Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,
Muryan Ali baba yaji yana cewa sweet sahiba, mun gama meeting din ga shinan zan taso yanzu jirgin mu zai tashi,
Jiyayi kamar ya wurgata da wayan kasa ta raratse a kasa don ta kaici,
Watau ashe koda ya hanani kula da Ali baba, saida na kulashi,
Kai amma Ali baba yakai katon shege ji yayi kamar afili yake ya shake shi don takaici,
Nan da nan barebarin suka hau,
Jin shirun da Alin yayi yasa yake cewa hlo hlo,
Muryan sheriff da tai kama da ta zaki yace kai dan iska na fada ma cewa kafita hanyar wanan yarinyar tun farko to tana da aure a kanta
Inba hakaba zan iya halaka ka wlh ,,,,yana mai kashedi cikin kakausar murya,
Alin baba ya kalli wayar tamkar sheriff yake kallo a filin yace lalai ashe za,a ji mu da kai ke na Ahmad lawan zanna ai ban taba son abu inyi saurin jayewa ba da sauri,,,,
Abincin da bai ciba ke nan ranan saboda bacin rai,
Yasa noban na Alin a block,,
Kamar kada yaba ni wayana yakeji saidai kuma yace bari kawai ya mayar min dashi, tunda yayi blocking line din,,
Ai zai kama ni nan gaba indai ban daina ba ,
Abinda bai sani ba duk layin na Alin gudu uku ina dasu, a wayana,,
Amal tadawo cikin fushi don na bar school batare da najirata ba kuma Yusuf yace bashi ya dauko ni zuwa gida ba yau,,,,,
Maman Umar ne ke fada mata cewa banda lafiya ne shiyasa nadawo da wuri yau,
Sheriff na can saman kujerar dinning yana magana da Mr William, a video call,
Wurinshi tawuce direct kamar bata ga aziza ba,,,
Yayanmu sannu da aiki a hankali yadago yace, mata baiji ta gaida aziza ba,,
Cikin dan turo baki tace nafa gaisheta bata dai karba min bane,
Murmushi kawai aziza tayi mai nuna da magana gaba,
Saida suka ci abinci su ka huta tukun duk lokacin sheriff' yana gidan mu yana ta aikin wasu takardun masu yawa,
A hankali yake tambayar Amal da salim dake gefen shi,cikin yaren kanuri,
Batare da yadago kan shi ba yace mata tun yaushe nafara waya da Alin baba,
Gaban Amal yafadi dajin wanan tambayan don batai zaton jin haka gare shi ba
Cikin dan rashin gaskiya take gaya mai cewa gsakiya bata sani,
Abinda yakeyi ya wane ya dan kura ma Amal din ido, nawa nidan lokaci can yace mata, wayan da yabugo mata yau har yana cewa agaida ke ba gaskiya bane ko,
A,hankali tacd gaskiya koni tai min fada nadai ki saurarenta ne kawai,
Amma ayi hakkuri bazan kara ba,
Kafin yai wani magana su Umar ne da Aisha suka dawo daga school cikin uniform din su,
Jallabiya ce fara sol na maza sai na mata bakar jallabiya don duk kusan haka uniform din yaran kasar yake,
Direct gurin sheriff suka nufa sukayi mubayi,a dashi cikin murna da dokin ganin shi,
Sheriff yana son yaran sosa, haka kawai yaji yana son su,
Duk yagan su sai yaji kamar ace shine mahaifin, shi,
Wasa yadan yi dasu kafin su shige ciki cikin nuna kulawa,
Tunda muka zo yasa Yusuf yasa wata makarantar dake acikin unguwar mu,
Hakan da yakeyi da yaran yasa ni da uwar su muke kara mutunta Sheriff din namu,
Don yana da kokarin kula da duk wani wanda ke kar kashin shi,
Salimata ne tazo da mijinta don ya ganmu yayi muna godiyar dawai niyar da mukeyi da ita don duk wani kula juna da mukeyi tafada mai,
Kuma ya yaba da hankalin mu so sai tun bai ganmu
Nan suka zauna falo da sheriff suka danyi hiran gida Nigeria
Sai marance lis na farka daga barcin ganin da naima salimat ne yasa ni dan mamaki har kasa irin gaisuwar mu na yan Nigeria nai mai saida kamar yadda kowa ke fadi wai ban iya hausaba,
Muna ta hira sai naga kamar Aziza a matse take da zama agurin tana ta ya mutse fuska kamar mai jin warin mutane
Nace mata koza ta dan shiga daga ciki ta huta ne
A,a tace min kawai don duk ta matsu su wuce ashe tundazu take mai test a waya akan su tashi su tafi tana son taje tayi wanka,
Sai yafita batunta kamar baiji ta ba,
Sunyi musayar noba da mijin salimat sheriff yai mai alkawarin in ya shigo Nigeria zai ne may shi insha Allah,,,,
Da haka sukayi sallama damu suka nufi masaukin su, don duk aziza tagwada mai tagaji sosai
Ashe duk hiran da akeyi sheriff yana nan yana ta harara na ne kawai ya ma rasa ta inda zai bullo min akan zancen,
Sai bayan wucewan su ne ce Umar yadauko min wayana in diba,
Kusan 4miss call nagani da layin etisalt din Ali baba
Nai mamaki da bai kirani da layin da ya saba kirana dashi ba,
Kiranshi nayi sai yace min in bari yakirani
Yace tundazu yake kirana don sundan sauka wata kaaane adan huta amma insha Allah yakusa tasowa,
Har zan kashe waya sai naji muryan shi yana ce min fadima Ahmad yana gidan ku har yanzu ko ya wuce ,
Damamakin yadda yasan cewa Ahmad na garin yasa nace yafita sun tafi inda su ka sauka,
Cikin sanyin murya yace min ya akayi yadauki wayan ki,
Da mamaki nace yadauki wayana fa,aini ga wayana a hannu na,,
Dan murmushi yayi har inaji tawayan yace min suyi waya dashi dazu tawayana
Indai bari inyazo zaimin bayanin komai,
Mukayi sallama yakashe wayan,.
Aiba shiri na ce ma Amal taji wai sherrif ya dauki wayana yau har sunyi magana ,,
Cikinbko in kula tace min may yasa na aje wan inda zaigani
Nafada mata yadda mukayi tun dawo wana gida har yadda,
Nayi barci nabar wayan, nawa a falo, inda yagani yadauka

Amasaukin su duk abin duniya ya ishe shi taya har Alin baba ya samu karbuwa a wurina
Saboda iya sanin da yai min ni mace ce msi kamun kai da sanin mutuncina na "ya mace
Saikuma gashi Alin na so ya cutar da ni ,
Baikai karshen tunanen shi ba wayan shi taikara, Abba ne yakira shi,
A sanyaye cike da girmama wa ya gaishe da Abban daga can dayan sashen Abban yace mai ya aiki ta jama,a
Ya ce to babana ina nan dai ina ma tuni akan matar ka kayi hakkuri kazo kadauki abin ka
Tunda tagyara halinta yanzu duk wanan mugun rayuwan ta daina su,
Shiru Ahmad din yayi yana sauraren shi,,, shi
Cikin hikima da iya kwanrar murya yaje fada ma Abban shi cewa yayi aure a dubai,
Abban yai dan shiru nawani dan lokaci,
Can yace ma sherrif din babana kai aure batare da sanin mu ba,
Yace Abba kayi hakuri auren ne yazo min abazata wlh,
Shiru Abban yayi tare da cewa to Allah yasanya alheri ya ansa ahankali da cewa Ameen,
Can Abba yace to ya makomar ita nafisat din yake yanzu,
Dan shiru yayi tukun sai yace yana nan Abba,
Zanzo insa agyara mata gida a Abuja ta zauna can, don yanzu kusan aikina zai dan koma can Nigeria ne,
Sukayi sallama da Abban da shi,
Abban yai dan shiru yana kallon wayan yana mai tausaya ma dan nashi saboda irin sanyin zuciyar shi,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
AMINCI WRITERS ASSOCIATION
🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁
🎁N🎁W🎁A

Almost true life story

Aiki sosai so sheriff sukayi a garin don company su da Abu Abdallah ya yi girma sosai kusan duk manyan biranen kasan na saudiya sun kafa ma,aikatar su,
Sai bayan kwana biyu Alin yazu gurina lokacin sheriff ya wuce washegari ke nan,
Nai mai komai nataron bako nida Amal yai muna tsara masu kyau kayan sawa ne irin na matan kasar Paris,
Sai wasu set din sarka da dan kune masu tsada gaske,
A falon mu na sauke shi, inda ya samu tarbo na mutunci daga gurin maman Umar,
Duk kunya ya lunlube ni don tunda nake bantaba tsaya da saurayi ba da sunan soyayya,
Yausai gashi wai nice akazo wa hira ,
Cikin dakiya da daurewan zuciya nake duk na wani daburce,,,
Daguda guda kowa ya watse falon aka barni da gani sai, Alin kawai,
Shiru yadan biyu baya kadan. Kaina yana akan wayana ina dan daddanawa,
Jin shirun da nayi yasa nadan dago kai inga komai yakeyi,,,
Ido muka hada dashi, ashe zaune yake yakura min ido kawai yana kare min kallo,
Acikin zuciyar shi yana yaba min komai nawa yayi mai yadda yake burin ya mallaki mace,
Dadin dadawa gashi ni yar karama ce sosai , don yanzu haka ban fi sha bakwai ba , yake gani,
Kunya ne ya kamani ganin irin kallon da yake min
Tambayana yayi yace min ya yaga na yi shiru, irin taron da zan mai kenan
Duk zumudin zuwa yaganenin da yake yi,
Da sauri nadan dago kaina nadan kalleshi sai kuma na kawar zuciya na fal da mamakin shi amma sai na dake na ce mai
Cikin murya mai jan ra,ayi da daukan hankali wanda ni kai naban san ina yi ba,
Nace wani kuma irin taro kake bukata wanda yafi wanan din da nai maka,
Matsawa yayi zuwa dayan kujeran da ke fuskanta na yace,
Yace min look fadima ina son kisan cewa aure nake son yi da ke
Very soon ba dadewa ba so ina son ki fadamin gaskiyan zuciyan ki
Don kisan yanzu ni bazance na tsaya wani wasan soyayya ba,
Indan kin amince min zan ga Ahmad yakaink gurin iyayyennki don in gabatar da kaina garesu
Yakarashe zancen yana mai komawa saman kushin din, yadan jingina bayan shi da makarin kujerar
Yakura min ido alamar yana jiran asa ta,
Jin shirun da nayi yasa shi kara ce min,
Ke nake sauraro don banson zuwa wurin Ahmada batare da naji wani kwakwaran magana daga gare ki ba
Ke nake sauraro fa na tsinkayi muryan shi cikin kun,nuwa na,
Bansan lokacin da nadan dan,dago kaina ba muka hada ido sai na sakar mai dan guntun murmushi,
Ok kina nufin kice min kin amince min ke nan ko
A hankali nadan daga mashi kai alamar eh,
Cike da mamakin wanan saurin amince mashu danayi yake yi
Don bai dauka abin zai zo mai da suki irin haka ba
Ajiyan zuciya yayi yadan tsinki Anebi da maman Umar ta aje mai acikin plate din dake gabashi tab da kayan fruits,.
Yana taunan Anebin din yake ce min ya akayi ranan na aje wayana har Ahmad ya dauka
Murmushi kawai nayi batare da na bashi ansa ba na ce,
A hankali nace mai lokacin banda lafiya ne, acikin mamaki yake ce min har ciwo nayi shine ban fada mai ba,
Haka mukai ta dan hira jefi jefi dashi cikin rashin walwala,
Sai marance lis yai muna sallama zai tafi kuma yace muna ba kwana zaiyi,
Har bakin motar da yazo da ita na rakashi,
Cikin kulawa da kuma kewar juna muke sallama hannu na yana irike da Aisha,
Wace keta dan kokarin in saketa taje tadan yi wasa,
Muryan Alin ce ke ce min Can I trust You fadima,,,sai na kada mai kai ahankali.
Yace duk ritsi da zamu shiga da Ahmada kada kice mai kin jaye zancan auren mu nida ke a nan gaba ,
Pls sai ya hada hannu shi guri guda duk ka biyu yai min alamar rokon Abu,,
Yashiga motar shi yana daga min hannu ciki shaukin so da kauna mukayi sallama da junan mu,,,,
Saida motar shi ta ba ce min da gani san nan nadanyi ajiyar zuciya na koma cikin gida,

Ina shiga gida na iske Amal tsaye da wayana a hannunta
Fuskanta kawai na kalla nasan cewa akwai magana ,
Inda take tsaye na nufa cikin damuwa nake tambayar ta ko lafiya naganta haka,
Batai min magana ba saida ta zauna saman kujera ta miko min wayana a hanmukeq,
Nakarba ina ma wayan kallon mamaki, sai kace zan fahinci wani abu acikin wayan,
Wuri na samu nima na zauna gefen ta kadan don nasan cewa da magana a irin yanayin da naga Amal ciki ,
Fuska a daure batare da ta kallo ni ba tace yayan mu ne ya bugo waya kisan idan ya bugo sai ya tambayi kowa abashi su gaisa nace mata eh hakanane
Yatambaye ni ina kike nace mai kina barci sai yace min ba gaskiya bane,
Don bai taba ganin kinyi barci by this hours ba,,,
Sai ce min yayi kina waje tare da Alin ko , shirunayi kafin in bashi ansa har ya katse wayar ko,,,
Wani dan dum naji sai kuma akarshe nace to ma maye na boyo aciki tunda ai dole yasani
Sai kuma na tuna irin warning din da yai muna kafin muzo karatu,
Nace to in har yafitar dani ai Alin zai iya karasa biya min kudin karatun har in karasa abina
Amal ido ta kura min tana kallo na ina cikin nazarin abinyi,
Sai tace min gaskiya fadima yadda kika bari har son Alin ya shige ki baki kyauta ba,
Tunda kinsan cewa yayan mu yai muna nasihan akan kada mu yarda mu kula kowa har sai mun gama karatun mu,,
Tunda ta fara magana bakinta na tsura ma ido har ta kare zancen nata,
Gani irin kallon da nake mata yasa tagane cewa nayi nisa ko cikin wanan tarkon da na fada,
Tace nidai shawarar da zan baki shine a matsayina na yar uwanki kuma mafi kusa dake shine
Kibi a,hankali tunda har kikaga yayan mu ya nuna bai ra,ayin hakan, to ki daina
Saboda shi namiji ne kuna shi ke tare dasu shiyasan halin su,
Don dai kinga bazai cutar da mu ba,
Tagumi nayi da hannaye na ina kallonta,
Itakuma sai taci gaba da fadin namiji abin tsoro ne,
Kibi a hankali don yanzu muke idan lokaci yayi sai muyi abin mu,
Magana kawai takeyi nikuma jinta kawai nakeyi don nayi nisa ko,
Ta lura da ni sai ba wai na yarda da shawaranta bane,
Don haka tashi kawai tayi tai shigewar ta tabar min falon,
Hakan da tai min sai naji banji dadi ba,
Hutu mukeyi dama ba wani karatu mai dan yawa agaban nima shigewa nayi abina,
Tunjiya nake cikin rashin walwala saboda maganganun da mukayi da Amal,,,,
Maganar tasani cikin damuwa don dai gaskiya ina son Alin
Amma kuma maganar sheriff tayi min tasiri azuciya na
Saboda irin taimakon da yadinga min ba cutar wa a rayuwa saidai shukuran tsakani na dasu,
Shin idan har naki bin maganar wanda yake kamar uba gare ni ai nayi butulci mai karfi ,
Tsuwar da wayana keyi yasani dan farfadowa daga cikin tunanen da nakeyi
Sai gabana ya dan fadi don nasan cewa sherrif ne ke kirana tunda tunjiya bamu gaisa ba
Wanda akullun dole yagaisa da kowan mu,
Saboda yaji lafiyan mu Sunan Salimat ce nagani ta ke kirana,
Saida nadanyi sanyayan ajiyar zuciya danaga itace,
Ina dauka tacs min mufito mutafi masallaci don mu samu jam,in jumma yau,
Cikin sauri natashi na shirya don sam na manta cewa zamu iya makara idan mun wuce shadayan rana bamu fita ba,
Bandau wani lokaci ba ina shiri nafito abina tsab dakin Amal na nufa itama acikin shirin ta nasamay ta duk da tun jiya sama sama muke da ita,
Saboda maganganun da mukayi da ita din,
Ganin datai min yasa tamike don tasan inda zamu,
Da kafa muke rafiya zuwa sallah jumma,a kudi nadauka da zamu fita,
Duk da saurin da mukayi mun iske har ta wajen haraban duk jama,ane zazaune suna jiran lokaci,
Har Ciki muka kusa muka samu wurin zama,
Saida naga mundan zauna nafito waje saboda na tabbatar da mun samu gurin zama ko,
Wurin saida alkama natafi na saye mai yawa, da hannu na naita watsa ma tanatabaru cikin masallaci wanan alkaman sadaka, akan ina bidan sauki ga al,amarina,,,
Saida nagama watsa masu san nan na nufi hanyar toilet naje nadauro wani sabon alwala nadawo inda mukasamu guri na zauna,
Har Umar da Aisha muke tafiya masallacin don haka da dan kulan abincin su muke zuwa don sai dare muke barin masallacin,
Har aka idar da sallah akayi na la,asar muna nan zaune,
Kafin ai sallah magrib muka tafi ziyaran rauda, muna dawowa muka fito wajen harabar masallacin don idan an idar da sallah mu samu hanyar fita dmukeyi
Muna nan zaune aka fara bude lemar haraban masallacin suka fara ma haraban feshin ruwan almuski da sanyi na,un,,,
Muna na har aka tashi saida mukaga Salimat ta shiga gidan ta sannan muka kama hanyar namu gidan,
Gab da zamu shiga kwanar layin gidajen mu ne kiran wayan sheriff yashigo min ,
Namika ma Amal wayar ta karba tare da yin sallama nan ya sheda mata cewa zai dawo saudiya gobe insha Allah muma yanason mu hadu a garin makka agoben tunda hutu mukeyi
Duk da ina son zuwa makka yau sai naji,
Sam sai banji dadin hakan ba araina saboda ina gudun haduwar mu da Sheriff din mu,

Tunda safe mukabar garin madina zuwa makka,
Kallon dajin kawai nakeyi wanda har kullun ina naga nisan tafiyan da mukeyi a mota, sai in kara jinjina ma Annabin rahama tare da masoyin shi Abubakar,
Da su arakumi sukayi hijara daga makka zuwa madina,
Amal ke ce min idan mun isa muje muyi umurah, kafin mu isa gida
Tunda sheriff yace daga Malishiya zai zo goben,
Kinga kafin ya iso mun sauke nauyin ko,
Kai kawai na daga mata don nasan cewa wanan tafiyan kusan don nice za,ayi shi,,,
Muna shiga gari muka wuce mukayi umurah duk kan mu,

Yau shekara daya dawata tara ke nan rabonmu da garin makka,
Kallon ko ina na garin nakeyi cikin jin dadi da tuna wasu abubuwan da suka faru da ni lokacin ina yar karama da nazo garin,,,,
Lunshe idona nayi ina tuna Rugaiyya ta yar uwata masoyiyata mai kaunana tsakani da Allah
Hawaye naji masu zafi sundan sulalo min a fuska na daga cikin idona,
A hankali na goge su sai kawai naji raina yawani yi min bakikirin wlh,
Nanda nan kewar Rugaiyya yadawo min sabo fill a zuciya,
Ko saudaya banta tunanen cewa wai Kudina yana gurin Rugaiyya ba,
Iyakadai ina mata fatan Allah yasa tasamu ta tsira da kudin ba,a karbe mata ba,,,
Gidan na Sheriff yana nan tsab kamar yadda muka wuce muka barshi
Saidai tun shigar mu naga wasu yan bakin fuska agidan ba wa yanda nasa ba ne ada,
Ina murna yau zanga yumma da su Sukaina da Mari,
Hjy ma fushi zandanyi da ita tunda sau guda taje tadiba ni ,
Amma duk dadewan nan ko waya babu
Troller's din mu aka kai muna cikin gida har da su maman Umar da mukazo wace muke jin dadin zama da ita sosai ,
Matace mai sanin yakamata kuma batayarda ta saba ma ko gudan mu,
Idan kuma taga zamuyi abinda ba daidai ba batayarda muyi shi,

Dakina na fada tunda mukazo nashige abina nafada bayi nai wanka nadauro alwala,
Bayan na sallamay sallah na nadan zaina gurin ina dan tunane,
Daga nan natashi don inje ingaida hajiyan mu da su yumma, tunda nazo basu zo suntare ni ba,
A hankali na ke tafiya cikin wani dogon riga mai kama da silk ina tafiya yana shaking,
Ina zuwa sashen dakunar su sai nai turus, wuri guda ganin dakunan nasu duk arurufe suke, ba alamar akwai mutane aciki,
Da saurina karasa har kofan dakunan nasu sai ga ,alamar andade ba,a cikin daku nan don duk wurin yayi dan datti da yanan gizo
Hakan bai isheni shedaba saida nadan tura kofan inji ko abude suke,
Gabana yaba da dam dam dam,
Cikin wani irin sauri nake tafiya kamar zan tashi sama, don sauri,
Tunane nakeyi azuciya ina hajiyan mu da su yumma, ina yan uwana, ina gatana ,
A falo mukayi kicibis da sheriff shida Salim ganin da yai min cikin tashin hankali kuma yasan daga inda nafito,
Cikin daga muryan da bantaba yi ba agabanshi yau nai magana da larabci mutanen akbass nake magana cikin sauri sauri nace ina hajiyana da yan uwana suke,
Ido ya kura min kamar wanda ba zaiyi min magana ba,
Sa can yai magana cikin murya mai taushi fa natsuwa yake ce min
Shine gaisuwar da zan mai kokuwa shine karatun da nakoyo,
Sai alokacin nadan sami nadan yi kokarin natsa kaina guri guda,
Nagane cewa ban ma gaisai dashi ba, sam na ma kasa ganin cewa yanzu

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment