Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muryan ta na tsinkaya cikin murmushi take magana daidai lokacin ta taso daga inda take zaune zuwa gurin da muke,
Cikin murmushi take cewa fadima unguwa za mu tafi yanzu , Ahmad yace kece zaki rakani ko tana fadi tana wani kashe ido irin na yan duniya,
Gaba na yadan fadi don jin abinda tace
Sai kawai na tuna da abinda naji tana fadi a waya,
Ganin da tayi kamar ina dan tuna ne yasa tace min ko baki son fitar ne yau, ai sai in fasa har zuwa gobe
Sai mu fita ko, takalleni tana wani kashe murya
Saida nadan yi ajiyan zuciya saina ce da sauri, haba, haba,
Ai kawai muje barin dan sa asshifal dina a sama kawai,
Nakoma daki nadauko wata sabuwar Asshifal, baka mai kyau na za saman jikina nada nan nagyara daurin dake kaina ya koma rolling sai na aza dan gyalen wanan Asshifal din saman rolling din kana gani na kasan nayo shigar mutanen musuluman kasar, Sydney
Ina fitowa falon inda take jira na muka hada ido da Amal saita sakar min wani irin uban harara,
Cikin larabci tace min indai bi a hankali da wanan
Murmushi kawai nadan yi mata don kada aziza ta gane cewa da ita mukeyi,
Yusuf driver ne zai ja mu, muna shiga mota sai tace min ince mai kada yai tuki sosai yabi da ita a hankali pls,.
Haka ko yakama tuka motar a hankali yake tukin ,
Naima yusuf magana nace yasa muna ki,ra,an Shuriem don ina son kira,ar shi sosai,.
Idanuna nadan lunshe ina sauraren kira,ar ina kuma bin shi a hankali, sai ina tuna ne a gaskiya ba abinda yakai alkur,ani dadin sauraro,
Muryan Aziza naji tana cemin acikin hausa shagon, saida kayan masu kyau zamu fara zuwa idan mun gama sai mu tafi wurin gyaran jiki ,,
Sabon shagon da aka bude a cikin Bin,Daewood na kai ta sainaga duk ta rude saboda kyau wurin
Komai akwai acikin shi shagone tundaga sama har kasa sai inda idon ka ya tsaya, da gani,
Ganin cewa danayi gamu cikin massalacin Ka,aba ai yakamata mudan yi koda nafilla raka,a biyu ne kafin mu wuce,
Nace mata idan mun gama sai mu tafi muyi sallah da dawafi, ko
Saida ta dafani tana murmushi tace min idan munce mu tsaya yin dawafi ai zamu makara da zuwa gurin gyaran jikin mu ko,
Sororo nayi saboda mamakin ta, ga wasu can nason suzo kota halin ka,ka
Allah bai basu ikon zuwa ba, ita gata tasamu har tana barin damar ta a banza,
Haka nabi bayan ta da mamaki fam a cikin zuciya naita
Saidai ina ta jiran inji ko zanga wani abin da yashafi maganar da naji tanayi a waya ranan
Sai banji komai ba shiru,,
Hakan yasani nadan sake jikina da ita
Munashiga shagon kayan kyalkaylin mata, sai, tafara jidan kaya masu kyau
Masu kuma tsada hatta su undies sai da muja jido su kamar hauka,
Har zan shiga wani shagon saida kayan kamshi sai ta kirani,
Da sauri nadawo wata riga ce mai masifar kyau irin tamu matasa yan mata,
Kala kala different design masu kyau, kowani da gyale ko wani abayan hada shi mai kama da alkyabba,
Cikin sha,awa tadinga gyada kai, tana, yaba kyawon kayan tana cewa wanan kan sai ku yan mata, fadima,
Ina kallonta takwashi kusan guda biyar kala kala,
Ina tsaye gefe ta biya kudin kayan ,mamaki kawai nakeyi irin yawan kudin da naji an ambata akan kudin da mukayi sayayya haka,
Saina tuna cewa ai ita,
matar sheriff ce fa ita dole in ganta da kudi hakana,
Muryan ta naji tana cewa Sannu fadima na gajiyar da ke yai ko,
Na gode kware ki ji bayau ba ina son fitowa inda zaga gari rashin samun abokin tafiya ne yasa ban fito,
Saida Ahmad yace min in je dake ai kin san ko ina a garin ke,
Tace sai kuma ban samu fuska agurin kuba kin san dangin miji tundai Amal na fuskanci bata ra,ayina takare maganan cikin muryan tausayi
Nace a,a haba dai aiko muna son ki sosai kedin ai matar,yayan mu ne kin ga ko dole mu soki,
Tunda muna son shi, aidole muso duk abinda yake so ko,
Cikin nishadi tace min kai amma kuwa yau naji dadin zancen ki walahi
Ban san cewa haka zan samayki ba ai da tun tuni mun dade da shakuwa a tsakanin mu,
Rashin ganin fuskan da banyi ba ne agurin ku yasa ko zama ban son yi wurin Ahmad,
Bansan lokacinda da wata yar dariya ta subce min ba nace kai haba hjy saboda mu zaki ki zuwa gurin mijin ki.
Muda ba ma,a garin muke ba, saida irin haka in munzo kawai, sha mudan wuce, abin mu,,,
Tsayawa tayi tana min wani kallo cikin mamaki tace hai fadima,
Fadima kema kinsan cewa gurin ki kawai nake dan samun sauki acikin ku muryan ta yai wani rau, rau kamar zatayi kuka,
Ban iya cewa komai ba don tabani tausayi harga Allah,
Haka muka karasa har inda muka aje motar mu a bakin tin da ke gefen haramm,
Daga nan muka wuce wurin gyaran jiki,
Ga mamaki na nadauka ko itace kawai za ai mawa sagashi dani da ita duk an muna
Nakoma kamar wata yar bakaken indiya komai na sur mace da nake da shi yakara fitowa tsab ajikina,
Tun a mota Aziza ke yaba irin kyaun da nayi sai murmushi nakeyi kawai don nasan cewa ba karya tayi ba ,,
Saida muka kusa shiga unguwar mu ne take ce min duk fa ke na siyo ma wayan nan rigunan ,
Cikin mamaki na,kalleta nace ,a,a aikin san cewa bani kadai bace sai dai ni da Amal ,
Sai ga tadan bata rai kadan can kuma tadan sake ranta tace kece kika rakoni kuma kedai na siyawa ,
Ba matsala zan raba da ni da ita kin ga tasamu albarkaci na aiko,
Har muka kara gida tana min hiran jin dadin da tayi na ganin nasake jiki da, ita,
Ko ba a fada ba nasan cewa Sheriff din mu yadawa daga tafiyan da yayi taniyar yin kwana biyu a babban headquarter kasar saudiya watau Riyadh,
Da mamaki nakai kallona ga motar shi da naga yana yawan shigarta,
Kamar Aziza ta gane mamakin da nakeyi azuciya sai tace ashe har sun iso don dama yau ba zai kwana a can ba don suna da wani meeting da ma,aikatar su gobe, Insha Allah,,
A falo muka samay su duk kan su har almustapha sun baza wasu takardu a gaban su suna dibawa,
Sallaman da mukayi ne yasa kowa dagowa kai don yaga ko suwa ye,
Dammm gaban shi yafadi saboda ganin da yayi ko yaushe kara canzawa kawai nake yi,
Cikin kwarewa da shagwaba take mai magana, har ka iso Sweet habibi,
Kai kawai ya kada mata alamar eh , ga kaya ahannu mu niki niki ta,isa inda yake tadan man na mai kiss a tsakiyan goshin shi,
Sai ta,Zube saman kujerar dake gefen ta tana cewa wassh Allah na duk nagaji wallahi,
Aikin da sukeyi yadan aje gefe guda yadan kalle ta yace,
U are to lazy, wanan dan fitan da kikayi kike cewa wai, kin gaji,
Suna juna wani irin kallo cikin shaukin so,,
Kayan nazo gaban ta na zube gefen kujera datake zaune,
Kai yadago A,hankali ya bini da kallo sai kuma yawani lunshe idon shi a hankali kamar maijin barci ,
Kamshin turarain da yaji ina yi duk yakara rikida shi,
Kamar mai rada yace mata wai har ina kukaje ne haka yau kuka kwaso wanan kayan mai yawa,
Ke kaya basa isan ki dai ko nuna ni tayi da hannu ta guda tana cewa yau ai duk kusan sayayyan ga mai su can,
Muna hada ido da Amal takara sakar min wata uwar harara da yafi nadazu,,,
Ida nake tsaye ina,sha wata uwar harara daga Amal yadan kalla lokacin kuma hararan da Amal take min yabani dariya,
Sai yayi sa,a ina dariya a lokacin, Abinda yadade baigani ba ke nan tun ina yar karama a Riyadh lokacin da nake shiga cikin ruwa ina wasa agidan shi,
Murmushi ne ya subce mai ba shiri saboda tunawa da yayi da wanan lokacin
Saboda yaga yadda nake wasa daruwa har dawo yakeyi ya tsaya ta glass din falon shi yana kallo na ,,
Saboda haka kawai yaji in burge shi dan banda tsoro ko fargaba kai tsaye nake abina,,,
Aziza ce tace min inzo in kwashi kayans intafi dasu,
Tazabe duk wanin abinda take bukata daga ciki tabar min sauran tarkacen da rigunonin,
Da alama sheriff yaji dadin hakan da tayi har cikin rashi yace mata
Kai amma dai wanan fitar dama na tane ko ,
Tadan rausaya kanta tace aikasan dole in saya mata tunda har ta bata lokacinta ta rakani batare da nuna gazawanta ,,,
Ina kwasan kayan gurin Amal na nufa direct dasu nara dai dai nace mata ta zabi duk wanda take so tabar min kashi guda,.
Dariyan yake tayi ko shi don yayanta ya gurin ne don kada yace wani abu da bata karbi kayan ba,
Amal tace a,a ki bari kawai in dauki wanan,
Wani dan rigar barci kawai ta dauka,
Tundaga wanan ranan wani irin shakuwa da amin taka ya shiga tsakani na da Aziza ,,
Amal tai min fada taimin nasiha tace inyi hankali da ita don yar duniya ce,
Badan Allah take so na ba ita tana ga da wani manufa take jana ,a jikin ta,
Sai naga cewa kawai, kamar dai don basu ra,ayinta ne kawai,

Yau shiru tunda safe banga Aziza ba a waje ganin da nayi cewa anytime tafito sai ta nemay inda nake ,
Yasa da banganta a waje ba na hausama zuwa dakin su,
Kwance take rub da ciki nai sallama a hankali ta ansa min ,
Tajuyo daga rub da cikin da tayi kwancen, sai naga fuskan ta ya kunbura idon ta da almar tayi kuka ma,i,shin ta,
Subbahanallah nace da sauri na isa gurinta ina mai kokarin dafa ta,
Nace cikin rawar murya hjy mai yasa may ki ,ko baki da lafiya ne,
Duk lokaci guda na sako mata wanan tambayar a jere da juna
Girgiza min kai tayi kamar karamar yarinya,
Ta, bude baki da kyat tace min babu ko daya
Fadima
Matsalata tafi karfin fahintar ki kona fada maki bazaki gane ba saboda,
Ke yarinyace, shiru nayi kamar ina na,zari, can nace to amma anty aiko banza gane ba ai zan yi kila taimaka maki ta wani hanya ko,
Saida tadan shere wani hawaye dake shirin fito mata daga cikin idonta, ta hade miyau da karfi sanan ta mike da ga zauna
Hannaye na takama duka biyu ta hada wuri guda tace Fadima inda zaki fahince ni da kin san cewa muna cikin tashin hankali dagani har Ahmad saboda matsalar da ta samay mu,
Sai duk naji na matsu da insan kowata irin matsala ce haka wadda har yasa wanan jarumar matar kuka haka ,
Dan Allah hjy ki daure ki fada min koma maye ko zan san abin yi pls,
Fadima muna cikin matsala rashin haihuwa nida Ahmad munje asibiti likita yace bazan iya daukan ciki ba,
Sai kuma tasa kuka wi,wi,
Sai naji duk hankalina yatashi,, saboda wanan maganar ba karama bace ga duk wani mahulukin da yasan ciwon kanshi,
Tana shere hawaye taci gaba da fadin ,sai wanan test din da mukayi na karshe likita yace muna inda zan samo wata wacce zata taimaka min asa mata cikin ma,ana ai mata dashen cikin
Idan ya fara girma sai amayar min da abina yace yana ganin haka zai sa in samu baby,
Kinga kuma shi Ahmad baya ganin laifin kanshi sai nawa kinji halinda naje ciki fadima, tanayi tana kallon fuskana don taga irin re,action din da zan nuna,
Fuskana fal da tausayin su ban san lokacin da nafara kuka ba ,wi,wi, nima don ba karamar magana bace wanan,
Mutun kamar sheriff ace ba zai haihu ba, treble,,
Muryanta naji tana cewa amma fa kada ki fada ma kowa wanan sirinane da mijina na fada maki,
Saboda yarda da nai miki yasa har na fada maki sirina,
Hmmm hmmm
Wani sabon kuka nasa mai tsuma rai an muka rugumay juna mukai ta kuka har saida muka gaji,
Nakoma dakina fam da tunane da tausayin su,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
6⃣7⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,

Cikin dare na kasa yin barci mai nauyi saboda yawan tunanen da ke ta addabata,
Juyi kawai nake yi ina faman ajiyan zuciya da dan guntun tsaki,
A, gaskiya na tausaya ma sheriff din mu so sai yanzu ace duk tausayin shi da mutuncin shi bazai haihu ba,
Ashe haka wasu Allah ke halittan su, batare da haihuwa both miji da mata,,
Saboda ni nadauka cewa mutun guda akan ce baya haihuwa mijin ko matar,
Amma su sai,gashi wai duk kan su case din su gudane,
Babu mai karfin haihu daga cikin su,
Dan sanyin da naji shine cewar da tayi idan an yi dashen cikin za su iya haihuwa insha Allah,
Kwancin bai min hakan yaban damar mike na shiga bathroom na dauro alwala na fara nafila ina fadin bukata na, a wurin Allah,
Nafilan nan da nadan samu na gabatar yasani jin sanyi a zuciyana ,
Har na dan samu barci maidan nauyi yadauke ni zuwa asuba ,
Hakan ne ma yasani makara da sallah asuba,
Saida gari yadan yi haske nafar ka zubur da salatina a baki,
Saidai duk jikina ba karfi hakana naje nadauro alwala,
Ina zaune inda na sallamay sallah asuba ina ta kwarara ma sheriff da iyalin shi addu,a,
Shawar da na yanke tun cikin dare shi na yi niyar aiwatar wa,
Amal na dakinta kwance nafito nace mata zan je masjidul nana Aisha ,,
Da mamaki ta kalleni daga kwancen da take tace min tunda safe haka,
Murmushi nadan yi mata, nasamu gefen gadon ta, na zauna ina gyara belt din takalma na,.
Ido takura min har na kare daura belt din sai tace min may ke damun ki fadima,
Cikin dan basarwa nace mata kamar ya fa,
Hmmm kawai tace min,
Sai kuma tace bana son ki sa kanki acikin fitinar da ba zai amfane kiba, wlh
Saida na mike tsaye da kyau nace mata ba wani fitinar da nasa kaina, aciki Amal kece dai ke hasashen hakan,
Amma for me ba komai ina fadin haka na sa kai nabar dakin
Zuwa masjidul bai dauki wani lokaci saboda sanin hanyoyin da na yi acikin sauki,
Ina isa nai addu,a na dauro niyar umrah nadinga addu,a da larabci, da hausa kai har mada turanci duk na hada ,
Saida na gama dawa,fi, nadawo daidai saitin indararon nan naita zuba addu,a
Saikuma na koma daidai kofar dakin naba mukamin ibrahim baya, nadinga kwararo addu,a agurin,
Dalilin dayasa nai haka gurin hjy Laila nataba ji suna hira da hajiyar mu cewa indan mutum yana neman haihuwa koda dan uwan shi ne keson haihuwa,
Sai yaje yayi dawafi, ga bakwan karshe saika dada addu,a agurin indararo saboda anasa rai cewa guri ne da duk abinda ka roki ubangiji agurin zai ansa ma insha Allah,
Indan ka gama sai ka dawo daidai saitin kofar shiga shi ai,nihin dakin ka,aban ka tsaya tsakiya, inda hali ka dauki ruwan zam,zam kayi wanan dawafin da shi,
Karoki Ubangiji Allah bukatar ka insha Allah Allah zai karba ma mutun,
Wanan ruwan zam,zam din sai kaba wa wace ko wanda ke da lalurar haihuwa ko wani ciwo yasha ya shafa tare da bissimillaj,
Sanin danayi cewa Aziza bazata sha ruwan ba kila ko nakai mata yasa ban dauki ruwan nayi mata dawafin da shi ba,
Saidai addu,an da na tsaya tsakanin mukamin Ibrahima da kofar dakin ka,aba nayi na Allah yataimaka ya bawa sheriff din mu haihuwa mai albarka a rayuwan shi,
Tare da kwararo wa sauran al,umman musulumi a ddu,a,
Daga karshe na tsaya daga can gefen yamma kadan nadibi ruwan zam,zam nasha sai nayi nafila raka,a biyu
Nagode ma ubangijina subbahanahu wata ,ala,
Dana gama nadade gurin zaune na zubawa dakin ido sai naji wasu hawaye masu dumi suna zubowa daga ido na,
Nadade a hakan sannan natashi nasamu guri na zauna a gefe guda,
Ranan anan nai sallolina har i,sha,i ina gurin,
Sai da dare na zo hanya don in tare taxi zuwa gida sai na dinga jin hayaniya,
Ko ban waiga ba nasan cewa yan bagaladine ke kokarin kama wasu daga cikin yan yawon takari,
Hakane ne kuwa don dai daga inda nake inajin muryan su sunacewa Nigeria,
Duk da hayaniyar da akeyi agurin bai hanai jin kuru,ruwar matar da aka kama ba
Azuciya na ,na,ce ya Allah yasa mutanen mu su daina wanan kazamin da bi,ar , tazuwa yawon takaru ba lasisi shiga kasar,
Idan ma mutum na so za,s iya bashi, lasisi idan har yabi ta hanyar daya dace,
Saida na ji cewa ni a halin yanzu zan iya zuwa ko ina saboda ina da kardan zama akasar ,,
Wanda bakowa ne yai min wanan hanyar ba sai sheriff Ahmad Lawal Zanna,
Zuciyata jinta nakeyi tai min shakat kamar an cire min wani nauyi acikin ta,
Haka na dunfari gida cikin wal,wala da sakin fuska ba wani damuwa atataredani,

Har kusan karfe shida sheriff baigan ni ba kuma baiga, na fito waje ba koda ko falon gidan ne,
Duk iya kannewar da zaiyi yayi har dai yakai ga tambayar Amal cewa yau bai gana fito ba koda sau dayane waje, ko lafiya nake,
Sai wannan lokacin Amal ke mai bayanin cewa tunda safe natafi masjidul
Kuma dama nace zan dan dade yau ban dawo ba,
Don haka lokacin da na iso gida suna zaune shida Aziza saman dinning table suna cin abin dinner,
A hankali nayi sallama cikin katafaren falon gidan namu wanda ba lalai bane wanda ke ciki yaji muryan mutun da ga kofar shiga,
Ganin da nayi masu zaune su biyu suna cin abinci yasa nayi niyar wucewa batare da na gaishe suba,
Aziza ce tafara gani ,wanda a zahiri ba haka abin yake ba, sheriff yarigata gani na sai yai wani irin sanyayan ajiyar zuciya,,,
yadai daure ne yai kamar bai gan ni ba , don alokacin inda ban dawo ba da saura kiris yaja almustapha suje bida na,
Aziza ce ke min fadima yau ina kika shigane haka tunda safe naje dakinki yafi sau biyu ban ganki ba,
Naso mudan fita zuwa cikin gari kadan,
Saina dan yi mata murmushi yake kawai badon komai ba sai wanda ke gefenta dake min wani kallo
Da ban iya cewa ga irin shi ko ma,anar shi,
Bangaren da nake tsaye yadan kalla yace min ina tafi ,
A marairaice kamar mai shirin kuka nace mai masjid natafi,
Yar karaman harara yasakar min yana kada spoon a plate yace,
Oho ashe yanzu duk inda kiga dama saiki sa kai kawai ki tafi batare da sanin kowa ba,
Nankan shiru nayi masa don banda ansan da zance duk da dai na fada ma Amal cewa zan fita,
Yace je ki duk abin da kiga yafi maki je ki yi tunda ba ki under control din kowa,
Jiki ba kwari batare da kuma na iya cewa yayi hakkuri ba na shige ciki, abina,
Tunda dai nasan cewa ba wani mugu wuri naje ba,
Ina shiga daki,na Ko Nanfal dina ban cire ba,Amal tashigo dakin tana cewa
Gaskiya yau fadima baki kyauta tun safe fa kika fita duk da nasan cewa ga inda kika tafi ai bai kamata ki kai har dare haka ba,
Don nagajarce zancen ko zan samu saukin bacin ran da naji nace,
Amma dai Amal na fada maki ai kafin in fita ko,
Kafin Amal tace wani abu sai naji murywn sheriff yana cewa
Don kin fada ma Amal ni kin fada min ne ko,ko zaman Amal ki keyi a nan,
Kaina yana kasa don ganin da nai wa sheriff tsaye a tsakiyar dakina
Yacigaba da fadin idan wani abin yaje yasa may ki can fa ya kike son muyi
Ace tun safe mutum yabar gida sai yanzu yana mai diban agogon hannun shi,
Acikin sanyin murya nace mai dan Allah kayi hakkuri bazan sake irin haka ba insha Allah,
Ido yadan kura min nadan wani lokaci kamar mai nazari na tukun sai kuma ya juya yabar dakin batare da yakara magana ba,
Dagani har Amal wani irin ajiyan zuciya mukayi na fargaba,
Amal takai zaune saman gadona tace min gaskiya Fadima yau kin batawa yayan mu rai sosai wlh,
Yayi fadan fitar ki ke kadai batare da kowa ba yace wai laifina ne da nabari kika fita kedaya ban hanaki ba,
Murmushi nayi nakai zaune ina cewa haba dai sakace wata bakuwar gari ,
Bace wa zan yi halan,
Kada dai ki kara irin wanan halin pls,
Kofar dakin aka turo maman Umar ne dauke da abinci kala kala cikin wani dan keken tura abinci zuwa dakuna,
Cikin mamaki naje cewa may yasa takawo min abinci har daki aida tabari infita waje in diba ko,
Dukawa tayi tafara zuba abincin tace min sheriff yace mata ta tabbatar da naci abinci kafin in kwanta,
Amal dake zaune gefe na tadan tabe baki tace kaji yar gatan yaya ko har da abincin ma sai yasa a,yi gadinki har ki ci ko,
Maman Umar tace

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment