Join Our WhatsApp Group

KU DUBEMU Complete Hausa Novel Document by KU DUBEMU


KU DUBEMU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 262900



KU DUBEMU

Reading Time: 21 Hours

Added On: 16, Nov 2023

Author: Batul Mamman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FIKRA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : +234 806 334 4334

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.35 mb

File Type: txt

Views: 1095+

Download: 1977+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: [7/4, 7:38 PM] +234 806 334 4334: A
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*5/2/2019*

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT da Ya bani damar fara rubuta wannan labari. Ina addu’a Allah Yasa yadda na fara lafiya na gama lafiya kuma ni daku mu amfani da abinda ya kunsa. Kuskuren da yake ciki kuma ALLAH Ya yafe min. Amin*

*HAKKIN MALLAKA*
©Batul Mamman

*Wannan labari da duka abinda ya kunsa mallakar BATUL MAMMAN ne. Ban yarda wani ko wata ya juya min ko da shafi daya ne batare da izini ba. Sannan ban yarda a yada min wannan labari ta kowace siga ba ta kafofin sa da zumunta, bugawa ko karantawa. Sabawa hakan zai janyo daukar mataki akan duk wanda aka samu da laifin. Nagode.*




*FARKON FARI*

*1992*



Gidan Mal Ali Gidado babban gida ne a cikin karamar hukumar Sumaila dake Kano. Attajiri ne wanda Allah Ya azurta da dabbobi masu tarin yawa. Garken shanu, tumaki da awakinsa bazasu kirgu ba saboda yawansu. Wata katuwar gona ya samu a can bayan gari ya zubesu yana kula da kayansa da taimakon mutane kalilan saboda bazai juri biyan da yawa ba. Bafillatani ne na usuli dan siriri ba kiba ko kadan amma kallo daya zai tabbatar maka an zuba kyau zamanin kuruciya. Mutan gari da iyalinsa suna kiransa Malamijo. Duk tarin arzikin Malamijo kusan kowa ya sanshi a matsayin rikakken mai mako da bakar rowa. Kudinsa basa tabuwa indai ba aure ya tashi yi ba. To a nan fa yarinya da iyayenta zasu ci su tada kai. Idan anyi auren ma amarya ita ce tauraruwa taci mai kyau tasha mai kyau. Gidan gabadaya hannunta sai dawo har zuwa lokacin da Malamijo zai gaji da ita ko tayi ciki. Daga nan fa ita da babu duk daya don gwani ne wurin wulakanta mata da cin zarafinsu saboda shima ya sani kudinsa suke aure.

Malamijo ko suturar kirki baya sakawa saboda kada ya kashe kudinsa. Sau tari zaka ganshi cikin kodaddun kaya yana yawo don bai taba yarda yayi dinki daidai jikinsa ba saboda gudun raini. A halin yanzu ‘ya’yansa goma sha biyar amma shida ne kadai da iyayensu mata a cikin gidan. Sauran taran basu da gata suna ga Allah suna ga Yadikko mata ta biyu a jerin aure auren Malamijo wadda har yau ya kasa sakinta saboda mace ce da ta gagare shi juyawa. Bata taba haihuwa ba kuma nata mahaifin ma da arzikinsa lokacin da akayi aurensu. Duk da haka dai auren nasu yana da tsahon rai domin kuwa duka ‘ya’yan Malamijo akan idonta aka haifesu. Idan ya saki uwar yaran tana kokari matuka wurin kulawa dasu sai dai rashin wadatasu da yake yi yasa itama abubuwan sai a hankali. Yaran da suka ci sa’a suma sun taso da nasu iyayen a gidan to duk abinda aka kawo wawaso ake dasawa mai uwa a gindin murhu ya tsira da abin arziki. Wanda babu tasa kuma ya koma gefe yasha kallo.

Duk bakin hali na Malamijo yaransa sun tsira da abu daya wato ilimi na zamani da na arabiya. Wannan ludufi da suka samu ya samo asali ne daga shawarar da abokinsa da suke kai dabbobi kudu tare ya bashi na cewa idan sunyi karatu shine zai mora domin zasu sami aikin gwamnati kuma a matsayinsa na mahaifinsu shine zaifi kowa jindadi da samun yaran. To dayake zuciyar ta nema ce kawai ba musu ya amince. Shi kuwa abokin nasa Mal Kallamu yayi haka ne domin ya taimakawa yaran da suke walagigi a cikin gari. Shawara dai irin ta abokai yana kokarin bashi bakin gwargwado akan tsarin rayuwarsa amma yaki ji. Banda Mal Kallamun ma waye ya isa ya fadawa Malamijo magana irin wannan kai tsaye batare da ya auna masa rashin mutumci ko da rabin kwano bane ya kai masa har kofar gida.

Yau yake dawowa daga kudu inda ya kai motoci uku na dabbobi. Duk yadda aka san Fulani da son dabbobinsu haka yake a wurinsa sai dai kudi ya fiye masa komai. Kuma gashi da nasibi don yana samun alkhairi sosai kamar yau din da ya dawo.

‘Ya’ya da matansa haka suka yi ta fitowa ana masa barka da dawowa yana faman hura hanci kada wata tayi gigin neman karbar jakarsa.

‘Yan mata biyu ne a daki daya tana kwance akan yamutsatsiyar katifa dayar kuma mai alamun ta girmeta tana daga tsaye a kanta.

“Wai bakiji shigowar Malamijo bane?”

Siririn tsaki taja tana juyawa daya bangaren “naji mana”

Yayarta ta da suke daga iyaye mata daban ta zauna a gefen katifar tana rage murya “Mairama kinsan idan bamu je ba duk abinda yazo dashi su Inno karbewa zasuyi ko?”

Cikin bacin rai Mairama ta juyo “Adda Salame ban fa hanaki zuwa ba.”

Batare da kosawa ba sanin halin kanwarta ta sake murmushi “Mairama ki dena wasa da iyaye babu kyau”

Tasowa tayi a harzuke sai dai ko kafin ta fara magana ta soma kukan abinda yake ci mata rai “Adda har kin manta ranar da zai tafi yace mana mun cika masa gida kamar ‘ya’yan Allah bani, wato irin wanda ba’a kaunarsu an dai haifemu bisa lalura. Gara ma ke kina zuwa wurin Innarki, ni kuwa da kasa ta rufe idon tawa bani da wani gata”

Kuka Mairama take sosai Salame tana bata baki. Yarinya ce mai zuciya shiyasa abubuwan rashin adalcin gidan nasu suke ci mata tuwo a kwarya. Ada da suke makarantar kwana idan suka tafi ko marmarin hutu bata yi. Gashi yanzu sun gama harda watanni. Da yake sune manya Salame mahaifiyarta ce uwargidansa ita kuma Mairama tata ita ce ta uku. Dukkaninsu babu wadda ta budi ido da mahaifiyarta a gidan. Yayin da Salame take da mugun sanyin hali ita Mairama saurin fushi gareta musamman akan yanayin gidan nasu.

Labulen dakin aka bankada Hajjo mai mulkin gidan a yanzu saboda ita ce amarya kuma yayinta bai kare ba ta sakar musu harara.

“To tabbatattu isassu. Kuna kwance a daki Malamijo ya dawo bazaku je ku gaishe shi ba”

Da rawar jiki Salame ta mike tana tayar da Mairama “yanzu zamu fito”

Tsaki taja ta koma suka fito babu kowa a tsakar gidan sai kannensu maza da mata kusan kowa rike da agwaluma daidai a hannu daga su har uwayensu. Hatta Yadikko rike take da guda tana lailayawa a hannu don taji dadin sha. Kallonsu tayi idanun Mairama jajir.
“Me ya hanaku fitowa da wuri har ya gama rabon tsaraba?”

Salame taji babu dadi don ranta ya biya. Kayan kwalama irin wannan da wuya yake musu tsaraba sai anyi matukar sa’a. Harara ta gallawa Mairama don ta tuna ya taba kawo musu agwalumar kudun akwai zaki. Tare suka shiga rumfar Malamijo. Fankar kasa ce aka sakar masa a ka yana shan iska kafin a hada ruwan wanka. Tabe baki yayi ya wani juyar da kai.

“Malamijo yaya hanya?” cewar Salame ya amsa da kyar.

“Barka da dawowa” Mairama tace tana gintse fuska.

“Chege ‘yar kunama wai nan fushi kike yi saboda nashe zan dena ciyar daku kafin nayi tafiya? Baffanku Kallamu ne ya fada min kuna gamawa zaku fara aikin gwamnati ku soma daukar albashi kuna yaga min kawai kuma sai naji shiru.”

Da mamaki suke kallonsa. Ashe dalilin tijarar da yayi musu kenan a ranar harda kiransu kattin banza ‘ya’yan Allah bani. Don kansa ya saki fuska yace yayi bincike an fada masa ashe sai sunyi wata makarantar ta gaba da sakandire.

“Qur’anin Ubangiji ni kuma bazan sake biya muku komai ba. Ku fiddo mazajen aure na kawar daku a sami sarari a gidan nan. Ga kannanku nan rida-rida dasu suma kullum cikin sasake ni suke. Wannan adashin da babu alamun riba na kudin makaranta na soma gajiya”

Dije mata ta biyu a yanzu tayi burum ta fado dakin

“Yasin Malamijo yarana sai sun gama makaranta. Haka kawai wasu ma suka gama bare nawa kuma maza”

Hularsa ya turo gaba yana kankance idanu “Ki shiga hankalinki dani Dije. Sai hegen labe kamar kadangaruwa kullum kina manne da bango. Ina jiye miki kada watarana ki jiyowa kanki sallama”

Idanu ta zaro cike da tsoro su Salame suka fita suka barsu.

Kwanakin da suka biyo baya gidan bai canja zani ta kowacce fuska ba sai ma tsananin da Salame da Mairama suka kara shiga na rashin kawo mazajen aure. Malamijo har ikirarin hadasu da masu yi masa aikin dabbobi yayi. Yaran nasa ne tubarakallah ga kyau amma fa babu farinjini….da farinjinin dai tsayayye ne babu saboda babu mai kaunar hada iri da Malamijo saboda halinsa kaf babu na zabe.
[7/4, 7:38 PM] +234 806 334 4334: **********
B

ARMY BARRACK SOKOTO
Sojoji ne ta kowane bangare a cikin barikin suna gudanar da al’amuran gabansu.

Yawancinsu sanye suke da farar t-shirt da dogon wandon khakinsu, kadan ne da cikakkun kayan suna bada umarni a bangarori daban daban.

Cikin jerin wadanda suke gudun da aka fi sani da 4-40 wasu matasa ne guda biyu suke magana kasakasa don kada a ji me suke tattaunawa.

“zamu din kuwa in fara shiri tun wuri muna gama training”

Wanda yake yiwa maganar yayi gajeren murmushin gefen baki “ta fada min tana da kanwa kuwa”

Yana kallon yadda farinciki ya bayyana a kan fuskar abokin nasa ya fadada murmushinsa. Baya bukatar wani abu da zai bata masa ranar ta yau domin burinsa bai wuce ya sami damar zuwa tadi wurin sabuwar budurwarsa ba. Mantawa suka yi da wurin da suke suka cigaba da hirarsu sai da suka ji tsawa daga wanda yake jagorantar training din nasu.

“Tureta and Murtala fall in”
Sun san manufarsa su daidaita kansu da sauran cikin sauri suka ce a tare “Yes sir, sorry sir”

Daya daga cikin wakokinsu na sojoji da suka saba suka fara yi tare da sauran suna gudun har lokacin da babban nasu ya dakatar dasu.

“Stand at attention ladies”

Captain Mustapha yace yana zagayesu.

Su biyun ne dai masu surutu dazu suka fara dariya. Ba komai ke basu dariyar ba kuwa sai cewa da suke idan aka kira su ladies wai sai su rinka hango kawunansu da sauran cikin kayan mata. Captain Mustapha ya gaji da halinsu don basa ji kwata kwata gashi a karkashin platoon dinsa suke. Sallamar sauran yayi dama duka a gajiye suke. Da yatsa ya yiwa samarin biyu alama da su cigaba da gudun sai sun sake zagaye uku zasu tafi.

Wanda ya fi fitinar ya dube shi hankali a tashe sannan ya kame cikin daga murya yadda suka fi yin magana da na gaba dasu ya roki alfarmar ya daga horon zuwa washegari.

Dayan Captain Mustapha ya yiwa kallon tambaya baiyi wata wata ba ya fadi uzurin abokin nasa, wato zance da zaije wurin sabuwar budurwarsa. Murmushi yayi don ya sami damar horasu yadda yake so.

“Zayyan Tureta”

“Sir” ya sake kamewa.

“Za ka sake yin zagayen nan sau biyar”

Baki ya bude sai kuma yayi saurin rufe shi don kada ya sake yin laifi. Yana kallo aka sallami abokin nasa don a bata masa rai tunda duka laifukan da suke aikatawa shine ja gaba. Hadir Murtala ya faki idon Captain Mustapaha ya yi masa gwalo sannan ya bar wurin.
Ko da zai kare da rarrafe ya sani bin umarni dole ne.

Juyawa yayi a matukar gajiye zai cigaba da gudun Captain yace yaje gidansa ya jira shi. Idan ya riga shi zuwa yana bukatar ya dawo ya ga a ina yake. Haka yake so yayi ta yi har sai ya iske shi a gidan.

A guje ya kwasa sai bangaren gidajen sojojin yaje ya dawo Captain yana nan inda ya barshi kuma yace ya sake tafiya. Sai da yayi haka sau hudu suna haduwa a kan hanya a wurare mabanbanta a na karshen suka hadu a kofar gidan. Zuwa lokacin Zayyan da kyar yake motsa gabbansa amma a haka ya kame a bayan Captain Mustapha.

Murmushi Captain din yayi masa. Yana kaunar yaron saboda kwazo da himma amma rashin jinsa yayi yawa.

“Kana jin yunwa na sani. Mu shiga ciki kaci abinci”

Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa don ba haka ya zata ba. Tunaninsa kullum Captain Mustapha shi yafi tsana duk cikin platoon dinsu. A waje ya jira shi ya fara shiga ya nemi iyalinsa su shirya zai shigo da bako.
Wani yaro ne da zaiyi kimanin shekaru bakwai ya fito a guje yana dariya yazo gabansa ya tsaya.

“Kaine Tureta?”

Sakin fuska yayi don akwai shi da son yara “nine”

Sai kawai yaron ya dane jikinsa har suka kusa faduwa yana kyalkyala dariya ya soma surutu

“kaine kayi karyar rashin lafiya don kada kaje training? Daddy yace rannan ka sakawa wani kunama a takalmi saboda ya shiga masallaci da takalminsa. Kuma wai ka iya karatu mai dadi amma baka jin magana”

Baki Zayyan ya rike yana kallon yaron yana ta zuba da bashi labarin abubuwan da yake na rashin ji tun zuwansa barrack din. Gyaran muryar Captain din suka ji yaron ya nutsu yana rike da hannun Zayyan.

“Awwab?”

Sunkuyar da kai yaron yayi yana kara matse masa hannu suka yi murmushi tare. Bayan Captain ya bi har cikin falon. Matarsa Hassana da ake kira Mami ta fito fuska a sake ta nuna masa wurin zama da dan tebur a gaban kujerar wanda ta dora tray din abinci da abin sha. Wuri suka bashi yana cin abinci Awwab na masa hira tamkar sun dade da sanin juna. Sai bayan rabin awa Captain ya sake fitowa sanye da jallabiya irin mai gajeren hannu da fadin nan. Zayyan ya dan gyara zama ya fusakance shi.

“Awwab ya dame ka da surutu ko? Halinku daya na fitina amma shi matsoraci ne”

Dariya Zayyan yayi yana kallon yaron da ya shiga ransa cikin kankanin lokaci. Basu dade suna hira ba Captain ya sallame shi bayan dogon gargadi akan halayyarsa idan ba yana da burin a kore shi tun kafin ya zama wani a cikin sojojin ba.

Har Hadir ya dawo Zayyan yana mamakin Captain Mustapha. Mutumin baya magana sosai idan ta wuce karbar umarni da badawa. Kuma baya nuna damuwarsa akan kowa amma ace wai banda sanin halinsa har labarinsa yake bawa iyalinsa. Hannun Hadir yaji akan kafadarsa yana jijjigawa.

“Zayyan lafiyarka kuwa? Inata magana kamar baka ji. Nace naje wurin Zainab mun daidaita kanmu”

“Na tayaku murna”

Cikin yanayin ko in kula yayi maganar hakan yasa Hadir taba wuyansa “zazzabi kake ko ciwon kai? Zainab fa nace mun hada kanmu. Da naje babanta ya fito yana yi min tambayoyi karshe yace in turo. Ina ta kokarin fahimtar dashi ba kai bane sai da ya tafi tace ta amince min itama. Nima kuma na gani ina so….”

“Wai kasan yau a gidan Captain naci abinci har muka yi hira? Ashe haka yake da kirki mune bamu fahimce shi ba. Kuma yana da da dan shekara bakwai abin mamaki yayi auren wuri inajin.”

Hadir ya kalli Zayyan ya tabbatar kalau yake sai ya rabu dashi. Washegari ne suka sake hirar bayan kowa ya dawo hayyacinsa. Hadir da gaske ya nuna yana son Zainab kamar yadda ta amince masa shi kuma Zayyan jin kansa yake ya kara girma saboda ya fahimci Captain baya kinsa. Kowa da nasa farincikin a haka abokan suka cigaba da zaman...


Read / Download KU DUBEMU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

6 months ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

5 months ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

5 months ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album