Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ibada da tsare dokokin Allah,
Yadda yakamata ,,,,, kuma nasan cewa duk wani kariya tsuhuwa ta tanadar maka dasu tun kana karamin yaro har izuwa yanzu,,,
San nan ina sane da duk wani gudun mawar da mijin mahaifyar ka ke yima,
Nikaina ina da wata yar alaka da shi wanda bakowane yasani ba kasancewar shi malam din mutum nei mai gaskiya da rikon amana,
Kuma inajin dadin yadda ka dauki malam din tamkar mahafin ka,,,,
Kakula ka kuma kara kula sosai da al,amura, su
Kaga yan uwanka da ke turai sam ban gane ma komai ba gamay da karatun da sukaje yi a can turai din
banda dan banzan kudin da nake ta tura masu,
Inbadon Allah yayini nai karfin arziki ba da yanzu na durkushe kasa warwaras,
Kuma mahaifiyar su bata son sam ayi mata zancen su,, ido nasa masu ita da su
Yakare maganar nashi yana hade wani irin malolon bakin ciki,, da ya tokaro mai a makogwaron shi,,,
Duk sai dan yaji badadi azuciyar shi,
Ada yadauka cewa uban bai damu da rayuwar shi ba sam,
Amma yanzu sai yake fahintan cewa ashe duk wani motsin shi mahaifin nashi yasa ni halarci ne kawai yake nuna rashin ko in kula gaban hjy,mama,,,
Muryan Abba ta dan dawo dashi seti,
Yace gamay da yarinyar da nai ma magana badiyar kowa bace illa diyar Alhaji abokina kuma amina,
Wanda ya nuna min cewa yana son hada zuri,a da daya daga cikin yara na da nashi,
Hakan yasa naga ba wanda yadace da wanan hadin sai kai,
Don duk cikin ku ba wanda zan iya tunkara kai tsaye da wanan zancen sai kai
Duk da kaima din bawai zan tursasa ka akan dole sai kayi bane ,aa kawi in kaga zaka iya sai kaje kuga juna da yarinyar intayi maka shi ke nan
Ahmad yadan dukar da kanshi kasa yace a,a Abba basai naje ba idan yariyanyar tayimaka is ok banda matsalar koma ni
Da mamaki mahaifin ke kallin shi wanda bai,taba zaton abin zaizo mai, cikin sauki haka ba
Hakika babana kadai halas ne tabbas nasan ka gado halarci gurin iyayen mu sosai
Don bakowani yaron wanan zamanin bane za,ayi juyashi cikin saukin kai haka ba
Tundai yadda kake jin kanka acikin lokacin ka, hakan ga, ga,kudi ga ilimin kowani iri katara,,
Nandai yabar komai wurin Alhajin nashi, akan yayi duk yadda yakamata don shi baida lokaci wada tace na kanshi yanzu,,,

Abuja yawuce ranan inda yabi jirgin da yatashi marance zuwa birnin taraiyan,
Saboda mr William's jirginsu zai yi saukan asuba ne,,

Komai ya kan kama a can birnin taraiyan inda shugaban ni sukayi farin ciki da wanan masana,antar da za,a kafa acikin kasa don cigaban kasa da al,ummanta,,
Kwanasu uku suka juya zuwa Dubai don kai takardun rije,jeniyar da akayi da Nigeria,
Al,amarin auren shi kuwa Alhaji da bashir tare da sauran yan uwa suka gudanar da komai kamar yadda addini da al,ada suka tanada,,,
Anje kano wurin iyayen amarya anyi komai cikin tsari,
Ansa lokacin daurin aure nan da sati uku masu zuwa
Don mahaifin nata yace yafi son taje can tayi azumi agidan mijinta,,,,
Duk wanan zancen hjy mama bata da labari saida aka tsaida komai na buki sanan yayan nata ta bugo mata,
Ga hauka irin nata aiko saita hau fada tana cewa an munafunce ta,
Ai diyar yayanta mace wace ta ke tayar wa taso hada auren ta dashi amma shine yayan nasu zai masu wanan cin layin
Hauka iri iri da zagi anjishi gurin hajiya mama,
inda take cewa ita ba ruwanta da wanan auren cin amana da yayan nasu yayi,,
Komai cikin mutunci aka,yishi tare da yan uwa da abokan arziki
Inda ango nacan Dubai yana yin sha,anin gaban shi,
Bashir ne yake gudanar da komai da yakamata ango yayi
Hjy tsohuwa tayi bakin ciki sosai da akace yar uwan hjy mamace Ahmad ya aura kuma tayi fada har tagaji inda akaita bata hakkuri,
Daga karshe tayi waya da Ahmad din yakwantar mata da hankali har ta dan huce,
Amma badon ta so ba yaghana dai batace komai ba ga al,amarin .


A saudiya kuma muna can abin mu munata harkokin gaban mu don ba wani aiki mai yawa da muke yi kamar da
Don tunda muka samu wanan aiki da hajiya laila tai muna hanya aikin gidan sheriff din mu
Agaskiya mun rage wahala so sai bakamar daba don yanzu ko abinci bai muna wuya
yanzu duk yan gidan mu sun,dawo da aikin su nan gidan
saboda aikin da za,ayi na abincin azumi dana lokacin aikin hajji , watau abincin Karama,,
A, yau muke sa ran dawowar sherrif din mu daga dogon tafiyan dayi nakusan wata guda, zuwa gida Nigeria da kuma kasashen larabawa ta tsakiya,,
Munyi aiki sosai saboda dawo wan nashi,,,,,,
, aikin kamar su ,,gyaran gida zuwa yin abinci mai kyau da kula da dabbobin gidan, saboda kada sheriff yace mun barsu da yunwa
Wanda agaskiya da yana nan da bai nan duk gudane muna kula da komai tamkar yana gari,,,
Don shi kuma ,akidar shi da ya iso daga tafiya in yayi, gurin dabbobin shi zai fara zuwa yadan diba lafiyan su sai dan yi wasa da su kadan san nan ya shige gida,,bai kara fitowa indan ya shige,,
Yau ma hakance ta kasance ina wurin da nake kiwon tsuntayen
Jiminan da ake kiwo a,gidan tana miko min wuya ta ina tsokanar ta ina ta dariya dagani sai tsutsayen a wurin,,,
Dariya na nake tayi hankali kwance don ganin tana son ta tsakwace min hannu niko ina cirewa cikin sauri,,,,
Kamshi yan company al,rahab naji duk ya cika min hanci na
Ko ban waigaba nasan Sheriff ne tsaye a wurin,
Don ni Har yanzu nauyin shi nake ji sosai tun lokacin da yasan cewa na fara period, ban son in,ganshi,,,
A,hankali yataka har zuwa inda kejin Akun shi yake,,
Sannu da zuwa nadan yi mashi sama sama lokacin yana magana da Akun na,shi,,,
Saina dan saci kallonshi naga yadan ramay har da baki yadanyi, kadan
Ganin bankalin shi naga tsuntsun yasa nadan juya ahankali don in,tafi,
Zan wuce shi naji muryan shi yana ce min ya jikin hajiyan mu,
saida nai mamakin jin wanan tanbayar daga bakin sheriff din na mu daidai wanan lokacin, dayake tare da gajiyan tafiya,,,
Nace mai taji sauki
Yace min, ,I hope tana ganin likitanta har yanzu nace mai
eh, kawai
Cikin gudu gudu nabar wanjen,
Don kada yakarayi min wani tambaya kuma,,,
Yagane ni sarai kunya shi nake ji
amma dai shi ina ruwan shi tunda yasan cewa mace nake
kuma ai dole inyi wanan abin,,,

Bayan yadawo da kwana biyu mukayi baki daga Nigerian
Sai murna nakeyi da rawar kafa ganin ga mutanen Nigeria sun zo
Don ji nakeyi kamar zasu bani labarin inna na,,,,,
Sunkai su goma maza da matan su
duk da mu bamu fahinci komai ba saidai munga ana ta gyara wuri
kamar irin dakunan dake rufe ba kowa acikin sh, kuma ba ko,,yaushe ake bude su ba,,
Sai gashi Yau ,duk an bude su ana ta gyara ana sa wasu kaya kamar na kwalliyan mata aciki, su,,,
Nidai ban fahinci komai ba
Sai kusan yamma zamu tafi gidane mama may abinci take ce muna wai muzo da wuri gobe saboda munga anyi baki yan kawo amaryan sherrif din mu daga Nigeria,,,,
Amarya na kara maimata maganar na ta,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:25] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Murna da annashuwa sun tabbata ga mutunin da tunanen hisabin Allah ya hanashi tara dukiyan ta hanyar haramu,,,,

Yan Huguma groups da Teema luv group maman fati group, mama nawal group Allah ya kara dauka yasa mugama da duniya lfy,,,

Almost true life story,,,,

Ta ce min eh
ai sheriff din mu yayi aure ,itace aka kawo shiyasa muka ga jama,a sun zo daga Nigeria,,,
A gaskiya munyi murna sosai dajin cewa sheriff din mu yayi aure
Farin ciki fal azuciyan mu saboda munyi sabuwar uwan daki,
Duk da ba musan halin taba mun dai yi murna da hakan,,
Ranan cikin farin ciki muka bar gidan muna jin dadi
Muna zuwa gida labarin da mukaje ma hajiya dashi kenan yau
Duk da bamu san ko wace ce, amaryan ba daga cikin bakin da,su kazo,,,,,
Saida muka gama komai muna zaune sai Rugaiyya ke min ita gaskiya bata ga alaman amarya daga cikin bakin da suka zo ba ,,,
Saboda may kikace haka inji yumma
Naga duk kamar ba yara bane kuma babu wace tadan nuna alamar lulubi ko wani dan jin kunya kunya, hakan ga kamar yadda amare ke yi,,
Ina gefe ina gyarawa hajiyan mu kayan wanki da nayi mata tun daren jiya
Yau da safe ban samu gogewa ba,
Hiran su yasa nadan shiga tunane cewa aiko koni din banga alamar wata yar gaye ko amarya wani sign na amarya ba cikin bakin,,,,
Sukaina ce tace ita,ko gani takeyi kamar wanan bakar mai dan rawan kan nan itace amaryan
Don taji lokacin da take cewa don may za,a ajeta dakin kasa
Ita tafi son sama tare da na sheriff,
Sai wata mata daga cikinsu tace ai tunda nan yabaki sai kiyi hakkuri dashi hakana
Taji ana cewa Nafisa don Allah kibi wanan mutumin asan nu kin daifi kowa sanin yadda akai wanan auren ,,,,,
Ki diba fa shekara nawa kina zama agida kuma kiji yadda kaunar mahaifinki tanuna hassadan ta da auren naki
Yanzu duk wani jidakai ko wani girmankai da iya boko irin naku yakare
Indan har kina son wanan daulan yafita hannuki kina ji kina gani to bissimillah ki ga ki ga ,,,,
Bata karasa maganar ba taga ina falon ina hada masu abinci sai tai shiru
Banji karashen maganar tasu ba inji Sukaina,,,,
Cabdijam inji Anty Rugaiyya
inko har wanan din itace matar gaskiya wata killa ba shi yabide ta kamshi ba,,,
Duk hiran da suke yi ina jinsu sai nazarin maganar nakeyi
Karshe na nisa nace koma dai may,ye aishi ya, auro abinshi mukan namu aiki mu bar masu guri,,,
Can cikin dare mun fara barci sai kawai muka dinga jin ihu har na tashin hankali,
Nai zubur zan tashi infita sai hajiyan mu tace min walahi duk nafita dani za,a hada
Tace min Askarawa ne da yanbagaladi suka kawo samamay yau shiyan mu,,
Wata kila watace suka gani suka biyo ta har nan don suka ma
Jin haka duk mukasha jinin jikin mu don tsoro, daidai kofar mu suka tsaya suna ta buga ma wa, yanda suka kama tsawa,
Muna labe munyi shiru kamar ruwa yaci mu ba wanda yayi ko dan guntun motsi cikin mu
Hakan da suka ji tsit yabasu damar wuce don suna zaton ba takari acikin gidan ,,,,,
Don da datakari da masu shi sunji tsoro sun fito dagudu, suna batun tserewa,
Amma jin shirun dasukayi unguwar tamu yayi,
yasa suke zaton sauran gidajen duk na,larabawa ne kawai,ba wani sauran takari wajen,,,,
Munajin tashin motocin su muka firfito, daga inda muka boye,saida wasun mu suka kewaya don tsoro,,
Nice, ta,farkon fitowa wajen gidan mu
don muga kowace ce aka kama daga cikin ,
Duk da gari bai karkare waye ba,
Amma mun,gane cewa lawisa ce aka kama
kuma ita lawisa din nan tanada diya biyu,mace da namiji,,,,,da ta samu dawani balarabe
yaran kuma sun biyo balaraben sosai,,,,,
Ashe koda aka kamata bada yaranta ba saboda ganin da sukayi yaran farare ne,,,
Haka muka karasa wanan daren cikin fargaba da tashin hankali,,
Dasafe kafin in,wuce naje gidan su lawisa na diba yaran nata,,
Aiko nasamay su zaune yaran suyi kuka sun gaji
sun hada kansu wuri guda sunyi tagumi zaban tausayi
Jawo su nayi zuwa wurin hajiyan mu
Aiko hajiya naganin mu tamike tsaye
tana,cewa, fadima kina da hankali kuwa
Kowa baije yadauko ma kanshi wahala ba ke zaki je ki dauko muna
muna fama da kan mu ,muma tamu ta,ishe mu ,,,,
Shiru nayi saida nabari tagama magana nace haba hajiya wa yan nan yaran fa suna bukatar taimako a yanzu,
Sanan kituna wasila fa tana iya kokarinta da mu,
Idan baki da lafiya muna gurin aiki takan zo tana diba muna ke,,,
Sauran yan uwana da basu fita ba sukayo kaina ca,,,,
Kamar zasu cinyeni dan ya,,
Yaran na takure gefe guda sundan rgumay hannun su ,sun wani man,ne majunan su ,zaban tausayi
Jawo su nayi nai masu wanka cikin sauri nadauko abinda zan karya kumallona da shi nabasu,
Har dan abinda zasuci darana saida na hada masu,shi ,sanan nafita zuwa wurin

Nikaina nasan cewa yau,na makara sosai,
Ina fita taxi, Kai tsaye na fito na mika ma mai taxi kudin shi ,
Duk da naga Almustapha a,kofar shiga gidan namu, kauda kaina nayi gefe kamar ban ganshi ba,
Don shima yasan cewa bazan gaishe shi ba,
Fada yafara yi min baiko kai aya biyu bu nadaga mai hannu alamar ya isheni hakana,
Cikin mamaki yake kallo na yana kuma yaba karfin hali irin nawa ,
Har shine zan daga wa hannu,
To yau kowaye min tsaye sai nabar gidan nan ,haka yake fadi azuciyar shi,,,
Na ci gaba da magana ina cewa shike nan don muna aiki bamu da incin kanmu ko wani lokaci na kan mu,
Ai yakamata a,dinga muna uzuri aduk lokacin da aka ga mundanyi wani abu bawai adauki matakin da babu dalili ba
Da in tsaya kana mari na ko zagina duk lokacin da kaga,,,,
Ban samu karasawa ba naga Sheriff's atsaye gaban mu yana muna wani irin kalon mamaki,
Mari mari fa,, Almustapha ,Subahanalla subahanallah ka doki mace macen ma,,,,,
Sai ya kasa karasa wa, naga kawai ya dunkule, hannunshi ya dan daki gudan da shi yana fadin subahanallah,,,
Nikan nasa kai na wuce cikin gidan ina jin yana cewa yaushe kai wanan aikin bansani
Ko kana dukan mace ita wanan din may zaka daka acikin ta,,,
Wuce wa yayi ciki gidan ran,shi bace dagani kasan yayi mugun, hasale ,yabar almustapha a wurin bakin get din, cikin damuwa,,,,,
Don ko yaga fushi yau karara a,idon sheriff din,,nashi wanda rabon shi da yaga wanan fushin yadade,,,,

Ban tsaya yin komai ba gurin tsuntaye nafara zuwa sudake da rai na basu abincin su,,
Don kusan kowani tsuntsu da kalar abincin shi,
Ruwa kuma akwai wanda nake sama ,magani acikin nasu, ruwan shan da samun kuzari da lafiya,,,,,
Danaga komai ya kam,mala sai na bar gurin aikin zuwa cikin gida don inyi aikina,,,
Daidai gurin da dawakai da dabbobin gidan suke yake tsaye ya rike ciyawa a hannun shi yana ba wani dan farin doki karami,,
Ke yace min cikin tsawa saida naji tsoro wanan kiran,
Ya,akayi mustapha ya mare ki yaushe ya,mare kuma a ina,,
Wani tambaya zan ansa daga cikin ukun,,,
Duk da ina jin kunyan shi yau sam banji ba
Saboda dama tun da daren jiyan abinda akayi wa lawisa a,kasan ya tayar min da hankali sosai ,
saboda naga bamu da wani gata ko daraja a, wanan kasan.
Batare da na bashi ansa ba sai na fashe da kuka mai kuna zuciya
Yana ganin na fara kuka sai ya rintse idanun shi don bacin rai jiyakeyi kamar a watsa ma garwashin wuta ajikin shi,,,,
In akwai abinda ya tsana yaga mace cikin yanayin kuka ko ban tausayi,
Ganin idona rintse yasa shi ya sulale yagudu yabar wurin don bai iya daurewa yana jin wanan sautin wanan kukan a rashi ,,,,,,,
Ni ko,kukan da , samun yin ,shi ,shiya dan sa naji wani dan sanyi azuciya na
Koda nagama kukan na dan kai dibana inda nagan shi tsaye sai naga wayyau, ba kowa wurin,
Haka na wuce nabar wurin jiki ba wani kwari don jinakeyi kaman ban iya tafiya,,
Ashe da sheriffudeen din mu yabar inda nake tsaye komawa yayi sama yana tunane azuciyan shi,,
May yasa almustapha zai dauki hukunci mai tsanani akaina,haka har da mari mari fa,,,,,,,,
Wurin nabari zuwa ciki don inyi aikina,
Ina shiga cikin gidan sam na manta cewa akwai bakin, agidan mutanen Nigeria dasu kazo jiya,,, saboda tashin hankalin da nake ciki,
Wa,daga cikin bakin,suna falon gidan zaune su,nata har kokin su,
Sai narasa ta ina zan soma aiki na ma , tsayi nayi wuri guda,,,
Don ku san ko, ina akwai mutane a falon,,,,,

Ina nan a tsaye tsakiyan falon sai naga wata yar dattijiwan takari bakuwace daga cikin mu, ta zo inda nake tana min murmushi ,,,,,
Cikin girmamawa take magana da harshen
larabci takecewa tundazu take jiran shigowa na ,,
tai min sannu da zuwa,
Tace min itace mai kula da aikin goge goge yanzun agidan
Da duk wani aikin da ya kushi cikin gida,

Mamaki ne ya kamani don naga aiko jiya nice nayi wanan aikin,kafin muje gida,,,
Sai,gashi jiya zuwa yau da safe wai an canza wata mai yi,,,
Kenan an,dakatar dani daga aikn ake nufi ko,,,

Daidai zan fita inbar falon naji mama mai abinci nace min inzo indiba ko abincin da suka dafa yayi ,,, kalonta nayi itama cikin mamakin
Don suna son su ba mutane abin kari,,,
Nuna kaina nayi ina waigen gefe da gefe na ina, nufin ni takewa magana kuwa,,
, tace min eh,,, dani take
Ba mussu nabi bayanta zuwa inda naga tabi, kitchen ta nufa,
Abinci ne na alfarma aka hada masu kyau da dadin gani,sai kamshin dadi ke tashi,,
Tana kokarin bude min kulolin abinci nace mata la,la,la ta bari don Allah komai ya yi,
Mama mai abinci tace min in bari ,in,diba in gani, in, akwai wanda bai yi ba sai su sake,dafa,wani,,,,,,
Nace mata yayi haba mama, yau kika fara wanan aikin,
Ta danyi murshi kawai na nuna kula da girmamawa
Niko duk mamaki ya cika zuciyana ga dinbin tanbaya min fal a,rai,,,,
Bayan anjera komai wurin very neat, ,
Rugaiyya tace min inje in fada ma mutanen gidan cewa table is ready,,,
Bayan mun fita Rugaiyya ke min bayanin cewa yanzu aikina shine kula da duk wani al,amarina aikin cikin gidan, nan nice da alhakin kuwa, dashi,,,,
Don Almustapha ancanza mai wuri zuwa can company

Nace ma Rugaiyya yanzu duk yawan mu sai nida nake yar karamar ku za aba wanan aikin
Wanan aikin aida mama mai abinci yadace bani ba

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎🐎
[10/4, 14:26] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣1⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


A, kulun muna gode ma Allah Subbahanahu Wata,ala daya Halice mu a matsayin musulumai,
Ya Allah muna kara gode maka da ka bakayi mu kafirai ba,
Allah yakara ma musulunci daraja da daukaka 👏👏👏

Allah ya kara rufa ma duk al,uman musulumi na duniya asiri

Almost true life story

Maimakon in yi farin ciki da cigaban da nasamu ,
Nikan hankalina yana gurin irin wulakancin da akeyi wa yan takari,,
Ga lawisa ta wuce tabar yaran ta acikin duniya, batare da sanin makomar su ba,,
Shin wai may yasa ake zuwa wanan aikin mai wahalar tsiya ,
Wahalar da ba riba ko kadan sai in Allah yataimaki mutum,, yatar fa wa garin mutum nono to shine zai tsira da dan wani abu,,,
Duk abinda aka girka a,gidan ranan , saida na sdibar wa,su hajiyan mu da yaran nan, na lawisa,
Tun lokacin tashi baiyi ba nabar gidan aikin na mu,
Sauri nakeyi zuwa gida don inkai ma hajiya abinci suci,
Natafi da niyar gobe insha Allah zan daure in ma sheriff din mu magana ina son ataimaka mu,na indinga zuwa gida da wuri don indan kula da hajiyan mu da yaran lawisa,,, ,,,,,
Cikin sauri sauri na isa gidan tun ban shigaba nake jin dan she,shekar kukan yar macen yarinyar,
Wacce ban ko san sunan ta ba ma
Da, sauri na karasa shiga ciki don jin ko maya sami yaran
Hajiya na zaune gefe tai tagumi, sukuma yaran sun dan tsuguna daga bakin kofa shigowa cikin gida,,,
Banko kalli hajiya mu ba wacce ta nuna mamakin ganina nadawo

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment