Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka shirya ma zuwan su
Su salim da Amal sai washe baki sukeyi,
Dan yaron Anty falmata na karba ina mai wasa UMMI tace min in aje shi kawai inzo muci abinci,
Kamar in ce bazan ciba sai dai nadaure natafi don kada UMMI taga banyi mata biyaya ba,
Sheriff dake zaune gefe da tasbaha a hannu shi guda,
Yanajiran azuba mai nashi sai dai duk idon shi na ga duk wani motsi nawa a fakaice,,,,
Wani irin shauki so da kaunar fadima kawai ke fisgan shi,
Ji yayi kawai yana son ya kasan ce tare da ita,
Bude abinci da maman Umar tayi don ta fara zubawa mutane yai daidai da shakar kamshin abincin da nayi,
Har ina ture Amal gurin tashi da sauri na toshe bakina da hannu guda na shige daki,
Duk suka bini da kallo gabadayan su,
Amal ce tace bansan wanan sabon salo da fadima ta dauko ba walahi duk aka bude abinci ko ta shaki warin turare sai ta ce wai ita mai, ta fadi karshe da alamar nuna ko oho,ho,
Ba sheriff ba hatta UMMI saida taji wani irin shock din zancen na Amal wacce ita bata kosan tanayi ba,
Ture kujerar dake gabanshi yayi ya nufi dakin nawa,
Ina ciki duke a bakin toilet inata kakarin amai
Ina,gamawa, sai nadago daniyar in ja kafa na zuwa kan gado na
sai na ji na kasa kuma ga sheriff a,tsaye gaba na ya kura min ido kur cikin tuhuma,
Ganin shi danayi tsayen cikin kallon tuhuman da yake min shine,
Yasa na, dan ja kafana nadafa bango don kiris ya rage min in fadi a yadda nake ji,
Hannu ya mika min alamar in miko nawa dole na mika mai hannu yakamani a hankali har ya kaini saman gado
Yazaunar dani ko yanzu ido yakara kura min, a hankali na sada kaina kasa
Don ban iya jure wanan kallon,
Muryan shi naji yana fadin may ke damun ki fatima,
Bakomai na ce mai haiyya ,,,
Kai kawai yakada yakoma falo zuciyar shi na ta mai wani irin tuhuma, akai na,
Lokacin da yashiga falon duk ido suka sa mai don jin ko ya mukayi,
Banda UMMI daketa cin abincin ta, mama umar ce ta yan ko min fruit a plate ta nufo daki na dashi
Sai Amal tace shine kawai abincinta yanzu nayi fada amma bataji sai ,,, bata karasa ba ya daka mata wani irin tsawa saida ta firgita don tsoro,
Ita batasan cewa maganar shi jinta yakeyi kamar zubar ruwan zafi a zuciyar shi,
Ummi tace Amal kin faye surutu da yawa kiyi mata fatan Allah bata lafiya kawai ba wanan surutun naki ba,
Sheriff baici abincin ba tashi yayi ya fita kawai duk suka bishi da kallo

Ina kwance ba barci nakeyi ba idona biyu hannu na rike da handout ina kokarin dubawa amma tunane ya hana ni shakat,
Sheriff na dakin nawa cikin wata jallabiya baka yasa yar fulla fara daidai tsakiyar kai,
A hankali nadago idona na bishi da kallo har ya zauna, kusa dani
Minti kusan biyu da zaman shi duk munyi tsit dakin yace Fatima na ansa a tausashe da na,am,
Yace min tun yau she ne rabona da inyi period, dina,
Sai a lokacin na tuna da zancen period din da nakai wani lokaci ban gane shi ba, fa,
Kuma batare da na damu ba na share zancen kawai, abina
Ganin da yayi cewa bazan asa mai ba yasa shi mikewa yabar dakin cikin tashin hankali,
Washegari kowa kokarin cin break fast niko yayan itace ne a gabana inata masu shan hauka,
Ummi ce ta min Fadima koba kyson cin abinci ki daure kici hakana kinji ko zaki amayar ba duka zaki fitar ba dole a samu wanda yadan tsaya maki a ciki
Don kinga bake kadai bace yanzu,
Maganar bai wani bamu mamaki ba tun da bawai mungane ko may take nufi bane,
Sheriff ne cikin kamar hasala yace min in shirya ya kaini asibiti kawai,
Batare da wani bata lokaci ba na mike zuwa shiryawa,
Ina fitowa naji muryan anty falmata na cewa UMMI sun dace a gaskiya da yaya wannan itace daidai da shi walahi,
Yariyar ta burgeni sosai walahi,,

Cikin shakku da fargaba nai wanan tafiyan zuwa asibiti ina ta rokon Allah yasa kada aga komai a tare dani,,,

Likita ya auna ni yadda ya kamata inda yace, ma sheriffudeen Ahmad matarka nada ciki na wata uku kwance a maranta, kuma munyi bincike abinda ke ciki lafiya lau yake,,,,
Wani irin dam dam naji azuciya na sai naji kamar in kurma ihu don fargaba da rasahin sani mako mata ga sheriff a halin da muke ciki,,,
Sai yanzu nake nadama da danasai ciwo ne na rashin shawar da banyi da kowa ba har haka yasa may ni
Nasan cewa konayi rantsuwa yafi dubu ba mai yarda da cewa ba zina nayi ba,
Aziza Aziza may yasa zaki min haka na pls, keda kika ce da zan ran ciki yadan tsaya zakizo a cire maki abinki amayar maki shine zaki min haka Y pls, Y,
Wani irin kuka mai tsuma zuciya nakeyi a can ciki ciki don tsananin nadamar da ya lulubeni,
Motar naji anyi parking da karfi har saida na dan razana,
Nadogo kaina a hankali na kalli inda muke don ni azatona mun kawo gida ne,
Gefen maikatar su ne ya parker motar hakana,
Yafidda wayan shi da sauri naga ya bidan wata nonba hankalina duk ya tashi don na dauka hukuma zaikira
Can kuma naga ya tsaya yajowa ni takarda a cikin yar briefcase din shi, yadiba wani rubutu,
Sainaji yadan yi ajiyar zuciya kadan
Kaina yana kife inata aikin kukan da yasa may ni,
Kiran mai shi yayi naji yana cewa, doctor, Khan,
Sai yadan zagaya bayan mota don suyi magana,
Bayan sun gaisa ne da doctor yake mai bayanin ko shiwaye,
Nandai yadinga jefo ma doctor tambaya akan artificial insemination din da matar shi tazo da yariya don ai mata ko yayi a lokacin,,,
Doctor kan yace mai no, no,no d girl is already have two, week's pregnant b4,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
7⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,

Motar yashigo tare da mai da kofar motar da karfi,,,
Saida nadan firgita, don tsoro, hakan bai hana ni cigaba da she,shekar kukan da nakeyi ba,
Shiru ya yi kawai ya dan kura min ido don takaicin wanan kukan da nakeyi yake ji ji yakeyi kamar ,,
Make ni saidai kuma da yai dan tunane sai kawai ya dan murmusa kamar bashi bane ke cikin bacin rai yan mintitika da suka wuce,
Jin hannun shi nayi ya dafani a hankali, tare da anbatar suna ,
Batare da na dago kai ba kuma ban iya ansa wa ba saidai na dan tsagaita kukan nawa kadan,,,
Wani irin ajiyar zuciya mai nauyi ya yi tun kun kafin ya fara zance shi,
Yadan dago min kai a hankali da niyar mu yi ido biyu dashi,
Amma sa na saurin kwantar da fuska saboda ban iya jure jimirin kallon shi ido da ido hakana,
Sai yadan yi murmushi kadan ,
A, hankali naji shi kamar may rada yace min nawa Aziza ta saye ki har kika amince da zuwa ai maki, dashen ciki ajinki ki,
Jin nayi shiru kamar ruwa ya ci ne saboda ba kara min mamaki nayi ba jin cewa yasan da zancen dashen ciki a jikina,
Wanan karon cikin daga murya, yake maganar shi,,,
Ina hankalinki yatafi, ina wayonda nasan ki dashi, ina amfani ilimin da kike yi yake,
Ashe ke zaman da kikayi da su hjy as a takari bai sa kin san halin dan adan ba, har yanzu,
Yadan tsagaita fadan yai shiru yana maida nun fashi guda guda kamar wanda zai make ni,,
Yace ki godewa Ubagiji Allah da wanan abin bai zama tabbatace da kin san kowa ye dan adam,
Nadago fuskana, cikin sauri jin danayi yana cewa wai dashen bai faru ba ,
Bayan yanzu likita ya yagama fada muna cewan ina da cikin wata uku a jikina,
Kamar yagane mamakin da nakeyi sai yace na,am kina da ciki a halin yanzu amma bana dashe ba, ciiii
Saina kasa daurewa inji abinda zai ce gaba nace,
Amma duk halin da nashiga ciki sheriff saboda kaine
Don ka na sadakat da rayuwa har akai min wanan dashen don farincikin ka,
Kataimakeni da yawa arayuwa wanda narasa may zanyi in saka ma dashi
Saiga Aziza ta samayni da bukatar intaimaka mata ai maku dashen ciki ajikina idan ya isa cirewa sai acire amayar ta da abinta a jikin ta,
Yan security da suka ga motar mu tadan dade tsaye gefe ne suka dan iso gare mu suna tanbayar mu ko lafiya ,
Sheriff yace lafiya shida matar shice,
Batare da yakara magana ba yaja motar zuwa gidan su na ainihi da nasa wanda mukafara zuwa garin madina muka sauka aciki dasu hjy tsohuwa,
Cikin gidan ya umurce ni da shiga ba tare da yin musu ba na bishi a baya,
Falon gidan muka zauna,
Yace in fada mai gaskiyar yadda mukayi da Aziza tun farko,
Batare da naso ba kuma banda yadda zanyi dole yasa na kwashe duk irin magan ganun da muka yi da Aziza har da likitan su nafada mai,,,.,
Dan teburin katakon dake gefen shi yabuga da karfi yace,
Aziza y pls y may yasa kikai kokarin rushe min farin ciki na,
Yamike tsaye yana cewa, Ya Allah, Subbahanal, Wallhamdullah Allahu, Akbar,
Kuka naci gaba dashi cikin sauti mai kashe zuciyar mutun dake sauraren kukan,,
Ji nayi ya zogab dani ta yarda har zan iya jin nun fashin shi yace min,
In dakatar da wanan kukan da baida wani amfani gareni,
Cikin kukan nace ya barni inyi kuka don abin kuka yasamay ni ni fadima may zan je gida in cewa mahaifiyata da yan uwana,
Yau nice dauke da ciki cikin da ba uban shi, atare da ni,
Shiiii naji yace min kamar yadda ake tsaida yaro idan yana kuka,

Cikin san yayyan murya yace min fadima cikin jikin ki ni ne uban shi,
Ni nai maki ciki da kaina kika samu wanan ciki, najikin ki batare da an maki wani dashe ijin ba,
Asali ma banda labarin plan din ku da Azaiza koda hakan ya faru,.
Zubur na mike tsaye da ga zaunen da nake cikin mamaki nace
Nace sheriff kada ka zolaye ni pls
Bantaba jin kayi wani abinda ba daidai ba a rayuwar zaman da nayi tare da kai,
Balle har ta kai ga kayi wa kanka sherin yin Zina da ni fadima har takai ina dauke da dan shegen ka,,
Banko karasa zancen ba yayo cikina cikin zafi,zafi yana fadin kada ki sheganta min baby na fatima,
Dan cikin ki dan Sunna ne kamar yadda kowa wani dan sunna ya ke tin kaho da ubanshi ni ma haka cikin dake,jikin ki ya, ke tin kaho dani Ahmad lawal a matsayin uban shi,, na sunna,
Da mamaki nadago saboda gani nakeyi son haihuwa yasa shi wanan haukar, da ikirari,
Anya kuwa sheriff ne ke wanan zance, ina yawan alherin shi da addinin shi ya tafi,
Kamar ya gane may nake nufi, ko tunane araina,
Sai naji shi ya rungumay ni cikin jikin shi,
Magana yake min kamar rada, rada kamar kuma akwai, wani kusa da mu wanda,zaiji may zaice min,
Yace min Fatima ki kwantar da hankalinki, ki saurare ni da kyau , kiji bayanin da zan maki,
Ina rugumay a cikin jikin shi naji shi yana fadin
Ina son ki yafe min akan maganar da zan fada maki,
Yau shekara uku da wasu yan watan ni ke nan da aure na da ke fadima,
Dasauri na dan jaye jikina daga jikin shi ina mai kallon mara hankali ko kuma wani zautace,
Ya ce min yes abinda kikaji haka yake,
Tun zuwan ku nan madina bada wani dadewa ba wanan abin yafaru,
Shehi shine hjyn ki tasa ya wakilci auren ki, dani tare da wani dan takari na tare da su,
Ni na hanna afada maki a wanan lokacin saboda a lokacin nadauka auren rufin asiri ne kawai mukayi,
Nikuma, ina son ko ba komai ki samu ilimi daidai gwargwado, yadda zaki amfanana nan gaba,
Sai dai ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba naji kawai ina bukatar wanan auren namu yaza mai daurewa har abada,,,
Na,kara daga kai na kalle shi, cikin mamaki,
Yadaga min kai tare da kafadan shi yace yes, I mean it,
Aure na da ke mutu ka raba ba wai na jeka na yi ka ba ne,,,Auren nadan wani lokaci kadan, a, a kireke a ranki cewa nida ke sai mutuwa,
Idona tab da hawaye, nace Sheriff yace min shiiiiii yasa dan yatsan shi ga baki alamar in yi shiru,
Tun da farko Fatima ban yarda cewa ina son ki ba nadai san cewa duk wani lamari naki tausayi yake bani,,,
Amma sai ga shi cikin ikon Allah naji na fara son ki,
Ban gama tabbatar da cewa ina sonko da gaske ba sai,
Sai lokacin da na sanki diya mace na dan dani zumar ki, nakuma gane baiwa da ni,imar da Allah yai maki, duk baki a cikin hankalinki,
A lokacin na tabbatar wa kaina ko zan rasa raina ba zan taba rabuwa da ke ba,
Ya nuna min cikina da hannun shi yace min ni nayi abina da kaina batare da taimakon wani likitaba,
Kara dagowa nayi nakalle shi again,,
Lokacin da baki da lafiya a makkah da Aziza tasamu urgent call daga Nigeria nadago da sauri na ina mamaki
Baki da lafiya aranan kina, ciwon ki na mara da kikeyi lokacin da kika gama period dinki,

Sai na dukar da idon kasa, wani irin kunya naji, alokacin,, sai,
Abinda ya faru ya fara dawo min dan tunawa tiryan tiryan a lokacin,
Dana farka bayan nasha maganin da sheriff ya bani barci mai nauyi yadauke ga kuma tsoron mafarkin macijin da nayi sai kuma gidan da ba kowa a,lokacin mun rage yaw,
Ina farkawa Sheriff nagani akaina cikin damuwa a fuskan shi ina tashi yai ajiyar zuciya ,
Shi ya taimaka min zuwa bayi har nakai kofan shiga bayin yace min idan nashiga tunda nayi mafarkin maciji in,yi wankan tsarki kafin in fito,
Sai na waigo da mamaki ina dan tunanen saboda mafarki da na yi,zanyi wanka,
Kawai dai sai na shege abina batare da wani kwankwanto,ba,
A bayi kuma ruwa zafi nafara anfani dashi, sai,daga baya nasa masu dumin da yace min indan shiga shiyasa har na dan ji saukin zafin da nake ji ,
Nadade acikin ruwa zafi na,gasa jiki dasu, hakan yasa har nadan iya, inya tafiya kadan da na fito , dana fito duk zafin da nake ji dazu ya rage min,,,,
Bayan nayi sallah ne, nakoma na kwanta tare da shan maganin da sheriff yakarabani a lokacin,,,,
Tunanen da yaga ina yi yasa shi yin shiru yana kare min kallo cikin tausayi,
Ina kai karshen tunanen nadago kaina da sauri muka hada ido sai ya kada min kai alamar eh haka zancen yake ai,
Durkusawa nayi kasa nakara rushewa da wani sabon kuka wi,wi,
Shiko, sheriff, Ido kawai yasa min nayi kuka mai isa na batare da yalalashe ni ba,,,

Fadima wanan kukan da kike yi yafi maki dadi ga wanda Aziza taso jefa ki aciki,
Nadago kai nakalle shi may ye babbacin hakan da wanda taso sani ciki,
Aini gare ni duk dayane, basu da bambanci agurina ,

A cikin zuciyar shi , wani iri yake ji gamay da fatiman , saboda duk ta birkice mai a lokaci guda,
Sai lumshe ido yakeyi, tuna ne kala kala, na shiga zuciyarsa,
Idon shin kan a kyakkyawar matar tashi,
wace yake ji tankar ya hadeye ta don so, a yan zu
Sai fadi yake cikin zuciyar shi yana cewa, Allah nagodema da kabani wanan yarinyar a matsayin mata ta,
kuma uwar "yaya na, anan gaba tabbas wanan yarinyar kyautace daga ubangijin shi,,
Duk da girman shi da kuma kudin shi da ikon shi, sai ga sheriff tsugune a gaban yar karamar yarinya fadima
Yadan riko hannu ta ya hade cikin nashi yace mata,
Fatima kiyi hakkuri ki rugumi kaddaran da Allah ya kawo muna ,ba don mun yi mai laifin komai ba,a,a hakan dai yaga daman bamu namu rabon,,,,
Cikin rashin fahinta, na kara kallon shi, inda yaci gaba da maganar shi,
Saidai ina son ki san cewa ni agare ni cikin yai min daidai, kuma yazo min a lokacin da nake bukatar shi,
Don Allah kadai yasan dalilin dayasa wanan cikin yasamu a wurin ki ba,a wurin ta ba can daban ,,,,
Don haka ni bawa ne mai rungumar kaddara, a,duk ta yanda kaddara ,yazo min,,,,

Ya mike tsaye yana cewa idan kin gama kukan ki sai ki share hawayen ki,
Mutafi in kuma anan kike son mu kwana har ki huce U are welcome,
Da sauri na mike tsaye don gani nakeyi kamar zai kara tursasa ni ne kuma,
Yadan yi murmushin ganin irin mikewar da nayi cikin sauri don yasan cewa aikin gama ya,gama ko,
Ina batun fita daga falon yace min dakata a inda kike tukun, cak na ja, na, tsaya guri guda don bin umurnin shi,
Yai dan taki kamar biyu ya iso inda nake yace min,
Wanan zancen ban son kowa yaji ina son ki barni da Aziza tukun ,,,
Kai kawai na gyada mai alamar naji,,
Ji nayi yadan rungumu ni zuwa, jikin shi, a,hankali naji yakai hannun shi saman marana yana dan shafawa a hankali,
Jin danayi bazan iya jure hakan ba don yau saina ga yakoma min kamar ba sheriffudeen Ahmad din da nasani ba,
Zukewa nayi na silalo kasa na zamay jikina daga nashi a hankali,
Yadan kalli inda nake tsaye ina maida numfashi na guda guda,
Saida ya lashi laben shi yadan shafa kan shi kadan yai murmushi, kawai,,,
A, Lokacin karfe kusan daya na rana, don haka muka wuce gida
A mota kowa da abinda yake kullawa azuciyar shi,
Nidai kamar a mafarki nake jin zancen cikin nan nawa,
Wai yau ni fadima diyar inna yar kulu ce, ke dauke da cikin wani na miji batare da sanin mahaifiyata ba,
Ni dawani irin ido zan kalli inna na,
May yasa hjy ta wuce tabar ni a saudiya
Data tafi dani da hakan bai faru ba ,
Ya Allah ni kuma irin tawa kaddaran rayuwan ke nan,
Abinda muke ji ko gani yana faruwa, yan takaru sun koma gida da goyo ko ciki shi yafaru akaina,,,
Gab da zamu shiga kwanar unguwar mu ke nan, nake wanan zamcen zuccin
Ganin da yayi nafara shirin sulalo da wasu hawayen yace min
Idan har ina son Amal su gane irin halin da nake ciki ne to sai in matsa inta kuka,
Dole nadan goge hawayen dake shirin fito min cikin kunar zuci
A hankali nafito daga cikin motar yana tsaye gefe guda yana min wani irin kallon tausayi,
Shikam shi gaskiya duk da ya son haihuwa baiso hakan ta kasance dani ba a lokaci guda sai kuma yai istigifar cikin sauri don yasan cewa ba ai ma Allah shishigi,
Har na shige ciki yana tsaye yana kare min kallo cikin tausayi,
Ummi ce nasamu a falo zaune tana kallon yadda ake ta kiran sallah a garin madina da kewaye cikin tv,
Da murna ta tare tai min alamar inzo inda take, in zauna,
Ina zamake nan take ce min ina mijin nawa yake ne yatafi dani ya barsu da tunanen ko lafiya tun dazu,
Da mamaki nake kallon UMMI watau duk sun san da cewa ni matar sheriff ne dama
Amma ba wanda yataba fada min
Anty falmata ce takawo min fruit cikin plate ta zauna kusa dani tace ce min in sha kozan dan ji karfi jikina tunda bana son komai,
Sheriff yashigo UMMI ce ke rambayar shi cewa ko mun ga liktata sai yake cewa daga can muke ai,
Ya zauna da niyar cin abinci sai wayar shi tai kara,
Aziza ya furta a sanyaye yadan daga kai yaga irin re,action din da zan nuna,
Niko da sauri nadago kaina muka hada ido nai saurin kawar wa gefe,
Aziza ke sheda mai cewa zata iso saudiya tana son zuwa ta ziyar ci, su fadima ta dan dade bata gan su ba,
Sai yake ce mata hakan nada kyau ai shima suna gurin mu sun zu da su UMMI ziyar mu,
Cikin yawan take ce ma yaka ganar min fadimar pls,
A, fadima tai wani girma tayi kyau da ita ai,
Tai murmushin mugunta har yana jinta,
Yadan daga wayan yakalla kamar itace yake kallo a fili,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment