Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya iso gidan daga tafiyan da yace yayi,,
Dakin shi ya haura sama batare da yakara yin wani magana ba,
Wurin Amal natafi tana zaune tana gyara kayanta, cikin jakar hannunta,
Ina shiga na fada jikin ta ina wani irin kuka mai gumza,
Duk hankalin Amal din sai yatashi, saboda ganin irin kukan da nakeyi
Da kyat tasamu tadan lalashe ni nadan tsagaita kukan nawa,
A natse take tambayana komay ke faruwa nakwashe abinda nagani gurin dakunan nasu nafada mata,
Karazancen da cewa kodai yan bagaladi sunzo sun kama su ne ba,afadamin ba,
Sai kuma nakara shige mata cikin jikinta ina wani irin kuka mai tsuma rai da zuciyan bawa,
Har maman su Umar saida ta iso dakin don jin ko mai ke faru ne haka,
Amal tadan dago min kai tace indan saurareta inji dan Allah,
Jin danayi tace dan Allah yasa nadan tsagaitata kukan nawa,
Ina saurarenta, tace min fadima kinsan dai duk inda suke yayan mu yasani ko , kai nadan kada alamar eh,
Tace kuma dai kinsan bazai bari ai masu wulakanci ba ko,
Kallonta nakeyi ina naxarin zancenta a hankali,
Ganin da tayi nadan tsagaita kukan yasa ta fara share min hawayena da hannun ta a hankali,
Bata barni ba saida taga nasamu dan natsuwa, tukun sanan tayarda naje daki na
Ranan ko abinci banci ba hakana nasamu guri nadan kwanta don indan samu natsuwa,
Tunda na kwanta ban tashi ba sai cikin dare, nafarka, natashi, nadauro alwala, nazo nayi nafila raka,a hudu kamar kulun
Saida gari ya waye san nan na tashi a hankali naje na gyara jikina tsab nafito cikin shigar wasu jajayen, da dan ratsinyau
ki,baki kayan yan na mutanen Japanese ne mata, rigan yanada dan budewa a kasan shi sai dan guntun hannu daidai, gwiwar hannu,
Bakin gyale nasamu nadan daure kaina dashi,
A hankali na ke tafiya kamar banson taka kasa, fito wa nayi zuwa falon gidan
Don indan samu abinda zan danci saboda tun jiya ban ci komai ba, yunwa nake ji yau
Zaune suke shida Salim a dinning table din suna cin abinci su hankalo kwance,
Ganin da nayi masu shi yasa nai niyar komawa daki sai kuma wata zuciya tace min ban gaida sheriff ba,

Takawa nayi har inda yake nadan karasa cikin ladabi na gaishe shi nai mai yaya hanya,
Salim yai min tayin abinci, yace min ya dauka ko nima barcin nakeyi don baiji motsina ba,
Batare da nace mai komai ba nawuce kawai zuwa cikin kitchen inda na saba diban abincin mu,
Saboda gaskiya ban iya zama inci abinci agaban sheriff din mu, yana kallo nha
Har nakai kofar shiga side din da zai sada ni da kitchen din sai naji muryam sheriff, cikin harshen larabci yana ce min inzo, a hankali nadawo har inda suke kujera dake gefen Salim ya gwada min in zauna sama,
Sai naji wani dummm narasa yadda zanyi sai naga ya mike yabar gurin yana waya,
Nawaiga a hankali sai naga yabar falon gaba daya, hakan yasa naji dadin zama nazauna naci abinci na hankali kwance,
Saidai zuciya cikie take fam da tunanen inda yan uwana sukaje,
Batare da sani wani
Ina tashi wurin maman Umar na nufa don inji komay mafitar zancen,,,
Itama dai hakkuri tabani tace min in bari zata bincika min a hankali,
Amma dai duk ida suke shariff yasani ai
Kusan kwdayataso baice min komai ba nikuma cikin damuwa nake sosai
Ranan da muka cika kwana biyu ne ina zaune a daki na ina nazarin a kan wani sabon computer da yafito sai naji anturo kofar dakin na a hankali,
Nadauko ko Aisha ce sai dai kamshin turaren da ya ruda min hanci yafada min kowaye
Cikin shigar kananin kaya yake yau kayan sunyi mugun karban jikin shi,,
In ganin shi sai nayi niyar saukowa daga saman gadon ,
Hannu yadaga min a hankali yai min nuni da inzauna inda nake,
Gefen mirrow dakin yaje yadan tsaya yajingina jikin shi da mirrow
Hannu shi cikin aljihun Kafan shi na harde cikin guda,
Ido yadan zuba min kusan na minti biyu sai yakira suna na ahankali, nakarba,
Ina mai dan dago kaina shima ahankali nadan kalle gefen da yake sai na sauke idon nawa
Yace min wani irin tambaya kikai min shekaran jiya,
Shiru nayi ba ansa yakara ce min haka yakamata kiyi tambaya,
Ko kinga cewa hjy zata bace a gida nane,
Karshe yace hjy da sauran yaranta sun koma gida Nigeria, dammm dammm gaba na ya harba
Wanan karon kallon shi nakeyi cikin ido sosai saidai na kasa dole na sauke kwayar idona da yacika fam da hawaye,
Na maimata maganar nace sun koma Nigeria,
Yaushe, kuma ta yaya san nan nifa ,
Ni may yasa suka wuce suka barni, sai kawai nasa kuka mai bala,in tsuma zuciya,
Ganin da yayi nafara kukan yasa shi fita dakin cikin sauri, duk da yaso son yai min bayani komai amma ina bai iya tsaya yanajin kukan mace a gaban shi hakana,,
Nai kukana har saida nagaji banda wani bayani dole na hakkura na maida lamari na ga Allah,
Sati biyu zamu yi a makka don haka muna garin sheriff ya wuce zuwa Nigeria wurin wani aiki dayataso mai akan sabon kamfanin su,
Don haka mu kadai yabari a gidan,,
Ganin da nayi bai gari yasa na shirya zuwa masfala wurin hajiya laila, don inji bayanin abinda ke faruwa tunda na fuskanci sheriff baida niyar fada min komai,,,
Ina zuwa sai nai rashin sa,a ance hjy laila ta koma birnin Riyadh da zama
Haka nadawo gida hankalina tashe, banda wani sukuni ko kuzari tare da ni ko kadan
Maman su umar ne nasamu take dan kwantar min da hankali yanzu,
Saiko Amal wace take iya kokarinta wurin kula da al,amarina ,

Saidaga baya na fahinci cewa aziza ba ,a garin take da zama ba ashe wai a Dubai take zama don a can take sana,a har tagamu da sherrif din mu awajen wani taron yan kasuwan kasashen afirika da akayi,
Tun lokacin ta lake mai so sai, da taga gurinta ya cika,
Tana son sheriff don yayi mata kuma tana ra,ayin kudin shi ,,,
Wanan zuwan da yayi Nigeria har da batun dawowa da nafisat gidan shi yakai shi,
Nafisat zata zauna a Abujane tunda yanzu zaidinga zuwa aiki can sosai,
Ita kuma aziza zata dinga zuwa nan saudiya ko kuma shi yaje can inda take,
Ya iske kaunar shi yayan su Amal ta hai ko suna ba,ayi ba
Yai mata sha,uku na arziki ita da mijinta har su shehi da sauran yan uwa sunji dadin wanan zuwan nashi so sai,
Kamar yadda maman su Umar tai min alkawarin bincken labarin su hjy mu haka din ne ko
Saida ta binciko mai tazo min da labarin yadda maganar yake cewa hjy da su yumma sunkoma gida ne da taimakon Sheriff saboda gwaunatin saudiya tasa anata binciko mata duk inda takari suke zaune akasan
Hakan da yagani ne yasa yai masu bizan komawa gida suka koma tare da su yumma,
Saidai akwai sauran bayanin da batai min ba tadan boye min su,
Jin hakan da nayi yasa nadan ji sanyi azuciya na sosai ,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣2⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,

Har muka kare hutun mu a makka Sheriff bai dawo ba daga tafiyan da yayi, don yace daga Nigeria zai biya kasar Italy
Mundawo madina lfy, munci gabada gudanar da karatun mu lafiya,
Bamu da wani matsalar rayuwa yanzu don koda yaushe sheriff yana turo muna da kudi
Duk da babu abinda muka rasa na rayuwa amma sai ya aiko muna da kudin nan,
Salimat tasamu ciki mai wahal da ita sosai, don kusan duk abinda taci sai ta amayar da shi,
Don haka yanzu kusan karatun mutum biyu nake yi , inyi nata inyi nawa,
Saboda gaskiya ba yabon kai ba wlh ina da gwargwadon kokarina sosai,
Shiyasa koda nake hada aiki na da na Salimat ba wai wani mugun wuya nake sha sosai ba,
Dagani har Amal muna iya kokarin mu wurin kula da ita saboda inkaga yadda ta koma sai ta baka tausayi sosai,
Ganin irin wahalar da take sha ne kuma gata gidan ita kadai ne aciki yasa mijin ta yabugo min waya cewa don Allah yana son mu taimaka mai salimat tadan dawo wurin mu ta zauna har taji dan sauki,

Saboda nasan cewa nima laba ni akayi sai ban boye mai gaskiya ba nace zan bugawa sheriff yawa in fada mai idan ya amince zan fada mai saita dawo gidan namu,,,
Sai da nafara yiwa Amal bayanin komai inda ita ma tace gaskiya Salimat tana bukatar taimako don ita kadaice a gidan batare da kowa take zama ba,
Tace min inwa sheriff magana ko zai yarda,
Saida dare bayan na gama komai kuma na tabbatar cewa shima yanzu duk inda yake ya dan natsu ,
Watakila yana sama computer shima,
Sainai dialing din noban shi,
Zaune yake shida aziza a falon su na garin Riyadh, tayi dan filo da cinyan shi ,
Shiko yana aikin latsan system din shi, wayar shi tadan yi kara kadan
Bai dauka ba saida kiran ya kusa tsinkewa dakanshi,
Sanan yadiba yaga kowaye,
Sunan fadima dayagani shi yabashi mamaki ,
Saida yakara maimaita sunan san nan ya ansa sallama da nai mai cike da mamaki yake don dai gaskiya bantaba kiran shi a waya ba saidai shi din yakiramu yaji lafyan mu,
Saida na gama gashe shi sai kuma nadan shiru, jin shirun da nayi ne yasa shi yadan daga wayar nashi yadiba kona kashe ne sai yaga ina online,
Hlo yace na ansa mai da naam yace min lafiya dai ko,
Cikin inda inda nafara mai bayanin salimat da kuma abinda yasa nakirashi,
Saida yagama jin bayani na san nan yace min fadima na ansa da naam
Yace kina ganin dauko da zakuyi ku aje agida bai zama maku matsala nan gaba kadan
A hankali na ansa mai da cewa a,a dan murmushi kawai naji yayi,
Yace min idan har kunga cewa hakan bazai shafi lafiyan karatun kuba ai is ok,
Nakasa boye farin cikina saida ya gane daga inda yake don na manta cewa ban kashe waya ba yaji sanda nake ihun murna ina fada wa Amal cewa ya yarda
Murmushi yadan yi wanda har saida aziza ta dan dago kanta takaleshi,
Bayan ta maida kanta kan ciyan yashine take tambayan shi ko may yafaru,
A,takaice yabata ansa yace mata shida su fadima ne ke waya kawai daga nan bai kara ce mata komai ba,
Yacigaba da aikin shi na tura sakon ni dayakeyi, amma zuciyan shi fam da tunanen son baby a ranshi, gashi da mata amma ba wace keda alamar haihuwa acikin su,
Ganin da yaiwa babyn sister shi daya je Nigeria ne tun lokacin yaji yafara son haihuwa don duk wanda ya ganshi sai ace aida shi baby ke kama wai kamar su guda lokacin yana karami
Don haka sai yaji yana son yaron aranshi sosai,
Kafin yadawo duk wani abin jin dadi na jarirai saida yasawa yaron,
Sai kuma yanzu maganar cikin Salinat da nai mai yasa shi cikin wani tunane mai dan zurfi,

Aziza yace cikin dan kasalalen murya ta ansa da umm sweet sahibi,
Yace mata when are u ready for our babies,
Wani dan shock taji wanda saida kyat ta iya saita kanta kafin tadan dariya
Tawani shake murya tace tun yanzu sweet sahibi,
Saiyadan dagota yace da sai yaushe kike shiri ke,
Tadan kashe mai idlafiya nan da two years coming ko,
Yace mata u are out of ur sense,
Niko yau ki shirya kikarbi dan Riyadh basai ma gobe ba,
Dariya suka sa gaba dayan su, saida suka dan tsakaita dariyan ne yasa ke ce mata gaskiya ina bukatar haihuwa, very soon
Aranan wanan maganan aziza ta kwanada shi azuciyar ta washe gari maganar na cinta sai taji sheriff dake kokarin daura tie din shi awuya yana ce mata ihope kin karbi ajiyan baby ko,
Murmushin dole ta sake don maganar baby nan yana tayar mata da hankali sosai walahi
Ya manna mata kiss a goshi yafita yana mai mata sallama,
Bayanshi tabida kallo bayan wucewar shi,
Wayan ta ta jawo dake gefen filo aje,takira layin Hindu ,
kira guda Hindu ta dauki yawan tana dariya,
Jin muryan Aziza cikin tashin hankali ne yasa tagane cewa ba lafiya
Tambayan Azizan tayi komay ke faruwa ne haka,taji ta badadi tunda safe haka,
Aziza tace bari Hindu Ahmad nason ya dauko min wani sabon bala,ai ne wai shi haihuwa yake so,
Dariya Hindu tasa mata mai cin zuciya , saida tayi mai isar ta tace
Aziza yar lashi, yo ke da mai kike nufi,
Ko kin manta cewa matashi kika aura,
Ai hakan nacikin ilar auren shi da na hango maki,
Shiyasa naso kiyi hakkuri da yan tsofin Alhazan da muke bi don su ba batun haihuwa gare su saidai life
Don sun riga sunyowa bariki shiri kafin su shigo sun aje dukiya sun kuma tara iyali,
Amma ke kudi da kyawon shi da kurciya suka debe ki,
Yo aiko shi in baice yana son haihuwa ba yan uwan shi na son suga zuriar shi
Nidan Allah kin isheni da zance Hindu kiranki nayi inji may abin yi yanzu,
To ki saurara da kyau don wanan maganar ba tawaya bace kibari har mu hadu sai musan abin yi,
Ahaka suka rabu hindu na ta kwantar mata da hankali cewa ta kwantar da hankalinta komai zai zo mata da sauki insha Allah,

Mu uku muka tafi gidan su salimat da salim da maman umar mun samayta tana jin jikin ta sosai yau,
Kayan sawan ta kawai muka dan diba sai wasu tan abin bukatu na mata da na tataro matasu cikin jakka hannunta,
Salim ya jawo mu zuwa gida da ita, ahankali yake tafiya da ita duk kyawon da hanyoyin keda baisa salim yin gudu ba saboda tausayin irin halin da yaga Salimat
A dakina mukayi mata masauki ,tundaga wanan lokacin maman umar ke kokarin kulada salimat
Don itace tasan yadda harkan ciki yake duk abinda salimat tace zataci shi za muyi mata,

Hjy mama tare da yayan ta akasar Spain taje ganin likintan ta da ke diba mata kafa ,
Zaune suke duk kan su saman kujerun da ke falon tana ta faman surfa masu masifa,
Akan may har suka bari Ahmad yafi tara abin duniya akansu ita bataga amfanin karatunsu a turai ba gashi duk wani dan dukiyan ta turo masu shi,
Suraj ne ya katse ta dacewa, haba mama arziki fa na Allah ne duk yadda mukaso yin shi idan Allah bai nufa ba baza muyi shiba sai lokaci yayi,
Imun shiru tace mai acikin daka tsawa kai ai kafi kowa bani mamaki har nan fa muka shirya dakai zakaje ka dibo muna wani irin sana,a yakeyi haka, har yai wanan mahaukacin kudin dan karamin yaro dashi,
Duk kun girmay shi fa amma jiku dan Allah bawani wanda zaitada wani, da cikin ku,
Suraj yace duk iya binciken da zanyu wlh nayi anaje amma banga wani abin tir da yakeyi ba,
In mabaki sani ba kisani mama don yanzune kudin shi zasu kara habbaka saboda ya hada hannun jari da Abu Abdallah na Dubai wanda ake gani kamar yafi kowa yawan dukiya a kasar ta Dubai da kewayenta
Salis wani irin dogon tdaki yaja yace niki duniya zai tara ba abinda zai damay ni
Koma dai may ye ai nasan cewa dan uwa na ne shi,
So ni banga abinda zaisa hankalinki yana tashi haka ba wlh,
Yasa hannun shi a aljihun shi yadauko karan sigarin shi ya kuna yakashe guntun asha nar,
Saida yadan busar da hayakin yace mata shi yatafi kuma daga yau kada akara kiranshi akan maganar Ahmad,
Yabuga kofa yafita abinshi, yawuce zuwa club,
Rai bace tabishi da kallon mamaki tajuyo wurin sauran saitaga su,ma suna kokarin wucewa ne,
Aikawai saitasa masu kuka wiwi,
Suraj ne yje yadan tsunguna gabanta yakama hannayenta biyu wuri guda yace mama kibi sannu
Zamu san abin yi nazuwa dan wani lokaci
Kidaina tayar da hankalin ki haka kinsan kinada hawan jini fa,

Balaifi yanzu na sake jikina sosai nadaina dar,dar din da nakeyi akan maganar Alin kulun kamar kara girma nakeyi,
Don yanzu na zama babban mace nayi wani irin hip, irin na mata masu cikakkiyar kira,
Fatan na yayi man wani dan lub lub tamkar irin na larabawan Pakistan
Kyau na da kamala na sun baiyyana sosai, dakaganin ni saikayi sha,awar kakara kallo na,
Ko tafiyana yasake yanzu ga suturu na alfarma ana sayo mun duk kasar da sheriff yaje aiki zai kwaso muna kayan da matan kasan kesawa na alfarma,
Amal takan min sheri tace wai fadima may sirin wanan canjin naki ne, sainake ce mata ai itace za,a tambaya
Saboda ni gani nakeyi tafini haduwa sosai,,,,itama din tasan cewa nafita haduwa shiyasa bata yarda, idan nace nafita haduwa,
Salimat tadan ji sauki yanzu mukan fita jefi,jefi zuwa makaranta tare da ita, saidai ba kulun ba
Yau ma hakane munyi jiran salim ya zo da mota yadauke, mu a school jin shi shiru da mukayi yasa muka dan fara ta,takowa da kafa,
Dan dogon tsaki Amal taja tace ban san may yasa Salim yake muna haka ba yanzu,
Ni gaskiya da ace mata suna jan mota a kasan nan walahi da sai ince yayan mu yasaya muna wata motar
Mufita harkan jiran salim ko yau saiya gama bata muna lokaci, tadan kara jan guntu tsuki,
Dariya maganar ta tabani nace aiko Salim yana iya kokarin shi damu yaudai ne akadan samu akasi,
Sanan kuma kinsan cewa babu yadda za,ayi yan saudiya su yarda da tukin motar mata akasar su,
Saboda tunkin motar mace yana cikin gurbatar tarbiyan diya mace,
Kinga ashe su ko bazasu taba yarda abada wanan dokar akasar su,
Duk wani abinda zai kawo masu lalacewan matasa da gurbatar addini bazasu taba yarda dashi ba,
Ba muyi wani dan nisa da makarantar ba sosai sai mukaga an park muna wata mota fara sol da ita har farin ta yana cin ido,
Duk inda mota takai da kyau wanan motar takai can,
Amal ce gefen da motar tadan tsaya sai salimat na tsakiyan mu nice agefen karashe,
Nacikin motar yadan zuke glass din motar baki balarabe ne daganin shi matashine saidai ba yaro bane kwarai,, salama yafara muna,
Da larabci yake magana yace muna may yasa muke tafiya cikin rana haka,
Muzo mu shiga ya sauke mu gida, mufada mai inda zamu
Sukan duk sai naga alamar tsoro a fuskan su saboda gani sukeyi zai cuta muna na
Kallo guda nai mai daga yanayin shigar shi har maganan shi sai nagane cewa saboda Allah ne zai taimaka muna,
Amal na bude ma gaban motan nida salimat muka shiga baya,
Basuyi min wani mussu ba duk muka shige ina mai kwatance kawai sai ya gane layin mu ,
Tundaga nan bai kara ko kallon gefen mu ba,
Muna shiru mukayi cikin natsuwa har muka isa gidan mu,
Naimai godiya nafito har zan shige sai yake ce min dan Allah mukama mutuncin mu badadi agan mu asaman hanya haka muna tafiya da kafa,
Godiya nakarayi mai muka shige abin mu cikin gida,
A falo sukai min ca waidaga ganin mutun sai kawai insa su fada motar shi, ni bani ganin komotar shi abin kallo ne,
Daga yau idan zan shigane inshiga ni daya,
Dariya duk suka bani don sai yanzu nagane nufin su,
Saida na samu wuri nadan zauna sanan nadan kalli Amal nace mata
Kinsan abinda yasa ya taimake mu tace a,a nace mata saboda tafiyan da mukeyi dakafa maza na ganin mu wanda hakan baidace ba ,
Wani wanda baida tsoron Allah zai iya shiga wani hali mara kyau idan yagan mu da kafa,
Mace abu ce maidaraja da kima ba abin wasa bace,
Saida na kalle shi tsab nagane cewa ba bu yaudara kishin addini ne kawai yasa yataimaka muna,
Sai alokacin naji sundayi ajiyar zuciya nace mata ai tana ganin shi tasan cewa badan karamin gida ba ne
Tsatsan addin ne kawai azuciyar shi,
Tundaga wanan rana bamu kara yarda mun tako da kafa ba,
Tafiyan mu da kafa shine zuwa masallaci kawai,
Salimat cikin ta yanata kara girma saidai tadan rage yawan alolayin ciki yanzu
Kwadai kawai take so na abu mai sanyi, koda yaushe,
Zaune take ta ta faman shan ice cream roba roba ta aje agabanta,
Dakatar da karatun da nakeyi nayi na tsaya kallon ta,
Ina mamaki yadda take shan ice cream haka a yini batare da yafita ranta ba,
Dan cikin nata yadan taso sama Allah

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment