Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya bata ansa ba sai kukan da nakara sawa wi,wi,
Shin inna ko dai mi na,na tun da har Allah yasa ta dawo gida ai sai ai hakkuri da shiya ko,,
To mi da baki hwda muna ba tunda kin ka taho,
Ai ke ga sai musan nayi ko
A hankali nadaga kaina nakalli hafsi na ce mata hafsi nifa ba shige nayi ba,
Cikina yana da uban sa na halak,,
Ke jiya ko cikina kuwa da gaskiya,
Wagga diya ke kashe mu wallah
Mi za mu wa cikin garin ga shim,
Daga haka ban kara cewa komai ba sai nai shiru,
Maganar hafsi na kona min rai,
Mariya ta ce oho shina suke ta,dawo muna da duk wani tsaraba da anka ba su,
Oho sunyi wa kansu, don su ka shirin jin kunya wallah,
Shigowar Abdull yasa su yin shiru, ga zan cen su,
Saida ya zauna yake cewa mariya wai yanzu ya gama fada da wasu yara sun ce mai yar shi ta dawo yawon karuwanci saudiya da yar shegiya da cikin shege,,,
Halan mi kace masu in ji mariya,
Hafsi ta tare zance da cewa mi zaicewa kuwa tunda ba karyana sunka hwadi ba maganar su dutse na,
Shim mika damunki na hafsi,,,,,
Da wani zamuji da zancen ki ko da ta mutane shin,
Inji innar mu tace wa hafsi hakana,
Fushi tayi batare da tai muna sallama ba tabar gidan cikin fushi ,,,,
Kallon mamaki duk muka bita da shi,
Mariya tace yanzu haka muna hukan gidan su na sun ka zugo ta,
Ita ko ta taho tana ma mutare bori,

🐎 ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI* ✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,,,


Tunda Amal tagane cewa, fadima bata gidan hankalinta yafara tashi,
Gidan Salimat suka fara zuwa don su bincika ko tana can,
Sai Salimat ta nuna masu cewa ai itama jin da tayi shiru bata ji motsin su sun laiko ta ba yasa take zancen zuwa gurin su, don ta bincika,
Hankalin su duk ya daga, saboda rashin sanin halinda fadima take ciki,
Maman Omar ta nuna cewa fadima ta wuce da Aisha batare da sanin ta ba,
Don haka Salim da kan shi ya tafi garin makkah don ya diba ko mun tafi can ne,
Saida duk inda yasan cewa fadima na zuwa yatafi don ya diba ,
Haka yadawo gida madina jiki ba kwari yai masu bayanin cewa bai samu koda labarin wanda zai ce ya ganta ba,
Hankalin Ummi duk yatashi sosai da jin cewa nabatane,
Aziza gari na waye ta fito falo don tayi break fast takuma yi abinda ta niyar yi a zuciyar ta,
Takai minti arba,in zaune gurin bata ji koda motsi na bane,
Tashi tayi zuwa ciki don ta ganewa idon ta abinda ke faruwa da ni har ya hana ni fitowa yin break tare da kowa,
Ganin da Amal tayi kamar tana cikin wani uzuri yasa hankalin amal ya koma wuein ta,
Aziza tana zuwa ta murda kofan dakin da nake ciki sai tagan shi a bude
Kutsa kai tayi ciki batare da fargaban komai ba
Saidai yadda taga dakin tsab alamar ban kwana a cikin sa, ba yasa ta zargin ba,a gidan na kwana ba,
Fitowa tayi da mamaki ta nufi gurin mama Umar tana tambayar ta ko ina fadima, ta, tafi, yau,
Maman umar tace ita ma dai bata gan ta ba, tun da gari ya waye,,
Amal na biye da ita duk wanan sintirin da take yi kamar mahaukaciya,
Wanan abin yasa suka gane cewa itama din bata san inda na nufa ba,
Sai dai suna zargin cewa akwai nasabar batana da ita,
Amal tana mamaki taya zan bar gida batare da sanin ta ko kuma salimat,
Ga sanin da taimin duk abinda zan yi sai na fada mata saboda daukar ta da nakeyi kamar elder sister di ta ,
Salim ko da yaushe yana shiga cikin massalaci koda Allah zai sa ya ganni a can,
Tun tafiya na da kwana biyu aziza ta shirya tabar gari cikin bacin rai don rashin samun aiwatar da nufin ta a kan ciki jiki na,

Rashin sanin abin da zasu fada wa sheriff indan yaji cewa na bata, ummi tace kada kowa ya fada mai su bari ya karasa aikin da ya kai shi, ai,duk inda yake ai zai dawo gida,
Tuna nen da ummi ke yawan yi, a gamay da ni,
ya nuna mata cewa, sheriff ne kawai zai san inda na tafi,
Saboda shi yasan kasar saudiya da kyau fiye da su Salim,
Don haka suyi shiru da bakin su, har yadawo,
Za ya gane duk inda nake, kuma tace masu ita zuciyar ta yana bata cewa ina gurin mai kyau ba wai mugu hannu kamar yadda su ke tuhuma ba,

Duk wani abinda Sheriff Ahmad keyi hankali sa na gurin iyalin shi musan man fadima wace tun kusan zuwan shi kasar spain da kwana biyu rabon da suyi waya da ita,
Abin yana damun shi so sai a ran shi
Sai yake ganin cewa fushi fadima ,takeyi da shi, saboda ya wuce batare da wani cikakken bayani ba,
Shima dai tafiyan haka tazo mai ba shiri daga Riyadh tafiyan takama shi sai suka wuce daga can,
Amal ce, yakira yau don ya tan baye ta, yaji cewa ko lafiya fadima take saboda baya samun wayar ta,a
Sai dai Amal din ta boye mai zancen tafiyar fadima,
Sai ce mai tayi wayar fadima ya ,bata
Kuma fadimar bata zama a gida sosai saboda tana zirga zirgan hada jarabawar ta,
Bawai sheriff ya gamsu da bayanin Amal din bane, kawai dai baida yadda zaiyi ne, saboda nisan da,yayi da saudiya,

Yau a gajiye yadawo gida saidai kuma lokacin tashi daga meeting din da suka shiga bai yi ba, saidai kawai ya kama jin ba dadi a ransa, don haka yafito abin shi zuwa masaukin shi,
Yadai dawo ne kawai saboda yau sam baya jin dadin jikin shi,
Yana shigowa masaukin shi ya aje yar briefcase din shi gefe kawai ya haye kujera ko takalma ya kasa cire, wa,
Nan waje barci ya kwashe shi kawai batare da wani bata lokaci ba,
Duk da barci bai yi nisa ba amma sai wani mafarki mai firgitarwa ya sa,shi farkawa a firgice yana mai yin salati da istigfar,
Gaban shi ne yakama faduwa saboda duk second sai yatuna da mafarkin da yayi,
Fadima ce yagani zaune a tsakar daji saman wani dutse, gurin duk ciyawa ne kore shar,
Saidai tana dago kai sai yaga duk cikin damuwa take da fargaba, ga hawaye jagab a fuskarta,
Wanan mafarkin ya tsaya mai a zuciyar shi,
Sai tunane yake yi anya kuwa, ba wani hali Fatima take ciki ba,
Tunda yasan cewa ta na cikin barazanar Aziza a ko wani lokaci,
Duk yadda,yaso mafarki yafita mai a rai ya kasa, duk abinda yake yi ,
Wanan mafarkin da yayi yake tunawa, abin har yana,son zama mai kamar fever,
A dadafe gari yawaye mai saboda duk ya matsu ya zo saudiya, hankalin shi a tashe yake,
Jirgin farko da ya sauka a saudiya daga Spain dashi a cikin sa,
Bai ko tsaya zuwa gidan shi na Riyadh ba,
Shatar mota ya dauka zuwa madina, shi kadai, ne a cikin, motar,
duk gudun da driver ke yi gani yake yi kamar baya gudu,
Karfe biyun rana suna cikin garin madina, direct gida ya dosa,
Duk wanda ke gidan saida yai mamakin ganin sheriff
Saboda ba su san da zuwan shi ba, a wanan ranar,
Gaba dayan su, duk sun shiga cikin rudanin ganin shi cikin wanan lokacin,
Kowa da ke gidan, yazo yi mai sannu da zuwa a daidai wanan lokacin,
Karba masu kawai yake yi yana dibar hanyar da zaiga na fitowan fadima,
Abinci mama umar ta gabatar mai a saman dinning table,
Kasa daurewa ya yi yace ma Amal wace ke zaune gefe guda duk a takure,
Fadima fa,
Amal kallo ta kaiwa ummi, don ta bada ansa, tambayar da yai mata,
Yadda yaga Amal na nunawa yasa shi mikewa tsaye a lokacin,
Kamar may rada yace may yafaru da Fatima Amal ,
A hankali Amal tace ba komai, yayan mu, kawai dai sai kuma tai shiru ta dukar da kan ta kasa,
Muryan ummi ce yaji daga bayan shi tana fadin ka kwanatar da hankalinka ka ci abinci tukun kafin ai maka bayanin komai,
Da sauri ya juya gurin da Ummi take tsaye cikin wani irin murya yace dan Allah Ummi ku fada min abinda ke faruwa da Fatima,
Ummi tace kayi hakkuri ka zauna insha Allah komai zai zo da sauki,ai
Girgiza kan shi yayi yace ban fahinta ba ummi, har yanzu ina fatimar ta ke ne wai,
Muryam salim yaji ta bayan shi yana cewa wallahi ta bata muna,
Da sauri ya juya gurin Salim ya riko hannu shi yace What,
Ta bata kamar wata dabba can, tun yaushe ta bata da baza,a fada min ba,
Har saida nagani da ido na,
Shiru duk sukayi,
Ba abinda yake nanatawa a bakin shi sai innalillahi wa,ina alahim raj,un, kawai yake ta fadi
Dan dir dir ya yi na rashin sanin abin yi sai kuma yasamu guri ya zauna yadafe kan shi da hannayen shi,
Nanda nan idon shi suka kada sukayi jawur, kamar garwashin wuta,
Duk suna tsaye tsarma tsarma suna kallon yadda ran yan maza ya baci yau,
Salim ya kalla yace mai kai min bayanin komai pls
Don insan ta inda zan fara bullowa zancen,
Salim ya fada mai dan abinda yasani gamay da batar nawa,
Amal ta karbe zance da yi mai bayanin duk abinda ya faru tun wucewar shi, sai kuma maman umar da ta bada nata bayanin ita ma,
Wani irin mugun kallo yai masu a lokacin cikin jin haushi da ta kaicin su,
Bai ce komai ba yasa kai kawai yabar gidan, cikin zafin rai,
Salim na ganin haka ya mara mai baya suka fita tare kusan lokaci guda,
Da farko gidan Salimat suka, nufa
Ita madai bayanin duk yadda fadima ta firgita da Aziza tai masu, amma ta kare zancen da cewa sun yi da ita cewa washegari zata dawo gidan ta ta zauna da ita har sheriff yadawo,
Sai kawai taji shiru kuma daga baya sai ga Amal ta bugo mata tana fada mata cewa fadima bata gida,
Shiru yayi nadan wani lokaci yana nazarin zancen ta,
Daga gidan Salimat gurin ja,mian tsaro ya nufa kai tsaye,
Batare da bata lokaci ba suka fara aiwatar da aiyukan su,
Dawowar sheriff da kwana daya su Salimat suka bar kasar saudiya ita da mijin ta,
Saboda ta kare karatun ta, dama karatu ta, tafiyi ga shi Allah ya nufa har ta kare,
A ranan bai kwana a garin madina ba Makkah ya wuce kai tsaye,

Washegari duk wani bincike da zaiyi yayi saidai babu labarina sam,
Babu ma wanda yace mai yagan,ni a garin, makkah
Hankalin sheriff yakara tashi sosai don ya rasa ko ta ina zai fara binciken,
Shin ta Aziza ko ta Alin, zai fara, wata zuciya tace mai duk kan su,
A bokin shi doctor kamal ne ya bashi shawaran su fara bincike akan Alin tukun,
Duk iya binciken su sungano cewa Alin baya zuwa saudiya har yanzu tun lokacin da yai yunkurin sace ni,
Sai suka dawo kan Aziza, kuma,

A Dubai ya samayta inda ya buda mata wuta akan cewa lalai sai tayi mai bayani akan abinda taje yi saudiya bayan tasan cewa baya kasan a lokacin,
A lokacin Aziza ta dauki zancen da wasa so sai dan bude baki tayi tace mai
Amma dai tana da right din zuwa duk lokacin da taga dama ko,
Ko saboda yayi auren yar kwaila zai zo ya damay ta
To bari ta fada mai indai akan fadima zai zo ya tayar mata da hankali sai tayi maganin su shi da ita,
Kafin ta fadi wani kalma wani irin wawan mari ne ya sauka a fuskan ta saida ta gigice,
Ya shake mata wuya da hannu guda ya ce ki fada min ina kika kai diyar mutane ,aziza,
Fadima ta bace a saudiya ba wanda yasan inda ta tafi,
Ido ta waro waje don jin kalamin shi
Ta ce ta bace fa kace ya dan sasauta shakan da yai mata ya ce kwarai kuma ke muke tuhuma da bacewar ta,
Nan ya koro mata duk abinda Amal da maman umar suka gani a gamay da ita, lokacin da tasa fadima a gaba,
Ta yi mamakin jin cewa a wanan lokacin da tai ta sintiri a kofar fadima a ganta,
Harda yunkuri zuba Meagan da zai zubar da cikin fadima datayi,.
Cikin sanyi murya tace wallahi ba ita ce ta sace fadima ba san da tayi cewa gurin hukuma za a kaita kara
Indan kuma anyi karanta kasar Dubai zasu dawo da ita kasan haihuwar ta ne ba zasu kara barin ta shiga masu kasa ba,
Tai wani yunkuri don ta mike shiya sanya shi dan ne mata kafa da tasa
Yar kara ta saki ta ta dibe shi da sauri, sai taga ya canza mata ba Ahmad din da tasani bane yau,
Muryanta na rawa tace wallahi bani na sa aka sace taba,
Ni yunkurin zubar da cikin da ta yaudare ni ne kawai nayi,
Wani irin mugun shaka ya kara kai mata ya saida idon ta yafito waje don azaba,
Tunda take ba,a taba gwada mata azaba irin wanan ba,
Duk yadda taso ta motsa ko ta kwace kanta ta kasa
Wani zogi da radadi ya ratsata,
Kallon ta yakeyi yana nazarin irin rudewar da yagani a idon ta,
Can tace wallahi Ahmad ka yarda da ni ban san komai a gamay da batar fadima,
Cikin wani irin zafin rai ya sake ta yana huci yace barin fada maki aziza muddin bincike ya nuna cewa da hannu ki a cikin wanan zancen wallahi bazan raga maki ba ko kadan,
Bai kara koda second ba ya juya yabar gidan cikin fushi,
Nan Aziza ta rushe da kuka mai tsuma zuciya tayi da tasani ga shirin da tayi niyar ai,watar wa a kan fadima,
Wani abokin su ne ya basu shawaran su koma saudiya su kara bincike duk yadda akayi zaau gane inda fadima take,
Su Amal sun rasa gane kan dan uwan su tun da wanan abin yafaru,
Ya koma masu kamar wani mahaukacin zaki, sai jami,an tsaro ke masu sintiri a gida,
Wanan lokacin duk wqni wanda ke tare da shi yasan irin kaunar da son da yakewa fadima,
A nacikin wanan halin aka bugo mai waya daga Nigeria cewa jikin hjy tsohuwa ya tashi,
Gabadayan su suka zo Nigeria dan diba jikin nata,
Kwanan biyu ya koma saudiya don ci gaba da bincike,
Nasir abokin doctor kamal ma aikacin yan sandan ciki ya basu shawaran zuwa ma aikatar tafiye tafiye don adiba masu,
Sheriff yace yasan cewa fadima bazata iya kai kanta gida ba saboda tun tana yar karama akabar Nigeria da ita,
Don haka da wuya ta iya komawa garin su,
Ganin cewa Nasir din ya nace ne yasa su zuwa maaikatar tafiye tafiye na kasar saudiya,
Sunayen wa,yanda sukayi tafiya a wanan date din zuwa yanzu aka fitar da photos din su ,
A madina suka fara bincike basuyi nasara ba sai suka tafi jidda,
Ganin ko a jidda ba suyi nasara ba yasa yace masu su bari kawai don shi dama ya san ceqa ba zan iya komawa gida ba,
Doctor kamal yace sam sai sun tafi Riyadh sun karasa bincikawa,
Binciken farko ya nuna masu photo nadana Aisha a ranan da mukabar gida ranan nabar kasar saudiya zuwa kasata ta haihuwa Nigerian,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,,


Tunda nazo dogon daji ban fita ko ina ba ina cikin gidan mu,
Don ko yaushe, ina tare da innar mu muna hira,, tana bani labarin bayan tafiya ta,
Duk ,zaman hiran da mukeyi da inna bata taba tambayana komai ba gamay da cikin da ke jikina ba
Don haka nima ban san taya zan yi rashin kunyar fada mata wani zancen ciki can
Shiru nima nayi kamar yadda tasa min ido, ba wanan zancan a tsakanin mu,
Yar uwata mariya ta na matukar, kokarin ta wajen ganin farin cikina don kusan duk wani dawai niyar mu itace mai yi batare da gaza wa ba,
Hafsi ce ke ban mamaki idan natuna yadda ta ke nuna min kyama karara,
Mariya kan ce min in fita batun ta ba laifinta ba ne ,
Ra,ayin mutanen gidan su ne take bi, shiyasa don tasan halin su sarai da iya kulla sheri,
Ina kwance cikin yar rufar karan dake kofar dakin Innar mu, muna shan iska .
Saboda rana yai zafi sosai daki bai zaunuwa a lokacin don haka nan muke dan zama musha iska ,
Abdull kani na yashigo gida da yar ledar shi a hannu dawowar shi kenan da ga makarantar bokon da yake zuwa shida mariya,
Ledar dake hannu shi ya miko min daidai lokacin da nake mai sannu da zuwa,
Nakarbi ledar cikin mutunci da girmana alheri,
Yace min umhumm, kwaida kwaina nis sayo maki
Yanzu niggani shi hanya a na suya nai dama jiya nai alkawarin zan sayo ma wagga diya wani abu da kuddin tarana,
Tausayin yaron yakamani har cikin rai na saboda ni da Aisha ya tauye kan shi yau bai kashe yar ashirin din shi ba, da ake basu,
Ganin da yayi ina tuna ne ban bude ledar ba yasa shi matsowa kusa dani yace ko baki cina naga baki bude ba,
Dan murmushi nayi na bude ledar da sauri,
Sai kamshin awara ya bugi hanci na da sauri cikin irin yanayin kwadai na mai ciki na dauki guda nakai a bakina,
Aisha na mikawa guda biyu saura kwara uku sai na bashi guda, na mikawa inna guda biyun da suka rage,
Inna ta ce aiko yau kaji kumya kaida kasawo kuma harda kai za,aci,
Duk muka sa dariya a lokaci guda,
Muna cikin dariyar mariya ta shigo itama a gajiye saboda dan karen tafiyan da suke sha kafin sukawo gida don makarantar nada dan nisa da cikin gari,
Tashi nayi na kara shimfida masu tabarma nadauko masu abincin su naje masu,
Daidai lokacin mariya tafito daga daki tace kai anty fadima mi da ki ka wahalal da kanki , dauri ki barshi kawai,
Ganin da nayi Aisha ta cinye kwai da kwai har tana yar lasar hannu ta yasa ta bani tausayi so sai,
Saboda nasan yariyar a tauye take ba wai ta saba da irin wanan rayuwar ba ne,
Sai a lokacin natuna da canjin kudin Nigeria da salimat tabani da zamu wanda tace min in rika don zai min rana so sai, idan na isa,
Ta shi nayi na shiga daki na jawo jakata da inna ta tura can kar kashin dan gadon karfen ta,
Gurin dauko kudin ne idona yakai ga wayana dake kashe tun lokacin da na zo Nigeria,
Sai kuma lambar su safiya da nagani a cikin yar pepper da na rubuta ta, tare data hjy umma,
Jakar nadauko gabadayan ta don daukar
Kudin da wayar, nafito waje da shi
Kudin dake acikin jakar gaskiya zasu kai kimanin dubu dari biyu, na Nigeria,
Yan dubu guda guda ne cur din su,
Bayan na zauna na zaro dubu guda duk da ba sanin kan kudin nayi ba,
Na mikawa Abdull nace yaje ya sayowa Aiaha takara ci,
Ido suka fitar waje duk kansu suna hada baki lokaci guda
Dubu daya za,a tai zuwa sayen kwai da kwai da shiya,
Mariya tace wanga kwai dakwai da ko dadi ba shi da,
Galala nayi tsaye ina kallon su da kudin a hannu na,
Mariya tace bari yanzu in tashi in soya maki in so nai kikai yahi atai zuwa sanyen wanda bashi da dadi,
Abdull amshi kudin katai ka sayo wake da mai ,
Tunda na zauna bayan fitar Abdull sai hankalina ya koma ga wata,
Nasan cewa caji ya kare, tunda tunda nazo ban kunnata ba,
Mariya ce ta karba ta dan diba tace wai wai wagga waya aita manyata,
Bari in kai maki ita nan gurin isah yasa maki caji don walleh ba mu da gurin sa caji gidan ga,
Murmushi nayi araina kawai don ba wurin sa caji ba duk gidan ma ai na son gyara,
Naso in dan bada kudi a

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment