Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan bidi hanyar abinci,
Ummi tace mata amma Amal baki da tausayi yarinya tana fama da lalura irin haka har zakina ce a kyale ta,
Dan murmushin yake nai ma Amal kawai azuciya na kuma ina cewa ummi ta kyaleta tana da gaskiyar ta sanin da tai min bana yan zuba,,,
Maman umar takawo min fruit's masu dan sanyi da kuma lemon kwanko,
Nadanci kadan sai kuma yau naji kawai ban ra,ayin ko fruit din
Wani irin amai ne yataso min narike bakina da hannu guda da sauri nature kayan plate din gefe na fada daki, na,
Aziza ce ta tashi da sauri tabi bayana don ita azaton ta ina shirin zubar da cikin ne,
Nafito daga bandaki ke nan tafado min cikkn daki a hasale,
Cikin tashin hankali take maganar ta, fadima may kikaje kikayiwa dana,
May aka baki ki kasha kike wanan aman haka,.
Don lafiya kalau kibar gidan nan koda natashi akace min kin tafi asibiti, wai,
Tana batun kara matsowa kusa dani , ni,ko ina tsaye ina kallon ta cikin mamaki,
Muryan Sheriff ne mukaji ta bayan mu yana cewa,
Aziza cikin ki ko nawa da mamaki ta waiga inda yake tsaye tana mai kallon mamaki,
Cikin rashi, facinta, ta ke mai, kallon shi wani iri,
Ya buga mata tsawa yace may kike zaton zatayiwa cikin da ke da uban shi,
Cikon da baida uba wanda ba,a yarda dashi shine ake ma yunkurin halakawa akoda yaushe,
Yanuna ni amma ba irin wanan mai uban ba, kuma uban mutum mai tsoron Allah irina ba,
Macuci wanda zai cutawa rayuwar yariyar da bataci ba batasha ba,
Ya karaso inda nake tsaye ya kama min hannu a hankali yace min in zauna,
Za taimagana yakara daga mata hannu yace may zaki fada min
Aziza shin mugun kudurin da ki kayi niyar yi, da yar mutane ko kuwa nida kike,so ki kulin ,sheri kikeso yi min bayani,,,
Dan murmushi tayi irin na yan duniyar mata,
Ta tako har inda yake tsaye,
Itama wani irin harara ta dankara mai tace kana nufin ka gane nufina akan wanan cikin da nasa ai mata dashe ko may,
Ya buga mata tsawa yace ke dan Allah yimin shiru,
In ba haka ba yanzu in kira maki hukuma atafi da ke,
Aiko kamar ya tunzura ta, ,, matstawa tayi har gaban shi ta rike kugun ta da kyau,
Tace har yanzu ban fahinci irin butulcin da kake shirin yi min ba,
O saboda rashi tausayi Ahmad shine zaka ce wai yanzu kai ne uban wanan cikin
Saida ya dan murmusa kadan yace mata,
Aziza kin so ki cuce Allah bai yarda ba kamar kuma yadda kikaso ki cuta wa mata, ta fatima da mugun nufin ki na kudirin sai kon haihu ko ta halin kaka,
Ai idar har kina son haihuwa da kin haihu da kanki
Kiga alokacin zan san cewa ki na kaina na

Cikin nuna alamar bata fahince shi ba take maganan ta still,
Tace au kana nufin kun hada baki ne da fadima ku cuce ni,
Tobari kuji,
Sperm dinka da nawa likiti yai amfani dashi yasa ma fadima
Kaga kenan abinda ke cikkn cikin fadima nawane nida kai ,,
Ita nata wahalar kawai shine tai min rainon ciki idan ta haife in karbi baby na nagama da ita,
Idan kuma har kana da ja ga wana maganaa shirye nake da muje wurin duk wani hukuma ta duniya don ai muna sheri,
Saida sheriff yadan kallo inda nake zaune lokacin da tai kalamin ta na karshe,
Kafin wanin su yai wani zance muryan UMMI ce ke tambayar may ke faruwa ne haka,
Shiru duk kan mu ukun mukayi a lokacin,
Mamata dan kalli gefen da yake tace mai matar ka bata da lafiya kazo kuma kuna daga mata hankali haja a gabanta,

Cikin mamaki take kallon ummi ta nuna inda nake da yar yatsarta tace
Fadima ce matar Ahmad kuma,.
Saita bushe da wani irin dariya tana tafa hannayen ta,
Tace mamaki yau kuma kulin sheri ne haka wai don aimin dabaran rabani da abinda na kwallafawa rai,
To karyan ku don baku isa ba wlh,
Ganin da yayi idonta ya rufe zataima harda ummi rashin mutunci yasa shi cewa cikin tsawa get, out my friend,
Ai baka isa ba Ahmad sai naji matsayin da kuke son ku sa cikina aciki tukun,
Ummi da bata fahinci zancen ba sai take cewa Alhamdullah mata biyu da ciki lokaci guda,
Aziza takara kawai ummi kallo tace wai nida wace matar tasa,
Wanan karon falmata ce a kofa jin da sukayi fitinar yana kara yawa suka taso gaba dayan su zuwa dakin ,
Tace kina nufin kice baki san cewa fadima matar shi bace tobarima kiji don inaga ita din ta rigaki auren shi, tana mai nuna inda nake zaune,,,
Tawani kyalkyale da dariya kamar wata tababa,
Tace yau naji na gani,
Hindu ce tayi kokari ta kusa kai cikin dakin taja hannun Aziza tana fadin ki kwantar da hankalinki Aziza muji bayanin su,,,
Hindu wa yan nan mutanen suna son su raina min wayo,
Kiji fa wai cikin da nasha wuya kafin samun shi ,shine yau suke son su cuta min akan shi,
Yai dan murmushi yace mata Hindu ki barta har in bata yarda ba sai mu koma gurin likita taji da kunnen ta ko,
Cikin fushi ta fita dakin Hindu ta mara mata baya,
Adakin su take ta zirga zirga taje tadawo,
Hindu tace saida na fada maki cewa karki yarda kiyi wanan plan din da wanan yarinyar kika ce min ai baza a samu matsala komai ba ke kinyarda da ita to yanzu gashi irin abinda ta jawo maki,
Kidiba irin wahalar da mukasha, da irin kudin da muka kashe akai,
Hanna tadaga wa hindun tana hade wasu miyau masu daci tace,
Bar wanan zancen Hindu aiba zaiko sabu ba wai bindiga a ruwa,
Ni za,ai wa wanan drama din,

Da sauri ta jawo jakarta ta lalibo wayarta,
Number doctor Khan takira bayan sun gaisa take sheda mai cewa tana son su zo wurin check up da da wanan yarinyar ,
Doctor Khan yai dan shiru nawani lokaci, can yace mata,
Ai bai ma wanan yariyar komai ba saboda yarinyar nada ciki already a lokacin,
Hakan yasa baisa mata komai ba don babu zancen yin artificial insemination, ga wanda ke da ciki,
Yakare zancen da cewa ta diba prescription din da yabata tagani zata ga komai ai a rubuce,
Da sauri ta jawo jakar da tasa takardun a ciki diban farko ya nuna mata cewa ba ai min wanan dashen ba,
Ta wurgar da wayan don ta daina jin zan cen doctor Khan wanda kamar ruwan zafi yake kwararo mata a kune,
Sai a lokacin take tuna nen cewa kudin da ta tura mai na aikin tabbas bai cire ba har tanawa Hindu complain din haka,
Aiko nan da nan idonta yakoma kamar garwashin wuta,
Sun wani kade sunyi jajir
Yau ita Aziza za aiwa rainin wayo haka,
Ita Ahmad zai wa cin amana haka,
Tare da yar yarinyar da take ma daukar yar ficiciya,
Wasu irin hawayen bakin ciki suka ahiga zubo mata, daga idon ta,
Tarike kan ta da hannu biyu,tana fadi sharaf saman gadon ta,
Tashiga rusa kuka kamar wata yar karamar yarinya,
Ita Aziza za aiwa rainin hankali irin wanan babu abinda zata sa agabanta wanda bata samay shi ba,
Babu wani wanda zai mata wanan rainin hankalin ta kyale shi,
Kowaye dole ne saita dauki fansa akan wanan cin fuskan da ake shirin yi mata,
Hindu ce takara kwantar mata da hankali akan cewa ta bari,a bisu a hankalin har ta dau fansa a,kan duk wani cin amanar da Sheriff yai mata,,,,


Dan Allah kuyi hakkuri saida na gama typing tun a,round six saboda yau weekend ne ashe banyi storing ba sai ya goge kuma wlh nagaji da typing,
Pls kuyi min afuwan πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
7⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,

Ina daki takure wuri guda, sai tunanen abinda Aziza tace min yanzu keta min yawo a hankali,
Watau Allah ne ya rufa min asiri da ya kawo min sanadin wanan cikin, najiki,
Da Allah kawai yasan irin bakin ciki da tashin hankalinnda zan shiga, akan wanan cikin ukubar da ta , tashi sani,,
Salimat da Amal suka shigo dakin a tare, yadda salimat tagan ni zaune, cikin damuwa,,
Amal ce tazo,Gefena ta zauna muna dan fuskantar junan mu nida ita,
Naji muryan ta na fadin Fadima a gaskiya kin bani mamaki kwarai,
Yanzu ace har kin yi wanan plan din keda Aziza muna tare wai ban sani ba fadima,
Tana kada kafa tana magana cikin fushi, ,
Takara waigowa takale ni tace min fadima na fada maki cewa Aziza ba mutumiyar arziki ba ce,
Ki ka ki yarda da duk wani shawaran da nake baki akanta,
Ki ga mace haka ai kema kinsan cewa ba tsarar yin ki bace,
Salimat tace Amal ke nan, ai ke ayadda ki,ka gane kowaye Aziza Fadima bazata gane hakan ba ,
Don tazo mata da fuskan musulunci ne saboda fadima ce tie get din ta dama,
Kawai kirabu da mutun macuci,
Yanzun dai ai Allah yafita yakuma fi sherinta,
Ina jin su amma har suka kare maganan da zasu yi ban iya daga kai na kalli inda Amal take ba,
Saboda kunya dakuma wani irin nauyinta da nake ji,
Don nasan cewa tanzu tasan cewa sheriff yai min ciki
To a yaushe ,kuma a ina, ?
Sai kawai na ji wani irin hawayen bakin ciki na silalowa da ga idona,
Subbahanallahi fadima na hanaki wanan kukan baida amfani wlh kisan cewa bake kadai ba ce yanzu,
Amal ta dafani tace min haba matar yayan mu
May kuma zai saki kuka matas sai nakara jin wani zafi,
Da bacin rai kamar in ta dukan ta, nake ji,
Salimat ta kawar da zancen da Amal ke ta tsokanata,
Ta ce min waiko fadima kina karatu kin san fa mun kusa fara exam ,
Sai a lokacin na tuna da zancen wani karatu can don, har na man da zancen karatun naga abinda yafi karatu fitina,,,
Saida Amal ta dan fita dakin Salimat tasamu tadan matso kusa dani kadan tace min,
Bana son wanan kukan dakike yi fadima watau baki rugumi kaddara ba ko ,
Mutum zai iya yiwa kasan abinda Allah bai tashi yi mai ba,,,
Nadan girgiza mata kai, kadan tace, kinga dai yawan bacin randa kikeyi zai iya jawo maki wata lalura,
Ki daina haka na ,ki godewa irin baiwar da Allah yai maki,
Haka taita min kalamai masu dadi har hankali yadan kwanta nai mata Alkawarin insha Allah zan daina,,,
Naji tai shiru nadan wani lokaci, can tace min
Fadima ina son ki yarda da mijiki don gudun shiga hakkin aure ,
Ada rashin sani ne yanzu ko kin san komai sai ki dauki damaran kyautatawa a tsakanin ku,
Saboda gujewa wa fushin ubagiji ki,
Da ma duk wanda yakama, hanyar Aljanna zaita haduwa da abubuwa, masu wuya wanda zuciyar mutun bataso
Haka na wanda yakama hanyar wuta shima zaita haduwa da abubuwa da zuciyar shi ke so,
Shiyasa aka ce daga cikin hakkuri, da ake son mutum yayi cikin rayuwan sa
Harda hakkurin biyayya ga Allah da manzonsa, da kuma,hakurin yarda da kaddara kowace iri ce dan gujewa sabon Allah,,,
Ki daure ki ja mijin ki a,jiki shike karasa shakuwa da yarda ta kara dauruwa a tsakanin ma,aurata,
Kisa ni cewa duk kan ku uku matan shine, kowa ce da ga cikin ku da halinta zai zauna da ita,
Don haka kada ki bari abarki abaya,
Idan baki zama ta farko ba kada ki bari ki zama takarshe a gurin shi,,,
Shiru nayi ina ta ina jin wani kuna a zuciya na,,
Ina kuma,sauraren ta har ta kare ta mike tana fadin cewa gobe in shirya zamu tafi ziyara don in kai wanan cikin gurin ziyara,
Hakan yasa nadan murmusa don ni kaina nasan cewa na dade rabona da zuwa ziyara,

Duk ilahirin gida jen shi yasa ansa mai CCTV a boye batare da sanin kowa, ba,
Saboda tsaro da gudun wani abinda za a iya kara kullawa,
Maganar Salimt ne keta min yawo a kwakwal wa na,cewa in bi mijina to ta yaya, hakan zai faru,,,

Washe gari da safe na fito falo ko zan dan wal,wale kafin mutafi ziyara rauda, anjima,
Aziza da Hindu sun sa sheriff tsakiya kamar ba bu abinda ya faru ,jiya tsakanin su,
Azuciya na ,nace tabbas salima kin yi gaskiya zama saida gwanan cewa,
Ummi ce ta fara hangoni ta ce min a fatima kin tashi ko zo ki zauna nan ki karya kinji,,
Sai nadan waiga inda suke zaune don gaishe su ,,,
Muna hada ido da Azizat tai min wani irin wawan, harara
Sai na dan dukar da kaina don a gaskiya ban iya mata rashin mutunci ko kadan,
Sheriff yace min inzo in zauna gefen su sai nadan marairaice murya na nace mai gurin UMMI zan zauna nagode,
Sautin murmushin shi na ji itama azizan shi tawaiga don ganun abinda yakewa murmushin,
Nice yabi da ido har na zauna, kusa da inda ummi ta mayar kamar dakinta gefe guda daga cikin falon,
Wai don ta jaye mai hankali shi daga gare ni sai ta dauko jam tana shafa mai a bread din shi tana wani , kokarin matse jikin ta da nshi,
Tamiko mai yace a,a barshi kawai na koshi zan je in sha fruit, da mai cikin can,,,
Itama yunkuri tayi ta mike tsaye tana fadin barin riga ka kagin ka isa, nima in taya ku,,
A hankali ya lunshe idon shi yai dan takaittacen murmushi,
saboda yasan cewa Aziza nada wani manufa azuciyar ta gamay da ni,
wanda ba zai taba yarda hakan ya faru da, ita insha Allah,
Dar dar nake da ita ta zauna tana wani nan ,nan da ni,
Sai kawai naji fruit din sun fita min a rai sam,
Ganin da yayi ta takura min har ban iya shan fruit din yasa ,
Shi mikewa yana cewa zai je ya dawo, yanzun nan,
Yana fita tabini da wani mugun kallo wanda bani ba har ummi saida ta tsargu da ita,
Suka tashi suka bar falin zuwa cikin dakin su da suka sauka,
Suna shiga Hindu tayi shewa tace mutumiyar kin yi wlh kinga gun ma da kika daure kika nuna afili cewa ba komai,
Kinga yanzu sai mu fara shirin yadda za mu bullo wa lamarin,
Tun bayan faruwan wan rikicin sai yau na kira sheriff a wayana wayanda bansan inda ma na jefata ba, da,,,,
Kiran farko yadauka yana mai cewa Assalamu aikum,
Cikin siri,riyar murya na ansa mai sai kuma na kasa mai magana
Nai shiru kawai ina kalon kasan daki,
Muryan shi naji yana cewa fatima kiyi magana mana,
A hankali na ke ce mai zamu tafi Rauda ni da salimat , anjima kadan,
Shiru yayi can yace aida ni yakamata mu tafi bada salimat ba don muje mu gaida fiyayyen halitta tare da Sahabban shi, ko,
Amma tunda da salimat zaku tafi sai kun dawo saboda ni har na riga kuzuwa don yan zun haka daga can nake dawo,
DΓ n Allah ku kula da kan ku saboda irin yawan da akeyi wurin ,
A hankali na ce mai to,

Tare muke da Salimat harda Ummi da falmata duk sun biyo mu,
Bayan munyi sallah muka isa cikin rauda don ziyara,
Nidake kokarin wajen tare wa, mutane fili don suyi nafila, raka,a biyu,,
Sai gashi yau na kasa dole nice aka tarewa gaba da baya har na samu na,idar da sallah na dade zaune gurin ina rokon Allah mafita akan lalura, ta tare da naiman kariya, daga duk wani sheri,
Ummi da falmata suna kallon yadda nake komai nawa acikin tsanaki da kwanciyar hankali,
Hakan yasa su kara godewa Allah da ya Ahmad irin matar da suka dade suna mai sha,awan yi,,,
Muryan falmata ne yakatse ni lokacin da nake tsaye ina ma manzo na salati,
Tana fadin kiyi adduan Allah bayas da masu albarka, dayawa,
Maganarta yasa ni dan yin murmushi kadan, kunya yakamani na dan dukar da kaina kawai,,,
Motar salim ce muka shiga, ina baya tare da anty Falmat da Salimat ummi ce gaba tare da Salim
Munje har bakiya aranan,
Muna kan hanyar mutadawo wane Sheriff yakira layi na,
Yace min ina fatan kun kama hanyar dawo wa yanzu saboda baby na kada ya wahala,
Kin san Allah ya sauwakawa mace mai ciki kaifin ibada,
Cikin jin kunya don banson zance yai nisa don gani nakeyi su falmata da salimat na jin mu ,
Na ansa mai a hankali da fadin eh,,
Mundawo gida lafiya bawa ni damu atare dani ko kasala kamar yadda nasaba ji ajikina duk kwanan kin nan,
Duk wanda yagan,ni yasan cewa ina cikin walwala yau din,

Abin mamaki yau harda dan abinci da ummi tasani gaba saina ci nadan tsankwara kadan,
Batare da nayi amai ba,,ni kaina nayi murnan hakan
Don har nake cewa salimat yau banyi amai ba,
Haka mukai ta zama gidan mu tab da baki kala kala,
Kowa ta shi irin lalurar da ya kawo shi
Irin Aziza da zaman hada plan kawai sukeyi a madina,
Saidai tayi rashin sa,a saboda ta manta cewa a babban birnin da isalama take ne duk cikin duniya,
Annabi yace idan duniya ta kusa kare har addini zai kasu kashi kashi, kuma duk islam ne
To idan har ana son a gane alkibila ta gaskiya aje garin Madina,
Har duniya ta tashi garin Madina suna akan sunna ce ta gaskiya,
Baza su taba canza alkibil da manzo ya dora su akai ba,,,,
Don haka addini ce sahihiya a madinan kusan duk bukata ta alheri ta wanzuwa ga bawa, amma banda na sheri,,,
Duk yadda taso ta fara aiwatar da niyar ta takasa dole suka shirya tafiya komawa Dubai har suje su kara hada sabon plan in yaso sai su dawo da shirin su,,,
Washe gari tunda safe suka shirya da niyar bin nirgi daga madina,zuwa Dubai,
Ina tsaye a dakina ina shirin fita zuwa school yau,
Aziza ta turomin kofar daki ,
Jin yadda aka turo kofan yasa na kalli hanyar shigowa da sauri, don inga kowani mara hankali zai min haka,
Ganin yanayin da takene ba cikin kwanciyar hankalin ta take ba yasa ni nadaure na gaishe ta, acikin sakin fuska,
Hannu ta daga min alamar inyi shiru,
Tadanzo gabana tazagaya harta bayana ta na kare min kallo
Ina tsaye cikin doguwar riga mai yar guntunwar hannu, baka tadan matse ta tsakiya, sakuma kasar rigar tadan bude kamar rigar indaya
Flower farin zare ne akai yi mata a tsatsaye nikaina nasan cewa rigar tai min kyau so sai,
Saida takare min kalli da kyau tadawo ta gabana ta tsaya gab da ni har muna iya jin nunfashin junar mu,
Ta nunani da dan yatsan ta tace fadima ina mai tausaya ki da kika yaudari Aziza a rayuwan ki,
Aziza ba a cutar ta a kwashe lafiya, kisani cewa
Ahmad nawa ne kaida bada kowace mace ba haka kuma wanan dan dake a cikin cikin ki nawane har abada ,,
Wani karfin hali naji yazo min da tace hakana,
Nadan kali inda take tsaye tana wani dan buga kafa nai dan murmushi irin mai ba mutun haushi
Nace mata, tunda har Ahmad din da kike gadaran cewa naki ne ke kadai bada kowace mace,ba
Gashi yau yadawo ga yar karamar yarinya har yakai ga mata abin dake kikadade kina bida da kudin ki da ilimin ki,
Taiwani kukan kura kamar zata shake ni, ashe Hindu nata wajen kofa tana kallon masu shigowa da fice agidan,
Ta rike mata hannu ta baya tana fadin ki,kan mantacewa agarin da shariar musulunci tafi karfi muke aziza,
Takai kusan minti biyu tsaye tana min wani irin mugun kallo na tsana
Ina tsaye kyam ina kallonta babu kowani tsoro,
Ganin kallon bai da alamar karewa yasa nadan geza da gefenta nayi tafiyana zuwa wurin mirroww na din in daura dan kwalina,
Saboda time na kure min na zuwa school,
Tai wani irin kutawa Hindu najan ta suka fita dakin suna fadin cewa zamu hade dake yarinya very soon,
Saida suka fita nabi suda kallo kuma ina mamakin kaina wai yau nice na iya tsayawa gaba da gaba ina bawa aziza ansa
Duk da nasan cewa bata da gaskiya amma nasan cewa hakan bsidace ba tunda ita ba warin yina bace,.
Kafin indaura Naifal dina Yashigo dakin rike da yar briefcase din shi, da alamar cikin sairi yake,,
Saida yai min wani kallo na sha,awa tukun sanan yace min ya muka kwana,
Ina tsaye nadan jingina da mirirrow kaina yana kasa,
Nace mai Alhamdullah,
Masha Allah yace, yakaraso ya man namin kiss a tsakitar goshina,
Kunyan haka da yake min nake ji sosai
Muryan shi naji yana cewa ina son in je in sauke su Aziza airport yanzu,
Yana fadi yana kallon agogon hannunshi,
Yadan kallo ni yace min kada ki damu kanki da duk wani barazanan da aziza zataimaki
Ashirye nake da daukar mataki a kanta,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment