Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gari da ciwon kai na tashi sosai saboda kukan da nasha yin nin jiya din,
Nice kullun mai kokarin tashi don inga an yi duk wani aiki da yakamata ayi da safen,
Jinda kowa yayi shiru yau gidan ba motsi na ba a,lamana sam
Yasa wasu daga cikin yan gidan namu fito,
Ciki harda Amal da Salim ,
Don Amal tun asuba ta koma dakinta ta kara gyara kwanciyar ta,
A falo Salim ya tsaya ganin cewa rana yadan yi saboda zuwan mu asibiti wurin ummi, gashi almost to time,
Amal ce takware da nake ciki yadda ta gani cikin bargon yadan bata tsoro,
Kwance nake ina rawan sanyi, ga wahaye tab ga ido na
Aisha na gefe na zaune tana kallo na ina jin lokacin da ta tashi tana ta dan jijigani cikin bargon
Tana cikin hakane sai ga Amal Allah ya kawo muna don ban iya dagawa sam wlh,,
Da sauri taje ta kira Sheriff wanda suka hadu yana shirin saukowa kasa ,, Dakin da nake suka nufa duk kan su hankali ta she,
Yana kallo na a yasan cewa har da fever ya kamani,
Ina nan dunkule sai kuma naji amai na shirin kamani,,
Da sauri suka taimaka min zuwa wurin mota, sai makyarkytan sanyi nakeyi,
Ina dunkulewa,wuri guda
Muna isa asibiti aka wurin doctor kamal abokin shi ya kai mu,
Ina ji lokacin da sheriff ke ma doctor bayanin komai tamkar nice ke bayani,
Bayan an rubuta magani ya kasan ce har da allura za ai min guda,
Aiko nan muka kwashe ta da nurse din don naki bari taimin Allura sam
Sheriff yasa Amal ta rike ni gam ina ta tsala ihu ina fadin Anna tazza habb
Suna waje suna ji na dagashi har Salim din murmushi suke yi suna min dariya,
Ina fitowa ina dan share hawaye na,muka hada ido da Salim da shi ,sai duk suka kwashe da dariya,
Hararan Salim din nadan yi tare da turo baki alamar jin haushin su,,,
Gida aka dawo dani saboda yau badamar zuwa asibitin da ummi ta ke nima ina fama da kaina,,,,
Barci mai nauyi ya dau ke ni bani na farka ba sai daidai lokacin sallah azahar
Duk da nauyin da jikina yai min bai hana ni tashi zuwa don inyi sallah ba
Abinda nagani yasani mamaki so sai don koda ake ma doctor bayanin abin da yasamay ni ban. dago cewa sing of period sheriff ke bayani ba don yanzu nadan rage yawan ciwon mara kadan bakamar da ba,
Don duk wani abu mai zaki na rage shan shi yanzu saboda irin wahalan da nakeyi,
Jiki ba kwari nadawo nakara nadewa saman gado, ,,,,,

Allah ya sa na dan ji saukin jiki na so sai har ina dan yin aiyukana na cikin gida
Yau ne muke sa ranan za,a sallamo ummi daga asibiti
Saboda samun saukin da tayi sosai jikin ta ya komal normal tasa mu lafiya,
Duk wanda ke gidan yazo taron ummi da dawo, anayi mata barka da arziki ,,,,,
Zaune kowa yake a falon anata nuna farin ciki muko sai zirga zirgan hada masu abincin lunching mukeyi don bayan azahar ne suka dawo gidan
Nafisa ce zance kusan karshen zuwa tariyan ummin wace tafito cikin kasaita da isa,
Batare da ko wani dar ba tasamu daya daga cikin kujerun ta zauna,
Sanan takewa ummin gaisuwa,
Daga haka mikewa kaiwai t ta koma dakin ta tana tafiya tana wani juya kwan kwaso, ta da karfin dole,
Ido kowa dake falon yabita da shi da mamaki irin hali ta na ko in kula da takewa ummi
Mudai ba musan cewa ita din yar uwar hjy mama bace balle mu fasara zance da wani manufa
Iya kadai muna ganin rashin tarbiyanta da kuma nuna wulakanci ga kowa,
Muryan Amal ce ke fadin dama hjy tsohuwa ta fadi gashi ko ya bayyana
Jinin su hjy mams ba jinin alheri bane tasan cewa wahala kawai aka hada yayan su dashi,,
A cewar ta wanan aida ta samu wuri da tafi hjy mama iya sheri,
Dadin abin yayan su ne bai bata wuri ba,,,
Ummi ce ta kwabe Amal din da fadin ta dai sa ido ga abinda bai shafe ta ba,
Sheriff na jin duk abinda Amal ke fadi dakuma kwabeta da ummi tayi baice komai,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
24/10/2017, 1:50:14 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣2⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

Almost true life story


🎁 *NASIBI* *WRITERS ASOCIATION*🎁

N 🎁 W 🎁 A

Dawowan Ummi gida da kwana biyu muka lunch zuwa sabongidan gaba daya gidan har hjy mu,
Saidai gaskiya wanan gidan yafi karfin wan,can tsoho gidan sosai gida wanda bazan tsaya maku bayanin shi ba, don girman shi,
Haka kuma naji yana waya akan wani gida daya saye a Abuja Nigeria inda naji yana cewa zaizo yagani kwanan nan,
Allah ya nufa da ummi za ai wanan shagalin komawar,
A ciki muka fara azumin watan Ramadan company su yafara aiki sosai a kasar wanda Allah ya basu nasaran samun kwastamas ta ko ina afadin kasar
Abinci sosai ake yi na bada karama wata katuwar mota ce ake wa loading abincin buda baki mai dadi, akai bakin haram aje anabadawa hade da abin sha ruwa da lemon kwanko da dabino,

Wani irin shakuwa da aminci mukeyi tsakanin nida Amal da salim,
Kusan ko yaushe idan ba aiki nakeyi ba zaka samay mu tare,
Muna hira ina koya mata larabci ko kuma muna karatun novel na hausa da tazo da shi,
Ummi na jin dadin zama dani kamar yadda nake nin dadin zama dasu.
Shehi yaso ya koma gida amma Sheriff ya hana acewan sheriff din ya tsaya yayi umurah tukun sanan ya tafi,
Inda ya aika wa sauran iyalan she da abin azumi batare da sanin shehi din ba,
Bashir yaba yakai masu duk yan uwa nagari Auno din sun samu wanan kyautar daga dansu jikan su Ahmad,wanda suke kira da baba karami,
Sai bayan kwana biyu iyalan malam Shehi,suka kira Shehi din a waya suna mai godyan kudin da yaturo masu,
Cikin mamaki shehin yace masu gaskiya bashi bane,
Saida uwargidan shehi tace bashir ne yakawo masu shine Shehi yagane cewa Ahmad ne ya masu aike,
Da safe Sheriff zaiyi tafiya zuwa yamal ,
Da sallama yashiga bangare da su ummi suke inda ya samay su zaune suna lazimi ,
Ya gaishe su cikin girmamawa da ladabi, ya juya gurin ummi yana tambayar ta lafiyan jikin ta,
Muryan shehi ce ta katse mai maganar da yakeyi da ummi din
Dai lokacin nagama hadawa ummi abincin da zatayi break tasha maganin ta,
Kasancewa rashin lafiyan ta baibari tayi azumi,
Likitoci sun hanna ta yin azumi saboda ulcer fa yai mata yawa, da ita da hjy mu ce basu azumi tare nake shiga kitchen in hada masu abinci.
Shehin yace hakika Ahmad kakai yadda ake duk wani mumini yakai ,
Musan man wurin kyautata wa yan uwa,
Kayi koyi da yadda hadisin mazon rahama yazo muna,
Akan idan zamu yi alheri muyi shi batare da hannu hagun mu yasan hannun daman mu yabayar da alheri ba,
Banda abinda zance sai dai in kara gode ma bisa ga alherin da kaiwa iyali har mada yan uwana,
Hakika da kai da mahaifiyar ka ku alheri ne gare ni,
Fatana gare ka shine Allah yabaka zuri,a masu albarka wa yanda zasu gado halin ka,
Saidai gaskiya wani hanzari ba gudu ba shine,
Sai shehi din yadan yi shiru kadan kamar kalman da taye son furtawa tana da nauyi,
Lokacin kuma nagama hada ma ummi abinci a gabanta,
Namike da niyar barin dakin sai naji muryan ummi nace min dan tsaya in bude mata drink din dana aje mata,
Kallona sheriff din yayi shima ahankali yakali kwankon lemon da ke gaban ummi,
Shehi yacigaba da fadin gaskiya kana bukatar kara iyali Ahmad,
Ahmad din da kanshi ke duke saida yadan daga yakali shehi din,
Shehi yakada mai kai alamar kware kuwa, saboda nan gaba akwai matsala inhar bakayi hakan ba,
Kai baba shehi kenan wanan din ma yayana iya da ita balle inkara jajibo wa kaina wani ma tsala,
Murmushi shehi din yakara yi yace zakayi ne Ahamad ko ba shiri idan har lokacin karawan yayi,
Da haka sukayi sallama yatafi yamal diba wani company tatar mai mallakin gwaunatin kasar saudiya da ya samu matsala ya tsaya
Zaije yada da sauran abokan aikin shi su tafi,

Muna ganin Sheriff yai tafiya ,muka yi shawaran zuwa zaga gari,
Nida su Amal naima driver da nake fita dashi sayayya magana akan zai kai mu unguwa, washe gari,
Sai da zamu fita nake fada wa ummi cewa zamu dan fita don suga gari,
Tace muna kada mu dade saboda ba sanin garin mukayi ba,
Dariya kawai nayi don nasan guri guda gudane ban sani ba,indai har idon garine,
Don ba inda bamuje yawon bara ba, a garin,
Cikin shirin mu ta alfar ma muka fito inda koni shigar tawa tabani sha,awa sosai,
Wata doguwar rigace ta larabawan Jordan nasa,ban taba sa waba,,, Rigar nafisa ce dayaje Dubai kwanaki yasayo mata ,
Tun nan inda yaba ta tajefo min tace batasa irin shi ita,
Itama Amal shigarta yai mata kyau sosai
Mun hade da Salim a gurin mota, har mun zauna driver zai tada mota sai ga nafisa da saurinta,
Wai mu fito zata fitane itama,
Nidai ina baya ina jin su har ina shirin balle murfin mota in fita Amal ta hana ni
Salim dake ta gaban mota ne yace mata sai kiyi hakkuri idan mun dawo kyatafi,
Yace ma driver ya mota mu wuce muna jinta tana ta haushi kamar wata tababiya
Har mukabar gidan suna mata dariya kamar mahaukaciya,

Munje gurare da dama agarin na nuna masu gurare tarihi sosai,
Sai kuma wasu shagunan kaya da muka ziyar ta, da gurare saida kayan abin motsa baki,.
Amal duk ta rude sosai dagani wani katon shago na saida kayan sawa na mata da yara,
Saida naga tagama rudewa ina mata dariya, daga karshe nake fada masu cewa ai shagon Sheriff ne ,.
Na nuna masu wani na saida kayan maza dasu carpet din sallah iri iri
Baki suka sake suna mamaki har cikin mota suna kara tambayana nace masu wlh nashi ne,
Wasu manyan motoci da sukayo loading mutane wanda da,alama baki isowar su kenan motar naga tana ta kallo har tana waige,
Nace mata ai indai wanan garin ne kada kiyi mamaki darin su sushigo kamar haka,
Nace mata gari ne da zaki ga taron bil,adam kamar duk duniya aka tara tundai ranan jumma, ranan da duk yan kauye da kewaye sun shigo ga baki sai kiga garin yazama kamar ba ko isakan shaka,,
Duk da dare yayi saida nakai su wasu shaguna dake cikin kasa inda shagunane sunfi guda dari akarkashi kasa akajera su birjit,
Shagon saida zinare dayafi kowani girma wurin nakaita,
Saida Amal tace min don Allaj fadima mu fita haka sanyin wurin nan ma yai min yawa ga girman wanan shago kada yasani mafarki pls,

Har muka isa gida tana santin shagunar da duk mukaje,
A bakin get mukayi tozali da sheriff wanda yafito da niyar zuwa masallaci sallah cikin jallabiya baka , mai dogon hannu kan shi da "yar fula karama fara, sai Almustapha dake gefen shi shima cikin farar jallabiya,
Tunda na hangoshi sai naji gabana yafadi don musan cewa bayau ne zai dawo ba, sai zuwa jibi,
Kamar munafukai muka fito motar muna dan nonokewa ,
Duk da yagane nufin mu bai ce muna kowulakan ,
Salim ya kalla yace mai ya harama zuwa sallah kafin ata da jam,i,
Muna shiga gida har mun manta da zancen nafisa ashe ita tana nan tana ta hauka tun wucewar mu,
Akan dole sai an dauki mataki akan mu tunda munyi mata wulakan
Masifa take tayi yasa ginan gida jen su ba irin namu na Nigeria bane,
Balle wani yaji yadda take masifa ,saboda su ba halin su bane,
Ina dakina bayan mun idar da duk sallolin mu sai natashi ,ina cire kayan da sa ajikina ji kawai nayi ambankado min kofa da karfi
Najuyo don ganin kowaye yai min wanan irin shigar daki,
Allah yasa ban cire riga ba nadai cire dan kwali da su yan kunneya na,
Nafisace tsaye tana wani irin haki gyalenta a hannu ta rike shi don masifa,
Tana batun finciko ni taji anjata baya da karfi ko da ta waiga saitaga sheriff ne ,wanda dawo wanshi kenan daga masallaci , zai shigo yaga wulgawanta ,zuwa sashen mu,
Sanin halinta dayayi yasa shi biyo ta yaga ina zata,
Ganin da yayi dakina ta dosa yasa shi biyo ta har ciki, ganin yaje yeta yasa tafara
Ai ko sai tahaudura min ashar ,bakar Ashar,
Takara yo wa kaina gadan gadan, hakan yasa na boye bayan sheriff din wanda bakin ciki ya hashi yin ko yin magana
Ganin da yayi cewa bazata fita dakin ba shikuma mutum ne wanda baison fitina
Hannu na yaja zuwa waje, muka barta can dakin,
Aiko saita sa kuka wi wi, wai ya wulakanta ta saboda yar aiki,


Tundaga ranan sheriff ya hanani duk wani aiki da yashafe fan,nin nafisa tunda tace sai ta halakani,
Hakuri Shehi yaba shi so sai tare kara mai karfin gwaiwa, akan ya jure,
Wanan fitinar da NAFISA tayi yasa muka sake jiki ga fadan da muke tsan mani gurin she,

Koda yaushe Amal tana bani labarin Nigeria dakuma labarin yan makaran tar su da sukayi karatu tare,
Ina jin dadi wanan labari sosai ,
Idan tana bani sai in yi kwance in yi shiru ina saurare ta gama yanzu da banda wani aiki sosai a gida sai aikin ummi,
Can mukan zauna muyi ta hirar mu,
Har kusan lokacin shan ruwa sanan indan fito inyi aikina,
Aikin yanzu baida wani yawa kamar da iyakata kula da masu ayukan gidan,
Saikuma in dan zagaya inga abinda yadace ayi ma ma,aikata,

Azumi na Ashirin baba Shehi yai haramar komawa gida don sallah wurin sauran iyalin shi,
Shirye shiye sosai a,kayi mai ,
Ummi tatura mu munje munyi wa yan uwarta sayyaya sosai
Jin da nayi ance hjy tsohuwa guri guda take da su, baba shehi yasa naje nasiyo mata maganin ciwon kafa da kuma magani ciwon ido,
Naba baba shehi yakai mata cikon kayan da na hada naga Amal ta jefa wasika tace akaiwa hjy tsohuwa,
Ana gobe malam zai wuce nashiga dakin su inkai wa ummi fruit sald kafin ta kwanta
Sai na iske malam she da yaran shi Amal da Salim, yana basu wani dan abu suna lasawa,
Har na juya zan fita yace min yaki "yata sai na dawo nasamu gefe nadan tsuguna daidai saitin da Amal take yace min indawo
Ni abinda tabasu yadibo ya bani in lasa,
Na lasa yace min in miko mai hannuwa na na mika mai yakama hannu na dama ya murza min wani abu fari kamar takarda sai naga abin yashige min a jiki,
Inata juya hannu ko zan gashi banga abinba yabi lafiyan jiki,
Karshe yace min intashi in tafi Allah ya tsare masu mu mukace Ameen gabadayan mu,
Washegari malam shehi yawuce yabar mu da kewan shi sosai,
Dattijo mai dadin sha anni, dakuma fadin gaskiya,

Saura kwana biyar sallah da dare har na kwanta sheriff yace akirani a falo nasa may shi yace min gobe in shirya in raka Amal madina kuma ga goben zamu dawo,
Sanin da nayi tsakanin Makkah da madina akwai nisa sosai yasa nadaga kai na kalle shi sai yace inda bamu gama bada wuri zamu iya kwana har jibi in sun gama mudawo,
San mako mukayi tunda safe muka kana hanyar madina,
Amal ta dauka ai ba wani tafiya bane mai nisa sai taga har ana batun marance bamu isa ba, nan ta waigo inda nake ta kallon dogon dajin da ma,aiki manzon Allah SAW sukayi tafiya hijira saman rakumai daga makkah zuwa madina,
Gaskiya mu munzo cikin musulunci mai dadi dibafa a mota muke ta tafiya haka amma bamu kai ba,,,,,
Amal ce ke ce min fadima har yanzu nace mata saura kadan insha Allah,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
24/10/2017, 1:50:16 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP ND NASIBI GROUP🐎
🎁 *NASIBI WRITERS ASSOCIATION* 🎁
🎁N🎁W🎁A

Ku _yi Afuwa arayuwan ku
Kuyi sasauci ,arayuwa,ku
Ku yawaita murmushi da godiya ga dan uwan,
Sadaka na kariya sosai ga bawa ranan tsayuwa jiran hisabi,
Allah yasa mudace,

Yan huguma group ban taba mantawa da ku ban manta alherin ku gare ni,
Nagode Nagode Nagode

Almost true life story,,,


Gab da sallah la,asar muka shiga garin na madina garin da duk duniya babu inda takaita gaskiya da son jama,a garin mutanen kirki ga mutunci, garin da ba ruwan ko da sa ido ko hassada ga dan uwa,

Cikim larabci nai ma driver mu yusuf magana nace ya wuce damu direct mai kai gaisuwa mu kuma kwaso lada tunda
Mun makara nasan cewa baza su samu yin abinda yakawo su ba yau sai gobe,
Don haka goben ba,la,lai bane musa mu zuwa da wuri kafin mu wuce,
Saboda nasan cewa madina bakamar garin makkah bace gari da komai acikin natsuwa akeyin shi,
Al,umman garin madina daban suke da sauran mutanen garuruwan su maci kusa,
Karfe goma anrufe massalaci Annabin rahama ba,a bari kowa ya kwana acikin shi,
Bakamar masallacin makkah bane da wasu ma anan masaukin su yake,
Nan suke kwana suke komai,
Iyaka sai in anzo shara su dan kwashe kayan su su a,gyara wuri sai su dawi
A gaskiya koda banda wayo nasan cewa kasar saudiya kasa ce mai albarka da hakkuri da jama,a,
Duk yadda mutum yake suna hakkuri da shi indai har ibada kaje yi,
Ba irim mu takari masu zuwa da wani manufa ba na dan ban don tara dukiyar duniya,

Saida muka kusa isa kusa da massalacin na juya nai ma su Amal da Salim bayanin abin da nagaya wa driver ,
Suma suka ce gaskiyane, nai ma Yusuf driver magana don Allah yayi kokari yakai Salim wurin ziyara manzon rahama idan an, sallamay sallah nafada mai duk yadda zai yi,
Cikin dauki Salim ya bar mu ya matsu su shige,
Saboda gajiyar da muke da shi,
Bayi muka fara shiga muka dan gyara jikin sanan muka dauro Alwala muka fito,
Duk da wurin ya cika tab da jama,a tun awajen baisa mun tsaya wajen ba ciki na rikewa Amal hannu muka kutsa Allah ya taimake mu muka samu wuri kusa da wasu yan tsufi mutum biyu mata, mutanen Indonesia
Muna zama yar tsuhuwar guda ta gyara muna wuri muka zauna gab da su jiran afara sallah gudan ce ta miko muna hannuta guda da baida tasbaha muyi mu,sabi,a da ita,
Bayan an salamay tsuhuwar guda tace muna mudan taimaka masu suna son suyi ziyara kada a matse su a gurin,
Tare muka jera da su har cikin Rauda, kusatawa naitayi cikin jama,a har bisa green carpet din nan da akace shine saitin kabarin Annabi yake,
Dole nice na tsaya masu suka samu sukayi sallah raka,a biyu sukayi gaisuwa ga maikin Allah tare da sahabban shi guda biyu da aka rufe su kusa da kusa,
Sanan na samu nima nabi ayarin wasu yan Syrian nayi nawa raka,a biyun na addu,a
Batare da bata lokaci ba na jawo yan tsuffin nan da Amal mukayi Exist kafin akore mu,
Anan muka sha ruwa mukayi buda baki dayake watan azumi ne bamuyi wahalan sayen abinci ba ga karama nan kalakala ana bi layi layi ana ajewa sadaka saboda Allah da Annabi batare da kasan kowa yakawo ba,,,
Sai bayan sallah isha,i muka, bar masallaci zuwa masaukin mu,
Dayake nasan gidan sai nai gaba wurin nuna masu, kowani sashi,
Kafin mu kwanta muna dan hira mu a falon gidan wayata na gefe wacce bata da wani amfani inba game ba dom nasan cewa banda labar kowa da zakira,
Shine samu yafi iyawa, gadai waya dankareriya amma ba lambar kira saidai gamen da sauran abubuwa,
Cikin ikon Allah wai yau wayan itace tayi kara alamar ana kirana,
Salim ne yace kirana akeyi nace mai, a,a bakira bane,
Yace to may nace mai oho,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment