Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake,
Yana wani dan lake cikin motar ,
Wacce ta katambayar gidan mu sai na farko ya nuna mu,
Shin wata ta nicce, sai ya kara lekawa can yace shin ko fadima ta,
Baiko tsaya na bashi ansa ba ,sai ko ya juya sheka da gudu yana fadin ita ta wallah
Sauran ma suka bi shi da gudu suna ihu, suna fadin fadima ho fadima ho,
Wani mutum yataso yatare yaro guda daga cikin su
Yana fadin kai minana kuka wagga dabi,a kuwa haka,
Sai yaron yace wai fadiman da ankace Gajiye ta saisuwa a saudiya
Ita ta tta, zakka, inda muke yau,
Kai dan neman ga wa hwda maka ita tah
Yaron yace Dule kanin ta munkajiya yana ihun fadima ta zakka
Shina muma munka bishi baya muna hwadi ta zaka,
Malam Abu yabi bayan yaran a hankali inda yaga sun dosa,
Daidai kofar gidan ya samu guri ya Parker motar shi,
A hankali nadaga kaina na kalli gidan inda aka haife ni kuma mahaifiyana take rayuwa da yan uwa na aciki,
Sai naji wasu hawaye masu zafi sun dan gangaro min a fuska na a hankali,
Abdull ya na shiga cikin gida tare da abokan shi ya iske inna zaune a bakin murhu tana kada miya,
Ganin da tayi masu kamar wa yan da aka koro daga waje yasa ta mikewa tana tambayar
Minana shin kuka shigowa idan mutun haka cikin tashi hankali,
Abdull yace walleh inna fadima ta tazzaka
Zubur inna ta karasa mikewa da abin kadi a hannunta tace
Mikkace shin? ya ce a wo
Fadima dai da kinka sani
Mariya daga daki tace
Kaikan Dule wallah kaga buni da wagga muguwar dabi,a
Wacce fadima shin ? fadiman da ko saninta bakayi ba zakace wai ita ta, ta taho,
Yace walleh in karya na ni kai shegeni ke inna,
Da ijiyana niggane ta, cikin wata mota,
Da sauri nakara mayar da dibana kan gidan cike da tunane, iri iri a zuciyana,
Na balle murfin motar nafito rike da hannu Aisha,
Ina karewa gidan mu na kasa kallo cikin tausayi nake tuna cewa wai mutane ke kwana acikin shi haka,
Kai tsaye na nufi hanyar shiga cikin gidan inada aka tare kofar dawani katon katako mai kama da icce,
Da sallama na kutsa kaina cikin gidan,
Inna na tsaye tana sauraren mariya dakewa su dule fadan haukar da sukazo masu dashi,
Ganin da tayi min na shigo yasa ta tsayawa da maganar da takeyi,
Da inna taga ta tsaya ta kurawa kofar shigowa gidan ido yasa ta waigawa itama da sauri, ta kalli kofar gidan,
Cak na ja na tsaya guri guda don jin danayi numfashi na yana kokarin daukewa
Sakin abin kadin dake hannu ta tayi ya fadi kasa don kaduwar da tayi,
Tace shin fadima ke ta ko kuwa gizo idona kayi,
Gudu gudu da sasarfa na isa gurin inna na na rugumaya ta,
Abin mamaki Itama inna rugumay ni tayi sai kuma mukasa kuka gaba dayan mu, nida inna a lokaci guda,
Muryan danake bege nake tunawa in yi kuka ko kuma ya hanani barci naji yau kamar a mafarki a bayana,
Tana cewa shin fadimata wagga ko kuwa wata ta,
Wani irin juyi nayi na sake inna na fadama hafsi muka runguma junan mu,
Muka dan dago muka kara kallon junan mu sai kuma muka kara rungumar juna cikin karfi sai mukasa dariya cikin murya mai cike da farin ciki ,
Takara dagoni tace walleh fadima har yanzu ban gaskanta cewa keta ba,
Nakar rungumo su lokaci guda ita da inna ina fadin kasa, kasa ,I miss u sai kuma nasa kuka mai tsima rai,
Ta bayana naji muryan Aisha tana fadi cikin larabci cewa zata tiyi fitsari,
Nadan dago fuska na da yayi caba caba da hawaye nadubeta nace tazo in cire mata wando in kai ta,
Sai a lokacin su inna sukaga Aisha,
Da muke tare, sai kuma kallo ya koma gurinta, kowa da mamaki fam a zuciyar shi,
Mariya da tagane ko may Aisha zatayi yasa tai saurin riko hannunta daga wurina zuwa bayi,
Hafsi takara matsowa kusa dani tace shin fadima ta a haka shin, cikin mamaki tana ta faman taba min jiki cikin mamaki,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,


Cikin dan kankanin lokaci duk labari ya karade gari dogon daji cewa,ai fadima ta dawo da ga inda Gajiye ta saida ita,,,,
Mutane sai tururuwan zuwa gidan mu sukeyi don tabbatar da zancen
Wasu kuma suna zuwa don gulma ne saboda irin yadda ake fada masu na koma kuma na,zo da diyar larabawa tare da ni,
Malam Abu ya sa aka shigo min da kayana cikin gida, mu,
Da taimakon mariya duk aka shiga da kayan dakin innan mu,
Duk da lokaci ya kure amma malam Abu driver ya ce a lokacin zai koma kano wai,
Wasu jallabiya masu kyau na mata na bashi yakawai safiya da Amman,
Shikuma na bashi irin ta maza, sai hjy umma da na baiwa turare da tasbah mai tsada,
sai fura ta shinkafa dakar hannu da nono mai kyau, inna tabayar akaiwa hjy umma,
Nasan cewa idan nabasu tun acan kano, baza su karba ba saboda kawaici,
Shiyasa nai wanan dabaran na bari sai malam Abu zai koma in ba shi sako ya kai masu,
Yawanci zaga cewa idan tafiya ta riske ka, har marance yai ma, zaka wuce wasu yan garuruwa da wutan lantarki,
Amma da ka shiga garin da zaka ko bangaren da kake sai kaga dundum babu wutan ,sai bakin duhu ko yan haske a yan tsirarun shagunan kauyen,
Don haka na lura cewa tun zuwa na har yanzu nepa ko kil basu muna ba da wuta,
Har kusan karfe goma dare jama,a ke ta shigo min barka da zuwa,
Ban kara samun lokacin zama da yan uwa na ba tun bayan isowana da muka dan kebe da su,,
Mariya ce ta raka, wasu gungun mata da suka fita a karshe,,,
Sai tabi bayan su tasa wa kofar gidan mu sakata, ta yadda ba wanda zai kara shigowa muna, gida kuma daga wanan lokacin,
Hakan yasa muka dan samu daman zama da yan uwa na a wanan lokacin,,
A hankali natashi daga inda muke zaune da su hafsi na koma inda inna take zaune
Tana kallon mu cikin so da kaunar irin ta uwa da diyanta indan sun hadu,,,
A hankali na riko hanun inna na tare da wasu irin hawaye masu zafin fita, daga ido ,,,
Masu dacin sauraro a kunnuwar mai jin ta
Nadago fuskana da yai cab cab da hawaye, nadube ta,
Nace mata inna dan Allah ki yafe min duk abinda na aikata a bayan tafiya na,
Wanda duk iya kokarin da nayi inga cewa nadawo gida gurin ki lafiya Allah bai nufa ba,
Da sauri gaba dayan su da tunda na fara magana sukayi tsit suna sauraro na suka kai kallon su ga Aisha,
Wacce ke kwance saman gadon karfen inna tana barci da alamar duk zafi ya damay ta da sauro,
Na dan yi shiru na kasa ci gaba da maganar da nake yi
Saboda kunar da zuciya na take min don ban san koda wani ido zan kalli inna in fada mata cewa nayi aure ba,can,,,,
Batare da sanin su ba har ma da cikin wata biyar a cikin jikina,
Inna kuka kawai tasa ita ma don ko ban karasa zance, na ba tasan cewa ba magana mai dadi zan fada ba a wanan lokacin
Saboda yadda taga ina kuka, wi, wi,
Hafsi ce ta taso tazo inda nake gurfane a gaban inna,
ta dan rugumay ni tace min,
Fadima am, ko ni bari kuka haka kejiya ko,
Ganin ki ma dai, da mun kayi ya wadatar damu da komi, wallah,,,
Ke san duk mutum bai wuce kaddaranai,
Tunda Allah yyah nufa kinka dawo gida lahiya lumui , aimu,
Godiya dai mukai gare shi ,
Duk abinda ya hwru da keyya ba lahinki na ba fadima,
Ko kusa baki da laihi sam,cikin wagga harkan,
tunda bake tah kin ka tai da kanki ba,
kai ki na ankayi,
Ke, ga ko, laihi naga wadda, ta tai, da ke,,,
Wani sabon kuka nasa sosai alokacin da tafadi haka
Ke, ko ni am share hawayen ki kejiya ko,,
Mariya da ke gefe guda tana sauraron mu ta ce,
Shin wai mi, na na abin kuka ,
Ai kowa ma na da kin ka gani, shina da, abin hwdi har da tus,suwa,
Bagare, ki na ah hwrau ba,
Sai yanzu na gane nufin su da sauri na kalli inna nace mata ,,,
Wallah wallahi inna tunda nabar ki ban taba aikata zina ba a rayuwa ta kuma ban taba daukan abin wani ba,,
Da sauri suka kara kallo na cikin mamaki da ya baiyyana a fuskokin su, lokaci guda,
Wa,a,dda waga diya shin,
Inji hafsi,tana kallo na cikin tambaya da son karin bayani,
Da sauri na kalli inda Aisha take kwance abin ta,
Duk da kuka nakeyi, alokacin, saida, tambayar ta yasa nai murmushin karfin hali,
Don jin inda suka dosa da zancen
Nace wanan in na isa haihuwar ta ai zaku ce kila ina haukane, ko,
Yaushe nabar gida da har zan haifi wanan "yar
Aisha, Diyar wata abokiyar zaman mu ce, a saudiya,
Tabani ita ce, tun tana yar karama nake tare da ita shine dazan dawo tace in zo da ita kada zumun cin mu ya yanke,
Uwarta na saudiya ubanta kuma mutumin Sudan ne, ya dade da rasuwa ko,
Shiru dakin yayi kowa da abinda yake sakawa a cikin, zuciyar shi,
Shin ko ma minana anty fadima ,am hakuri na zamuyyi , kawai,
Tun da har Allah yamaido muna dake gida lahiya,
Shin mi rage kuma,
Duk uban daka magana shi tai shitayi shiyajiwo
Shi an nan,
Dauri da suka cewa saishe ki na ankayi hwa,
Ko yanzu da suka tururuwan tahowa inda ki ke da sunan sun taho maki barka da sauka,lahiya, walleh duk karya na sukai,
Da ijjiyan ga nau nagga sanda Tumba ka nuna ma Dije wagga diyan da kunka taho ita,
To, mi suka nuhi da hakan hafsi, ,
Hafsi tace Su,dai sunka sani ,wallah,
Duhuwar mutum mai kosai,
Ina jin su amma ban ce masu komai ba sai ma shirun da nayi kawai a lokacin
Ina nazarin ko yaya zasu fassara wanan cikin da ke a jiki na yanzu,
Saboda gashi da ga irin hali na mutanen kauye saboda gulma har suna daukar Aisha a matsayi diyata,
Yaushe har nabar garin da zan iya haihuwar kamar Aisha yar shekara kusan tara,
Shiru nayi kawai ban kara cewa komai daga hakan,
Wanan rana ta kasance mara misaltuwa a gareni don duk wani abu da nake yi tankar mafarki na ke ga shi,
Wai yau nice a a gaban mahaihaifiyata da yan uwa na kuma a kasata ta haihuwa,
Babu wani fargaba ko shakkun korar kare da akewa mutane saboda rashin galihu, in badon taimakon da nasamu ga sheriff ba,
Gabana ne yafadi dam saboda tunawa da nayi da zancen sheriff,
Tunda na iso sai yanzu na tuna da sheriff,
Saboda farin cikin da nayi na kasancewa ta a gida, tare da kowa nawa
Mun kusa raba dare muna hira da yan uwa na da mahaiyar mu,
Barci ya kaurace wa idanuwar mu dan murnan wanan ranan
Suna bani labarin abin da yafaru bayan tafiya ta
Dariya muka dinga kyale kyalawa,
Saida inna tai masu maganar cewa su bari in kwanta in huta saboda ina tare da gajiya a jikina , gobe ma ranace tunda ina garin,
Mariya ce ta gyara min inda zan kwanta wai saman gadon inna tare da Aisha,
Nasan cewa ba zanji dadin kwanciya hakana ba saboda ,karantar gadon ,
Don haka sai na dan wayance da cewa a,a zan kwanta a kasa, kusa da inna ta ne, yau,
Ke mariya kije ku kwanta keda Aisha kawai,
Wanan ranan kusa da mahaifiyata na kwanta inda ita da hafsi suka sani a tsakiyan su,,
Saboda mijin hafsi ya barta takwana gida yau don murna,
Haka mu ka gwamatsu dukkan mu cikin dan karamin dakin inna na laka,
Duk yadda nake a gajiye hakan bai bani damar yin barci ba, a wannan daren,
Sai juyi nakeyi saboda tunane da farin cikin yau nice a dakin inna kamar a farki,
Ban wani dade, da fara,barci ba naji anfara, kiraye kirayen sallar asuba
Saboda sabawar da nayi na zuwa yin sallah asuba a,massijid
Yasa nakasa komawa barci mikewa nayi tsam da ga kwanciyar da nayi da, niyar zuwa in dauro alwala,
Don inzo inyi nafila
Saina ga ashe har inna ta ta rigamu tashi,, saboda zaune naganta tana tasbihi,
Azuciyata nace Allah sarki inna ashe tana nan da wanan yawar ibadan nata, da nasani,
Koda na idar da salla ban bar lazimi ba har kusan karfe bakwai na safe,
sannan na mike kai tsaye na fita waje inda inna ta da hafsi ke kokarin dama koko da kuma zuba ruwa a cikin wani plask , don shan tea,
Ina kokarin zama in gaida inna da hafsi ne naji muryan inna ta na fadin fadima
Mi, da kin kahito, wuri yanzu
Dauri ki koma wanki, barci ai,,, ,
ke fa san cewa, kan ki ya na iya imiki, ciwo,
Nace wallahi inna naso in kara yin barci saidai na gan ku a waje kuna aiki ne,
Sai wani hamma yazo min nakarasa zancen cikin yin hamma,
Da sauri inna tace maza tashi tai zuwa daki ,ki samu wuri ki dan huta ke jji ya,,,
Ke san doguwar tahi na kin kayi, wallah ,
Hutuwa, dai ,ki ka bukata,
Ba,musu na juya dan gaskiya a gajiye nake dama,
A nutse na tashi na koma daki nadan samu guri gefe guda na dan kwanta,
Kafin wani lokaci sai barci, yadauke ni mai nauyi kuwa,
Kusan barcin minti talatin da biyar nayi, a cikin baracin, lokacin sai nadinga ji kamar ana kiran suna na a lokacin natashi zubar,
Kawu salihu ne tare da mai gari suka shigo har cikin gidan inna yi min barka da zuwa tare da wasu dattijan gari kusan su goma sha,
Daganin su kasan cewa tun, da suka tafi, masallaci wurin sallah asuba basu koma gida ba,,
A ho yar kulu,
Yar kulu bar kadai da,wagga,arzikin, ke ji,,
Ashe fadima andawo gida,
Tace, awo rankashi Allah sabbanani,,,
Allah yayi dawo war ta,
Sannu da arziki ke ji,
Wagga diya Allah yai mata arziki tunda ya, maido muna da ita gida lahiya,
Daidai lokacin nafito cikin wata doguwar rigar da na,zurawa jikina,
Cikin ladabi na durkusa har kasa ina gaishe su,
Kusan bakin su guda suna fadin ingwaiyya, agaisheki ke ji,
Barka da arziki ke ji,
Fadima ho, ke taho lahiya, yaya kin ka baro su can,
Ina ta karbawa ina fadin lafiya kalau, na samay ku lafiya ,
Wanan ya leko ya ce mi fadima ho,
Maigari yace min fadima a she saudiya an ka tai da ke,,
Saida baya munka jiya duk mun shiga cikin, wani hali da kin ka bata,
Allah da annabi nai sunyi gaskiya wallah ,
Komi kabar ma Allah insha Allahu kana ganin sakayyanai,
Ke ga dauri duk mun ta da hankullan mu cewa sai, she kina Gajiye ttayi,
Saiddah bayana mun,kajiya cewa kina saudiya gurin Alhj Ayuba da kin ka ba sako yakawo ma tsuhuwan ki,
Sannu ke ji sannu da shan wagga duniyar,
Yar kulu ho, agaishekki, barka da wanga arziki ke, ji, walleh anyi arziki kan, inji sauran yan tawagar hakimi suke fadan hakana,
Duk maganar da sukeyi ina gefe na tsuguna nadukar da kaina kasa cikin ladabi da biyyaya,
Ba su dauki wani dogon lokaci ba sukai muna sallama suka tafi,
Daki na shiga da sauri na bude wani jakkan nafiddo masu da tasbaha da yan turare masu kamshi,
Sai jallabiyar maza mai kyau na ba maigari,
Mariya ce ta,sheka da gudu ta kai masu saboda har sun dayi nisa kadan da gidan mu ko,
Abin karin kumallon safe aka dinga aiko min da shi daga gidan jen yan uwa da abokan arzikin innar mu,
Kamar su,masa koko da kosai, sai tuwon shimkafa da aka lema miya aciki, ,

Wata sabuwa zance kuma da ya bullo min shine,
Duk da inna ta bata gane cewa ina da ciki a jikina ba amma sai da Tumba makwabciyar mu,ta gane cewa akwai ciki a jikina hakan
Saboda tsabar gulma ko yaushe Tumba tana gidan mu zaune wai tana taya mu karban yan zuwa min barka da dawo wa,
Mai mako ta fadawa inna ta kai tsaye,
Ai sai kawai ta wuce don gulma gidan Dijen yabo,
A,a Tumba ta at, tahe yanzu da wagga uban ranan,
Nita ke dai Dije, am
Kudin adashen ki na nattaho in kawo nauwa zubin,
Aiko sau,biyu ni, aika inda kike, ankace min wai ketahi unguwa shin,
Bari kedai Dije ina can inda wagga bakuwa ta makkah ina kare mata, kallon mamaki,
Mamaki shin , mi, ar na mamaki kuma,
Shin ina Dije ta ce gani tumba am,
Ke taba jin inda "ya mace, ta tai yawon duniya ta dawo gida lahiya lumi,
Shin , a, a diya ttah,, taka tahiya tsawon wagga shekaru ,ace wai tadowo gida lahiya
Walleh karyata,
ke ga wata yar diya dattataho da ita yar diyan larabawa shi,,
Sai kuma ta dan yi shiru ta fidda goron da ta daure a gefen zani ta tadan balla ta tauna ,
Sai ta dan matso kusa da inda Dije take zaune ta na gyaran ganyen soborodo,
Ta dan tausa, murya ciki ciki tace wai ko kesan fadima cikina aggare ta,
Ke tumba bari wagga maganar, dan Allah dai wane irin ciki kuma,
Don ke ga tayi dan magurjin jiki, tai kyau,
Babu karya cikin magana na ta, Dije am,,,
Uwar diyan ma bata san da wagga zancen ba da ni ka hwada maki,
Don ko da su shatu,, mai kitso sunka taho taron ta
suna cewa wai fadima tayi kyau, sai cewa uwan tayi wai ai shekarun girman ta na ,
take yanzu shinassa, tai kyau haka,
Dije tace to ke Tumba shin,a,a kinka gane cewa cikina a,ggare ta,
Walleh Tumba ki bar boni (bala,i)shi kwana, in ba so kikai a kan maki ba,
(akama ki ba)
Yau ko ga Dije, inji Tumba,
Sottdiya,i gwalmadiya,i, shin ni na kuma ban san ciki ba Dije am,
Don gudun wagga irin tuhum yassa saida ni binkcika da kyau,
Sanda anka kawo mata tuwo ashe anzuba man shanu a cikine,
Saida duk ta amaye dan abin da ta ci,
Ni da kaina nibbata dan goro ta tamna,
Salati Dije ta sa tace tabbasa tumba ke san ciki wallah,
Yanzu waga diya dama yawon balaguro na takai a can kasa mai tsarki,
Kedai Dije am hwadi, yanzu zuwa nikai, duk yan tarkacen tsaraba da anka bani maisuwa nikai,
Don walleh ban son kayan zina

Wanan maganar ta Tumba itace ta bazu cikin kauyen mu cewa yawon bin maza na yi a saudiya nadawo da cikin shege har da yar diyar shege na zo,
Hafsi ta far jin wanan labarin gurin mijinta ,
Bai boye mata komai da ake fadi gamay da ni ba a cikin gari,
Da kukan ta, wi,wi hafsi tashigo muna gida musalin karfe sha biyu da,rabi na rana,
Ina zaune tare da inna ina bata labarin zamana a kano, mariya ta na bakin murhun tana ma inna girki,
Ganin da mukai mata cikin tashin hankali yasa mu fitowa daki da sauri gaba dayan mu
Cikin rikicewa muke tambayar ta ko lafiya duk a rude muke,
Cikin kuka take nuna ni da, dan yatsarta tace shin fadimaa wagga batu da mukajiya a gari shin gaskiya na ko ,
Inna ta ce mi kun ka jiya shin,
Fadima wai da ciki tta taho, kuma wai wagga diyan ta,tatah,,,,tana mai nuna Aisha dake zaune tana ta wasa da kasa gefe guda,
Kafin inna tai magana mariya ta cabe zancen tace,
Yau ,ko kuji min wani zance
A,a duniya na ta rugumo ba ciki ta,taho dashi ba,
Banyi magana ba daki na koma kawai na zauna sai naji wasu hawaye na zubu min masu zafi,
Ba komai yasani hawaye ba sai nasan
Saboda nasan cewa cikin jikina zai sheganta ga bakin mutane gari ke nan,
Hafsi tacigaba da fadin fadima mi da kin, kai muna haka shin
Ke san halin mutane garin ga sarai da sa, ido mi da zaki taho da ciki ,cikin wagga gari,
Dakin suka shigo su uku lokaci guda , ganin da sukai min ina kuka yasa su yin kukan su ma alokacin,
Inna ce tai karfin hali tace min,
Shin fadima da gaskiya na ciki na aggare ki,
Ban

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment