Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ruwan lemo gwangwani gwago takaiwa bakinta saitake ce min wai may yasa baki sa hakori ba duk zaman ki a kasan nan,
Dan murmushi nayi nace wallah gwago ban taba yin wanan tunanen ba arayuwata,
Taiwani tabe bakin ta,baki tace wagga diya kan ai halin ta sai ita,
Ita ko dan kurin nan da matan masu kudi kayi banga tanayi nai ba,
Dani da mariya duk dariya mukasa mata har da maman Umar wace ke kokarin zuba masu abinci,
Duk hiran mu a she Sheriff najin su yana zaune inda yake zama don ansan sakwan,nin shi,
Karar watan shi naji ana kiran shi yasa nagane cewa yana cikin falon ashe,
Satin mu biyu da dawowa saudiya mun murje mun yi kyau daga ni har yan rakiyar mu ga wani irin kulawa ta musan man da muke samu daga sheriff gaba dayan mu,
Nida yar kaunata mai kaunata fiye daduk yadda zan yi bayani mariya,
Tare yau muka tafi wurin gyaran jiki, duk wani abinda za,aiwa mace dan gyara ta an muna shi nida ita,
Mun yi kyau sosai amma sai naga mariya duk tafi rude ma nawa kwalliyar,
Tunda muma dawo gida nasa mu yaran sunyi kuka an dan lalashe su,
Ina zaune falon mu ina basu nono kaina ba dan kwali don tun shigowar mu nacire duk lailaiyar jikina wata yar body hook ce na sa mai ruwan Ashe,
Sheriff ne yashigo alokacin da alama daga gurin ma,aikatar su na Company maita kasar saudiya yake saboda irin kayan shiga mai katar daban ce,
Kallo guda yai min sai naga yanayin shi ya canza lokaci guda,
Sama yahau yana shiga dama ya debo gajiya a jikin shi, wanka ya fada kawai dan yadan ji dama,
Tashi nayi naje dan in tare shi ganin da nayi ya shiga wanka yasa nadauko mai simple riga doguwar jallabiya na aje mai, da turaren shi da kuma yar hullar shi,
Komawa nayi dan jin kiran sallah da akeyi a cikin tv nasan cewa zai fito da sauri ya tafi massallaci ne,
Dakina koma nima dai wanka nashiga saida na gyara jikina, ,
Nafito don in gabatar da sallah na ina a rakar farko Sheriff yafado cikkn dakin nawa, alokacin cikin mamaki yake kallona don sam baisan nafara sallah ba
Ganin ina sallah yasa tabar dakin dan yana da online meeting alokacin,
Maki nai fam a,zuciyar shi tun yaushe nafara sallah ne bai sani ba,
Inko har nadade dafarawa gaskiya ban kyauta mai ba,
Bai samu dawo dakin ba har wani lokaci saboda meeting din yadan dauki lokaci a tsakanin su,
Dan suna son a canza launin aiyukan su na kowani kasa, yanzu don cigaban da ake samu,
Dole sai sun hadu a Dubai anyi meeting na face,to face,
Zuwa gobe insha Allah,
Mariya ta kwaso min yaea saboda dama karfe taran dare, nake shimfede yaran,
Bayan ta kwantar min dasu ne take ce min ita zata shige kenan don duk agajiye take yau , saboda dadewar da mukayu a wurin gyaran jiki,
Tabarni ina sa yar rigar barci na mai ruwan pink da yar adon duwatsu bakake, amma ba ainihin stone bane,
Kamshin jikina ko daga nisa kake zaka iya shakan shi, dan man baki na shafa ina kokarin in je in, ma yara addu,a naji an turo kofar daki na,
Mamaki naji dana ganshi sama a yanzu don nasan cewa sai kusan shadaya da wani abu yake baro falo koyau saboda tarin aiyukan dake gaban shi,
Cikin mamaki nake kallon shi har ta iso inda nake zaune gaban mirror
A saman mirror ya dan jinki na jikin shi,tadan baki baki,
Sai nai dan dum saboda ban sam may yakawo shi ba awanan lokacin,
Magana yafara yi cikin yanayin damuwa da kuma tausayi,
Yace haba maman twins, tun yaushe kikafara sallah ban da labari,
Gabana ne yai wani irin dam don ban tsanmaci wanan maganar zai min ba sam,
Kasa magana nayi sai kuma wani irin rudanin da nashiga cikin lokaci guda,
Shirun da taji nayi yasa yakara maimaita tambayar shi,
A hankali nace mai tunda muka dawo da kwana hudu,
What, ya fada cikin zaro ido sai kuma naji yace subbahanallahi,
Yai shiru nadan wani lokaci,
Sai ya sake tausasa murya yace haba Fatima baki tausayin dan bawan Allah,
Shin kiko san halin da nake ciki Fatima, kalli fa yadda na koma na ramay duk na wani lalace, nayi wani irin baki duk saboda rashin tsarkin ki,
Shim kiko san halin da nake ciki kuwa,
Yaidan shiru nawa lokaci sai yacigaba yace,
Allah ma ,yasan nayi hakkurin wallahi, don tun barin ki saudiya rabona da mace,
Jin wanan kalamin yasa nadaga ido da sauri na kalle shi mukayi ido hudu ya kada min kai yace kwarai da gaske Fatima,
Cikin yar siririyar a
a na ce mai yi hakkuri, ban san cewa haka ake yi ba,
Magana ta dariya tabashi, har ina dan iya jin sautin dariyar da yayi,
Yace Fatima ni nasan baki san yadda abubuwa suke bane kasan cewar ba agaban inna kika karasa girman ki,
Amma duk da haka kina kokarinki, shiya sa koda yaushe nake maki fatan alheri, dan kina da saurin fahintar da muta,
Kiyi hakkuri ki tsimake ni Fatima basai munyi koyi da al,adaba ba kamar yadda su gwago suke nufi,
Ina bukatar kasancewa da ke Fatima, ako yaushe amma sanin yadda al,ada yake yasa nake kokarin jajir cewa zuciyana,
Kullun da wanan abin nake kwana araina dashi nake tashi,
Kaina da ke sunkuye nadaga da sauri na kalle shi danjin yadda muryan shi ke sarkewa alokacin,
Ban san ya akayi ba sai kawai na tsinci kaina da rugumo sheriff zuwa jikina,
Wani irin ajiyar zuciya naji ya sake lokaci guda tare da kai hannu shi a saman jikina,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,


Yan uwa kutaya mu murna mun samu, karuwar, Sister MAIJIDDA HARZIMI ta huguma group ta haihu jiya mun samu baby girl, Allah yasa mata albarka a rayuwan ta naduniya da lahira,,,


Sheriff a ranan godiya yai wa Allah dan bai taba sanin mace nada wani fa,ida na musan man ba sai kan Fatima,
Don farin cikin kasan cewar shi da fatima baya ko misalttuwa,
Yana rugumay da ita bayan komai yakan,mala, a tsakanin su,
A hankali yakira sunan ta cikin wani yanayi mai nuna jindadin kasan cewa a tare,
Idona a lunshe na ansa mai cikin shagwaba,,
Yace Fatima kin taimakawa rayuwa ta daki yardan min nakasance dake a yau dan da ban san halin da zan shiga ba,
Kasan cewa dake wani abune tankar rabin rayuwata,
Duk abinda namiji zai bukata gurin mace Allah ya wadatar maki shi Fatima,
Idan har zanci gaba da samun kula irin wanan daga gareki ,
Kingama da rayuwata Fatima,
Dadi yasa ni na kara kankame Sheriff, nai yar murmushi,
Yace baki ce komai ba to, saida na lunshe idona sai kuma nadan bude nace may zance maka, sheriff,
Da sauri naji yace min la, la,la bana son sunan Sheriff din nan pls,
Nace sai may ,yace acanza min pls,
Yace wanan sunar masu aikina kawai zasu iya kirana dashi,
Nace ainima har yanzu ina cikin masu aikin ka don haka ina neman izini abarni in dinga fadin haka na pls,
Nadan marairaice muryana kamar zanyi kuka,
Ya jawo sosai cikin jikin shi yadan rada min akune na yace wayo kike son kimin ko,
Yar dariya nai mai nace aigaskiya na fada saboda sunan yana min dadi idan nafada,
Dan shiru ya,biyo bayan zancen nashi, sai kuma yace yadda kike so, kawai,
Yace gobe zan tafi Dubai kuma ina sa ran zan dan yi kwanaki acan, insha Allah,
Inda su gwago basa nan da daku zamu tafi kawai muje can mu huta
Da sauri nace mai hutu kuma aiko yanzu muna hutawa, nan, ma,
Hmmm kawai yace dan baki san cewa rashin ki a kusa da ni yana haifar min da wata illa, ce ba,
Dan haka yanzu sam bana son abinda zaikai har muyi wasu kwanaki bakwa atare dani,
Haka mukai ta hira wanda zance sai yau muka dan yi magana mai yar tsayi sosai dashi,
Yana barcin shi agefe na hankalin shi a,kwance,,a hankali nazamay jikina ganin da nayi yaran sun fara motsi alamar zasu iya farkawa anytime,,,
Wanka naje nayi alokacin , saboda in tsarkake jikina, kada yaran su falka, daga barci,
Fitowana kuwa ummi ta ,tashi, nadauko tà nafara bata nono,
Ina zaune ina bawa, ummi nono,,ina karewa sheriff kallo, nai wa Allah godiya da mallaka min sheriff a matsayin mijin aure na, kuma uban diya na,
Sai asuba yatashi yakoma dakin shi don ya kintsa ma tafiyar su da wuri,
Karfe bakwai na safe duk komai ya kan,mala ko, yai sallama da su gwago,
Yadan dade dayaran a hannun shi san,nan ya a jesu yatafi, cikin ran shi yana jin shi cikin farin ciki, da anshuwa, ayau,
Haka rayuwa, rayuwar mu tacigaba da guda agidan sheriff tare da su gwago na da yan zu kusan watan su biyar kenan tare da mu, acan,
Sheriff yai alkawarin da zaran an gama aikin hajji na bana za,adawo dasu gida insha Allah,
Yarana sunyi bulbul da su gwanin ban sha,awa duk wanda ya gansu sai yai mamakin irin girman da sukayi a lokacin,
Yanzu Sheriff arzikin shi ya bungasa sosai don hannun jarinsa da yasa a cikin company Abu Abdallah ya samu riba a yan shekarun nan mai girma,
Al,amari da larabawa babu cutarwa aciki don haka su da kan su suka bukaci ya bude company kanshi a kasa shen turawa, da kuma wasu kasa a Africa,
Don haka batare da bata lokaci ba, yadukufa wurin wanan aikin har Allah yasa komai ya kammala,,
Cikin dan Lokaci kadan sai gashe ya tsewa wa duk wani sa,an shi,
Farin cikin mu a kullun kara karuwa yakeyi a gidan mu,
Matsalata daya shine har yau ina fargaban zuwan aziza a garin saudiya,
Saidaga baya nake jin cewa ai Sheriff ya saketa tun wancan lokacin da takai muna takaka agida ranan sunan su twins,
Kuma an mata dokar hana shigowa kasar saudiya tun lokacin har ita ranta,
Matsalar mu yanzu itace hjy mama kawai da iyalin ta,
Saidai duk wani sheri da zatayi wa sheri bai ko kawowa gareshi Allah ke kare shi,
Sam ban san cewa Sheriff ya biyawa su inna makkah ba dan bai fada min ba,
Sai kawai baki mukayi daga Nigeria ganin bazata mukayi masu,
Abin yaban mamaki matuka,dan ,daga Inna, da hafsi,da kawu, sai wasu mutum biyar a bangaren mahaifina, maigari, da malam Basiru,
Wanda wai yazo ke nan da zama shida matar shi wace har yau Allah bai basu haihuwa ba,
Aiki zaiyi ma sheriff a,daya daga cikin ma,aikatar su, da ke nan kasar saudiya,
Tsohon gidan sheriff na mai,katar su da muka taso, a can aka sauke bakin mu
Mutum goma a bangare na goma bangaren shi sai goma side din nafisat,
Mutum, Talatin cur suka zo sauke farali, daga kasar Nigeria wanda sheriff ya biyawa,,
Dana zauna nai nazari sai naga cewa aini anawa bangaren nafi su duk jama,a, ai, don ga su gwago da mariya duk zasuyi aikin hajji bana,
Maman umar tasamo min yan takari mata da maza su ashirin daga fannin girki da gyaran gida da aike duk mun tanadar ma wanan fanin masuyi muna su,
Tun zuwan su inna da sauran jama,a bamu da hutu agidan mu don haka , nima nai niyar bin yan uwa dan sauke farali,
Ashe da sauran jama,a atafe don fanin su Ummi suna hanya andan samu matsalar tasowar su,
Abin yabani mamaki kwarai da gaske dan ban ji zancen aikin hajji gs bakin sheriff ba,
Saida naga duk wani abinda nakeyi nakuma tabbatar da yarana sunyi barci,
Cikin shigar wata rigar barci mai kyau dakuma daukar sha,awa nake,
Sai kamshin turaren dake tashi ajikina don tun yarana suna kanana bazaka taba jin cewa ina karnin nono ba sam,
Idan baka ga ina shayarwa ba baka ganewa,
Yana zaune da alamar bai,dade da fitowa wanka ba, yana diban wasu takardu a hannun shi,
Dan karamin tire ne a hannu na wanda ke dauke da cups guda biyu, sai spoon a,gefen tire din,
Tun da na shigo dakin ya kafe ni da ido har nakai tire din saman dan stoll din dake gefe na aje,
A hankali najuyo zuwa inda yake tsaye bakin save din shi,
Ta bayan shi na zagaya na rungumo shi, inajin lokacin da yai wani ajiyar zuciya,
Kaina na aza a,saman bayan shi nadan lafe nawani lokaci, inajin shi yana murmushi,
Can naji yadan kira suna na yace Fatima na ansa, cikin kissa,
Yace baku kwantaba ke nan,
Nai yar ajiyan zuciya na zagayo ta gaban shi, still ina rike da shi,
Nace cikin murmushi ya zan kwanta ban gama hidimar maigida ba,
Murmushin jin dadin abinda nafada har cikin ran shi yayi,
Ya girgiza kanshi yace ina alfahari dake fatima na san cewa duk wani lalurana kina kokarin kiyaye wa, duk da wahalan shayar min da yara da kike yi,
Nadan yi murmushi daidai lokacin da na riko hannun shi zuwa daidai kuguna yarike ni,tsab yana mai sun,sunar wuyana zuwa kaina,
Nace ai lalurar yara duk kan mu keyi tunda in kana gida kaine mai kula da su,
A cikin saitin kunne ya rada min yace ai ya kamata ki shirya daukan wasu baby din haka na ko tunda wayan nan sunyi wayo,
Bansan lokacinda nai kokari kwace kaina dafa rikon da nasa ysi min ba,
Girgiza kanshi ya kara yi yace cikin kashe murya yana kashe ido yau din nan nake son yi ma twins kanne insha Allah,
Dariya maganar tabani sosai kafin ince au har ka manta da fadan gwago ke nan ko,
Yajanwoni zuwa jikin shi sosai kamar za mu hade guri guda yace ai itama abin alfaharintane ai ace mun haifa mata jikoki da yawa,
Kawai kiyi addu,an Allah yakawo masu albarka ban son raki, idan anzo zace a fake ga gwago, ta ce,,,,,,
Ina dariya na dan kwace kaina zuwa bakin gado,
Saida na zauna sosai in fuskantar shi na ce nazo in yi godiya fa,
Yadago kai da sauri yace namay fa nace na Alhazai da aka kawo saudiya batare da sani na ba,
Hannu kawai yadaga min batare da nakai karshen zance ba yace nafada maki ba godiya atsakanin mu fadima,
Shin dakike fadin haka wai,mako kinsan cewa wallahi kunyar inna nake ji haryanzu don narasa may zan mata wanda zai sai taji dadi tabon rashin ki da taita fama dashi,
Abu guda Bashir yai min dabarar yi shine kada in bari su komada ga ita har hafsat Abdull kuma za,azo min da shi daga Maiduguri, ne,
Bansan lokacin da jin dadin wanan maganar ya sana furta I love u my Sheriff,
C ,U ya ce min tare da yar dariya yace ai badan ke nayi ba dan twins nayi hakan don su kara shakuwa da kakan su,
Wani irin kunya naji da tace haka dan nasan cewa maganar shi gaskiya ne so sai hakan zai sa yara su san inna ce kakar su ta fannin uwa duk da mu talkawane na gaske,
Tunda naji cewa su inna bazasu koma da sauran jama,a ba yasa na fara murna har ban iya boye jindadi na,
lnna ce kawai nake jiwa dan nasan cewa za,a kwashi yan kallo kafin ta yarda ta zauna damu,
Sayayya sosai nai wasu gwago don tafitan su gida,
Duk kan su an saya masu gadaje acewar su zasu kai wayaran su ne,
Sai tsarabar riguna jakkuna,da kuma su dardumar sallah masu kyau,
Sheriff yai kokari sosai gaskiya don kayan su a cargo akai don a auna masu shi,
A madina muka hade duk kan mu da sauran alhazai,
Wa yanda sheriff yakai duk agidan mu suke basu gani na akoda yau she, saboda kulun busy suke,
Kwanan mu goma muka dawo makkah don hawan Arafat,,,
Motocin maikatar su sheriff guda biyu irin dogayen luxurious din nan dasu mukai ta jigila duk inda zamu,,
Don haka bawani dogon binciken da ake muna dan ganin tambarin maikatar su da akeyi a jikin motar yariga kuma ya kama muna hema inda zamu zauna,
Duk inda zamu shida salim ke daukar yaran ko malam Basiru,
Don haka bazance nawa sha wuya ba a wanan aikin da muke yi, ina manne da innata ko kuma sheriff,
Munji dadin aikin sosai , don abin yazo muna cikin sauki,
Alhamdullah anyi lafiya ankare lafiya duk wani wanda yazo karkashin sheriff yasamu kyauta sosai,
Gashi kuma da dabi,ar zuwa, shi kadai a massalaci yabada zakkah ko kuma sadaka mai tsoka wanda sai mutum ya girgiza,
Zakkah bana a dogon daji ya aika dasu saboda ganin irin wahalar da mutanen kauyen mu ke fama dashi,
Ko maigari bai sani ba don yana saudiya gurin mu Bashir ne yakai ma su can kamar yadda sheriff ya bukaci, malam Basiru yai list ,,,
Waya kawai suka bugowa maigari cikin farin ciki suna sheda mai irin alherin da,akai masu dakuma ragunar layya da aka kaiwa, sauran iyalin su kawu a,gida da na maigari,
Ina sama ina gyara ma sheriff, daki, mariya takirani a waya, in sauko ina da baki a falon mu,
Ban bata lokaciba na sauko zuwa kiran da ake min,
Da mamaki nadan tsaya ina kallon su, su kawune tare da maigari da sauran abokan tafiyan su yan uwan nafisat da Sheriff, din mu,
Da sauri nasa akawo masu abinsha nakuma bada umurnin ai, masu,abincin cikin sauri,
Guri, na samu nadan tsuguna daga gefe ina gaishe su cikin ladabi,
Nasheda masu cewa maividan baigari yatafi Riyadh yau da safe amma zuwa gobe zai dawo, insha Allah,
Anan mukayi ni da bakin mu ina ta yi masu hidima,,
Gabadayan su sun yaba da halaiyan mu na girma ma nagaba da mu dagani har maigidan,
Sukuma sheda min cewa daman sun zo suyi mai godiya suka yi mai barka da saukowa Arafat,
Naji dadin hakan da sukayi dan haka nima nai madu kyautan da badu zaci samubadaga gareni,
Ni e sukar suyi wa mutanen gida tsaraba dashi, sunji dadi sosai inda suka shiga samin albarka da fatan gamawa lafiya,,
Sheriff nadwo wa na sheda mai zowan yan tsofafin gida ai bashiri yasamau su a masaukin su, da kanshi,
Donshi gurin shi ,shine yakamata ya tafi,gurin su neman albarka,ai,,,,
Ance sabo turken wawa da kukan mu, muka rabuda su gwago ranan da zasu koma su kuka mu kuka,
Sai zabga godiya sukeyi wa sheriff wanda ke tsaye yana kallon mu cikin dakewar zuciya dan shima yaji kamar a,ce da mu zasu zauna anan, ba,zasu koma ba,
Gwago sai washe hakiran gold takeyi abinta wanda yai mata kyau cif a,fuska,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI* ✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA🐎


Almoy True Life Story,,,



Wuce wan su gwago yasamu cikin halin damuwa sosai musan man yaran da suka yi wayo a gaban su gwagon mu,
Duk da ga su Ummi da Inna agidan sai mukaji gidan yai muna wani irin girma so sai, kamar ba mutane acikin ta,
Mun saba da gwago idan tafara zuba ko ba ka, son surutu sai kayi shi,
Ita koda karamin yaro magana take yi abinta, hankali kwance,
Na lura cewa innar mu a takure take agidan bata son dogon motsi,
Kullun ta na daki ita baka ganin ta waje sam, bakomai yasa haka ba sai kunya da take ji wai idan angata za,ace tazo gidan surikin ta ta zauna,
Ummi na jin lokacin da take fadar haka sai ummi tace idan har tace haka to itafa,
Ai ita avidan dan farinta tazo ta zauna, tun tana jin kunyan haka har tadaina, acewar ta,
Tun lokacin inna ta ta rage, zancen jin kunya a gidan surukin ta,take,
A kida tace shiga kitchen da kai na dan yin cooking wa mai gida na har mada sauran iyayyen mu,
Nasan cewa yana gari yau dan haka, abinci mai kyau da kuma abinsha ns hada masu,
Nasan cewa dare yafi son yaci tuwo kowani iri ne,
Don tun ina aiki a gidan shi nasan wanar a kidar tashi ta rashin son wani abin da ba tuwo ba da dare,
Hakan ke sa shi shan wuya idan yai tafiya, zuwa waje,
Tuwon semovita nai mai da miyar kuka wanda inna takawo, muna lokacin da zasu zo, miyan yaji daddawa da kayan yaji sosai,
A, leda na kwashe wa kowa nashi mariya dake gefe ita da maman Umar
Suna tayani aiki suka shiga mikawa mutanen gida nasu don kowa da inda za,akai mai nashi,
Muna gamawa, da sauri nafada dakina dan in dan gyara jikina kafin sheriff yadawo gida,
Duk gidan yadauki Kamshi da na turare dana girkin gida,
Yau atamfa ce a jikina, super wax, doll colour, dinkin zani da riga ce, sheriff baya son dinkin buje da riga, acewar shi,

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment