Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon film din su, na, turawa ,amma banga irin haduwa haka ba,,,,
Maman Nailabin mace ce mai yawan ibada ga natsuwa da kuma sanin darajan mutum,,,,
Ita,ma a,nata bangaren tana jin dadin yadda nake kula mata da yar ta so, sai ,musan man, goyata, da nakeyi anytime,,,
Abinda ban sani ba ashe akwai camera a,dakin na suna kallon duk wani abu da zan ma yar su,,, kusan kwana bakwai ana daukar irin kulan da nake wa Nailabin,,,,,,, abin ya basu mamaki don idan tana kuka nai lalashinta batayi shiru ba nima kukan nakeyi,,,,, acikin kukan kuma zan jawo yarinyar inta lalashin ta,,,,,,, sai mun gaji muyi shiru,,,,don kan mu,.
Barci kuma kusan a jikina takeyin shi ko a goye ko abisa cikina.
Jindadin hakan yasa baban Nailabin ya sayo min kayan sawa iri,iri ,,,,,, idan ka gani baza ka ce fadimar kauye bace
Saboda son da nakewa Nailabin da kula da ita tsakani da Allah yasa
Iyayen ta sukayi shawar taimaka min ,,,,,makarantar da ke unguwar su suka sani makarantace ta "ya" yan masu kudin kasar sai wani da wani ke makarantar,,,,komai dakwalarcin ka dole kasan abu kafin wata biyu,,, Ranan alhamis da jumma,a ba mu zuwa .
Amma lahadi da asabar har da yamma muke zuwa ,,,,
Hakan yasa suka dauki wata yar aikin don kula da Nailabin ,,,, ita wanan matar balarabiya ce yar uwan,,su.

Tunda natafi gidan aiki na ban, karajin labarin yan uwan tafiya na ba.
Karatu da rainon Nailabin kawai nasa a gabana .
Duk lokacin da zan wuce makaranta sai na laika wanan gidan na kusa da mu indinga kallon yadda ruwa ke fito wa cikin dutse yana zuba a kasa.,,,,,,,,
Cikin haka wata rana, na leka naga ba kowa a wajen gidan ,,,,,,, Cikin sanda na lalaba har naje inda ruwan yake fitowa nadinga tara hannu na ruwan yana zubu min,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:37] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣7⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Jinjina gare ku yan uwa na na huguma group novel da fatima luv group novel, da fadila group novel, musha karatu group, maman fati group novel,,,,,, nagode maku kware wlh Allah bar zumunci,,,👏👏👏👏👏

Almost true life story,,,


Sam ban jikaran bude kofan da akayi ba daga cikin gidan
Wani balarabe ne abayana cikin jallabiya fara sai kan shi saye da jan kafiya,,,, Da alama fada yake min
Bayanshi wani farin mutum ne saye cikin kananen kaya ,,,,, wandon jens sai wata bakar riga tie shet mai guntun hannu,,, hannu shi na rike da waya yanayi,,,,,
Cikin fushi, na farkon yai niyar jawoni baya ,,,, amma sai wanan wanda nake gani da alma shine oga,,, Ya daga mai hannu cikin wata murya da banji ba yace ya kyale ni kawai,,,,,,,
Baiko kara waigowa ba ya nupi wata bakar mota da ban ko kula da tana cikin gidan ba ma sai yanzu ,,,,,, cigaba nakara yi da wasa da ruwana duk na jika jiki na dashi
Saida nagaji nafito don kai na badon wani ya hanani ba ,,,, , Koda nafito ido yai wani ja alamar nasha wasa da ruwa.

Wanan balaraben na farko na,gani tsaye yana jiran in fito ya rufe kofan da na sata nashigo ta ciki,,,,,
Harda bye, bye na mai da zan wuce duk na jika kayana sai digan ruwa sukeyi.
Sadaf sadaf nake shiga gidan mu don kada agani cikin kaya jikake,,,,,
Jinayi anja min kune ta baya kawai saina sake jakata ta makaranta ta fadi kasa,,
Jikina yadauki bari ,,,,,,,,
Muryan shi kawai naji nagane baban Nailabin ce ke magana yakama yi min fada ina naje tundazu antashi daga makaranta amma ni ban dawo ba,,, gashi hankalin su ya tashi sosai
Ina dan magana cikin rashin gaskiya nace motar ruwace taimin bari akai ,,,,,,
Baice min komai ba kunsan su larabawa basuyi ma diyan su fada irin namu nan Nigeria
Maman Nailabin tazo da sauri ta jani zuwa bandaki ta sake min ruwan dumi tace in sauri in watsa in fito,
Kada sanyi ya kamani, don su tsoron mura sukeyi sosai don bai raga masu.

Tun wanan ranan in,zandawo sai nadan tura kofar gidan inji ko zanyi sa,a injita ,a,bude,,,,,
Yau ma ina turawa naji a,na min hon din mota abaya na koda na waiga saina tabas gidan za,a shiga nadan, Rakube jikin bango gidan har aka bude get motan tashiga,,,,
Nima nadan sudada nashiga ciki kafin arufe get din bayan motar na labe har, na cikin motar yafito,,, nadauka mai shi ya shige ciki ne sai nafito daga inda nake labe na nufi gurin ruwan dutse nafara tara hannu na ke nan naji ance ke baki gudun cuta yakamaki ne wai,,,,
Firgita nayi dajin maganar shi ina shirin gudu na hadu da gudan mutumin ta bayana.
Yace min in fita cikin tsawa suku, suku nafita ina dan waigen bayana kamar wace za,abiyo baya,,, da guda na karasa waje
Ina jin sun rufe get din su garam da karfi nikuma na aza da sauri nashige gidan mu

Ina shiga gida nadinga jin hayaniya da kuka abinda bantaba jiba muryan mace na kuka tunda nazo kasar,, shi,naji yau a,gidan mu,,,
Matar da ke kula da Nailabin ce ,nagani tsugune tana kuka sai wasu maza guda biyu da alamar jami,an tsaro ne su,,,,,
Maman Nailabin nata sharbar kuka ita kuma ,Nailabin din tana hannun wasu masu fararen kaya
karar mota naji ta asibiti anzo kofar mu,,, saida naga anfita da Nailabin kamar matatta a hannu ,ai bansan lokacin da na fara kurma ihu ba ina fadin nashiga uku da larabci ina tambayan may yasamu yar kaunata,,,,
Muna kallo aka wuce da ita zuwa asibiti cikin motar mu, muma muka bisu a baya,,,,,
Muna shiga asibitin ko fita ba muyi ba akace mu juya zuwa gida ai Nailabin tarasu,,,,,,,
Munyi kuka sosai hankalina ya,tashi da mutuwar wanan yarinyar sosai don wlh duk da nasan ina son yara ,,, to itakan Nailabin nata daban ne don cikin yan watanin da nayi dasu mun shaku sosai da ita,,,,,,
Bayan sati biyu da mutuwar Nailabin tunda safe maman Nailabin tace in shirya muje
Wani wuri mukazo ba mutane da yawa agurin amma akwai jami,an tsaro sosai,,,,
Sai naga anfito da wata mata ansa mata wani bakin buhu an rufe mata fuska dashi,,,,,
Aka tsugunar da ita ana bude mata fuska sai naga ashe matar nan ce mai raino ,,,,, tana ta fadi da larabci wai ba itace ta kashe ta ba,,,,
Kukanasa nima wi,wi nari,rike maman Nailabin duk na shishige mata ajiki ina,noke kaina ajikin ta,,,,,,,
Muna ji muna gani akasare mata kai,,,,,,

Tun lokacin a tsorace nake a gidan nan,,,,,, sai daga baya nake ji ashe mai, rainon Nailabin itace ta wurgo ta daga saman gado sai akayi sa,an wuyan ta ya kare ,,,
Ita kuma bata san akwai camera ba,a dakin. Nima sai a lokacin nasan cewa akwai camera a duk gidan,,,,
Ansa muna cassette din mun kalla naga baban Nailabin yana kuka da hawayen shi,,,,
Sai sun baka tausayi wlh,,,,

Ni abinda ban sani ba ashe su maman Nailabin ba mutanen kasar saudiya bane,,,
Mutanen kasar Egypt ne su aiki ya,kawo su saudiya kawai ,,,
Uguwar , da nake uguwace ,ta ,engineers din matatar mai ta kasan saudiya . duk wanda kagani aunguwar mu kusan a matar mai yake ,,,,, sai babban kusan kasar ke wurin...
Bayan yan kwanaki, sai baban Nailabin ya shigo gida ina dakina ya kirani nazo nadan zauna .
Yace min Fatima zamu koma kasar mu don ban iya kara zama wanan kasar ,idan na zauna zandinga tuna Nailabin dina ne ko yaushe.
Kuka nasa sosai ina fadin zanbisu.
Dakyat ya bani hakkuri ya lalashe ni nai shiru, yadauko takardu yabani yace min wanan shedar gama makarantar da nayi ne yakarbo min ,,,yace in ina da sha,awar karawa gaba ina iya zuwa.
Yakawo kudi masu yawa yabani yace inkai ma hajiyan mu
Ina kuka sunayi suka maidani har gidan hjy Laila,,,,,,,
Rabuwana da su maman Nailabin ke nan, mutanen kirki da bazan taba mantawa dasu ba arayuwata saboda sun tai maka min da abubuwa da dama ,a rayuwata ga ilimi nasamu ga kuma waye ,,,,


Hakana nadawo gidan da hajiyan mu ta kama da zama ,,,,
hajiyan mu tayi murna sosai da abin arzikin da nadawo dashi har da albarka ta dinga samin
Tana cewa da a,ce duk kan mu zamu samu irin abinda nake samu ne ai da mun koma gida ba da dadewa ba,,,,,,,
.

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:44] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Fatan Alheri gare ku yan uwana kuma abokai da kuma masoya wanan novel din nawa

Almost true life story


GARIN MAKKA


Ba mufi wata biyu ba muka bar garin Riyadh muka zo garin makka saboda lokacin zuwa umarah ya kusa kuma baza,a wani dadewa ba za,afara aikin hajji,,,,,
Hjy Laila ta taimaka ma hajiyan mu muka samu wurin zama a garin makka can saman wani dutse ne ta bayan gari,,,,
Akwai kau,yuka da dama a bayan dutsen akasarin mu yan zuwa cirani nan muke zama a gefen gari.
Munyi sa,an samun wurin zama maidan kyau sai,dai matsalar hawan saman dutsen da ba mu sababa
Hjy Laila taba da shawaran mu dan fara saida abinci kafin baki su kara cika gari don Umurah sau kadan afara, ,,,,,
Masa ,muke sayarwa da shinkafa kaza,da miya sai shinkafa da wake da maidayaji da salad,,,,
Wani lokaci harda fura muke sayarwa
Wasu samari majiya karfi hajiyan mu ta dauka aiki suke sauko muna da kayan abincin mun kasa don gaskiya bamu iya saukowa dashi mu,,,,,

Allah naba,mu,sa,an sayar da abincin mu don gaskiya ba laifi mutane, suna yabawa, da aikin mu.
Idan mun saida abincin mu da wuri sai kuma mu canza kama, zuwa wurin bara kafin agama abincin marance,,,,,
Mune kanani muke zuwa yin bara sukuma antyna Rugaiyya suna zuwa su saro gumama su dinga sayar wa a saman gefen titi ,,,,Saidai da anji jiniyar jami,an tsaro dagudu za a sheka abar kayan don da sunkama mutun to babu sauki wulakanci zasuyi ma mutun su kuma kaika duk kasan da suka ga,dama suyar da kai
Wanan maganar da aka fada muna tun zuwan mu aka koya muna gudu,,,,,
Mukuma masu bara za,a samu nama danye fresh mai kyau, shiza a,daura ma,mutun agefen kafa ko hannu, da ka kalla saudaya baka kara waigawa ka diba,saidai ka bada sadaka ka wuce
Za,a daure ma mutum kafa ko hannu idan kani sai ya baka tausayi kamar kayi kuka,,,,,zaka, ga kamar dungu ne kawai mutun haka aka haife shi,,,,

Wani kuma za,aba mutum keken guragu ka, nade cikin ke kamar mai shan inna kana dan wani nokewa kamar gaske,,,,
Duk wanan salon baran na, iya su kamar nadade cikin harkan.

Musalin karfe shadaya na rana ,,,Daidai in da motoci ke cunkoso dayawa ,,, wutan titi yanuna masu alamar su tsaya tukun,
Nazo da muryana kamar ta rarara ina fadi cikin harshe larabci
Ina fadi a,taimaka min da abinda zan kai ummeena asibiti
Wata mota na,nufa mai glass karara ana ganin wanda ke bayan motar zaune yayi irin kwanciyar bayan motar nan,,,,,, Fari dogo kan shi, sai shining yakeyi da ka diba kasan akwai jindadi wurin wanan mutum din,,,,,

Hankalinshi, Yana ga laptop din shi yana ta dikilanta dagani, hankalishi yadauku sosai,,,,, ,, Jin murya na,da yayi ta i,she da kuwa, yadan, dago kashi don yaga mai wanan muryan rarara ,,,
Ya dago a hankali yakai diban shi inda nake tsaye ,,, yakau da kai,, sai,kuma naga ya waigo ni da sauri
Daidai lokacin wutan ba da hannu na titi yanuna kore ,, alamar a,wuce anbada hanya ,,,,
Daidai lokaci ya dauko kudi masu yawa cikin wata jaka agefen shi,,,yamiko min na karba ina ta godiyan jin dadi.
Motar ta wuce nakai dibana ga kudin saida na fidda ido na don ganin yawan kudin da ke hannu na.
Cikin Aljihun, rigata mai zip, da hajiya tai muna, na kulle, ina murna wanan rana mai albarka
Motar ta,dan wuce green light din kadan saina bayan yace ma driver ya,ga kamar ya gane wanan yarinyar kuwa saidai ya manta inda yasanta,,,,,,,,,
Sai driver yace bai kalleta ba don haushi taba shi saboda nasan baka son hayaniya baka kaunar masu wanan dabi,ar baran musan man ma bakar fata
,,,,,
Bayan mundawo wurin sa,na,ar mun ta marance, Mungama saida komai namu zamu tafi gida
Saina jawo antyna Rugaiyya, gefe na nuna mata kudin da na samu yau, Ido ta zaro waje
Ina kika samu wanan kudin fadima na fada mata ,yadda akayi tai shiru nawani dan lokaci.
Sai,tace min mutafi gida to.

Koda muka isa gurin hajiya itama saida tayi mamakin wanan kudin masu yawa ,,, ta,dinga samin albarka tana ta washe baki,,,,

Antyna Rugaiyya nasamu waje, zaune gefenta nima nazo na zauna ashe, kuka,takeyi a wajen bansani ba saida na yi mata magana sai naji tai min shiru nakai dibana ga fuskanta sai naga hawaye,,,
Rugumay ta nayi ina kuka nace mata may yasa may ki yar uwata ,,, kuka yakara kubce mata,,,,
Tace fadima baki ganewa ne ke,,,,yanzu don Allah haka zamuyi ta bautawa hajiya bazata maida mu gida ba,,, idan har tace sai mun biyata kudin jirginta ai ina gani dai yanzu ta samu ko
Amma wanan ai bauta mukeyi mata cin amanar yai yawa,,
Nadafata nace aikin san tun agida aka bata mu ,, muyi mata bauta ko ,,, saboda haka sai muyi hakuri har ranan da Allah zai kawo muna mafita,,,, Dan Allah ki daina wanan kukan hakana pls,,,,,,,,,,



🐎ZEEE MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:49] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKWA🐎

Gaskiya muna saki a wanan zamanin da wasu abu biyu da manzon Allah Annabin Rahama yai kwadai ta muna yinsu zai kaimu Aljanna barin su zai iya kai mu wuta. Hakin,makwabtaka da Zumunci ,,,,, Allah ubangiji yabamu ikon kula da makwabtan mu da kuma yin zumuci da yan uwan mu Ameeen👏👏👏👏

Yan uwana yan Huguma group ina maku godiya kulun tare da sauran yan wani group da ban fadi sunan su ba,,,,,,

Almost true life story



Ni fadima na iya bidan kudi kala,kala kamar yadda kusan kudi baya isan TAKARI , Duk wani sallon bara da sana,a an koya min na iya gani yar shekara sha uku zuwa sha hudu,,,,,
Amma hajiyan mu tana alfahari da ni sosai wlh saidai bata fadi a,gabana acewanta idan ta yabani a,gabana zan yi sanyi indaina samo mata kudi,,,,,


Watan Azumi ya kama ibada akeyi yanzu sosai yan kasar mu ta Nigeria dama wasu sauran kasa she ,sun cika garin makka da kewayen ta sosai,,,,,
Munji dadin wanan cikar don kasuwar mu ta budu so sai
Muma muna kokari wurin zuwa ibada,,, Rugaiyya tabamu shawaran kulun kafin, mu fara sana,a mu ,ko,karta mu ,shiga cikin Masijid muyi , Dawafi

Yauma kamar kulun misalin karfe sha dayan rana nakusa cikin dandazo jama,a ina Dawafi,,, kafin in fita in fara bara don bamu abinci saida Yamma muke yi,,,,,
Dandazon yan Serbia sokayo kaina duk sun matse ni banko iya nunfashi saboda kowa nason ya kai bakin kofar shan madara,,,,,
Ji kawai nayi an,dagoni Cak daga cikin rutsun da aka matseni, An ajeni gefe guda,
Saida na maida nunfashi na daidai naga wani mutum dogo, fari, kyakyawa gabana yana min fada ,cikin harshen larabci muryan shi kamar yana lalashina amma daga yanayin fuskan shi fada yakeyi min,,,,
Ke wata irin yarinyace wai kina ganin taron yan Serbia kowa na kaucewa ke bakijin tsoron su ,zo su, tatakaki, su wuce ,,,,
Nidai tunda nasamu na tsira ban ko tsaya nai mai godiya ba na wuce abina ,,,,,,,,,

Bayan kwana biyu da yin wanan rutsun cikin haram da nayi fitar kutsu ,,,,
Dadai da angama sallah azahar lokacin baran mu yayi ke,nan .
Saidai ni nakan canza hanya ne bani zama guri daya,,, idan nai kwana daya ko biyu sai in can wata kofar in kuma canza sallon barana

Yau ma kamar kullun sabuwar kofa na sake ina zaune kamar wata mara hannu ina bara sai naga anzo daidai kwanon bara na , an ,aje, min kudi sabbi fill acikin kwano ,,,,
Koda na daga kai inyi godiya sai naga mai,shi har ya wuce ko,,,,, bayan maishi, kawai nagani amma cikin daga murya nake mai godiya,,,,,
Kudine masu yawa nagani ,Aiko baran da na bari ke nan ranan ban kara zama ba.

Kwana uku tsakani kuma na canza wata kofa don zan canza kama ,,,,,
Kofar da ake shiga da gawa don ayi mata sallah itace na zauna na kawo wani nama na aza akafa na sai kuda ke bi,,,,
Duk da nasan ba kowa ke bi ta wanan hanyar ba sai lima,mai da wasu manyan malamai da mutanen masu son yawan ibada su ke yawan bi wanan hanyan sai ko idan andauko gawa ,,,,,
Idan mun zauna muna yawan samun sadaka daga yan uwan mamata,,,, bakowani mai bara ke yawan zaman nan ba don wasu tsoro suke ji,,,,,,,

Muna zaune tare da yan tsirarun almajiran da ke waje jama,a nata bautar Allah aiko sai a,kace ga gawa nan za,a shigo dasu na wasu mutanen da sukayi hatsari ,,,,,
Cikin Almajiran mu Atika da take zaune kamar gurguwa aiko sai ta manta yadda ta nade kamar musaka,,,, dadai taji ana fadin tarik tarik tarik aiko saita mike tsaye tana shirin gudu,,,
Wata mata, dake gefenta zaune tare da mijin ta tanuna ma mijinta Atika,,, tai, mai bayani cewa itace fa, zaune kamar gurguwa, dazu,,, saiko ya mike, yadanko wuyan Atika ta baya, nan suka fara rikici, tana fadin yasake ta tun suna yi su biyu har takai sunfara ji
Jama,an da ke,wurin ko sukayo kanta wasu na duka wasu na fadin akaita wurin jami,an tsaro,,,,, muna zauna saiga wata da gudu take fada muna ai ankama Atika,,, nan tashiga yi muna bayani ,,,, kafin kace kwabo yan bara sun shiga watsewa saida wanda ke da nakasar gaskiya,,,,,,

Maimakon in gudu sai kawai na nufi gurin da aka kewaye atika ana duka tanata tsala ihu,
Wani balarabe ya rike mata wuyan riga ta baya,,,,
Duk tausayinta ya kamani,,,,
Sai kawai nai kukan kura nafada cikin taron nadauko naman da nasa akafa kamar gyambo na jefa ma taron aiko sai aka watse da gudu ,,, daidai lokacin jami,an tsaro suka iso suma saiko naja hannu Atika muka ar,ta da gudu nace mata mu raba hanya,,,
Ina cikin gudu na ji an,fisgoni anzaunar dani bisa wani abin sallah har jamian tsaro sukazo suka wuce mu kaina na duke,,,,,,,
Saida naga lalai sunyi nisa sai nayi niyar mikewa in gudu
Muryan wanda ya jawoni ranan daga cikin taron Serbia wa naji,,,, yana fadin ki tsaya nan har sugama bincke ,,,, duk wanan maganan baiko waigo inda nake ba,,,,,
Ana tada sallah la,asar namike nabi jam,i akayi sallah tare dani ,,, koda naga an,kusa sallamewa sai na sulale a hankali batare da sanin wanda ya taimakeni ba,,,,
Kafin ace haka har lbr yakarade yan bara cewa ankama Atika Ankama Atika,,,,
Koda nadawo gida ban fada ma kowa ga abinda ya faruba yau,,,,,
Cikin dare na fara barci kawai naji ana tashina ,,,, nikuma lokacin ina jindadin barci na don dan lokacin da muke samu muyi barci kadan ne ba muda time,,,,,
Jin murya hajiyan mu danayi shiyasani mikewa dasauri ,,,barci na ya watsake kamar bani ba.
Waje ta fito dani sai naga wasu mutane su uku tsaye maza biyu da mace guda,,,
Hajy tace masu itace wanan ko sukace eh itace


🐎ZEEE MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:57] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP & KAINUWA WRITERS GROUP🐎


Yan uwa musulumai muso wa "yan uwan mu abinda muke so wa kan mu,,,,,,

Almost true life story




Ido na kara ra budewa inga ko suwaye ke bidana cikin wanan daren
Gaskiya ban san su ba kuma ban taba ganin su ba ma,
Babu abinda ya fado min a raina sai abinda ya faru dazu a wurin bara
Aiko sai naji gabana yai wani dam,,,,,,
Muryan daya daga cikin mutanen ya katse min tuna ne na, ,,,,
Yace fadima munzo ne muyi maki godiya ,bisa ga irin taimakon da kikayi wa yar uwa guda dazu,,,,,
Agaskiya ba kowane zaiyi irin wanan

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment