Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasu rigar barci light pink, wando da riga,
Nadan sa ma kaina wani hula mai hooking din kan mutum,,,, baka jin komai sai karan A, c dake ta faman aiki,
Kusan irin zafin da ake yi a wanan kasan,
Shiyasa idan kana tafiya zaka ga tankin ruwan sanyi masu kudi sun aje gefen gidajen as a sadakatujar, sai dai mutun ya tsiyaya yasha ya wuce,,,
Shiyasa koda yaushe,AC kune yake muna,,,
Aisha ce a tsakiyar kafafuna tai barci sai dan buga mata kai da nake yi don ta samu tayi barci da kyau kamar yadda uwaye kewa diyan su,,,
Wasu hawaye masu zafi ke tsiyayo wa daga ido na, babu kakauci,
Kallon yariyar nake yi wace tausayin mu ya ke kara sa hawayena zubu min,
Yanzu a haka zamuyi ta zama ba wani galihu atare da mu
Kulun gamunan kamar wasu marasa gaskiya, ashe mu,
Kamshin da naji yasa nasan kowaye a dakin nawa,
Kallon agogon da ke dakin nawa nayi goma da rabi na dare yanzu,
Sheriff nace cikin siririyar murya, gyara kan Aisha nakeyi don in tashi ,
Hannu yadaga min alamar in zauna inda nake,
Ina zaune shima yasamu gefen guda abakin gadon yazauna,
Batare da ya kalleni ba yake magana,
Bazaki daina wanan kukan haka ba ko,,,,, ko so kikeyi ki shiga cikin wata matsala, wanda zai saki cikin wani hali,
Yakamata yanzu ki bidi mafitar da zai fishe ki,ne baki zauna kina wanan kukan ba,
Dan sheshekan kukan nake yi kadan kadan
Muryan shi nakara ji yana cewa kin taba yin karatu ne kai na kada mai alamar eh
Nafada mai ko aji nawa nake agida kafin gajiye ta zo dani kano,
Sai kuma karatun da na a Riyadh wanda baban Nailabin yasa ni,,,
Ina takardun naki, suke, nace mai suna nan
Ya mike yana fadin da safe ki kawo min indiba, ingani,
Ki kwanta hakana ki daina wanan kukan zan san yadda za,ayi ku koma gida duk kan ku Insha Allah,
Banko yi mai godiya ba yafita gami da jamin kofar daki na,
Koba komai naji dan sanyin wanan maganar tashi sosai
Don ko waye ke cikin wani hali yana son maidan bashi magana,
Don haka gyara ma Aisha kwanci nayi najawo bargo muka shige ciki,
Ba da wani dadewa ba barci yadau ke ni tare da dokin gobe yayi,,

Washe gari ban fito ba saida nayiwa Aisha wanka muka gyara jikin mu,
Nida ita gurin da hjy mu take muka nufa don mu gaishe ta kafin in fara aikina,
Umar na dakin tare da hajiyan mu, nan nakaishi ya kwanta don kar mu barta ita daya,
Saboda yaron nada kwazo yana kuka da hajiya,
Wanka nasa shi yayi bayan na gyara masu daki yadda yakamata,

Saida nadiba komai na abincin gidan da aka dafa,kamar yadda ya kamata sannan nakai saman tebur din su,
Nashirya komai neat ,bandade ba naji fitowar su,
Nafisat na bin shi a baya tana cewa gaskiya ita ba tagane ba duk inda zata sai ace dole saita fita da wanan yariyar
May ake nufi da ita ne ko yana nufin wanan yarinyar ta fita wayewa ne,
Sai alokacin ya juya yadan dube ta cikin takaici,
Ya kuma juya ,yacigaba da tafiya zuwa dinning table , yaja kujera yazauna,
Saida nagama hada mai abinda yake son ci ina kokarin wucewa,,,
Yace min in shirya zamu fita da nafisat unguwa cikin ladabi na ansa mai da toh,,,,
Har na juya zan wuce sai yace min,,, ina takarda da yace in bashi, cikin sauri naje nadauko mai nakawo mashi
Batare da ya duba ba yasa cikin briefcase din shi yarufe,
Wani wawan harara nafisat ta watso min daga inda take tsaye,,,
Niko, ko in,kula nai mata,,,,
Dakina na nufa na dan kara gyara jikina sama,sama,
Natura Aisha wurin su hajiyar mu har in dawo
Duk cikin sauri sauri nake,komai don kada in sa nafisa jirana har inyi laifi,
Aiko ina zuwa a mota nasamu, su ita da driver zaune suna jira na
Ina ganin su sai nadan ji shock kadan amma sai na dake ban nuna ba,
Zaune take tana dakilan wayan ta ko kallo ban ishe taba tayi wani kicin kicin da fuskanta,
Nadan masu sallama nagaishe ta,
A wulakance,ta ansa min gaisuwar nawa, gami da watsa min harara,
Tace min sai ki shigo mutafi tun dazu muna jiran ki,
Sai lokacin da kika ga dama zaki fito,
Ke wanan yariyan na lura da ke tunda kin samu shiga gurin maigidan shine,
Kike kokarin hada kanki da ni wlh ni maganin ku zan yi,, yar kauye kawai matsiyaciyar banza
Sai na gwada maki cewa tsintacciyar mage bata zama mage,,
Naikamar banjita ba,ban masan dani ta ke
zancen ba ,,,,
Ina ganin haka na bude gaban mota nashiga abina nai ko in kula da ita,
Saina kama magana da larabci da driver ina ce mai ina zamu ne,
Yace bata fada mai ba shima, kawai sai muka sa kai muna ta tafiya,
Haka muka hau titi babu wanda ke maganar cikin mota,
Har mukayi dan nisa da gida
Danaji shirun yai yawa a motar, sai kawai na jawo wayana dake cikin jakata na fara, game,,
Aiko tana kyala ido taga wayana da nake game da ita,
Ji kawai nayi ta wauto wayar daga hannu na tajuya tajuya sai naji tayi tsuki kawai ta wurga min saman cinya na,
Mashal plaza muka je cen kusa da top ten plaza,
Kayan make-up tadan saye da sauran kayan bukatun mata,
Muna futowa muka shiga cikin top ten ,
Anan naga kayan yara masu saukin kudi sai na dan sai ma Umar da Aisha
Saboda duk kayan su mubar su can gidan mu,
Kuma badamar wani yaje ya kwaso masu,,,,
Ina kallon anty Nafisa na saurin zuwa biyan kudi don kada ta hada danawa,
Dariya tabani kawai don inda sabo nasaba da halinta, don komai nata ba mai ci agidan nan,,,,, nidai na biya kudina cikin chiefest price, saida nayi mamaki, jin kudin cikin sauki haka,na,,,

Bayan mundawo, gidane tawuceni fuuuu zuwa cikin gida, kayan nakwaso zuwa dakin ta,
Koda nashiga nata nasamayta har ta dan kwanta saman gado, tana waya,
Daidai lokacin tana fadin wlh duk tsiyar da zamuyi salwa saidai muyi
Mutun ace bai san darajan mace ba shi nashi kawai zuwa aikini kodyau,she ,,ni gaskiya ban iyawa,
Saida kawai ace wai yar aiki ce zata raka mutun don kitifi,
Kayan da ta sawo nake gyarawa asaman dressing mirror dinta
Amma azahiri ita nake sauraro ba wai aikin nake yiba,
Yaushe ne zaki ba da sakon a kawo don in fara barbada wa dan banza,.
Wani iri naji lalai wanan matar batada dama aiko zamu kwasa da ita ke nan,
Muryanta naji ta cigaba da fadin ai ina nan ina kokarin binciken inda takardun suke fara daukowa
Kalonta nayi cikin sauri wanda ita din ma,kallo na tayi batare da zargin ko naji may take cewa ba,
Tai min nuni da hannu cewa in wuce,
Daki na nakoma cikin yanayin damuwa, don nasan cewa akwai aiki ja agabana,

Tundaga wanan ranan nafar sa ido ga al,amuran nafisa sosai,
Tundai ma danaga wata bakuwa tazo wurita daga Nigeria
Wai umurah matar tazo shine aka bata sako takawo wa nafisan,
Aiko zargina yazama gaskiya don wasu magunguna ne kuli kuli a,kabata
Bayan kwana kamar uku, da kawo sakon Allah yabani sa,a ta tafi ganin masaukin bakuwar
Anso zuwa dani sai na kwanta nace banda lafiya,
Suna wucewa na kwashi sakon maganin sai masfala gidan hajiya laila,
Duk wanda muka bude an rubuta bayan nin shi da yadda zatayi amfani da shi,,,
Hjyan ce tai min dabara tasamo kayan mata masu kyau muka sa mata cikin kowani leda, ,,,ba wanda bamu canza ba
Nadawo gida na mayar mata da abinta inda taje,
Naci gabada harko kina,
Ina kallon ta lokacinda take barbada mai wanda akace ta sa mai ga abincin shi,
Dariya yakamani nagudu zuwa dakina naci dariya na can kamar in nutse,
Washe gari koda nashiga in gyara mata daki na isketa tayi daidai sanan gado tana wani lagabewa,
Aikinta takeyi waya, tana fada ma salwa cewa kwanan nan batasan may yasamu Sheriff ba don bai ko tausaya mata,
Dariyan keta yakamani
Nace lalai hjy laila takai tsuhuwar bariki,

Yanzu hankalin mu kwance gaskiya don mun rage wani fargaba kasan cewar muna da mafaka mai muhinmanci,
Baza,a taba zargin muna da halaka da takari ba in mun fita don duk inda zamu da motane ba wani labe labe ko bin lungu lungu, gudun kada akama mu,
Yauma nafito ne don in sayi kayan abincin mu da yadan kare,
Ina cikin wani shago sainaji hayaniyar mutane a kofar shagon,
Da sauri na biya kudina nafito bakin shagon da ,
Wasu takarine askarawa suka biyo su uku gudan wai tana suyan dankalin turawa sukuma saura su tsaye abakin titi suna saida gumama da rana,
Suna ihu suna bidan agaji amma ba wanda ko yakalli inda suke,
Inaji yar matashirya wace muna iya yin wari da ita tana fadin cewa uwar da ubanta duk suna gari ita ba takari bace,
Cikin dakiyar zuciya ganin kowa yaki ceton ta naje gurin nace masu ai,yakamata suyi mata uzuri tunda sunji abinda tace
Jinda sukayi larabcina tsab bakamar na yan koyo ba yasa sukadan saurareni,
Suka kalli yanayina sai sukaga banda alamar shigan banza
Nan shugaban nasu yace min intanbayeta ina iyayenta,
Karya nai masu nace iyayen ta suna nan harda kakaninta ma nabasu wrong address ,
Wanan yariyar tasamu tasha da kyat wurinsu nima dim gabana sai faduwa yakeyi,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

Almost true life story


Saida naga cewa mun daina ganin yan bagaladin mun masu nisa sosai
Daidai,Lokocin na danyi ajiyar zuciya, nakalli yariyar da muka kwato daga, hannu yan bagaladin,,,,,
Wace sai dan she shekar kuka takeyi tana, ajiyar zuciya kai da kai tanayi, tana dan share hawaye, a fuskanta,,,
Dafata nayi ina Tabayarta ko daga wani unguwa take
sai da ta dan share hawayen da ya dan silalo mata,
lokacin take ce mun ai daga wani dan kauye dake kusa da gari, take shigowo ,
Kauyen baida nisa da cikin gari can tsakan wasu duwatsu yake, larabawan daji ke zama agarin
Inda Mafi yawan yantakaru sun fi labewa a kauyu, ka mafi kusa da garin makka, don gudun kora,,,
Gida nazo da ita, nadan bata abinci ta ci ta, huta, amma duk a firgice take saboda tayi fitar kutsun yau,
saida naga hankalinta ya dan kwanta,san nasa a,kaita har inda zata samu motar da zai kaita kauyen na,su,
Tawuce tana ta zabga , muna godiya tana sharan fuska,,,,
Muna tsatsaye a waje duk jikin mu yai sanyi
Don muma mun san cewa bamu wuce hakan ba,,,
Duk sai ta bamu tausayi wlh,,,, wasun mu harda kuka,

Washegari dayake ranan weekend ne saboda su kasar saudiya,Alhamis da jumma,a, ce weekend nasu,,,,
Don haka nasan cewa mai gidan yana gari don duk sallar jumma,a a garin makka yake yin ta,
Hakane ma yasa yafizama a garin fiye da ko ina, don yana yawan yin dawafi duk ranan jumma,
Shiyasa mukatashi dawuri don muyi aiyukan mu saboda tun karfe goma yake wucewa masajid
Saboda koea yassn cewa idan kakai shadayan rana da wuya kasamu cikin masallacin saidai kasamu gefen masallacin ta waje koshi a mamatse,,
Don haka, Tunda safe natashi don mu yi aikin mu cikin lokaci kafin ya fita,
Nasan cewa yana dakin motsa jiki don halinshi hakan da yadawo daga sallah asuba indan sungama karatun Al,kur,ani maigirma,
sai ya sauya kayan shi zuwa na games wear,,,
Idan nasan yana dakin yin exercise ka,ida ne dole inkai mai cup da goran ruwa mara sanyi guda sai kuma milk mai sanyi ,sanyi guda,
A gefen wani dan standing table dake gefe tsaye nake aje mai,
Duk da nasan cewa bai shan koda rabin kofin milk din saidai hakan bai hana kulun in aje mai ,milk din ba, amma,na ruwa sha, kan shanyewa yakeyi kafin yafito,,,,

Yauma haka dine ya kasance,,, ,yana tsaye yanata tafiyan daba iyaka bisa exercise machine,din shi,,
A hankali na shigo dakin hannu nadauke da tire din drinks,
tunda nashigo nagan shi saye da dogon wando irinta maza masu exercise, da bakar singilati, sai yar karamar tawul da ya, rataya saman wuyan shi,,,
A hankali na isa saman dan tebur din na aje mai dan ture din da na hado mai drinks din ciki,
Na juya don in fita dakin,
Karar waya shi da yaji,,,yasa shi dan tsagaita tafiyan da ba tsayi din, dayakeyi,,,
Da hannu ya nuna min gefen da wayar ke yar tsuwa,,,
Nagane nufin shi indauko mai ita yake nufi,
Wayoyi ne kusan guda uku a wajen, ashe,,,
Ita mai tsuwar ita ce nadauko mai, ashe wanyan mutanen Nigeria ce, sunan yan uwan shi ne kawai aciki sai abokai shi, yan kasar Nigeria,
Malam baba naga an rubuta baro,baro, a fuskan wayan
Ina mika mai wayan yadiba yaga kowa ne ke kiran shi yanzu cikin wanan lokacin daga nigeria
don yasan cewa ana batun sallah asubu ne yanzu haka a Nigeria
Tunda munan a,lokacin karfe bakwai darabi nasafe, ne
Wanda yayi, daidai da karfe hudu darabi na asuba, a Nigeria,
Yana ganin sunan malam saida yaji gaban shi yafadi, don yasan cewa ba kiran lafiya bace
Don iyakar malam din yakira shi da misalin karfe biyun rana na nageria lokacin muku ma ana batun yin sallah la,asar
Daidai lokacin danaga yadaga wayar
Nikuma ina shirin barin dakin sai naji yana fadin Innallahi,
Da karfi na waigo don nasan cewa wanan kalman ba karamar kalama bace ,sai idan tashi hankali yasamu bawan Allah,
Ganin ina kallon shi cikin tashin hankali yasa shi dan controlling din kan,shi,,,
Jinayi yana fadin tun,yaushe ne ciwon yafara mata haka malam,
Sainaji ya ce dan Allah malam akaita asibitin Maiduguri zai ma Abba waya kafin ku zo, asan abinyi,
Karshe dai yace ma malam din insha Allah gashi nan zuwa, shima,
Batare da yadauki ruwan da na aje mai,ba yasauko daga machine din,yanufi hanyar fita, dakin yana fadin ,
Kiramin Almustapha, da sauri,,, pls
Bayan shi nabi cikin sauri don zuwa kiran almustaphan, din

Kafin wani dan lokaci komai na tafiyan shi,an kan mala mai, anshirya komai zuwa Nigeria
Su Almustaphane suka kaishi jidda don booking din jirgin su kayi tun kafin su iso ,jidda wasu ne sukayi mai hanyar komai, don sun saba dashi,tun baro Nigeria dayayi zuwa nan
Suna isa sunyi sa,a dama an mai booking din jirgi
kusan daidai time din da jirgin zai tashi su, suka iso wurin

Mudai mun san cewa ba tafiyar lafiya sheriff, yayi wanan tafiyan ba
don ni agabana akai mai waya din, akan mara lafiyan da yatafi,
Amma sai gashi ga mamakin mu,
munga matar gidan sai busha shanta takeyi,ba abinda yadamayta,ita
Don har wata kawa tasamu wai ita yar lici,,,, wata fara duk man bilicin ya bata mata fuska kamar kuturuwa,
Tana magana tana kashe ido tan turo baki, wai ita yar takari,,
Saboda yanzu kusan sau biyu kenan ina ganin Yar lici agidan namu,
Wace hararane kawai ke rabani da ita, idan tagan ni,
Don ina ganin ta sai naji kawai batai min ba don wata irin gogagiyace da ganin ta,,,
Tunda sherrif din mu ya wuce zuwa nigeria
suke zama a falo suna ta sa kade kade da raye raye dasu, wake,waken su ,na bin rawar,
Mu ko, Sai, Abinci da muke ta aikin dafawa, kala kala,
Don basu koshi sam sanan
Ga wani irin shewa da sukeyi kamar an gafarta masu, zunuban su
Yau duk nagaji da aikin da mu kasha saidai kuma idan na tuna cewa sheriff din mu yayi tafiya cikin tashin hankali sai inji duk zuciya na ta min,suya,,,
Duk da bansan koma may ye matsalar ba, ,hakan baisa nadaina jin bacin rai ba,don nasan ba ta kyauta wa mijin nata ba
,Don inga mutunci ai duk abinda yasamay shi ai yasamayta, itama,,,,
Amma sai ga amatsayin matar shi tana, ta holewar ta, ba abinda yadamay ta ita,,,,,
Duk gidan kowa sai mamakin ta yakeyi, don dama da ganinta kaga tantiriya,

Tafiyan shi da kwana biyu ina zaune dakina ina gyara ma Aisha kai sai naji wayan intercoms na dakina ya na ruri da alamar ana bida na afalon, gidan,
Batare da bata lokaciba na isa falon, cikin sauri,
Almustapha ne nagani tsaye yana jirana da waya a hannun shi
,ina isowa yamiko min wayar, dake a hannun nashi,wace dama a kune take nikawai ake jira inzo in ansa,,,
Nakara wayan a kune na ina mai sallama,
Muryan sheriffudeen din muna ji cikin muyar mara sauti daji zuciyan shi badai
yana mai kara yi min sallama shima,
Nakarba da wa,alaikumu salam,
Yace min don Allah yana son in taimaka mai in gyara mai wasu dakuna daga cikin gidan
wasu dakuna ne ke cikin gidan da baki ke sauka wanda ke kusa da shiyan nafisa,
Sai kuma yacigaba da fadin,
Kuma in yi kokari don Allah, in,bidi abincin da masu ciwon sugar ke ci in,tanadar mai su agidan kafin ya iso,,,
Cikin siririyar muryan da take dauke da kama da kasala,
Yace ina ji na ce eh ina madaga mai kai kamar yana gani na,,,, yace min
Idan har ina bukatar kudi in tamabayi Almustapha zai bani,
Sai dan shiru ya biyo baya,saina ji yana magana,,
Yace yaji ance nafisat bata gida kuma ko jiya yakira an fada mai cewa tafita,
Saina ce mai nayi ai badadewa zatayi ba yanzu zata dawo,,,,
Cikin tsawa yake fadin kira na ukune fa yai mata yanzu
Yakare da fadin ina fatan kin fahinci duk abinda nace ai,min ,,,
Cikin sanyin murya nace mai to insha Allah za,a yi,
Daga karshe kuma nai masu fatan iso wa lafiya, tare da
fatan Allah yaba mara lafiya, lafiya ya ansa da fadin ameen ya gode,, yakashe wayan,,,
Almustapha na mika ma wayan sai yake ce min sheriff yace ya bani wasu kudade dazanyi amfani da su,,,,
Kudin da yabani sai naga suyi mugun yawa don haka,saina, nadauki dai wanda zai i,she ni
na mayar mai da saura,,,
Mamaki yakamashi saidai baice min komai ba ya juya kawai ya wuce, abin shi,
Nikuma nakoma cikin gida ina tunanen maganar da muka yi da sheriff din,
Ashe mahaifiyar Sheriff ce bata da lafiya ciwon sugar ya kamata,
Shine ta rikice masu, acikin dare har hankalin malam mijin ta yatashi,
Don yadda ciwon yabugeta sun dauka ko bazatayi ba
Shine malam din yakira sheriff din a rikice yana fada mai abinda yasamay ta,
Asibitin FMC Maiduguri aka fara ajeta kafin sheriff ya iso, daga saudiya,,
Mahaifin shi Alhj lawal zannah shi yadauki dawai niyar duk wani abinda akai mata a asibitin
Ya basu kulawa sosai yadda duk yakamata, yanu cewa ita din kaunar shi ce ta ji,
Isowar sheriff din mu keda wuya yaga halin da mahafiyar nashi keci yasa duk hankalin shi yatashi sosai
yasa akai mata biza ita da malam mijinta
Da,kuma yan kan,nen shi mutum, biyu zuwa saudiya
don mahaifiyar nashi,tazo saudiya adiba lafiyar jikinta da kyau aji komay ye matsalar da ke damunta,
Shine ya dinga bugo ma nafisa waya don ya fada mata abinda yake so ai masu kafin ya su iso, da bakin nashi,
Ita kuma bata gida yanata bugowa anace mai tafita,
Ranshi ya baci sosai yana mamakin ina taje haka cikin garin da bata san kowa ba,
Duk taka tsantsan dayakeyi a,kanta baihana ta yin abin da ranta ke so ba,
Don a bincikin da yasa bashir ya yi a kanta ya,fada maicewa tana shan drugs, tun a makarantar da tayi a kasar waje,,,
Baida yadda zaiyi ne saboda umurnin mahaifin shi yake bi, shiyasa ya aureta har ya zauna da ita dole,
Ashe shine dalilin da yasa bai yarda ta fita ita kadai sai tare da ni,
Wanan maganar Sirun sune shiyasa baifito fili yace ga abinda yake so indinga kula mashi da ita ba,
Sai dai yasan cewa ga wayo da irin hankalina zan iya

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment