Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take fada min cewa gidan da take aiki sundawo daga tafiyar da sukayi,,,,
Nan muka hadu tare da ita muka gyara hajiyan mu ,, nadan fito da ita kofar gidan mu don ta dan kara warware wa,,,
Da alamar taji dadin hakan don yau harda yar hira munyi da ita,, awajen
Matsala guda ce take min complain kafarta takeji yana mata nauyi sosai,,,
Tundaga rana nake dan yawatawa da ita acikin uguwar mu duk da yake saman dutse muke,,,



Kofar kitchen din su yake kallo daga bakin kofar shiga falon su,,, duk wani motsi da takeyi idon shi na a,kanta wanan abin ya fara isan ta gaskiya ibadon wanan aikin yazama kamar na dole ba da tabar masu gidan su,,,
Duk lokacin da maigidan yake a gida matsalar da take fuskanta kenan ,,
Idan sun hada ido wani lokaci har lasan lebon shi yakeyi kamar maye,,,
Azuciyar ta tace ka boye matar ka ko kuda baya ganin ta amma ni ka hanani shakat da wanan mugun kallon


Cikin dare suna kwance da matar shi tace mashi maigida nasan duk halin da kake ciki da yar aikin mu ,,, babu matsala zan kawo maka ita har nan gidan tadawo da ,kai na,,,, ni nasan kufi sha,awan wa,"yan nan matan fiye da mu matan ku,,,

Tundaga wanan ranan matar ta fara rarashin anty na Rugaiyya tana wani haba haba da ita,
Abinci lafiyaye ake bata tana ci sai kuma sutura masu dan kyau da aka sayo mata,

Tundaga ranan da aka sai mata wa,yan nakayan sawar masu kyau antyna tafara shiga damuwa saboda tana yawan tsorata da mugun kallon da maigidan ke mata yana shafar gemay shi yana lunshe ido,,,,,
Tundaga ranan tadawo gida cikin damuwa,,, tana shigowa ta jefo min ledar kayan da aka sai mata ajiki tana kokarin cire yar bakar rigar da muke sawa sama,,, Don wanan kowa yasan al,adan larabawa ne, bayan sungama kwaliyan ciki dole akwai bakar riga da hijjab ko gyale da zaka rufe fuskan ka dashi takalmi kuma mun fi sa flat cover,,,,
To muma TAKARI ,, haka mu tamu shigar saidai lokacin umurah da aikin hajji wasu sukan dan yi dressing din kasar su,,,,
Ledar nabida kallo ina fadin may ke cikin wanan ledar yar uwa, nakai dibana zuwa gareta don jin ansa,, yo kibude mana ki gani,, kayane masu kyau dogayen riguna da yan kayan unders aciki rigunan kala hudune,,,
Daga ina daga uwar daki na matar hamza Abdallah,,
Nakalla nakara juya kayan nace gaskiya suna da kyau, halan sun samu wani alheri ne haka,, ta waigo tadan debeni dadai lokacin tana cire kayan kan,ta,,, azuciyar ta, tace ansa may zan baki maryam da sauranki nasan bazaki fahince ni ba,,,
Kawai sai ta wuce dakin hajiya don ta gaida ita,,,,
Tanunawa hajiya kayan ,takuma bata dan abin sa ma bakin da tazo mata dashi,,,
Dakin nashigo na zauna gefen gadon hajiya nace mata,,,,,
Gaskiya hajiya yakamata ki fara fita hakana koda Haram ne ki dan dinga zuwa kina dawafi , zaifi maki wanan zaman , agida kulun .
Zama wuri guda zai ta kara maki bakin cikine arayuwar don babu ranar da wanan damur zata barki in bakibar tuna wa ba,,,,
Rugaiyya tace ai na fada mata ba yau ba saboda naga tadan ji saukin jikin nata ai
Saida hajiya ta gyara zaman ta kadan tace insha Allah zan gwada zuwa ,,, kuma nagode maku sosai da kulawar da kuke bani ,,,, ayadda na dinga cuta maku amma sam baku gujeni,,, sai ma kara shigata jiki da ku,keyi,,,,
Amma sai gashi Sukaina da mari sun fi karfina don suna ganin banda komai yanzu,,,,
Takare maganar ta ta tana share kwalla,
Dama tunda bata da lafiya nadawo dakinta da kwana saboda dare,,,

Ankara min yawan aikin gidan yanzu saboda mai kula da goge,goge baida lafiya kwana biyu baya zuwa,, ,,,,,, Bance komai ba
Tunda safe nake zuwa inyi aikina kafin wani lokaci sai wanan tangamay,may falon yakoma sai kyali yake yi kawai,,,
Gyaran mace da na miji ba daya ba,,,,don komai na falon sai nai mai tas ,,,,
Koda Ahamad yazo daga Riyadh inda yafi zama saida yayi mamaki yadda yaga canji a,falon mustapha yai mai bayanin cewa wanan yariyar mai ba flowers ruwa ke gyarawa saboda mai kula da gurin baida lafiya ,,,,,
Shiru yayi acikin zuciyar shi yana nazarin rayuwa irin na fadima,,, da kwazo , yarinya karama amma ace duk abinda za,a samu kudi akansa zata iya,,,
Gaskiya yana son jin labarin wanan yarinyar dakuma sunar ta da inda tafito,,,,,,
Sabod tsoro lamarin ta yake bashi,, ace duk inda yaje sai yagan ta,,,,,
Almustapha yadawo dashi daga wanan tunanen yana fadin amma kayi hakkuri nima nasan bazata iya ba don dai kada abar gurin hakane yasa nace ta dinga taimakawa,,, amma daga yau,,,,, Hannu yadaga mai alamar yadakata,,, hakana, yace wurin yayi kyau fiye da da kuma ko da mutun uku akace sunyi wanan aikin zanji mamaki balle wanan yar ficikan yarinyar,,,
Ina gurin Flowers ina basu ruwa yafito cikin wani bakin jallabiya, mai laushi, yana shaning, Sai kamshin turare shi Al, madinal ,noor
Jin kamshim kawai nayi nasan cewa shine yafito,,, ,,,,Waya yake yi azahiri amma ni yake kallo cikin zuciyar shi yana fadin wanan yarinyar bata gajiya ne da aiki,,,,,,,, Saida yagama wayan shi atsaye,,,
Al,mustapha yakira yanuna mashini ,yace aiki nawa nakeyi gidan
nan, yafada mai duka,,,
Saida yadan nisa yace ,, haba Al,mustapha, aikin ai yai ma mutum yawa ,, katausaya mata mana,,,
Yadan sosa kanshi, yace za,a gyara insha Allah,,,,
Duk abinda suke fadi inajin su,,,
Amma ban waiga na kalli inda suke ba don ma kada in gaishe shi,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 08:21] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣0⃣
B Y
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Duk Abinda bawa yatarar akabarin sa na alkhairi ko na sherri to, Tabbas shi ya aikata abinshi, domin Allah subahanahu wata,ala ba,azzalumi bane baya zalunci acikin mulkinsa,
Ubangiji mu sarki Allah mu na rokon ka kabamu ikon aikata alheri arayuwar mu👏👏👏👏


Ina jinjina maku yan TEEMA Luv group novel, Yan HUGUMA group, gaskiya banda bakin gode maku saidai in maku fatan alheri arayuwar ku ako yaushe, Duk masu kaunar TAKARI novel ina maku fatan alheri Allah yai muna Rahama acikin rahamar sa,,,,👏👏👏

Almost true life story




Yana tafiya a saman titin 57 up zuwa kwanar , massfala junction, Yafito,ne da,niyar zuwa, wasu,shagunar su na, saida kayan sawa,, na maza, saboda,lokacin da ake odar sabin kaya kafin mahajjata su zo ya kusa, za,diba kayan da suka dan dade sai ayi gwanjon su akawo wasu sabi lates,,,,,
Wayar dake mane cikin aljihun shi tayi yar tsuwa ,
Duk da sautin ki,ra,ar ,wasu yan yaran rabawa dake tashi cikin sauti mai dadi a,motar tashi bai hana shi jin wanan tsuwar ta wayan shi ba,,,
Rage gudun da yakeyi da motar shi yayi don diba mai kiran nashi ,, idan ba mai muhinmanci bane ya aje har ya sauka,,,
Ganin sunan da ke a screen din wayan yayi barobaro ABBANA. Jikina rawa yadan samu gefen titi ya perker motar shi gefe guda, fuskanshi manne da yar guntuwar murmushi wanda sai kila bayan wata yake irinta,,
Saida yabari kiran ya tsinke tukun don haka al,adasa take indai kirace daga Nigeria bai,dauka saidai shi yakira ka saboda yawan cajin kudin da akeyi ma mai shi,
Cinkin sallama yafara magana sai mahaifin nashi ya ansa mai asanyaye shi don duk kusan halin mahaifin nashi ya dauka,,,
Haba babana wai fushine kakeyi damu ko kuwa dai rashin kulawa da mune yasa yanzu ko yar wayan ma da kake bugowa don muji lafiyar ka, ka daina sam,,,
Murmushi yayi mai tsada har uban na jinshi tacikin wayar,,,,Cikin muryan tashi mai kama da baya son magana sai dole,,, la,la,la, Abbana, haram,,haram ,,,,,
A,kawai dan business din danakeyi a Dubai ne yanzu wanda yadan dauke min hankali da komai,, kwanan bana cikin lokacina ko kadan wlh,,, amma ina mai roko da ayafe min dan Allah ,,, naso in,zo but time ne banda sosai yanzu insha Allah nan badadewa ba zan shigo Nigeria ,,,,
Uban yace a,a kayi zaman ka mu ai zamu zo don mu gan ka, dama na bugone infada ma cewa zamu zo umurah nida maman ku don adiba muna lafiyanta,
Yadan yi murmushi yana susan kanshi kamar agaban uban yake yace, amma kilama zan riga ku zuwa,
Shima uban dariya yakarayi,, yakauda zancen yana fada mai cewa harda tsohuwa yake son su zo don taga dan lelenta, saboda tana damun su da zancen shi,,,
Yace ashe inada babban bakuwa kenan dole in samu lokacin in ma wanan zuwan shiri na musan man,,,
Sundan yi hirar lokaci da kuma yan uwa,,,,, sosai
Sukayi sallama uban yana ta farin ciki da jin dadin dan nashi ,,,Saboda hankalinshi, uwa,uba ga ilimin addini ,kusan duk abinda zakuyi dashi cikin ladabi da kuma tarbiya irin na larabawan asali zai ma,,,,
Lunshe ido uban yayi yana tuna su salis da ya kai turai karatu ,koshida yazauna turai har ya haifesu can baijin turancin tsiyar da suke mai inyana waya dasu,,,
Garashi ladabi ko waye suna kokarin bashi hannu su gaisaa ba kunya sam ga al,amarinsu,,,
Sabanin Ahamada da duk zaman ku bakajin yai turanci saidai laranci, cikin tsanaki,,,



Shiko Ahamad karasawa yayi shagon nasu, yadan didiba abinda yakamata ayi wa shagon nashi,,,
Yadawo gida cike da tunanen zuwan mahaifan nashi,,
Bazuwan kowa yafi mai dadiba kamar na yar tsohowar nan babarbara mai yawan fitina,,,
Annurin fuskan shi ta dan sauya lokacin da yatuna cewa bada mahaifiyar shi ba cikin masu zuwa gurin shi,,,
Rashin mahafiyar shi tare dasu yana yawan kona mai zuciyar shi in,yatuna.. Duk wanan daular da suke samu agidan su bada ita ake ci ba,,,,,, Duk da yana kokarin tura mata da abin anfanin rayuwa yadda yakamata saboda tun yana yaro ,yana jin tsohuwa na yawan yi mai addu,an Allah yasa yasamu ya kula da mahaifiyar shi da yan uwan su,,,,,,,
Saidai abinda ke dan yi mai sanyi ya lura dacewa inda take aure yanzu tana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya,, kuma mijin nata yana nuna mai karanci sosai kamar shi ya haifeshi ,,,
malam na yawan lurar dashi addini tun yana karami inyaje hutu kauyen,,,
Shiyasa har gobe yana ganin mutuncin shi don yarike mai uwa amana.
Da wanan tunanen shiga falon shi ,,, ya wurga da key din motar shi a bisa kujer da ke gefen shi,,,,
Kujera mafi kusa dashi ya zauna gami da dafe kanshi, da hannun shi guda,,,
Hjy mama hjya mama , hmm,,,,
Ya lunshe idanun shi yabi lafiyan kure da yake zaune ya jiginu da yan shi yana murmushi mai nuna bakin ciki a fuskan mutun.
Shi duk labarin da aka fada mai nazaman maman shi da ita bai kona mashi zuciya kamar yadda tadinga gwada mai rashin kauna kirikiri ba boyo ko kadan,
Idan har wasu na iya boye mugun halisu ita sam bata iya boye nata,, akan shi,,,,
Duk abin da baban shi zai mai na alheri saida in bata sani ba za,ayi shi inko tasani yaza ma tarihi,,,
Koda kuwa za,ayiwa yan uwanshi ne idan anzo gare shi sai salo ya canza ,,,,,
Falon yabida kallo nadan wani lokaci yanisa saboda yasan cewa tunda yatare wanan gidan nashi mama bata shigo saudiya ba,,
Tun yana zama a Riyadh ne kawai ta sangidan shi amma sai da ta nuna hassadanta cewa, ina yasamu wanan kudin haka.
Waiko dai uban shine ke turo mashi da kudi aboye,,,
Inba haka ba ya zaifi yan uwanshi samu wuri haka,
Cikin fushi tabar kasan ,
Ashe lokacin da taje turai ziyaran yaranta ta dauka sunfi Ahamad jin dadi ne da samu wuri,.
Donshi baya magana kuma baya nuna cewa shidin wani abu ne can
Har aikin da yakeyi baban baifada mata ba saida tazo tagani da idon ta,,,
Amma duk da hakan bata gamsu da cewa komai na Ahamad din ne ba
Gani takeyi ai na company da yake aiki ne aka bashi ya zauna,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 13:32] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

GiBA wata,kalmace mai saukin fada saida kuma mai nauyi ce wurin fasarar ta Allah ya haramta, zina, sata, shangiya, da kakausar harshe ,,,,saikuma gashi duk GIBA tafisu karfin haramtawa, ,
Allah zai iya yafe ma bawa tsakanin shida bawan amma banda tsakani bawa da bawa,
Yan uwa munisan ci Giba atsakanin mu
Yi,da junan mu shiyafi komai faruwa yanzu,,,,GIBA watau Gulma,,,,


Gaisuwa da fatan alheri dukkan masoya TAKARI NOVEL ,,,,,,, Antys din huguma ga jinjinan ku nan na girma akoda yaushe,,,

Almost true life story,,,,,



Girki ta hada masu lifiyaye irin ta kasar su ,, ta shirya masu akan dining table ,,,,
Akawai dakin da aka tanadar masu don hutu agidan ,can takoma don ta dan huta bayanta kintsa jikinta tsab da sungama takwashe kayan tawanke sai kuma gobe indan Allah yakaimu basu kara cin wani abinci mai nauyi kuma,,,,,
Yau ma hakan ne ,, kiranta akayi a intercoms din gidan don kowani daki mai aiki akwai shi, agidan.
Cikin sauri tagyara rolling din kanta ta isa falon ,,Zau,ne suke saman kujerun dake kewaye da dining table din,,,
Cikin gimamawa ta gaisu tana dan dukawa na ban girma ga shugaban ka,,,
Idon shi kur akanta ko kifta su baiyi ,,shi akulun wanan yarinyar kara sha,awa ta yakeji a ran sa, ,,,,,,
Sai wani lunshe ido yakeyi kamar may maye,,

Matar tace ma anty na ta kwashe kayan abincin sungama zasu fita amma don Allah tadan jira su har su dawo kafinta wuce ,
Rugaiyya ta ansa cikin gimamawa,

Har wani lokaci basu dawo gida ba sai zuwa dare lokacin badamar tabi hanya zuwa gida yan bagaladi na hanya,,,
Cikin damuwa da fargaban iri iri zuciyar ta yake,, don tasan cewa hankalin yan uwanta zai tashi sosai don duk inda mutum ya dole yadawo kafin dare yayi,,,
Matar ce tai mata bayanin cewa tayi hakkuri ta kwana da safe zata kira Albani din ta taimata bayanin cewa tana tare da su,,,
Saboda dole ne duk wanda ya kawo ma ka mai, aiki ka dauki lanbar wayan ,Albani din shi ,,,,

Cikin rashin jindadi ta isa dakin da take hutu aciki idan tazo gurin aikin.
Uwar dakin nata ce tashigo dakin cikin fara,r ta da sakin fuska, Ma,isha bata da jiki sosai gajera ce maidan tsawon fuska,,, takai kimanin shekara talatin da wani abu da haihuwa,,

Cup take rike dashi a, hannu ta wanda ke cike da madarar shanu mai kyau mai kauri ta asali ,ko kallon cup din kayi kasan madarar yadauki sanyi,, so sai,,
Gefen gadon da Rugaiyya ke sama ta zauna wanda ita kuma Rugaiyyan ke kokarin tashi ta zauna saboda girnamawan, shigowar uwar dakin nata dakinta,,,,,
Ta mika mata cup din tana fadin tasha madarar don zaimata amfani sosai,,,,, kallon madar Rugaiyya keyi kamar batasan ko maye madara ba da mamaki,
Mika mata cup din tayi gami darike mata hannu guda tana murmushi, tace madarace mukasha ,shine nakawo maki naki don nasan kina gidan yau kinzama bakuwata,,, takarbi cup din tana godiya.
Saida ta tabbatar tasha sai tamike tana ce mata tasake jikinta mana ainan ma gidane ko bata saba da su bane har yanzu,,,
Dan murmushi tayi cikin girmamawa tana fadin ai ba ko mai tunda za,a fadama Albani din ta, cewa tana nan saboda dare yayi mata yau,,,,,,,

Shiko maigidan yana can saman bene, daidai wani dan dake saman harabar gidan nashi yakasa tsaye yakasa zaune, yaje yadawo yana mazurai, da ido yana lunshe su yana shafar gemun shi,,,,
Ahaka matar tacin masa tsaye yana yawo tsakiyan haraban su yana dunkular hannun shi,,,
Tabayan shi ,Ma,isha ta rugumo , shi,.
Yai wani ajiyan zuciya a hankali,
Yajuyo da Ma,isha ahankali ta gaban shi suna fuskantan junan su,,,
Itace ta fara magana ,, tace nasan ganin da kaima wanan yariyar a yau ,shiyakara saka cikin wanan yanayin maigida,,,
Yace wani abu nake tunane kawai ba wanan ba,,
Jan hannu shi tayi suka koma ta cikin bedroom dinsu,,
Tace mai magida na riga na gama shirya komai ko ,,,yadan yi murmushi ya rungumota,
Tace nan,da dan anjima kadan kana iya zuwa gareta ,,, kalassss,,,
Ta juya tana shirin kwanciya ,,,

Amma cikin zuciyar ta tana fadin ita tasan cewa baza ta iya gamsar da maigidan nataba in badon haka ba bazata yarda da wanan akidar tashi ba,,,.
Saidai kasssh duk yadda tayi yafi gane ma bakaken mata don acewar shi sunfi dadi da juriya dasu,
Yakuma sheda mata kuma itama din tasani kusan gidajen da kaga yariya bakar fata tana aiki to aiki biyu ne da ta lalurar maigida sai kuma ta zahir,,,, amma bakowa keda wanan akidar ba sai wanda zuciyar shi takekeshe,,,

Saida yadauki dan lokaci yana gyara jikin shi,,,,yagama duk wani shiryeshirye shi na kwanciya,,, azuciyar shi yana kiyasta yadda zai kasance da Rugaiyya yau,,, yana fatar tafi waccan da tatafi dadin harka saboda ko banza Rugaiyya tafi, wacan kurciya,,
Saida kuma yakan tuna irin dadi damore rayuwa dayayi da,zakkiya yar, kasar, niger,,,, yaji dadin zamanta dasu sosai, ita,din ma,tasamu alheri awajen shi dakuma matar shi,,, idan ko Rugaiyya haka take zai kasan ce mai farin ciki
Don haka dole yasan irin yada zai kyautata mata da kuma irin kyautar da zai mata,,, dan yajar ra,ayinta,,,

Rugaiyya tagama shirinta tsab ta kwanta,,
tare da addu,oin neman tsari daga Allah kamar yadda ta saba,,
Saidai duk, jikinta bata jin karfin shi ,sam tunda tasha madaran da ma,isha ta bata jitakeyi kamar duk gabobin jikinta basu aiki,,,,,,
Tana kwanci Barci mai karfi,ya dauketa, daga kwancinta,,,

Tafe yake a hankali yake tafiya, cikin dogon baradan dake gidan inda dakunonin yan aikin gidan yake a jere ,,, kusan duk basu yan aikin basu ciki, kasancewar dare ne mafi yawan su sun tafi gida basu kwana agidan ,,,
Kofar dakin yatura a hankali yai ,sa,a kofar a bude take,batare da yasha wani wahala ba,,,,,
Tsayawa yayi yana kare,mata, kallon irin halittan da Allah yai mata gaskiya ba laifi yasan zai more rayuwar sa anan,
Cikin barcin da takeyi mai nauyi take jin ana shafarta,, a,hankali ta gyara kwanciyar ta don ta dauka ko duk dadin barcine a gidan masu kudi,,
Shiko gogan yaji dadin hakan don yadauka ko shi ta gyara mawa yan kayar fulanin ta sunyi ciciko sunyi tsaye,,
Nandanan yashiga su ya,,,,,,,,,
Shafarta yakeyi gami da tsotson wasu sasan jikinta,,,
Ahankali ta bude idon ta dake tap da barci mai nauyi,,,
Duk da barcin da ke idon ta bai hanata zabura ba da kokarin mike wa, zaune, cikin tsoro,,,,,,
Shiko gogan sai ce mata yakeyi cool dawn cool dawn , ,,,,,,
Data ga zaicigaba saita kama ture shi tana fadi ,,,.la,la la, zina haramu,,,
Kiss yakara kokarin kai mata,,,,
Aiko tasa hannun ta da karfi da ja gemen shi iya karfin ta saida yayi wata yar kara, na wahala ido waje, ,,,,,
Allah yabata sa,a ta jawo Cup din da aka bata tasha madara shi,,,,ta buga mai a fuska jin zafin da yayi yakai mata mari yakai mata wawan mari, cikin fushi
,,,,,,yasa hannun shi guda ya rike mata wuya, gudan hannun, yana shafar fuskan shi inda yaji kamar sanyi ashe jini ne,
Ta kara kai mai cizo a wuyar hannun shi guda,baisan sanda zafi ya sa yasake ,ta ba,
Dakarfi ta ture shi gefe tasamu ta sauko sama gadon ,tasa hannu taja rigarta da ta cire gefe
,, Sa,arta guda yamanta da yashigo hankalinshi yadauke da ganinta da yayi kwance bai rufe kofa ba,,,

Da guda tafita hanyar zuwa get din gidan duk suna a rufe ,,
Dabara yafado mata tashige parking area na gidan tashige karkashin wata mota landrover,,, talafe tana maida nunfashi ahankali kamar za,aganta takeji ita,,,

Yadafe fuskanshi da hannu guda don jinin dake zuba mashi dakin matar shi yanufa don yasan ba inda zatabi tafita gidan da daren nan ,,,,,
Matarshi naganin shi tataso da saurinta tana tamabayar shi ko may yafaru haka,,, jayeta yayi gefe yana fadin kinsan cewa wanan yarinyar ba irin wacan da kika samo min bace kika,kaini ta jimin ciwo
Sai nasa andaure min ita sai an fitar da ita kasan nan,,,
Hakana yaita fadar shi ita kuma tana gyara mai gurin da jinin ke zuba ga zafin cizon da akai mai,,,
gurin yai ja jarir,,,

Shike ta fada yana ce ma masu gadi su diba ko ina , nagidan akamo mai ita,
Duk sun diba har gurin motocin da

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment