Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,azuciyar shi kuma, yana tunane kawaici irin na mahaifiyar na,shi har yai yawa, watan ita dai haka Allah yai mata rayuwar ta cikin sanyin hali,
Hmmm Allah guda gari bambam ,,,,,Wai hausa ne sukeyi haka wanda sai da kyat nagane may suke cewa,
Get muka shiga ,muna paker motar mu mukafito,
batare da Amal ta tsaya ba tai niyar wucewa cikin gida abinta don duk a,gajiye take,
Niko lokacin na dauko basket din da aka kai muna abinci da rana ga flasks din ruwan tea da nake kokarin dauka wa cikin motar da hannu na guda,,,
Wani wawan tsawa ya,daka mata ta,tsaya wuri guda cak,
Tare da yi mata masifa, wanda ita dai duk iya saninta dashi baitaba yi mata hakan ba,,
Kayan dake hannu na yace mata ta tayani kwasa zuwa ciki,
Flasks din ta karba a hannu na ba shiri, jiki a sanyaye,
Shi kuma salim ya kwaso sauran kayan da muka kwaso daga asibitin,yashiga dasu,
Bin mu yayi da ido yana tausaya min irin wahalar da nasha yau,
Shin wai ita wanan yarinyar haka zuciyan ta yake ne,
Don dai gaskiya inbadon yasan ni tun ban karasa kai haka ba da sai yace kila don asani nakeyi wani abu,
Amma shi duk abinda zanyi sai yaga na tsakani da Allah ne babu kissa aciki,
Tsaki yaja lokacin da yake kokarin rufe motar,
Da ya tuna da Nafisa,
Wace ta nuna mai halin ko in kula, ga mahaifiyar shi,
Shi yarasa ita kowace irin mutunce mara tunane da lissafi,
Ace ankawo mahaifiyar shi asibiti daga Nigeria
Amma wai har ta biyo shi asibiti tana request din kudi a wurin shi,,,
Ita bata da aiki sai dai yawan tambayar shi kudi da bukata
Kuma sai yau yakara sanin halinta sosai don,ganin halin ko in kula da ta nuna mai akan ciwon mahaifiyar shi,,,
Da wanan tunanen ya shiga cikin gidan,,,,

Satin mu biyu muna cikin wanan sintirin zuwa asibiti da gida,
Inda ummi ke jiyan jikinta,
Saidai gaskiya ba laifi jikin nata yayi sauki sosai
Don yanzu har ummi na iya tashi mudan yawata cikin asibitin da ita,
Shakuwa sosai ya shiga tsakani na da Amal da Salim,
Saboda yawan zaman da mukeyi wuri guda, da su,
Sai ya kasan ce kamar mun san junan mu da ma ,har ina jin dadin su fiye da zaman da muka danyi da su jamila da mairo da suka zo kwanaki
Duk da nasan cewa Amal ta girmay ni sosai amma hakan bai hanamu zama guri guda ba da ita,
Muna mu,amula kamar kawaye,
Har tafiya Sheriff din mu yayi zuwa Riyadh yin wani aiki na musan man da yataso mai shi da mustapha suka tafi,
Nice yabarwa kula da duk wani lalura na asibitin
Har zuwa lokacin da suka dawo daga tafiyan
Tafiyan da kusan itace tafiyan da ta zama makowa nagidan alheri nan gaba,
Don ko Sheriff din mu yasamu cigaba sosai don yanzu ya samu sa hannu a kusan mafi yawan company tatar man fetur ta kasa,saudiya,
Saboda kasan cewar shi kwararen engineering da suka sani
Saboda suna ganin cewa zai iya barin kasan any time daga yanzu saboda hada hannu da suka ga yayi da company Abu Abdallah dake Dubai,
Cikin dare ya iso garin don haka direct asibiti suka nufa,
Suna iso wa lokacin su Amal na waje suna shan iska,
Nikuma ina tsaye kanta ina kokarin hada mata ruwan shayi,
Jin anyi yasa na waiga inga ko waye don nadauka ko Amal ce
Sheriff ne sai su almustapha dake binshi abaya,
Gurin mahaifiyar nashi ya nufa direct tana zaune saman gadon asibitin jikin ta yanuna alamar tasa mu lafiya sosai,
Mun mai sannu da zuwa inda yake ansa muna cikin muryan shi maikama da yanajin kasala ko yaushe,,,
Da kyat yake magana mai karfi don in kaji muryan sheriff to ta baci,rai ya gani tare da mutun ,,,
Waje nafita batare da sanin kowa ba don in dan basu wuri su dan zanta, shi da yan uwan shi don kusan nice kwai bare,,a cikin su,,,
A samane dakin da aka kwantar da ummi yake, don haka waje nafito, nadan tsaya,,,
Daga sama inda nake tsaye ina kallon ina iya hangen katon agogon nan dake mane a kofar shiga masallacin ka,aba,
Wanda duk inda kake cikin garin makkah za ka iya ganin shi
mutanen dake shige da fice cikin kofar asibitin, nake dan kallo jefi jefi,
A zuciya na kuma ina, Tausayin yadda naga sheriff ya,damu da mahaifiyar shi ne yakamani,
Don nasan cewa idan yai wanan irin tafiyan yadawo bai fita ko ina har wajen kwana biyu,
Yana gida yana hutawa saboda gajiya
Saidai in rana,kun ya dace da jumma,a a ne acikin ,, shi,,,, Amma yau sai gashi direct asibitin yanufa don gani mahaifiyar shi,,,,
Ya shiga yaga ni ,Yana,Ganin jikin ummin yayi sauki sosai yasa shi fitowa daniyar komawa gida, don yadan huta ma ranshi kadan,,
Turus yayi daga bakin kofar dakin lokacin da fito,
Don, yaga fadima tsaye wace hankalinta na ga kallon waje saidai kuma hawaye take gogewa a fuskanta
Wace ita kadai ce tsaye a wajen,,
A,hankali yatako zuwa kusa da inda take yadafa karfen dake gaban su, yace mata lafiya,
Kaduwa tayi duk jikinta sai yakama rawa saboda jin muryan da tayi na bazata, alokacin,
Kara tambayar ta yayi ko may take ma kuka hakana,
Cikin daburcewa tace mai ba,kuka takeyi ba abune ya fada mata a idon ta,
Bawai ya yarda da ansar data bashi bane kawai ya barta ne don yasan bazai samu ansa ba, a lokacin,

Nafisa ce zaune a falo tana waya ga Tufan da Anabi, aje agabanta sai madarar kwali wanda kwalin yasha rabar sanyin, friged ,da ke aje gefe guda tare da cup,
Waya take yi a,binta hankali kwance tana yi tana tsunkar Anabi din tana kadawa baki,
Sautin kidan yan kasar sudan ya tashi a cikin tv, dake man ne a falon, a hankali,
Kafarta guda saman dan stol din tangaran da ke falon
Har ya shigo falon yakare mata kallon Allah waddai,ya hau sama bata ankara da shi ba,
Sai gab da zai shiga dakin shi taga wulgawan shi,

Cikin sauri ta tashi ta rufa mai baya ,
Tana shiga ta iske yana na balle butur din rigarshi yana son shiga wanka,
Ta bayan shi tazo ta rugumay shi tana sun,sunar shi,
Batare da yace mata komai ba yadan juya ta kadan ya wuce zuwa bayi,
Ido tabishi dashi tare da mamakin wai shi wani irin mutum ne haka,
Sam mace bata agaban shi,
Kwanan shi kusan uku baya gari yanzu kuma da yadawo gashi ya nuna mata bata a gaban shi,
Zaunawa tayi tana jiran shi ya fito daga bayin,
Daure da rigar wanka yafito ajikin shi ga mamakin shi sai yaga Nafisa kwance rub da ciki, saman gadon shi tana dan daga kafar ta da ta mayar baya, a hankali sai hannuta da take, lalatsa wayanta, dagani abinda takeyi a wayan yadauke mata hankali sosai,
Wardrop ya nufa ya ciro wata jallabiya mai ruwan A,she,colour yasa
daidai yana zura rigar ta taso daniyar rugumar shi ,,
Dakatar da ita yayi cikin tsawa, yakama hanyar fita dakin,
Binshi tayi abaya tana fadin walahi ita tagaji da wanan halin ,
May wai yake nufi da ita ne ma, da zai dinga mata wanan wulakancin ita yau tana bukatar shi,,,,,
Daidai lokacin mukayi, Ido hudu dashi kuma a,daidai lokacin da take wanan furucin nata,
Ji yayi kamar ya nutse a kasa don kunya,
Saidai kuma ya basar da zancen nats kamar ma bada shi takeyi ba,,,
Ita ko bata daina ba sai kara ci gaba da fadin kalmar da bata dace ba da takeyi,,,
Takardan da muka dawo dashi wanda zai je yayi filling, gobe akan gwajin da za,ai wa ummi na karshe,,,,
Na mika mai gami da juyawa da sauri, don ganin irin halin da na riske su ,.
Dakatar dani yayi don jin bayanin abinda takardan ya kunsa,,,
Batare da bata lokaci ba nai mai bayanin takardan a gurguje don jin irin hucin da Nafisat ke yi a bayana kamar wata zakanya,
Da sauri sauri na,sauko saman step din don ji nake kamar zata biyo ni a bayana,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
24/10/2017, 1:50:13 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣1⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,

Tun karfebakwai na,safe muke asibiti don yaune gwajin karshe da za,ayi wa ummi,
Kuma ance ya kasance muna wurin kafin a shiga da ita
Saboda zasu fitar da result din abin da yake damun ta
sosai, hankalin mu yatashi jin cewa ya kasance suna gurin ,
Anshiga da ita wani dan daki da zasu sa mutun cikin einjin don awo,
Muna waje tsa tsaye dukan mu cikin da muwa saboda bamusan ko wani irin saka mako zamu samu ba,
Shehi da sherif din mu sai addu,a suke yi daga inda suke tsatsaye,
Ina gefe tsaye bakin kofa, sai Amal da ke daidai inda nake tsaye ta dan zauna Salim kuma ya na daga waje zaune,,cikin zulumi,,
Jin karan bude kofar da akayi ne yasa hankalin mu duk koma gurin, da aka bude kofan
Wani, Dan likitan balaraben yafito yana mai cire kayan da yayi aikin da shi
Ummi ce aka garo ta kamar matatta, babu ko alamar ta na motsi ko kadan,,,,,,,
Aiko muna ganin haka muka bi bayan su da sauri, , cikin tashin hankali
Kwance take saman gado asibtin inda nunfashin ta ke tafiya a hankali
Wanda zaka gane hakane a jikin dan abin nuna nufashin dake mane kusa bango, gefen kanta,
Dakin yayi tsit ,ba wani mai kwakwaran motsi cikin, sai karan fanka dake tashi da sauran na,urorin
Waje na sulale ba wanda yasani nakoma narike karfen da ke saiti da dakin mu,
Bansan lokacin da na fara hawaye ba,daga haka har nadinga kuka wiwi ni kadai a waje,,,
Bakomai yasani kuka ba sai ganin halin da ummi ke ciki duk da gatan da aka mata,,
Sai kawai tunanen Inna da ke yawan damuna kwanan nan, yadawo min sabo
Ganin da nayi zuri,an ummi,duk sun kewaye ta cikin damuwa da tashi hankali,
To inda Inna na ce yaya zatayi,
Sai tuna ne ko cikin wani hali take ciki yanzu haka,
Idan ma tana cikin damuwa ne ba wanda, ko wani rashi lafiya saidai hafsat tayi ta kokari,
Ita daya batare da ni ba,
Kenan ni bazan samu ladan da "ya" ya ke samu wurin iyayen su ba
Hakan ke sa duk naga babba ina kokarin tausaya mai,
Don nasan cewa nima inna na tana can tana bukatar taimako
don hafsat ba,zata iya ba ita kadai,

Kuka ne ya zo min wi,wi babu kakautawa,
Jin kukan da sukayi yasa su duk fitowa inda nake gaba dayan su,
Duk sun kidime, don basu san,komay yasamay ni ba haka,na ba yanzu yanzu
gashi nice mai kokari wanjen kula da ummi
Amma yau na gaza sai kuka nake yi masu duk hankalin su sai ya tashi,
Shehi ne yazo kusa dani ya na tambayana cikin larabci ko may yasamay ni ko banda lafiyane inyi magana mana ko zasu fahince ni,,,,
Sheriff yana daga baya tsaye ido kawai ya kafa min yana sauraren sautin kukana kamar wanda ake watsa ma ruwan zafi a zuciyar shi,
Ganin da yayi dattijon da su salim su dan riko min hannu,
Yasa shi yin magana daga inda yake
Muryan shi sukaji yana fadin baba kyale ta,
Gida take tunane babu abinda yasamay ta
Da sauri nadaga ido na dasuka yi jajir,saboda kuka, ina kallon shi cikin mamaki yadda san abinda yasani kuka,
Takowa yayi a hankali har zuwa inda nake, duke
Ya dan dagoni tsaye da hannu bibiyu, sai ya rugumay ni ajikin shi yana dan buga min baya yana cewa ,
Hayya hayya, alamar ya isa niko sai na kara nokewa sosai a cikin jikin nashi,
Nakara aza kuka sosai, duk hankalin su sai yakara tashi,,,
Abinda yasani dan tsagaita kukan jin karan yar da jakar hannu Nafisa da tayi abayan mu,, wanda
Kusan kowa ya juya don gani ko may ye yafadi hakana a lokaci guda,
Banda ni da kaina ke ajikin sheriff din mu wanda nake ji tankar yayana na ji daya
Wanda tun zowa na garin makkah yake taimako na da alheru
Wanda a,halin yanzu shine yazamo min jigon rayuwata tamkar uwana da ubana nake jin shi
Tunda har a sanadina ya iya daukan dawai niyar mu gaba dayan mu nida yan uwan tafiya na batare da gazawan hakan ba,
Wanda ko sau daya bai taba nuna muna kyama kamar yadda sauran masu kudi kewa yan aiki,ba
Muryan ta ya dawo da hankalin kowa daga kallon jakar da tayar akasa,
Ahmad gaskiya ban fahinci may kake nufi da wanan yar ficiciyar yarinyar ba wace na tabbatar da ko da haila bata fara ba
Balle, nasa cewa koda hannu ta karike ba wani abinda zai kara ka dashi na jin dadi,
Jayeni yayi a jikin shi a hankali ya dan jingina ni ajikin Amal,
Tako daya yakai gare ta yace,
Ke Nafisa Allah waddan hali irin naki hali irin na rashin imani da rashin tausayi,.
Shin ma dai kina cikin hankalin ki kuwa kodai yau din ma kiyi shaye shayen naki ne, daki ka saba,
Kalman shaye sheye da ya furta shiyasa ta kaduwa so sai,,,
Don bata taba tsan mani yasan tana shan drugs ba,
Saita wayance zancen da cewa ni ban san ko ta ina
Ka,hada alaka da wanan yar munafukan yarinya ba mai shegen iya yi,
Yarinya kamar manyya ta wani kafe ka da idon ta kamar gonar madara,
Walahi nayi hating din wanan yariyar a rayuwa na,,,,

Shehi ne dake shiru tunda tafar surfa min zagi imani duk ya kashe shi yana tsaye sai mamaki ta yake yi
Kowata irin mata Allah ya Ahmad haka da ita, wace bata ko san maye aure ba balle dalilin yin auren, ,
Dama shi yana ganin ta yasan cewa bata da tarbiya,
Ba,irin matar da yaso Ahmad da ita ba ke nan,,,
Sai ga shi yau tanu ita din kowace,ce wurin yi ma yaron kirki kamar Ahmad
zancen na haushin wai har kazafi take kokarin yiwa Ahmad din
da cewa wanan yar karamar yarinya kirki mailadabi,
Don haka shehi din yace mata
Yo, wanan din ai tana bukatar kulawa ne bawai ita din, ta kula da mutun ba, kamar
Yadda yaga ita ce wai mai kula da su
Wa na min din aiba wace za ai wa sheri bace irin wanan domin kwazon ta yayi yawa ga kowa,
Batare da shehi yakai karshen maganar shi ba ta juya tana kuka batare da ta shiga gurin ummin da sai taga dama take zuwa gaishe ta ba,
Koshi sai idan hjyn ta tai mata fada a waya take dan zo,wa
Duk zanan mu asibiti zuwan ta na uku ke nan,yau din da tazo,
Shiko sheriff, baiko damu da tafiyar ta ba idon shi na akaina ganin da yayi Amal na min dan magana kasa kasa ina daga kaina,
Cikin dakin da ummi take kwance muka shiga nida Amal
Ido yabimu da shi har muka shige,
Duk ranshi bai mai dadi,ba, ga matsalar kukan da nake ta faman yi ga kuma, sherin da nafisa taimai gaban yan uwan shi,,,,,,
.Koba,a fada ba yasan kukana bai wuce dayan biyu ,ba,
Ko kukan zaman mun a haka kamar bayi ko kuma na tuna yan uwa na gida
Tunda bazaice don ganim yanayin jikin ummi danagani yau nake wanan kukan ba,
Ai inda sabo na saba daganin ummi din a haka
Saida ya lura yaga nadaina kukan, nadan sake jikina kadan
Salim ya karbo muna shayi,
muna zaune muna sha. Coffee din nida Salim da Amal,
Sukan sha abinsu ,sukeyi sosai saidai ni gaskiya shan bugi nake yi wanawa ,
don cup din da dan storot din da ake tsotson coffee din kawai na rike inayi kamar mai sha,
Sai kuma can nai shiru, ina tuna ne,
Mu ukune zaune saman kujerun dake fuskantar dakin da ummi ke ciki, Tsakiyan su nake zaune nai shiru, da cup din coffee din ahannu na,
Ido ya zura min daga inda yake zaune,sai a lokacin ya lura da cewa na ramay nayi baki,
Gaban shi ne yafadi dam,
Yace kar dai a ce aikin da nakeyi ne yai min yawa haka ,har na dan ramay batare da yasani ba,
Aiko dai kada ya shiga hakkin yar mutane, da yawafa,
Yasan cewa dama nayi yar karama da wanan irin dawainiyar da nake yi,
Kwazo kawai irin nawa kesa ana sani wani abinda ya kamata babba yayi,
Tashi nayi don injefa cups din kwalin da muka sha coffee din a dustbin
Lokacin yakara ganin yar raman da nayi ba kadan bace,
Saidai kawai nadan kara girma ne ta kasa na,kadan saboda nadan buda alamar girma, ya fara baiyana min,
amma zuwa sama na duk na dan ramay sai dai na dan kara tsayi sosai,,
Shehi ne yakatse mashi tunanen shi da cewa, Wanan matar takakuwa diyar cikin aminin mahaifin naka ne,
Murmushi yadan yi natakai ci dai dai lokacin da yake kauda idon shi akaina lokacin ina kokarin zama inda natashi,
Yace ma Shehi a gaskiya baba ni bansan komai gamay da gidan Alhajin kano ba don ni dai nasan cewa tun ina yaro saudaya ma nataba zuwa gidan lokacin da zamu koma hutu, suraj yace ma driver ya bida mu ta kano din,
Kuma muna komawa gida hjy mama ta haushi da fada don may sukaje dani har aka ba mu kyauta iri daya dana,su,
Tun wanan lokacin naji duk wani dangi na hjy ma ma yafita min arai, na,,,
Abba na ne yai wanan hadi nikuma na wakilta bashir na mu na wurin kawu sale da ya gabatar da komai kamar yadda Abba ke so ayi,,
Nadauka cewa Abba zai yi min zaben alheri ni ba wai irin wanan zaben na danasani ba,
Kuma duk abinda take min bazan iya fada ma Abbana ba don nasan cewa zai iya shiga wani hali idan yaji,,,,
Haka na wuni arana cikin rashin walwal, duk tunanen yan uwana ya addabe ni ya hanani shakat,,
Bayan mundawo gida duk wanda yagani aranan yasan ban cikin hayacina da akwai abin dake damuna,,,
Ina saye da rigar barci ajikina doguwar riga ce pink sai hula fara da rufe kaina na kawo zani nadaura saman rigar,
Har nadan kwanta sai na tashi saboda da muka dawo,,
Kowa yaci abinci amma ni na kasa cin komai don haka kitchen na nufa don in dauko madara in dan sha,
Har na dauko sai naji wani sabon kuka yazo min har yafi nadazu,
Ashe Amal na biye dani zuwa kitchen din, ganin da tayi ina kukan
Hakalinta ya tsahi ta je da sauri takira, sheriff wanda ke zaune yana latsan laptop din shi a falo,
Cikin sauri ya taso ya biyo ta har kitchen din inda nake durkushe da kwalin madara a hannu,
Jinayi yana ce min, Ta,al ya ukhti, Ana asfan,,
A hankali nadan daga kaina sai nagan su a tsaye bisa kaina,
Namike da sauri, nafada masu ajiki shida Amal ina mai kara sautin kukan nawa,
Har daki na yakaini saman gado inda Amal ta dan tsiyaya, min milk din a cup ta miko min,
Ba musu nakarba saboda irin kallon da yake min,,,saida nasha kusa rabin cup din namika mata ta karba ta juya don ta mayar da cup din da sauran milk din
A gefen gadon yake zaune shi ma ya hada hunnu shi biyu wuri guda ya dun kule, su,
Nan yake ce min natuna da inna ne ko,
Don ganin da nayi ma ummin su ko ba musu na kada mai kai alamar eh,
Yace min in yi hakkuri bada dadewa ba zan tafi gida insha Allah
Dago kai nayi da sauri na kalle shi don in gaskanta maganar nashi,
Muna hada ido dashi yadaga min kai alamar eh,
Gaskiya da na,hango a idon shi yasa na gaskanta zancen nashi,,
Amal dake tsaye kofa tadan kara sa shigowa daga ciki, dakin
Ai Amal bata ko zauna ba aka turo kofan cikin fushi
Idon mu duk kofan yake kallo don mamakin ko waye ya turo kofa haka,
Nafisa ce a fusace daganin ta kasan tana cikin fushi saida ta kare muna kallon rainin wayo gaba dayan, mu, duk ka ukun sanan ta juya tana
Kallon banza Sheriff din yabita da shi batare da yai wani magana ba yatashi gami da ce muna saida safe,

Yanafita Amal da rakashi da kallo tace wanan shegiyar sai nayi maganin ta don naga bata da mutunci sam wlh,
Ranan nan mu uku, muka kwana mun sa Aisha tsakiyar mu,
Washe

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment