Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk da haka ana iya ganin juna don duk guri gudane,
Wata yar matashir mata fara yar kabilar yarbawa ce, da baby ta, ina ganin haihuwar fari ce mata,
Yaron yanata kuka tunda sukazo, tayi lalashi yaron yaki yin shiru,
Kusan kowa a wurin ya tausaya ma yaron yadda yake ta faman tsala ihu,
Zuwa nayi na karbe yaron a hannu ta nawuce cikin gida dashi, da ita,
Ruwa nasa masu zafi nai ma yaron wanka wurin cire pampers naga a she kashi yaron yayi,,,
Naimai wanka na gyarashi tsab tabani wani kaya na saka mai,
Lokacin da muka fito wajen taron, mu tararda har an fara cin abinci kowa sai yabawa yake yi da irin girkin da akayi,
Nafisa tana gefe fuskata babu ko alamar fara,a
Tun matan abokai na janta da yar hira har suka gaji su ka kyaleta,,
Tana ta wani matse fuska kamar mai jin warin mutane,
Muna ji suna hiranta kasa kasa suna cewa wanan ai ta tsofe ma Ahmad
Wata kuna tace yo ai auren zumunci ne inbashi ina zaikai wanan ai gwago ce,,,
Gyalen da nasa yana da sulbi sosai, gashi kuma ban iya yafa gyale ba dama sai dai inyi rolling din kaina kawai, gyalen yanata sabule min,
Ga kuma yaro a hannu na, duk na tsawala ina kokarin mika yaron wurin uwar shi sai gyalen ya karkare faduwa kasa,
Subbahanallah aiko idon maza caaaaa akaina cikin sauri na jawo gyalen na mayar akaina, daidai lokacin naga sheriff din mu yai min wani irin kallon banza
Wanda banji dadin hakan ba,
Duk sai naji na tsargu wlh,
Don ni ban san may nayi ba,
Daga inda yake yaga nadan shiga damuwa sai yadan yafito ni da hannu, Sukaina ce ke fada min yana kirana,
Cikin ladabi na isa inda suke zaune shi da su Yusuf,
Fura yace min in debo masu a cups,
Nakai masu furan sai santi sukeyi,,
Ga al,adan su duk wanda zai tafi sai ya aje wani kyauta mai muhinmanci arayuwar ma,auratan wasu na bada kudi masu yawa, suce aba ma amarya wahalar girkin ta,
To muma dai haka din ne don wani katon tire aka dinga zuba duk wani gift da aka samu a wurin
A gaskiya ba laifi don dai an samu alheri so sai,,,
Muna kallo bakin mu suka dinga barin mu da guda daguda har suka watse suka bar mu mukadai agidan,
Saida na ga duk mun gyara ko ina agidan sanan nasamu natsuwa,
Kayan gift din na hada wuri guda na nufi cikin gida da su wurin anty nafisa,
A Falo na samay shi zaune yana waya daganin shi yana cikin nishadi yau
yana ganin zan wuce da kayan gift din,inkai ma,anty nafisa,, dakinta sai yadakatar dani da hannu
naja nayi tsaye cak wuri guda,,,
Ina sauraron shi inji mai zai ce min,
Yana gama wayan ya dakai diban shi gare ni
yace min in,bude komai yagani a gaban shi na ,aje kayan
nan na duka nadinga cire kayan guda gudu ina kuma karanta mashi,sunan wanda yaba da gift din
Abin mamaki ina kai ga na karshe sai naji yace min, duk gift din kayan sawan in dauka,
Kudi kuma in dauka in raba ma duk wanda mukayi hidimar dashi,,,
Saura in,dauka,cikin mamaki nadago kaina don jin zancen shi,,,
Zan yi magana ya dago min hannu yace min ya isa
Jiki ba kwari na tashi don in wuce,
Sainaji yace min yagode da fitar dashi kunyan da nayi,,
Ina dan murmushin jin dadi ban san cewa anty nafisa tana bayana tsaye ba tun lokacin da na fara nuna mai kayan,
Gani ta dayi tayi murtuk da fuska yasani dan ja tsaye ,
Kauce mata nayi nadan bi ta gefen ta nawuce abina da kayan
Muryan ta naji tana magana cikin tsawa take cewa wanan ai wulakanci ne,
tayaya zai dauki kayan yaba yar aiki
Acikin azama naji yace mata wace,ce yar aiki,
Nida take gani zaman kaunar shi da suke ciki daya yake dauka, ba matsayin yar aiki nake ba.
Yace ko kin taba ganin yar aiki tafidda shugabanta kunya kar yadda taga nayi a yau din
Yace ko kintaba yakara tambayar ta cikin tsawa,,
Nidai na wuce abina nabarsu nan yana ta gagasa mata maganganu masu zafi,
Bayan na aje kayan dakina gurin Rugaiyya na tafi,
Na bata labarin yadda duk mukayi da Sheriff din kan gift din su,,
Ta dafa min kafada tace fadima halinki ne na alheri ya ja maki,
Duniya ance indan baka da kudin da zaka taimaka wa mai kudi to kataimaka mai da karfinka,
Kinga kinfitar shi kunya ,
yin hakan yasa shi jin dadin alherin da kika mai a yau ko mai yai maki kin can can ci hakan ne fadima,
Tana fadi tana har hada kayan ta don zuwa gida na mika mata kudin duka nace mata ta aje cikin wanda muke tarawa,,
Ashe duk kudin na a cikin jikin ta nan take boyewa gudun kada a sace muna,
Saida ta hada komai tadauki jakar ta da dan abincin da zata kaiwa su hajiya da su Umar,
Kawai sai naji banji dadin da zata wuce ba jinayi dama muntafi tare don ina kewan su hajiya, ina son ganin su ina son in kwanta tare da su muyi ta waka da labari har barci yadauke mu kamar yadda mukeyi kullun,
Ina kallo ta wuce ni raina yai min baki,kirin



Rugaiyya har ta kai kusa da gida ashe bata sani ba yan bagaladi suna biye da ita,
Tundaga unguwar su sheriff din mu suke biye da ita tunda sun san cewa duk bakin da akayi sun koma garu wan da suka fito, su,,,
Bata ankara ba kawai taji sun kewaye ta sun mata circle, ba ta da daman gudu,,,,,,,,,,


🐎 ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Allah ka tai Maki Musulumi Duk Inda yake,,,, ,Ya Allah Karufa ma Kullumin musulumi na Duniya Asiri Ameen

Anty Halima Garko

Almust true life story,,


Wa,iyazu billah abinda kawai take fadi kenan idon ta a rintse ,
Inbanda Allah ba wani abinda take iya fadi,
Basu yi wani dogon bincke ba suka gane cewa takaru ce ita bata da takardan zama yar kasa,
Rugaiyya bata basu wani wahala ba don haka bata wani sha wuya ba, wurin su,
A, haka suka tafi da ita zuwa inda ake tara kamamun irin su,,,
Duk wanan abinda yafaru a idon wani makwabcin mu ne, yana ganin an wuce da ita ,
Da saurin shi ya isa gidan hajiyan mu yana sheda mata duk abinda yafaru,
Sun yi kuka sunyi bakin ciki sosai wlh,

Ina can dakina jiki ba kwari tunda anty na ta,tafi har na kwanta sai naji bana jin barci , duk da gajiyan dake jikina,
Don haka sau,kowa nayi daga kan gadon na zauna kasa,
Kanya gift din da aka bani na jawo ina fitar wa guda guda ina kalon su,
Duk kusan dogayen riguna ne har guda hudu nace a raina sai muraba nida Rugaiyya na
Sai kuma dikin shadda redmaid masu kya kusan guda uku suma nazabi guda nace biyu in bata tasa don tana son irin wanan kayan tun muna kano,,,
wani kwali da najawo waya ce mobile cellular mai shegen kyau, cikin kwalinta tare da tarkacen ta,,,
Aiko ina ganin wayan ban san lokacin da na ture komai na hau murna ba,
Koda banda wanda zan kira na dade ina sha,awar waya kodai photo na kalla kuma inyi game,
Jona ta nayi a wuta don ta samu caji,
Ganin wanan wayan yasa nakasa karasa kallon kayan da nakeyi,,
Nakoma saman gado na kwanta ina jiran wayan tayi caji,
Maganar da naji sheriff nayi da matar shi yafado min a rai na,
Allah sarki sheriff ai nice ka taimaka don ban manta irin taimakon da yaitamin can baya kafin ma inzo gidan shi,,,
Juyawa nakarayi ina Allah Allah gari yawaye in nuna ma Rugaiyya wayata,
Da haka barci barawo ya dauke ni,
Firgice natashi duk jikina yajike da zufa,
A c na kalla naga yana aiki, har nadan gyara kwanci sai mafarkin da nayi ya fado min a rai,
Gabana ne ya fadi dammmm,,,
Tiryan tiyar na fara tuna abinda nagani a mafalkin nawa,
Rugaiyya ce ke shiga cikin wani abu mai matakala kamar gidan sama tana murmushi tana min bye,bye,
Zubur na mike don wani zafi naji tundaga kafana har cikin kaina,
Bayi na fada nai wanka cikin daren nan nadauro al,wala nazu nayi nafila raka,a hudu,
Nan wurin na zauna har akai asuba
sam jikina bana jin dadin shi wlh,
Barci ya kara kwashe nan gurin da nai sallah asuba,,,
Wanan karon Aisha yar karama nagani ta kankamay ni ajikin ta,,, tana kuka,
Zubur natashi sai naga ashe har hasken rana yafito yau ban fita ba,
Cikin sauri nadan gyara jikina kodan make-up din danakan yi yau ban tsays yi ba,,,
Kitchen nanufa direct ina shiga sai naga yau mama mai abinci ce ita kadai tana aikin breakfasts taya ta nayi muna sauri don kada sheriff din mu yafito bamu gama aikin mu ba,,
Tun ina hakkuri har nakai ga magana nace ma mama yau babu wace tazo daga gidan hajiya wai ko lafiya
Ba,afi minti uku ba sai ga su sun shigo , daganin su suna cikin tashin hankali,
Ban kula sai cewa nayi aikin da muka sha jiya duk ya sa mu gajiya,
Nadauki kayan break din nafara kaiwa falo aiko na iske sheriff na saukowa daidai lokacin muka gaisa da shi sama,sama nakoma don in dauko sauran kayan
Abinda kune na yaji Sukaina na fadawa mama mai abinci yasani yanka wani irin ihu, daga inda nake,
Duk suka razana don basu san cewa har nadawo ba,
Yake jiki nayi nafadi ina ihu mai kunar zuciya,
Duk wanda ke gidan sauri take yi ya iso inda ihun nawa yafito,
Kusan ta,tare suka iso gurin,
Duk kan mu kuka muke yi har mama mai abinci,
Cikin tsawa Sheriff din ke tambayar mu abinda ya faru,
Sukaina ce tai karfin halin fada mai abinda yafaru da Rugaiyya jiya bayan tabar nan gida a hanyar ta na zuwa gida,,,
Shima ya shiga tashin hankali sosai wlh don baiji dadin ace ta sanadiyar shi hakan yafaru ba,
Inda na rakube jikin wani standing fridge ina kuka ya kalla,
Ya kau da kai don jin tausayi saboda ya tuna da labarin da Anty nawa taimai a madina lokacin da banda lafiya,
Nafisa duk da bata jin larabci tasan cewa wani abu munmuna ne yasamu Rugaiyyan,
Barin kitchen din yayi zuwa falo inda Nafisa itama ta rufa mai baya,
Da ya juyo ya ganta ya dakata, har ta iso yace mata, ke baki da tausayi ne abin kuka yasamay su , amatsayinki na mace yar uwan su baki tsayawa ki basu hakkuri,
Sai cewa tayi yo ni maizan masu tunda basa jin hausa basa jin turanci,
Ta kaici yakama shi yama rasa may zai ce mata, yaji sanyi,
Ga sautin kukana yana ji har inda yake tsaye, yana tayar mai da hankali,,,

Muryan mama mai abinci ne naji tana cewa inda za,aga cikin shugaban nin mu na takari ai masu magana wata kila akwai yadda za,ayi sufitar da ita,
Jin hakan yasa hajiya laila ta fado min a rai,
Batare da bata lokaci ba na koma daki na na shirya cikin bakaken kaya irin namu nadauko takalmana Tommy nasa nadan gyara fuskana kadan jakata nadauka,
Nafita cikin sauri taxi natare nace akaini Masfala, by pass,,,
Tafiyan minti kusan hamsi yakai mu maspalan naba mai taxi kudi
Gidan hjy laila na nufa kai tsaye nasa may ta tana shirin fita, wai zata SHARMANSOOR gidan wata aminiyar ta batada lafiya,
Kallo daya taimin tasan ba lafiya,
Cikin tashin hankali take tambayana may yafaru,
Ina kuka nafada mata abinda duk yafaru da Rugaiyyan
Itama hankalinta yatashi sosai wlh,
Tashi mukayi zuwa gidan wani Alhj Aliyu bandi shugaban matasa na wanan erea din
Bayan bayani da mukai mai ne ya nisa yafara fadin akwai kudi ko da zasu bi sugani ko za,aiya fitar dasu,
Nace ma hjy laila duk kudin namu na wurin Rugaiyya dashi ta wuce,
Kassh yace yawani dafe kan shi, yace ashe ba zancen bi kenan
Kusan wuri uku mukaje amma zancen shine akwai kudi,
Daga karshe dayake hjy laila bata iya cin amana ba sai tace min in kyale su mudawo gida,
Gidan ta muka koma tai ta min nasiha ta kwantar minda hankali,
Muna nan zaune kafin in tafi mukaji ana sallama da hjy laila mun dauka ma ko maganar Rugaiyya ce aka samu wani labari
Da saurin mu muka fito shugaban matasan takari na uguwar da mukafara zuwa wurin shine yazo,
Yan dan wani sosa kai yana gyara yar falmaran da ya aza saman nalabiyan,
Hajiya tace mai Alhj bandy lafiya dai ko sai yace a,a dama nazo inji cewa ita wanan din a ina take da zama,
Kai haji bandy walahi kafita idona,
Kaida keda mata uku a ina zaka sa wanan din
Haba hjy kada muyi haka dake fa tace mai har hiya da haka ma sai muyi,
Inajin haka na banka mai wata irin hara na wuce cikin gidan hajiya,
Ban wani dade ba nai sallama da hajiya laila mata mai mutunci da karan ci
Taimin alkawarin zata zo gidan hajiyan mu don jin bayanin may ake ciki.

Koda na isa gidan hajiyan mu a tsorace na samay su ita da umar da Aisha,
Suna gani na duk sukayo kaina suna kuka,
Tausayin su ne ya kamani har cikin raina tundai hajiya kuka takeyi kamar wace akaiwa mutuwa mai karfi,
Saida naga maran ce yayi nace zan koma gida saboda yanayin hanya,nai ma hjy alkawrin zandawo badadewa ba,,,,,,,,,
Ashe can gida kuma hankalisu duk ya tashi saboda rashin gani na da basuyi ba, din fita nayi batare da na fada ma kowa ba,
Ina shigowa gida nagan su hankali a tashe duk sunyi tsaye cirko cirko a wajen gidan
Fadawa nayi a jikin Yumma ina kuka mai kona zuciya cikin sauti mai ban tausayu
Dafani naji anyi a hankali nadan waiga sai naga sheriff din mu tsaye bayana handkerchief ya miko cikin dakiyar murya yace min kukan ya isa
A hankali nadan tsagaita kukan nawa, Almustapha yace ma abude masu yumma dakin ma,aikatn dake ta baya su zauna ciki kafin ansan abin yi,
Ina ji haka cikin kuka nace hjy da su Umar fa,
Wurin wa za abarsu,
Da Yumma suka tafi dashi hargidan namu sun samu har sun rufe gida ta kwan kwasa musu dakyat suga bude masu bayan muryan ta da sukaji
komi da muke bukata yumma ta ta dauko muna
bawani abinda zai iya nuna shedar cewa mun yi zama, agida koda anzo bincike,,
Sam bansan cewa anje dauko hajiya ba dasu umar,
Gani Aisha kawai nayi ta rugumay ni tabaya,
Wani irin dadi naji dana gansu tare da mu,
Ashe ko mungode Allah mun gode ma sheriff din mu,
Don cikin dare yan samay suka kawo muna farmaki don suna zaton cewa ba rugaiyya bace kawai a shiyan,
Koda suka shiga gidan namu ba kowa sai yan tarkacen mu na aiki,
Basu gane komai sukatafi don sun san cewa ko sun tanbayi mutanen uguwar ba su gane komai,

Tunda akasa su,a ajirgi kasar, Niger jirginya je ya sauke,
Dayake ita tana da kudi tab ga jikin ta sai bata samu matsala ba sosai,
Motar zuwa Nigeria ta shi ga sai kano,
Da wayon ta tabar gida don haka bata sha wani wahala ba wurin gane gidan su,,
Mahaifiyar ta na daka a soron gidan su taji sallama
Tana waigawa sai taga wata yar gayu kamar Rukaiya amma dai wanan din tana da haske
Zuwa tayi da gudu ta rugumay mahaifiyar nata tana fadin
Ashe da rabon zan kara ganin ku ,
Nan ,da nan gida yacika da jama,a yan zuwa gani bakuwar makka,.
Kamar yadda takari kan dawo aimasu rade radin sun je yawon duniya ne hakane yafaru ga Rukaiya
Zancen ya bazu dan kauyen nasu Rukaiya tadawo daga yawon takari da tabi wata hajiya mai kudi saudiya,
Tadawo bata da komai, sai hakorin makka da tasa a bakinta,
Ita dai komai batace ba don yanzu ba lokacin bayani bane,
Saida komai ya lafa bayan kwana biyu cikin dare ta zauna da yan uwanta tai masu bayanin irin rayuwan da tayi a makka,
Tabasu labarin abinda hajiya tai muna da kuma yadda ta baro mu can,,,

Sai bayan komai ya lafa matane tasamu wani malami tace ya raba muna kudin tsakani da Allah yadda baza ta cuta min ba.
Bayan an raba kudin sai tafara business da nata,
Saboda a lokacin duk matasan garin su maza, ba wanda ya nuna yason ta don gani sukeyi karuwan ci ne taje yi can,,,
Sai wani dan uwantane mai mata guda ace wa dashi hamza shine ma yadan nuna yana ra,ayinta,
Bata kulashi ba don tasan cewa baza tai zaman lafiya da matar shi ba don haka share kowa tayi,
Takama sana,ar ta haikam, taje kano tasaro kaya kala,kala zo kauyen su ta,saida,,,,,
Cikin hakane ta hadu wani dan kasuwa a kano wanda ya yaba da hankalin ta yanuna yana son ta da aure,
Ko shi Harunan da yazo neman aurenta saida aka ja shi gefe aka fada mai yakosan ta taba zuwa yawon duniya har kasar saudiya,
Duk da hankali shi yatashi sosai da jin wanan maganar sai yadan dake yana son ya kara gwada hankalin ta yagani,
Kamar ta sani bayan ya koma gida suna waya shine ta dan bashi labarin rayuwanta kadan,
Saida ya nisa tukun sanan yace mata ai an fada mashi akauyen su da sukazo,
Saidai shi yabari ne dama yaji daga bakin ta kozata fada mai,
Idan har bata fada mai ba to tabbas gaskiyan mutanen kauyen ne yawon baza ta,tafi,
Saigashi kin fada min da kanki,
Rukaiya nayarda dake dari bisa dari don bakowace mace ce ba zata iya fadin gaskiya haka,

Kafin ayi bukine ta shirya tafiya zuwa sokoto,
Kamar yada akai mata kwatancen garin mu,
Da yake tafiyan safiya tayi sai ta isa sokoto da dan wuri wuri marance bai riga yayi ba sosai
Motar da zai kai ta dogon daji tayi shata ,
Ana batun kiran sallah magriba ta isa garin dogon dajin
Tambayan gidan inna yar kulu tayi batare da bata lokaci ba aka nuna ma driver gida ,
Har kofan gidan namu ya kaita
Yafido mata da kayan ta, taciro kudi tabashi tana godiya
Wasu yaran makwabtar mune da ke wasa saman yashin da aka tare gefen gida makwabcin mu,
Sutakira sukazo suka kwashe mata kayan ta zuwa cikin gida,
Ina dake alwala taga yara nata shigowa da kaya niki niki akai,
Sai kawai ta dakatar da alwalan tana kallon ikon Allah
Saboda dai yar matashirya matan da ke bin yaran inna bata taba ganin ta ba,
Asalima dai ba yar gari bace, ita daganin ta
Sundan gaisa sama sama sai anty tace abata buta taje tayi alwala
Ba musu inna ta bata butan itama,,,
Tabar man kaba kato inna ta shimfida masu a waje don suyi sallah
Bayan sun gama ne sun gaisai sai shiru ya biyo baya,
Anty ce ke tanbayar Hafsat da datti kanin mu
Mamaki inna tayi da jin bakuwar birni har tasan sunan yaranta
Can dai inna ta daure tace ban fa waye kiba yar nan,
Rugaiyya tai murmushu tace daga wurin fadiman ki nake,
Wacce ke saudiya zaune
Cikin kidima inna ta kara matsowa kusa da Rugaiyya tana rike ta tana fadin ina fadima,
Allah kada ka kasheni sai ga fadima na roketa gafara,
Rugaiyya ta kwashe duk labari na da ta sani ba inna har zuwa ranan da aka kamata,
Saida inna ta nisa san nan tai ajiyar zuciya mai karfi
Sai kuka shaaaaaaaaa

Nandai suka kusan kwana suna labari kamar sun san juna dadewa,
Tunda safe tadauko kudina taba inna mu ,.
Sam inna tace bata karba takoma dashi can biirni taita juyawa,
Saida kyat akasamu ina tadan dauki dubu dari uku kawai daga ciki,
Anyi ta zuwa gani bakuwar inna,,
Dakuma son jin wai fadima na makka,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣7⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

Son duniya bala,i ce don babu komai acikin duniya fa,ce rudin shedan,
Kusani cewa duniya saida kudi, lahira ko sai da hali mai kyau,,,

Almost true life story,,,,

Zaune nake saman gado na cikin

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment