Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hasken da ke hasko min ta jikin window daki na,
Na rintse idona ina ci gaba da addua acikin raina,
Saboda na sadakar da raina cewa nawaya kare kawai a wanan ranan,
Can kuma sai naji shiru nadaina jin motsin komai kuma naga a daina wanan gittawan da ake ta min,
Duk da nasan cewa na rufe dakina yau da makulli, amma hakan bai hanani jin tsoro ba,
A haka barci barawo yazo yadan yi awon gaba dani,
Sai da asuba nafarka cikin dan firgita don ji nayi kamar za a shigo min ,
Saida na kwanatar da hankalina sannan na gane cewa ai ba komai har yanzu,
Saida na tabbatar da cewa gari ya waye kuma tabbasa kowa yadan fara fitowa waje
Natashi naje nai wanka nafito kenan ina shiri naji alamar ana buga min kofan daki da karfi kamar za,a tsaga shi biyu,
Na nufi kofan pa gigice nabude a hankali, hannu na guda yana rike da dan towel din da nake tsane jiki na da shi,,
Ga mamakina Aziza ce tsaye tana ganin na bude daki naga tai wani irin shock na nuna alamar mamaki,
Kallonta nakeyi sosai babu kaukautawa,na zuba mata ido, nima,
Ganin da nayi cewa , kallon nata bana girma da arziki bane,
Kallon tababiya naimata na kallo ta wani irin shekeke,
Na juyawa nayi da zumar in koma cikin dakina,
Sai naji ta turo kofar ita ma da karfi kamar zata bangaje ni,
Turus na tsaya gami da rasa na yi hannuna, yana rawa, ina kallon ta don inga abida zatayi,
Cikin tsayin wani lokaci shiru ya biyo baya sai dai na kula da ita kamar tana kokarin kallona tana na,zarin wani abu,
Nadai daure da nagaji da kallon kallon da mukeyi na ce mata lafiya dai ko hjy,
Cikin dakewa ta ce min da akayi may fa,
Cikin rawar murya nace mata, naga kamar kina bukatar wani abune a nan,
Ta buga min wata uwar harara ta kuta saida gabana yai mugun faduwa da ga ni irin yadda tai min,,
Tawani irin juya da karfi kamar mai fada da iska tawuce,
Nanta bar ni tsaye da mamakinta,
Gakuma wani irin tsoro da firgicinta da ya kamani
Don nasan cewa a yadda taimin yanzunan zata iya aiwatar da komai akaina,
Inda tawuce tabarni nan nake tsugune amma tsabar fargaba abinda take shirin yi min yasa ni zarya a corridor
Ina ta tunanen mai yasa Aziza take farautana haka saboda kawai na auri mijin ta ne ko ko may,
Da sauri namike na isa inda wayana yake jone a caji na ciro cikin sauri na kira layin ,
Sheriff tsayin wani lokaci naji shiru, sai can daga bisani naji computer tana gaya min wayar a kashe take,,
A rude na nemi layin Amal, itama hakan ne ta kashe wayar ta,
Sai dabaran kiran Salimat yazo min,
Ina samun ta ta dauka,nan na shiga, fada ma Salimat cewa tazo ba lafiya,
Hankalina a tashe nake maganar , hakan yasa tace min gata tafe,
Kafintazo saita bugowa maman Umar waya tasheda mata cewa tazo dakina da sauri ta diba mata halin da nake ciki,
Maman Umar tasamay ni na dan rakube a bakin gado ina kuka,
Ban boyewa maman Umar komai ba tun abinda Aziza tai min safiyan jiya,
Har zuwa cikin dare dakuma yadda mukayi yanzu da ita,
Salimat tafado dakin a rude nafada mata duk yadda na kwana a dakin da kuma abinda mukayi da ita yanzu
Saida ta nisa sosai can tace min shawar guda zan baki fadima,
Tace min ina passport dina nafada mata cewa yana nan,
Ita ta shirya min duk yadda komai zai kasance gare ni,
Tasa maman Umar ta kwaso min duk wani abin bukatana adakin dakuma wasu kudi masu yawa da naita boyon su da dadewa,
Salimat ta kwashe kayan zuwa gidan ta batare da sanin kowa ba,
Ta yadda ko CCTV ba za a gane cewa kaya ta dauka ba,
Duk wani motsin da za a yi a wanan yini a tsorace muke nida su salimat da maman umar don ko ruwan gidan nadaina sha yanzu,
Azizako sai fita takeyi tana dawo tare da wata yar doguwar takari fara wace tayi bleaching duk ta kode,
Ranan dole tare muka kwana da maman Umar adaki daya,
Washegari tun da safe nai shirin zuwa makaranta, saboda kasancewar itace ranan da zan rubuta jerabawar karshe,
Ina kallon Ummi cikin tausayawa saboda har yanzu jikinta baida wani karfi sosai,
Amal tana ta jana da hira saidai sama sama naje dan ansa mata,
Can dai tace min wai may yasamay ni ne yau taga duk bani cikin hayacina sosai,
Nadan kakaro murmushin dole nace haba Amal yaune fa zan gama exam dina aiko kinga dole in dan damu,
Dazamu tafi naba maman umar takarda nace taba sheriff idan yadawo kasan ,
Ina gama exam ko min ti biyu bamu karaba muka dauki shatan taxi nida salimat sai jedda,
Ina rugumay da Aisha wace mamata ta ce min in wuce da ita duk inda zani tabar min ita,
Batare da bata lokaci ba akai muna screening duk na ka gu inga mun shiga jirgi
Ina jin anfara kiran yan jirgin mu sai kuma kuma al,amarin ya juye min duk naji ba dadi, a raina,
Saboda nasan cewa Ummi bazata ji dadin abinda nayi ba,
To amma yaya zanyi dole ne in tserar da rayuwana ,
Karfe tara na dare jirgin mu yatashi daga jidda zuwa Nigeria,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story



Addu,an Ku a,gare ni tankar wani ruwa, ne mai karawa fulawa karfin tofowa daga kasa
Banda abinda zance maku sai dai in muna fatan alheri kasancewa a aljannan fiddausi a tare ranan gobe kiyama,
Allah ubangiji ya kara rufawa duk kan musulumi asiri duniya da lahira,
Allah yasa muna cikin wa,"yanda Annabin rahama zaiyi alfahari da su gobe kiyama, Ameen Ameen 👏👏
Nagode kware da irin kaunar da kuka nuna min tare da kulawa da fatan alherin ku a gareni



Muna tsatasye saboda jin da mukayi cewa matafiyan wanan lokacin su matso kusa,
A hankali na daga kaina na kalli Salimat wacce ke tsaye rugumay da baby Asma,u a kafadar ta,
Wani irin hawaye masu zafi da kuma kunar zuciya, suka dan silalo min daga ido na,
A hankali cikin dishashiyar murya ta kuka nake wa Salimat godiya bissaga arin taimakon da taimin,
Itama muryan ta a dishe take min magana, fadima naso ace wanan tafiyar da Sheriff zakiyi shi,
Saboda irin dadewar da kikayi baki gida kuma gashi yanzu kina a cikin lalura,
Kinga zargi da tuhuma zai biyo bayan isarki, gida a haka,
Saida na hade wasu miyau masu daci tukun nakuma goge hawayen da yakara zubo min na ce ai Allah shine shedata ,
Mundan kai wani dan lokaci a tsaye gurin salimat ta , tabani shawarwarin yadda zanyi idan na sauka a Nigeria, saboda tace saukar safiya zamuyi,,
Muna a haka har aka kira mu zuwa cikin jirgi, hanun ta na kama, saboda umurnin karshe da mukaji,
Na sake ta a hankali na nufi cikin jirgi, tafiya daya biyu sai kuma na juyo da sauri na nufota na rungumay ta,
A gabanta na tsaya, Itama kuka tasake mai karfi a lokacin, ta rungumoni zuwa jikinta, tace min kiyi hakkuri kinji hakuri zakiyi fadima
Kowa da irin rayuwar da Allah ya zana mai, ke taki kaddaran ke nan fadima,,
Ina kuka tanayi nasake ta dole badon mun,so ba,
Karfe tara na dare daidai jirgin mu ya ta shi daga birnin Riyadh zuwa Nigeria,
Tunda jirgi ya rufe nake kuka saida nagaji don kaina, nayi shiru tare da lomo tankar mai barci Al,amuran da dama suka dawo min tamkar yau suka kasan ce,,
A cikin jirgi ma ina ta dan sheshekar kuna, Ina tuna kalamin Salimat a gareni na karshe inda take ce min fadima ki gashe min da iyayen ki da yan uwanki insha Allah da na dawo Nigeria zan bide ki,
Kuka na sake a lokacin dan, tunawa da wanan kalamin,,,
Na kan kame Aisha dake gefe na tana barci abinta hankalin ta a kwance,
Ina kallo kowani set mutane na ta barcin abinsu niko idona, kem nakasa koda rintsawa a lokacin,
Saboda tunanen da ya addabi zuciyana, a lokacin, nasan cewa nayi nisa ke nan da su Sheriff da su Amal,
Can kuma wani sabon tunane yazo min ,
Ko yaya zan riski inna na da yan uwana,
Sai kuma kewan hafsi da mariya ya zo min fam a hankalina,
Ta gefe na naji wata yar siririyar murya na ce min hjy ko akwai abinda kike bukata ne,
A,hankali nadago na kalli gefen yar matashirya ma,aikaciyar jirgin ce ke min wanan tambayar,
Kai kawai na girgiza mata alamar a, a kawai sai naji tai min godiya ta wuce a hankali,
Sai kusan asuba jirgin ya sauka a filin jirgin malam Aminu kano,
Sain da jirgin ya sauka saida yakara wasu yan mintina masu tsayi sannan aka, bude kofar a ka manna matakalan jirgin,,,
Ban ko motsa daga mazauni na ba ina zaune har kowa ya gama fita,
A hankali na kama hannu Aisha muka sauko ,
Koda na sako kaina wajen jirgin sai naji na nashaki wata iska, mai yar tiririn dumi,
Saidai a cikin raina wani sanyi naji yau yau ni fadima ni ce a cikin kasar Nigeria,
Abinda nadade ina mafarki da tunanen hakan,
Sai gashi yazo min da sauki,
Bayqn shekara takwasa da nayi rabona da kasar ,
Sannu a hankali nake saukowa daga jirgin na rika aje kafa na ina maida yar uwar ta,
Sai na lura da cewa duk wanda ya ganni sai ya kara kallo na karo na biyu,
Ashe ni ban sani ba tafiya ta da irin shigar da nayi yana nuna cewa ni din wata hamshakiya ce ko matar wani babban mutun
Saboda yanayi na ya nuna a ,sarauce ko koma mulke nake komai nawa,
Wanda ni sam ban san cewa haka nakeyi ba,,,
Shigar da nayi irin dogon rigar nan ce mai mannewa a jiki nasa a ciki,
Sai sama nakawo daya daga cikin ire, iren dogayan rigunan da Sheriff ya saya min lokacin da mukaje kasar Arab ta tsakiya da kuma Dubai,
Don haka daya daga cikin su na sa a sama, rigar alkyaba ce mai tsananin tsada rigar da ganin ta kasan cewa ta matan mayan ce,
Ko a cikin larabawan sai wace ta isa take sanyata,
Yau ni fadima diyar inna yar kulu itace min a jikina,
Hular alkyabar ma tana da ban sha,awa, sosai, don zan iya rufe kaina da ita lif ,
Indan kuma naga dama zan iya sake wani dan mayafi dake manne a jikin rigar, ko in dan zarga shi yana rito a kasa,
Kamar na yafa shi, idan kuma mutum bai so sai ya sake shi ya biyo alkyabar ta baya kawai,
Toni sai na dan yafo yai min tamkar dai irin matan masarauta larabawa,
Alkyabar har wani dan jan kasa takeyi ina ta faman dan kamata a cikin style, Aisha na rike da hannu na guda, cikin shiga ta ban sha,awa itama,
Sai wani kamshi mukeyi saboda irin turaren dake a jikin mu,
Muryan wata yar matashiyar budurwa naji a gefena tace min dan Allah yar uwa ki dan tsaya muyi photo pls,
Sainai mata murmushi nace mata ai ba damuwa,
Mungama clearing na komai mun fito wajen airport din kadan ,
Ga kayana agabana kusan akwati uku ne da trolley dina,
Sai kuma nasake ganin wa yan nan yan matan da mukayi photo da su dazu acikin wata mota sun dan tsaya a gabana,,
Wacce nake tsanmani ita ce babba daga cikin su ce take magana yanzu,
Tace min har yanzu masu daukarki ba su iso bane,
Sai maganar da Salimat tafada min yafado min a rai inda tace min kada in nuna alamar cewa ni bakuwa ce a kano,
Don in banyi hankali ba zan iya fadawa mugun hannu,
Sai nadan yi murmshi nace ai zan tare taxi zuwa cikin gari yanzu,
Karamar ta riga babban magana tace anty safiya mu rage masu hannya mana, pls,
Sai naga mai suna safiyan tadan waige ni tace min idan badamu hajiya sai mu sauke ki inda zaki sauka don dama muma sako mukazo karbawa maman mu,
Driver su ta umurta da ya kwashe kaya na zuwa cikin Burt din motar su,
Saida mu fara tafiyane safiya ta dan waigo inda nake tace min wani unguwa zamu sauke ki hjy
Cikin murmushi nace mata inda zan samu motar zuwa dogon daji,
Takara maimaita sunan garin tace dogon daji,
Inane hakana kuma pls ta kalli yar uwar ta ita kuma sai tace wi malam Abu ka san dogon daji,
Tana tambayar drive su,
Shima dai cewa yayi gaskiya bai sani ba,
Safiya tace gaskiya hajiya ina ganin kawai muje dake gida indan yaso in kin dan futa sai a tambaya maki ko,
Sai nayi masu godiya da wanan taimakon da sukayi min,
A hankali gari na kara yin haske har muka isa uguwar su ta G R A
Ina kallon ko ina a unguwar gini ne na zamani kalakala kamar ba kudi aka kashe ba gurin yin su,
Wani katon get maigadin gidan ya wagale muka shiga,
Sai a lokacin nasha jinin jikina ganin wanan irin katon gidan da muka shiga, nakara matse hannu Aisha acikin nawa,
Ina karanto addu,an da yazo min a baki a daidai wanan lokacin,
Wata yar matashir dadtijiwar mace na tafi daga wani daki zuwa falon sanye da hijab har kasa hannu ta rike da tasbaha,
Cikin fara,ar ta take masu sannu da zuwa tana sa masu albarka,
Ganin da taimin tare da su yasa tai saurin kallon su da mamaki,
Karaman ce ta zagaya gurin hjy tace umma bakuwa ce muka zo da ita daga saudiya take sai muka ga ba,azo daukanta gashi kuma gari bai gama wayewa ba alokacin shine muka bata lift zuwa cikin gari,
Sai a hanya ne muke tambayar ta ko wani unguwa zata shine take fada muna cewa ai wani gari zata ba anan kano zata tsaya ba,
Hjy ta dan kalleni jin da tayi cewa aiba a kano zan tsaya ba,
Kujera ta nuna min tace in zauna mana gamu a tsatsaye,
Gashi nadauko gajiya atare da ni,
Bayan na zauna ne take kara tambayana inda zan tafi,
Nikuma a lokacin nake kara gasheta ,,,
Bayan mun gaisa ne take kara tambaya ko wani gari zantafi,
Nace mata dogo daji,
Saida ta kara nanata sunan garin saita dan kalle ni tace min a wata jaha garin yake sai nai shiru,
Ido hajiya ta tsura min nadan wani lokaci can ta juya inda safiya take zaune tace ki kaita dakin ku tadan huta kafin a hada abin kari,,,,
Da alamar dakintane takaini ita safiya din don gani katon photo ta danayi a gefen gadon tare da na mahaifiyar ta
Wankanayi nadauro alwala nagabatar da salla da ban samuyi ba, tunda asubah,
Barci yadaukeni inda nake ,zaune ina lazimi, nadan wani lokaci,
Daidai lokacin da na farka ne hjy umma ta shigo dakin na safiya,
Ganin da nai mata yasa ni kokarin tashi zaune, takaraso inda nake zaune tazauna gab da ni bisa bakin gado, nadan gyara zama na, na gaisheta, shiru yadan biyo a cikin dakin nadan wani lokaci,
Can tace min may sunan ki diyata, a hankali nacr mata fadima, tace min masha Allah suna mai kyau,
Fadima kina da aure , tambayar da taimin yasani saurin daga kaina na kalleta sai kuma na dukar da idona a kasan dakin ina mai wasa da yan yatsun hannu na,
Can dai na ce mata eh,
Sai naji tayi murmushi irin na manya tace min naga alama ai don kina da natsuwa so sai,
Dogon dajin garin kune ko garin mai gidan ki,
A hankali nace mata garin mu,
Sai mukayi shiru gaba dayan mu,
Can tace min ki sake jikin ki da mu fadima Allah ne ya hada mu dake
Ai ba yau ba nake tura yarana dauko min sako ko kuma ni inje da kaina amma bamu taba dauko kowa a motar mu ba don gudun shiga matsalar rayuwa,
Takara dan matsowa gab dani tace kada kiji komai ki fada min ko may ke faruwa da ke haka
Don tun shigowar ki gidan nan nake zargin kamar akwai abinda ke damuwar ki,
Nai shiru ina tunanen maganar ta da ga karshe dai na daure na fada mata dan kadan daga labarina,
Yadda Aziza ta sani gaba don ganin ta halakani ko ta halin ka,ka,
Taiwani irin ajiyar zuciya tace gaskiya fadima kina da sauran kurciya atare da ke
Aida ba ki wuto Nigeria ba da a gidan Salimat kika zauna har minin ki ya dawo sanan kuma ai saudiya ba Nigeria bace akwai security ta ko kada kiyi mamaki duk wani plan nata hukuma saudiya suna sane da ita,
Sai nadan dago kaina da sauri na kalleta ta daga min kai alamar eh kware da gaske kuwa,
Kada kiyi mamakin jin hakan daga gare,
Sai tace to yanzu dai yadda za,ayi kitashi ki je ki yi breakfast tukun kafin a tambayo min ko wani state garin ku yake,
Lokacin kusan bakwai da rabi na safe, don haka ban tsaya jiran komai ba na tashi na dan kimtsa zuwa falon gidan,
Saida muka gama yin breakfast din ne su safiya take dan ja na da hira kadan kadan, ina bata ansa jefi jefi,
A lokacin hjy umma ta shigo falon cikin shirin ta na zuwa office,
Daidai lokacin malam Abu ya kirata a waya yake sheda mata cewa a cikin jahar sokoto dogon daji yake,
Ta iso gurina cikin fara,ar ta tace min fatima kin ji a she a cikin jahar sokoto kuke,
Don haka zaki bari har gobe idan kin huta malam Abu driver yakai ko ya ,ya,
Sai da na dukar da kaina kasa nace, a,a umma yau dai zantafi insha Allah,
Tunda akwai lokaci shiru hjy umma ta yi har nawani dan lokaci, sai kuma naji ta dafani a hankali ta ce fatima ba,damuwa zan sa a kaiko gida yau insha Allah,
Daga haka bata kara cewa komai ba sai ta mike tsaye tadaga wayan ta tana kiran layin malam Abu driver,
Karfe takwas da wani abu mukabar garin kano muka dauki hanyar sokoto,
Ina bayan mota nida Aisha ina ta kallon hanya da irin cigaban da garin kano yasamu yanzu,
Saida mukabar gari da nisa muka kama hanya dakyau
Nadinga kallon irin yadda titin Nigeria suka lalace,
Sai natuna da yadda titin kasar saudiya suke da kya da lafiya
Amma dai ba garuruwa da yawa kamar munan kasar, Nigeria,
Yayinda muke ta kara shiga gargada da kuma rashin kyauwon hanya,
Duk hakan bai sa nadamu ba nidai gurina kawai inga mun isa gurin su inna na kawai,
Bayan irin mugun gudun da malam Abu yayi da mu saboda yana da gurin komawa yau, kano,
Sai kusan la a,asar muka shiga garin sokoto, duk a gajiye muke
Sabosa lalacewar hanya da baida kyau, ko kadan,
Saida muka dan yi nisa a cikin garin malam Abu yadan samu wani guri gefen gari yake wani dan fari saurayi mai suffan fulani dake gaban wani shago,
Ko ina ne hanyar zuwa dogon daji,
Dan saurin yace mikewa zakayi inda kaga godabe ga ta lakwasa zakabi, har sai ka kai inda flyover, sai ka kara dau hanya kamike street,
Malam Abu yai godiya yakama hanya, damu ina baya sai waige waive nakeyi ina kallon garin sokoto da mamaki,
Kwatacen saurayi muka bi har Allah ya kai mu inda muka mike hanya zuwa garin dogon daji,

Mun isa lafiya mukaga katon signboard da aka rubuta alamar iso wa garin dogon daji,
A hankali malam Abu ya gangara zuwa cikin gari ina baya ina raba ido ko zan gane gidan mu sai dai gaskiya na kasa ga ne wa,,
Kamar yadda kowa yasan cewa kauye a na yin daba daba na matasa dakuma manyar dadtijai ko a garin dogon daji ma haka muka gani
Kasan cewa marance yayi sosai a lokacin kusan kowa na waje, gurin hira,
Wani daban yan matasa malam Abu ya tsaya da motar shi,
Yadan yafito wani dan matashi dake tsaye gaban saura yana ta zuba surutu,
Da sallamar shi ya matso gurin mu saidai idon shi na bayan mota don yaga ko suwaye a cikin motar,
Dan Allah tambaya muke yi malam Allah yasa na sani
Gida inna muke tambaya ,
Inna wacce ina inna ai yawa aggaresu garin ga,
Daidai lokacin suma abokan hiran matashi suka iso gaban motar mu,
Yawaiga yana cewa yan uwan shi da ke tambayar shi kai wai minana,
Tambayana sukai wai gidan inna suka tambaya
shina nice masu wassan iyakan innan da aggarin ga,
Daga bayan mota nace masu inna yar kulu maman mariya da Abdull,
Sai mutum guda daga cikin su yace kai gidan yar kulu na sarakuwa illu teacher,
Sainag duk sun juya inda wasu yan matasa keta wasan guje guje,
Sai yace Dule kai, dule taho nan ga wata mace na tambayar gidan yar kulu
Da sauri yaron da akakira da Dule ya iso gurin da motan mu

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment