Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data,ke kwance tana jin su sai addu,a takeyi abakin ta,,,,

Kiran sallah akeyi ko ina taji lokacin da yake fadin kada a bude kofar gidan har sai sun dawo sallah asuba,,
Ita kuma lokacin tana daidai bayan dakin maigadi,,,
Allah yabata sa,a maigadin yashiga daki dauko abu,,, aiko ta lalaba tafice dagudun tabar gidan ,,,,
Gudu taitayi tana waigen bayanta ko ana binta abaya, ,har Allah yasa tasamu mota masu zuwa dawo sallah asuba tabiyo,,

Yadda naga dare haka naga rana don ina cikin mugun damuwar rashin dawowar yar uwata kuma masoyiyata maikaunata da alheri,,,,
Don dai ni nasan cewa ba gudu tayi ba akwaidai wani dalili mai karfi sosai,,,
Gari yafara yin dan haske mutane sun fara zirgazirga nafito wajen gidan mu natsaya batare da kowa yasani ba,,,
Sai ko ga Rugaiyya nagani cikin tashin hankali da firgita janta nayi gefe nace ta nuna babu komai har kowa yafita don ba wanda yasan batadawo gida ba,,,

Hankalina atashe nabata ruwa tai wanka muka shirya kamar kullun, mukafita gidan ,,,
Saida mukai nisa da uguwar mu sanan muka rike, junan mu mukaita kuka,
Saida mukayi mai isar mu ba mai bamu hakkuri sai Allah,
Nice nadanyi karfin hali na fara magana cikin sheshekar kuka, ahankali nake tambayar ta may yafaru da ita,,,,,,,,
Kara rugumay ni tayi takara rusa sabon kuka dakyat na samu tadan tsagaita kukanta,,
Sannu ahankali ta warware min komai tun farkon yadda al,amarin yafaru da ita , dakuma yadda tasamu ta tsira
Mun aje cewa koda hajiya tace ta koma gidan aiki bazata koma ba wanga karon,,,,
Haka muka dunguma dani da ita muka tafi gidan aikina a,ranan



🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 13:37] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣2⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,,,

Imani acikin zuciya take ba,a zahiri ba , Allah yana amfani da aiyukan mune, na zuciya,bana zahiri ba Allah yakara muna imani 👏👏👏👏👏 , Ameen,,,,,,,,


Tunda safe muke barin gida zuwa gurin aiki na ,ba mu dawowa sai da dare ,,,
Don muna gudun kada azo a,kama Rugaiyya ,,, kamar yadda mugun yai ikirari, cewa zai sa afitar da ita acikin kasar da karfin tsiya,,,
Koda mukadawo Yumma ke tambayar mu ina Rugaiyya ta,tafi yan gidan aikinta sunzo har sau biyu bidan ta,,,,
Cemata,nayi ta kyale su don ta,canza wani guri aiki ko,,,

Tun lokacin bamu kara jin komai ba tun muna dari dari ha muka gaji muka sake jikin mu,,,
Saidai hajiya bata san cewa bata zuwa aiki ba,, abin da muke gudu shine kada lokacin kawo kudi yayi bamu kawo mata ba,,,
Duk zuwan da mukeyi da Rugaiyya masu gidan basu sani ba dayake gefen mu daban ne,,
Shiyasa har muka dan dauki lokaci, agidan ba wanda yasani,,

Shirin zuwar yan Nigeria umurah akeyi, su hjy mama,
Sai gyaran gidan ake tayi sosai tundaga fentin gidan har furnitures ancanza sabo sai kuma kayan electronic sabbi nayayi lates,
Gidan yakara wani haske fayau kamar ancan wani fasalin gina ne,,,

Al,Mustapha yake fada ma wanan yar dattijiwan mai aiki suna son karin yan aiki mutum biyu ,,,,,, mata biyu mata maza kuma uku,
Daidai lokacin na shigo kitchen din don dawo da kayan abincin na,,,
Saida nabari yafita nadawo gurin matar nai mata ,,,
hannu na bibiyu nake rokon ta don Allah ta taimaka ta daukar min Rugaiyya daga cikin ma,aikatar,,,
Shiru tayi tana nazarin maganata,
Can tace inzo mata da ita gobe tagani ko zata iya,,,
Nace mata aitana nan gidan tare muke zuwa,,,,nan nabata labarin abinda yafaru da Rugaiyyan agidan aikinta
Gaskiya matar ta tausaya muna sosai tai muna alkawarin zata gwada aikin ta tagani ko ta iya,,,

Washegari kuwa ta,fara gwada aikin Rugaiyya ,tagani ko zata ,iya,,,
Abinci muka hada mata maidadi kusan kala uku tare da abin sha,,, mafi saukin hadawa,,,

Kofar, Get din gidan aka wagalle, motoci ne guda uku suka shigo gidan maigidan ne wanda yai tafiya zuwa kasar Dubai tare da baki ,,,,
Yaje wani aikine na gagawa a kamfanin wani mai kudi a,Dubai .
Inda yai masu gyaran wata na,urar,
Tatan mai da kusan mutun uku ana,daukowa don su gyara hakan baiyi ba,,,
Shima shiganshi tabiyu ke nan ,ana biyun Allah yabashi sa,ar gyarasu,,
Wanan gyaran ta sa yasamu alheri sosai ,,,
Don har gurin Abu Abdullah , aka kaishi don su gana,,
Abu Abdullah wani matashin dan kasuwa ne akasar Dubai, mai tsananin arziki da dukiya akasar ta Dubai,,Arzkinshi bana haye bane na gadane,,,,, ,
Duk,wanda yagan shi,, dole maishi yasamu alheri sosai arayuwa,,,, Don mutun ne wanda shi kanshi bai san yawar arzikin shi ba,
Shiyasa duk mutumin da ya yimai abin farin ciki arayuwa shi,har yaji dadi,
shikuma zai jika maishi da daula daida gwargwado,,,,
Saiga Ahamad yaci sa,ar wanan daular shima,,,,
Don dama Abu, Abdallah,yayi bakin cikin rashin aikin na,urar da Ahamad ya gyara mai, kasancewar kafin a,yarda mashi ya mallakesu saida yasha wuya sosai don an nuna mai hassada so sai, tun mahaifin shi nada rai suke wanan project din,,,,,,
Yana murnan sunshigo hannu sai kuma gashi,sun,ki aiki yadda yakamata,,,, ,,,,,,,
Angwada engineers har biyu kafin,Ahmad,abin sunki aiki ,,,,,
Wani abokin karatun Ahmad da a,ka,kira dan paris tare sukayi karatu da yaje karo ilimi, a,kasar paris,,,
Abokin shiya, ce akira Ahamad dake saudiya agani,,, yasan dawuya in bai iya gyara su,, ,,,,,
Cikin ikon Allah sai gashi ko ya tayar dasu duka,,, ukun yanzu ba su da wata matsala,,,
Jindadin hakan yasa,
Aka shirya yar karamar walima don farin cikin wanan nasarar da akasamu,,,,
Wurin walimar ya hadu da abokai kala kala, harda baban manajan companonin, Abu Abdullah, agurin.
Bayan waliman shima yagaiyace shi zuwa gidan shi shan green tea,,,,,,
Nan ne suka kulla,business dashi,,,
Yakumayi ma Ahmad alkawrin za su shi cikin harkan kasuwancin su sosai,,,
To shine yadawo gida yau tare da abokan shi yan Nigeria da suke can saudiya tare,,,
Su sukaje airport su ka taroshi saboda murnan alherin da yasamo,,,,


Kusan su biyar ne suka shiga tangamaymay falon nashi cikin raha da farin ciki kowa na fadin albarkacin bakin shi,,,,
Al Mustapha ne keta dawainiya dasu,,,
Daya daga cikin su yace aishi yunwa yake don tun safe baiyi break fast ba ma,,
Abinci yace akawo masu suci,,,
Cikin sauri Almustapha ya shiga gurin yar dadtijiwar matar mai abinci yana fada mata baki na bukatar abinci,,,
Gabanta ne ya fadi don dai yau ba itace ta girka abincin ba mune akaiwa gwaji aiki yau,
Bataboye mai ba tafada mai aiko yabita, da fada, har yana ikirarin cewa har ita sai ya kora aikin nan,,idan har ansamu matsala,,,,,

Abinci suke ci suna hirar su, na duniya,,, daya daga cikin sune ya tsiyaya hadin sobo da mukayi na ainihi,,, yasha,,,
Dago kai yayi yana tambayar Ahmad inna yasamo mai ,mai aiki kamar agida Nigeria ,, aishi rabon da yaci abinci irin tamu ta Nigeria har ya manta wlh,,,,
Shima gudan dake gefe yace kai wlh ka rigani magana ne umar,,,
Wanan abincin yasa na tuna da gida sosai yau,,
Almustapha dake gefe yana jiran ayi mai complain yai wani irin ajiyar zuciya gami da hamdala, saboda sam baison abinda zai bata wa maigidan nashi rai,,,
Don Ahmad mutum ne mai yawan hakkuri duk abinda kaji yai magana to abin akwai matsala akai,, don haka yake taka tsantsan dashi,,,

Muko muna can matan nan tasamu gaba tana tamuna fada wai naja mata hasarar gurin aiki mafi daraja da ta,taba samu arayuwar ta,,, fada take yi kamar zata doke mu,,, mun dukar da kai kasa Rugaiyya tana ta bata hakkuri,,

Cikin girmamawa da kula ya bakowaninsu kyautar da saida suka girgiza da shi ganin ,,,,, kudin daya basu mai yawa haka ko bakin godiya basu samu ba,,,
Yace umar mayye amfanin mutum yasamu bai kyautatawa natare dashi ba,,,
Nasamu amfani sosai a, wanan tafiyar kaga kuma da muke tare aidole in taimake ku,,,
Baysn sun wuce Ahmad yakira Almustapha ,,,
Duke yake yana serching wani sabon engine a,cikin computer shi,,, kanshi na duke ,,,,,
Yace Almustapha wayai muna abinci yau agidan nan ,,,,, shiru mustapha yayi kashi na duke akasa,, dama yasan dole atuhu mayshi da wanan laifin maigirma, dan ba kowani abinci oga ke ci ba ,.ko ita wanan matar saida yagwada ta kafin adauketa,,
Idon shi yadago yakai diban shi ga almustapha,,, bakaji bane yakara tambayar shi,,,
Cikin in,iniya yace mai dama dama ,,yau wanan matar bata da lafiya ne shine ,,, shine nasa wanan yariyar mai ba Flowers ruwa, ta yimuna,,,,
What ya,mike tsaye,, gami da ture computer shi gefe guda,,
Yace kana nufin wanan yar yarinyar tai wanan abincin yace mai na,am,itace maigida,,,,,,,,
Kai yakama girgizawa yaje yadawo,atsakiyar falon,
Azuciyar shi yana tunanen anya fadima mutunce, kuwa,,, yarinya kamar wata Aljanna gaskiya lamarinta akwai bincike don dai she is to young da wa, yanan abin da takeyi gaskiya,,,
Don dai ko agida Nigeria,kamar wanan yarinyar bata isa tayi wanan girkin haka,ba,,,
Yajuyo inda mustapha yake tsaye yace tana ina,,,,,
Sim sim na shigo falon hade da sallamata sai faduwar da gabana ya,keyi, don dama jira kawai nakeyi akirani ,asallameni,,daga aikin gidan,,,,, ko dayake nasan cewa mun yi aiki yadda yakamata don ni banga abin laifi aciki ba,,,
Amma sai naga almustapha da wanan matar duk sun tsorata, nima shiyasa hankalina ya daga
Don ina gudun inyi sanadin barin aikinta,,,,
Gyafe guda,nadan rakube a falon,kamar zan shige a,kasa, don ladabi,,,
Saudaya yadan daga ido ya kalleni yakauda kai,, azuciyan shi ya jita kamar wata ta kirki wani lokaci kuma ta iya shedan ci,,,,
Cikin kakausar murya yace min,, Keda wa kuka hada abincin gidan nan ,,, nikan nace masa Rugaiyya ce,
Da sauri ya kalli inda almustpha yake tsaye kamar mai rokon gafara,,,,,,,
Dukan su shida almustapha,,sukace Rugaiyya nace eh,,,,,
Nai masu bayanita kamar yadda naiwa matar nan,,,
Ita ma,Rugaiyyar,kiranta akayi har matan nan mai abinci,,,,,,, saida yadan yi nazarin mu sanan yafara magana cikin muryan shi mai taush,,,,,
Yai muna godiyan aikin da mukayi masa na,yau tunda, har bakin shi sun yaba, da aikin mu,,,,,,
Sai kuma yabar zancen yafara wani
Ida yace muna mahaifan shi zasuzo daga Nigeria yana son don Allah mu basu kulawa ta musan man dakuma girmamawa, duk wani bukatar su da dawainiyar su mu taimaka masa dashi don shi ba mai zama bane,,,,,,,
Yakawo kyauta da yawa ba duk, wanda ke gidan,
Kyautar ta girgiza duk wani saboda kusan albashin mutum kashi biyu ,,,,,
yaba kowa agidan yace alherin da yasamo gurin tafiyar dayine, shi ne muma yabamu,mulasa musa mai albarka arayuwar,,shi,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 13:43] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈.
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Duniya saida kudi Lahira kuma saida hali na alheri,, Allah yasa mu dace,,,

Gaisuwa da Jinjina ga Yan Huguma group tare da sauran masoyana na takari novel,,,

Almost true life story,,,,,


Jirgin air max ta sauke bakin Nigeria tun karfe hudun asubahi,,
Sannu a hankali mutocin da suka ,, kwaso su daga airport suke tafiya dawo,wa gida,
Daga gurin taron bakin Nigeria, motoci ukune jere na farko driver ke janye da wasu maza su biyu,,, Saita biyun Ahmad ke jan motar,babanshi ne da hjy mama sai tsohuwa,aciki,,,,motar ta uku kuma Wasu yan matane su biyu sai driver, da,ke jan su,,,,,
Mu,na, gidan dama tunda safe duk wanin abinda yakamata muyi don taron bakin, munyi,,, saboda tunda muka zo bamu zauna ba , Don saboda aiki da yai muna yawa,
,,,Aikin yau, ba kadan bane don yawa gare shi sosai,
abincine da abinsha kala kala muka hada,irin ta taron baki na musan man,,,,,

Cike da doki nake son sai naga wa,"yan nan bakin da kowa ke ta rawar kafa saboda da zuwan su har mai gidan, namu,da muke ma aiki,
Wanda ko kallo mutum bai ishe shi ba da wuya kaji yana magana dawani agidan inyazo dan dama dama Almustapha ko kuma bawani dogon magana bane,,,,,,,
Duk girman gidan nan saida, hayaniyar isowar bakin,mu duk ya ruda gidan da murna da kuma dararakun su, irin na yaushe rabo,,,,,
Suna shigowa muka dinga kaimasu gaisuwa ,,, suna ansa muna da larabci don ina ganin basu ga almar mun iya hausa ba saboda yanayin shigar,mu,,,,
Wata yar tsohuwa daga cikin su tafi dauke min hankali saboda yadda naga kowa na haba,haba da ita ,,,,
Almustapha yasa aka kwashe masu kayan su zuwa cikin dakunar gidan

Abinci muka gabatar masu dashi suna gamawa,sai wurin kwana,muka kai kowan su yaga inda zai sauka,, agidan mu mata mu muka taimaka wa su matan zuwa masaukin su,,,,,,,
Duk wanan dawainiyar da mukeyi, da baki maigidan yana zaune a gaban wani desktop din shi dake falon kamar bashi keda bakin ba,,, yana kallon movement din kowa har mu yan aiki ,, amma azahiri zakadauka aiki yakeyi daga zaunen,,,,
Ba abinda da yafi bani sha,awa kamar yar tsohuwar da aka so da ita ,, wace zata iya kai shekara kusan,,, tamanin da hayi ,aduniyar kila,
Duk abinda takeyi hankalina yana gurin ta duk wani motsin da zatayi sha,awa yake bani wlh,,, gata da fada irin na tsofi,,,,
Zuwa nayi nakira Rugaiyya don tazo, ita,ma taga yar tsohuwar mai ko,kari, kamila mai yawan ibada,, ,,,,,
Muka dan labe gefen labule muna lekenta
Zaune take a dakin da akai mata masauki agidan da ,alama tasbihi takeyi a zaunen don bakinta nata motsi ga tasbaha a hannu ta,,,,
muna nan labe bayan dan labulen da muke leken ta,,,Dan hira mukeyi,,,. muna dariya a hankali komai nata yana burgeni
Nace dama ace wanan tsohuwar kakatace,,,wlh Rugaiyya da naji dadi so sai naso ace nima ina da yan uwa haka har da kaka,,,, da kullun ina tare da abina ina bata kulawa,,,


Koda ban waiga ba,naji kamshin turaren shi ya bure muna hancin mun hakan ya nuna muna cewa maigidan ya gurin,da muke labe,,,,,,
Da sauri na sake labulen da na dan hankade muna leke.
Nayo baya daniyar gudu sai kawai na,ji na yi karo da kafa, shi,,,
Ahankali, nadago kaina nakai dibana gare shi,,, fuskan shi a daure murtun,,,
Muka dan zagaya ta bayan shu muka wuce sim sim da mu,,,
A,she duk abin da muke fadi yana tsaye bayan mu hannayen shi cikin aljuhun wandon shi,,, ido ya zubu muna, har muka bace mai,,,,,,

Bayan su yabi da kallon mamaki ,, azuciyar shi yace may wa,"yan nan yaran ke nufi ,,,,
Suna nufin basu da kowa ko may ,, lalai sai na samu time inji labarin su,,, yadan leka don yaga may muke kallo wurin tsohuwa,, yaga ai zaune take tana ibada,,,
Murmushi yayi yace mai ran karfe ke nan hajiya tsohuwa ,,,,
Ba ita ba ba mai iyawa da hjy mama,,
Don yasan ko wanan zuwan da akayi da ita don shine tazo,,
Tunda Abba bai fada mai da ita za,azo bada fari,,,,

Saboda aiki yau mun makara sosai bamuje gida da wuri ba,,,
Almustapha yasa driver ya kai mu gida , don dare yayi. Ana iya kama mu,,,

A , hankali muka shiga gidan namu gami da sallama,
Mun iske kowa na harkan gaban shi , takalmana tomy na cire na wurgat gefen da muke aje takalmi,
Sai niliyata danake warware a hankali, don indan ji iska ajikina , dagani sai yar wando da riga da suka dan matse min jiki kamar wata diyar larabawa kaina dana kule da ribon shima na dan walwale shi don in samu saida agida,,,,
Nakai kallona ga sukaina ina tambayar ta hajiya fa,,
Tace min ita ma bata ganta ba tunda tadawo, ido waje nake kallon Sukaina Don ai wanan rashin imani ne,,,,, aiko banza hajiyace silar zuwan mu nan,,,
Inga mutunci aidole mu mutun ta,ta,,,,,

Daki na fada da sauri na,,,
Kwance na samu,hajiya jiki ba kwari
Cikin tashin hankali nake tambayar ta ko tasha maganin ta,,, ban tsaya jin ansar taba nafita waje da sauri na,,,
Tea na hada mata mai kauri sai ruwan dumi da na jona mata tai,wanka nabata maganin ta, sha,,,,,

Tunda safe kuma na tashi na kara hada mata abin kari , nabata maganin ta,sha,,
Nacewa Rugaiyya ta tafi,ni bazanje ba ,yau,,,,,
Hajiya ce tace min in tafi ai taji sauki yau sosai,,,
Hakana natafi badon raina yaso ba, don gaskiya naso in kula da hajiyan mu sosai,,,saboda tausayi take bani don ni har a raina kamar inna nake daukar ta,,,

Muna isa tun da safen nan muka hada masu abin karyawa ,,,kamar irin na mutanen Nigeria mu,,,
Bayan komai ya kam,mala mun jera masu a, dining table ,,,
Daya daga cikin yan matan nan tafito tace muna, wai baza ta iya cin abincin mu ba, wai akwai warin tafarnuwa aciki da yawa,,,
Duk da nasan cewa bamu sa tafarnuwa ba acikin girkin mu,,,
Saboda wanan dattijuwar matar da muke aiki tafada muna yan Nigeria basu son tafarnuwa don haka kada muyi masu girki da shi,,,
Jiki ba kwari muka kwashi kayan da niyar mukara zuwa mu dafa wani,,,

Muryan maigidan mukaji abayan mu ya na fada, muna cikin larabci mu ,maida komai inda yake mu wuce kuma kada mu dafa abinci rana dasu,,,
Zasu tafi haram masijid yin dawafi daga can zai su wuce asibiti da hjy mama,,,
Yana ma matar da muke aiki tare bayani,,,

Ya juya wurin yarinyar da yakira da mairo, idan abincin baiyi maki ba kina iya shiga kitchen ki dafa abinda kike so,,,
Aikin dafa abinci sau biyu kawai nai alkawari dasu , ba,kowani lokaci suka ga dama suke aikin ,ba
Amma in,kinga zaki iya biyan su hakin aikin da zasuyi maki sai su je suyi maki, wani irin wanda kike ra,ayi ko yafada cikin nuna serious,,,,,alamar ba wasa ga zancen shi,,,
Tsohuwan nan ce abaya shi,ta karbe zancen da cewa ai basu san darajan mutum ba su ,
Sun dauka kowa za,su iya takawa don su na da kudin hakan ,,,
Saboda irin rashin tarbiyan da ba,a , nuna masuba, agidan su,,,
Kasan cewa agida yan aikin su kamar bayin su suke,,,
Sabanin nan da komai a,ka,ida akeyin shi,,,,

Daidai lokacin na iso bakin taburin cin abincin ina kokarin taimaka ma tsohuwar don ta zauna,,,
Plate nadauko mata ,sai kuma tambayar ta da nakeyi cikin hausa may za,a zuba mata,,,
Kallon gefen da Ahmad yake tayi, tace mai,, kai nifa banjin larabcin da wanan yariyar ke min,,,
Tsohuwa ai hausa take maki ita madin, inji Ahmad,,,
Cewa tayi may zakici azuba maki,,,,
Murmushi nadan yi kadan har fararen hakorana suka dan baiyana waje,,,bayan na zuba mata sai na bar dinning area din don in,cigaba da aikina dama don in,danji dumin tsohuwar naje kusa da ita,,, kalon mamaki yabini da shi ,,,,
Ina wucewa naji tana fadin ita wanan min ma yar aiki ce hakan ,,,
Bai bata ansa ba sai mairo ce tace ai tunda kika ganta tana aiki nan kema kin san yar aiki ce
Wata kila anan aka haifeta , ma,,

Dakin yar tsohuwar nan nashiga na gyara mata komai tsab kamar ba,a bata ba,,,
Na kun na kayan kamshi ko ina gidan yadauki kamshi na musan man,,,
Sai sanyin AC da ya karade ko ina na gidan,,,

Ahmad ne yafito daki cikin shirin shi nafita, jallabiya yasa fara tas ma laushi da sulbi kan shi da yar karamar hula fara sol itama, sajen shi ya kwanta lub a fuskan shi kamar shiyayi kansa,,,

Hannu shi rike da dan makulli motar shi,,,,
A tsakiyar falon ya tsaya yana ba Almustapha umurnin kula da komai yadda ya kamata,,,
Mahaifin shine suka fito tare da hajiya mama,, suma a cikin shirin su ,,,
Tana wani yatsine yatsinen fuskanta kamar wacce gidan bai mata ba,,,
Azuciyar ta kuwa sai mamaki takeyi da irin canjin da tagani ga Ahmad ,,, budi da arziki yataso ma yaro kamar shi yafi kowa iya karatu,,,
Tasan duk yadda Alhaji yai mata rantsuwar cewa baida masaniyar komai gamay da,sana,ar da Ahmad din keyi,,,
Ba wai ta yarda bane jira take yi kawai da su koma gida dole asan yadda za,ayi gaskiya,

Tsohuwa ake jira tafito su tafi tace ita atabau baza taje ko ina ba ,,
Su tafi kawai don ita tagaji sai gobe zata fita,
Haka suka tafi batare da ita ba,,,,
Hakalin maigidan bai kwanta ba da barinta da akayi gida ,,, yasan dai da wata a zuciyar tsohuwa,,,,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment