Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wayanta kara yin ruri alamar kira nabiyu ya kara shigowa kuma,
Shi yai min received ya kara min a kune na,
Abin mamaki wai muryan Sheriff din mu naji radam awayan nawa yana sallama,
Saida nadan daga wayar nakalla cikin mamaki sanan nakara sawa a,kune na,
Jinayi yana ce min ya muka isa nace mai lafiya,
Kafin yai wani magana namika ma Amal,
Saina koma gefe ina mamaki, don ance kira saida sim to aini ko sim din bansa ba balle insa kudi,
Abinda yafado min arai shine kafin mu bar makkah a daren jiya su sheriff da Salim suna zaune nazo wucewa Salim ke cewa sai faman rike waya nakeyi kamar wace za,akira
Yace min inbashi wayan ya gani na mika mai naga yafara game sai nawuce na barshi da ita, kawai
Sai zuwa zan kwanta nazo nasamu wayan an aje min samar wani dan tabur dake gefen kujerar zaman Sheriff inda yake yawan zama ya bude system din shi,
Anan nasamay ta aje nadauka ina gode ma Allah nafisa bata gani ba, aida yau narasa wayan ke nan,,,,,
Ban kai karshen tunanen ba naji muryam Salim nace gashi zan bata,
Dama da larabci yake min magana ni dashi dinma yacigaba dayi min ko yanzu,
Yafada min cewa kada mu makara gobe zuwa wurin da zasu don Allah inyi sakko in kai su na ansa da fadin na,am insha Allah,, da haka yakashe wayar yana mai min godiya
Wayar nabida kallo kamar yau na fara rikata mamaki fal a,zuciyana,
Amal tace min aiko tunda yawa na da sim zata kira wasu kawayen ta da sukayi karatu a FGC bauchi tare , saboda ta fada masu cewa itakan tana saudiya,
Ganin mamaki a fuskana Salim yace min halan bansan cewa ansa min sim bane , yace min jiya Yayansu yasa min sim sabo yakuma yi loading din kudi saidai baisan ko nawa bane a ciki,
Bamu dade ba muka kwanta saboda musamu zuwa inda zamu da wuri da safe,

Karfe takwas na safe yai muna a office din mutumin inda ya kaimu wani guri da za,ai muna interview,
Nikan yar rakiyace don haka binsu kawai nakeyi hankalina kwance sabanin su danaga duk sun shiga damuwa, sosai
Kwantar wa Amal da hankali kawai nakeyi,,har nasamu naga tadan shiga natsuwa,
Lokacin da aka kira su sai na zauna ban tashi na bisu ba,
Mutum ya waigo yace min in yasauri mana intaso kada muyi delay
Na dan waiga gefena inga kodawa yake magana sai naga tabas dani yake saina ce Ana, yace min Na,am
Da mamaki natashi na gyara nabisu baya tare muka shi mu uku,
Abu na farko da na lura dashi shine sun fara diba shigar mune, sai kuma natsu,
Bawani dongon tambaya sukai muna ba sundai tatace takardun dake gaban su cewa mudin ne bawasu bane,
Don haka suka ce muna mufito waje,
Mamaki min fal a zuciyata don ban san ko may ke faruwa ba,
Mutumin da yai muna jagora ne yake ce muna gaskiya munyi sa,a sosai saboda shigar da mukayi ya nuna masu cewa muna da kamala kuma sun auna tarbiyan mu sunga ba mu da matsala shiya sa muka samu saukin interview din,
Amal ce ta kallo ni don ina ganin ta tuna da yadda mukayi jafin mubar gida dazu
Don wani dogon riga tadauko English wear zata sa na ce ma, la,la,la,
Kada tasahi nazaba mata wani dogon jallabiya baki maidan adon duwatsu bakake naba ,sai ta kama ce min ita gaskiya bata iya wanan shigar tamu kulun mutun ko yayi kwaliya mai kyau sai yadauko wani bakin riga cen ya aza sama,
Ban kulataba na gyara mata rolling dinta baka ganin komai nata sai dan fuskanta kadan duk da bataso bataki tanawa ba,
Munfito falo naga Salim da wandon jeans da riga yar karama duk ta matse mai damtse hannunbshi surar jikin shi yafito,
Shima magana nai mai yai kamar zai make ni da dan filon dake kan kujerar falon sai nadan kauce ina dariya
Amal tace mai nima kaga yadda tasani shiga kamar wata yar shi,a can
Zuwa yayi yasako jallabiyar shi fara, tare da yar fullashi fara,
Yafito nace mai to ko kai fa, ya zakazo wa mutane haka kamar mai zuwa wasan wrestling,
Dariya mukasa muka sa gaba dayan mu, sai muka, fita zuwa wurin mota,
Hannu na Amal tarike gam batare da taimin magana ba,
Har muka gama komai tana rike da hannu na cikin nata,
Saida muka shiga mota don dama mun fitogaba dayane da niyar komawa gida,
Amal take ce min kai Fadima anya kuwa, ke ba,, sai kuma tai shiru,
bataci gaba da magana ba,
Wata ce tai yar tsuwa alamar kira yashigu, nadauka tare da yin sallama cikin tatausar murya ya ansa yana ce min
Yacigaba da cewa shukuran shukuran ya ukhtin Ana asfan,
Murmushi nayi kadan har fararen hakora na suka dan baiyana afili,
Ashe sautin murmushi har inda yake yaji shi, alamar naji dadin yabon da yai min,
Kafin yafadi wata magana sai na mika ma Amal wayan ,jinayi tana cewa yayan mu nice
Dariyan danaji tana yi yasa nadan waiga gefenta sai naji tace walahi yayan mu Fadima Allah bata wayo itace fa tasa mu wanan shigar har ina fada da ita,
Salim harda maketa yatashi yi don tace baza mu fita dashi hakana,
Salim din ya karbe wayan hannun ta shima yashiga hira da dan uwan nashi,
Akarshe yadan ihu da murna najin dadi yana fadin an aikawa wa yayan mi cewa duk andauke mu a makarantar
Murna mukasa a cikin motar Allah yasa Yusuf gwanine da saidai yadda hali yayi, kawai,
Bayan mundan tsagaita murnan Amal ke ce min wai yaya nasan cewa suna considering da shigar mutun ,
Saina bata labarin lokacin da baban Nailabin zai sani karatu yadda mukayi a makarantar, dasu wurin ganin shigar da wasu sukayi,,

Mun isa gida lafiya cikin murna dafarin ciki dakin ummi muka wuce direct,
Yadda nags sun rugumay ta nima kusan hakan naje na rugumay ta tajowo ni sosai cikin jikinta,
Bansan lokacin da na fara hawaye ba, ummi tace a,a,a tajeye Amal takara jawoni sosai cikin jikinta tana share min hawaye tace asha fadima godiyan da zakiyi wa Allah ke na ta dagoni tana mai girgiza kanta tace min inyi sadaka in nafila ingode ma Allah shine abin yi ba wai kuka ba,
A gasikiya ni dai bansan may zance wa wayan nan mutane ba don godiyar da baki bai yi sai dai shukuran,
Saboda irin halarcin da suke gwada min yai yawa walahi banda wani matsala yanxu sam
Matsalata gudane itace Nafisat wace kusan kowa agidan taza mai ciwon ido,
Har maigidan takai mai ko ina, arayuwa bin umurni mahaifi ne kawai yasa shi yin hakuri,
Dana tashi gurin hajiyar mu na nufa naje naimata bayanin komai da akeci,
Taimurna so tayi farin ciki dajin bayani da nai mata inda tayi min addu tare da kara roko na gafaran abinda taimin can baya,
Har kullun ce mata nakeyi ni batai min komai ba don komay yafaru da mutun tab batacen al,amari ne,
Tun ran gina tun ran zane duk abinda zai samayka saifa yafaru,
Don haka zuwa na gurinta da kuma zuwa na makkah koba ta dalilin taba saina zo

Sheriff din mu bai gida yatafi Riyadh gurin aiki don haka koda muka dawo mun samu baya gari,
Don haka hankalin mu kwance, muke komai kasan cewa gidan mu na yanzu babba shiyasa badole bane wani yaga wani inba da wani dalili ba,
Nafisat zan iya cewa rabon da naganta tun ranan da ta,tashi shaka na aka ceceni gurin ta,
Yanzu wanan kawar data samu itace tadauko mata yar aiki wace itace ke mata komai,
Mudakeyi da duk andakatar da mu, ko sai dai muyi aikin mu na tsakar gida zuwa fannin sheriff
Komai na sheriff nice mai kula da su duk da kasan cewar shi ba mai zama gida bane ,,,
Anytime yana gurin aiki,n shi, shida Mustapha,
Yau na zo zan wuce ta ban garen dakin nafisat aiko sai naji muryan su kasakasa ita da yar lici
Waya na dan na record
Daidai lokacin tana cewa, gaskiya yar lici, malam garin nan aikisu baici don daini gaskiya banga wani canji ga Ahmad ba yace sai na kori wanan yarinyar ajiki na aiko zaiyi amma gashi bata tare dani har yanzu nakasa samun kan Ahmad din
Kada kidanu uwar daki komai zaizo daidai insha Allah kinsan cewa,
Yanzu watan azumi ne basu faye yin irin miyagun asiran nan badon iskokai andaure,su
Ko shekaran jiya dazai wuce na yi,nayi dashi yaban wasu yan kudade amma sam yaki,
Sai ce min yayi kyautar shi sai yaga dama kuma ko yayi niya idan mutum yatambaye shi shi bai badawa kuma,
Dama yau nazo in fada maki cewa akwai wani malami dan kasar ghana da yazo gurin shi zamu kafin ya koma,
Don insha Allah wanan karon sai mun gwada mai mun fishi sani duk wani takon shi,
Har zan wuche saina da tsaya nakara saurarawa, jinayi nafisa tayi dan tsaki tace wlh indan yafi karfi na sai kawai insa akashe min shi har shegeyar uwar tashi kawai ingaba da komai nawa,
Sainaji sun tafa,
Kafana naji baiko iya dauka na don tsoro, dabayabaya nabar gurin nakoma dakina
Aiko atake zazzabi ya sauka min
Gazafin ciwo ga tunane ya isheni, azuciyana
A kan gado na zube sanan na lumshe idona bugawar zuciyata kawai nake sauraro yadda yake kara karuwa,
Meye abin yi? Tambayar da nayiwa kaina ke nan
Cikin wani hanzari na mike nafada bayi don inyi alwala sai kawai naga bani da tsarki, ,,,
Adadafe ranan naje kitchen haka na daure nadafa masu hjy da ummi abinci har dani,
Adakin na koma don in nazauna dakina tunane zai min yawa nikadai,
Acan naita fama da ciwon mara na ana min sannu,
Dana danji sauki saina debi abinci don in,dan ci
Nafara ci nakai cibiyu nabiyu kena sai mukayi arba da
Sheriff wanda ke tsaye bakin kofa yana kokarin dauko wayan shi, dake tsuwa aljihun shi,
Cibin na mayar don kunyar danaji yakamani,,yai min wani irin kallo na C U, Salim dake bayan shi ne ke fadi kai amma fadima,

_ 🐎ZEEE MAKAWA🐎
24/10/2017, 1:50:21 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎
🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁
🎁N🎁W🎁A

Almost true life story

A kofar gidan da maman umar tai kwatancen take muka tsaya gidane mai hawa goma sha biyu gidane wanda yan umarah ko aikin hajji ke zama aciki shi,,,
kimanin dakuna ,dari da hamsim ke cikin gidan ,
Nice nafita zuwa wajen yan matan takarin da naga suna saida abincin a kofar gidan,
Na,tambaye su ko bakin da suka sauka da ga Nigeria suna ciki,
Ko sun tafi, tunda anyi sallah ba za su tsaya ba wuce zasufara yi,
Tunda nasan cewa tashigo kasan ne amatsayin wacce tazo yin umurah,
Kuma nasan muddin bata samay muba zata iya zaman boyo bazata koma ba sai taga yaranta,
Nuna min wata mata da ke xaune ta ba mu baya, tana saida wasu kayan tarkace akofan masaukin da mukazo sukayi,,,
Matar tana da dan tazar damu kadan don haka ba lalaine taji maganar muba daga nisa,
Na,isa gurin da take zaune ta kasa kayan su takalma da rigunar barci sai su hijab,
Duk wanan abin su Almustapha da Salim na cikin mota suna kallon na
Sallama nai wa matar ta waigo a hankali daidai lokacin tana ciniki da wani mutum mai son sayen hijjab agurin ta
Fadimar mama Sharwali,
Tamike tsaye,cikin sauri ta dafe kirjin ta tana dan kokarin waigen bayana kazata ga garan,
Cikin kidima da rudewa take ce min Umar da Aisha fadima suna ina don Allah,
Dama nasan cewa zasu samu taimako daga gurin ku insha Allah ,,,,
Sai kuma ta fashe da kuka, mai tsuma rai, ,,, ganin da nayi tana shirin tara muna mutane,
Yasa ni jawo hannu ta muka nufi, motar da mukazo da ita,
Muna bayan motar nida ita take ce min tunda aka kamata da kwana biyar aka wuce da ita kasar ghana can jirgi ya zube su,
Allah yasa tana da dan kudi ajikin ta shine tasamu tazo gida dashi, katsina,
Tana fadin wanan maganan sai zuciyana tatuno min da Rugaiyya na,
Nace ko tayi sa,a tasamu jirgin yan Nigeria ankaita gida,
Sai natuna cewa koma ina aka kaita insha Allah tana da wada,tacen kudi wanda zasu kaita, gida,,,,
Motar muna tsayawa umar ne yafara taron mu, ya inda flower's suke yana wasa
Tsaye yayi cikin mamamki yana kallon uwar don gani yakeyi kamar idon shi na gizo ne,
Zuwa yayi ya rungumay ta, tam yana cewa ummi ke ce ko kuwa ummi may yasa kika gudu kikabar mu ,
Tun yana surutu yana sambatu, har yagaji yai shiru yana sha shekar kuka,
Aisha kan fafir kin zuwa tayi wurin mahaifiyar nasu ba yadda ban yi da ita ba amma sam taki,
tace ita,sam bata zuwa, gurin uwar,,,,
Saida Sheriff yadawo nagabatar mai da ita tare da yaran nata
Inda nake zaune itama yarinyar anan take zaune duk falon yayi tsit kamar ba, kowa ciki,

Saida yandayi gyaran murya san nan ya fara magana, bayan sallama yai ma Allah godiya da ya nufe mu da ganin wanan ranan, mai albarka da anfani
Saida yai ma kowa dake wurin nasiha so sai mai kashe ma bawa jiki da kara imani a zuciyar mutum,,
Sanan yajuya inda duk muke zaune har ummi da su Yumma da hajiyan mu,
Yafara da tambayar ta yace itace ta haifi yaran kokuwa tace mai itace,
Yace to yanzu zata bar kasa saudiya da su ne ko kuwa zata kara zama acikin kasar ne kaman da,
Amatsayin yar takari, Saida tashere wani gumi da ya keto mata, tunkun sanan ta dan daga kai ta kalleshi,
Hannu bi,biyu ta daga tacewa don Allah yatai make ta ya ce,ci rayuwan su,
Idan tace zata koma bata da kudin jirkin daukar yaran,
Kuma idan taje dasu Nigeria za,ace yaran basu da uba ,
Nasan cewa ganin da naimata ta,tana kuka zai iya sani kukan nima,
Don haka dagawa na tsab rike da hannun Aisha muka shige ciki,
Ina tashi yabi inda nabi da kallo yasan abinda zanje yi ,, watau kuka ke nan,
Yace mata tadaina kuka zai taimaka yaba su sana,ar yi wanda zasu dan samu,
Amma fa su sanda cewa nada wani dan lokaci insha Allah zai taimaka masu kowa ya koma gida,
Kafin yabar kasan, kowan su yayi murna akayi godiya ,
Bayan an watse ummi tadinga samai albarka tana mai godiya,
Ina ciki ina kallon Aisha cikin tausayi don nasan cewa tabbas za,a raba mune da ita ne yau
Shiru shiru ina ciki ina jiran azo ace min in kawo Aisha zasu tafi sai naji shiru,
Jin shirun yai min yawa saina dan gyara mata kwaciyan ta a hankali na fito waje,
A hankali nake saukowa daga step din dagani na kasan banda wani kuzari ajikina,
Shiru naji wurin yayi ba motsin kowa, a wurin cikin mamaki nakarasa saukowa ,
Ganin ba kowa yasa wuce wa dakin ummi,
Don in gani ko may ke faruwa nida nabar falo tab da mutane , dazu sai gashi cikin yan mintina nafito banga kowa ba,,,
Ummi ce kawai adaki daganin ta ta idar da sallah nafila ne don dai lokacin sallah da sauran tsamu
Gefen kujerar dake dakin ta na,dan samu gefen hannun kujerar na zauna,
Inajiran ta shafa addu,an da na samay ta, tanayi,
Ina dan wasa da yatsun hannu na ina lankwasa su,suna ba dan kara wani dawani dan sauti,
Muryam Sheriff ne naji yai sallama dakin, zubur nayi na gyara zamana ,tukun a tsorace nadan waiwaya kofar shigowa dakin na ummi,
Barka da rana, nace mai cikin sanyayan murya,,,
Saida ya dan kalli gefen da nake zaune sai ya kauda kanshi
Wani, irin dan guntun murmushi ya makale, agefen fuskanshi , yace yawa,
Sai Yace min nazo ne in ma ummi ruwan hawayen da nafi kowa iya zubar wa, itama tagani ko,
Sigar da yai maganar sai yasa nadan sake jiki ga tsoratar danakeyi mai
Tun jiya ban son mu hadu dashi,
A hankali yatako yazo ya shiga dakin,,
Ta inda nake zaune dole zai wuce tagabana, yana sanye da farar T shirt an rubuta agaban rigan iam proud to b a Muslim, da jan kala, sai dogon wandon chunus da yasa mai kyau kalar ruwan toka,, Wani farin agogo ya makala na kamfanin D&G wato, Dolece & Gabbana, sai wasu fararen takalma masu daukan ido ruffafu, dasu, amma a kofa yacire takalman,
Yazo tagabana yawuce hancina kamar cikin kwalban turare na nutsa shi,
Don kamshi shikam sheriff Allah yabashi son kamshi sosai don har abin ya bi mai jiki,
Don ko wuri ya zauna yatashi kamshin bai barin wurin,
Danaga ya shigo saina dan mike da niyar in fita waje,
Cikin saurin yace min in zauna abina ba zama zaiyi ba sako ne yazo fada mata,
Kaita dago a hankali tana kalllon shi, saiyake ce mata Abban shi yai mai waya zasu iso nan da gobe insha Allah,
Adduan tadan katse cikin lokaci guda , tace sai in koma wancan gidan naka ke nan ko har subar gari,
Dan murmushi yayi wanda yakara mai kyaun fuska,
Yace koda sunkai su dari ne insha Allah inada inda zan aje su ummi, basai kin bar gidan ki ba,,
Idan baki so su ganki ne ,har su koma babu wanda zai ganki,daga cikin su,,
Tace aishi zannah dan uwa hauwa nane ka ga bazan ce ban kin ganin shi mu gaisa amma sheri irin na hjy mama nake ma gudu,
Saboda gwanace ta kware wurin kulla sheri
Nidai Inajin su nai tsit kamar ruwa ya cine,
Don nauyin da nake ji,
a dakin sai nakoma takure cikin su gashi ina son fita tun farko ya hanani,
Ya ce ummi ki kwantar da hankalin ki don mama a halin yanzu kinfi karfin duk wani sheri da zata iya yi maki yazama tarihi insha Allah
Ummi tace ai inaga halin nasu a jini yake don kusan itama wanan yarinyar ta wurinka ba inda tarage halin Aminar
Saidai kawai muce Allah ya gyara tunda kun riga kun gaurayu da su ko,
Yace amin a sanyaye ya dan satan kallon na inda nake zaune,,
Duk hiran da suke yi shida ummi kaina yana kasa ban daga ba don duk a tsawale nake, cikin su
Saboda ba maganar da za,ayi agabana bane,,,,,
Sai alokacin ma natuna da nafisa don tun wurin cin abincin sallah jiya ban kara ganin ta ba
Dakina na koma batare da na tambayi ummi maganar mahaifiyar su umar ba,
Amal ce ta fado min a raina don nasan cewa zanji komai da yafaru a wurinta, gamay da maman su umar din,,
Tana zaune saman gadon ta duk tai dadaya da kayan ta wai ta fara shirin tafiya makaranta ne, inji ta dariya nai mata nace ai akwai sauran time,
Da sallama na karasa shiga dakin nata, tana duke tana ta faman gyaran takardun ta,
Wani littafi mai hoton wasu ma,aurata nagani a gefen ta sai na jawo nadan fara diban hoton dake jikin bangon
Nace mata gaskiya sunyi kyau sosai wallahi,
✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎
🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁
🎁N🎁W🎁A

Almost true life story

A kofar gidan da maman umar tai kwatancen take muka tsaya gidane mai hawa goma sha biyu gidane wanda yan umarah ko aikin hajji ke zama aciki shi,,,
kimanin dakuna ,dari da hamsim ke cikin gidan ,
Nice nafita zuwa wajen yan matan takarin da naga suna saida abincin a kofar gidan,
Na,tambaye su ko bakin da suka sauka da ga Nigeria suna ciki,
Ko sun tafi, tunda anyi sallah ba za su tsaya ba wuce zasufara yi,
Tunda nasan cewa tashigo kasan ne amatsayin wacce tazo yin umurah,
Kuma nasan muddin bata samay muba zata iya zaman boyo bazata koma ba sai taga yaranta,
Nuna min wata mata da ke xaune ta ba mu baya, tana saida wasu kayan tarkace akofan masaukin da mukazo sukayi,,,
Matar tana da dan tazar damu kadan don haka ba lalaine taji maganar muba daga nisa,
Na,isa gurin da take zaune ta kasa kayan su takalma da rigunar barci sai su hijab,
Duk wanan abin su Almustapha da Salim na cikin mota suna kallon

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment