Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na dukar da kaina kasa
🐎ZEEE MAKAWA🐎
,✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,

Saida komai ya lafa, ne kowa ya dan natsu guri guda,
Maman Umar tagama gyara komai sai ,Sheriff din ya shigo dakin don yaiwa salima sannu da kuma barka da arziki,
Ina kitchen naje hada mata abincin da zata dan ci , abinci mara nauyi nai mata,
Sam basan cewa ya shigo dakin ba don da banshiga ba alokacin,
Salimat nagani na ta ce min sannu fadima da kokari,
Nagode kware da hidimo min ki,,
Gare ni Ubangiji Allah ya baki miji na gari,
A kunyace na ansa mata da amin aiba komai,
Sai alokacin nagan shi tare da su Amal da Salim suna ma baby wasa,
Amal tace aidole ki godewa Fadima salimat, tunda itace yau nurse mai karban haihuwa
Cikin mamaki Sheriff yace, what fatima, yana mai dan nuna ni da yatsa yace
Yace interesting nd welldon,
Ke yar karama da ke har kin iya karban haihu kuma agida,
Dan murmushi nayi gami da sadda kaina kasa,,,
Amal tace ai fadima tayi kokari don daini gaskiya bazan iya ba,

Sheriff yace gaskiya dole a,tafi asibiti da baby da uwar don adiba lafiyan su
Yadan kalli gefen da salimat ke zaune tana wani irin zufa yace mata kin san kunyi kasada kware don haihuwa ya tatare da matsala acikin shi
A sanyaye tace wallahi sheriff a bazata abin yazo min don ban dauka cewa haihuwa bane,
Allah yasa fadima tazo itace ta taimake ni,

Acikon mota sheriff zaikai mu asibiti tare da Salimat da baby ta,
Amal ta mika min baby tace in zauna da ita agaban mota itada Salimat su shiga baya,
Ahankali yake tuki motar sai kira,an dake tashi nawani dan saurayin matashin balarabe,
Baby tai dan wani hirgita kadan tare da ajiyan zuciya madan sauti,
Cikin sauri sheriff yadan duko inda nake zaune da ita ,yadan kware showul din yana diban fuskan babyn
Wace ke ta sharan barci abinta,
Amal na kallon mu daga bayan mota da suke zaune, daidai lokacin ta dauke mu hoto a hanka, batare da sani na ba
Saida muka je aka diba lafiyan jariri da na uwa aka tab, batar da duk suna lafiya,
Sheriff ne da kan shi yabuga ma mijin salimat waya yasheda mai cewa salimat ta haihu,
Sunyi mamaki sosai don duk dauka akeyi ba month din haihuwanta ba ke nan,
Ba karamin kokari sheriff yayi ba saikace shi akaiwa wanan haihuwan
Satin ta biyu a saudiya mijinta yazo yadauketa zuwa Nigeria ,
Yai muna godiya sosai kafin su wuce , duk bamuso su tafi da baby Asma,u, ba wai sunan mahaifiyar mijin ta ke nan,,,

Karatun mu mukaci gaba dayi duk da bawai dogon lokaci yarage muna ba,
Saidai karatun namu sam bai hanamu yin ibadan mu ba,
Ko yaushe muna zuwa muyi sallah idan an idar da sallah mushiga muyi ziyara
Mufito wani lokaci kuma salim ne zai kwashe mu ga mota yakai mu baki,ya muyi ziyaran kaburbukan bayin Allah da sukayi sha hada,
Ina son zuwa ziyara a bakiya don ko ba komai zakaji wani karin imani nashigan ka,
Don zaka dinga gani kamar ace sahaban manzon Allah SAW dake kwace cikin wanan makabartan zasu tashi ka gansu,
Sai mutun yaji indan ana bada tarihin su kamar ace shima a wanan lokacin aka halicce shi yazaman to a cikin su,
Gurine da akayiwa security ankewaye shi da waya saidai ka tsaya ko kuma idan zaka iya hawa dutse ka,hau kaje kai masu addu,
Salim yana yawan sha,awar zuwa ziyara a bakiya, don kusan duk ranan alhamis sai yakaimu ziyara munyi masu addu,a tare yiwa kan mu ,muma fatan cikawa da kyau da imanin ubangijin mu,

Za,zaune muke duk kan mu cikin falon muna hira, kamar yadda muka saba yi indan weekend ne zama mukeyi inda mun dawo daga masallaci ayita hiran rayuwa
Yau,ma hakan ce ta kasan, da mu,
Amal ce zane a tsakiya ta magana wayanta yana a hannun ta tana dube dube,
Photo na dake cikin wayan ,sai idon ta yakai ga wanda tai muna ni da sheriff da baby Asma,u, wace muke ce ma husna,
Saida tadan tsaya taima hoton kallon tsab sanan take gwada muna,photo,
Mamaki yakamani kware daganin picture don basan lokacin da ta dauka, ba,
Idan ka gan mu a cikin photo zaka zaci cewa ko wasu ma,aurata ne nida shi,,,,
Salim yace kai dama ace wanan baby na yayan mu aida basan irin farin cikin da zaiyi, ba,
Kusan koyaushe sai yai min korafi akan yana son haihuwa , yana son yasamu baby shima,
Ace ai wanan baby shi don yace hjy tsohuwa tana yawan yimai korafi indan sun hadu,
Amal tace banga wace ke shirin haihuwa ba cikin wa yan nan yan gayun mata nashi,
Tace du matan nashi ni gaskiya basuyi min ba babu wace ta dace dashi acikin su,
Sai lokacin nasa masu baki a,zancen su, da sukeyi
Nace ,a a Amal ai aure mukaddari ne matan mutun kabarinsa,
Aiko duk matan nashi suna son shi kuma idan lokacin haihuwan su yayi ai zasu haihu komai fa dan lokaci ne,
Daga haka ban kacewa ufan ba, daga zancen nasu,
Wanan zancen yasa naji duk tausayin sheriff yakamani nai alkawri araina insha Allah zan sa shi a,addu,a ta, koyaushe,

Aziza ce zaune duk ta rikita mai lissafin shi adole sai sunje sunga likita a kasar Germany, yadibata
Saida yagama jin korafinta yadan yi murmushi yace aziza mubar ma Allah zabin sa idan lokaci yayi sai yaba mu bawai sai munje muna ta nuna rashin tawakkalin mu akai ba,
Allah da yayi mu bai manta da muba,
Ganin da yayi shima dai din yana son yaga baby shi a duniya yasa har ya amince mata
Bayan aune aunen da sukayi likita yatabbatar masu cewa lafiya lau, maigidan yake kuma ita ma din zata iya samun ciki saida akwai wani abokin shi dan kasar indiya yafishi kwarewa ta wanan fan,ni sosai,
Don haka yace suna iya zuwa su ziyarce shi,
Bayadda aziza batayi da sheriff ba amma yace shi tunda lafiya lau yake bai zuwa ko ina,
Itada hindu sukaje gani doctor Khan a indiya din bayan duk wani awo da zai mata yayi ya,kam,malla ne yake sheda mata cewa, agaskiya mahaifarta bazata iya daukar ciki ba da kanta saidai inda zata yarda ai mata artificial insemination, to ko shi din sai kila ne cikin zai iya tsaya mata,
Haka suka dawo gida cikin tashin hankali ,don tasan cewa idan ko har baza ta haihu ba , ba makawa sai sheriff ya kara wani aure tunda nafisat itama har yanzu gata can shiru ba wani labarin ciki,
In akwai abinda bata kauna shine taga Ahmad dinta, da wata mace koda ko abokiyar aikinsa ce,
A ranan tashi yi mai mita ke nan , shi mamaki ma take bashi, saboda irin mugun kishin ta,
Tun ajirgi take ta rusawa hindu kuka, hindu tai rarashin kawar nata har tagaji,
Jiki ba kwari tadawo mai a Dubai suka hadu yana ganin ta tagane cewa batai nasaran tafiyan ta ba ,
Shima dai din cikin zuciyar shi baiji dadi ba,
Saida dare bayan sun gama komai sun kwatane take mai bayanin da likita yai mata, saida ta boye mai cewa ance ko artficial insemination din bazai zama dole ya tsaya mata ba,
Tana kai karshen zance yamike har zaune daga kwancen
Yana fadin tir Subbahanallah wa,iyazu billahi
Ai wanan rashin imani ne da kuma aikin jahilci, taya za ace mutum bai imani da Allah ,
Idon shi yai ja sosai don irin masifan da yake ta balballa mata,
Yakawo mata aya da ku hadisai masu kashe jiki,, yai mata,
Rai bace sukayi barci a wanan ranan batare da kowa ya kara cewa tak ba,
Tunda safe ya shirya tafiya a ranan saboda bacin rai yabaro Dubai din zuwa saudiya,
Satin shi guda ta wuce Nigeria saboda wayan da akai mai cewa hjy tsohuwa ba lafiya sosai,

Yana zuwa yaga irin yanayin da take ciki yasa adauko ta zuwa asibitin Abuja,
Cikin ikon Allah hjya tadan samu sauki,don tasamu kulawa sosai,
Acan Abujan ma bai tsira daga fitinar nafisat ba don ita ma din so takeyi suje suyi gwajin haihuwa ita dashi don aji ko may ye matsalar,
Shi mutun ne mai kokarin fitar wa natare dashi da hakkin zaman tare,
Don haka baki zuwa ba bayan da likta yai ma su shiya tayar wa nafisat da hankali,
Inada yace masu mahaifar ta ya samu matsala drug's din da take sha yasa ba zai taba iya daukan ciki ba,
Cikin takaici suka iso gida ga kukan da nafisat ta i she, shi da shi
Suna shiga gida tazauna tai tagumi hannu bibiyu ta ta zub da hawayen bakin ciki,
Tunda ya ajeta ya fita bai dawo gidan ba sai cikin dare yadawo,
Zuciyan shi duk ta jagule mai,
Duk kan su, su,biyu kusan case din su guda ne, ba zasu iya daukar ciki dan dama azizan da yake tana kan tracings na doctor ne tukun,
Yana sa ran cewa zata iya samun ciki indan har Allah yakawo,
Hakuri nafisat ta kama bashi akan don Allah yayi hakkuri kada ya bari iyayyen ta suji wanan zan ce,
Bai samu ce mata komai ba saboda bacin rai,
Tunda safe yaje gidan Bashir don yagaida hjy tsohuwa don tace sam bata zuwa gidan nafisat ta zauna
Saboda hakane aka kaita gidan bashir din don ta zauna can
Bayan sun gaisa ne da hjy sai ga ya shigo dakin dauke da,yar diyar shi tana wasa da fuskan baban nata,
Sheriff Ahmad ya mika hannu don yadauke sai taki, zuwa, ta kara rungumay mahaifin nata,
Bashir yadan hada kai da fuskan yar yarinyar yace, baki zuwa daddy ya,dauke ki ko,
Dariya yar diyar tayi na kuyya,
Hjy dake kwance gefe tace, yanzu Alhaji karami ba zan ga zuriar ka ba , sai bayan na mutu,
Sai tadan kama kuka kamar wace akai ma wani abu,
Dakyat suka samu suka lalabata shi da bashir, har tai shiru yai mata alkawarin cewa,
Insha Allahu zata gani bama zata mutu ba sai ta yi ta goya mai zuri,an shi,
Dahaka tadanji sanyi ,sanyi tai shiru tana fadin Allah yasa Allah yasa,

Amal ce ke son muje makkah mudan yi hutu can ni na rasa may yasa yanzu Amal ke son muje makka hutu,
Badon naso ba nashirya muka tafi, muka rufe gida sai makkah
Cikin dare muka isa garin don haka kowa dakin shi ya nufa saboda gajiya ga dogon tafiyan da mukasha,
Dasafe natashi da dan ciwon kai don haka ban fito ba barci nakoma yi,
Sai da rana yayi so sai na samu kan nawa yadan dai,na min ciwo,
Nafito cikin wani buje da riga yar rigar ta matse min jiki duk suran jikina yafito da kyau,
Sai bujen rigar da yani bude kamar dawisu daga kasa, shi gyalen jayan ne nadan yi rolling akaina, sai takalmana plat shoes da nasa akafa na,
Abinci na yana a cikin cooler saman tebur saboda dama nasan cewa any time natashi zan iske abin karin nawa da zafin shi,
Sam na manta cewa yau weekend ne Sheriff nagida yau baya fita ko ina sai massalaci kawai zai,sa,shi fita gidan,
Na zauna kenan zan fara cin abinci Salim yafito yace min yajikin nawa
Saida naja kujera na zauna tukun nace mai naji sauki dama gajiyan jiya ne kawai yan sa min ciwon kai,
Har zai fita nace mai dan Allah ina son in nagama yaikaini kundifal zan je in dan siyo wasu yan kaya ne da na manta bandauko ba,
Salim yace min zasu fitane da mustapha yanzu,
Cikin rashin damu nace mai ba matsala zan tafi da taxi idan na kare ai,
Ina ganawa na gyara jiki na tsab ba inda zaka iyagani surar jikina a waje don na rufe shi lif,
Taxi natare da niyar in shiga zuwa kundifal sayen kayan kwaliya irin na mata ,
Har zan bude motar naji maganar Sheriff a bayana yana cewa
Cikin dakarkiyar fuska yake ce min ina zan je batare da izini ba duk sai na dan dabur ce,
Don nasan cewa ina fita ko ina ai batare da fada ma kowa cewa ga inda zani ba,
Balle ma ni yar takari ba lasi,.
Aiko ina zan iya kutsawa dan nema kudi cikin gari batare da wani shamaki ba,
Wata zuciya tace min kidibi kan ki a,yada kika koma yanzu, ba da bane
Kina da ban banci sosai da da din,,,
Naba mai taxi hakkuri yatafi najuya da niyar komawa cikin gida
Sai dai ina ina kaiwa tsakiyan compound din gidan naga yafito da wata,
Landrover jeep let's one ban ma ko taba sanin yana da ita sai yau nagan shi da ita,
Bude min gidan gaba yayi ta gefen shi na zauna,.
Nasan cewa mawuyacin abune sheriff ya ja mota da kanshi saidai aja shi,
Ina zama ya sa lock yakule ko ina , wani irin sanyi da kamshi motar keyi,
Batare da ya kalle ni ba yace min ina zan tafi ne ma wai,
Cikin murya kasa, kasa nace mai ka Kundifal plaza zani,
A hankali yake tukin motar cikin gwanewa kira,ar sudes na tashi a hankali don kusan ko yaushe kira,ar shi yake sawa a motar shi,
Natakure wuri guda cikin rashin wal,wala, saboda bawai nasba dashi bane har yanzu,
Dan dama dama idan su Amal da salim na kusa nikan dan sake jikina kadan in suna hira insa baki,
Tambayar bazata naji yai min saura wata nawa mu kare school, cikin dan in,da,inda nace ina ganin kamar takwas yarage muna nace mai,,,
Yace o iam not even sure gani kawai nakeyi ko,
Abinda yasa ni dan yi murmushi ke nan yau a gaban shi ,
Nace takwas din daine kawai,
Zaiyi wani magana wayan shi tayi tsuwa alamar kira yashigo mai,
Nikan sai na maida hankalina saman titi ina ta kallon manyan gine ginen da ake tayi acikin gari ina mamaki irin cigaban da kullun aje samu agarin,
Agaskiya gwaunatin saudiya na kokarin wurin kula da jin dadin al,uman kasan don komai na,zamani su na kokarin su yi shi akasan daidai yadda bai saba ma shari,a ba,
Mun kusa kawai wane hankalina yakai ga wata yarinyar takari yar baka da ita tana tallan kaya a saman hanya duk tayi zufa saboda rana gata kuma a tsorace take don tana yi tana waige waigen yan bagaladi,
Tausayi yarinyar tabani don da gani yar sabon shigane,
Wani irin ajiyan zuciya nayi wanda har ya dan baiyyana afili,
Shima yana lura da hankalina yana gurin yarinyar da nagani yasan cewa dole in tuna wani abu dama,
A hankali na furta Alhamdullah, wanda ban tsan mani zai kai a kunen shi ba saboda dan rage karan kiran da ya yi lokacin da zai fara waya,
Kallona naga yayi cikin sauri yana mai dan lunshe ido yana sallama da mai wayan
Wanda nake kyautata zaton aziza ce don naji yana cewa saita zo din,

A cikin shago sashen saida kayan mata naje nadan zabo abinda nake bukata,
Sheriff ne na hango can layin saida kayan mata expensive one yanata dibawa yana zabe,
Tsayawa nayi ina kallon shi da mamaki a raina nace ashe dama shima zaizo sayayyane, a gurin,,,
Kallin shi kawai nakeyi da naga yayi layin saida gold ina binshi a baya ahankali ,
Wasu yan kune da sarka masu kyau Dubai naga yadauka, yamika mamai binshi abaya asa a gram,
Saida yagama ya,hada kudin dana wanda nadan zaba, ya biya, aka kai muna kayan har cikin mota,
Bayan mun shiga mota ne nafara yi mai godiyan kayan da ya biya min
Hannanu shi yadaga tare da rike min yan yatsuna da nake kokarin yi mai godiya yana ce min la,la,la,
Basai nai mai godiyaba yace duk abinda yai min kamar yaiwa kanshi ne don na can can ci hakan agare shi,
So daga yau duk abinda yai min baya son in kara yi mai godiya ko kadan,
Yana mai kallon gefena yace nagane ko nadan gyada kai a hankali alamar eh,
Inba mafarki nayi ba to tabbas yadan murza min karshen yatsa na abinda yasani cikin dan rudani kadan ,
Koda muka isa gida na dan tsaya na kwashe mai kayan da nasawo na hada da nawa,,
ban kawo ko mai a raina ba
Zan shiga ke nan naga motar Almustapha da salim a,she har da Amal suka fita ban sani ba,
Gani da kaya niki,niki a hannu na
Mun rigasu shiga ciki sai nawuce daniyar in kaimai kayan part din shi tsayawa yayi yana kallo na da mamaki yace min ina zan kai kayan
Tsaye nayi sororo nadan kali kayan shima na kale shi sai yace in tafi dasu duk nawa ne,
Cikin mamaki ido bude nake kallin shi,
Jin tafiyan su Amal dayayi shigowa yasa shi shigewa part din shi nan nadan tsaya sororo da mamaki
Wai yau ni fadima yar takari keda wanan kayan alfarman dana ga ansiya a,kundifal,
Jiki ba kwari na wuce dasu dakina kafin su Amal, su shigo ciki,

Sai cikin dare na bude kayan nadiba gaskiya saida gabana ya fadi sosai gani irin kayan da sheriffudeen din mu Ahmad ya saya min,
Dan kit din gold din na bude inata shafan set din a hankali,
Tex nagani ya shigo min a wayana,
Kaman kada in karanta sai na bude short note ne kamar haka
Wear d blue dress tomorrow morning ,,,
Da sauri nakai kallona ga blue dresses din dake gabana, nadan daga shi wani dogon rigane mai shegen kyau na yan lebon, ka taushi ga santsi,
Dogo ne har kasa da wani irin aiki a gaban rigar da fararen duwatsu, sai dan gyalen shi da ribon dake makale a jikin shi,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣5⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAW🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,

Bakaramin mamaki text din yabani ba saidai ban gama mamaki ba naji anturo min kofar dakina,
Firgigit nayi natura kayan gefen gadona na zauna kamar ba komai nakeyi ba,
Amal ce tashigo dakin da murmushin ta zo har inda nake tadan zauna bakin gado tace min,
Ashe baki barci ba nace mata eh, saita ke ce min yanzu yayan mu ke fada min cewa wai gobe akwai inda zamu da karfe, hudun marance,
Sainake cewa ko kin sani shine yace min yafada maki ai kin san da zancen
Mamaki yakamani tunda nasan cewa bai fada min komai ba,
Iyaka ce min yayi insa blue din kaya gobe kuma bai fada min komai, ba ai,,,
Washegari sai ban fito ba har wani lokaci ina daki ina karatu abina kusan ba wani abin da zan bukata wanda babu shi,
Aisha ce tazo min dakin da kukan ta wai umar ya dake ta,
Dole natashi nafita daga buyar da nakeyi yau, agidan don kusan ince
Yau ba wanda zaice yagani acikin gidan sai maman umar da taji shiru tabiyo ni dakina da abinci na tace min inci
Ta hanyar baya nabi don kada su gan ni cikin rashin sa,a sai gashi na hade da salim
Murmushi yaimin kadan yace wai fadima maye sirin ne kulun fa sai kara girma kikeyi da kyau,
Salim baka gajiya da zolaya kai ni yau ko mirrow ban diba ba bale in gyara fuska na,
Kafin inkai wurin Umar din saigashi yasamay mu inda muke tsaye da salim,
Nadan mai fada akan ya daina saurin dukan mutun ,
Idan yasaba ba zai ji dadi ba nan gaba in ya girma,
Nan na fara ba salim labarin marin da Almustapha yai min lokacin da na raki hajiya tsohuwa dawafi,
Salim yadinga yi min dariya kamar a lokacin abin yafaru,
Nima dai dariyan na kama nacigaba da fada mai yadda nadinga ji kamar in rama marina in gudu alokacin
Salim yana nunani yana dariya yace fadima an fada min cewa bakyaji kina karama sosai,
Dariya muka karasawa gabadayan mu nayo baya da niyar in dan waiga gefen tsuntaye na ingani sai naci karo da
Sheriff tsaye cikin wasu yan kananin kaya sunyi matukar daukan shi kamar shi yayi kan shi,
Fuskan shi atamke babu alamar dariya cikin dan dukawa nayi cikin ladabi na gaishe shi,
Batare da ya ansa ba yake ce ma salim yabi yo shi sutafi,
Saida naga sun bace min azuciya na ce bahagon mutun ba,a gane gabas dinka sai kaso,
A falo nukayi kicibis da Amal tace min kin gama kwanciyar dakin kin fito ne,
Murmushi kawai nai mata don nasan komay zance mata bazata yarda ba sam


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment