Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya baci yai mata tas,
Tai yar murmushin tsofafi tace ki kula da kyau da duk wani abinda Amina zatai maku keda yaran ki don sherinta yawa gare shi,
Nima kin ganni nan to zamana duk yakai mata ko ina wurin nan,
Ni kaina zaman dole ne nakeyi anan dan can kauyen mu yafi mun nan sosai,
Tace dazun da mijin ki yashigo gaida ni saida nai mai korafi akan yabarni in koma dakina koda ma mutuwa zanyi in mutu a dakina,
Jin dogon jawabin hjy tsohuwa akan mama yasa duk jikina yakara mutuwa sai tausayin sheriff ya mamaye min zucita a lokaci guda,
Nace Allah sarki ashe shiyasa yake ta damuwa akan su mama da yaranta watau shi ke son su , su basu kaunar shu sam,
Inko haka dole in kara jawo mijina ajiki dan in kawar mai da damuwar da yake ciki,
Washe gari gidan anty Falmata mukaje yini, gabadayan mu harda hjy tsohuwa tun a mota tasa sheriff agaba akan sai ya maida ita gida kafin ya wuce,
Anty falmata taimin wani irin hadaden miya nadabab tace min wai shi sukewa masu jego kafin suyi arba,in,
Kazace aka dafa taci kayan hadi da kayan kamshi, sai sauran sake saki da aka dafa su tare, da ruwan rubutu,
Tace min ko wanan nasamu naci kawai kafin in yi arba,in yawadatar amma in son samu ne sau uku yakamata inci kafin inyi arba in,
Jin haka yasa na dan faki idon su gwago nace mata tayi kokarin dafa min sauran kafin mu tashi,
Tai yar dariya tace ai zan dafa maki fadima , yadda kika nuna kina kauna na kuma kina kaunar dan uwan na ai dole ni ma in soki fiye da tsanmanin ki,
Sha kurumin ki ai kafin kubar nan zan sa aimaki komai daya kamata,aiwa mace mai haihuwar farko kamar yadda muke yi anan kasar,
Naimata godiya sosai danjin wanan harar cin nata,
Ashe gwago taji tace ke kisha kurumin ki mu kan ai indai kayan hadine gida kikazo nida kaina zan hada maki walle sai kin bide ni kinmin godiya,
Duk muka sa dariya a cikin lokaci guda, anty falmata tace ai ki kwantar da hankaliki fadima duk abinda zan yi wa kaunata ta ciki guda inshaAllah zan maki ke ma,
Saboda naga kishiyoyin ki duk yan bariki ne,
Ni tausayi Ahmad ma nake ji har ina mamakin ko ina ya gangamo da ire,iren su haka,
Dan kin ga shi mutum ne salihi wanda bai magana,
Karar kiran wayana ne ya katse muna hiran, nobar Sheriff ne nagani a wayar
Nakai wayar a kun,ne na, daidai lokacin da yake sallama a cikin natsuwa da tausa murya,
Nima dai tausa muryan nayi na ansa mai yace min yana fatan ba matsala dai ko in harda matsala yazo ya kwashe mu zuwa gida,
Cikin sauri nace mai ba komai gamunan muna ta hira har su gwago sai nani yai yar ajiyar zuciya,
Alamar yaji dadin jin duk mun sake jikin mu da yan uwan shi,
Sai kuma yace min zai zo zuwa hudu yatafi damu mu gaida mahaifin Bashir ,
Dan yana ganin gobe zamu wuce gurin su ummi dan zai koma Saudiya very soon insha Allah,
Gabana yai matukar faduwa dajin cewa zamu koma saudiya tun yanzu,
Don dai gaskiya ni nafi son in zauna nan Nigeria abina,
Duk da bai anbaci cewa dani zai tafi ba nasan cewa mawuyacin abune yabar ni nan,
Shirun da yaji nayi yasa shi cewa hello, na ansa da naam,
Ya, Ce ina fatan kin fahince ni ai ko nace mai eh kawai, yace min ok take care,
Duk hankalin su yana agurina dan ganin cikin dan lokaci kadan na canza fuskana,
Anty falmata ce may tambayar komay ke faruwa,
Ban boye mataba na fada mata cewa wai gobe zamu tafi,
Kuma soon zamu koma saudiya,gaba daya, kuma ni gaskiya bana son komawa can wallahi,
Tace cikin sauri kada ki fara kice bazaki koma ba, fadima , kituna cewa bake kadai bace fa matar shi,
Idan har baki je ba sai wata ta tafi, nadan turo baki nace su tafi mana,
Gwago dake jin mu tun fara zancen tace ke arrr, da wanga hali naki,
Wasu nason atai da su ke ko wai son zama kikai, inkin zauna zaman mi zakiyi, ke dai,anan,
Shiru nayi ina jin maganar gwago da anty falmata
Sai jikina yai sanyi da nasihar nasu don ba yadda na iya dole in bi mijina in koma saudiya kenan,
Wasu hawaye suka dan silalo min natuna cewa ko hjy maisharwali da takai ni saudiya ta dawo Nigeria abinta, da duk wasu wa yanda mukaje tare, alokacin ,
Ni kadai kawai Allah yai zamana acan ke nan, cikin dabara nagoge hawayen ahankali,
Ashe anty falmata ta kuladani, a cikin dabara tajani har zuwa cikin bedroom din ta,
Tace min fadima may kikewa kuka akan komawar ki saudiya ne ko,
Ido ta kura min taa jiran ansa na ganin da tayi banda alamar bata ansa yasa tacigaba da maganar ta,
Tace fadima ki godewa Allah da yabaki Ahmad a matsayin miji, aure, yau kuma gsshi har da zuria a tsakanin ku,
Sam kada ki dauke ni a amatsayi yar uwar mijin ki,
Kisan wasu dangin miji suna zama ma mutum abokan gaba da zaran sunga dan uwan su na son ka, sosai,
Ni tun banganki ba naji kin min kawai don gurin Bashir nake jin labarin ki wanda shima ina ganin gurin Ahmad yake dan samun labarin ki,
Nai maza nadan dago kai ina mamakin maganar ta ,
Tadaga min kai tace kwarai da gaske hakane ko ki na ganin baki isa yai maganar ki a gyefe bane,
Ta ce har in ki na shakku ki daina don ni gaunau ce ba jiyau ba don a gaba yake fadawa Abba da hjy tsohuwa irin halaiyar ki, da abinda yasa har ya aure ki,
Dan haka ki shirya kawai duk lokacin da ya bukaci ku koma ki bishi kawai batare da nuna bacin rain ki ba,
Shin idan kin tsaya nan may zaki tsinta mijin anan din idan har kin tsaya,
Daga kai nayi ina mamakin ta, kodai don bata san ko shekara nawa nayi can batare da iyayyena ba,
Sai naji ansar kuma a bakinta, tana cewa kina yar karama ma ,kin inyi zama batare da iyayyenki ba balle yanzu da kike da aure a kanki,
Kenan tasan koni waye tun farko wasu hawaye naji sun sulalo min a fuska na,
Dafa ni tayi a kafada tace ki zama ma jajircewa akoda yaushe don ki lashe duk wani lanbar yabo daga mijinki ,
Ki zama mai mallake mijin ki ,koya mai yin adalci acikin ku, duk da nasan yana kwatantawa, saboda shi haka ya tashi mutum mai tsoron Allah,
Kiyi kokari ki tarbiyartan da ya'yan ki cikin hikima da dabara ki hane su ga duk wani abinda zai kaisu ga koyon lalacewa,
Hakan bazai kai ga samun nasaran ki ba sai kina kusa da mijin ki uban diyan ki,
Dan haka kada ki kara bata ranki ga wanan tafiyan ki je ki zama mai yi nayi bari na bari kamar yadda aka san ki,
Daga haka bata kara ce min komai ba sai shirun da yabiyo dakin, ido kawai ta zuba min,
Sai can nadan yi ajiyar zuciya, na nisa, nadago kai na kalle ta na ce cikin siririyar murya na gode kwarai anty kuma zan yi kokari in koyi da duk abin da kikace,
Kafin mu fito falo nai ma anty falmata godiya sosai acikin ziciya na kuma ina mai gode ma Allah da ya hada ni da ita ,
Hudu daidai sheriff ya iso inda suka kwashe mu zuwa gidan su Bashir
An muna taro na arziki so sai an kuma nuna muna so da kauna na gaskiya,
Ba mu wani dade ba saboda dare yayi mukayi sallama da su muka dawo gidan Abba,
Washe gari har hjy tsohuwa muka dunguma zuwa garin su can wani local government ne,
Ummu ta tare mu cikin jin dadi dakuma murnan ganin yan jikokin ta duk tana kokarin boye wa,
Nikan sai ince gida nazo don gidan wan mahaifinane nazo,
Aiko zuwa dare nan da nan yan uwan su Shehi dake zaune agari aka diga shigowa gani na ni da mariya,
Duk wanda ya gan ni sai ace wai lalai, mun mafi diyan shi kama da shi,
Hjy tsohuwa tasa fitina akan dole gidan ta da zamu sauka dan haka kwana guda kawai nayi a gidan Shehi na koma gidan hjy,
Duk da Sheriff yafada madu mun fasa yin kwanakin da mukayi niyar yi anan da farko ,saboda wasu dalilai da suka taso daga gurin aikin su,
Gyaran jiki sosai akai min dakuma kitso irin nasu na yan maiduguri,
Gajikin jego dake samun kyakyawan kula ga kuma adon da aka yarfa min a,jikina
Haba ai sai kawai na ko.a kamar wata bakar balaraba can
Tunda nazo bamu kebe da Sheriff ba sai yau muka hade a dakin hjy tsohuwa,
Ina zaune ina bawa Abbazannah nono yashigo tundaga kofa dakin idon shi na akai na duk daga mutane adakin yau sheriff baiji kunyar kowa ba,
Kallo guda nai mai naga irin kallon da yake min sai da gaba na yafadi sai kuma yabani tausayi,
Don a gaskiya yana da hakkuri sosai namiji lafiyye kamar sheriff mai mata uku yazauna kwana da kwanaki hakanan,
Cikin murya kamar ta mai kasala yake min magana yace fadima maganar su gwago ne da man nazo dashi,
Saboda gobe da mun koma ranar jumma,a da asuba zamubar kasar nan,
Duk da naso in daure amma sai nakasa nadogo da sauri na kalle shi,
Murmushi yai min kawai yaci gaba da zancen shi,
Don haka ko can tare da su zamu tafi tunda maigari da kawu sunce sai kunyi arba,in kamar yadda al,adar hausawa take,
Don hakane ma tun muna maiduguri na bugawa maigari na sheda mai cewa yayi hakkuri dasu zamu tafi, gabadaya
Wani irin murna naji ya sauka min azuciya na, wanda banko iya lissafawa,
Yace saboda agaskiya naji dadin zuwan su tare da mu sosai saboda irin kulawar da suke ba ku akai da kai,
Azuciya na ko cewa nayi aini nafika jin dadin hakan don ni zama dasu sai jinaje kamar da innata nake zaune,
Saboda gwago ta canza sosai saikace ba itace mai hattarata ba da ake zaton cikin shege da shi,
Sam banga laifin su don sona yasa sukai min haka yanzu ko da suka gane gaskiya sun fi kowa farin ciki,
Muryan shi naji yana cewa ina fatan zaki masu gamsashen bayani ko,
Godiya nafara mai sai kawai naga yadaga min hannu, alamar bai so
Ina jin lokacin da Sheriff ke shedawa Ummi zan cen airen Amal yace bazai dade zai dawo dan ayi bukin takoma can
Naji dadin jin haka don ko ba komai zan samu yar uwata a kusa dani,
Don haka nafara mata sherin cewa duk tafiyan mu guda nida ita tunda zama kasar mu yagagareni,
Munyi sallama da yan uwa cikin wani yanayi kamar kada mutafi dan dan sabon da mukayi da jama,a,
Gwago da mama matar mai gari jin labarin tafitan su sukayi kamar almara,
Don basu taba zaton haka ba,
Saiga shi cikin ikon Allah tafiyar yazo masu a cikin sauki,
Mariya ko ina ga tafi kowa murna dan ina fada mata tai wani ihu ta kankamay ni saboda farin ciki,
Da kanta taje yiwa sheriff godiya,,
Kamar yadda yace hakan ne yafaru don da Asuba muka bar Abuja zuwa saudiya,
Inda muka sauka ta jidda don haka Makkah direct muka nufa,,,,,,



🐎ZEEE MAKAWA🐎


✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,


Allah yakawo mu gida lafiya cikin dare muma shigarin makkah,
Mun samu maman Umar a gida tai muna taro na musan man,
Sai murna take yi daganin mun dawo tare da yar ta lafiya,
Ba karamin chanji nagani ba a gidan amma dayake nasan halin sheriff, da son abubuwan zamani dan shi bai jin zafin sayen abin rayuwa a gidan shi,
Sai dai may azuciya wani irin kallo nake wa gidan sai kace yau na fara zuwa ciki,
Ina tuna cewa a wanan gidan ne fa nasamu cikin da zankira da rabo,
Murmushi kawai nayi azuciya dan nasan ba,a wasa da ikon Allah,
Dakina na aini hi na shiga da niyar zama kasan cewa nasan cewa sama na Aziza ne da Sheriff,
Ina tsaye a tsakiyar dakin ina kallon yadda maman Umar ta gyara min shi, tas,
Sai naji an banko kofar dakin da karfi, cikin firgita nadan waiga dan gani kowa ye haka,
Sheriff ne nagani a tsaye yana min wani irin kallon mamaki ,
A hankali ya karaso har inda na ke, tsaye,,cikin fuskan mamaki yake ce min, sai bangaki adaki ba shiyasa daman nasa rai cewa kina nan,
To may kuma zaki anan din, don naga kayan ki nan,
Saida na kai zaune bakin gadona ina kokarin gyara, wani dan kit din yan kunen da na cire a kune na,
Nace cikin sanyi murya Sheriff ina zan kai kayan nawa to,
Ina ce nan ne dama dakina a gidan, ko,
Yar murmushi yace a da ke nan ko Fatima, yanzu kema kin san cewa kin wuce zama a kasa saida sama ko dan kici gaba da kula da Sheriff din ki kamar yadda kika saba ko,
Murmushi nayi nace aiko anan zan dinga kuka da shi fiye da tsamanin shi,
Wani irin laulausar murmushi ya sake , yace umurni na bayar bawai fa shawara nazo bayar wa ba,
Sai kawai yajuya da niyar barin dakin bayan shi na bi da kallo dai dai lokacin shi ma ya juyo gareni,
Yace min mariya ta dawo wanan dakin ita da Aisha su gwagwa su zauna dakin da Amal ta fita, dan nasan cewa baza su yarda araba masu daki ba,
Kai kawai na kada mai ina son ince mai idan Aziza tazo fa yaya zanyi zan kara barin dakin ne kamar yadda tai min a madina,
Kamar yasan tunane na sai yace ko kina ganin a halin yanzu akwai wata matar da zata zo nan tace ki bata daki har ki yarda ki bata kamar yadda kikayi a baya,
Murmushi nayi don tuno da wanan lokacin da yake magana, don ni kadai nasan irin kukan da nasha a wanan lokacin
Ga ciki ajikina ga tashin hankalin Aziza,da tasani agaba saboda hauka,
Murmushi nakara yi na Allah nagode ma da baka sa na biye ma aziza ba, muka dinga hauka alokacin,
Tashi nayi na nufi kofar daki dan in diba su gwago in masu bayanin inda zasu zauna
Suna tare da maman umar anata labarin abin da ya shafi cikin garin makkah da kewayenta,
A cikin larabci nai mata bayani nakuma bukace ta data kai su gwago su yi umurah zuwa gobe idan mun huta,
Tare da mariya muka hau sama don ganin dakin da aka umurceni in koma ciki,
Dakin na nan a gyare kamar kulun sai kamshi ke tashi cikin shi, tankar a kwai mutun adakin,
Wardrobe na fara zuwa na bude dan inga komay ke cikun shi,
Kayane ciki na mata birjit sababi fil a sheke ko ina dasu,
Gurin dressing mirrow na nufa abin mamaki kayan shafa ne irin na mata babune kawai babu agurin,
Mamakin yaushe akai wanan abin ya kamani sosai ,dan dai a,gaskiya abin yabani mamaki so sai,
Itako mariya sai santin dakin takeyi tana cewa kai anty fafima shine har kika iya barin nan kika gudo zuwa gida,
Cikin mamaki na kalleta nace lailai ma mariya da sauran ki,.
Anfada maki cewa akwai inda yakai gida dadina agurin duk wani dan halak,
Da taimakon ta muka sa komai inda yakamata daga cikin dan abin da mukazo da shi,
Su gwago duk mamaki da imani yakashe zukatan su,
Wai ace a wanan kasar nazo tundaga dogon daji yar karama da ni nai rayuwa a cikin ta batare da iyayyena ba,
Matan maigari mama tace gaskiya rashin sanin yanan kasar yasa har wasu yan sheri sukayi saurin zarga wa wanan yariyar sheri,
Gwago tace ni wallahi har kunya nake ji idan an tuna wanan maganar,
Saboda alokacin idona ya rufe sai nake ganin maganar su tumba itace gaskiya kamar yawon bariki ne kawai yariyar tazo yi,
Tabata muna sunan zuri,a don duk wanda zaiyi magana cewa zai yi ai iyalen gidan mu ne,
Amma tun wani rana da tazo gidan mu yini a hiran su da kawun ta nagane cewa tana da aure duk yadda akayi
Saboda duk bayanin ta acikin natsuwa taiwa malam shi,
Mama tace kedai bari agaskiya zato zunubi ne sosai wallahi,
Suna cikin wanan hiran sai ga sheriff yace ai sai su fito za akai su suyi umurah,
Don ba kyau mutum yazo garin makkah har ya kwana batare da yayi umurah ba indai har farkon zuwan mutum ne,
Fitar su gabada a lokaci guda yasa nagane cewa zaman su a tare da ni yana da matukar amfani,
Don ni kadai na dinga lalurar yaran kafin su dawo,
Gaba daya tun fitar su gidan ina sama tare da yaran , duk na rude na rasa yaya zan yi dawainiyar su ni kadai,
Azatona tare da sheriff suka tafi yin dawafin, ashe shi har yatafi yayi ko yadawo,
Dakin yashigo daure yake da bath robe, zaune ya samay ni ina kokarin sawa Abba permpers ga kuma ummi tana ta tsala ihu daga kwance,
Cikin sauri ya dauko yarinyar ya rungumay ta a jikin shi,
Sai kuma ya koma kallon wanda nake sawa permpers din shima ya fara kuka ,
Wata irin ajiyar zuciya yayi don har cikin ran shi na bashi tausayi don yar karama dani ya zanyi rainon yara biyu alokaci guda
Duk da kwazon da yasan ni da shi lokacin ina yarinya so sai,
A hankali yazo inda nake zaune rugumay da yaron a hannu na ya hada mu gaba daya ya rungumay,
Kuka na fashe da shi kawai, batare da ya bani hakkuri ba yana nan rike dani har nadan ba kaina hakkuri,
Yace min Fatima cikin murya mai rauni, baki godewa Allah bake nan ko,
Allah mai kyauta da kari shine yai maki wanan baiwar a lokaci guda,
Kina son ki nuna mai cewa baki gode bane ko kuwa,
Yadan kara mannani ajikin shi yace nasan ki da kwazo sosai na san cewa zaki iya wanan dawainiyar
Amma kuma nasan cewa a yanzu baki saba da wanan harkan ba yana daga cikin hikimar da nayi don zuwa da su gwago har zuwa lokacin da zaki dan saba da lalurar su,
Yakare zancen yana mai ce min kikara daurewa, ki kula da yaranki,
Kiyi kokari cewa duk wani bukatar mu nida yaran mu kin kokarta kin muna shi,
Idan kin muna haka, ki kingama muna kimai don mun zama yan gata agareki,
Jin kalaman shi yasa nadan murmusa, kamar banice mai kuka ba yanzu,
A hankali na ce baku da matsala daga yau insha Allah,
Yace to ki rikeni amana nida yarana pls,
Rugumay shi nayi nace in sha Allah zaka samay ni mai rikon ku amana,
Yadan mike ya lakuto min fuska yace to koke fa ,
A, hankali na ce nagode da wanan fadakarwan,
Yace ni dai zan gode maki nida kika yi wa wanan kyautar
Kin mayar min da gida na kamar yadda kowani magidan ci ke bukatar gidan shi ya koma,
Kin ingata min rayuwana kullun acikin godiyar ubangina, nake da ya zanto na mallake ki amatsayin mata ta uwar diyana abin alfaharina ako yau,she,
Dariya maganar shi tabani daidai lokacin na aje yaron dake a hannu na tafi daniyar in karbi yarinyar da tai barci a hannu mahaifinta,
Ji nayi kawai ya nemo bakina ya manne da nashi, wuri daya,
Can wata duniya muka tsinci kan mu cikinta, irin duniyar nan mai mantas da mutum inda yake,
Saida ya gaji dan kanshi ya sake ni ya juya da sauri yabar dakin namu,
Bayan shi nabi da kallo yana mai bani tausayi don hakkurin shi bai sa ka gane damuwar shi,

Sai dare sosai driver yadawo da su gwago saigasu da tsarabar su him wai sun fara sayen tsarabar da zasu kai gida,
Alokacin har na fara barci saboda na gaji da zaman motar da mukayi, dazun,
Jin motsin su ne yasa ni saukowa dan in masu sannu da zuwa
Ganin su da kayan danayi anata warewa yasani tsayawa turus cikin mamaki,
Sai kuma abin yabani dariya, nace gwago wanan kayan fa sai ce min tayi wai tsaraba ne suka fara sayi,
Matsawa nayi kusa da su nace haba gwago indan kun tashi aini da kaina zaikai ku kusayi duk abinda ranku ke so insha Allah,
Amma ai wanan duk tarkace ne kuka kwaso yan riyal goma goma,
Cikin mamaki gwago takalleni tace haba fadima ,
Ina mukaga wanan acan balle kice muna tarkace ne,
Kedai kawai bari mu fara aje abin mu idan lokacin yayi sai mukara kawai,
Abinci nasa maman Umar ta kara gabatar masu sanin cewa dani sun shawo wahala acan dole suji yunwa yanzu
Murnan kayan ma ya hana gwago cin wani abinci,sosai sai kallona tayi tace min wanan matar zata kai mu inda akesa hakuri gobe,
Ido waje nake kallin maman Umar wace tai masu alkawarin zuwa sa hakorin gwal,
Nace gwago ai,zaku sa amma ku bari akaiku inda ake sa na kwarai a madina,,
Cikin sauri mama da tun da muka fara zancen batai magana ba tace aiko na nan a samuna duk dayane ai,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment