Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

runguma junar
Wani irin dadi Ahmad din ke ji azuviyar shi ganin yau dsn uwsn shi yakawo mai ziyar a inda yake
Ai Suraj bai rude ba sai da yaga irin gidan da suka tunkara wanda ake nufin cewa , wai Ahmad ne, ya mallaka, shi,
Wani irin dan huci yayi mai fidda iskan zafi abaki saida kusan kowa na motar yaji shi,
Sai yadan basar da cewa duk gajiya ce saboda yafito nisa,
Sai cikin dare suka karaso gidan don haka ni koda suka isa har na kwanta barci, abina,
Saboda ina tashi da wuri yin aiki safe, shiyasa na saba da kwanci da wuri,
Wani bangare guda na gidan aka ware mai inda akaimai masauki ke nan,
Maman su umar ce ta gabatar masu da abinci
Kasancewar tana da kula da aikinta ga tsabta ga iya girki kamar na wani gidan saida abinci,

Na shirya komai nawa har na Aisha sai dan abin da ba, arasa ba kawai nabari adakin namu,
Da safe ma saida na hada ma sheriff komai yadda nasaba sanan na wuce don inyi wanka in shirya,
Dogom riga na sa yau pink kalar ta amshe ni sosai, ajikina,
Ina kokarim daura dan kwalina naji intercoms din dakina yai kara alamar kira daga falo,
Cikin sauri nafito dan in ansa kiran oga na sheriffudeen Ahmad,
Zaune suke su biyo a dining table din suna kokarin fara bude abincin
Saida nagan su su biyu sanan natuna cewa ai yana da bako
Gashi kuma abincin shi, shi kadai na aje agurin table din,
Cikin ladabi na iso tare da sallama na,
Sheriff din wanda kanshi ke din ban kasa yadago daniyar yimin bayanin in karo masu plates da spoon,
Sai idon shi ya caraf ga irin kwaliyar da nayi yau din,
Cikin mamaki da kuma shauki yake min maganar cikin harshen larabci,
Yace min bansan yai bako bane nakawo mai abinci kamar shi kadai,
Nace ma la, agaskiya ban sani ba saidai ina mai neman afuwan gare,.
Saida ya dan lunshe idon shi kadan yace min ba matsala ina iya zuwa in karo masu ,
Shi ko bakon jin muryan dayayi kamar s,na busa sarewa yasa shi dan waigowa,
Sai yaga wata yar sabuwa mata shiyar budurwa ce ke tsaye a bayan shi tana wanan zazakar muryan,
Ganin da yayi suraj yadan bini da kallo yasa shi ce min inbar shi kawai zasu yi manage da wanan na gaban su,
Ban karasa fita ba itama Amal tashi dining erea, din cikin shiga ta kamala,
Azuciyar suraj yace kai Ahmad din ya hada kyawawan yan mata haka may su keyi agidan ne wai,
Jindayayi Amal na magana cikin harshen kanuri yasa shi budar baki da mamaki yana kallonta, sai ya hango dan kama da tayi da mahaifiyar Ahmad yagana,
To ita kuma waccan ta farkon fa ,hakan yai daidai da kara waigawa dayayi yana kallon hayar kofan da nab
Sheriff ya kula da shi sarai shiyasa ya canza shawara koda zu,
Saima ya tuna cewa ai yau zasu wuce madina abinsu,
Don haka sai yai bar wanan zancan zucin da yake,
Suka hauhirar yaushe rabo
Suna gamawa sukaje gurin ummi don ya gashe ta
Ummi tayi farin cikin zuwa ziyarar dan uwan shi dayayu, tundaga kasar turai har nan
Bai ai,wani dadewa ba salim ,yasa kowan mu fitowa da kayan shi don Aloda a motar da zamuyi tafiyar da ita,
Wata yar far mota ce ake ta loader kayan mu a cikin, wace da alama da ita zamuyi tafiyar,
Kowan mu yafito cikin, shiri shi, gun ,hajiyar mu na nufa don mu bankwana da ita,
Allah yagani banso wucewa inbarta ba saiga shi itace ma ta kara min kwarin gwiwa akan in tafi in yo karatuna watara zai amfane ni ne,

Ganin da suraj yayi munfito ana muna rakiya yasa shi tambayar ko ina zamu haka na
Atakaice yabashi ansa da fadin madina,
Yakara tambayar shi may yasa bazami bi jirgi ba
Yace mai ai jirgi bai shigowa garin makka, sai dai sauran garuruwan dake gefen makka,
Wata tambayar yakara watso mai saboda may jirgi bai zuwa,
Dan murmushi sheriff yai mai yabashi ansa atakaice da cewa Ka,abah,,,
Ganin da sheriff yayi muna kokarin shiga motar yasa shi saurin karaso wa wurin mu duk da Almustapha ya yi a ranging din mu yadda yakamta, amma saida yasa aka maida umar wurin salim dake gabar motar tare da yusuf driver,,,,
Daidai motar zata tashi kowa na daga muna hannu mukayi ido biyu da ni da sheriff wanda naga bakin shi na motsi yana fadar wata kalma da ban gane ba,,,
Da sauri na kauda idona cikin nashi wanda hakan yadan sashi wata makalalan dariya,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎






✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁
🎁N🎁W🎁A

Almost true life story,,,,,,

Haka motar mu ta harba saman titin hanyar garin madina,
Tafiyane mai tsawo a gaban mu, saboda ba wani gari maidan girma da mutum zai gani ko ya ce zai dan yada zango,
Gidan larabawan kauye ne jefi jefi a cikin dajin,
Danjin wanda babu yalwan manyan itatuwa sai dai tsaunika madai daita da zakai ta gani,
Mun dan yi nisa sosai dagarin makkah duk zukatan mu badadi sam
Ina tunanen hajiyar mu ne koda yake nasan cewa Yumma zata kula da ita sosai
Muryam salim naji yana cewa wai shi wanan ta ina yafito yazo muna nan ne,
Amal da tadan kai kwance daga bayan motar, ta dan jingina jikin ta a sit din motar
Tace yazo gurin dan uwan shi ne mana, tunda kasan dole suyi zumunci tsakanin su,
Salim yace nikan duk ban yarda da yaran mama wlh don suna iya yin komai ga yayan mu,
Ina jinsu sai alokacin nadan yi magana nace ma su au
Wanadin dan uwan Sheriff ne, aiko naga kamar suna da dan kama da junan su,
Saidai sheriff yadan fishi tsayi da fari ko,
Salim ya ce kai basu da wani kama a ko kadan, ai shi Yayan mu duk kawu ya kwaso,
Suko sun biyo mahaifiyar su ce inaga tundai yanayin jikin su yanada kama,
Haka sukayi ta zancen su muba jin su har suka gaji sukayi shiru, don kan su,,,
Bayan isan mu ne mukasan cewa an canza muna gida,
Ida muke zaton zamu zauna ashe ba a nan bane,
Munyi farin ciki sosai na ganin irin gidan da aka kama muna,
Afalo muka zube gaba dayan mu,
Salim ne yace bari ya, tashi yadan zagaya gidan, don yaga dakin da zai dauka,
Kafin yatashi ne Yusuf driver ke mai bayanin akan dakunan,
Yace sheriff yai mai bayanin inda dakin kowan nen mu yake,
Dani da Amal dakin mu kusa da na juna ne, sai maman su umar dake can ta bayan mu kadan kusa da kitchen,
Salim da Yusuf driver mu nasu bangaren daban mai kama da namu side din
Suna ta farkon shigowa cikin gidan ne su,
Komaimirrow agidan ba wanin abinda zamu ce mun bukata na zamani,
Maman Umar bata da sanyin jiki muna zuwa bata bi ta gajiyan da muke dashi ba
Kitchen ta fada ta dafa muna abinci mai saukin sarafawa,
Daga nan kowan mu ya fada dakin shi don gyara inda zamu zauna,
Dakin bai bukatar wani gyara komai neat ne, akwai gado da mirrow sai wardrobe , sai tv da dan karamin fridge, dake dauke da kayan sanyi,

Washe gari tunda safe muka shirya saboda yaune, zamu fara shiga lectures,
Makarantar babba ce ita jami a mafi girma agarin madina,
Bamu samu wani matsalaba wurin gudanar da komai,

Ahakana mika dinga karatun ba kama hannun yaro,
Muna samun kula sosai ga sauran yan uwan mu dalibai don ganin da suke muna cikin shigar mutunci koyaushe,
Sannu sannu na fara fice a department din mu kowa yasan da ni,, koya malami yakoyar dani insha Allah zan hadace shi akaina,
Wanan kokarin yasa nadan fara fice sosai ga kawaye na,
Mun hadu da yan Nigeria can da dama , suma sunzo karatune kawai,
Akwai wata Salimat yar kano damukr yawan hadewa wurin karatun mu da ita,
Saidai ayadda na fahinta ita matar aure ce, don ba yarinya bace,
Dafarko salimat bata kulani amma ganin da tayi inada kwazo sosai yasa ta dan sake jiki dani,
Hakan yasamo asaline watarana da akai muna test bata zo ba sai na kokarta nai mata,
Kafin in mata saida nasha wuya aranan don da kyat nasamu information nata,
Bata shigo school ba sai bayan kwana biyu ,Ashe bata da lafiya newai kuma tarasa wanda zata aiko,
Abin mamaki saida akazo rabon test din sai taga ai har da ita kuma abu guda muka samu,
Ina can gefe ban ko kali gefen da take ba na,
Ina karatuna sai ganin ta nayi gaba ta dafa fan table din dake gabana tana mai yi min sallama,
Ahankali nadago kai na kalle ta ina mai ansa mata sallamata
Sai take ce min tazo ne taimin godiya don tasan cewa duk wanda ke wanan ajin na computer science ba wanda zai iya taimaka mata bayan ni,
Naso in boye mata cewa bani bace nai mata amma ina sai tace min,
Ba yauba ina lura dake kina da hakkuri da sanin yakamata,
Nimatar aure ce mijina ya hanani hulda dakowa don gudun gurbatar tarbiya,
Shiyasa kikaga ban kula kowa acinkin wanan department din na mu
Don gudun saba ma Kama train da tadauka kafin tazo, amma inyi hakkuri zatayi wa mijin ta bayani komai gamay dani
Tundaga wanan lokacin muka yi sabo da salimat sosai,
Inda nagane cewa ita kadai ke zaune a gidan ta, karatu yakawo ta madina ,
Mijin ta yana Nigeria da zama,,salimat tana da kishiya a Nigeria wace nake gani kamar yar kasuwa ce tana kano to Dubai,
Nafahinci hakane indan suna waya da mijin in ta tambaye shi yara da maman su sai yace ai ta tafi dubai. Koyace ai tadawo rana kaza,

Karatun da mukeyi bai hana mu yin ibadar mu ba, don kusan kulun muna zuwa sallah a haram , saidai ba kowani lokaci ba,
Amma sallar ranan jumma,a bata wuce mu sam,
Saboda itace ranan weekend muna zama tun safe har dare acan
Ranan alhamis mukan taya maman umar gyaran gida da sauran aiki gida da ya kamata
Idan mundawo wani lokaci mukan dan zauna da maman Umar mudanyi hira kokuma in koya ma su Umar da Aisha karatu,,,
Kusan watan mu guda a madina, Sheriff din mu yazo ziyar mu, tare da ummi da hajiyan mu,
Munji dadin wanan ziyar so sai don ji mukayi kamar mun kai shekara bamu gansuba,
Koda suka iso bani gida mun fita dani da Aisha, munje wurin gyaran kai ,
Wurin baida wani nisa da gidan mu sosai don haka da kafa muka tako dazamu dawo,
Waje nasamu sheriff shida,Almustapha, yana waya a,lokacin,
Tunda na bude gida zan shigo idon shi ke akaina, nima ganin da nai masu na bazata yasani mamaki,
Cikin fara,a na isa gurin su ina masu sannu da zuwa,
Kamar yadda yake ansa min a dakile yau din ma hakane,
Cikin zuciyar shi kuma sai mamaki yakeyi, may yarinyar ga ke ci haka tawai wanan girman cikin lokaci guda,
Anyako madai tana karatun kuwa kodai jin dadinta kawai takeyi abinta sai kuma wata zuciya tace mata a,a ina bayazatayi hakana ba don yasan ni da kokari sosai,
Balle ma yasancewa ina son karatu sosai arayuwa na,
Muryan mustapha ce takatse mai tunanen shi inda mustaphan ke ce min ina mukafito haka,
Nikuma ina washe bakin murnan ganin shi,nace mai ai,nafito can wurin gyaran kaine, nida Aishan
Azuciyar shi yace badai tsafta ba kan wanan yarinyar akawai kulada kai,
Ciko na shiga inda yabi bayana da kallo da sauri ya kauda kanshi don gudun yin sabo,
Saboda wani irin mugun girma yaga nayi mai lokaci guda, saida gaban shi yafadi,
Inashiga cikin gida, kuma nai arba da ummi da hajiyar mu zaune a falon mu,
Da dan ihu na, naRugumay su ina murna,na daidai lokacin shima sheriff ya shigo cikin gidan
Saida nagama murna na san nan natuna cewa, aiba abasu komai ba na dan motsa baki,
Da sauri na shiga na hado masu kayan sanyi a ture tare da dan fruit ,
Ummi tace aidama nace diyata bata gidan ne tunda naga ko ruwan sha ba,abamu ba balle,
Ina dariya ina tsiyaya mata a cup nace mata murnan ganin ku ne ya hanna ta baku ai,
Sheriff na zaune yayi kicin,kicin da fuskan shi,na iso da cup da lemon zan zuba mai,
Agaban shi na dan tsugun na gab dashi sai kamshin, turaren na da ke hawa mai kai,
Yana min wani irin kallon mamaki a fakaice,
Bayan nadan tsiyaya mai ne nadan dago kaina a hankali nace mai ga lemu na yasha
Hannu yadaga min kawai alarmar godiya,
Natashi a hannakali cikin tafiyar da ni ban masan cewa ina yin irinta ba, nabar gurinshi
wurin mustapha nanupa don shima in tsiyaya mai,
Ban karasa kawai wurin mustaphan ba naji karan cup din da na zuba ma sheriff lemo ya fadi,
Cikin sauri na aje cup da gwangwanin lemo agaban mustapha na juyo wurin sheriff da sauri,
Lemon ya zube a kasa har yadan taba mai rigan shi kadan,
Ruwan da ke gefe na bude nadan zuba mai daidai inda lemon yataba mai riga,
Cikin rudewa na cire gyalen da na yane fusaka na dashi na fara goge mai wurin,
Kaina da akai ma gyara sai kamshi ke tashi ya dan tsira ma ido
Yana kallon yadda gashina ya kwanta lub bakikirin da shi,
Ga kamshin mangashin dana turare na ya rude wurin ,,,
Idonshi yadan rintse kadan gabanshi nata faduwa,
Don shifa gani yake wanan kamar ba fadimar yar takarin da ya sani bace,
Saboda canzawan nawa yayi yawa cikin dan lokaci guda haka,
Idonshi yadan kara lumshewa yana mai dan maida nufashi, a hankaki ta yadda ba mai iya ganewa,
Cikin kidima naje da sauri nadauko moper na goge kasan , Sai faman yi mai sannu nakeyi,.
Saida na gama gogewa san nan hankalina yadawao daidai
Ko da na daga kai in kara yi mai sannu sai naga idon shi a lunshi sainadauka ko ranshi ne ya baci ,
Cikin sanyin murya nace mai dan Allah yayi hakkuri ba san zai zube mai ajiki ba ,,
Idon shi yabude wanda naga kwayar idon shi yai ma jajir ,saida naji tsoro,.
Hannu yadaga min alamari is ok,

Bayan fitar su sheriff ne muka zauna muna ba ummi da hjy labarin makarantar mu
Nafada mata yadda ake karatu a wurin da kuma salimat da na hadu da ita,
Wacce yanzu nake jinta tankar wata yar uwan na najikina,
Nan sukayi muna weekend saida sheriff da mustapha ba anan suka sauka ba su,
Washe gari sheriff yace min zaiyi baki,
Mudanyi mashi abincin da zasuci don wani meeting zasuyi
Shago mafi kusa natafi ta sayo duk wani abin bukarar da zamuyi amfani da shi,
Don mu a shago ake saida kayan abinci a can ba wai a kasuwa ba,
Abinci kala kusan biyar muka hada masu nida maman su Umar,
Saida muja gyara falon yayi neat sai kamshi ke tashi ko ina, da sanyin A C
A,babban dinning table muka hada masu wurin yayi kamar za ai wani dan kwara,kwaran walima,
Su hudune suka shigo dai almustapha da ke tare da sheriff ko yaushe, suka zama su biyar,
Sun gaida ummi da hjy cikin ladabi da girmamawa,
Bayan dan hiran lafiyar jikin ta da sukai mata wanda duk kusan bayanin hajiyar mu ne ma mai basu ansa, don ita ummi bata magana,
Nice shigo falon cikin wata doguwar riga ja, wacce a hannu ta kawai da kasar rigan keda ado,
Saida na gashe su tunkun sanan na juya wurin da sheriff yake nai mai bayanin abinci is ready
Wani irin kallo yai min wanda ban iya fadan dalilin hakan,
Ina cikin damuwan naji muryan wanidaga cikin bakin yana fadin masha Allah,
Ahmad kai keda kauna haka akasan nan kuma ban sani ba
Sai naji sheriff dake kokarin jawo plate agaban shi yace to aikaga yanzu ka sani ko,
Batare da jin kunyar kowa ba a wurin shi mutumin ke ce min
Sunan shi Ali Baba don Allah yana son in soshi, dama yadade ya son mata mai irin duk siffan dake gare ni bai samu ba,
Ashe ma wanan mugun yana da ita a gida yabarni kulun ina cigiyar yar matashiya, mai,,,,,,,,
Sheriff dakatar dashi da fadin Aliyu is enough don Allah kazo gaban yar yarinya kana faman zuba shirmay kamar wani karamin yaro,
Wanda aka kirada Aliyu yace to be Frank ba wasa a zance Ahmad naga sister ka kuma ina so
Idan har ba zaka taimaka min ba nida kaina zan bidi so a wurinta gakuma ummi a gari,
Bai kakarasa yasake ce mai ban fa son shirmay wanda ke karatu zaka zo ka damay ta, ka koya mata shirmay,
Aliyun yana dariya yace o shirmay ko zaka gani in shir may zan koya mata
Sai ya sauko daga kujerar da yake zaune yadan tsuguna kasa yai kasakasa da muryan shi yace ma sheriff ina wuni yaya,
Gabadaya falon suka sa mai dariya banda sheriff da ya dan tsuke fuskan shi,
Yace ma Aliyu dan iska wanan ta wuce yaudar ka ka koma can wurin yan duniya irin ka kuyi tayin duniyar cinku,
Yace Iam telling you wanan karon wlh ba wasa acikin magana na Ahmad,
Nidai ina gama zuba masu abinci na wuce ciki abina batare da nasan ya suka karasa ba,
Ina shiga dakin kiran wayan salimat ya na shigowa mani,
Nadauka tare da yi mata sheri ina cewa anty amaryan ke nan,
Tanbayana tayi bata gan mu ba masallaci wanan weekend din,
Sai ina fada mata cewa wlh su ummi ne da hjy sukazo muna weekend harda yayan mu
Fada takama min tace lalai fadima baki da kirki yanzu har su ummi su zo arasa wanda zaikirani yafada min cikin ku
Hakuri na bata nafada mata cewa suna nan ai tukun don sheriff na wani dan aiki ne,
Taimin alkawalin zata zo zuwa marance insha Allah,
Ina jin hayaniyar su sheriff har suka gama suka fita,
Inda Aliyu ke ce mai yakirani muyi sallama dan Allah ko kallon shi baiyi ba don takaici,,
Sai kuma gani nafito zanje gurin maman Umar dake aiki a baya,
Duk da sheriff yasan cikin rashin sani nafito amma saida yaji haushina sosai,
Aliyu na mai dariya yace brother in-law kaga ikon Allah ko ga ta tafito da kanta,.
Banko waige su balle insan sunayi wurin da zani nasa kai, har zan shige sai naji shi yana cewa yar uwa dan tsaya min inzo pls
Waigawa nayi kowani angul banga kowa da yake ma magana ba sai ni don haka sai na dan dakata mai,
Ya tako cikin tafiya gayu har inda nake tsayee,
Yace shi sunan shi Aliyu baba dan kasar Nigeria ne shi mutumin katsina ne aiki yazo yi a wanan kasar daga Nigeria,
Kuma baida mata amma ya gane ni yana so na kuma yai ms sheriff bayani komai,
Mamaki yakamani kamar ni yar aiki wanan dan gayun zaice yanaso
Sai nadan leka don inga ko da mai ganin mu
Aiko sheriff ne tsaye cikin wani irin mugun kallon da yake min ina nai abinda ba daidai ba.
Dayagane cewa na ga sheriff ins jin tsoro sai yace min ba matsala zaidawo ya gan ni amma may ye suna na
Cikin sauri zan wuce nace mai fadima,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA





✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story

Cikin hikima da dabara Aliyu baba yafara koya min So,
Saboda bayan tafiyan su sherrif yakawo muna ziyara alokacin ni bani gida ina school
Noban wayata yace salim ya bashi zai kirani yaji ko banda bukatar komai,
Salim bai fada min ba lokacin da na dawo har kusan kwana biyu,
Misalin tara na dare naga komai da nakeyi nasamu guri nadan zauna indayi nazarin wani takardan da muke da test akanshi cikin sati mai zuwa,
Wayana naji yana kara, cikin mamaki nadauka don nasan cewa ba, a kirana a wsnan lokacin,
Bakon noba ne nagani mai kiran don dai dama daga Salimat ne sai Sheriff din mu ko shi ba koyaushe yake kirana

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment