Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

👣👣👣👣👣
5⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎


Inna yar kulu zaune a dakinta cikin dare bayan ta idar da sallah dare kamar yadda tasaba, Tana kai kukanta ga Allah akan Allah yasa wanan tafiyan da za,ayi yazama mata alheri,
Allah kuma tsare mata yaranta aduk inda suka shiga.
Duk wanan addu,an da takeyi a cinkin zuciyar ta takeyin shi, ,,
Shin wai ma wazata tura wanan tafiyan cikin hafsat da fadima .
Duk iya tunanen ta takasa tantance wacce zata bari a,tafi da ita,,,,,,,,
Washegari karfe takwas na safe sai ga Gajiye acinkin shirinta na,tafiya,,, A,zuciyanta tana fadin ai,tunda malam sale ya yarda bazan kara kwana ko guda ba kada in,zo in samu matsalar tafiya,,, Don ita ga haukanta duk yaran biyu zata tafi dasu saboda samun banza.
Da sallama tashigo yar kulu ta, tare ta da mutunci, Saidai acan cikin zuciyar ta addu,atakeyi ,,,,,,
Bayan sun gaisa cikin gimama juna,,,,, Sai yar Gajiye tace tau ina fatan yaran sun shirya ko ?
Innna dake shirin mikewa ta dauko mata koko tadakata tace yaran kuma ,"eh mana inji Gajiye bada hafsat da fadima zamu ba ,,,,,,,, habadai Gajiye idan na,bakisu dukka nidawa zan zauna au baga Maryam da DATTIJO ba,,,,, a,a gaskiya hakan bazai yiba , ai,ko mutun gudan dazan baki kawai dai don kece an riga anzama daya
Duk da ran Gajiye ya baci amma sai tadake tanuna ai ba komai ko hakan ma ai, ta gode tunda an,yaba da ita har anbata,,,,,,,, Saidai acikin zuciyar ta fada takeyi,,,, yo ga matsiyaciya nizaki kulla ma tsiya inga samu inga rashi haba wanan wata irin shu,umar mace, ce
Muskudawa tayi tare da gyara zama dan taji dawa zata tafi,,,
Juyowa inna tayi daidai lokacin tai ajiyan zuciya gami da cewa,,,,,,, Ban riga na gama shawaran ko dawa zaki tafi ba tukun ,,,, au mutafi da hafsat ma tunda itace babba.
A,aa gaskiya hakan zaiyi wuya donkin ga itace maidan wayo daga cikin su. Kinga ko zaiyi wuya inbari tayi nisa dani . Duk da yake fadima itace kusan ke taimakawa hasfsat din, kinsan abu ga tallakka ai sai a hankali.
Acikin zuciyar gajiye tace duk kigama tsiyar ki sai naci riba dake,,,
Inna abu yasha mata kai tara wace zata tura birni,,,,,,,,Caraf fadima da ke da saurin wayo da fahinta tace inna nizani abar hafsat dasu maryam
Aiko inna taji dadin hakan don dama tana shakar zuwan hafsat, Saboda shiru shirunta yai yawa za,a iya cuta mata batare da ta dauki wani mataki ba.
Fadima duk da yarinyace amma ta gane cewa inna batason zuwar hafsat din don ko cikin dare , da ta, farka taji inna na,maganar ,,,,,,,
Duk zancen da inna tayi cikin dare fadima naji ,,, A ,hakanan ta kwanta zuciyar ta fam da tunane tana fadin,,,,, Kiyi hakkuri inna tunda kin riga kinyi alkawari ,, nayi alkawarin ni fadima nizanje koda kuwa zuwan nada illar kamar yadda zuciyar ki ke fada maki ,,,, kuma gashi kinyi alkawari baki son fasawa,,,, kada Gajiye taga rashin cika alkawarin ki.
Kuka inna tasaka tana fadin Allah yaimaki,albarka fadima ,,,saboda ta fahinci fadima tagane manufar ta.
Kiyi hakkuri zan maki addua ,,, Sanan kuma ina son jan hankalinki duk da nasan tarbiyan da nayi maku, amma dai inason kisan yanzu birni zaki ba kauye ba ,,,,Don Allah ki kula ki kauda kai ga abin duniya ba ruwanki da abin mutane kiyi abinda yakaiki watau zumunci ki kulada rayuwar kamar kina a gabana,,,Don Allah ki kiyaye ki kare mutuncin ki,,, Sannan nasan ki da rawan kai to ki rage don Allah,,,, Allah yayi maki albarka yakare minke daga duk wani abinki ya azurta min ku da ilimi mai amfani ,,, Zancigaba da yi maki adduan alheri har randa akadawo min dake ,, Allah ya kaiku lfy
Da kyar ta kai maganar ta da kuka a fuskanta.
Gajiye ta mike tsaye tana fadin haba yar kulu sai kace wani guri zata haka.,,,,, aiki kwatar da hankalinki fadima gida zata.
Hmmm Gajiye aikin san danyau saida fada ,,, tau hakane kuma
Gajiye tace ina kayanta akadauko wasu yan tsumakara da duk basufi huduba acikin wata tsohuwar leda bage baka aka bata
Kuka fadima keyi ta kankamay yan uwanta tana kuka kamar bazasu kara haduwa ba,,,Gajiye tace haba fadima ki yi hakkuri daina kuka ba wai dadewa zakiyi ba ai idan zan dawo tare zamu dawo, ba wai an rabu ne gaba daya ba . Wanan kuka haka ai sai yasaki ciwon kai.
Gurin inna takoma ta kara riketa tana fadin inna ki yafe min dan Allah ,,,, ita ma inna fadi takeyi cikin kuka baki man komai ba fadima Allah ya kai ku lfy.
A waje suka tarar da,su Ramatu da wasu yan uwan gajiye suna jiran fitowar su,
Haba shiru haka inji Ramatu ai mundauka kun fasa zuwa yaune,,,,
A,a ,a haba dai mun dai tsaya adan kintsa ne kinsan rabuwar da da mahaifi da wuya tun dai irin wanan da ba,a taba zuwa ko ina ba.
A haka suka samu motar da zata kaisu sokoto nan bakin hanya ,,, Ana daga masu hannnu fadima ma tana daga masu hannu tana kuka har saida ta daina ganin su,,,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 16:34] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Girmamawa Gareku masoyana👏👏,👏
ANTY Mariya SB
Hafsat yusuf
Safiya mai Huguna
Fatima Garba Teema luv
Maman Rufaida
Maman Ihsan
Anty Amal.
Nagode maku sosai,,,,




( FARKO )

Allah sarki ,,,, Yau litani itace rana ta farko da ni fadima nafara fita nabar kauyen mu dogon daji dake cikin jahar sokoto ,,,itace kuma rana tafarko da na fara shiga mota.
Tun ina kuka har nadaina gabana ko yanata faduwa ina ta rintse idona ,,,,,, anawa haukan wai,na ga itace na ta gudu .
Ba ai wani dadewaba muka shigo garin sokoto .
Muna isa tasha muka samu motar kano saura mutum uku, Gajiye ta biya kudin mutun uku din wai batason a matseta a mota.
Tun a sokoto nafara ganin canjin fuska a wurin Gajiye. Cikin hali irin na yaro nadan sa guiwar hannuna bisa ciyar ta haba aikawai naji ta fisgar min da hannu ta hankadeni gefe guda . tace kada ki kawo min sakarcin nan irin wanda uwar ku ta koya maku,,,,
A, hankali nadaga idona na kalleta idona tab da hawaye,,
Wani irin a jiyar zuciya nayi na maida fuskata hanyan titi,,,,,,, Ga fitsari ya cika min mara amma tsoron Gajiye ya hanani magana saida naga fitsari na batun balla min mara nasa , ihu cikin kuka nace wayyo Allah fitsari nake ji
Driver yataka burki da sauri yana fadin subahanallah shine baki magana,,,,,, Gajiye takai min rankwashi akai tace ja,ira fita da sauri kada ki min ajikina. kafin in tsuguna har yafara fita ko.
Karfe uku da rabi muka shiga KANO, zokaga kallo wurin yar kauye in waiga nan in waiga nan . muka sauka a saman hanya Gajiye takara tsaida wata a daidaita sahu sukayi jinga akaita Tarauni.
Mun isa tarauni cikin dan kan kanin lokaci, Gajiye ta biya mai adaidaita sahu kudin shi yatafi
Wani gida muka dosa gidan akusan tsakiyar layin gidan yake, saidai yanayin wurin yaimin kama da kasuwa a gurin saboda yawaan mutane da kuma abin hawa.
Gidan yana darumfa ga katuwar baranda an shimfida tabarmar roba babba ga benci kuma an jera su kala kala
Muka zagaya ta baya naga wasu yaran mata suna ta gaida Gajiye,,,,,, HAJIYA tana ciki ne inji gajiye tana tambayar "yan mata wata gutuwa tace mata eh tana ciki,,,, Dakata nan kijirani inji Gajiye .
Daya daga cikin yan matan tace Allah sarki Yumma dibi wanan yar yarinyar don daukar alhaki wai itama ankawota aikatau ko bauta,,,,,,, Yarinya da uwar ki tasani da bata barki kinzo ba .
Duk da yarinya nake saida cikina yabada kara naji wata iri don, Kande mai aya tagarin mu tana muna hiran yadda turawa suka dinga bautar da mutane da yadda shehu yazo ya dinga yaki da kafirai,,,,,, wanan zancen na kande na tuna.
Wata murya ta katse min tunane na tace Sukaina ance kiba wanan bakuwar yarinyar abinci taci inji hajiya
Saida nagama cin shinkafa da miya sai wani ganye da aka zuba sama,,,, bantaba cin ganyen ba sai na yayeshi gefe naci shinkafar kawai mai shegen dadi da nama guda uku aciki, aka kawo min ruwa masu sanyi nasha nayi hamdala.
Ina gamawa na mike naje gurin wacce akace tabani abinci nakai mata kwano takarba tana fadin kin koshi ko nace mata eh,,,,, saidai don Allah inason inyi sallah ne .
Tadafa min kai tace Allah sarki zoto in gwada maki wuri, wani dan daki takaini ansa wata tsohuwar kwali agefe tace min yi nan, muma anan , muke dan labewa muyi,,,,, dam sallah kuma ake labewa ayi nafadi haka a zuciya ta.
Ina cikin sallah naji ana fadin hajiya tace wai a,shigo da bakuwar yarinyar da tazo yanzu
Akace mata ina sallah takoma tafada masu,,,
Bayan na idar wanan Sukainar tace min inzo muje gurin hajiya,,,,Da sallamata na shiga su,biyu ke cinkin dakin maikama da shago, GAjiye tana zaune samar tabarma, itako, hajiya mai sharwali na saman wata kujerar roba fara.
Cikin gimamawa naje har gabanta na rusuna nace ina wuni hajiya takarba min ba yabo ba fallasawa, najuya na gaida gajiye itama,,,,Ido matar ta kuramin ina nan a tsugune har nadan wani lokaci,,, ina ganin matar nazari takeyi akaina.Dakin yai shiri nawani dan lokaci, kaina yana kasa duke, naji muryan matar tana fadin a,gaskiya Gajiye don dai kin fada min matsalar ki data uwar yarinyar gane da bazan dauki karaman yarinya irin wanan ba .
Ai wanan wahalar rainonta kawai mutun zaiyi Ita, ko Gajiye tana fadin ayi hakkuri hajiya , ataimaka muna.
A,zuciyata nace taimako kuma ashe dama inna sayar dani ta hada baki da Gajiye suyi shine ban sani ba ,,,,,, Allah sarki inna har talaucin da ake kira muna yakai hakan,,,,,, wasu kwalla masu zafi suka sulalo min ga fuskata na share hawayena na dan, gyara tsugunawa na,sake cewa, Allah nagode ma da ba hafsat tazo ba don ita bata kaini lfy ba ance tana da shawara ajikinta kuma inda tazo ya saurayinta I,Lu zaiyi yadda suke son juna,,, kusan mu kauye da yarinya takai shekara goma zancen aure yafara ke nan duk wani abu na mata zata fara iyawa....
Ina cikin tunane naji hajiya nacewa to amma gaskiya bazan baki kudin taba duka sai naga yadda yanayinta yake . Ai ba matsala inji Gajiye nasan insha Allahu zakiyi alfahari da ita.
HAJIYA taba Gajiye kudina ina kallo tanata washe baki har kune ita kakanta ya yanke saka.
Hajiya ta waigo tana fadin maye sunanta ne Gajiye ta ansa da fadin FATIMA saidai mu can kauye muna ce mata FADIMA ai, to shike nan sunar yayi kinsan mu nan muna canza ma mutun suna saboda bat,da, kama,,,,
Da Gajiye zata tafi tajawoni gefe taja min kune tana fadin to fadima ki kula da duk wani aiki da a,kasaki kuma banda kwadai don nasan kinga abinda baki saba gani ba don Allah ki kula sosai
Wanan kudin kuma zan je dogon daji in kaiwa mahaifiyarki su tasan abinda zatayi dasu,,,, (kaji makirci) irin ta tsofin kilaki,,,
Har ta fara tafiya cikin muryan kuka nace Inna nan zaki barni tace, "eh fadima amma zan rika zowa ina dibaki ke kuma dan abinda kika tara saiki bani inkaiwa maman ki.
Wasu hawaye masu zafi da kunar rai suka kara sulalowa a idona nace to kigaida su hafsat,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITES🐎
[10/3, 16:40] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣
BY
🐎ZAINAB MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Akullun ina gode maku yan Huguma groups gaba daya da kuma TEEMA Luv Hausa Novels
Anty mariya sb
Anty hafsat yusuf Ali
Godiya dubu dubu gare ku.


Tun wucewar Gajiye sai nasamu wuri gindin wata bishiya na zauna nayi ta gumi,,,,,
Ina kallon yan matan dake ta ai yu kan su babu mai kula wata daga cikin su, Wacce naga tana karban kudi kuma nake ganin itace babban su, naga ta biyo ni tace zo kira cin abinci, don idan muntafi gida sai da safe zamu sake cin wani
Ido na fitar waje, nida inna ta saba aje muna fura da koko duk wanda yadawo ko yashigo yadiba yadda yake so yasha har dare watabi kuma da dare taimuna tuwon mu mai dadi muci.
Yau nice wai sai gobe zan karya Allah sarki rayuwa.
Sai misalin takwas nadare muka rufe shago , ina rugumay da dan kulin kayana cikin leda ta baka,,,, naga wani mai adaidaita sahu yazo muka lodu ciki mu biyar ,
Tafiya maidan nisa yayi damu sai gamu wani dan gida karmi baida get amma ginane kamar ginan mutun daya,,,,,, Falo sai dakuna guda biyu agefe da makewayi a bayasa andanyi makewayin kwano dan karami ashe inda muke kewaya wane , shi wancan naciki na hajiyace ita kadai.
Muna shiga dakin naga sun,jawo wata tsohuwar tabarman roba sun shinfida
Kowa nata wasoson wurin kwanci saboda sunga bakuwa suna ganin ai wurin bai isar mu . Daya daga cikin su ko ince wacee dazu tace nakara cin abinci tace, min ,zo nan ki kwanta wurina ni sai in kwanta kasa,,,,,,,,, Naga taciro wani tsohon zanin ta, tashinfida akasa ta jawo ghana most go din ta, ta aje allamar filo ke nan, koda na kalli sauran naga suma duk sunyi irin yadda tayi.
Nima hakan nayi nadan aza ledar kayana na kwanta
Sai,naga wasun su, sun tashi suna wankin yan kayan su watau ke nan basu da time din wankin kayan su sai cikin dare suke wanki in,sun dawo sai su shanya kafin gari ya waye ya bushe,,,,,,,,,,
Rugaiyya ta dan juya tace min maiyye sunar ki kaunata, ? nace mata fadima .
Allah sarki tace daga ina aka dau koki nace dogon daji ,tace ina ne kuma hakana nace mata can can ,,,,,,,
Tace to ki kula da aikin da,duk a,kasaki kinji ,,,,,,, Nace to
Saita nuna min sauran tace wacan itace Yumma wacan Mari wacan Sukaina nikuma Rugaiyya kinji kuma kowa kice mata anty nace to,,,,,,,
Karfe hudu na asuba ina cikin barci na mai dadi naji ankai min duka a baya ana fadin tashi dan Allah kinji mu kwashe shinfida,,,,,, Tunda an fada maki barci kikazo yi, aida ki zauna gida kita barci, amma tunda uwar ki nason kudi ai barci baiga idonki ba yarinya.
Anty Sukaina ce ke fadin hakana , Rugaiyya tace haba dai Sukaina yakamata ki tausaya wa wanan yarinyar dan Allah bai kamata mu matsa mata , ba,ai,,,,,,
Mari, dake gefe tana gyara kunshin kayanta tace ai bidan kudi tazo yi kamar mu,,,,
Yumma tace ai maganar Rugaiyya gaskiya ne idan munyi tunane kamata yayi muso junan kamar yan uwa ba wai mudinga cuta wa junan mu ba,,,,, mutaru mu rufawa juna asiri .
Saboda wanan yarinyar tayi karama da yawa gaskiya ,rashin taudasayine kawai irin na mutane da kwadanyi iyayye kuma ,,,,,
Nidai ina jinsu ina kallon kowa da irin halinta.

Cikin duhun nan sukayi sharan gida suka goge , wasun su ,suka debo ruwa a famfo suka cika wani katon roban ruwa,,,,,
Kafin karfe shidda yayi har an wanke wake ankai nika,,,
Mai adaidaita sahun jiya, yazo yadauki Yumma da mari da markaden wake da su, mai ,yatafi ,dasu
Sukuma sauran naga sun hura wuta a wajen gidan mu suka fara suya,,,,,
Duk wanan abin nadauka hajiya bata a gida sai misalin karfe takwas ,,,Rugaiya tashiga gida ta bata ruwan wanka tafito tsab da ita
, aka zo a kadauketa zuwa shago.
Koda tara na safiya yayi duk mun hada komai cikin gida, muka rufe gida, muma mukatafi shago rayuwar ke nan

🐎ZEEE MAKAWA 🐎
🐎 HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 16:43] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Godiya ga masoyana yan uwa na
Mariya SB
Hafsat Yusuf da maman Rufaida
Ummi Rabiu da maimuna Adam duk a huguma group



Tundaga wanan rana rayuwar ta fara canza min, nasan mayye duniya, Ruyuwa ce ta bauta ko , ko tarashin galihu,,, gamunan dai haka gari zaiwaye muna dare ya riske mu a wahalce,,,,,,,,,,,

Gari yawaye rana ya hudu daga gabas alokacin muna suyan kosai a acikin uguwar mu kafin mutafi shago,,,,
Ni aiki na shine a zuba min kosai da yawa a far roba indaga bin gidajen masu kudi in sun fito da safe suna saya suna sadaka,,,,,,
Abayana almajirai ke bina wa yanda ke karban sadaka ,,, idan nai sa,a za,a iya saye robar kosan gaba daya alokaci guda ,,aba ma almajirai sadaka .
Bakaramin cigaba hajiya tasamu ba ganin irin ribar da take samu damu yasa ta kara yawan kosai da muke sayarwa har da gudun mawar koko a wurin mu,,, kawai mutun yazo ya,saya koko da kanci inda kana son sikari mu zubama,,,


Da rana zuwa goma mun isa shago don fara abincin rana. Wanan yazama ka,ida dole goma taimuna a,shago, duk da aikin mu yafi yawa kuma munfi kawo kudi masu yawa,,,
A gaskiya ina jin dadin zama da sababin yayyen da nasamu suna kula dani sosai saboda ko aiki sukaga zaimin yawa zasu taimaka min dashi
Duk da dai aikina bawani mai yawa bane sosai,,,,,,, Idan an,ci, abinci nice zandauko kwanoni in hada su gurin wanke wake muna da almajirai masu wanke muna,, Sukuma abasu abincin da akaci aka raga suci
Wata rana natafi dauko kwanon da akaci abinci a tsallaken shagon mu ,,,,,,, abinka da yar kauye ban kulaba ashe akwai mota tafe kawai jinayi wata wuta ta,gitta min tun lokacin bansan inda nake ba,,,,,,
Muryam mutane nadiga ji sama sama akaina wasu na fadin ai,tana motsi ku,taimaka akaita asibiti,,

Bankara sanin indanake ba,,,, ita hajiya mai shar wali ana fada mata ta mike da sauri tai waje ,,Tana fadin kada ku bari yagudu ku kama min kowaye,
Tana wani fiszege fiszege irin abin nan na yan duniyan mata

A she driven wani alhaji ne ya dauko yara zuwa gida daga makaranta ,,,
Asibiti aka, kai fadima ,Likita ya,dibata ga babu kariya saidai inda tadan ji ciwo.
Likita ce za,a bani gado aga yadda jikin zaidan kasance tukun,,,
Hajiya kan kakanta ta yanke saka,, saboda mai motar da aka bugeni shi yadauki dawainiyar zamana asibiti
Abubuwan marmari da su kayan tea haka aka jibga muna su ga kudi wurin dubu hamsi yace a,yi duk lalurar da za,ai min inbasu isaba a tambaye shi,,,,


Tun daga wanan ranan da na kwanta ciwo bana iya cin komai daga kwanciya sai kwanciya , itako hajiya duk abinda aka kawo daga gidan Alhajin cinyewa takeyi.
Har kusan kwana goma ina cikin wanan halin,
Tunanen gida da kewan yan uwa na yadawo min sabo acikin zuciyata ,,,, Saidai kaga hawaye na zuba min a ido idan antambayeni ko maye sai ince ba komai ,,,
Naramay na yankwamay duk nasake sai yar wuyan da na danyi saboda rama.
Duk kudin da hajiya tasamu gurin Alhaji ssboda ni baisa tabar min fada ba wai lalaci ne kawai don ina mata bakin cikin dan cikin kosan da take samu ,,,,,,

Rugaiyya sukan ce min inyi hakkuri hakana hajiya take ko kana ciwo bata tausayi ka, ita dai kaji sauki ka,bido mata kudi kawai,,,
Sannu a hankali na fara samun sauki ina danjin kwarin jikina,,
Nikan zauna a daki ni,kadai inyi ta kuka saboda a, tunane na da

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment