Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusan shida inda suka mara mata baya,
Cikin shigar su ta yan gayu suka shigo wurin kowa idon su na akan su saboda irin yanayin shigar su,
Duk da sundan rufa yan gyale a kan su kamar ba matan aure ba,
Don daga kasan cewa ba,a tunanen mutuwa zata iya riskan mutun anytime, an shagala da duniy kawai, ba a tunanen gamuwa da ubangiji
Kallo guda nai mata daga inda nake zaune naga tadan kara kiba sama da sanin da nai mata,
Amma banda shi tanan bakar ta bata shafa man da matan zamani ke shafawa ba dan suyi haske,
Daga inda akai masu mazauni muka hada ido da ita, duk da nike yarinya na hago ki shina karara a cikin idon ta,
Nasan ko ba komai bane sai ganin yadda na sake lokaci guda na canza daga fafima yar takari zuwa Fadimar Sheriff Ahmad Lawal Zannah,,,
Taro ya,watse cikin jin dadi da annatshuwa inda aka raba wasu manyan traveling bags dake dauke da showel da su sabulai da kuma kayan snacks a ciki da su sweet kalakala,
Yan dogon daji da sukazo zasu koma gida matan su kowace turmin zani da dubu biyar mazan su kuma shadda da dubu biyar, ga kuma kayan buki kalakala,
Hakanal yan maiduguri su ma kyauta iri guda akai masu da yan dogon daji,
Naso hafsi ta tsaya saidai kuma saboda tafiyan mu maiduguri yasa na bari tabi sauran yan uwar mu zuwa gida,
Su hjy umma wace take zama min kamar uwa yanzu takara min nasiga sosai akan zaman duniya inda ta lurar dani yadda sherin mutanen zamani yaje da kuma yadda zan zauna da mijina a cewar duk kishiyoyina ,suna da matsala atare da su,
Da zu tafi kamar kada su tafi su barni nake ji don duk kusan lokaci guda suka wuce bayan alherin da Sheriff yai masu ta bajinta tare da yi masu godiya,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
[12/4, 11:20 PM] ‪+234 703 300 7734‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣2⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,,,



Tun cikin dare bayan tafiyan bakin mu, muka soma shirye, shiryen tafiya, zuwa maiduguri,
Natambayi sheriff ko a nan zamubar su gwago da su mariya yace mi aida su zamu tafi,
Shiru nayi saidai a zuciya sai ina gani kamar mun yi yawa ga tafiyan ace duk yan uwana har kusan mu biyar
Zamu je masu bakun ta a,gaida a gaskiya ina gudun abin magana saboda ban san irin rayuwar mutanen can ba,
Duk wani abinda ya kamata mudauka dan bukatar mu mun dauka , dan ba musan abinda zamu tarar ba acan,
Tunda sheriff yafita da yamma baidawo gidan mu ba saidai a waya ne mukai magana da shi, inda yake sheda min cewa tafiyan safe zamu yi,
Sai da safe ya shigo gidan mu a cikin shirin shi tsab
Duk da mun shirya karyawa kawai yarage muna muyi a lokacin,
Ina zaune bakin gadona ina baiwa ummibanan nono ya shigo dakin mariya dake tsaye gabana tanawa Abbazannah wasa tana jiran dayar tagama shan nono ta miko min shi tai niyar fita dakin,
Da hannu sheriff yadakatar da ita ta tsaya abin ta ba zama zai yi ba,
Inda nake yazo ya kai min dan sunbata a gaban goshi cikin larabci yake tambayar lafiyar mu na ce mai kowa kalau masha Allah,
Yace min duk wani gifts da yakamata arabawa mutane sa acan yasa Bashir ya tanadar min zan samay su acan ko,
Nai mashi godiya tare da yimai addu,oi da fatan alheri akoyaushe,
Sai kuma ya ce min duk da bai san ko kwana nawa zanyi can ba yana son dan Allah duk abinda muka gani dani da su gwago muyi hakuri da shi,
Nace mai duk abinda za ai muna insha Allah bazamu dauke shi komai ba tunda bashi yai muna ba,
Ankawo min abinci har dakina muka karya tare da shi don irin sakkon dayayi zuwa gidan mu nasan cewa baici abinci ba,
Yana cin abincin yana kara yi min bayanin cewa har gurin ummi yake sonmuje mudan kwana biyu
Na nuna mai murna na afili wanda hakan yasa shi jindadi sosai aranshi,
Duk mun fito cikin shirin mu tare dasu gwago inda ,
Suna rugumay da yara niko Aisha ce kawai na rike da hannu na zuwa bakin get,
Dan ni azato na da mota zamu tafi ashe jirgine zamu zuwa can, saidai wasu kayan mu za,a biyo mu dasu,
Cikin kwaliya muke na gani na fada saboda nasan cewa Sheriff mutum ne mai son yaga matar sa acikin shiga na kwarai na alfarma da mutunci,
Shima hakan ne dan wasu yadi yasa na maza na India Pakistan, yadin yana da kyau so sai kuma dinki kusan irin nasu ne,
A hanyar muta airport ne muna zaune a bayan motan nida sheriff nake tanbayar shi,
Amma dai shi ba dadewa zaiyi a can bako zai koma gurin aikin shi,
Saida yadan murmusa min kadan yace har kun gaji da gani na ne ko kuwa,
Cikin sauri na ce, mai haba wa ,ai bana fatan ranan da zangaji dashi a duniyar nan,
Yace to kina tsoron kar in bar ku can ne ku kadai,
Wani murmushi na danyi,
Sai nadan matsa kusa dashi kadan na kwantar da kaina saman kafadar shi,
Nai magana acikin tausa murya kamar mai rada na ce ba tsoron nake ji ba sheriff,
Indai son mijina a kusa dani ne kawai, bana son mu ni,santa da junar mu ko kadan,
Shiru yayi batare da ya ce min komai ba,
Saidai ni nasan cewa shirun shi na nufin wani ansa ce hakan nan , dole in sa ido in fahinci ansar maganata nan gaba,
Muna isa airport muka samu time din tashi har ya kusa batare da bata lokaci,ba muka shige sai tafiya,
Tayi ce mai dan nisa sosai mukayi wanan karon din yafi wanda mukayi daga sokoto zuwa Abuja nisa,
Wani tunane yazo min acikin jirgin ina tuna yadda zan je in bakunci wasau mutanen da ban saba rayuwa da suba acan baya,
Kuma gashi da alama ba sajin hausa akasarin su duk yare suke yi,
Ban san ko ya mahaifin sheriff zai tareni ba kasancewa ta yar talkawa, badiyan masu arziki ba
A yadda naji su Amal na hiran arzikin shi da kuma irin rashin ko in kula da yakewa yan uwan shi,
Uwa uba kuma irin yadda zan riski hajiya mama,
Tuna ne sosai nayi har zuciya ta takoma min tunanen irin matan sheriff da zan yi zaman kishi da su arayuwa na,
Sai dai kuma wata zuciya na ce min ina ruwa na da su suda suke gidajen su mai zai hada ni da su ,
Alokacin naji dadin tunanen da nakeyi har nakai kaina a makarin kujerar da nake zaune dan inji dafin tunane,
Nace nadai ji manya na fadin Namiji ba dan goyo bane, watau ke nan koni in yi hankali da Sheriff kenan arayuwana, dan zai iya zuwa wata rana ya juya min baya,
Na ce hmmm ni ko asani na ai namiji shi mafi darajan mutum wanda ke haska mace komai mukamin ta ko arzikinta ko mulkinta, ko kuma kyau,
Dazaran baki da aure duk wanan daular yatashi a free dan baki taba daraja a idon duniya,
Sai kawai a zuciyana nasa aikoda anan gaba sheriff zai juya min baya zan ita hakkuri da shi badon wai abin hannu shi ba ko kuma kwadan zama dashi,
A,a saidai kawai dan bazan taba mantawa da irin mutuncin da yai min ba arayuwa ta san nan kuma ga zuria, a tsakanin mu,
Nakara dan lunshe ido na nakara cewa acikin zuciya na,
To ai shi sheriff ma dole mace taso shi saboda irin hakkurin da Allah ya bashi ga kuma kyautatawa a tsakanin shi da mace,
A haka naita nazarin rayuwa ta da na sheriff a cikin zuciya na ni kadai keyi kuma ni kadai keba kaina ansa,
Jin sheriff dake zaune a kusa dani ,nayi yana dan murza min hannuwa na yace min batare da ya kalle ni ,ba yace, may kike tunawa haka kike ajiyar zuciya,,,

Mun isa lafiya Inda motocin gidan su Sheriff sukazo taron mu kusan guda hudu,
Tun a airport naga irin taron arzikin da mutane ke muna sai sambarka sukeyi wa sheriff,
Duk da rana yadan yi a lokacin da muka isa don haka kai tsaye vidan mahaifin shi muka wuce direct,
Wani bangare guda daga cikin gidan aka bude muna nida su gwago,
Duk wurin idan kagan shi zaka dauka cewa ba isa,shen fili ashe idan ka shi gida sukutun a guri don da kunoni ne kusan guda shida acikin plat din,
Batare da mun huta ba ko tsayawa cin abinci nasa muka tashi zuwa cikin gida gaida su Abba,
Alokacin yamma har yafara yi , don haka dakin hjy mama muka fara shiga,
Mun samay ta zaune falonta tare da wasu mata su uku, sai masu aikinta,
Durkusawa nayi kasa nakai mata gaisuwa, tana saye da wani farin,glass a idon ta,
Ina kokarin gaisheta ito idonta na ya na kan zanin dake jikina , tana kokarin tantance ko super ne daura ko kuma yar kwaikoyo, ce nadaura,
Gwagona kokarin mika mata yaron dake hannuta still idon ta na kaina,
Ganin haka yasa na dan gyara da kyau dan taga zanin dakuma zobban gold da na jera a hannu na,
Saida ta ware ido da kyau lokacin da taga wa yan nan zobban na hannu na,
Da kyat ta iya ce min ashe kuna tafe,
Ai mu bamu da labarin cewa zaku zo nan dauka muke yi acan za kuyi ta sha,anin ku kawai,
Na yar murmushin gefen kumatu nace haba dai ai muzo neman albarkan ku,
Shiru tayi kamar bata jini ba ,,,
Nai,dan murmushi nace mun samay ku lafiya da kyat ta ansa min tace lafiya kalau banda shi ba wanda yakara magana daga cikin mu,,,
Shiru ne ya,biyu dakin ba wanda yace komai kowa na maganar zuc Daidai lokacin sheriff ya shigo dakin shi ma,
Fuskan ta ba yabo ba fallasa aciki, yadda nayi haka shima din yayi a kasa ya zauna ya gaida hjy cikin girmamawa,
Tana daga kishingide take ansa mai da kyat tace ashe kana Nigeria har yanzu,?
Tambayar taba shi mamaki sosai ,sai kace wace batasan ai mai haihuwa ba take mai wanan tambayar,
Basar wa yayi yace mata tare da nuna mata yaran da hannu yace ga wa,yanda suka hanani komawa nan,
Ga su ankawo maki su kigan su,
Sai cewa tayi a,a kun dai kawo wa hjy tsohuwa ita da ke ta damuwar mutane da zan cen sai kace bata taba ganin anhaihu ba agidan
Daidai yana mikewa yake ce mata mama kin san wanan daban ne dana ko yau,she shiyasa ta damay ku,
Kafin ta bada ansa yakai waje kofa ko,ganin yafita yasa ni mikewa nacewa wasu gwago suzo muje ,,
Bayan shi mukabi zuwa shiyan da hjy tsohuwa take ciki tana jin ya tare da yan jikokinta biyu daga can kauyen,Auno,
Hjy tsohuwa tana zaune da chasbaha a hannun ta ja tana dan gyangyadi daga zaune,
Yin sallamar mu yasa tamike tana fadin
Alhaji karami koba shi bane,
Yace nine hjy Amaduna zo nan zo in ganka,
Ina kashige nake ta ma aike kazo katafi dani baka zo ba,
Ina fatan kazone mutafi ko, ina yaran naka, ?
Duk a cikin kanuri take mai magana yace mata hjy ai tare da su muke,
Gasu nan nakawo maki su ki gansu ai ba sai kin zo ba hjy,
Sai kokarin mikewa takeyi, daidai lokacin muka shigo katon falon da take zaune a ciki.
Hjy tanan kamar yadda nasan ta sai dai ta dan kara tsufane kawai
Dakin yana ta kamshin turaren wuta don har yafi dakin hjy mama kamshin dadi,
Tana kokarin gyara lafayan ta tana kuma kokarin miko hannu dan karban yan jarirain da ake mika mata alokacin,
Dole tabar gyaran lafayan takarbi yan yaran tana ta washe baki cikin farin ciki da jin dadi,
Sai kuma ta,hau yin hamdala ta aa dauko addua dake bakinta tana tofa wa yaran,
Saina kula da cewa ko su gwago sunfi jin dafi dakuma sake jiki a gurin hjy tsohuwa, fiye da dakin hjy mama da muka farq zuwa,
Nan da nan yan matan nan suka kawo muna Birabisko, da kunun gyada,
Hjy na fadin (uno biri yo biski )
Mudai murmushi kawai mukayi, nan muka baje a shiyan hjy tsohuwa abin, mu, har bayan sallah magrib mu,na nan sai lokacin
Sai musalin karfe tara na dare ,sheriff yai min waya yana sanar dani cewa mushirya akawo gurin Abba, mu gaida da shi,,
Yana zaune saman wani ddaduma mai laushi da kuma sulbi sai ya'yan itace dake a gaban shi da alamar su yake ci a lokacin,
Cikin murna da farinciki Abba ya tare mu yana ta fara,a da zuwan mu, aka mika mai yaran dadauka daya bayan daya yana sa masu albarka yana mai nuna faricikin shi,
Yajiyo yana tambayana mutanen garin da yan uwana suna lafiya ko, acikin ladabi dakuma kunya na bashi ansa da suna lafiya kalau,
A,lokacin hjy tsohuwa tashigo falon tana wani busan iska tawuce zuwa inner room fuuu, can kuma takara fitowa kamar bata gan muba,
Nima ban kara gaida ita ba duk wulgawan da takeyi agaban mu,
Sai alokacin ta dawo tadan zauna tana ce min, duk wa yan nan tare kukazo da sune ? ko kuwa, ?
Duk da tambayar nata yai min zafi amma sai nadake kawai, araina nace mata eh,
Wanan gwago tace wanan kuma matar babana ne,
Abbane ya karba da fadin masha Allah haka yati kyau mungode kwarai da kulawar ku,
Allah ya raya muna yaran yasa masu albarka, kowa dake wajen akace amin, bandani da na karba a cikin zuciyana, ba,a fili ba,
Ba muwani dade ba muka taso zuwa falon hjy tsohuwa don muyi mata saida safe, saboda gaskiya a gajiye muke,
Wai ashe duk zaman da nayi falon hjy bata gane ni ba saida Sheriff yai mata bayanin, ko wace ce ni,,
Ina shigowa naji tace min U,ro, Uro,
Tana min alama da hannu inzo gurinta tanace min ashe abokiyar zuwa dawafi na ne ban gane ,
Kece haka kika girma masha Allah , sai kuma tasa kuka kamar yadda tsofafi keyi indan sunji dadin abu,
Nace mata ta daina kuka dan Allah ai yanzu mun zama daya ba inda zani, kuma muna tate muyi ta zuwa dawafin mu atare,,,
Koda muka koma shiyan da aka ba mu mun samu wayan nan yan matan sun gyara muna shiyan da aka sauke mu sai kamshi yake yi,
Aiko su gwago sukace indai harda sheriff a shiyan zai sauka sam su baza su zauna ba saidai su koma gurin hjya,
Sai ko ga wayan shi yana sheda muna cewa shi ya wuce gurin da zai kwana gidan Baban, Bashir, acan wqni unguwar Bulama,
Jin haka muka sake jikin mu mu kadai saidai duk daki guda muka kwana saboda sam gwago tace ita bata yarda da hjy mama ba,
Hakana muka kwana acikin daki guda, gabadayan mu,
Washegari gashi dai munyi wanka mun shirya tsab, amma har zuwa goma da rabi na safe ba akawo muna abin karin kumallo ba,
Gashi cikin jegone mun tun ina daure wa gwago nata masifar fada tana cewa gaskiya wanan abi da niyya akai haka,
Mai aikin hjy mamace tashigo da sallamar ta dauke wani dan kula abinci wanda, ko mariya da Aisha ba zai kosar ba ,
Kwaine soyyaye da dankalin tura har yayi sanyi, wai hjy ce tace akawo muna ,
Har takai kofa sai gwago tace mata, tazo ta dauka tamayar tace ai mun koshi,
Naso in magana tai cikina da fada so sai tace da wanan cikin jegon naki za,a kawo muna wanan dan abincin haka,
Ganin munkai har rana yasa kawai naiwa sheriff text nace muna jiran abin breakfast,
Cikin mamaki yakirana yana tambayana nan na sheda mai duk yadda akayi kuma na fada mai gwago ta ce amayar mata dashi,
Ba afi minti ashirin ba sai ga take away na wani restaurant ankawo muna gudan mai yawa mukaci har muka koshi,
Sheriff yazo yabawa su gwago hakkuri, tace ita abinda yasa tace amayar saboda idan mun karba ko gobe haka za,a kawo muna kuma ba mai sani ,,
Naji yace masu saboda zuwan mu komai yasa ankawo don bukatar mu
Gwago tace barta kawai munsan irin wanan
Muda muka fito hausa muza,agwadawa barkado,
Kuma muna nan bamu wucewa sai mungama abinda yakawo mu,
Sheriff yaji nauyi sosai amma dayaga su gwago madu yi ne sai yaji dadin hakan don yasan zasu iya maganin mama,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,


Kafin karfe biyu duk wani simple stock an tanadar muna shi a side din da muke zaune a cikin gidan Abba,
Sau biyu ina zuwa side din hjy mama dan mu,gaida ita amma gurin yana a kulle,
Saida mariya tagama gyara muna ko ina san nan muka kwasa muka koma side din da hjy tsohuwa take ciki,
Mariya da yan manta sukayi muna abincin da zamuci ,
Sai bayan sun kam,mala komai ne suka zubowa kowa a inda yakamay,
Falon hjy tsobuwa muk banje muka fara cin abin cin mu hankali kwance,
Hakan bakaramin dadi yai min ba dan dama duk a tsorace nake da hjy mama,
Dan kada tabar mu da yun wa, gashi tare da su gwago muje bamu kadai bane, duk da sun san halin irin wasu matan a gurin kishi,
Banyan mun gama cin abinci mu kazauna nan falon hjy tsohuwa zaman hira,
Sai a lokacin Ummibanan ta farka daga barci tana ta tsala ihu,
Ruwa maidan dumi nasa mariya tadan zubo min a cup in bata tasha ,ihun da takeyi yasa gwago ce min kada in koya wa yaran fitina man,
Yaron da baya kuka indan aka kyaleshi yana kuka har zuwa wani lokaci zai koyi kukan banza daga wanan lokacin,
Har uwa tarasa gane kan yaro saboda yawan kukan da yaro zai dinga yi,
Hjy tsohuwa dake gefe guda tana jin abinda gwago ke fada tace min,
Dan Allah Fatima ki kula da wa yan nan yaran kinji, kinga uban su abin tausayi ni a duniya
Saboda shi shikadai ya tashi batare da sanin dadin yan uwa ba ,
Tanuna kofar side din hjy mama tace kin gata can bata da halin kirki ko daya,
Tunda kurciyar ta, har yanzu da girma ya kamata mugun haline tatare a zuciyar ta
Hassada da bakin ciki shike cin rayuwar ta akan wanan yaro,
Gashi diyan nata da ta nuwa wa so kamar ta mutu duk ba nagari daga cikin su,
Tun ban san ko wace ce Alhaji karami ya aura ba nake farin ciki da jin cewa wanan karon yar mutunci ce ya aura kuma yar yarinya kamila,
Nai farin ciki kwarai dajin hakan daga bakin Bashir
Saboda duk matan shi na farko sai ina ganin kamar daga, sherin hjy ce yake samun su don babu wace ta dace dashi daga cikin su,
Kawai sai labari naji cewa wai ai matar Amadu na ta haihu, bakaramin farin ciki nayi ba dajin wanan labarin gaskiya,
Tana nuna min yaran da hannu tace wa yan nan yaran da Allah yabaku kawai sun ishe ku a bin tin kaho a duniya,
Kwana nawa ne ,in ubangiji Allah yaraya, maku su za su girma
Kin ga daga wanan lokacin shi kan shi duk wani kwakwan da yakewa yan uwan shi don su shirya dashi zai ragu yadawo ga nashi iyalin,
Zuri, ar Amina ba zuri ar arzikiba ce wlh, tun farko ban so auren yaron nan da ita ba fin karfina ne kawai akayi da kuma rabon iyali atsakanin su,
Don haka ki zama mai hakkuri da mijin ki, kibawa diyan ku tarbiya nagari tayadda za su zamo abin alfahari a cikin duniya baki daya,
Shi kanshi maigidan naki na bukatar kulawar ki sosai don zan iya ce maki duk halaiyar shi guda da mahaifin shi,
Amma kinga shi mahaifin nashi rashin samun mace ra gari wace zata dinga karamai karfin gwiwa wajen kara habbaka rayuwan sa , bai sa,a da hakan ba,
Gaba daya ita gurinta shine tamallake komai nasa ita kadai sai iyalin ta,
Shine yasa kike ganin tana mugun bakin ciki da mijin ki,
Don ita aganin ta ba,aiwa diyanta , yan uba,
Wanan son kan nata yasa har ta cuci kanta da kanta diyanta suka lalace,
Ta girgiza kanta tace Allah ya shirya wa yan nan yaran,
Kamar yaron nan mai mutunci da sanin ciwon kanshi ace diyan shi sun shigo wanan garin da kitso akan su,
Tace fafir Amina ta hana akai Amadu karatu kasan turawa saboda hassada wai zai je inda diyanta suka tafi,
Sai gashi ashe alheri ke kiran shi kasa mai tsarki, don zuwan nashu yanzu yazama duk wani dan uwan mu alheri,
Don kin ga kusan duk yan uwa yai masu sanadin samun wuri madogara,
Wanan hassadan na Amina yanzu haka sai kara ruruwa yake yi akan shi,
Ganin cewa duk diyan ta ba wanda ya kama kafan sa,
Kwanaki har da sherri ta hada wai aje abincike shi yana saida haranttatun kaya akasar saudiya,
Salati su gwago suka sa dan jin abinda hjy tace tace kwarai da gaske sai daga baya ne asirinta ya tonu gurin dan karamin dan ta ,
Yai mata fallasa so sai agaban mutane saboda taki yarda ya auri baturiya ran shi

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment