Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara gyara amma sai naji irin maganar da ke ta bin gari cewa yawon karuwanci naje yi a saudiya,
Hakan ne ya hanani yin komai tun da nazo,
Ga kudi nazo da su a jakkata amma ina jin tsoron ba inna su don kar tace aida gaskiyar mutane,
Don zatayi mamakin ina na samu wanan kudin haka,
Duk da nasan cewa tarana gaskiya zatai halinta,

Kafin wani lokaci har mariya ta soya muna kwai da kwai muka zauna mukai mai cin gaskiya ni da Aisha,
Sai dai na lura da inna ko kwara daya bataci ba raina yadan sosu kadan don nasan hakan nada nasaba ga kudin da na ba yar a sawo kayan suyar,
Amma daga baya sai naga ai tana da gaskiyar ta tunda bata san komai ba a gamay da ni,,
Na, inna jin lokacin da mariya kewa innar mu maganar rashin cin wara da batayi ba da aka bata,
Inna tace ma mariya wallahi kawai bata ci ne ba wai taki bane,
Mariya duk yar karamar yariyance amma tasan ya,kamata,
Gashi Allah ya sa mata taisayi na a ranta tanada son yan uwa sosai,
Shi ko Abdull kusan ko yaushe sai ya sayo min kwaida kwai tunda yaga ina so,
Hakan yasa nakara son yan uwa na sosai kuma ina ji da su,
Rashin zuwan hafsi gidan mu da batayi yasani cikin damuwa ina kewar yar uwata so sai,
Yau ba makarantar boko don haka muka shirya fita zuwa unguwa nida mariya da Aisha,
Cikin shiga irin ta mu na can saudiya nake don bazaka iya ganin komai nawa ba,
Gidan kawu salihu muka fara zuwa nai sa,a nasamay shi a gida tare da yaran shi suna gyaran darnin gidan su,
Kawu yayi murna kware da zuwan da nayi ziyaran shi,
Cikin fara,a yake ce min fadima ta yau agidan namu,
A gaishe ki ke ji,,,,, ,a,a gajiyan tahiya
Nace lafiya kalau kawu mun samay ku lafiya,
Sauran yaran kawu suka zo muka fara gaisawa da su,, cikin wasa irin na barkwaci,
Matsala guda shine irin kallon wulakancin da matar kawu tai min uwar gidan,
Amma ita amaryan far far muka gaisa da ita,
Na lura da ita sarai amma sai na share kamar ban fahince ta ba, sam,
Har gabanta naje na tsuguna nace gwago mun samay ku lafiya, kamar ba,zata amsa ba sai dai ta ansa min a dakile,
Har natashi zan wuce sai tace amma dai albasa batai halin ruwa ba,
Kamar diyar yar kulu za ace ta tafi yawon duniya ba kunya kuma har ta tako kafarta har gida da tsarabar yawon duniya,
Jiki a sanyaye na dago daga gurin ta nadawo inda kawu, yake zaune ,
Na zauna gefen kawu kadan Aisha ta dawo kusa da ni ta zauna,
Kawu yace min kuna can kasa mai tsarki abin ku fadima
Nai murmushi kawai batare da yin magana ba,
Gwago da ga inda take zaune ta jefo bakinta cikin zancen tace
Aida wanan gara mutum ya zauna a kauye yafi mai,
Duk muka kalleta lokaci guda batare da mun mata magana ba,
Sai jin muryan mariya nayi tana cewa a, a ha gwago zato zunubi ce
Shedar zina abuce mai girma ga addini,
Kawu yace saratu ina rabaki da wanan mugun hali naki na hassada,
Wanakewa hassada yace aikin fini sani,
Idan ma har diyar yar kulu tayi wani abin kunya nadauka ke ma abin,ya shafe ki ai, diyan yar kulu,
Jinin diyanki ne ko kin ki ko kinso tunda dai jini ya gauraya, ko,
Amma babu komai duk abin da kikayi bazaki rabani da yar uwar haihuwata ba,
Don da dadi da daci ni ina tare da su, idan kinga dama ki fadi alheri ,
Shiru kawai nayi a zuciyata ina wa Allah godiya da ya nuna min zuciyar kowa a gamay da ni,
Nakali kawu a hankali yadda naga ranshi ya yi mugun baci,
Cikin natsuwa nace kawu kayi hakkuri dan Allah
Yadda suke tsan mani abin ba hakana yake ba, da sannu kowa zai gane gaskiya ,
Mundan yi hirar bayan rabuwa da kawu tare da wasu daga cikin yaran shi,
Cikin hirar mu ne kawu ke, fadawa min yadda yayi da innar mu lokacin da Rugaiyya ta kawo mata kudi ,
Yaso ace inna tayi amfani da kudin ta gyara gidan ta da shi amma sai taki karba kudin dukka,
Yace yanzu yasan cewa a matse muke a gidan don rashi wadataccen wuri,
Ya ci gaba da fadin kowa da irin hanyar da Allah ke azurta shi ,
Mu namu hanyar arzikin ke nan da Allah ya tsago muna
Yai min nasiha so sai akan cewa kada indamu da zancen mutanen gari
In barwa Allah al,amurorina kawai shi zai min mafita insha Allah,
Naji dadin wanan nasihar ta kawu so sai wallahi, har cikin rai na,
Bayan dan wani lokaci mukayi sallama da kawu da yaran shi da niyar zamu tafi gidan hafsi a lokacin,
Kudi na debo masu yawa naba kawu na ba sauran yaran nashi nace suma su raba,
Kallon kudin kawu yayi yai shiru,
Can yakira suna na a hankali yace min fadima da kin bar kudin nan don nan gaba za suyi maki amfani so sai,
Don ko banza kin ga gaki da ciki kesan lalurar haihuwa yawa gare shi,
Cikin nuna rashin jin dadi nace wa kawu, na Kawu ko kaima kana kyaimar cin kudi na ne,
Ya ce ko daya fadima saboda na san cewa zargin da akw maki ba gaskiya bane ,
Gani nayi cewa dai kuna bukatar kudi don gina rayuwan ku da ke da maihaifiyar ki,,
Dan murmushi nayi kadan nace kawu ka karba kawai ina da kudin da zamu amfana da shi dagani har yan uwa na, nan gaba,
Ya karba tare da samin albarka yana min fatan alheri,
Jibrin yaron kawu yace hjy fadima ashe zamu zo karban jari a gurinki ke nan ko,
Mariya ce ta bashi ansa da fadin sai kazo baka jin ba bu ai in har zaka amince da tazama shugaban ka,
Dariya muka sa gaba dayan mu
Mukayi wa gwago sallama wace na hada da nata kudin ,
A kofar gidan su hafsi a kwai yar karamar kasuwa a gurin inda mutane ke taruwa manya da yara suna saida yan abubuwan tabawa,
Tundaga nesa naga duk sun zu,bo muna ido caaaaa suna kallon mu irin kallon kauyawa,
A hankali nake takawa har muka dan gwauta inda mutanen suke
Muryan wata yarinya ce mai tallar fura take fadin wallahi nidai wanan matar tabani shawa so sai ta kusa da ita tace ke dallah gafara can itace fa wace tafito yawon duniya kasa mai tsarki,
Dayar tace ke waya fada maki wallahi naji an ce ka,zafi ne akai mata,
Ni ce na hana mariya ta kula su, har muka shige cikin gidan abin mu,
Hafsi tana kofar dakin ta tsaye tana gyara tsabar farar shinkafa ta tuwo ,
Sarakanta da sauran matan yan uwar mijinta suna tsakar gida zaune gidin wani katon iccen lim,
Sallamar mu yasa duk suka juyo gaba dayan su suna kallon mu,
Direct inda suke zaune na nufa na gaishe su cikin girmamawa,
Suka ansa muna ciki ciki, mariya ko kallo basu isheta, ba don har tayi gaba abinta,
Ina bada baya naji muryan wata daga cikin su tana fadin kai wanan wa zaice haihuwar dogon daji ce
Duk ta kwade tayi wani fari kamar balarabiyar gaskiya aida gani kasan larabawa sun more a nan,
Wani irin miyau mai daci ne naji a baki na haka na hade su cikin bacin rai,
Maimakon hafsi ta yi farin ciki da zuwa na sai ce min muna tayi wai lafiya muka zo
Bamu jirata tazo gida ta samay mu ba gaskiya ita bata ji dadin da na shigo gidan su ba da ciki a jiki na,
Duk da duhun da nake gani a wanan lokacin bai hana in wayence ba
Don kada mu taru mu zama daya da yar uwata, murmushin ta kaici nayi mata nace
Naji kewar ganin yar uwata ne shine na biyo ki har gidan ki tunda naga kin dauke kafarki da gidan mu,
Ai dole indauke kafata fadima don ina bakin cikin ganin ki da wanan cikin ajikin ki,
Mariya wacce bata ko zauna ba tace anty fatima tashi mu tai, tana mai kokarin jan hannu Aisha, zuwa waje,
Nace a,a mariya barin shiga dakin yar uwata mana in ga ni koda saudayane,
Muryan mijinta mukaji daga bayan mu, yace a,a yan TAKARI makkah ne yau gidan namu,
Yana min wani kallo cikin raini hankali,
Mariya tace ai gara da TAKARI da yan cin amana masu raba zumunci da karfin ta,
Ke mariya inji hafsi kada ki kawo wa mutane dibar albarka,
Don ke baki da kunya ,
Ita wacce tai laifin ta daure tai shiru sai kece zaki dinga yiwa mutane fitsara,
Zaman da ban yi ba ke nan a dakin yar uwar haihuwata, wace itace muna kamar uwa idan ba inna,
Yau gashi duniya ta zuga ta sai wulakanci take min akan tuhumar da take min ,
A hankali nadaga kaina na kalli hafsi ido tab da hawaye nace a gaskiya hafsi ban taba tunanen haka daga gare ki ba a rayuwa ta,
Nadauka cewa ko duk duniya sun guje ni kece mutum ta farko da zaki fara rungumata bayan mahaifiyata,
Dan girgiza kaina na cikin takaici na ce sai gashi kece agaba wurin nuna min kyama da hattara ta,
Kafin in karasa zancen hafsi ta cabe da fadin ,
Oho ke kin bata rayuwar ki shina kin kazo ni ki kashe min nawa auren duk mu koma gida mu zauna mu lalace ko, ,
Duk yadda naso in boye hawaye na wanan karo hakan bai yu,yuba don saida hawaye suka zubo min, daga idona suka diga kasa, don haushi da takaici,
Shi ko mijin ta yace ato in madai kin biye mata matsalar ki ce don dai ni wallahi har na fara shakkar hada zuria,a da ku ko,
Ashe dama yabon banzane akw maku,
Mariya tace kai mutumin banza mutumin wofi, ban bari takarasa ba narufe mata baki
Najata muka fito shin yan yar uwar mu rai bace,
Yan gidan dake hira sunyi tsit suna son su jiwo maganar da akeyi daga lungun hafsin,
Rai bace muka iso gida duk kan mu, cikin tashin hankali,
Tun a kofa mariya ke kuka tana kokarin fadawa inna irin cin mutuncin da hafsi da mijinta sukayi muna,
Murmushi kawai naga inna tayi na takaici tace halin hafsi ai sai ita ,

Duk yadda naso inyi barci da dare na kasa sai juyi nakeyi saman shimfidata,
Ina ta sake sake cikin zuciyata, ta yadda zan bullowa wanan al,amarin
Nasan cewa duk yadda zan yi bayanin cewa ina da aure ba yarda zasu yi ba don ba,aga zahiri ba,
Hakan yasa tun farko na ja baki na nai shiru har ranan da gaskiya zai baiyana,
Amma yanzu ya zama dole in fadawa yan uwa gaskiya koda kuwa baza su yarda da zancen nawa ba,
Duk yadda naso bama zuciya na magana akan kawai indake abin ya fassakara da zaran natuna da kalamin hafsi da mijinta sai inji wani irin kololon bakin ciki hawaye su dinga fitamin a idona,
Washegari da safe wayana dake hannun Abdull suna game shida Aisha mukaji yana tsuwar kira,
Cikin mamaki duk muka kawai wa wayan kallon mamaki,
Mariya uwar rigima ce ta dauka cikin gidimi tace sallamu alaikum
Jinda tayi ana fadin fadima fadima yasa tai saurin kawo wayar ta manna min, a kune na

Muryan salimat ne naji tana fadin fadima mutanen Nigeria anshige Nigeria an manta da mu, ko,
Da yar murna nada na kwana biyu banyi farin ciki ba nakira sunanta
Munkai wani lokaci muna magana da ita a wayar tana fada min yadda sheriff yadawo yake bida na a haukace,
A hankali na tambaye ta ko Aziza tabar saudiya,
Nan ta fada min dan abinda ta sani, takuma sheda min cewa ai ta dawo Nigeria ko ,
Nai murna so sai duk da ba a gari guda muke ba amma naji dadin hakan
Bayan mun gama wayan ne na tuna da lanbar hajiya umma, ba bata lokaci na kira layinta shima yashiga,
Da farko bata gane ni ba saidaga baya bayan nai mata bayani ne ta ce, haba fatima
Tunda kika tafi nake ta jiran kiranki amma shiru nadauka ma mun rasaki ke nan baza ki kara bidan mu ba,
Naidan murmushi nace zan bide ki mana hjy ai wawa ne kawai ke mantawa da halarci ,
Hjy umma ta bukaci in ba inna waya su gaisa,
Batare da tunanen komai ba na ba inna wayar suka fara gaisawa da umma,
Bayan gai suwa da kuma yar ja,jantawa irin ta manya sai hjy umma ke tambayar inna ko maigidan naya yasa mu zuwa Nigeria,
Duk da mamakin da ya rufe inna sai ta wayence zance tace bai zo ba tukun ,
Hjy umma tace zai zo ai insha Allaj fadima kurciya ne ya ci ai bai kamata ta wuta batare da sanin mijin ta,
Ina gefe naga wani irin kallo na mamaki da inna tai min
Sai naji duk jikina ya mutu, a lokacin,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣2⃣
BY
🐎ZAINAIB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,


Tunda mahaifiyata ta gama waya da hjy umma naga jikinta yai sanyi sosai
Amma dai bata ce min komai ba sai kawai ta share zancen,
Tun ina dari dari, sai na fara sake jikina,
Shirun da naga tayi yasa nadauka cewa ai ba komai ne hjy umma ta fada mata ba,
Sai kawai na sake jikina naci gaba da harkokina, na yau da kullun,
Bayan wayan mu da salimat da kwana biyu sai gata har dogon daji,
Nayi farin ciki kwarai da zuwan Salimat, ko ba komai nadan rage samun zargin da yan kauyen mu ke mi kullun,
Ganin irin dankareriyar motar da yusuf mijin salimat yazo da ita,
Don ba shakar komai suke tambayar mijin salimat a masallaci da aka sallamay sallah, labari na,
Wani ke ce mai ashe tare mukayi zama saudiya da su,,
Yusuf, Bai san mai suke nufi ba dan haka sai ya ce masu a,a da matar sa ce da sukai karatu tare acan saudiya,
Sai kawai ya shiga yabo na kawai a gaban su,
Yana fadin cewa a gaskiya sunyi dace da yarinya mai ilimi da hazaka a garin su,
Ya ma su ai da,taimakon na har yasa mu matar shi ta kammala karatun ta,
Saboda ina da ilimi sosai a cikin makarantar mu,
Anyi, dace, Wani abokin mijin hafsi na cikin massalacin a lokacin da ake wanan hirar da yusuf,
Da sauri ya tambaya yace kana nufi fadima tai karatu a can saudiya,
Baban asamau yusuf, yai dan dariya yace sosai ma, kuwa don ta hada digree din ta ko,
Kafin suci gaba da hiran su ne wayan shi yai kara sai hiran tasu ta katse a lokacin,
A cikin harshe larabci muke magana da Salimat,
Tayadda nasan cewa innar mu ko mariya ba zasu fahinci maganar mu ba,
Na sheda mata cewa kada ta fadawa inna cewa nai aure pls, ban boye mata komai ba na sheda mata duk yadda ake zagina acikin gari,
Ran Salimat ya baci kwarai dajin cewa cikin da ke da uba kamar sheriff ake shegantawa haka, don rashin sanin daraja,
Tace min in bari kawai tafadawa inna gaskiya maganar ko zata fahinta
Cikin sauri nace mata dan Allah kada tace wa inna komai tabar har sheriff yazo da kanshi tukun,
Don ban san ko ya inna zata dauki maganar ba,,
Muna nan har mariya ta gama muna girkin abinci da ta dafa muna shikafa da mai da yaji sai salad da aka yanka,,
Katon sabon tabarma na shim fida muna a cikin rumfar inna,
Abdull ya kira baban Assama,u ya shigo daga ciki don yaci abinci,
Muma mariya ta, zuzzuba mana har da su Aisha da Abdull
Mijin Salimat yace a sokoto za su kwana don haka muka sake jikin mu so sai mukai ta hirar mu, hankali kwace,
Salimat tace min tana tuna nen zuwa yanzu sheriff zai iya gane cewa ban cikin kasar saudiya,
Ita a gaskiya ta so ta fada mai cewa ina Nigeria alokacin da yazo gidan ta a saudiya, Amman sai tsoro ya hana ta don ta na gudun yayi karar ta ga hukuma akan ta san da bacewar matansa,,
Ga kuma gwaunatin kasar saudiya da tsanani, so sai,
Nayi murmushi na ce ai bazai yi karar ki ba tace min, ke dan baki ga yadda hukuma ke ta bincike akan zancen ba ne,,
Tunda tumba taga motar baki a kofar gidan mu ta kasa zaune ta kasa tsaye, saida ta shigo gidan mu ganin Salimat don in ta tafi asamu abin fadi,
Sai da yamma so sai suka bar garin dogon daji zuwa cikin garin sokoto inda zasu kwana a wani katafaren hotel, mai suna five star,,,
Da zata tafi nabata kudi don ta sayo min yan kayan bukatu irin na mata,
Saboda tunda na shigo dogon daji ban shiga cikin gari ba ko ma agarin namu bana zuwa ko ina,
Washegari tunda safe muka hada masu breakfast saboda anan zasu dawo, su karya acewar salimat,
Inna tasa akai masu fura mai kyau na shimkafa zalla, yar asali dakan hannu,
Sai man shanu da su daddawa da kuka, duk ta hadawa Salimat, tsaraba,
Tumba ma takawo man gyada tace a basu shima kawu, ya kawo wa mijin anty zuma pure one yace yayi hakkuri da shi, ba wani tsaraba a kauye,,
Salimat tayo min sayayya so sai cikin garin sokoto, don da gani sakon ya fi karfin kudin da na bata,
Duk wani abinda tasan cewa za mu bukata nida Aisha saida ta sayo muna, shi,
Har mariya da Abdull duk sun samu nasu tsarabar,
Na rasa bakin da zanyi masu godiya wanan da wainiyar da sukayi min,,,
Sai gashi sukuma su ma murna tsarabar da inna da abokan arzikinta suka hado masu, har suna fadin wai kayan sunyi yawa ai,
Da za su tafi duk sai naji badadi a raina kamar in bi su na dinga ji,
Tai min alkawarin cewa zasu dawo badadewa ba insha Allah tunda sunga guri,
Kamar abin hadin baki su salimat sun tafi washegari sai mukaji tsayuwar mota a kofar gidan mu,
Cikin yan mintitika sai naga ana shigo da kaya irin na masarufi,
Kamar su shimkafa yar gwaunati da sugar tomatoes da man Turkey,
Mamakin kowaye kuma yakawo muna wanan kayan, haka duk ya kamani sanin cewa jiya jiya su Salimat suka bar garin na mu,
Don haka, nasan cewa ba su bane dai suka dawo,
Rugaiyyace ta shigo gidan da sallamar ta, ai,daga cikin dakin inna nake saman gado bansan lokacin da na dako wani wawan tsalle ba da yar ihu na nayo waje,
Cikin mamaki tace fadima shin,
Sai ta kalli inna da mariya da mamaki tace yaushe fadima ta zo Nigeria bata da labari,
Rugumay tana yi mun dade rike da junar mu muna irin gaisuwar larabawa,
Mariya sai dariya take muna,
Duk idon mu yakawo kwalla,
Ko ba komai ganin junar mu yasa zukatan mu ya tuna da wasu abubuwa da suka faru da mu a da, can,,,,
Sai can ta sake ni ta juya zuwa waje batare da tai muna wani magana ba,
Ita da mijin ta suka shigo wanan karon har ciki da sauri na koma na dan dauko Naifal di na lailaya, na koma kamar bani bace
Mun gaisa da shi cikin mutunci da girmamawa, ,
Mutumi mai fara,a da kuma son mutane don har ya ja Aisha ta zauna saman jikin shi ko,
Yaushe kika shigo Nigeria fadima nai yar dariyar rashin gaskiya nace mata na kai wata guda gaskiya,
Ta juya inda inna da mariya suke zaune, tace,
Gaskiya baki kyauta min ba ace kina cikin kasar nan amma banda labari haba dai fadima,
Yar dariya kawai nai mata nace mata ai kin san tunda na shigo dole ne in bide ki ,,,
Tace, Ko yanzu tun sati biyu da suka wuce muka so zuwa , mu diba su inna,sai kuma hakan bai samu ba,
Sai yau muka samu lokaci muka zo, ,
Bayan yan gaishe gaishen da mukayi a tsakanin mu da kuma inna,
Sai kuma hiran bayan rabo ya fara,
Nai mata godiyan irin dawainiyar da takeyi da iyayyena, da yan uwa na
Ta ce min fadima duk abinda nai masu kece sila don kinfi nan a gurina, murshi nai mata,
Duk hiran da mukayi da su sam bata gane halin da nake ciki ba,
Nai murna kwarai da na kula da cewa sam bata gane ina da ciki a jikina ba,
Kusan za su wuce ne take tambayana labarin sheriff
Sai da naji gabana ya fadi dam saboda ambatar sunar sheriff da tayi,
Sai ce mata nayi ai nabar aiki a gidan shi tun bayan barinta kasar

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment