Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saida yaji maganar da musa ya ci gaba da fada min ne, yagane cewa ba wasa bane wanan zance, ta shi,
Musa yaci gaba da fadin,
Don isa ma har yawon nuna sheda takewa mutane a cikin gari,
Ni wallahi su baba ma sun cuce ni da suka hana inturo masu yar uwar su,
Tun batazo nima watarana ta haifa min mugun iri a gida ba,,
Idan mace tana jin cewa kudin yawon duniyar ta na iya ruda musa ne wallahi tayi karya,
Dan ban ga wanin abin arzikin da aka zobda shi duk wanan uban dadewar, da akayi a uwar duniya,
Yai wata yar dariya irin ta yan iska, yace,
Dan musan gaskiyar komai wallahi, duk gumama ne aka tsira da shi, kawai,
Mariya ce ta,yi kokarin tsayawa dan ta bashi ansa
Duk da na, hana
mata hakan cikin tsawa hakan bai hana ta cewa idan baka sako hafsi ba yau daga gidan ka musa lalai uwar ka da zina ta haife ka,
Kokarin shirin dukan ta yayi saida malam Basiru ya tare shi ya ce mai baka da gaskiya musa,
Don dai yaran nan basu ce muna komai ba banda gaisuwa,
Malam basiru ya juyo inda muke yana mai bamu hakkuri,
Nasamu naja mariya muka shige gidan kawun mu
Mariya tana ta bambamin ta,
Jin muryanta da kawu yayi ne yasa su fitowa don jin komai ke faruwa,
Nan mariya ta kwashe komai ya faru ta fadawa kawu, salihu,
Kawu ranshi ya baci so sai yace aiko musa zaka ji kunya wallahi,
Dan daukar alhakin wanan yariyar da kukeyi a garin nan yai yawa wallahi don nagane cewa bakomai bane hassada ne yakawo hakan
Saboda kawai anga cewa yar kulu da yaranta Allah ya rufa masu asiri,
Bayan mun gaisa da kuwun mu wanda nasamu da kyat ya hakkura yai shiru, da fadan da yakeyi da musa,
Dan yace sai yai karar musa gurin maigari akan irin wulakancin da yake min,
Bawai wani dadewa mukayi ba agidan nakawu sai mukayi sallama da su mukabar gidan,kawu salihu
Don mariya na son zuwa gaida wata kawarta da bata da lafiya,
Saboda nasan yariyar sosai tana yawan zuwa gaida ni ko kuma ta dauki Aisha zuwa gidan su tai mata kitso har da kumshi,
A gidan su yariyar nasamu taron arziki sosai shine gida na hudu da nataba shiga tunda nazo dogon daji,
Gidan mu gidan kawu salihu, saiko gidan su hafsi inda akai muna mugun wulakanci saboda kawai hassada,,,,

🐎ZEEE MAKAWA
[12/3, 9:40 PM] ‪+234 706 078 6258‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,

A, jere motocin suka gan gara cikin garin na dogon daji lokaci guda,
Duk wani wanda waje a lokacin yaga shigowar su cikin garin,
Wasu mutane ne maza mutum biyu ke tafi a gefen hanya gudan mutumin yana ta faman sababi ,da alamar fada yakeyi,
Motar da security ke cikine yadan tsaya a gaban mutanen biyu dan tambaya,
Bayan sallama da sukai masu gudan ya karba masu ne sai na cikin motar yake tambayar su dan Allah suna tambayar gidan mai gari ne,
Kwatace malam Basiru yai masu na inda zasu bi zuwa gaidan mai gari,
Gefe suka dan rabewa motacin don su wuce, sai dai duk suna bin motocin da kallo
Ta yadda za,su iya ganin wa,yanda ke cikin motar zaune,
Mota tabiyu ce tafi daukar hankalin musa so sai,
Yace kai mutumi kaga wani hadaden guy cikin wanan motar da ganin shi shege, naira ta zauna mai boko ya ratsa ko ina,
Har motocin suka shige kwanar gidan mai gari suna tsaye suna masu kallon kurullah
Basiru yace kila wasu jami,an vwaunatine suka shigo yin wani aiki,
Sai musa yace ka ko ga wanan motar ta bayan da alamar kaya ta dauko acikin ta,
Kawai gara mu isa kada aba mu labari,
Suka bi bayan motocin cikin sauri kamar zasu tashi sama,
Duk wanda yaga motar sai shima yabi don zuwa ganin ko may ke faru ,
Irin dai yadda kauye ke samun abin gulma duk akewaye,
Bayan security sun fito sukai saurin shiga wurin mai gari don naiman isa tare da jagorar malam illa,
Batare da bata wani lokaci ba fadawar maigari suka gyara masu guri zama,
Nan da nan mai gari yasa akawo masu ruwa mai sanyi da abin sha na gwangwani,
Inda aka masu masauki kafin suga maigari aji abinda yakawo su garin
Sallah suka fara gabatar wa,tukun acikin jam,i
Suna gama sallah saiga wasu yara sun shigo da furar shimkafa yaji nono da kan kara
Wanan irin taron da maigari yasa akai masu duk da bai san ko su suwaye ba,
Yasa sunji dadin hakan gaba dayan su ,,,
Cikin zuciyar Sheriff yace yanzu yafara ganin inda nadauko sanin darajan mutane,
Iso akai masu har cikin zauren maigari inda securities suka tsaya wajan zauren,
Sauran jama,an gari duk suna daga gefe sunyi cirko cirko dan jin ko wani irin sako aka zo dashi,
Malam illa ne yafara yiwa mai gari bayan dan abinda yasani na cewa daga Abuja yazo dasu don suna cigiyar garin shine yai masu jagora,
Bayan maigari yai masu barka da zuwa ne sai Shehi ya dauki zancen da cewa mai gari,
Lokacin ne Kawu salihu yazo wajen da niyar karar musa wurin maigari don sherin da suke kulla ma fadima yai yawa,
Kawu na zama daidai lokacin Shehi yaci gada fadin,
Mun shigo wanan garin ne a saka makon nemar wata yarinya da mukazo
Wace muke zaton cewa yar wanan yakin ce daga saudiya ta fito batare da sanin mijin ta ba lokacin da ta bar saudiya saboda yan wasu dalili lai nata,
Kafin Shehi yaci gaba da bayani, sai kawai muryan
Kawu Salihu ya cabe maganar yace ko fadima, cikin razana Sheriff da sauran suka shakka babu itace,
Ai sai kawai wuri yadauki salati,
Inda har nawaje suka shiga leken ko may ke faruwa da har ake salati haka,
Saida wurin yadan natsu ne maigari yace wanene mijin nata cikin mamaki
Da sauri Bashir ya nuna Sheriffudeen da hannun shi,
Cikin jin kunya Sheriff ya dan noke kan shi kasa don nauyi da kunya da suka kama shi a lokacin,
Maigari yace ma wani daga cikin mutanen shi ya tashi Sheriff yadawo nan,
Kawu salihu da sauran jama,a suka dauki murna da kuma shewa kamar yadda dattawa kan yi indan sunji dadin abu,
Kawu ya ce akan zancen ta ne nazo wanan gurin yanzu wallahi alheri ne ke kirana ban sani ba,
Ai, nan da nan maigari ya nuna masu kawu a matsayin kawuna kuma uba na dan shine mai kula da duk wani lalurar mu,
Kasancewa uban mu baida rai tun muna yan kana,na,
Gaida kawu suka karayi cikin ladabi,
Wani bafade maigari ne yadaga murya sama dan sauran mutanen dake waje suji saboda leken da suke tayi ,daga waje,
Yace Allahu akabar zato ko zunubi ne danko yau Allah ya wanke yar kulu da diyar ta fadima ,
Allah yakawo mijinta uban cikin ta har gida,
Yau zargi yakare ga munahukai yan hana ruwa gudu,
Ai kafin ace kwabo wajen fadar mai gari yadauki zancen cewa mijin fadima yazo daga saudiya
Wa, Sukuma su ce kila dai sheri nayi aka biyo ni daga saudiya,
Amma ina fadima ina wa yan nan mutanen haka,
Sun dai boyene, kawai,
Kai mutum baka iya sa wallahi, sai Allah
Batare da bata lokaciba maigari yasa a,kaisu gidan mu dan su tabbatar ko ni ce,


Masu karatu nadai fada maku irin fasalin gidan mu tun farkon labarina,
Dan haka gidan mu gidan laka ne mai dauke da dakuna biyu na laka saman dakin mu jinka ne,
Gidan mu an kewaye shi da zana ne da kuma karar marasa,
Yan kayan aikin mu suna a tsakar gida gefen darni inda muke girki,
Sai yan dabbobin da inna ke kiwo a gidan raguna guda biyar da awaki sun kai hudu,
Sai kaji, da kuma tantabaru, da Abdull ke kiwon su,
Don haka da zaran ka aje wani abu yanzu kiwon nan na inna zasu far ma abin da ci ko tono,
Shiyasa bamu aje komai a fili duk cikin daki muke aje kayan mu,
Tafiya sukeyi da kafa sai jama,a dake bin su a baya mata harda leke sukeyi a darni gidan su dan ganin zahiri,
Sheriff sai waige waige yakeyi yana nazarin irin gidajen da ke gare mu a kauyen,
Yana tunane a ranshi cewa a wanan irin gidar fadima ke rayuwa aciki,,
Ganin da sukayi kawu ya nufi wani dan tsukarken gida
Wanda a,ganin su bai fi daki daya ba,don kilama ba filin gida acikin shi,
Anan kawu ya tsaya kofar gidan yana kwada sallama,
Kawune akofar gidan innar mu yana kwada sallama, Abdull da Aisha dake wasa ta tsakar gida suka amsa mai
Innar mu dake fitowa daga daki tace mai ,
Koni am shigo mana Salihu sai kace wani bako can,
Yace aida bakina muke shinassa
Bakin shim to lale marhabin da bakin mu inji inna,
Tace mai shigo dai ni,daita agidan,
Sheriff da doctor sai bashir dake bayan su duk suka kutso kai cikin gidan na inna bayan ison da Kawu yai masu,
Ganin datayi bakin sam ba suyi kama da mutanen kauyen mu ba yasa inna saurin jan zanin da ke daure a sanan wanda ta daura dama kusan da bi,ar mutanen kauye ne daura zani biyu,
Ko kuma a aza guda a saman kai
Aisha da ke ta zagayan gida wata yar akuya karama tana kora akuyar sunata faman guje guje
Daga kan da Aisha zatayi sai kuyi arba da sheriff,
Wani irin ihu tayi don gani da taima cikin mamaki tana fadin Abu,Abu,,
Ware hannayen shi yayi tafada mai ajikin shi karamar yarinyace sai kawai tasa kuka,
Duk wanda ke gurin saida hannkalin shi yatashi dan yadda Aisha ke kuka,
Daki inna tai masu shimfida, a samar wata tabarmar kaba mai ruwan ja da shudi,
Bayan fitowar mu gidan kawar Mariya bamu tsaya ko ina ba sai gida,
Abinda na dan lurada shi ,shi ne yadda yau nake samun gaisuwa ga yan kauyen mu ,
Koda ban san mutum ba zai ce min fadima ho,
Mariya ce ke cewa ingwaiyya,,
Duk da ganin mutane dani kofar mu hakan ban kawo komai a raina ba illa saurin da nakeyi kawai in shige cikin gidar mu
Kaina yana a duke har muka shige batare da na tantace ko suwaye a waje ba,
Ashe salim na kallona da shi da Almustapha acikin su,
Ganin da sukayi mun dukar da kai a kasa yasa suka kyale mu
Wai sun dauka ko al,adar garin mu ce hakana,
Uwar,Tunkiyar inna ce ke fitsari samar takalmar sheriff takalman da akalla zasu kai dubu saba,in indan ankiyasta da kudin Nigeria,
Mariya na kokarin cewa inna ga wasu mutane fa akofar gidan mu tsaye,
Sai kawai hancina ya shar min kamshin da bazan taba mance mai amfani da wanan irin turaren ba arayuwata,,

Hakalina a tashe na furta a hankali na ce Sheriff,
Sheriff mariya ta maimaita abinda nace ina mai nuna mata kofar dakin innar mu,
Ta, waiga da saurinta ta isa kofar mutum uku ne zaune sun cika muna daki da kamshi sai innar mu da ke can ta kuryan daki rusun,ne,
Cikin sauri ta isa kofar tana kokarin lekawa, cikin dakin,
Sandarewa nayi tsaye inda nake don sam bantaba zaton cewa Sheriff zai biyo ni har kauyen mu ba,,
Nadauka cewa mun rabu ke nan har abada, dashi,
Don ban zaci cewa kamar sheriff zai tsaya bata lokacin shi ga yar aiki irina ba,
Waigiwar da sukayi dan jin muryan mariya yasa su hango ne tsaye cikin mamaki,
Doctor kamal ne yai min larabci yace min inshigo, mana,
Ganin da yayi kamar ban motsi a tsayen yasa ya fadawa sheriff,
Cikin sauri duk suka nufo inda nake tsaye sandare ina dogon tunane,
Jin muryoyin su da na yi a kusa dani yasani dawowa a cikin hayaci na,
Cikin sauri sheriff ya rike min hannu na muryan shi naji gab dani ya na ce min in zauna tukun,
Zama naji bisa dan turmin dakar inna da ke kife a gefe na,
Kaina nakama jin ya na wani juya min a lokacin dan haka sai nadan dafe kan da hannu na guda,
Mariya ce tazo da saurin ta ,ta dan dafani tana fadin anty fadima may ya samay ki pls
Har yanzu na kasa magana sai ido nake dan binsu dashi cikin mamaki da fargaba,
A hankali duk suka karaso inda nake daidai lokacin innar mu tasa mariya tafito da tabarmar a waje,
Cikin damuwa nadan daga kaina da kamar wacce zatai magana sai kuma na kasa na kara dukar da kaina kasa,
Inna tace wa mariya ke maza kuna sunka taho,
Sai mariya ta washe baki saboda jin dadin zancen inna
Tace Allah mungode ma,
Da na rasa abinda zanyi sai kawai nasa masu kuka kamar yadda Aisha tayi,
Sheriff yace min cikin larabci Fatima may yasa kika barni may yasa kikai min haka,
May zai sa ki wahal da kanki da baby na,
Fatima ba kya gudun wani mugun abu yasamay a hanya
Kin ko san irin kasadar da ki kayo haba Fatima,
Sai na kara sautin kukan da nakeyi,
Sunana yakira a hankali,
Yace min ya rokeni Allah indaina wanan kukan
Kada mutane na su dauka ko wani mugun hali yake min acan,.
Yadan langabe kan shi alamar maganar shi ba wasa acinkinta,
Batare da kalle shi ba na mike a hankali da niyar in shige dakin mu,
Duk wanan drama a gaban su inna da kawu har da tumba wace ta shigo gidan da niyar gulma
Batare da yadamu da mutanen da ke wajen ba ya dan jawoni kadan zuwa jikin shi
Nai sauri na gwauce da ga rikon da yai min,
Yace haba fatima aiko doctor dai kya tsaya ku gaisa da shi ko
Ga kuma Almustapha da salim a waje har da Shehi,
Da sauri na waiga dan in gaskanta zancen shi aiko Shehi ne tare su
Suna shigowa cikin gidan mu,
Da sauri na mike zuwa wurin shehi mutumi da nake jin shi kamar mahaifina
Kuka kawai nasa mai agaban shi kamar wata yar karamar yarinya,
Yace fadima bana son inga kin kara wanan kukan ,
Ba kuka yakamata kiyi godewa Allah yakamata kiyi,
Duk yadda na so inyi shiru abin ya faskara kukan kamar kara min shi ake yi,
Nakasa yin magana dakowa daga cikin su,
Har nadan wani lokaci,
Bashir ne ya fita tare da su almustapha da salim da niyar zasu tafi cikin garin sokoto don suyi booking din hotel
Inda zasu sauka gaba dayan su, anjima, saidai sun bidi taimakon wanda zai masu jagora hakan,
Mariya ce tasa aka kira malam basiru wanda dama yana kofa atare da sauran securities din da suka zo da su,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
[12/3, 9:43 PM] ‪+234 706 078 6258‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost True Life Story,,,


Idon sheriff na ga cikin jiki na kyam don ya tabbatar
Cikin ya wani turo wa kamar wacce zata hai hu a lokacin
Duk na rasa inda zan sa kaina a wanan lokacin nauyi da kunyar bakin mu duk ya cika min ido,
Zaune nake a gefe guda duk zullumi ya cika min ciki, sai tuna ne nakeyi ya akayi suka san garin mu har suka zo,
Ganin da nayi hankalinsu na gurin masu zuwa sokoto, ana muhawaran ko wasu su tsaya nan garin ne,
Sai na mike tsaye a hankali,nadan sulala na shige cikin dakin mu,
Sheriff da duk wani tako nawa ya ga idon shi yana lura da ni,
Ganin da yayi na shige cikin dakin innar mu yasa shi,
Biyo bayana ganin mutum nayi kawai a cikin dakin
Kokarin rike ni yayi alokacin ,
Iya karfi na nasa nadan ture shi baya kadan , murmushi yadan yi min kawai
Ya ce min fadima nan fa gidan mu ne banga abinda zaisa ki kokarin hana min abin da ya halat a,kaina ba,
Ina son inji lafiyar ki ,ina son kuma inji dan dumin baby na da kika hana min ji,
Ya fadi hakan cikin muryan da dole ya ba mutum tausayi a lokacin,
Kaina nadan dukar kasa saboda na kasa hada ido da sheriff sam, duk yadda yasa mu hada ido da shi na kasa,
Ganin da yayi ba zan saurare shi ba
Yasa ya kara tausa muryan shi kasa,kasa yace min
Fadima fushin ki a gare ni yanzu tankar wani barazana ce mai kokarin rushe duk wani tubalin da zuciya ta ta gina akan ki,
Fatima banyarda da zuciya ta ba da farko sai lokacin da ki ka bar saudiya, batare da sani na ba ko wani nawa,
A lokacin nasan cewa son ki da kaunar da bi,un ki sun min illa acikin rayuwa ta,.
Fatima kin taimaki rayuwa ta fiye da duk yadda zan fada maki,
Dan zaman rayuwar da nayi da ke yasa na fahinci wasu abubuwar a zaman duniya,
Wanda ada sam ban dauke su wani abu ba can mai muhin manci a,rayuwar mutum,
Kin sadaukar da rayuwar ki akaina, kin kuma bada duk wani lokaci naki akaina,
Alkawarin da nayi a kan mace, a,da
A,yanzu duk na jaye shi araina saboda ke nagane cewa mata suna suka tara,
Fatima ki sani duk wani abinda da namiji zai bukata a gun mace kin tara su a yanzu kyau ,hali, ilimi,
Duk Allah ya baki su a lokaci guda , taya,ya kike ganin zanyi sakaci da kuma sa,ar da Allah yabani akan ki ya wuce a banza,
Yazama wajibi a gare ni duk inda kika shiga cikin wanan duniyar in bideki ,
Banyi aune ba saiga namijin duniya kamar sheriff mai jin kan sa wanda yasha gwagwal maya da larabawa kala,kala da turawa har ma yan china,
Mutum mai ji da kansa ya zube min a gabana gwiwa biyu, biyu,
Yana kuka a gaban yar karamar yariya kuma cikin dakin uwa ta, a cikin ginan laka,
Ban san lokacin da na mike tsaye da sauri na tallabo shi tsaye ba
Saboda sanin dani kowaye sheriff da kuma sanin darajan shi a idon al,uma,
Ban san lokacin da na kankame shi ba ina mai kuka cikin sauti mai ban tausayi nace mai ,
Daraja ta da kimata bai kai har ya rusun na min ba kada ya manta da cewa ni ce fadimar nan yar aikin gidan shi har yau,
Hannu yasa kafin in fadi wani kalma ya toshe min baki na yace daraja na da kima na tun farko yafi karfi yar aki a gare shi,
A yar uwa yadauke ni, ba yar aiki ba ko da can,
Shigowar mariya dakin yasa mu ka dan jaye jiki a na juna badon naso ba ni ma,,

Sai alokacin yake ma mariya magana cikin harshen turanci saboda ba hausa sheriff ya iya ba sosai daga harshen su na kanuri sai ko turan ci sai kuma idan yaci sa,a mutum najin larabci harshen da ta zauna mai a baki daram kamar itace yaren shi ta gado,
Murmushi mariya tayi mai tana dan bashi ansa a cikin dan turacin ta wanda bai nuna ba,
Lokacin sallah magrib da yagabato ne yasa shi fita daga dakin na inna,
Din shi duk abinda yake yi hankalin shi na ga ibadar shi,
Sai bayan fitan su sheriff ne wanda kamar bai fita ba saboda kamshin da suka bar muna acikin gida
Inna ta samu yi min magana,
Tace min fadima kada kiyi wasa da damar da Allah ubangiji ya baki akan rayuwar ki,
Naga kamar shedan nason ya rude ki kiwa wanan bawan Allah wulakanci,
Duk da ban san komay yahadaki da shi ba ina mai kara horon ki a rayuwa da kizama mai hakkuri da yafiye, aduk al,amari,
Taci gabada fadin fadima idan har kinyi fushi dashi banga amfanin
Lokacin da na kwashe wurin koyar da ku tarbiya mai inganci,
Nace inna aiba fushi nakeyi dashi ba ,
Tace fushi kikeyi mana tunda baki yi dibaiyar cewa sun fito daga wata uwar duniya zuwa nan gurin ki ba,
Ai da kamata yayi a ce kin tare su da hannu bi,biyu tunda har suka zo mahaifar ki,
Ba saboda komai ba sai saboda darajar ki,
Ga alama fa bake ka daice a gurin shi ba kamar yana da wata matar,
Amma ya iya biyo ki har kauyen ki kuma yazo batare da yanuna muna wani kyama ba ko raina kama,
Tace mu mata sauda dama muna wasa da damar da Allah ya ba mu gurin nuna jayayya da hukuncin ubangin

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment