Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 1

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



******* ****** ******
Zaune suke a falon su wanda yake a gyare sai tashin kamshi yake ga sanyin AC da ya karawa dakin ni'ima. TV na ta aiki, komai na dakin red kaa ne daga manya manyan kujerun har labulayen dakin da center carpet din dake tsakiyar dakin mai uban taushi, wata dattijuwar mata da ba zata wuce shekara arba'in da biyar zuwa da takwas ce zaune gaban ta system, sanye take da less mai kyau da tsada daga yadda take kallon system din zaka san aiki take a cikin ta. Sai gefenta wani dan yaro kyakyawa wanda a ido bai zai wuce shekara biyu ba, sanye yake da wasu riga da wando bakake wanda suka kara fito da hasken fatar sa, gashin kansa a kwance baki sidik sai sheki yake, wasa yake da mota, sai wata kyakyawar budurwa da bata wuce shekara sha tara ba sanye da maroon kalar hijab wanda yake har kasa, waya ce a hannun ta tana daddanawa gaba daya hankalin ta na kan wayar. Sallama akai dabwata muryar mai dadin da zaki, daga bakin kofa amsawa sukai a tare. Wanda yai sallama ne ya shigo cikin takun sa na kasaita sanye yake da suit ash kala wacce ta amshi shi sai bakin takalmi sau ciki baki, hannun sa rike da brief case din sa. Fari ne tas dogo ga saje, idanun sa manya wanda suke ko da yaushe a lunshe sai dogon hancin sa, da madaidaicin baki sa ai agaye da pink lips masha Allah kyakyawa ne sosai.

Yaron dake wasa da mota ne ya d'ago yana ganin sa ya mike yayo wajen sa a guje yana fadin
"Abbi Oyoyo!"

Brief case din ya ajiye akan kujera ya daga yaron sama ya rumgume shi, yana murmushi wanda kumatun sa suka lotsa kan yaron ya shafa yace
"My Son ya gidan?"
"Abbi i miss you (nayi kewar ka)"
Ya fada da harshen da zaka san magana bata gama zama a bakin sa ba.

Matar dake aiki a system ce ta d'an d'ago tana kallon sa, ya karaso cikin falon ya zauna a kan carpet din dake tsakiyar dakin tare da d'aura kan sa a gefen kafar matar yace
"Ummi nah sannu da gida ya aiki?"
"Alhamdulillah Dr ya aikin?"
Ta tambaya cike da kulawa.

"Alhamdulillah!"
Ya fada yana shafa sumar kansa da take kamar ta indiyawa sai sheki da kamshi take. Budurwar dake zaune ce ta dago fuska ba yabo ba fallasa tace
"Sannu da zuwa Yaya."

"Yauwah!"
Kadai yace ya mike rike da yaron yai hanyar dining inda wata kofa take suka shige. Da kallo ta bisu ta d'an tabe baki mikewa tayi tace
"Ummi bari naje wajen Inna."

"To ki gaishe ta."
Ta fita tana tafiya a hankali kamar ba zata taka kasa ba, saboda wayar da take dannawa kamar daga sama taji an zare wayar hannun ta da sauri ta d'ago fuska ta marairaice tana kallon wanda ya amshe wayar, wani kyakyawan saurayi ne wanda ba zai wuce shekara talatin ba, dogo ne fari tas dashi wanda yake da faffadan kirji, yana da idanu da hanci da bakin sa dan madaidaici, murmushi yake wanda ya kara masa kyau, fuska ta kara shagwabewa kamar zatai kuka tace
"Yaa Faroukkk"

Wanda aka kira da Yaa Farouk ne ya zuba mata ido wannan yasa tai saurin yin kasa da kan ta tana son wucewa ta gefen sa. Ya d'an kamo gefen hijab din ta, ta juyo yace
"Kina tafiya kina danne danne sai kin fadi kinji ciwo ki barewa mutane baki kina kuka ko?"

Ido ta zaro ta, tace
"Kai Yaa Faroukkk ni din?"
Ta fada tana nuna kan ta.
"Eh ke din fa ke wa ya kai ki ragwanta, ko Haidar ya fiki jarumta."

Baki ta dan turo tace
"Uhmm ai kuwa na fishi wancan dan mitsitsin yaron."
Yai murmushi yace
"Shi fa. Yanzu ina zuwa?"

Bangaren Inna ta nuno masa tana fadin
"Wajen Inna."
"Nima can zani. Wai me kike dadannawa a wayar ne ko chat kike da siriki nane?"

"Kai a'ah ni ba ruwa na Yaa Farouk."
"A'ah fah ki fadan gaskiya in dashi ne a bani mu gaisa."

"A'ah Yaa Farouk ni bani da wani saurayi fa, da Jawahir muke chatting fa."
"Wannan Jawahir din dai har na gaji da labarin ta ita bata kawo wa mutane ziyara ne?"

Ido ta zaro tace
"kai Yaa Farouk ranan fa nace maka tazo itama tana ta tambayar ka, kasan ma me? Kun fiya sabani shiyasa."
"Duk tsiya dai watarana zan ganta in ma bakya so na ganta ne."

"A'ah ni ba ruwa na."
Suka karasa kofar sasheb Inna wanda yake babban compund ne da aka zagaye ahi da shuke shuke wanda ya karawa wajen kyau, kofar dakin Inna suka karasa sukai sallama ta amsa suka shiga.

Daki ne madaidaici wanda yaci set din kujeru Ash kala da kayan kallo bakake, labulayen da center carpet din duk ash and black ne, dan a gyare yake sai kamshi da yake, tiles din kuka kamar kaga kanka a ciki haka kayan kallon sai kyalli suke kamar wanda aka shafe da mai. Maryam ce ta fara shiga tace
"Inna tah."

"Na'am Maryama yau ina kika shiga tin safe baki leko ba."
Wata tsohuwar mata da zata kai shekara tamanin da wani abu, saye cikin atamfa super tai kwaliyyar tai maganar tana kallon Maryam din cike da so da kauna. Maryam ta zauna a kusa da ita tace
"Ina can ina aiki na danyi sanitation ne a bangaren mu."

Inna tace
"Sannu ina Haidar din?"
"Yana wajen Abbin sa."

Baki Inna ta tabe ta kalli Farouk tace
"Ai sai ka zauna ko ka tsaya sai kace wanda ya hadiyi tabarya."
"To wa ya sani."
Farouk ya fada yana danna wayar Maryam.

Inna ta gimtse baki tace
"Ai da ba lafiya."
Maryam tai dariya tace
"Ai kuwa dai Inna."

Ya zauna yana kallon Maryam yace
"Kina biyewa Inna Allah batawa zamuyi."
"Yo ku bata din mana, sai me kuma me kake mata ci ko sha ko sutura."
Inna ta tambaya tana hararar sa.

"Dukka."
Ya bawa Inna amsa yana zaro wayar a aljihu.
"Ba mu gani ba."

"Ai daman Inna ke ba komai kike gani ba."
"Tinda ga makauniya ko?"

"Nifa bance ba Hajiya Inna."
"Kai ka sani dai."

Inna ta kalli Maryam tace
"Dazu nayi dambun nama ni dan ke nayi ma wallahi to sam baki shigo ba."
"Zamu ci dadi."
Farouk ya fada yana mikewa daga kishiginden da yake.

Inna tace
"Duk jikokin na babu kwadayeyye kamar ka Umaru kuma in naga dama dandanawa ba zakai ba."
Dariya yayi yace
"Mai gidan naki guda."

"Kai tafi can ai na fiyi da wancan mai fuskar shanun."
Baki ya bude yana dariya yace
"Lalalah Yaa Haidar din Inna ai kuwa sai na fada masa."

"Ba abinda yayi sai hada mutane fada to yanzu shi yaji ne amman kin ji shi wai zai fada masa salon dan abinda yake bani ya daina bani."
Murnushi Maryam tayi tace
"So yake ki sammishi kuma Yaa Aliyu ba yadda zai ba."

"Ai dai mai hada husuma bashi ba Allah."
Dariya Farouk yayi yace
"Hajiya Inna ai kin fada dai."

"Kai ka sani."
Wayar sa ce tai kara da sauri ya dago yana kallon Maryam dake wa Inna magana sam bata san ma yana yi ba da sauri ya mike ya fita yana kara wayar a kunnen sa.

"Hello Baby."
"Kana ina Baby kace zaka zo kuma naji shiru."

"Kinga magarib ta kusa ki jira ni bayan magrib zan karaso."
"Ok ina jira."
Ajiyar zuciya ya sauke ya koma dakin.

Inna ta kalli Maryam tace
"Yau na ganki duk wani iri me yake damun ki?"
"Ba komai Inna yanayi ne kawai."

"A'ah in akwai abinda ke damun ki ki fada min ko ita Aishan ce tai miki wani abu?"
"A'ah Inna me Ummi zatai min?"

"Ah na sani."
"Ni ba abinda tai min."

"Wannan mai fuska a dauren fa?"
Baki Maryam ta tabe tace
"Shi da dawowar sa kenan."

"To shikenan."
"Hajiya Inna kudi zaki bata kawai."
Farouk ya fada.

"To ina ruwan ka. In kudin take so ai zata fada min ko Maryama."
Kai Maryam ta gyada tana jingina da kujera. Wayar tace tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dauka tayi ta kai kunne tace
"Hello Jawa."

"Na'am wai ya zancen addimision din kine?"
"Nifa har yanzu su Ummi basu ce komai ba."

"Kuma ke ba zaki iya musu magama ba?"
Mikewa tai ta fita tana fadin
"Ai suna sane na sani."

"Shikenan ni dai gashi nan an amso min gobe Dady yace naje nayi registiration da so nayi muje tare."
Kofar dakin Inna ta juya tana kalla tace
"No Jawa kije kawai ba matsala in zan yi kya raka ni kar kije ki samu matsala."

"Shikenan amman ki fadawa Yaa Aliyu mana."
"Zan masa magana bai jima da dawowa ba ai."
Juyowar da zatayi taga Aliyu tsaye a wajen Haidar kuwa har ya shige falon Inna.

Kai tayi kasa dashi da sauri ya wuce dakin Inna ita kuma ta juya tayi sashen su. Ummi ta sama a inda ta bari sama kawai ta haye, Ummi ta d'ago tana kallon ta sai kuma ta d'auke kan ta. Tana shiga ta fada bandaki tai alwala ta fito ta tada sallah bayan ta idar tai addu'a Alkur'ani ta d'auko ta fara karantawa tana zaune har akai isha'i ta mike tai sallah tai addu'a tare da shafa'i da wuturi. Mikewa tai ta cire hijab tare da cire kayan ta, wanka ta shiga tayi ta fito ta saka kayan bacci ta feshe jikin ta da turaren ta mai kamshi. Kan gado ta hau duk da ba bacci take ji ba amman so take ta dan huta.

Tana kwanciyya aka turo kofar d'akin Ummi ce ta shigo da sallama mikewa zaune tayi. Ummi tace
"Kin ci abinci ne naga kamar kin kwanta?"

Cikinta ta d'an shafa tace
"Ummi na koshi ne."
"Me kika ci?"

Kai tayi kasa dashi. Ummi tace
"Tin abincin rana ko? To maza sauka kije kici abinci."
Kafarta ta diro kasa ta mike ta d'auko hijab ta saka sannan ta fita a d'akin Ummi tabi bayan ta, ba kowa a d'akin dan haka ta karasa dining. Abinci ta fara ci kamar ba zata ci ba, sallamar sa ta jiyo sai ta ji Haidar ma na sallama a ciki ciki ta amsa ya shigo bai kalle ta ba yayi d'akin sa. Haidar ne ya karaso yace
"Addah kalli abinda Abbi ya siyon."

Ya fada yana mika mata ledar hannun sa, amsa tayi ta leka tace
"Yaron Abbin sa kace angode?"
Kai ya gyada tace
"Good to jeka."

Ya ruga a guje ya shiga dakin Abbin. Abincin ta karasa turawa da kyar ta mike tana kwashe kayan Haidar ya dawo yace
"Addah Abbi yace kizo."

"Ni!"
Ta fada cike da mamaki. Kai ya gyada mata, tace
"To jeka gani nan."

Ta dibi kayan ta kai kitchen sannan ta dawo ta nufi dakin Aliyun. Sallama tayi ya amsa, ta shiga kanta a kasa, Masha Allah wani kamshi da sanyi ya doke ta, ta lumshe ido, ta bude yana daka kan kujera yana danna system. Komai na dakin fari ne tas sai kace ba a rayuwa a cikin sa, daga gefen kujerar ta durkusa tace
"Gani Yaa Haidar."

Da sauri ya dago kan sa ya kalle ta da lumsassun idanun sa, lumshe du yayi sai kuma ya dauke kan sa, envelope ya mika mata. Amsa tayi ta tsaya jin ko zai magana amman bai ba mikewa tayi tace
"Nagode."

Ta fita sama ta hau ta shiga dakin ta, ta ajiye envelope din akan side doruwa ta zare hijab ta hau kan gadon addu'a tayi ta kwanta ta gefen dama envelope din ta gani ta mike da sauri ta dauka budewa tayi ta zaro takardun dake ciki ta zube su akan gadon daya ta dauka ta fara karantawa da sauri ta zaro ido murmushi ya bayyana akan fuskar ta.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah nagode maka ashe nima zan yi karatun nan."
Sai hawaye ya hau zubo mata a saman fuskar ta. Shin wa zata fara fadawa wannan abun farin cikin Ummi, da sauri ta mike ta fita a guje a dakin hannun ta rike da takardar addmision din, kofar dakin Ummi taje tai knocking Ummi ta bata izinin shiga da sauri ta bude ta shiga tana shiga ta karasa wajen Ummi ta rumgume ta tana fadin
"Ummi kalli ki gani."

Ummi ta amshi takardar tana dubawa itama murmushi ne ya sauka akan fuskar ta tace
"Masha Allah. Allah yasa a fara a sa'a."

"Amin Ummi nah ki tayani yiwa Yaa Haidar godiya."
"To Maryama Allah bada sa'a da nasara."

"Amin Ummi."
Ta mike ta fita a dakin. Dakin ta ta koma ta duba dayar takaradar form ne na banki sai wasu kudi masu yawa kirgawa tayi taga dubu dari biyar ne. Ido ta zaro tace
"Na menene kenan?"

Tsaki ta dan saki tace
"Yaa Haidar shi ba zai yai min bayani ba ni nasan menene da zai ban abu kawai ba bayani to da ban bude ba fa."
Ta fada tana lallubar wayar ta.

Jawahir ta kira tana dauka tace
"Albishirin ki?"
"Goro."

"No ban son goro ni ba tsohuwa bace."
"To chocolate."

"Hmmm yanzu Yaa Haidar ya bani takaradar addmision fa."
"Da gaske Angel?"

"Wallahi yanzun nan fa."
"Alhamdulullah kinga gobe sai muje registeration tare ko?"

"Eh nawa ne registeration din?"
"Sai mun shiga ckul amman dai naji Yaa Khalid yace kamar 150k ne."

"Ok Allah kaimu goben."
"Amin sai da safe."
Sukai sallama.



**
Washe gari da safe da wuri ta shirya tana kitchen tana aiki taji Haidar na kwala mata kira yana fadin
"Addah Addah!"

Da sauri ta leko, ta ganshi sanye cikin wandon jean da jar riga, sai agogo daure a hannun sa, ta kamo hannun sa tace
"Ya akai Boy."
Hannun ta ya hau ja zuwa dakin Aliyu tace
"Haidar bari na sako Hijab d'ina."

"Aah Abbi na so kizo yace."
Yai maganar da gwaranci. Zatai magana Aliyu ya fito da sauri tai kasa da kai shima kallon ta ya danyi tana sanye da doguwar riga wacce ta kamata, daga sama, kan sa ya dauke yace
"Kin cike form din da na baki jiya?"

Kai ta girgiza, saboda ba ganin ta yake ba, ya dan d'ago ya kalle ta da shanyayyun idanun sa yace
"Magana fa nake."
'Dagowa tayi sanye yake da wasu Blue kalar suit wacce tai masa kyau, gashin kansa ya kara baki sai sheki yake, leben sa ya kara yin pink sai kyalli yake kamar wanda ya shafa masa janbaki ko man lebe, suna hada ido sukai saurin kawar da idanun su, jiki a sanyaye tace
"A'ah."

"Ke zan tsaya jira to kije ki cike ki kawon kar ki batan lokaci."
Tai saurin fita tai sama, da gefen ido ya rakata ya zauna akan kujera yana mai lumshe idanun sa. Tana zuwa ta cike form din. Hijab ta saka ta fito ta same shi a kasa. Tana mika masa ya mike har ya kai kofa yace
"Nayiwa driver magana zai kai ki banki wajen aboki na shi zai bude miki account daga nan sai kiyi registeration dan a satin nan za a rufe."

"To nagode Allah saka da alheri."
Ya juya ya fita tace
"A dawo lafiya."

Hannu kawai ya daga ta koma ta karasa abinda zatai. Tana fitowa sai ga Ummi ta sauko cikin shirin ta na tafiya aiki. Ummi tace
"Ya zancen registeration din naki?"

"Yaa Aliyu ya bani kudin yace anjima driver zai kaini nayi."
"To madallah ina Haidar din?"

"Sun fita tare."
"To shikenan sai kin dawo ki kula dai."

"Insha Allahu!"
Ta koma sama. Waya sukai da Jawahir suka dai dai ta fitar tasu wajen sha daya ta fita driver ya kai ta banki tana zuwa Jawahir na zuwa dan haka tare sukai komai nan da nan suka gama suka fito suka je ckul suka fara abubuwa wanda suka ga har an kafe time table next week za a fara exam haka suka koma gida.

Tana shiga ta samu Farouk a compound yana ganin ta mike yace
"Daga ina haka?"
Tace
"Makaranta?"

"Wacce makaranta?"
Murmushi tayi tace
"Naje nai registeration yau."

Ido ya zaro yace
'Masha Allah. Allah ya bada sa'a kace sai fara makaranta."
Kai ta gyada yace
"To ni mai zan miki na zuwa ckul?"

"Addu'a."
Kai ya girgiza yace
"No anjima zan kai ki kiyi shopping na abinda zaki bukata a makaranta."

"Ni me zan nema Yaa Farouk nagode ka barshi kawai."
"Ba kyau mai da hannun kyauta baya."

Tai murmushi tace
"To nagode."
Ta nufi sashen Inna ta sanar mata da komai sannan ta koma part din su dan yin aiki. Karfe biyar Ummi ta dawo anan ta same ta tace
"Ya makarantar?"
Nan ta hau bata labari Ummi tace
"To a tsaya dai ayi abinda a kaje."

"Insha Allahu."
Bayan magariba, tana zaune sai ga Farouk da kan sa ya shigo ya fadawa Ummi inda zasu ta kalli Maryam tace
"Sai kun dawo."

Maryam ta mike tabi bayan sa dan daman da hijab din ta a jikin ta. Kaya masu yawa ya siya mata dan ita ta ki daukar komai shi ya dinga jidar mata dogayen riguna hand bags da sauran su haka suka biya akai total ya kashe mata kudi masu yawa suka fito suka yo gida.

Yana parking taga Aliyu zaune a cikin mota shi da Haidar kai ta dauke ta fita. Farouk ya fito rike da ledar da yayo mata siyayya yabi bayan ta har sun kusa sashen su yaji wayar sa na kara zarowa yai yana dubawa yaga Mama ce kai ya daga yana kallo barender ta, wata farar mata mai jiki ce tsaye a barrender sanye da atamfa daguwar riga, kallon sa take wannan yasa ya dauke kai ya kai wayar kunnen sa yana fadin
"Hello Mama!"
"Kazo yanzun nan."

Maryam ya kalla da ta kusa kofa ya kwalawa mata kira, ta juyo ya karasa tare da mika mata ledar yace
"Sai anjima."
Tai murmushi tace
"Nagode."
Ya juya yayi sashen su. Dakin ta ya shiga wanda ya gaji da haduwa da wasu purple kalar kujeru da labuyale, zaune ya same ta akan kujera kafa d'aya kan d'aya zama yayi yace
"Gani Mama."

"Me ya hada ka da wannan yarinyar?"
Ta tambaya fuska a hade, kan sa yai kasa dashi yace
"Yaa Aliyu ne ya aike mu."

"Na fada maka bana son ina ganin ka kana kula yarinyar nan amman ka'ki kaji ko? Ka fita idona na rufe fa."
"Kiyi hakuri Mama."

"Tashi ka ban waje."
Ya mike ya fita yana mamakin halin Maman sa shi sam bai ga aibun su Ummi da Mama take musu wata irin kiyayya. Sashen Inna ya wuce kawai.



Maryam na shiga ta samu Ummi a Falo kayan ta dire tana nuna mata wayar Ummi tai kara ta duba tace
"Hello Aliyu lafiya?"
"Turon Maryam."

"Ok."
Ta kalli Maryam tace
"Yayan ki ke kiran ki."

"Ni kuma?"
"Eh."
Mikewa tai ta fita. A parking space din ta same su cikin mota yace
"Shiga mana."

Ta bude baya ta shiga ya tada motar. wani super market ya nufa dasu suna shiga ya kalle ta yace
"Ki dauki abinda kike so."

Yaja hannun Haidar sukai bangaren kayan maza. Fara zagaye wajen tayi tana kallon kayan wajen tafi rabin awa ba abinda ta dauka, har suka gama bata dauki komai ba sai kallon kayan da take dan burge ta sun burgeta amman kuma abun da sukai mata yana da yawa banda dawainiyyar ta anya kuwa. A haka suka karaso wajen basket din su cike da kaya kallon ta Aliyu ya tsaya yi can yace
"Me kika dauka?"

Kan ta tayi kasa dashi a hankali ta girgiza
"Ba abinda kike so kenan ko?"
Shiru tayi ya kama hannun Haidar yace
"Muje!"

Suka bar wajen bayan su tabi suka bayar aka gama masa total ya biya sannan suka fita mota ta shiga, ya ajiye Haidar ya koma ciki bai jima ba ya fito rike da leda ya bude motar ya shiga ya tayar suka koma gida. Tara saura suka koma gida dan haka ta dauki Haidar sukai sama. Wanka tayi masa itama tayi ta shirya shi ya kwanta sallah ta tayar kan ta idar har yayi bacci. Sauka kasa tayi dan ta zuba abinci ta samu leda a bakin dakin su, kasa ta sauka ta dauki nono ta zuba suga ta sha sannan ta fito tayi sama, kayan ta kwashe ta shiga daki.

Akan gado ta zube su kaya ne masu kyau da tsada a cikin ledar dayar kuma under wears sai turarukan sa da su alawa biskit chocolate adana kayan tayi a wajen da ya kamata sannan ta kwanta.

Bata jima da kwanciyya ba taji an bude kofar dakin dagowa tayi Ummi ce ta mike zaune tace
"Kun dawo?"

"Eh Ummi."
"Abban ki ke son ganin ki."

"Toh!"
Ta fada tana mikewa hijab din ta ta saka ta bi bayan Ummi yana dakin sa ta shiga da sallama ta zauna a kasa tace
"Barka da dare Abba."

"Yauwah Maryam ya gida?"
"Alhamdulillah Abba ya aiki?"

"Alhamdulillah dazu Ummin ki ke fada min, Yayan ki ya samar miki addmision har da kudin registeration Allah ya bada sa'a ni gudunmawar me zan bayar tinda ya riga ya gama wadan nan?"
Kan ta a kasa tace
"Abba addu'a kawai nake bukata."

"Kullum muna miki addu'a Maryam sai kuma me?"
Kai ta girgiza. Yace
"To ya kamata ki bude account ko dan kudin makaranta da abubuwa ko?"

"Eh dazu Yaa Aliyu yasa an bude min."
"To ai sai a bani account number ko?"

"Nagode Abba."
"Ba komai ina Haidar din?"

"Yayi bacci."
"To sai da safe."

"Nagode Abba Allah tashe mu lafiya."
Ta mike ta fita. Komawa dakin Ummi tayi ta same ta tace
"Ummi na fito."


"To sai da safe."
Ta tafi dakin ta, ta kwanta tare da addu'a



***
Washe gari da yamma tana bangaren Inna suna hira Haidar ya shigo a guje ya fada jikin Maryam ta dago shi tana fadin
"Haidar ba zakana tafiya hankali ba ko?"

Dariya ya hau yi mata tace
"Yaushe ka dawo."
"Yanzu Abbi na kiran ki."
Ya fada yana zuwa ya zauna a cinyar Inna. Inna ta shafa kan sa.

Mikewa tayi ta fita yana dakin sa ta shiga da sallama ya amsa, ta dan kalle shi, sanye yake da wando cotton dogo ruwan omo sai riga ruwan madara mai dogon hannu, idon sa a lumshe bai ko bude ba tace "sannu da zuwa."
"Yauwah!"

Ya nuna mata wata leda dake kan kujera da hannu yace
"Dauki."

Dauka tayi ta tsaya, duk da idon sa a rufe yake yasan tana wajen a hankali ya bude idanun nasa ya zuba a saman fuskar ta, da sauri ya janye idon sa, itama tai saurin yin kasa da kanta dan Aliyu ba karamin kwarjini yake mata ba, bama in ya daura idon sa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment