nuna ma hajiya ai yaudaran ta akayi ba sai ta ba hajiya shawaran mai zai hana mu fara bidan kudi tunda muna da yawa ,,,,,,,
Shawaran matar hajiyan mu ta dauka,,, mata ita taima hajiya hanyoyi kakala don mu fara sana,a a jidda,,,,,

Aiki aka samo muna a gida jen larabawa don mu samu abin kula da kan mu,,,,
Gidan wasu turawa nasamu aka kaini inda zan dinga kula ma matar da yaron ta na goye gaskiya na ji dadin aiki a gidan saboda da turanci muke magana
Ita kuma antyna Rugaiyya goge goge a ka samo mata a wani ma,aikata,,,,, saidai Hajiya Laila tace aikin ba mai dadewa bane zamu bari mu koma Riyahd ne,,, saboda can anfi samun kudi,,,,,

Uwar dakina Rita ba laifi gaskiya iyakata daukan yaro in,dan mashi wasa sai ku ma da dare indan nane dinshi ta tafi gida ne nake aikin
Amma ina samun kulawa sosai daga wurin Ritan,,,,,
Ina yarinta sosai alokacin don haka ban damu da komai na duniya ba,,,,,
A lokacin da zamu fara aiki an muna huduba cewa ba ga albashi kawai zamu dogara ba,,,, zamu dan rika hadawa da , dabara samun kudi bawai muce sai abinda aka bamu ba,,,,,

Yan uwana kowa na na,shi aikin daidai sun fara sabawa da aikin bidan kudi,,,,
Ranan lahadi da mutanen gidan mu zasu je wurin ibadan su sai suka sauke ni gida wurin hajiya kafin su dawo,,,,
Nasamu hajiyan mu bata jin dadin jikinta dan abinda aka bani in kawo mata ,,,,,,,, Da kyat ta iya dagawa donta gani ko may ye acikin katon ledar da nashigo dashi,,,,
Duk hajiya sai naga tabani tausayi sosai ,,, amai tafara yi can kuma sai gudawa,,,,,
Nakama ta na kaita ban daki na gyara mata jiki,,, tea mai kauri na hada mata daga cikin kayan tea da aka bani inzo dashi daga gidan aikina,,,
Hajiya bata dade da kwantawa ba sai barci yadauke ta,,,
Natashi nadan gyara mata dan tsukaken dakin namu,,,, daidai naga ma gyara Rugaiyya tadawo daga wurin aikinta,,,
Munyi murnan ganin junan mu sosai da Rugaiyya ta rungumay ni tana hawaye,,,
Sai nasa hannu na nashare mata nace kai anty kibar kuka mana ,,, tace Fadima aidole inyi kuka tunda bansan ranan da zamu bar wanan kasar zuwa gida ba,,, nace mata ai babu komai
Mundan jima muna hira tana tanbayana lbr inda nake aiki daku ma yadda nake zama dasu,,,,,
Tace fadima don Allah duk ritsi kada ki yarda ki zubar da mutum cinki na diya mace,,,,,, ki kama darajan kanki don Allah
har zuwa lokacin da Allah zai kawo muna mafita nace to,,,,,
Iyayen gida na suka dawo suka,zo suka daukeni muka koma gida,,,

Kamar yadda akace aikin wata biyu zuwa uku zamuyi haka din ne kuwa
Saidai ni abin yayi min daidai don dai uwayen dakina ma sungama contract din su zasu koma garin su,,,,
Kayan afani masu yawa nasamu wurin su
Nakawo ma hajiya ta sayar muka hada yan kudin mu muka kulla sai birnin Riyadh,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:15] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣6⃣
BY


🐎ZAINAB IDIRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Muna godiya ga ubangijib mu sarki Allah da ya nuna muna wanan lokaci mai albarka , Allah ya bamu damana mai albarka ,,,,,,,,
Jinjina gareku yan huguma group , musan man Anty hasfsat yusuf da anty mariya sb sai mai group din safiya Abdullahi huguma ,,,

Almost true life story,,,,,,,



GARIN RIYADH


Garine mai cike da jama,a kala kala ,,, saboda kasan cewar garin itace babban birnin kasar saudiya,,,,,,
Bamu sha wani wahala ba sam wajen samun aiki gaskiya,,,, da taimakon hjy laila muka samu wuraren ai yukan mu still wani gidan raino aka kara kai,ni.
Wanan karon wani katon gida aka kaini mai kyau ga shuke shuke iri iri a gidan . Muna shiga gidan naga tunda nake bantaba ganin gida irin wanan ba. Cikin gidan wani swimming pool ne,ga ruwa yana ga ruwa yana bulbulowa ta cikin wasu duwatsu,suna ba wa grass carpet ruwa da fulawowi , Abin takar a film nake kallo ba ido biyu ba ,don dai ni bantaba ganin irin haka ba arayuwa ta,,,,,,,
Ina ta murna a rayuwata zan ji dadi ashe ba gidan da muke nupin zuwa bane muka shiga,,,,,
Bayan hjy tayi sallama wani dan matashi mutum yafito ,,,,,
Cikin harshen larabci yake tambayam mu wa,muke bida ne tace gidan Al, shahideen bin Utuman mukazo
Sai yace mata ai ba nan bane sai ta kara gida na gaba,,,,,
Kusan gidan iri daya ne amma dai akwai bambanci a,gina gidan iri daya,ne dan bambancin kadan ne,,,,,

Muna shiga cikin gidan muka iske wata, balarabiyan mata, a,kata faren falonta na alfarma tana kallon talabijin tashar tashar makka ce daidai lokacin da suke sallar azahar .
Matar ba wata babba ce ita ma tana saye da dogon riga sai wani dan karamin hijab akanta,,,carbi rike a hannun ta guda tana ja a,hankali cikin natsuwa,,,,,,
Ta ansa muna sallamarmu cikin fara,a daidai lokacin kuma ta mike tazo da fara,ar ta tare mu,,,,,
Suka rungumay juna ita da hjy Laila ta sunbanci gefen kumatun hjy Laila,,,,,,, ni, dai ina gefe ina kallon ikon Allah , wai ashe gaisuwa ce hakanan ,,, sai kuma naji sun buge da yaren larabci,,,,,
Ina dan gefe tsaye naga hjy Laila tana magana tana nuna ni, da alamar magana ta akeyi,,,, dariya naga sun sa har fararen hakorar matar ya dan baiya na waje,,,,
Hannu matar ta mika min alamar inzo gurida a
Nazo tai min yadda suka gaisa da hjy ,,, sai ta dan lakaci kumatuna tai wani magana cikin larabci.
Tajawo hannu na ta zaunar dani kusa da ita,,, maganar cikin larabci take fadin wai gaskiya tana so ,na , saidai nayi karama da aiki,,,,, amma idan zan iya yimata rainon yarinyarta zata daukeni,,,,,,
Tana shafar kaina tana magana cikin mutunci da girmawa,,,
Sukayi cinikin aikina da hjy Laila,,,,,
Mama Nailabin ta shiga daki ta dauko kudi masu yawa, wanda ni alokacin bansan adadin su ba taba hjy Laila wai kudin aikina ne

Hjy Laila takira ni gefe tace min to ita zata wuce don Allah in kula da aikina kada in, bari a samu matsala ko kadan daga fanni na don maman, Nailabin tana da kirki so sai,,,
Tunda,ga wanan ranan aikina yafara a gidan Al,shahideen bin Utuman ,,,,
Ni duk wanan abin da akeyi hankalina ya,na can a wancan gidan da muka fara shiga na farko ina son in koma wurin ruwan nan da naga yana fita acikin duwatsun nan dake malala a green carpets ,,,,,

Daki guda aka bani ni kadai dakin babu dai ne babu acikin shi don dai wasu abin ma dai ni ban taba gani ba koda nai zama wurin madam Rita a,jidda muna

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment