Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni,
Mamaki duk ya cika ni jin cewa wai shine daki na,
Cikin mamaki da kuma nuna hankali nake karewa dakin kallo,
Fitar Amal ya bani damar cire kayan da ke a jikina a, hankali don duk a gajiye nake a lokacin,
Sheriff ya shigo dakin a lokacin shima a gajiyen yake saboda dan bata lokacin da jirgin mu yayi a Dubai kafin ya taso,
Ta bayana yadan zo yana kokarin tayani cire rigar,
Saida yaga ya cire saura yar breezeir kawai da dan bujen ciki yasa ya dan kyale ni, rigar barcin da nagani a saman gado nadauka, na sa ajikina,
Sai a lokacin na fahinci cewa ashe wai daki guda zamu zauna da ni da sheriff ,
Tirka shi, ga ummi ga su salim da Amal zan zauna da shi daki guda
Gaskiya da sake bazan iya ba sam
Yagane mai nake nufi sarai, saidai bai nuna min yagane ba, wanka yaje yayi yana fitowa ina zaune bakin gado har yanzu sai ce mun yayi bangaji ba ke nan tun da ban kwanta ba ko,
Nadai san cewa bazan yi wanka ba a cikin daren nan ba, ko,
Saida na dan bata rai nace, ni gaskiya dakin Amal zan koma,
Kafin in wani maga sai kawai naji ya kwantar dani ta baya a hankali,
Bada son raina ba dole na hakkura hakana na kwanta tare da shi daki daya,
Duk da gajiyan da muka kwaso hakan bai hana mu farkawa da wiri ba don yin sallah a suba ,
Sai dai ina idar,wa na kara kwantawa kuma ,sai wani barci mai nauyi yakara daukana,
Yuwa kawai ya sani farkawa, da ga barcin,
Wanka nayi nafito cikin shigar wata doguwar riga irin ta matan Brazil,
Rigar light blue ne, har kasa take saidai hannuwan ta shara shara ne haka bubude, cotton ne sosai sai wani sulbi da yauki takeyi, nasa yar gyalenta na daure kaina,
Saida naci abinci so sai na koshi a lokacin ne, nake tambayar anty falmata,,
Amal ke sheda min cewa ta koma gida tun bayan wucewar mu da kwana uku,
Gaskiya banji dadi da ta wuce bani a gari ba don,
Salimat da ke gefe take ce min fadima waiko kinga yadda kikawani kara girma ga fari dakikayi,
Kinyi wani kyau sai kace irin matan nan da muke gani a TV ko muji rabarin su,
Murshi kawai nai mata nace aike dama kullun haka kike cewa idan kin kwana biyu baki gan ni ba,
Tace gaskiya wanan daban yake, ba kamar na kullunba Allah sai kace an maki wani famfon girma,
Duk muka dara gaba dayan mu dake a cikin falon

Mun dawo bamu wani dade ba sheriff yakoma harko kin sa,
Sosai yanzu arzikin sa ke ta bunkasa kamar daga sama,
Ikon Allah ke nan, don har yan uwan haihuwan shi su suraj yana kokarin taimaka masu
Duk da hassada da bakin cikin da hjy mama ke nuna mai hakan bai hana shi sasu cikin harko kin shi ba,
Don suma din sungane gaskiya tunda wayayyu ne ba su bari hjy mama ta ruda su ba,,
Mahaifin su yaji dadin wanan abin da Ahmad yayi wa yan uwan shi ya sha albarka so sai da fatan alheri ga tsohon,
Hankali na a kwace na ci gaba da harkokina sosai saura yan kwanaki mu gama karatun mu,
Gashi da mun gama zasu tafi Nigeria don daurin auren Amal da Almustapha da za,ayi a can mahaifar su, Amal din,
Ranan da na samu wanan labarin gaskiya nayi farin ciki sosai saboda nasan cewa Almustapha mutumin kirki ne ,
Kuma gaskiya sheriff yayi dibaiya so sai wuri bashi yar uwan haihuwar da ya aura,
Almustapha mutumin kasar Sudan ce , gurin aikin su guda da sheriff yana zama a matsayin yaron sheriff ne,
Hakan sai wani shakuwa da yarda yashiga a tsakanin su,
Har abin yazama masu kamar zumunta,, mai karfi a tsakanin su,,,
She nice ban sani Amal sun dade suna soyayya da almustapha ,
Wani irin rana ake fatsamawa agarin kowa kagani yadan samu wuri yadan boye ma wanan zafin ranan,
Don haka nima ina fitowa daga exam nakira driver mu na ce yazo yakai ni gida,
Don haka, a cikin wanan ranan nadawo daga makaranta a gajiye nake saboda nauyin da cikina yafara yi min ga kuma zafin ranan da akeyi, yau din
Ina shiga gida dakina na fada da niyar in tube kayanan jikina inda watsa ruwa ,
Aziza ce kwance a she me,me tayi da daya a saman gadona tana waya abinta hankalin ta kwan ce
Da yar mamaki makale a fuskana, na tsaya sororo tsaye ina kallon ta,
Allah yabani ikon karanto mata addu,oin kariya daga duk wani sherin dake tare da ita,
Cikin daurewa nai mata sannu da zuwa
Hannu kawai ta daga min batare da ta ansa min ba,,
Ganin danayi wulakanci take son tai min kawai yasana juya daniyar in fita waje, sai ce min tayi daga yau kada inyi gigin cewa zan tako mata daki,
Da kyar na iya lalubo na tsuwata wuri guda nace mata dan Allah tayi hakkuri bansan cewa tana ciki ba,
A hankali nadawo baya ina mai rufo mata kofar dakin,
Duk gajiyar da na debo da zafin da nake ji sai na bide su na rasa, alokaci guda,
Wani irin duhu da na tashin hankali nake gani don gani aziza ba alheri bane gareni,
A hankali nake tafiya cikin yar doguwar corridor da ke sada mutun da daku nonin gidan
Zuciya tab da tausayin kaina saboda dama nasan ko mijin suwa na aura,
Daga Aziza har nafisat na san su nasan halin su,
Jikina gabada daya yayi san yi na rasa ma wani guri zan dosa a lokacin,
Maman Umar ce ta fado min a rai gurinta na nufa kitchen,
Itama din tana gani na ta taso cikin sauri ta tare ni, tace min cikin larabci kada in nuna ma Aziza nadamu da zaman ta a dakina ko kadan tace min ta gyara min daki guda dake gudan bangaren mu,
Murmshin karfin hali nayi mata nace mata aiba komai rayuwace duk hakan,
Maman umar ce ta jagorance ni zuwa dayan dakin kusan komai na dakin iri dayane da wanda nake a ciki,
Saidai dan banbanci kadan dakuma irin kayan bukatu da yasa min ciki,
Ko wanka da nake ma sauri banyi ba na fada saman gado na kwanta a hankali,
Ashe tun fita har dawowan mu da maman Umar Aziza ta labe tana kallon mu,
Tai wani dariyar mugunta ta koma cikin dakin tana karewa dakin kallo saboda irin tsaruwan da dakin yayi,
Tai mamakin yadda sheriff ya haukace akan yar karamar yarinya alokaci guda,
Mai wanan yar kwailar yarinyar keda shi wanda ita bata dashi har yake rawan kai akanta,
Zanyi maganin ta in har don wanan cikin yake wanan rawan kai haka zata barar da cikkn kowa ya huta,
Don ta riga tasha alwashin cewa bata barin garin nan sai taga cewa ta halaka cikin dake jikin na ni, fadima,
Idan yaso tasan kuma yadda zata raba wanan aure da yake ikirarin cewa ya dade da,aure bada sanin ta ba,

Niko tunda naga aziza tazo sai nake tsoron cin komai na gidan duk da maman Umar na iya kokarinta wurin ganin cewa
Tana kula da duk wani tako da kuma kulli da Aziza keyi, akaina,

Gurin Salimat nake yawan zuwa inci abinci kafin in dawo gida, ko kuma kafin in tafi school sai in biya incika cikina fam, in wuce,
Sannu a hankali maman Umar ta san kwaso min wasu kayan bukata na tadawo min da su cikin dakin da nake zaune, a yanzu,
Ganinda Aziza tayi cewa duk wani kullin da takeyi bai ci yasa ta sake min fuska faran faran,
Duk da yarinya nake hakan baisa na yarda da shimfidar fuskan sherin da take, kulla min ba,
Satin Aziza guda a gidan ,duk su Ummi har Amal ba su san cewa ba,a dakina nake zama ba,
Kuma gashi kusan ko,yaushe muna tare da Amal amma ban taba fada masu cewa ai Aziza adakina take ba,
Sai a yau da Amal tazo gurina ansan hand dryer dina saboda nata yadan samu matsala,
Da yar sallamata tafada dakin kamar yadda mukeyi a kullun,
Ganin mutum tayi saman kadon tim kamar antara kayan wanki, wuri guda,
Duk da tasan cewa ciki ke gareni amma dai ban kai ko kwatan haka tari ba,
Da mamaki ta isa har bakin gadon tana kare ma aziza kallo cikin tsana da kiyayya, take mata kallon raini,
Takara juyawa takalli dakin tsab taga cewa ba wani alamar da ya nuna cewa na kwana acikin dakin,
Cikin sauri tafito waje zuwa wurin Ummi don ta fada mata cewa bata ganni ba a daki na sai dai aziza dake kwance,
Maman Umar da ta dauko min abin breakfast wanda ta kasa ta tsare a kitchen din ko gusawa bata yarda tayi ba saida ta gama min komai tadauko zuwa dakin da nake ciki,
Ina zaune dagani sai yar doguwar rigar barci har kasa mai yar kuntun hannan shimi,gefen rigar ta kasa andan tsa, tsaga ta, kaina babu dan kwali,
Kusan atare suka shigo dakin ina zaune a gaban mirrow da waya a hannu na,
Cikin mamaki da masifa Amal take min wani irin kallo ,
A hankali maman umar ta aje min abincin a saman wani dan stol ta na kokarin gyara dakin ,
Amal tace min cikin fada fadima ban gane ba shin da yardan ki Aziza ta zauna maki a daki ko kuwa ,
Saboda may zaki dawo wanan dakin ki zauna kibar mata dakin ki,
Murmushi nai mata na jawo dan teburin abincin a gabana wanda, nadade banci abincin gidan ba,,
Kafin in bata ansa maman Umar ta kwashe yadda akayi tun ranan da Aziza ta iso muna school ummi tace a kaita dakin da sheriff yace a dinga aje baki nagida,
Amma sai tace ita ina ne dakin Sheriff maman umar tace mata ai daki guda muke
Sai tace to ita a nan zata sauka,inda sheriff yake, da tace mata to ni fa sai cewa tayi wai in koma dakin baki
Dakin sheriff nata ne ita dashi fadima bata kai matsayin da zata zauna inda taje zama ba,

Da sauri Amal ta juya cikin fushi tabar dakin nawa, A dakin Ummi ta samay ta rai a bace take mayar ma ummi da komai dake faruwa agidan
Hakalin UMMI yatashi matuka don sam bata zaci hakan ba daga Azizan,
Ina kwance a daki kasan cewa yau ban shiga school, yasa da nagama abin da nakeyi sai na koma na kwanta , saboda in samu indan huta,
Jin sallaman Ummi na daga sama a cikin dakina nayi mamaki kware har na nuna mata hakan a fuskana,
Mikewa nayi zaune daga kwanciyar da nayi, ina mai gaida Ummi, dake kokarin zama saman yar kujerar da aka a je a cikin dakin
Shiru yadan biyo bayan zaman nata,
Can takira sunana a hankali tace may yasa kibar ma Aziza dakin ki
Alhalin kisan cewa wana dakin shine dakin ki na halal malal,
Saboda ko wanan gidan saboda ke ce yasa aka gyara shi,
Idan har ba zata zauna inda yace na baki ba da ai sai ta koma inda tafito
Don ni ba ga abinda yakawo ta wanan garin ba tun da Alhajin karami baya kasar, ban san zaman may take anan ba,
Saida na barin ummi ta kare zancen ta duk kai na yana a kasa,
Can nadago kaina ido na sunyi raw ,raw alamar kuka ,
Nace , La, ummi ai ba komai anan din ma inda nake babu wani matsala gaskiya,
Ummi kinsan cewa ita ce, matar sheriff, itace ta can can ci zama a wanan dakin bani ba,
Ummi kinsan cewa aurena da Sheriff kawai nufi na ubangiji amma ai ni ban kai matsayin auren shi ba,
Ummi tace min assha, fadima aure ai baida wani can,can ta ko sa,ayi,
Abune mukaddari daga Allah,
Idan har kikace haka to gaskiya baki godewa Allah da ni,imomin da yai maki ba,
Nace a hankali na gode mana Ummi, baga shi ko ina godiya akai ba,
Dan murmushi na manya mai nuna cewa yaro dai yaro ne tai min,
Tace fadima wa,yan nan kishi yoyin naki da kike gani basu san Allah, don basa aiki da maganar Allah,
In bashi ba gaskiya da batayi wanan abin kunyar da tayi ba
Donko kowa yasan cewa ai ba dakinta bane dakin ko,
Son zuciyane kawai irin na marasa tsoron Allah, wa yanda basa tsoron gamuwar su da Allah
Aida tana da imani da ta tausaya maki acikin wanan halin da ki ke ciki haka,
Amal ko tana waje sai faman kiran layin dan uwan su takeyi bata samu ba,
Sai a na karshe ne tasamu layin nashi ya shiga,
Bayan sun gaisa ne take tambayar shi ko yasan cewa aziza tana saudiya kusan sati guda,
Yadda yai ihu mamaki saida Amal taji shi,
Yace nafada mata cewa ina na turkey muna kokarin muga cewa duk kayan mu ansa a conterner neno anturo muna dasu gaba daya,
Maimakon Amal taji yai magana sai taji kawai ya ma kashe layin nashi gabadaya,
Dif kake ji,
Wani haushe yakamata tadan kali wayar tai tsaki,
Tace in fa yayan mu yasan cewa bazai iya daukar wanan amanar ba gwara kawai saki diyar mutane
Don kada su taru shida matan shi su cuta min, tunda duk sun fini wayo da sani ta duniya,
Azizs na daki abinta hankali ta akwance sai waya takeyi ta yarda zata samu ta samu, sa,ata taci
Nasarar lalata min cikina ko ta halin kaka, sai taga bayan cikin nan,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣6⃣
BY
🐎 *ZAINAB*IDRIS *MAKAWA*
🐎 *HUGUMA* *GROUP*🐎


Almost true life story,,,,


Jirgi dare ya biyo zuwa saudiya, A, Riyadh ya sauka ,
Daga Riyadh, shiga mota sai madina,
A madina safiya tai ma shi,,a cikin gidan mu,,
Mudai mun tashi munga bako don mun san cewa saura kusan sati guda ko kwana goma yadawo,
Tsaye nake bakin dressing mirrow dina ina dan gyaran jikina saboda ina son inyi samako zuwa wurin salimat inci abinci,. Don yau natashi ina jin yunwa sosai,
A, hankali yaturo kofar dakin cort din shi na sagale a kafadan shi, hanaye shi zube a cikin aljihuwaye shi,.
Waigowa nayi don inga kowaye yashigo min daki a lokacin,
Kafin ma in karasa juyawa hanncina ya isar min da sakon sheriff ne,
Mamakin gani shi na yi a wanan lokacin da safe haka,
Don nasan cewa badai ta madina yai landing ba don da Salim ya tafi dauko shi,komai dare
A hankali yatako har inda nake tsaye yazo ya rugumay ni ta baya,
Yana kokarin juyo dani don in yi facing din shi da kyau,
Cikin yar siririyar murya nace mai sannu da zuwa ya hanya a lokaci guda,
Dan murshi yayi dai, dai lokacin da ya man na bakin shi cikin nawa yana fadi a hankali wani zan ansa maki cikin gaisuwar,
,Alokacin kuma maman Umar ta turo dakin don ta kawo min abin breat fast,
Takoma da baya cikin sauri tana fadin muyi hakkuri batasan cewa yana a ciki ba,
Asalima dai batasan yadawo ba, daga tafiyan , ganin ta baisa ya sake ni ba niko duk nauyi da kunya ya rufe ni,
Ta koma da baya baya, tana mai bada hakkuri tajawo kofar dakin,
A lokacin yakara dan matse ni cikin jikin shi sosai, ya dan sun sunan kamshina yana wani lunshe ido,
Amma sai na dan jaye jikina dagana nashi a hannkali, cikin hikima
Sai yadan tsaya tsaye sororo yana kallo na,
Najuya da niyar indan gusa daga gare shi kadan,
Sainaji ya riko min hannu na ta yadda bazan iya juya wa ba da kyau,
Kokari yayi mu hada ido amma sai na kasa saboda gaskiya bazan iya ba don har yanzu mugun nauyi da kun yar sheriff nake ji,
Murmushi yayi yadan kalleni cikin tausayi yace min,
Fatima bakiyi murnan dawo wana bane,
Nadan dago da sauri na kalle shi nace saboda may,
Sai yaji kawai na bashi tausayi, don ko ba komai yasan cewa ina bukatar kulawa so sai a yanzu, da cikina yafara girma sosai
Kuma gashi wana yar ballija,un ta zo ta takuramin,
Sai a lokacin yakare wa dakin da nake ciki kallon a hankali,
Sai yaji wani mugun tausayina yakara shigarshi,
A lokaci guda yaji sam bai kyauta min ba ,
Saiya dan tsaya jin yana dan tunane da nazari,
Yarasa abinda zaice min sai ya sakar min hannu, a hankali,
Wanan lokacin ne rana na farko da yaji yaji kunya na da nauyi na sosai, aran shi
Ada kam baidauki wai don ya aureni zai sa yaji wani abuba akaina, ba
Sai gashi yar karamar yarinyar da yake ji yake kuma gani kamar bata da wayyo , tana batun wuce wa da lissafin shi,
Yau yana jin kunyarta da nauyin ta, sosai
Don yasan cewa an raina mata hankali da yawa kuma baisa tace zata dauki mataki ba, akai,
Ko ta kirashi ta fada mai abinda ke faruwa, ko da a waya ne,
Kenan ta bar mai hukunci a hannun shi, sai yaji wani iri a ranshi yace kada Allah ya kamani da laifin hakkin wanan yariyar fa,,
Bakin mirrow yasa mu yadan zauna kadan, yana facing di na,
Cikin son mu hada ido yake har yanzu , duk na gane nufin shi sai naki daga kaina
Niko sai kokarin gyara Nafal dina kawai, nakeyi batare da na kalle shi ba,
Sai lokacin Yace min fatima lafiya kika dawo wanan dakin da zama,
Cikin mamaki na dago kaina a hannkali na dan kalle shi don tambayar ta zama ta rainin wayo ko hankali,, nake gani,
Yakara nanata tambayar sai na dan dago kadan cikin sanyin murya nace mai ba komai,
Yanayin muryan danayi dole taba mutum tausayi so sai ,,,
Sai yace to may yasa ki ka dawo nan din kuma,
Can fa yafi maki nan, don kinga nan ba wani abin da akasa sosai don jin dadin ki,
Shiru nayi, saikuma na ga kamar ai baisan cewa Aziza tana gidan ba shiyasa,
Yake min mugun tambayar nan, da nake jinta har cikin raina,,,
Ji nayi ya kara riko min hannu karo na biyu,
Yace min ko dakin bai maki bane,,,
Sai nai rau,rau da ido na kamar mai shirin kuka nace
Matar ka fa ke ciki wancan dakin , tayaya zan zauna a ciki tare da ita bayan tace wanan dakin baidace dani ba
Saboda dakin kune kaida ita,
Asalima ita sam bata yarda da cewa ka aure ni ba don bata da wanan tabbacin,
Cikin hasala gami da mikewa ya ce may yasa baki kirani kin fada min cewa Aziza tana gari ba don in dawo ,, cikin lokaci,
Kinsan fa cewa Aziza zata iya maki komai don ba tausayi ke gare ta ba,
Nace banyi zaton cewa zata iya kai har war haka agarin nan ba don baka nan,
Shiyasa ban kiraka ba saboda nadauka cewa zata tafine bayan kwana biyu,
Yaja dogon nun fashi yana kokari cire nicktie din dake a wuyan shi,
Sai a lokacin nadan daga kai na kalleshi nace mai, ai ba komai tunda ita bakuwa ce idan ta gama abinda takeyi, tafiya zatayi,
Wanan kalami da nayi yafi komai nauyi a tare da shi,har wani dan gumi ya ke keto masa ya rasa abinda zai ce min,
Yai dan tagumi ya kura min ido yana nazarin wasu abubuwa, da ga zuciya na
A hankali na ce mai don Allah kayi hakkuri, ina son in karasa shiryawa don zan fita school ne,,
Sheriff yace haba Fatima wanan hakkurin da kike bani yana kara min kunya da nauyin ki,
Ki daina bani hakkuri dan Allah,ke ce yadace in baiwa hakkuri da zalluntar da Aziza tai maki,
Ke da dakin ki da komai na sirin ki a ciki tasa kikafita kikabar mata daki
Kikadawo nan ki zauna saikace wata bakuwa ko wace batada iko da gidan ta,
Wanan gidan naki ne don ki na saya don farin cikin ki da na yan uwana,
Ita na ta gidan na Dubai da Abuja don tace bata iya zama a saudiya saboda zafi da kuma yanayin garin da bai mataba,
Niko kinga zamana anan yake saboda anan Allah ya tsagamin arzikina,
Kinga ko dole in gyarawa iyalina inda zamu zauna cikin don rayuwa tare da yan uwana,
Dan murmushi nayi mai,irin mai, nuna alamar bakin ciki azuciyar mutum,
Nace bam cancanci kabani hakkuri ba sheriff saboda ko da can nasan wanan rayuwar zai biyo baya daga matan ka,
Babu wacce ban san abinda zata iya ba da wanda baza suyi ba,
Don haka don nadawo nan ai ba wani abu bane saboda duk cikin gida gudane kuma dan bambancin dakin kadan ne kawai,
Saboda haka duk wani cin fuska da aziza ko nafisat za suyi min zan hakkura dashi matsayin ba rayuwata ko lafiyata zasu yi kokarin tabawa ba,
Da sauri ya rufe min baki yana fadin ki daina fadin haka Fatima ,
Ya dade rugumay da ni a jikin shi yana dan shafa min baya kamar wacce tai kuka ake lalashi,ta,,
Sai kuma ya sake ni

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment