Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauri naga ya wurga da tie din shi saman gado, yafita waje da sauri,
Ina ganin fitar shi nai sauri na suri yar jakata na fita cikin sauri nabar gidan,

A kwance take abinta saman gado tayi wani shamay shamay da ita tana ta kwasan barcin ta a hankalin,ta kwance,
Daskarewa yayi wuri guda yana mata kallon takaici da tsana,
Mace kamarta ace,bata ina kwanciyan cikin kimtsi ba, ko na tsuwa,
Wanan ai sha shan ci ne,
Kwace take tana saye da yar doguwar, riga, kusan duk rabin cinyarta a waje yake, tim,,
Saida ya gyara tsayi yadan lalubo natsuwar shi saboda takaici da haushin ta da yake ji,a lokacin,
Gurin gado ya nufa rai a bace, don yasan cewa ko sallah batayi ba a lokacin,
Labule dakin yadan daga sai hasken rana yadan baiyana,
Dan bubuga mata kafa yayi tai wani irin mika, tadan bude ido da niyar yiwa mai shi masifa,
Sai sukayi ido biyu da sheriff, dake tsaye fuska tamau, a gaban ta,
Harara ya dankara mata yace mata kinyi sallama dai kuwa,
Takara yin mika tace yanzu nake batun tashi in yi fa,
Yakara tsayawa saitin kanta yace may kike yi a dakin Fatima kuma,, cikin wani irin dakiya yai mata magana,,
Ban fahince kaba Ahmad ,
A ina kake son in sauka dama
Cikin mamaki yace mata duk gidan nan ba wani daki ne sai wanan da Fatima take aciki,
Daga kwance tai wani gyara kwanciyar ta tace ina, wanan shine dakin ka,
Kuma aciki na sauka,
Shout up my friend, baki da ko kunya da zaki fadi wanan maganar,
Itama dai wani mikewa tayi zaune, tace,
Ta dankara mai wata muguwar harara, tace ban fahici hausar ka ba ada amma yanzu nagane nufin ka sosai
To bari kaji, niba wulakantancciya ba ce, balle ka wulakantani ka kaini masaukin baki kace in sauka a ciki,
Ya buga mata tsawa da bai taba mata irin shi ba sai yau yace,
Ke dan Allah ki yi min shiru, in ba haka ba, yanzu ki san ko waye Ahmad,
Tayi murmushi ta mike tsaye daga zaunen da take,
Tazo gaban shi, gab da shi ta tsaye da kyau a gaban shi tace , au tau,
Ashe da ban san kowaye Ahmad ba zaune nake da kai kawai,
Tayi wani irin murmushi mai nuna takaici,
Ai,Saika gwada min ko kai waye yau in gani tunda na shiga dakin yar kwailar matarka saboda ita saika dake ni ko,,,
Tana wani jijiga jiki da kafa,
Kafini sanin ko wacece Aziza,kuma kasan kadan daga cikin aiki iskancina ya damay naku ya shanye,
Ahmad ni bani kwadayin dukiyar ka kai kawai nake so,
Wani malalacin kallo yai mata a lokacin da tace ita bata da mu da dukiyan shi,
Batasan cewa CCTV ya tona mata asiri ba ko,
Taci gaba da fadin akan wanan yar kwailar baka isa ka wulakantani ba,don kaga ina sonka har za kai min wulakanci a kan wata,mace,
Yau ran yan maza ya baci so sai, gashi ba halin shi bane bugun mace ko zagi,
Kafin yadauki wani mataki maman Umar tashigo daki don dafa mata ruwan zafi
Ganin da tayi Aziza natawa sheriff masifa kamar zata dake shi, ta juyo zuwa gurin su da sauri
Kafin tai magana sai ya juya yabar dakin rai a bace,
Dakin da nake yakoma yana shiga ya iske har na wuce ko,
Ya samuri ya dade a tsaye yadan dafa bango, ya na ta tunane,
Idanu shi sun juye sun yi ja jarir tunda yake baitaba tozarta irin yau ba,
Wai matar da yake aure ce hakana kamar zata dake shi,
Inda ace shi mai dukar mace ce bugu daya zaimata sai an zuba mata ruwa,,,
Itako Aziza yana fita dakin idon ta yakade, yai jawur, ta dinga tuna ko ita wace da har za,ai mata wulakanci akan fadima,
May fadima ke nufi da itane a rayuwa yadda take son AhmΓ d ace yau, shida kan shi har zai mata wulakanci akan yar aikin matar shi,
Wasu hawaye suka zubu mata na bakin ciki ta fada saman kado ta shiga rusa wani irin kuka,
Saida ta gaji ta mike don kanta, tace fadima sai na ga bayan ki kafin in bar kasan nan,
Gobe bazaki kara tsaya min agaba ba,,,

Gidane ginan laka irin na kauye duk da gidan tsohon gidane bazaka gane ba saboda sabon yaben da akaiwa gina ga sabon jinka asa asaman rufin dakin ya koma kamar sabo,
Ta kofar dakin ayin mai sabon shafe irin na kauye laka laka,siminti ,siminti,
Darni gidan na subur karan dawa ne akayi amfani da shi,
Ga icen zogala da na durumi an zagaye darnin gidan da su gefe tulun na ruwa ne da babban randar ruwa suma sabbi fil da su,
Daga can gefe han yar zuwa yauce (makewayi) turke ne na raguna manya manya sai wani fasashe rada inda ake zuba ma dabbobin abinci,,
Ga kaji nan sunkai goma irin na gargajiya suna ta kiwo atsakar gidan,
Tafito dakin da tana gyara daurin zanin ta da ke kokarin banyewa irin daurin zanin yan kauye da ake tankwahewa gefe guda,
Hannu guda na dauke wani dan karamin kwarya,
Cikin kwaryan gumba ne wanda zata dama kunu dashi don karin kumallin su na safe,
Inna yar Kulu ke nan mahaifiyar Fadima,da ke zaune a garin dogon daji mai rijiyar biri,zam,zam dake acikin jahar sokoto,
Duk da mutanen kauyen nawa inna yar kulu kallo wata wacce ta ke cikin wani irin daula ,
Ga kiwon tumakai da akuyoyi da takeyi, ga kuma shanu har biyu da ta turke gefe guda,
Duk cikin kudin da Ruggaiya ta kawo masu ne, duk da inna taki karban kudin duka a hannunta,
Bakin murhu ta zauna tana dan gyara iccen da ke kama da kara sai tarin hayaki da ya bude gidan dashi wanda har makwabta a na iya hagen shi,
Alamar cewa ke nan ta hura wuta a gidan ta kasan cewa bakowani gida ake dama kunu ko yin wani abin kari ba,da safe,
Saidai fura da za,a aje a cikin wata r langa ko kwarya ko fanteka,
Wanda aka dama tun jiya ko kuma an kirba shi tunjiya, yayi tsami har yagaji,
Shiza asama ruwa a motsa kowa yazo yadinga diba, a yar korya ko roba ana sha,kamar yadda kowa yasan kowani kauyen hausa sukeyi,
Abinci sai ranan jumma,a ake dan yin tuwon shikafa ko na dawa, yara su dinga murna suna fadawa junan su cewa yau jumma,a
Kowani gida za,ai girki tuwo da miyar yakuwa da alaihu, da kabewa,
Wasu kuma tuwon kullun dawa da miyar danyar kubewa ,,ko kuka, fara fat da ita,
Hakan yasa suke ganin cewa inna ita tanajin dadin ta sosai don tun filazan ita gidanta tana dafawa yaranta abinci ko ba dadi sai sunyi shi sau ukun nan,,,
Gidan inna ko yaushe tsab yake da shara, duk da kiwon da takeyi bai hanna ka gane cewa tayi shara, a rana,
Saida ta gama dama kunun ta sa ma mariya kira wacce ke daki tana shirin zuwa makaranta boko ita da dan autar inna Abdul wanda suke cewa datti,
Mariya tafi cikin kayan makarantan ta tazo inda inna ke dan motsa mata koko a cikin wata yar roba mai fadi,
Inna tace mata ta koma daki ta dauko sukari a cikin leda wanda suka siyo jiya ya rage,
Alokacin Datti ya shigo gida da yar leda baka a hanun shi wanda ya sayo kosai da shi,
Ya mika wa inna laidar tadan jawo wani dan plate din silver ta kasa masu kosan kashi uku ,kowa guda guda,
Saida Datti ya fara shan kokon ne yace inna ai na manta ban hwda maki ba,
Kai wai wani irin yarona haka duk sanda kattaho cin abinci sai kayi dumi, (magana)
Waga dabiar banzata koda yaushe ina hwda maka,
Ko ni,an inna ki kasani ko wani sabon batu na yyajiya shina shika son shi,hwda muna,
Ke,ke ke banison shegantaka kejiya,
Mariya dake gefe takalli Abdul tace tadan tausa murya don kada inna taji su tace,
Shin minana kaka son cewa Adullahi,
Ke ko ni an bashi tun da wanda abin yya shahwa tace in bari to ni mi nika hwdi kuma,
Inna dake jin su ta waigo takawai mariya rankwashe akai tace
Kai waga diya anyi yariyar kawai,
Shin kuna sauri kutaizuwa makarantaga ko ko sai kun yi abinda mallam yattabi jikin ku,
Abdull daya tashi yana sa takalmin shi na roba na makaranta saida yakai kusan fita bakin gida ya waigo inda inna ke tsaye ta sance kullin kudin da tayi a gefen zanin ta,wanda zata mariya kudin kashi, haka yara ke kiran irin wanan kudin safen da uwaye ke basu dan sayen dan wani abu,
Ya waigo cikin dan daga murya don inna taji maganan,
Yace mariya ke,
Macen nata wadda akacewa ta sace fadima ita ta naggani jiya ana taratara da inta anka hiddo ta cikin mota wai bata da lahiya ,
Tasamu mutuwar jiki,na shina za,ashiga da ita cikin gidan su dan isah yyacce wallahi tallahi shikam sam bagidane ba tunda yawon dandi ttahito ,
Wassani ko mugunyar ciwona, takkwaso ta taho ta watsa musu duk su mace har ita,
Inna da mariya da ke tsaye suna sauraron shi duk sun maida hankali gare shi,
Cikin karaji inna yar kullu tace , shin wata macce na kaka nuhi,
Badai Gajiye ba ta gidan su Dan isah
Ya awo ita ta mana naka nuhi,
Ko yanzu da natai z duduwa mai kosai maganan na nijjiya suna yi ita da tunba,
Salati inna yar kulu tasa sai da duk yaran suka kallo inda take tana ta rafka salati,
Shinka wa hwda maka wagga mugunyar magana,
Nihw da ijjiyana naggani inda muka warigi dadare nan na motat tatsaya aka tambaye mu gidan su dan isah,
To, to to kutai zuwa inda zakuna dawagga bakar labari dakkatare mu da shi tunda wagga farar sahiyan,
Bayan hita yaran sai duk maganar da Abdull yafadi ya dami inna acikin zuciyar ta duk sai taji bata da sukuni,
Tana gama duk wani dan aiki dake gabanta tashiga daki tadauko hijabin ta tasa tasa ma kofar dakinta kwado padlock,,, kamar yadda takeyi idan zata fita ,,
Gidan su yar Ammo mai masa tafara shiga don jin ko maganar gaskiya na ttajiya,
Aiko tana shiga, cikin gidan su yar Ammo ko gaisauwa bata barin sunyi tace
Tace aho yar kulu, agaishiki,
Inata ingwaiya,
Kun kwan lahiya,
Kedai wagga an ko gaisuwa ban bari munkayi ba,
Shin nicce ko ke jiya
Minana, inji ina,
Batunga da anka hwdi mana Ganiye ta tazaka naniyagga da cutar kabari kusa,
Ke ga dadi yayi kai ke nan,
Ta ballo goro da tadauko daga cikin radan ruwan ta ta balla ta miko wa inna dan guntun balli,
Inna ta ce a,a ha, aini yanzu sam banicin gora, wadda nicci shi hakana zaita wahalsam,
Shina, sa, dai nibari kedai,
To yanzu a,a ankaciki da ita shi,
Kedai bari yar kulu am,
Ance saida maigari yakkiranwo dan isa da kainai yamai hwada
Yanzudai can dakin da suka aje tumakainai da can na yaggyara mata,
Jin haka sai tausayin Gajiye ya kama inna tun bata ganta ba,
Ita da su Yar Ammo suka tahi gaida Gajiye inda suka hadu da wasu mata, yan gulma sunyo turuwa sun gano gajiye zasu fito daga cikin gidan,
Suna gani inna sai suka kama magana cimin tausayi
Allah sarki ke gani ba dakanta ttataho gaisheta,
In, nita wallai banzuwa gaida wagga bakan mace
Wadda taimin sanadin batan "yata ta salwanta cikin duniya,
Sherin tana kacin ta,
Inna dai tabi ta gefen su ta raba ta wuce batare da ta tsaya sunyi wani dogon gaisuwa ba,
Cikin gidan kuma suka iske wasu tsatsaye gefe ana ta maida fadi,
A ho yar kulu inji wata bakar mata yar likutitiya da ita,
Kema ketaho nan niya inda Gajiye kiga wadda Allah yai maisheta,
Jin yar kulun da Gajiye tayi an ambata daga cikin dakin da take kwance cikin ban tausayi, yasa ta dan yin yunkurin dagowa da sauri,
Nan take mata suka sa ihu suna shirin watsewa da gudu, don tsoro ,,
Inna ce tai karfin halin shiga don ta leka taga Gajiye saita ganta kwance cikin, kazanta duk ta bata jikin ta, salati ina tayi tadibi wanan matar tace mata,
Habadai inno a,a kuka barin maralahiya cikin wanga kazanta haka,
Ke yar kulu waka zuwa kusa da ita yakwaso wakainai cutar zamani,,
Cikin karfin hali innata ce abata baho ,
Inno ta ce a,a walla wakabada baho nai a halaka mai,
Dan haka inna ta koma gida dasauri ta dauko bahon ta sabo da hafsi ta aiko mata, dashi lokacin da ta haihu ba goyo,
Wanka inna tai mata ta gyara dakin tas tasa turaren wuta na tsuke sai dakin yadan canza kamshi,
Saida ta gama mata komai saita bata dan sauran kunun da suka sha dazu ita da yara,
Hakan da inna taiwa Gajiye sai kawai ta kama zubda hawaye tana cewa inna ta yafe mata dan Allah,
Dan tasan cewa ta cuce su ita da diyarta,
Dan isah ne ya shigo gida cikin sauri lokacin da yan gulma suka fada mai cewa inna taiwa Gajiye wanka,
Can yadan tsaya ta kofa ya ce ,
Shim ina yar kulu inata ce gani nan ,
Yace mikkai ki wanga kasada, innatace tamay fa dan isah,
Wankafa ankace kin mawagga muguyar bakuwa da tazzaka da cutan zamani,
Ganiye na kuka tana fadin ita ba cutan zamani ke jikinta ba,
Hawan jini ne yakamata,
Yace kaji yan nema bakar mugguya, aniyar ki ta biki,
Lokacin da kike, Gajiyen ki wakika kulawa cikin mu,
Yanzu da ciwi yakam maki shinakin kasan kina da yan uwa nananga ko,
Innata ko ni am dan isa karaga mata ko taji dan dama dama,
Shin dawane zataji,wagga tsiyaye dakaka mata ai shizaisa takara kawai kwance,

Hakana inna tadauki dauniyar Gajiye har abincin ta,
Anna cikin haka watarana Allah yakawo Ruggaiya taxo ganin inna ita da mijinta suka zo ma inna da kayan masarufi kamar yadda takeyi bayan duk wata uku uku saitazo ganinsu takawo masu kayan amfani ,
Inna ta ba Ruggaiya labarin gajiye sai Ruggaiya tace kai inna kusan dai duk halinki ashe fadima ta kwasa ke nan,
Inna tace to maye duniya ai mutum bai wuce gaddaranshi,
Allah ya nufi Gajiye ce sanadiyar rabani da yar diyata
Amma ko kusa ban rike taba don nasan cewa komai mukaddarine,
Rugaiyya ta taimaka ita da mijin ta don akai Gajiye asibitin sokoto dan agane ko may matsalar ta,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
7⃣7⃣
B Y
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,

Assalamu Alaikum yan uwa musulumai,
Dan Allah a tsakanin marubuta da makaranta yakamata asamu kyakyawan facin ta,
Bawai challenge's ya shigo ciki ba, idan har marubuci tayi wani abin da yadan kauce wa addini ko tarbiyan mu yakamata akirata in prevent aimata gyara ,
Babu wanda yawuce gyara aduniya, tundai na fannin addin mu,
Yima marubuci cin fuska a bainin jama,a baida amfani wlh,
Wanan rubutun da kuja ga munayi abune mukaddari daga Allah, akwai masu so soyi amma Allah bai basu ikon yi ba,
Bakaramin wahala ke cikin rubutun novel ba yan uwa,
Yakamata duk yadda marubuciya tai novel din ta a gode mata, indan har da gyara akira mutun a gefe not in public aimai gyara,
Pls mukuma marubutan Allah yakara bamu hakkuri a tsakanin mu mukara daurewa da makarantar , duk abinda kayi ba aima korafi akai ba, wanan abin baida ma,ana ne ,,,,,
Idan nafadi ba daidai ba ina mai rokon gafaran ku yan uwana,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘





Kitchen din shiru yake babu kowa acikin shi sakamakon kashe na,urar da zata sada ma kitchen din da ruwa,
Hakan yasa ma,aikatan fita waje don ganin ko may ye matsallar ,
Maman Umar abin ya bata mamaki kasancewa ko a daren jiya itace tayi aikin karshe a kitchen din kuma ruwan yana zuwa normal,
A hankali ta fito daga dakinta tana tafiya cikin sanda har ta shiga kitchen din,
Saida ta leka ta tabbatar da ba kowa a waje lokacin ta ciro wani dan koya daga cikin gefen breast din ta ta jefa a cikin flower sinasir da maman Umar ta kwaba ,
Tafito da sauri tana dan waige waige, bayanta,
Tana shiga dakin ta tashige bayi ta wanke hannuwan ta tsab, takoma saman godon ta kamar wacce bata tashi daga barci ba,
Bayan angyara matsalar ruwan maman Umar ta dawo taci gaba da aikin ta,
Tanagamawa ta jera komai a carpet saura kuma masu ci a table aka kai masu nasu, saman tebur,,
Saida kowa kusan ya hallara a falon wurin karin kumallon safe,
Kusan nice ta karshen zama a falon saidai ba a saman kujera na nufa ba,
Wurin Ummi na nufa don a saman carpet, take zama ,
A hankali na dan durkusa gami da kara gaida Ummi karo na biyu,
Saida na sawa plate dina komai da nake sha,awa, nadan tsiyaya ruwan sha, a cup na aje a gefe na,
Nai bissimillah nadauka zankai wa bakina,
Aziza dake zaune daga gefen mu ta kura min ido, Allah Allah take yi in kai a bakina,
Daidai lokacin da zan kai a bakina sai wayana dake gefe yadauki ruri
Mayar da sanasir din nayi cikin plate na, nai saurin daukar wayan , diba massage din,
Ganin nobar Amal, da nayi yasa ni saurin ta shi kusa da Ummi ,
Kada kici abincin nan fadima ,
Kuma in kin karanta kada ki dago kai ki debe ni pls,
Gashi dai nagama karantawa amma sai na kasa daga kaina sama,
Wani irin mugun tsoro ne yakamani saboda nasan cewa Amal bata maganan banza
Maimaikon in juya sai na mike kawai daga, gurin da niyar tashi ,
Muryan Ummi ce na ji tace min fadima da wo mana kici abincin cikin sanyin murya nake ce mata,
Ummi zan dauko ma salimat takarda ne a daki, yanzu zan dawo, sai kuma wani dabara yafado min nace ma ummi bari ma dai intafi da abincin daki na kawai sai inci a can,
Wani wawan ajiyar zuciya Aziza tayi,jinda tayi cewa zantafi dakina in ci,
Mutun biyu ne Allah yanufa suci sanasir din, dayake suna da rabon wahala,,
Da Salim sai Ummi duk yadda Amal taso ta hana Ummu ci acikin hikima hakan baiyi, ba,
Ciwon ciki ne mai karfi ya turnike su sai ,
Tun ana abu wasa wasa har takai ga anyi rushing din su asibiti,
Nan likita yai masu dan bayani akan cewa akwai abinda sukaci Allah nai yatai make su sun kawo su asibiti da wuri,
Yace amma inda mace mai cikine taci gaskiya da abin yafi nan worse,
Jin hakan yasa hankali kowa tashi kowa da abinda yake tunane acikin zuciyar shi gamay da abinda likita yace,
Kwanan su biyu , a asibitin aka sallamo su zuwa gida,
Har a lokacin Amal batace min komai gamay da text din da tayo min ba,
Hakan dai danaga irin wahalar da su ummi suka sha yasani shan jinin jiki na sosai,
Sai yakasan ce duk gidan hankali na a tashe yake so sai,
Gurin Salimat na tafi da kukana nafada mata duk yadda mu kayi da Amal,
Itama dai shawara tabani sosai akan yadda zan zauna da kowa agidan
Tace min akwai abinda Amal take zargi a gamay da ni,
Hakan yasa tunda ga wanan ranan Salimat ce ke kawo min abinci a boye ko kuma intafi gidan ta ince a can,
Yau bazan tafi school ba don haka na koma nadan kwanta don in huta,
A can cikin barci na rika jin kamar ana tabani sama sama,
Sai kuma na dinga jin kamar ana kiran suna na a hankali,
Cikin karfin hali na bude idanu na a hankali, tayadda ba kowa zai iya gane cewa na bude ido na ba,
Aziza ce tsaye da wani abu kamar jan kyale a hannun ta,
Can kasan gadona naga ta duka ta aje kyalen a hankali kuma ta taso ,
Ta kama hanyar kofar dakin fita zuwa waje,
Ido kawai nabita dashi a hankali har ta kure min
Bakina duk adduan da na sani na tsari saida nayi shi a lokacin wani ba ni ko karasa shi nake daukar wani,
Sai da na tabatar ta wuce tundazu sai na sauko da bissimillah tare da naiman tsari ga Allah ,
Ta gefe gudan nabi ban yarda na bi ta inda nagantaba tsaye,
Bayi na fada da wayana nakira Salimat na sheda mata abinda nagani,
Ba,adauki wani lokaci ba ta shigo gidan da shirinta,
Ita da Amal ne suka dauke wanan jan kyalen suka samo wani jan kyale na rigar Amal irinshi suka aje mata agurin,
Mamaki duk ya kashe mu, Salimat ce tafara magana daga cikin mu,
Tace wai may yasa wanan matar batada imanine haka,
Mundade muna shawara a tsakanin mu so sai,
A ranan ga dare ya raba amma sam babu alamar barci a ido na,
Duk da nasan cewa sun fitar da mugun abin a dakina
Tunane nayi ko may yasa sheriff yin tafiya tun ranan da yadawo batare da yadauki ma aziza wani mataki ba ,
Ajiyar zuciya na saukar cikin tausayawa kaina ina tuna nen wanan sabon rayuwa da na tsinci kaina a cikin sa,
Gaba sai bugawa yakeyi saboda alamar gitawa da naga anayi ta dan

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment