Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya taimake ta rigunan,ta kusan duk dogaye ne in bashi ba daduk basu daukanta,
Maman Umar ta kawo mata wani dan ruwan shayi mai suna azahab lai, green tea ne kusan matan larabawa idan suna da ciki shi suke yawan sha, don yana rage ma mace yawan zaki da sanyi
Yanasa baby kuzari tun a cikin ciki, sai ciki yakai kaman wata biyar ko shidda ake shan wanan ganyen shayin,
Kusan duk wani green tea yana ma mace mai ciki wanan taimakon,
Zama tayi da cup din tea din a hannun ta don ta tabbatar da cewa tasha tea din
Saboda ralura cewa bata son shan shayin saidai ice cream kawai komai dare zata fito falo ta zauna tasha sanan ta kwanta,
Robobin ice cream din na,kwashe gefe guda na ce mata sai tagama shan ruwan shayin sanan inbata abinta,
Tadan jingina da bango tace min baki ganewa ne Fadima,
Bawai bani son shayin bane walahi wani irin suya nake jin zuciyana yake min shiyasa kikaga ina son insha ice cream din koda yaushe,
Amal tafado dakin ta iske muna wanan rikicin da Salimat,
Tace ma salimat gaskiya tasan cewa mu nan duk bamu san komai gamay da ciki ba,
Amma tunda maman Umar ta ce mata tadinga sha zai taimaka mata dan Allah tafake da shan shi kada azo asamu wani matsala, nan gaba,
Salimat tasa hannu ta karbi cup din shayin ta kurbe shi gaba daya,
Daga inda nake zaune naga tana ya mutsa fuska sai tabani dariya
Duka takai min tace min ai ita ma watarana zata ramane,
Kafin inbata ansa sai wayana yashiga ruri alamar kira ya shigo min
Alin babba ne, tashi nayi niyar yi inda fita daga waje don kada su damay ni da hayaniya
Amal ce tadan harare ni cimin wasa tace min wazan gudu mawa cikin su,
Dadariya nabar dakin falo na koma muna waya inata dan dariya na,
Sam banji alamar mutun ba saidai kaiwa kamshin da ya mamaye min hanci na tako ina
Ahankali na bude idona sai ko nai arba da sheriff tare da salim tsaye a tsakitan falon namu,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
&
AMINCI WRITERS ASSOCIATION GROUP

Almost true life story

Hannu shi ya miko min alamar in,bashi waya na,
Wani iri naji a,raina don da kamar kada in bashi sai wata zuciya tace min kada shedan ya rude ki,
Mika mai wayan kurun duk abinda zaiyi ki gani kiji yafi ki,mai taurin kai don sheriff yafi karfin haka gare ki,
Cikin sanyin jiki na mika mai wayan jiki ba kwari nayi niyar tashi inbar wurin
Alamar inzauna inda nake yai min shima gefe guda yasamu ya zauna ran shi bace,
Kashe wayan yayi yadibi noban wanda nake magana dashi ,
Idon shi ya nuna mai cewa Alin ne, zuciyar shi ji yayi kamar Alin na kusa yau yagane kuren shi,,,
Cikin wata irin murya yace fatima, may yasa wai bazaki min kyakkyawan fahinta ba,
Wallahi da za ace min kece ke wanan halin batare da nagani da ido na ba bazan taba yarda ba,
Kifahince ni fatima bada wani manufa nakafa maku wanan dokar ba sai don kwakwarar hujan dake gare ni akan ku,
Duk kan ku kuna da tabaibayi akan ku wanda yin hakan agare ku babban ilace agareku ,kuna da bambanci mai yawa da da, da yanzu, try to understand me,
Mace mai shekaru irin naku suna bukatar kulawa da sa,ido akan duk wani motsi nasu, don gudun fada ma halaka,,,
Wanan da bi,ar bataku bace, na san koke ba lafin ki bane nasan kowaye Alin nakuma san sherin shi, fiye da kowa,
So don haka ina rokonki fatima daga yau kada kikara barin sherin Alin yayi tasiri azuciyar ki , wanda yin tasirin zai iya ilatar maki da rayuwan ki , agaba,
Kaina dukar ina kallon kasan falon sai kawai na ji kunyar kaina da kaina, da har na bari shedan da Alin yayi nasara akaina kan kin umurni da kuma dokan da sheriff yasa muna, tun farko,
Saidai kuma naji sam yananu baya zargina, don haka zargin da naje tunanen yake min yawanke araina tas
Tabbas sheriff da zuciya daya yadaukeni har cikin ran,shi
Don gashi ya fada min gaskiya kamar yadda zan iya fada ma Amal ,
Yakuma rikeni kamar yadda yake rikon ita Amal din,
Ina fatan zaki fahinci kalamai na da kyakkyawan manufa fatima,,
Cikin sauri na gyada mai kai na alamar eh nafahinta din,
Idona da yacika taf da hawaye dama jira kawai sukeyi su zubo suka samu hanyar silalowa, daga idon zuwa saman fuska na,
Da kyat nadan iya bude bakina nace ma,sheriff dan Allah yayi hakkuri insha Allah ban kara tsallake dokan shi,
Murmushi yayi mainu alamar dacin rai, yadan gyara zaman shi yace nasan ki fatima nasan halikin wanan aikin bayinki bane aikin Alin ne kuma zanyi maganin shi don yasan halina fiye da kowa

Nuna min hanya yayi alamar ina iya tafiya,
Dan dar dar nayi nayi narashin sanin abinyi tukun
Kara dagowa ina mai bashi hakkuri,
Kan sa ya dan rausaya gefe yace pls u can go, ki kula da kanki daga yau,
A sanyaye ganin idon shi na akai na yau ko kauda su bai yi kamar da, nadan juya a hankali nabar falon,
Ido yabini dashi zuciyar shi cike da mamakin yadda halittana ya koma cikin dan kankanin lokaci,
Juyowa yayi inda salim ke zaune yana kallo da sauraren mu,
Yai wani irin sanyayan ajiyat zuciya, gami da kutawa
Yace Alin Alin hmm hmm, zamu hadu, dakai,
Ina shiga daki nafada saman gado ina wani irin kuka mai tsuma zuciya,
Salimat bata hanani ba saida taga nayi kuka mai i,sata tukun don kaina nadan tsaigaita,
Ruwa ta miko min tace insha, ba musu nakarba nadan kurba na mayar mata da cup din,,,
Nakara matse waje guda zuciya tab da takaici da danasanin yarda da naiwa Alin har yai galaba da soyayyar shi akaina,
Gashi cikin ruwan sanyi sheriff ya walwale min manufar wanda ni nakas fahintar shi tun farko,
Nadan kara hadiyar zuciya na takaici na ce araina sheriff zai min daukar maiyawan son maza ce ni, kila,
Sainaji wani irin mugun kunya da nauyi yakamani,
Salimat ce ta dafani shiru tadan yi nawani lokaci tana mai kura min ido,,
Suna,na takira a hankali
Na ce mata na,am a hanakali
Ido ta kura min tana nazarina ,
Ta ce min fadima kiyi hakkuri ki daina wanan kukan haka pls
Sai tai shiru bata kara cewa komai ba kamar mai tunanen wanin wani abu,
Can sai tace min naganki da sheriff a falo dazu, kuma nasan wanan kukan yana da nasaba da ganin da nai maku din dake dashi da salim,
Kifada min ko may ke faruwa da ke haka,
Wani irin nauyi naji azuciya na da kunya, sai na janye hannunta daga dafa nin da tayi,,,
Karo na biyu ta koma kirana tace min kina jina
Kar ki boye min komi ki daukeni tankar yar uwar ki fadima,,,
Wani sanyi naji a raina, naga ai maganar ta gaskiya ce, komai na son abokin shawara,
Dakyat nai shiru na labarta mata komai tundaga farko har karshe dakuma irin taimakon da sheriff yai min a rayuwata,
Bakina ta kurawa ido tunda nafara mata bayani
Cike da mamaki take jin cewa ni ba yar uwa su Amal bace
Asali ma dai ni yar takari ce ba wata ba,
Cikin mamaki take kallo na tana nu,nani,tace min fadima ke takari ce takari fa,
Tai wani dan ajiyan zuciya tace min gaskiya ki gode ma Allah don kin shigo takari da kafar dama,
Don kisan cewa babu wani abu cikin takari banda kaddarar rayuwa kala kala,
Don takari da kyata yake sha in har yasamu komawa gida da lafiyan shi yagode ma Allah,
Ke gashi Allah ya hada ki da dan albarka kin samu har zaki hada digree din ki asanadiyar takari,
Tace zan baki shawara kamar yada duk wani dan uwa zaiba nashi shawara,
Agaskiya baki kyauta ba fadima yadda kikayin nan da ace shi ba mai sanyin halin bane zai iya daukan mataki akan ki, tunda ga kaunar shi ma tayi kokarin kiyaye dokan daya sa maku
Kiyi kokari duk wani doka dakuma abinda zai cutar da shi ko ke ,ki kare shi daga gareshi,
Takara dan dafa min kafadana tace min kikula fadima duk dokar dayasa maku ki kiyaye shi pls, babu cutarwa acikin shi insha Allah,,,
Tagumi nayi da hannayena ina kallon ta
Ina kuka nace mata insha Allah zan kiyaye daga yau,
Tace min to ki daina wanan kukan hakana kisake jikin ki,
Asake nace mata to yanzu yazanyi in ba sheriff hakuri
Tai dan murmushi tace ai yana da saukin kai sosai don da wani ne da abin bai kyau,
Tace min ki kwatar da hankalinki text zakiyi mai kiba shi hakuri,
Sai kuma kiyi kokari kisan yadda zaki nuna mai agaban shi cewa ke din diyace kin rabu da Alin din har abada,
Tadanyi murmushi tace kinga hakan zaisa yasan cewa shi din ya isa dake, kuma ke mai bin umur ni ne,
A sanyaye nace mata nagode kwarai da kulawar ta,
Tace min ai itace da min godiya ba ni ba,
Tunda nashiga ban fito ba dama,
Nadan gyara cikin wata yar riga da ta matse min jiki tam, nadauko wayana da niyar zuwa falo indan samu wani abu, in ci,
Sam basan cewa yau sheriff a gidan mu ya sauka ba ganin cewa wancan karon ba,a nan ya sauka ba,
Ina shiga falon wayana yana tsuwar kira ya shigo ko bandiba ba nassn cewa bakowa bane sai Alin ne
Shine din kuwa, da sallama ta karba wayan Sheriff dake zaune agaban computer shi yai shiru yana sauraren ta da kuma mamakin abinda yakawo ta falo cikin daren nan,
Gurin fridge yaga ta nufa tabude tadauko lemun gwaba da corns acikin leda kujera da ke kusa da ita ta zauna,
Tana shan lemun tana waya sai yagane cewa yunwa yafito da ita yanzu,
Muryan ta yaji tana cewa adake nan yanzu nafada maka cewa banda lokacin wanan agaba na,
Sai yaji tadanyi shiru tana sauraren maganar da ake fada mata, tana kurban lemun da ke hannunta tana jefa corn din guda guda a bakinta,
Tace aiko mada sheriff din ne yace min in rabu da kai yayi gaskiya tunda ya isa akai na,
Zai iya sani zai kuma iya hana ni, duk lokacin da yaga dama,
Balle kawai zato kakeyi, sheriff baiko da labarin ina tare da kai, yanzu,
Kawai ra,ayi nane in maida hankalina a karatuna indaina bata lokacina
Don ni ba yanzu zanyi aure ba ,,,
Haka mukayi ta musayar magana daga karshe nai warning din shi cikin kakkausar murya akan daga yau kada ya kara kirana pls,,
Idan kuma yakara zan fada ma sherrif don yadaukan min mataki akanshi,
Murmushin takaici naji tayi yace ai baku isa ba daga ke har Ahmad din,
Nace mai Allah yafika Alin duk yadda kaso ka cutar da ni Allah bai yarda na,kashe wayan ina ta fada kamar yana a fili inda nake,,,,
Sheriff yasan cewa ban gashi ba har nagama natashi zuwa cikin daki abina,
Cikin tausayin hali irin nawa yabini da ido har na shige part din mu,

Cikin dare nai mai text nabashi hakuri nakumayi mai alkawarin cewa bazan kara yin abinda baiso ba insha Allah,

Hindu na zaune tana fuskantar aziza wacce du ta dan ta da hankalinta,
Cikin tausa murya tace ma aziza gaskiya kamata yayi kisan yadda kikayi dabaran janshi kuje wurin likinta da yasan kan ciki sosai
Tunda naga ke kina ra,ayin hakan,
Hindu gaskiya ban son inyi loosing din Ahmad a rayuwa na don naga alamar in banyi da gaske ba wanan maganar na iya kawo muna matsala arayuwar mu, nan gaba,
Aziza na fada maki cewa ki kwantar da hankalinki tunda har kina son mijinki zan yi iya kokari na inga cewa kin mallaki baby, tare da shi,
Sundan dade suna ta tattaunawa akan yadda zasu shawo kan sheriff zuwa wurin wani likita a kasar indiya, wanda zai diba su da ita dashi,

Bayan kamar sati yai mata waya cewa zai je Nigeria gurin Nafisat,
In akwai abinda taki jini shine taji cewa wai ita aziza tana da kishiya,
Don ita arayuwa bata kaunar kishiya sam koshi don son da take mai ne yasa har ta amince
Kuma ganin da tayi cewa shi ba mazauni guri daya bane,
Yadda sukayi da aziza haka sukayi da Nafisat akan haihuwa, itama din tadan shiga cikin rudu,
Don ta tabbatar da cewa sai Allah in mahaifar ta na iya daukan ciki saboda yawan kwayoyin da tasha tun tana yar secondary tafara harkan shan kwaya,
Wanda ansha warning din ta cewa zai iya mata illa amatsayin ta na mace,
Don haka maganar ya tayar mata da hankali,
Tunda safe ta ziyar ci wani likitansu inda yaba ta appointment cewa taje tadawo aimata gwajin agani ko zata iya daukan ciki,

Saura kusan shekara guda yarage min inkare karatuna, don haka ba bu kama hannu yaro, babban burina shine nagama da sakamako mai kyau
Danagama in wuce Nigeria wurin yan uwana da iyayye na ,
Don babu ranan da ban tunawa da inna a cikin rayuwata,
Karatun sai yazamamin biyu saboda salimat cikin ta ya tsufa sosai yai mata wani irin girma kamar cikin ta gwaye,
Duk zaman da takeyi agidan mu bata taba haduwa da sheriff ba sai yau , koda ya iso itace zaune dirsha afalon mu duk da sanyin A C dake ta aiki a falon ita sai zufa takeyi,
Duk kan mu munfito muna mai sannu da zuwa yazauna yana kokarin cire sock din dake kafar shi,
Drinks nahado mai a ture na zo na aje mai gap da shi,
Wani irin kamshi da sanyin A C suka hade suka canja launin shakar mutum
Yadda naji nashi kamshin shima haka yaji nawa kamshin cikin kasala ya dan kara dukowa yadauki cup da niyar zai zuba ma kanshi sai hannu mu suka hade wuri guda da sauri naga yaje hannu shi yana fadin
Subbahanallah, cikin lunshe idon shi duk wanda ke falon saida yadan waigo mu,
Na tsiyaya mai ahankali yakarba tare da fadin Shukuran,,,
Sock din kafan shi da yacire don ya dan sha iska na duka gefe ina tsincewa, mangashin da nai gyaran kaina na dashi ya kara shaka,
Tun lokacin yadan ritse idon shi cup din drink rike a hannun shi,
Salimat ce tayi kokarin tashi daga inda take zaune sai ta kasa dariyan da yaji na Amal yasashi dan bude idon shi daga zurfin tunanen da yashiga,
Abu kamar wasa sai salimat takasa cire kafar ta ga sheriff a falon duk mun rasa dabaran da zamuyi don ta samu ta tashi don tashi da kyat takeyi,
Dan tabur din da ke gaban sheriff nainiyar indan tura dakafa idan yaga haka zai maida hankalinshi ga tebur din har salimat tasamu ta daga don naga kunya take ji,
Sainai rashin sa,a nafada dani da tebur din duk saman jikin sheriff wanda ke zaune yana waya,
Ji kawai yayi nafado mai a jikin shi babu shiri gaba daya na,
Wani irin yarrrrrr gaba dayan mu muka, naso in mike sai dan kune na ya lake mai a aljihun rigar cort din shi tagaba,
Duk kamshi kaina yana shaka a hanncin shi,
Wanan karon bai samu kiran subbahanallah din ba
Rikeni ya dan yi gam ajikin shi yadda har muna iya jin hucin junan mu, yasa hannu shi guda yazagaye ni dashi, a hankali ya cire dan kunin a jikin rigan shi,,,
Duk wanan abin rabin Idon shi a lunshe yake,
Salimat har tasamu tadaga ,
ni ba,a sake ni ba,
Sai can yadan sakeni a hankali yace min are u, ok,
Kai kawai na iya kada mai tare da mikewa tsaye cikin sauri,
hannun shi na rike da ni har saida yaga na mike da kyau , ya sake ni a hankali,
Sai yace min b/careful
Daga haka sai, yamike zubur yadauki wayan shi dake saman hannun kujera yayi hanyar waje,
Alokacin ita kuma, Amal tasa min wani irin mugun dariya tace min daga zuwa taimakon salimat gashi nan natashi jin ciwo,
Inbadon a jikin yayan su nafada ba da tabur din yajin man ciwo abanza,,,
Duk maganan da takeyi ban fahintan ta saboda wani abu da na,ke jin yana , min yawo ahankali cikin jikina har kwakwalwana ,
Abinda bantaba sanin ana,jin shi a rayuwa ba yau shi ne naji ga jikin sheriff din,
Har takaraci dariyan ta tagama ban ce mata uffan ba
Saboda weak din da jikina yai min,

Yanafita waje cikin mota yashiga da niyar ya bar gidan ko yasamu dan relief a zuciyan shi,
Don tunda yake bai taba jin irin wanan yanayi ba,
Don dai da shi yadauka cewa duk mata iri daya ne ba banbanci,
Ama yau yafara shedawa cewa akwai banbanci sosai a tsakanin mata,
Shi bai tada motar ba kuma shi bai fito ba,
Ahaka salim yazo yasa may shi zuwan salim din ne har yadan yi kokarin saita kanshi,
Suka fita cikin gari da salim din, dole badon yaso ba yau salim din ne mai jansu a mota,
Don shi jin shi yakeyi kamar duk an zare mai lakkan jikin shi gabadaya
Barci daine barawo har ya iya dauka na don da na rintse idon abinda yafaru nida sheriff nake gani,
Duk na rasa sukuni sai juyi nakeyi kamar wacce, ake muntsula, ajiki
Da haka har barci ya sace ni cikin wanan yanayin,
Washegari tunda safe natashi nafada kitchen don in hadawa sheriff abin karin kumallo don idan yana garin ko in munje hutu makkah nice mai yi mai duk wani hidimar da ta shafe shi,
Don kowani yayi mai yakama korafi ke nan kamar zai tashi sama,
Amal bata so sam tasa hannu ga duk wani abinda yashafi aikin sheriff din,
Don gudun korafin shi,
Nasan cewa yanayin aikin su na madina tunda safe suke fita su dawo zuwa karfe dayan rana,
Shiyasa nake tashi da wuri in mai break fast,
Ina gamawa na fada dakin mu don indan watsa ruwa a jikina,
Salimat ce na iske cikin wani irin yanayi, naban tausayi,
Gurin da take na nufa cikin sarsarfa, tana kasa kusa da hanyar shiga bayin mu
Ta dan zauna tayi dai,dai da ita tana maida nunfashi guda guda,
Dasuri nakarasa gurin ta ina mata sannu,
Kai kawai tadan daga min alamar ansawa ta na cizon bakin ta da kyat sai gumi dake ta zubu mata kamar an,tsa mata ruwa,
Duk sai na firgice na duka saitin ta ina mata sannu,
Tace min cikin karfin hali fadima kila haihuwa zan yi,
Ido waje nace mata what cikin karfin hali ta daga min kai,
Nace to barin kira maman umar tazo muje asibiti ko,
Har nakai kofa sai naji tayi wani irin nishi gami da salati mai karfi,
Aida sauri nayo kanta ina fadin sannu salimat
Wanan karon bata karba min ba ido kawai ta zuba min duk sun firfito waje,
Sai naga tafar wani irin nishi makarfi
Da sauri na rungumay ta ina kokarin daga ta sai naji duk taimin wani irin nauyi, kamar ba salimat ba,
Kafin in kifta ido har ta sullubo yar baby ta tana fama calara ihu irin na jarirai,
Wani irin mugun tsoro naji yakamani, don bans an abinda zan iya taimaka mata dashi ba,
Idonta a lunshe tana hamdala tace min fadima kira maman umar da sauri tazo
Aiko aguje na kwasa da gudu na manta sam banda wani rigan kirki ajiki,
Sai falo ina ihun kiran maman umar,
Suna falo suna break sukaji ihu na kowa sai ya watso min ido don jin komai yafaru hankalinsu tashe,
Da sauri maman umar tafito kitchen din cikin rikecewa,
Mu kaci karo a kofar kitchen din da ita,
Ina haki nace salimat ta haihu,
Duk a rude suka tashi tsaye cikin mamaki suna kallo na,
Maman umar da sauri ta shiga dakinta ashe ita dama da shirinta take,
Muka bita diiiii abaya sai dai wanan karon akofa na tsaya munajin baby nata tsala ihu duk ta karade gidan ,
Sai da tagama gyara su sanan ta miko muna yar baby fara sol da ita kamar uwarta, an nade ta cikin farin shawul,
Amal akafara ba sai ta wuce direct inda Sheriff yake tsaye nisa da mu cikin damuwa,
Saida yakare mata kallo ban sha,awa sanan ya kalli gefen da nake tsaye yace min indauko mai dabino da ruwan zam,zam cikin sauri natafi na debo mai su nakawo mai
Na iske yanawa baby kiran sallah da yagama yakarbi dabino yadan tauna yasa mata abaki,
Yakama dan lasa mata ruwan zam zam din,
Saida yagama yadago kai mukayi arba dom dama duk mun kewaye shi,
Da sauri

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment