Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ita madai din shi tabi ni dashi tana tafiya tace min fadima karfe uku da rabi zan shigo wurin ki mu gyara jikin mu don tafiya zuwa wajen walimar da za,ayi na yan African Youth Found mazauna saudiya saboda tallafawa yan uwa musulumi kasa shen,baka ken fata ,
Nace mata to a zahiri
Amma cikin zuciya sai cewa nayi wanan ba wurin zuwan yar takari ba ce saidai ku masu hali,
Bama zan koyi rigimar cewa zan tafi ba tunda ko mai gidan bai sheda min ba,
Kuma na hadu dashi dazu bai ce min komai ba kenan wanan fitar bai shafe ni ba,
Saidai in ita Amal din keson ta kasa dani,

Hakalina naga littafin da nake karatu na course dina danakeyi,
Hankalina yatafi sosai ga abinda nake nazari akai,
Amal tashigi dakin da yar fara,ar ta ganin da tai min zaune ko niyar tashi don in shirya banda,
Zama tayi gefen gadon da mamakinta ta fisge littafin a hannu na,
Wani irin ajiyar zuciya na sake nadago kaina nazuba mata idona cikin nata,
Lokaci guda na karanto bacin rai a kwayar idon nata,
Muryan ta naji tana cewa lalai ma fadima baki da dama,
Yanzu duk tuna makin danayi cewa zamu fita yau kuma fitan mai muhin manci ne sosai bai sai kin maida hankali ba don mushirya da wuri shine zaki zo ki kama karatun ki,.
To san nu alhudahuda sarkin karatu,
Na, uhum Amal ba hakana bane gaskiya naga cewa sheriff baice dani za,a wanan gurin ba kamar kece kawai ke kokarin zuwa dani,
Dariya tadanyi min mai dan shewa tace o watau ni daban ce da ke yau ko,
Saboda yayanmu bai fada maki cewa, dake za,a ba da bakin shi shine rashin daukar maganar tawa da gaskiya ko,
Murmushi nayi nace a,a wlh ba hakana bane,,
Ta,tare nida cewa hakanane mana,
Jiya da yafada maki cewa zaku fita da bakin shi aikin shirya kun fita mu biyu, ko,
Jin na kaina nayi nace haba Amal ko jiyan ai a hanya ne tafiyan ya hadamu,
Tana mikewa tsaye tana cewa ki dai tashi da iya salon takon ki ki shir kin ji don ba,zaki samu bata lokaciba
Dama tun safe nagane nufin ki kina wani noke ma wanan tafiyan don baki son zuwa,
Gaskiya ba hakana bane kawai dai bani ,,,,
Hannu tadaga min tace min kin makaro yarinya zuwa ba fashi don sai kin je shi,
Fita tayi tabarni da tunane fam azuciya saboda irin canjin yanayi dana nake gani iri ga sheriff din mu
Nifa yar takari ce wana wuri kuma wurine na bada donations ga kungiya to ni mai zai kai wurin,
Wurin da yan kasan Africa daban daban musulumai ke haduwa don tallafawa al,umomin su,
Har na kwanta da niyar ban zuwa sai kuma hudubar salimat yafado min arai nakuma tuna da irin hararcin da sheriff ke min tun haduwa na dashi koma bai ce inje tunda yar uwan shi ce tabukaci inje aidole in tafi,
Wanka nafada yi bayan nafito nadade gaban dressing mirrow, gashi na nafara gyarawa bayan na gama sai na fara gyaran fuska na
Ina gama gyaran fuska sai text din nan na jiya yafado min a raina,
Kayan nadauko nasa nadaura dan ribon din kayan na kama kaina dashi,
Nida kaina nakarewa kaina kallo a,mirrow saina ga ashe rigar tsakiyar ta a matse take ta ciki tasama andan buda ta
Ajiyar zuciya na saukar a hanakali ina kallon kaina wainice fadima inna yar kulu na koma haka yau,
Najawo kit din sarka da aka siya min jiya jiya na daura ma wuyana nasa dan kunen
Wohoho sai kin gani da kanki zaki karasa bayanin yarda na koma,
Daidai lokacin naji anturo kofan dakin nawa, ko ban diba ba nasan cewa Amal ce
Sainace mata Amal kidiba kigani yarda nakoma yau ni fadima yar takari diyar inna yar kulu yar mutan dogon daji, nice,,,,
Bankarasa zancen bada naji shirun yai yawa sai na waiga inga may yasa tai shiru bata ansa min ba,
Sheriff ne tsaye ya zuba min ido cikin shigar wasu kayan Indians Pakistani, farare sol kayan wando da riga kayan sun karbi jikin shi sosai
Takowa yayi a hankali cikin tafiyan shi na kasaita, irin na matasa masu tashen nairai,
Yatako har inda nake tsaye gaban mirrow,
Gyalen kayan yadauko ya mika min yai min alamar in yafa ma kaina batare da yai min magana ba ya juya yafita yana mai kallon agogon hannun shi da yadaura,
Ina gama shiri a bakin kofa nasamay duk cikin shigata alfarma, irin ta musulumai,
Motocin ne guda uku a jere waje kowani yakai akirashu mota,
Dan jin nayi tsaye don basan ko wace zamu shigaba nida Amal,
Salim ne yai min magana kasa kasa yace min waccan farar itace zan shiga,
Ga mamakina sai naga Amal ta nufi gudan motar wadda naga mustapha ya shiga bayan ta itama dai din bayan motar tashiga,
Nadan waiga na kusan nikadai ce a,tsaye wurin don salim har yafara tafiya zuwa motar da zai shiga tare da wani mutun bakon fuska da nagani,
Banda zabi motar da salim yagwada min inshiga itace din na nufa,
Ina isa kusa da motar da driver motar ke rike da gambun motar yana jiran karaso wana,
Ga mamakin da zan gani ciki sheriffudeen din mu ne Ahmad zaune a bayan motar yana waya,
Kamar in,koma baya don fargaba,
Sai kuma, nadaure nai dan kokarin shiga na zauna ahankali,
Batare da na waiga gefen da yake zaune ba na takure gefe guda kamar ankai buzuwa yaye,
Yana gama wayan dan kallo ni a hankali yace ko sanyin A C yaimin yawa ne na takure wuri guda,
Nadan kada kaina alamar a,a
Bai ce min komai ba kuma yadan tatara hankalin shi ga titi ya na kallon hakali kwace,
Mun iso gurin wani babban dakin taro ne da ake kira da King Fahad central, holl,
A cikin larabci akai rubutun,
Nan muka dosa don ni nasan gurin mu kanzo bara ko goge goge, indan anawani occasion, a lokacin da nake takari
Motoci ne birjit agurin ga security nan kala kala, sai mutun yaji tsoro indan bai saba ba saboda irin tsaron da akasa agurin,
Ko ina hasken fitilo ne keta wal,wal,wal suna haska mutane, dake guri kala kala,
Koda mu muka fito daga motar zuwa cikin dakin taron,
Akwai dan tafiya maidan nisa kafin mu shiga cikin dakin taron,,
Tafiya muke yi a jere da juna batare da dayan mu ya yi magana ba, muna gab, da shiga dakin taron naji sheriff din mu ya riko min hannu na, yarike cikin nashi sai sanan yadan rada min akune ne ya ce min
Kinyi kyau sosai, fatima,
Sai naji, nakasa controlling kaina
Kamar a mafarki naji zancen nashi ji nayi kamar in nutse acikin kasa saboda kunya,
Ban tanka ba daidai lokacin kuma ,muka kutsa kai cikin dakin taron wanda ke cike da yan uwa musulumai bakaken fata, na kasa kasa
Shigar mu keda wuya a ka fara taken kasar saudiya, tare da daga tutar su mai photon dabino da takkuba,
Bayan angama malamai kala kala suka dinga jero addu,oin su tare da yin nasiha, akan cigaban addini, musulunci,
Abinda na lura dashi agurin shine duk wanda keda mata ko miji gefen su daban tare da tawagansu,
Wanda kuma basu zo da matan su ba suna gefe guda na maza gefe guda namata,
Saida aka nuna muna inda gurin zaman mu yake ne nagane cewa ashe su mustpha na bayan mu cikin tawagar company Abu Abdallah wanda sheriff ne ke jagoranta su,
A gaskiya tsaya infadi irin kyaun da mukayi aguri bata lokacine,
Yan jarida ne kawai keta faman daukan photo kala kala a,gurin
Zaune nake kusa gab da sheriff din mu idan ka gamu zaka dauka ko wata mata da miji ne sabon aure saboda yarinta na ya baiyana sosai , daka diba kasan cewa Allah yayi hadin shi agurin ,,,,,
Koma mai nawa baka iya gani sai dan round din fuska na kawai ya dan baiyyana afili,,,,
Kowa nata harkan gaban shi sai donations ake ta bayar wa kala kala,
Yawancin duk wanda ke gurin zaka ga yana magana da abokin tafiyar shi,
Banda ni dake zaune gefen sheriff ina ta faman, dan wasa da wayana dake a hannu na,
Banyi aune naji ana kiran sunan sheriff da tawagan shi sufito suba tasu gudunmawar,
Hannu yamika min nagane nufin shi nima sai na miko mai yadan makale hannun nawa cikin kafadar shi muka mike atare, lokaci guda,
Kyauta sheriff ya gabatar irin ta alfarma da bajinta da kuma kulawa da addini,
Inda jama,a keta sa masu albarka dashi da kamfanin su,,,
Andayi hira dashi har ake tambayan shi sunan amaryan nashi nadauka zai ce aziza ko nafisat,,,
Sai kawai naji ya fadi suna na full da mamaki nadan kalleshi cikin dabara, sai yadan kashe min ido guda
Duk wani irin kunya da nauyi ya kamani agurin, duk wani motsinawa yana akan idon sheriff tunda naje gurin banyi magana da kowa ba,
Yana rike da hannu na duk gaisawar da yakeyi da jama,a
Jinayi ana dan tafawa a hankali abayan mu, batare da na diba ba kowaye ba tun da ba wai sanin su nayi ba,
Na ance kai amma ko gaskiya kun dace da hakan aida kace min in bar maka ita din takace bana kowa ba,
Gabana yaba dam don ko ban waigaba nasan cewa wanan muryan Ali baba, ne
Alin ya zagayo da kyau ta gaban mu yasa hannu cikin aljihun shi yana muna wani irin mugun kallo,
Doctor kamal abokin sherrif na gurin bai gane may Alin ya ke nufi ba sai ya ce
Walahi nayi farin ciki da wanan auren na Ahmad fiye da kowani auren da yayi abayan
Don wanan itace daidai da aure ka
Alin da ke gefe yace o ko asai akace yayi kwace ga wani don kawai tazama mallakin shi,
Sai lokacin sheriff yace ma Alin kai dama dan akuya ne acikin mu karasa wacce zaka bida sai wacce keda aure akanta,
Murmushi Alin yayi yace wacce da aka kwace ake shirin aure ko,
Zaici ga ba da magana security din company su sheriff sukazo suka dan jaye Alin din gefe
Inda muka ratsa tagaban shi tare da sauran tawagar mu muka wuce shi cikin mamaki,
Almustapha,ne yai, mai dan bayani a takaice sai yabimu da wani irin kallon mamaki har muka bace mai da gani,
Danaga mun fito daga dakin taron nadauka zai sake min hannu nane sai naji yadan kara rike min su tsam,
Ahaka har muka shiga mota, ranshi a bace akan abinda Alin yai mai ne,
Tafiya motar keyi sit ba wanda ke magana daga cikin mu,
Can naji sheriff yakara kamo yan yatsun hannu na ya dan matsa su a hankali,
Sai nai kokari jaye su,saboda nasan cewa ba abu mai kyau ba ne hakan haramun ne,,,
Amma ga mamakina sai naji ya rike su gam yadan daga kai ya kalle a hankali,
Cikin wata irin murya mai kasala yace min, haram haram kada ki haramta min abinda Allah ya hallata min pls,
Haka na kyale shi yai ta yadda yake so da yan yatsun nawa,
Mun kusa shiga kwanar unguwar mu naji rikon da yai min har yafi na dazu,
Duk jiki sai naji ba karfi, daga rikon hannu sai naji, ya kwantar dani a saman kirjin shi ya rike ni gam kamar zai maida ni acikin zuciyar nashi,
Inajin yadda zuciyar nashi ke bugawa sai wani irin tsoro da fargaba ya kamani,
Ga driver nata tuki mota amma sai,nake ganin cewa kamar a tsaye yake wuri guda ba tafiya yakeyi ba,
Duk na storace na shiga wani yanayi nadaban wanda ban taba shiga ba,
Saida motar ta tsaya naji yai wani irin ajiyan zuciya madan sauti,
Sai a lokacin nasamu ya sake ni a hankali,
Inajin yasake ni, ban ko tsaya jiran wani abuba na balle gabun motar
Dai dai lokacin naji muryan shi cikin kasala yana ce min Shukuran shukuran nafita da sauri,
Bina yayi da kallo har na bace mai da gani sai yakoma yadan jingina bayan shi da sit din motar ya lunshe idon shi
Sai yaji yadan tabo wani abu daidai inda nayashi ashe wayanane nabari saboda sauri,
Daidai lokacin da zai dauki wayan nawa ne yaji massage ya shigo mai atashi wayan
Batare da ya diba ba ya shiga cikin gida
Dakin shi yawuce harda wayan nawa,
Saida ya kan,mala komai yafito falo dauke da wayoyin mu a hannu shi,
Alokacin ne yabude wayan shi don ganin sakon nidake gare shi,
A sako na hudu ne yaga wani sako da Amal ce ta turo mai shi,
Yabude don yaga kowani irin sako ne taturo mai,
Photo mu da ta daukeni ni,dashi da baby asama,u, lokacin da aka haifeta zamukaita asibiti,
Saida ya gyara zaman shi da kyau don photo ba karami burgeshi yayi ba,
Waya na ya dauka daniyar yakaimi abina,
Da sallama ya,shigo dakin kwance nake rub da ciki tunda muka dawo inata gaman fidda hawayen takaici da bakin ciki may yasa sheriff yai min hakana vc.
Sai kuma naji muryan shi adakin dai dai wanan lokacin zubur nai niyar mikewa daga kwan ciyar da nayi,
Zama yayi gefena tayadda babu dama in tashi zaune
A hankali yace min may yasa nake kuka don ya taba ni ko kuwa don ban so,
Ya cigaba da fadin in yi hakkuri komai naga yayi da sannu zan gane manufar shi,
Sai dan mike tsaye tare da aje min wayana gefen bedside,
Yace inkula da kai pls saida safe,
Duk kan mu wanan daren ba wanda yai barci a cikin dadi don kowa da abinda yake tunawa,
Ba komai sheriff ke tuna ne ba sai wanan photo da Amal ta turo mai photo da yasa duk hankali shi yau yakara tashi,
Ba abinda yake bukata da muradi arayuwan shi yanzu kamar a ce matar shi tasamu ciki,
Niko ina can ina cewa wai ko sheriff na cikin hankalin shi saboda duk iya sani nada shi ban taba ganin shi ko jin yayi wani harkan banza agabana ba
Sai yau ko yau din ma yana kirarin cewa wai kada in damu ,
Hmm aiko dole ne indamu da haka naita sakawa ina warwalewa, nikaida sai Aisha dake gefena kwance tana barcin ta hankali kwance sai naji dama ace nice ke barci haka hankali kwance,,,

Washegari muka wayi gari da babban bakuwa, Aziza ce tazo daga Dubai don ita yanzu can tafi zama, da tana zuwa Nigeria kaida kai amma yanzu ta daina,
Zuwan ta yasa nadan saki jikina kadan wai ni ina gudun tagane abin da yafaru ni da mijinta,.
Sai har yanzu ban iya hada idona sam da sheriff saboda wani irin mugun kunyar shi da nauyin shi nake ji sosai walahi
Da ina da dama dana koma madina in karasa hutuna acan don zaifi min
Shiko ina lura da shi da munda hada ido ko nai wani dan motsi sai yadan wani lunshi idon shi,
Don hakane ma na koma daki abina ban kara fitowa ba,
Photo da Amal ta turo mai ne ya dauka yake nunawa Aziza yana mata bayani akan photo,
Saida ta kalli photo tsab sai wani tunane da tadade tanayi ba mafita yafado mata a rai
Cikin wani irin yanayi ta dan gyara zaman ta don taji dadin yin nazari akai

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣6⃣
*BY*
🐎 *ZAINAB *IDRIS**MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP 🐎

Almost true life story,,,,

Tabbas wanan yarinya yakamata ta taimaka mata, badon komai sai don hakan zaifi mata sauki da rufin asiri,
Ganin da tayi cewa sheriff din mu yayi barci mai nauyi yasa fito daga dakin
A cikin duhu take tafiya saboda kashe duk wani haske dake falon da akayi
Saboda koyi da,sunnan maikin manzo sallalahu alaihim wasallam,
Sai yanzu nake jin yuwa na dan damu , dama bani abu bane abinci drink's ne nake yawan sha, da corns,
Don haka na tashi nafito falon gidan don inda samu abinda zan agaza wakaina, dashi,
Dayake ahankali nake tafiya na sai naji kamar ana magana kasa kasa acikin falon don haka sai nadan rage tafiya na don jin kowaye, cikin wanan uban dare,
Ga mamaki na sai naji muryan mace kuma da harshen hausa take magana,
Kara matsawa nayi daidai gurin da sautin ke futowa,
Aziza gabana yaba da dam,
May takeyi haka acikin dare koma dai may ye sirine bata son kowa yaji ta,
Har zan juya sai wata zicuya tace min indan dakata inji ko da kadan ne,
Murya kasa,kasa take cewa Hindu na fada maki cewa bazan samu matsalaba ga wanan yarinyar insha Allah zata yi yadda nake so,
Hindu tace Aziza wanan maganar ba karamar magana bace fa, maganace da ke bukatar siri acikin ta,
Kinga ko gara mufita waje can mu samo wacce zata yi muna aikin mu cikin rufin asiri batare da kowa yasanaikin
Sai, Muba ta kudi mu sallame ta tayi gaba in bukata ya biya,
Azizs tace hindu wanan yarinyar itace zata iya zama dai,dai da nufin mu, baki ganewa ne shiyasa,
Hindu, tace kidai bari mu, mukara dibawa ko zamu samu wacce ta dace da aikin
Haka sukai ta sakawa suna walwalewa a tsakanin su,,
Ina labe ina jin su duk jikina yai sanyi kamar in zunduma ihu,
Ban gushe daga inda nake labe ba naji motsin Aziza alamar tagama waya zata dawo, dakin su,
Shan jinin jikina nayi na lafe a bango, saida tazo dai kusa da inda nake labe sai kawai taja ta tsaya dai gurin,
Gabana yafadi dam don a,zatona tagan ni ne har na rufe ido na ,nasadakat kawai ta gani,
Shirun da naji yasa nadan diba sai naga a she, wayan take kashe,
Saida naji takon, kafarta ta wuce har ta haura sama dakin su ta rufe,
Nai ajiyan zuciya, da sanda na la,laba nadauki lemu na koma daki na hankalina a tashe,
Juyi nake tayi barci ya ki dauka na, sai, Tunane kawai nake saboda bansan kowa ni irin shiri ba ne zasu ai,watar, hakana,
Hakana na kwana da wanan tunane cikin zuciya na sai sake sake nake tayi har gari yawaye,
Tsakani na da sheriff tunda wanan abin yafaru tsakanin mu bamu kara haduwa ba,
Sai na bari rana yayi nasan cewa yafita zan dan fito waje,
Yau nasan cewa yatafi ma,ia,katar su ta Riyadh aiki,
Don yaune ranan zuwan shi can Riyadh din sai ya kwana biyu ko uku zai dawo garin makkah,
Wando da riga nasa wandon jeans baki ,mai kafar pencil sai yar wata riga da nasa wanda tsawon, rigan yatsaya min iya gwiuwa na, hannu shi ma hakana ya tsaya min,
Bakin gyale na daura a kaina, sai fuskana da ban mai wani makeup ba,,,
A hankali na,tako zuwa falon gidan Salim na samu zaune, yana kallon wani shirin na Arabs got talents,
Sai Amal dake gefe tana waya cikin kashe murya kamar wacce batason aji may take fada,
Gefen salim na zauna don muyi kallon tare, ban wani dade da zama ba, wayana yadinga tsuwar alamar kira in agaza mai,
Salimat ce takirani dan ihun murna nayi don jin dadin jin ta, danayi
Dauki wayan ina fadin maman As,mau nayi fushi gaskiya,
Tace ,a,a haba dai fadima idan kinyi fushi dani ai ko na shige su,
Nace kawai kin wuce, abinki ko ki tuna da mutane
Tace fadima kin san matsalar Nigeria har kauye saida naje gashe su, wani guri babu ko services da zan kira ki,
Yanzu ma mun dawo kano ne shine,nace barin kira ki mu gaisa kiji motsin diyar ki,
Munyi hira sosai har ina ce mata gaskiya na matsu ta dawo walahi ina kewan ta so sai,
Amal da tagama waya ta zagayo ta baya na ta fisge wayan ta shiga yiwa salimat ,sheri
Karshe dai taba mu hakkuri tace muna zata dawo bada dadewa ba Insha Allah,
Saida muka natsu daga dariyan salimat da muke yi ne,
Sai Amal ta jefo min tambaya wai fadima lafiya bakya fitowa waje duk kwana nan,
Salim dayaji tambayar Amal sai na ji yana dan gyaran murya kamar wani mai shirin yin magana,
Gaba dayan mu mukai diban mu gare shi, don ji ko ganin may zai ce,
Dariya yakama yi yana ce muna ya mukr kallon shi haka,
Amal tace fadi dai muji may zaka ce, kada kabari a ciki ya kashe ka, kai daya,
Sam ban gane mai yake nufi ba sai naji Amal nace kai dai kace ba ni nace,
Aji shi a bakin ka ba ruwana,
Kafin wani da cikin su yakara fadin watakalma Aziza ce tafi to daga sashen su cikin shirin fita,
Daya daga cikin wasu saitin kujerun da ke can gefen mu ta zauna a saman guda,
Waya takeyi tana wani murmushi tana gyara rigar da tasa da kyau,
Duk hankalin mu ya gurin kallon TV da salim keyi,
Amma dai gaskiya muna kallon ta ta wutsiyar idon mu,
Tundai ni da na ke fargaban shirin da naga tana kokarin aiwatar wa, a boye,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment