Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uguwar da muka zauna kafin mu dawo gidan shi,
Ga mamakin shi duk bakin fuska ne agurin duk wani bayani da ya yi a gamay da mu ba wacce ta gane mu, daga cikin su,
Haka yadawo gida ga gajiya ga bacin rai duk atare da shi,
Bayan kamar kwana uku da yawon nai manta da yaketi bai gane komai ba , yasa yafara shiga cikin wani sabon damuwa,,
Yau yana zaune da dare bayan ya gama komai,
Cikin rashi ba wani dafi a tare dashi,
Salim ne ya kira shi dan su gaisa da yayan nashi,
Inda yake tambayar shi ko anji labarin fadima din,
Cikin rashi wallawala yace mai tana Nigeria saidai yarasa ko a wani gari take a can din,
Salim yace yatam bayi Amal ko tasan inda nake kasancewa zaman da mukayi tare da kuma irin shakuwar da ke tsakanin mu,
Sheriff yaji dadin wanan shawar so sai don shi sam ya manta da zancen tambayar Amal,
Kiran Amal din yayi bayan yar vaisuwar da sukayi ne
Itama din taje tambayar shi labarin fadima ya sheda mata cewa tana nan a Nigeria
Saidai bai san a kowani state take ba, kuma duk yatambaya amma ba,a samu wanda yasan garin su ba,
Shiru tayi a lokacin tana tuna wani hirar da muka tabayi da ita,
A likacinda muke kallon lambobin da yan makaran tar su suka bata,
Inda naga sunar wata yar class dinsu na nace mata akan wai sunan yar garn mu ce
Nace mata sai ta buga min wayar ta muji ko tasan iyayyena,
Duk iya buga wayar da mukayi bamuyi sa,a mai lanbar wayan ta dauka ba,
Tun ina tambayar ta akan tabuga min idan mun buga ba mu samu yasa har uka daina
Shirun da sheriff yaji tayi ne yasa yace mata ya, naji kin shiru Amal,
Nan tadan bashi wanan labarin a takaice,
Cikin zakuwa yace mata may ye sunar yariyar da nake son takira min a lokacin wace nake ganu kamar yar garin mu ce,
Tace mai murja dogon daji,
Yakara maimaita sunar yace murja dogon daji,
Dogon daji a wani state yake tace gaskiya brother ban sani ba wallahi,
Amma dai a lokacin ita wanan murja din a kano take zaune,
Shiru yayi yana nazari ko ba komai yasan cewa zai dan samu wani dan aarin haske a wanan labarin, insha Allah,
Amal tai sallama dashi akan cewa ita ma zata kara kokartawa ko zata samu layin wanan murja din,
Yai mata godiya so sai kamar ance mai ai an gane garin da nake ne ma ko,
Duk wani bincike yabar shi ahannu bashir kafin su shigo kasar Nigeria din
Bashir din yai mai alkawari ya kwantar da hankalin shi insha Allah indai har a cikin kasar Nigeria nake za,a gane inda nake,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎


[12/3, 9:38 PM] ‪+234 706 078 6258‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,


Duk wani bincike da yakamata Bashir yayi akan wanan garin da suke tuhumar cewa fadima ta na can ya yi shi,
Da kyat da sudin goshi yasamu wani bawan Allah mutumin kano yace lalai ya taba jin wanan sunan abakin wani abokin sanar shi,
Sai dai yana tuhumar cewa garin yana can cikin jahar sokoto ne
Hakan yasa suka bidi wani mutumin jar sokoto da ke cikin kasuwar wuse
Don jin ko yasan wanan sunan gari , sanan ta ina ne garin yake dan Allah,
Dan dattijon malam iliya yai yar dariya yace kwarai kuwa ba shakka nasan wanan garin a can cikin jahar mu ta sokoto take , garin baida wani nisa sosai da cikin garin sokoto so sai,
Dattijon ya kara yar dariya irin ta manya yace Dogon Daji mai rijiyar Biri zam,zam ke nan,
Yace ai gari ne mai tsohon tarihi, acikin yakin sokoto ga arzikin noma da kiwo Allah yaba mutanen wanan garin,
Bashir yaji dadin samun wanan labarin dayayi
Saboda bai son wani abinda zai sa dan uwan shi cikin tashin hankali,ko kadan,,
A hanyar shi ta komawa gidan shi ne yai wa Sheriff text a waya akan cewa an gama komai, ko,
Sheriff shima da alokacin yana hanyar madina zuwa makkah yai yar murmushin jin dadi tare da shafar suman kanshi,
Har cikin zuciyar shi yaji dadin wanan sakon na Bashir don gani yake yi kamar har ya isa garin su fadima ko,
Yasan kowa ye Bashir dama shi yasa yake kara son shi yasan tun suna yara Bsshir yana damuwa da damuwar shi,,,
Yai yar ajiyar zuciya yace fadima i will surprise u, insha Allah,
Duk inda kika shiga cikin duniyar nan zan iya tono ki,
Yai dan murmunshi da saida fararen hakoran sa suka baiyyana waje, yace,,,
Ke tawa ce ni kadai fatima, bazan iya rabuwa dake ba, duk ritsi bazan barki ba,
Tun a wanan lokacin yaji kamar yai tsuntsuwa yaje Nigeria,
Sai yaji kamar an sauke mai wani nauyi ne a kan sa,

Shigar safiya su kaiwa garin kano su biyu ne a tafiyar tasu Khalid bai samu biyo su ba, kamar yadda yaso, sai Al, mustapha da ke tare da Sheriff din shi akoda yau she,
Tafiyan su ta zanto tamkar kamar ta official ne, don jirgin ba wai wasu passenger ya kwaso ba masu yawa,
Daga Riyadh Abuja jirgin ya sauka, bayan duk wani bincike da ya dace ai masu angabatar
Motocin company su Ahmad ne har guda hudu Suka zo don taron su inda aka lodawa hilux kaya masu yawa a bayan ta,
Sai a lokacin doctor kamal yaga irin kayan da Ahmad ya jibgo don tafiyan,
Cikin mamaki ya juya inda Ahmad din ke tsaye yana kokarin bude kofar mota,
Bayan sun zauna ne Doctor yace wanan uban kayan fa da ka dauko,
Murnushi yayi lokacin yana kokarin ciro wata yar karamar system din shi new model don binciken wani karfe,
Yace wa Doctor duk kayan fadima ce Doctor,
Cikin yar zarar idon mamaki yake kallon shi,
Shiko cikin ko in kula yace yes
Da da farko ba,a gaban iiyayen ta, na nemi auren ta ba duk wani abin da yakamata ai wa fadima ban mata ba,
Wancan lokaci kasani kai aure ne kawai na wani manufa,
But yanzu ko ta riga ta zama wani sashe na jiki fiye da yadda nake tsamani,
Shiyasa zan tafi mata da wanan kayan a matsayin lefen ta, a gurin iyayen ta na aini fi,
Don su ma in basu hakkin su tare da hakkuri, da duk wani kuskure da aka tafka alokacin na rashin bidan yardan su,
Murmushi doctor yai mai don gane hikimar yin hakan
Yana son Ahmad wurin bawa kowa hakkin shi komai kan,kanta abu
Yace wanan kuma fa gaskiya ne Ahmad, hakan nada wani fa,ida so sai,
Musan man ga mutanen mu hausawa da suka maida kayan lefe kamar wani sunna babba,
Zakaga koda yaro baida halin su kamar dole sai ya nemo su ya kai gidan yarinya,
Wasu ma don jahilci har rainawa sukeyi, agaban yan uwan yaro,,,
Sannu a hannkali motocin ke tafiya a bissa titin cikin garin Abuja,,
Saidai yar go,slow da suka samu a hanyar don gurin yadan cike da abin hawa,
Doctor kamal sai yaba garin Abuja yake yi, ga irin girman da takara acikin yan shekarun nan,
A zuciyar shi yana fadin cewa a gaskiya gwainatocin Nigeria suna iya keep karin su dosai wurin inganta rayuwar al,uman su,
Babu gwaunatin da zata hau mulki da baita wanin abin ci gabar al,uma ba akasar
Duk wacce ta hau sai tayi iya kokarinta ga jama,ar ta,
Suna tafe suna hirar su, Ahmad na fada mai cewa shima yana son yabar kasar saudiya yadawo kasarsa da zama,
Saida har yanzu gwaunatin saudiya sun ko sake shi ,
Koda yaushe kokari kara mai ci gaba sukeyi a gurin aikin shi.
Ta yadda ba zaiyi tuna nen dawowa kasar shi ba, saboda amfanar da sukeyi dashi,
Maitama suka ga an rubuta baro, baro a titin shiga layin uguwar,
Agaban wani kyakyawan gida suka tsaya, inda mai gadin kofar gidan ya wagale get motacin suka shige ciki gaba dayan su
Gidan Ahmad na maitama, ke nan, wanda bai ko tare a cikin sa ba,
Sabone shiya gina abin shi tun lokacin da yafara aiki a kasar yai tunanen yin wannan ginan don gaba,
Don ita Nafisa tana zaune A so Rock, a gidan shi da company su na nan Nigeria ta gina mai ,
Don haka a can maitama ya yanke shawar sauke doctor,
Saboda Doctor ya huta yasa su zuwa maitama direct,
Doctor kamal yayi mamaki kwarai da wanan katafaren gidan da Ahmad yagida a kasar shi ta haihuwa,
Saidai mamakin nasa ba wani mai tsawo bane saboda sanin da yai,wa Ahmad din ,
Akan irin kudin da yake samu a kowani wata, daga guraren aikin shi da kuma masana,artan su ta Abu Abdallah, dake Dubai,
Dan ma Ahmad din ya kasance mutum mai son taimakawa addinin sa ,
Yana yawan taimakawa kasa shen musulumai baka ken fata da tallafi, da kaso nai tsoka daga cikin dukiyar shi akoda yaushe,,,,
Sun samu Bashir ya aiwatar da komai da yakamata don taron baki a gidan,
Saida ya tabbatar da cewa, doctor yasamu natsuwa daga gajiyar da suka kwaso ne,,
Sai yai mai sallama da niyar wucewa gidan shi da nafisa take zaune a ciki,
Al, mustapha ya bar mai, don kauda shiru agidan shima kuma mustapha din agajiye yake a lokacin,
Sam nafisa bata da masaniyar cewa Ahmad zai zo yau saboda ta san cewa yafi shigowa karshen wata, duk da bawai ko wani wata bane yake samun shigowa Nigeria din,,
Duk da rashin shigowar shi time to time bai sa tadamu da rashin zuwan na shi ba,
Ita dai gurin ta ta zauna a matsayin matar shi a rayuwar ta don gani take yi kamar babu sauran namijin da yakai Ahmad din ta komai yanzu,
Don haka tasa wa ran ta yin hakkuri da zama dashi ko ta yayane, zata iya jurewa da shi din,
Don haka babu wani tanadin da tai mai na shirin zuwan nashi Kamar yadda ya kamata duk wata, mace ta tarbi mijin ta a duk lokacin da zai ziyar ce ta,,,,,
Nafisat ta canza halinta so sai yanzu ba kamar da ba , duk wani shaye shaye ta daina shi yanzu,
Zaune take a cikin tanga may,may falon ta tana waya yar aikin ta na gefe guda ta na dan goge gogen kayan cikin falon,
Duk da safiya ne yanzu, bai hana nafisa ta tsara kwaliyar ta ba tankar wace mijinta ke a gari, zaune,,,
Da sallamar shi ya shigo cikin falon nasu, duk da gidan shi ne, amma shi akidar shi ce yashigo da sallama,
Ganin da taimai girshi sai da gabanta ya fadi, cikin nuna yar faduwar gaba tace Ahmad ,
A yar razane ta mike tsaye daga zaunen da take,
Tana mai sannu da zuwa cikin mamaki,
Inda take yadan nufa yadan sunbaci tsakiyar goshinta kamar yadda larabawa kewa matan su ko diyan su,
Kaine tafe babu ko sanarwa, batare da ya dakata ba ko ya dan tsaya ya wuce kai tsaye zuwa hawan stairs ,
Binshi tayi da kallo tace a zuciyar badai, miskilanci ba Ahmad,
Itama saman ta haura tabi bayan shi,
Koda ta shiga dakin ta samay shi yana cire botton din rigar shi,
Zuwa tayi don taimaka mai cikin kissa irin ta yan duniyar mata,
Duk da yagane nufin ta hankalinshi bai wani daga ba ga duk wani kisi,sinanar da take ai,watar wa,
Kara tanbayar shi tayi ko lafiya ya shigo batare da fada mata ba, zai shigo ba
Jaye taye daga gaban shi kadan, ya nufi hanyar bayi,
Daidai kofar shiga toilet yace mata, batafiyan ki nayo ba shi yasa ban sanar da ke ina hanya ba, yashige bayi abinshi,,
Ta yar murmushi kamar ta mugunta tace aiko nice mai tafiyar ba aiki ba,
Bayan yafito ne ya shirya ta kara shigowa dakin cikin kwalliyar da yafi nadazu, kyau,
Abin breakfast ta gabatar mai duk da ya danci wani a abu acan gidan da suka fara sauka da doctor
Hakan bai hanashi karban tayin da tai mai ba na abincin don ya fitar mata da hakkin ta,
Kasa stair ya sauko don ya ci abincin,
yafara cin abincin da ta sa aka shirya mai a saman dinnig, a hankali saboda sam bai jin cin komai a halin yanzu,
Kunun cookeroth yadan kurba, kadan sai wayar shi tai kara alamar kira,
Bashir ne a layin inda Sheriff ke sheda mai cewa ai ya iso ko tun dazu kuma yana gidan nafisat,
Aiki ne yataso maku haka ba shiri kashigo a gagauce,
Nafisat ta kara tambayar shi a karo na biyu,
Kai tsaye yace mata a,a aikin kaina ne wanan karon,
Mata, ta ce nabiyu , shiyasa kika gan ni a wanan lokacin,
Duk da maganar yadan daki zuciyar ta amma sai ta daure don kawai alkawarin da ta daukar wa iyayen ta,
Tai dan murmushi tace Aziza ce sai ka biyo ta har nan wacce ba wani zama takeyi ba a kasar da har zai sa ka biyo ta,
Daidai lokacin da yake mikewa tsaye yace Aziza kuma,
Ai Aziza ba sai na biyo ta har Nigeria ba tunda ba,a nan take zama ba,
Kafin wanin su yai wani magana ne Bashir ya shigo falon cikin sallamar shi,
Dan rugumay juna sukayi bayan misa bi,ar da sukayi,
Bayan gaisuwa da kuma tambayar sauran jama,a
Sai suka zauna a lokacin Ahmad ke cewa Bashir to ya mutumin da zai gwada muna hanyar garin ya shirya tafiyan ko,
Sai a lokacin nafisa da ke tsaye ta sandare cikin mamakin maganar da Ahmad ya fada mata, tun dazu,
Tadan gyara zaman ta don jin zancen takeyi kamar ta almara har yanzu,
Bashir yace a gaskiya ba karamin kokari yarinyar nan tayi ba, da ta kamo hanya ita kadai tun daga saudiya har wanan gari da akace yana da nisa sosai,
Ahmad yadan yi, ajiyar zuciya ,cikin muryan tausayi,yace ba komai ke kara tayar min da hankali ba kamar cikin da ke ajikinta, Bashir,
Banason ace min wani abu yasamu cikin nan don duk wani hope nawa a yanzu bai wuce kawai inga ance min an haifi abinda ke cikin cikin nan ba,
Ido waje Nafisa ta kara kallon shi ,
Ta mai,maita a zuciyar ta tace ciki fa,
Wace matar tashi keda ciki wacce ban sani ba,
Kai wanan dai kila matar wani ne can suke zance,
Shiko bai ko san cewa tanayi ba ma,
Don haka cigaba ya yi kawai da zancen shi, batare da yako kula da wani zaran ido da nafisat keyi ba,
Bashir ne yadan kulada halinda take ciki a lokacin don haka ce mata yayi,
Kina mamaki ne ke ma ko Nafisa, a ce mace ta baro saudiya da ciki zuwa nan kasar aiba gaskiya bane koma dai may ne ai zata bari har ta haihu ai ko,
Nafisa tai karfin halin bashi ansa tace watakila wani abin ne yabata mata rai har yasa ta tafiya mai nisa haka,,
Ahmad yace ma bashir cikin murmushi
You know she is still young,
Bawai wata babba ba ce, barazanar Aziza ce yasa ta firgicewa a lokacin, don yadda taga Aziza tana farautar rayuwar ta dole ne ta firgice da ita,
Don a ranan Amal tace sintiri ta kwanayi a kofar na ta,
Tabbas kuwa ba aziza din bace inji nafisat ke wanan zancen acikin zuciyar ta,
To wa ce ce wanan mai cikin wace har kira da wai matar shi, don dai gaskiya ita a iya sanin ta bayan Aziza da ya aura a bayanta bataji yakara wani aure ba,,
Sunda dade nan gurin suna hiran su shida bashir don daga karshe duk kusan rabin hirar na hjy tsohuwace,,
Fitar Bashi keda wuya Ahmad ya mike da niyar ya shiga dakin shi yadan kwanta,
Nafisace tace mai wai wata matace kake zance Ahmad don ban fahinci maganar taku ba sosai,
Matata, Fadima wace kika sani a saudiya mana,
Fadima gabanta yaba da wani dam dam,
Takara nanata sunar a hankali ta ce fadima yar takaru,
Yace mata kwarai kuwa ita,
Matar kafa kace kuma harda ciki,
Cikin mamaki ya kalleta yace kina nufin kice duk tsawon shekarun nan bakisan na auri fadima ba ko may,
Zaune takai daga tsayen da take duk da sanyi A, C dakuma dan sanyin garin bai hana Nafisa fidda wani zufa ba a goshin ta,
Cikin rawar murya tace nasan za,a rina fadima nasan cewa zaki iya yin haka wallahi ko,
Wani irin kallo yai mata cikin rashin fahintar maganar ta
Yadan kalle ta kawai sai ya wuce nan yabar ta da dinbin tambaya a zuciyar ta,
Duk wani zagwadin kasan cewa da mijin ta da takeyi sai taji ya fice mata aran ta
Wayanta ta dauko ta dan na lambar mahaifiyar ta, kira na biyu tadaga wayan,
Cikin tashin hankali take magana da maifiyar nata,
Tace mama na shiga uku ashe Ahmad yana da wata matar bayan nida Aziza,
Wai har matar nada ciko a jikin ta,
Yanzu haka ma zancen da nake maki ma yana cikin kasar nan wai matar tashi ta gudo daga saudiya,
Saboda Aziza da tasata a gaba akan sai taga bayanta,
Sai da uwar taji ta idar da zancen ta ce maya nafisa ki kwatar da hankalinki ki natsu ki saurari abinda zan fada maki,
Kada ki manta yadda kika koma gidan Ahmad wallahi duk kikayi wani abin da ki ka jawo wa kanki matsala ba ruwana a ciki,
In ba abinki ba tunda ma har Aziza ta nuna cewa bata kaunar wanan matar ke mai zai hana ki nuna kulawar ki akai ta yadda Ahmad din zai kara amincewa da natsuwar ki,
Kafin uwar ta ce wani abu nafisa tace mama wanar yar iskan yarinyar yar aikin namu ce fa fadima nake nufi ya aura,
Uwar tace ina ruwanki aikowa da halinsa yake zama a gidan miji,
Badon taso ba uwar har taci karfin ta tai nadama, da zancen,
Washegari ne tafiyar su zuwa dogon daji,, motoci ukune kamar ta jiyan na hudun su hilux ce mai dauke da kaya ,
Motar farko wanan mutumin da zai gwada masu hanya ce tare da security guda biyu,
Mota ta biyu Sheriff ne tare da doctor kamal a, baya sai driver da ke jan su,, tare da Shehi a gaban motar
Mota ta uku Bashir ne ke jan ta, sai Al,mustapha da salim a ciki a tare da shi,
Bayan su kuma hilux ce dauke da kaya sai security ma,aikatar su a cikin motar,
Ba karamin gudu suke yi ba duk da kasancewar hanyar ba kyau ke gareshi ba,
Gudu kawai suke yi abinsu,
Doctor kamal ya,dan kalli Ahmad wanda ke ta , dajin da ake ta wucewa, tun dazu,
Cikin kada kai yace wa aminin shi, ya ce kadiba fa irin wanan nisan har a ce wai wanan yariyar ta biyo shi ita kadai,
Ahmad yadan nisa kadan ya gyara zaman shi, yace ma doctor, kamar kasan abinda ke acikin zuciya na wlh,
Yadda wanan matar tadauki yar karamar yarinya tun daga nan har zuwa kano da ga kano kuma wai har saudiya,
Wai bidar kudi kawai,
Kai mutane ba imani wallahi, doctor,,
Karfe uku daidai na rana su na cikin garin sakoto saboda uban gudun da sukayi,
Kasan cewar motocin su duk lafiyyau ne,

Yau tunda safe da na tashi sai kawai naji raina ya na baci don haka ba wani maganar kirki nakeyi ba,
Dama mariyace abokiyar zancen nawa sai ko innar mu da muke yawan zama tare, duk da wani lokaci Tumba takan shigo gidan mu hira wurin innar mu ,
Amma ni sam har yanzu ban sake jikina da ita ba sam don matar batai min ba,
Saboda mariya ta ji cewa wai zuwa takeyi dan taga ko wani irin launin da zan haifa,
Saboda tagane cewa dan larabawane ko bakar fata,,
Don taji dadin zuwa ta yada a gari, don gulma
Ganin da mariya tai min yau, shiru shiru ne yasa ita ma baitai wani damuwa na da surutu ba,
Bayan mun idar da sallah azahar ne innar mu ke ce min indan kokarta in tashi muje mu diba lafiyan kawu salihu
Wanda yai fama da gudawa yan kwanakin nan,
Duk da ba son fitar nakeyi ba amma ban iya cewa inna mu ban jin dadi jikina, yau, haka na daure na fita
Nashirya nida mariya muka fita, zuwa gidan kawu salihu,
A kan hanyar mune muka hadu da musa mijin hafsi, tare da malam Basiru,
Da alamar gidan kawu suka fito su ma don yar kwarkwadan da zata sada mu da gidan kawu ne muka hade da su,
Cikin girmamawa malam Basiru ya gaishe mu,
Sai kawai musa yace amma dai Basiru anyi mutumin kawai ,,,
Karasa wacce zaka duka ka gaida sai wacce ta fito yawon bariki,
Malam basiru ya dauka da farko ko wasa ne musa ke muna,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment