Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girgiza yace
"Ki fada min abinda yake damun ki."

Ka ta girgiza yace
"To tashi mu tafi."
A hankal da kyar ta mike ya bude mata kofa ta fita yabi bayan ta. Kitchen suka karasa wajen Ummi tana ganin su tace
"Ah ta sauko?"

"Gata nan zamuje ta dan tattaka."
"To a dawo lafiya."

Suka fita yana fadin
"Kinyi azhkar dai ko?"
Kai ta gyada yace
"Good girl."

Dan murmushi ta saki suka fita a gida suna tafe in ta gaji ta tsaya ta huta su cigaba sun yi tafiya mai tsayi ta tsaya ta marairaice idon ta dan yadda taji kafar ta da bayan ta sun rike kallon ta yai yace
"Ya dai?"

Hannu ta yafe ta nuna masa bayan ta, yace
"Ko haihuwar ce?"
Ya tambaye ta dan ya manta Maryam bata san wata haihuwa. Kai ta girgiza ta masa alamar ba zata iya tafiya ba. Napep ya tsayar ta shiga ya shiga suka koma gida kan suje gida har kafar ta saki da kan ta ta shige gida ya biya mai napep yai alwala ya wuce masallaci.

Tana shiga ta wuce sama da Ummi ma bata kasa alwala ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta tada sallah a zaune tayi tana idarwa wani bacci ya dauke ta. Cikin baccin taji wani a zababen ciwo ta farka tana ciccije baki tare da addu'a a cikin zuciyar ta. A hankali taji ciwon na sauka zuwa can koma taji komai ya lafa.

Ummi ce ta shigo tace
"Maryam sauko kici abinci."
Kai ta girgiza, Ummi ta durkusa tace
"Dan Allah meyake damun ki? Ki fada min ki dauken a matsayin uwa na fada miki."

Kai ta kuma girgizawa. Ummi ta kalle ta tace
"To sauko kici abinci."
Nan ma kai ta girgiza. Ummi tace
"Yau fa baki ci komai ba ki fada min ko akwai abinda kike so sai nai miki."

Dagowa tai tana kallon Ummi idon ta cike da kwalla. Gyara zama Ummi tayi tace
"Bana son kukan ki sam Maryam ki fadan me kike so?"

Hannu Ummi ta kama ta matse a cikin nata tare da lumshe ido, Unmi ta bita da kallo daga baya ta saki hannun nata ta sakar mata murmushi abun da take rubutu ta dauko tace
"Ummi bana bukatar komai ki daina damuwa."

"To shikenan me zaki ci?"
"Bana jin yunwa Ummi."

"Yau fa tin karin safe baki ci komai ba ko dan cikin ki ai kya ci wani abu ko? Bari Dr ya dawo nai masa magana ya samo miki wani abu."
Ta mike ta sauka. Bayan Isha'i Aliyu ya shigo ya zauna a falo yana kallon kafar bene Ummi ta sauko tace
"Yauwa daman kai nake jira."

"Haihuwar tazo ne Ummi?"
Ya tambaya da sauri. Murnushi Ummi tayi tace
"Oh oh oh likita ba ita bace."

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"To menene Ummi?"
"Taki cin komai tin safe rabon ta da abinci fa."

"To me take so?"
"Sai da a tambayo ta wai ita bata jin yunwa."
Mikewa yayi ya hau benen kofar dakin ya isa ya buga kofa fitowar ta daga bandaki kenan ta saka hijab ta nufi kofar ta bude, sannan ta juya yace
"A'ah dawo ai fita zamuyi."

Dagowa tai ta kalle shi cikin fuskar tausayi yai murmushi yace
"Ban daukar wani excuse zo muje kema kya samu nishadi a waje."
Ba dan ta so ba ta biyo bayan sa suka sauko.

Ya kalli Ummi yace
"Zamu fita Ummi sai mun dawo."
"A dawo lafiya."

Ummi ta fada tana kallon Maryam da katon ciki sai kace na yan biyu. A hankali tabi bayan sa suka fita. Shi da kan sa ya bude mata kofa ta shiga sannan ya rufe ya zaga ya shiga dayan side din ya nufi gate yaba saka kai Motar Mama na shigowa kallon juna sukai yace
"Barka da zuwa Hajiya Mama"

Tsaki ta saki ta dauke kai ya saki murmushi yaja motar ya bar wajen ta bisu da kallo tana fadin
"Na tabbata akwai wani abu tsakanin yaon nan da yarinyar nan sai rainawa mutane hankali ake bari dai yau naje na samu Alhaji."

Ta shiga da mota tai parking ta fito ta nufi sashen su. Dakin ta ta shiga ta ajiye jakar ta da mayafi sannan ta fito ta nufi bangaren Abba. A falo ta same shi yana kallon BBC ta shiga tana fadin
"Ashe ka dawo?"
"Daga ina kike da daren nan."

"Haba Alhaji naga na fada maka zani bikin yar Hajiya Karima ko?"
"Amman karfe nawa yanzu bayan isha'i ake dawowa daga unguwa na fada miki bana son ana fita ana kaiwa dare amman ke sarar ki kenan."

"Kayi hakuri."
"Kada ki sake na fada miki."

"Naji."
Ta fada ya dauke kai daga kallon ta gyara zama tayi tace
"Wai Alhaji kayi bincike kuwa game da yarinyar da Aisha ta kawo gidan nan?"

Juyowa yai yana kallon ta yace
"Me ya faru?"
"Eh to nifa ban yadda da wai tsintar yarinyar nan sukai ba ina ganin ko dan ta ne ya dirkawa yarinya ciki iyayen ta suka koro ta shine suka kawo ta nan ta haife su mai da ta gidan su."

"Wane d'an kenan?"
"Zai wuce Aliyu tinda ita bata ganin laifin sa sam, komai yai dai dai ne ita ke daure masa gindi shiyasa ya raina mutane yake abinda yaga dama yanzu ma fa na ganshi tare da yarinyar sun fita me yake hadasu in ba wani abu tsakanin su."

"Keee ya isa haka Barira na rantse da Allah ki kiyaye ni da kwason ko wanne irin shirgi kina fada min. Yanzu a gaban ido na kike tuhumar d'ana da fasikanci, kada ki manta Aliyu fa d'anane na ciki na amman ko kunya bakya ji, waye zai boye miki gaskiya. Wallahi Barira ki fita a ido na da irin wadan nan halin naki, shikenan ba zasuyi taimako saboda Allah ba da izinin Allah ban haifi fasiki ba bare wanda zai kawon dan shege ba dan haka ki kiyayen tashi ki bani waje."
Mikewa tai tana magana kasa kasa
"Uhmm kada ka yadda ai nasan ko banza na saka maka wasi-wasi kuma nasan zaka bincika Allah yasa cikin sane in an bincika a lokacin naga da wane ido da baki zakai min bayani."

Ta fice a daki komawa Abba yai ya jingina da kujera yana tunanin maganar, Mami ce ta shigo da sallama yana daga inda yake ya amsa ba tare da ya bude idon sa ba. Juice din da ta shigo dashi ta ajiye akan center table sannan ta karaso ta zauna a kusa dashi tare da dafa shi tace
"Lafiya Alhaji?"

Ta saka dayan hannun ya kamo hannun ta tana wasa da hannun nasa sun jima a haka wajen minti uku sannan taji ya sauke ajiyar zuciya. Sakin sa tayi ta mike ta zubo masa juice din a kofi ta kawo masa a baki ta saka ya kurba tare da lumshe ido yana mai kara sauke wata ajiyar zuciyar. Sai da ya sha rabi ta janye ya kalle ta yace
"Matar Aljanna Allah miki albarka."

Wani dadi Mami taji a cikin ranta tace
"Amin Mijina kana hakuri da halin da ka tsinci kan ka kada kace zaka dauki wani mataki a duk abinda za ai maka mai hakuri shike da riba kuma ko wanne tsanani yana tare da sauki, kuma Allah yana tare da mai hakuri kayi hakuri Mijina."
"Madallah ga matar Aljanna ina alfahari da kasancewa tare dake a ko da yaushe kin ban soyayya kin bani yara masu albarka ba abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da mafificin Alheri."

"Amin godiya nake miji na taso muje kaci abinci."
Ta mike tana son kamo hannun sa. Kamo hannun ta yayi yace
"Zauna muyi wata magana tukkuna."

Komawa tayi ta bashi hankalin ta ya kalle ta yace
"Me kika sani akan yarinyar da su Aisha suka kawo gidan nan?"
"Oh Maryam ina ce Inna tai maka bayanin komai."

"Ina so na kara ji daga bakin ki dan nasan ba zaki boye min komai ba baki tabai min karya ba kuma nasan ba zaki fara ta a yau ba."
"Me ya faru ne Alhaji?"

"Ba komai fada min."
"To kasan tafiyar da sukai Bauchi a can suka dawo da ita a hanyar su ta dawowa suka kade ita yarinyar da aka kai ta asibiti bata farfado ba har washe gari to kaga ba zasu tafi su barta ba to data farfado suka so su gana da dagin ta amman bata san komai akan rayuwar ta ba kamar tayi losing memory kuma bata magana wani abun al'ajabin ma ciki da ita amman tace tana da miji da mahaifiyar ta abinda take iya tinawa kenan. Kasan Aisha da tausayi wannan yasa ta kasa barin ta acan, dan bata san wane hali zata fada ba kaji dalilin tahowar ta da ita gida."

Tinda Mami ta fara magana yake kallon ta har ta gama yace
"Kin tabbata?"
"Eh Alhaji."

"To tashi muje."
Hannun ta sa ta kamo tace
"Meyasa kai min wannan tambayar?"

"Ba komai."
Ya fada yana mikewa tabi bayan sa dining ta zuba masa abinci yaci sannan ya shiga dan yai wanka bayan ya fito ya shirya cikin kayan bacci ta window ya leko yana kallon harabar gidan ko ina tsit dan dare ya fara lokacin kusan goma da wani abu. Mami ce ta karaso tana fadin
"Alhaji baka kwanta ba daman?"

Ya juyo yace
"Eh aiki ma nake son nayi ko zan samu ruwan dumi."
"Bari na kawo maka."

Ta fada tana ficewa. System ya dauka ya koma barandar gidan ya zauna yana aiki a haka Mami ta kawo masa ta juya ta koma daki ta kwanta har sha biyu saura yana wajen yana aiki.







*Allah ya jikan mu yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*



*Antty*
[11/23, 12:32] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 52

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*******
Wani waje ya kai su, ya fito ya bude mata mota ta fito tana bin wajen da kallo bata taba ganin waje mai kyau da tsari haka ba. Harabar wajen yalwace take da shuke shuke ga haske da ya kawata wajen. motoci ne manya a wajen yai gaba ta bi bayan sa. Wata Kofa suka nufa security dake wajen yai sauri ya bude musu hanya ya bata tai gaba yabi bayan ta, suka shiga. Wani sanyi da kamshi ne ya doke ta. Wajen take bi da kallo duk da hanyar wucewa ce amman an kawata ta. Sai da sukai tafiya mai tsayi sannan ta fara ganin wajen saida abubuwa kala kala. Wani waje ya shiga da ita suka nufi can karshe duk da wajen ba mutane suka zauna. Basu jima da zama ba aka kawo musu lemo da menu. Amsa yayi yai ticking sannan ya mika mata, rasa me zata zaba tayi ya amsa ya zabar mata sannan mutumin ya juya.

Kallon wajen take dan wajen ya matukar burge ta, ga sanyi ga ni'ima suna zaune aka kawo musu abinda suka zaba. Maryam ta dauka ta fara ci Ido ta lumshe tana jin wani dandanno da dadi a bakin ta.

Sun dauki kusan awa a wajen sannan suka bar wajen dan ya riga yai musu transfer.

Cinema suka nufa, nan ma suna zama aka kawo musu pop corn da lemo aka ajiye a gaban su.

Aliyu ne ya fara ci amman ita ko kallon sa batai ba Idon ta na kan film din da ake nunawa. Dauka yai ya bata ta amsa batai niyyar ci ba yace
"Kici da dadi."

Diba tayi tai Bismillah ta kai bakin ta, tana taunawa ta lumshe Ido dan ji tayi kamar Madara kadai take taunawa ga wani dadi da bazata iya misalta shi ba. Kadan Aliyu yaci ya ajiye amman sai ga Maryam ta tashi da nata gaba daya. sai da aka gama film din suka mike zasu tafi ta kalli Aliyu ta kalli ragowar 🍿 din yai murmushi yace
"Dauko mana muje ma mu siyarwa Ummi dan tana sonsa."

Kan ya rufe baki har ta dauki abin ta suka fita ya siya da yawa zasu fita ta kalli shi ta nuna masa wajen da suka fara zuwa yace
"Wani abu kike so?"

Kai ta gyara suka shiga ya amshi menu ya bata ta kara zabar abinda ya siya mata dazu aka bata ya biya suka fita tana gaba yana bin bayan ta.

Suna fita suka nufi wajen motar su zasu shiga wata mata da tin da suka shigo take kallon su dan ba karamin burge ta sukai ba bama da yazo ya bude mata ta shiga ya rufe ya zuba kayan a baya har ya zagaya ta karaso wajen inda Maryam ke zaune tace
"Sannu 'ya ta."

Dagowa tai ta sakar mata murmushi. Dai dai shigar Aliyu ya kalle ta yace
"Sannu Hajiya."

"Yauwah sannun ku. Allah raba lafiya Allah kara baku zaman lafiya."
Tana fada ta juya Aliyu ya bita da kallo Maryam kuwa ragowar popcorn din sa take ci a haka suka bar wajen suka nufi gida.

*
Sha biyu saura suka karasa gida. Abba yana ta zaune a inda yake yaga shigowar su ya zuba musu Ido har Aliyu ya fito ya bude mata mota ta fito tai gaba yabi bayan ta da kallo ya bisu har suka shige bangaren Ummi. System din gaban sa ya rufe ya mike ya shiga dakin baccin su. Mami tai bacci shima kwanciyya yai yayi addu'a ya kwanta.


Suna shiga tai sama shi kuma yai dakin sa. Kayan jikin ta cire ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta saka kayan baccin ta ta hau kan gado tana addu'a Ummi ta bude kofar ta dago tana kallon ta.
"Sai yanzu kuka dawo cikin daren nan?"

Kai tai kasa dashi dan itama sai yanzu taga dare yayi sosai har haka. Ummi ganin tayi kasa da kai tace
"Kinci abincin?"
Kai ta gyada mata. Shigowa tayi ta rufe kofar ta kwanta tace
"To kiyi addu'a kinji."

Kai ta gyada tai addua ta tofe jikin ta. Sannan ta kwanta. Tin da cikin ya shiga watan haihuwa Ummi ta bar barin ta ita kadai suke kwana tare dan kar nakuda ta zo musu cikin dare.


Da asuba ta tashe ta ta shiga tayo alwala ta tada sallah tana idar wa ta fita a dakin. Maryam ta tasa ta fara sannan tayo awala tazo ta tada sallah tana idar wa ta yunkura da nufin ta mike sai taji wani irin ciwo ya kunno mata komawa tai ta zauna da sauri tana runtse idon ta hadi da ambatar sunan Allah. Jin azaba tai azaba ta bude idon ta tana fitar da wani nishi mai sauti kan kace me ta fita daga hayacin ta gaba daya ta rasa inda zata saka kan ta. Da kyar take iya fitar da numfashi.

Karfe bakwai ya fito cikin shirin sa na tafiya asibiti dan yau yana da aikin da zai yi da karfe takwas. Kitchen ya leka ya tadda Ummi na soya dankali karasawa yai ya durkusa ya gaishe ta. Ta amsa tana fadin
"Dr yau fitar sasafe ce kenan."

Dankalin da ta tsame ya diba a wani dan karamin plate yana fadin
"Akwai aikin da zamuyi tin last week aka saka za ai aikin sai kuma aka samu akasi ba ai ba shine aka saka shi yau da karfe takwas."

"To Allah yasa ayi a sa'a."
"Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!"
Ya gama ci ya dauki fresh yoo a firij yana fadin
"Sai na dawo."

Har ya kai bakin kofa ya juyo yace
"Ummi Maryam fa?"
"Tana sama ina jin bacci take."

Fita yai ya nufi sama yana zuwa ya tsaya a bakin kofa yana knocking amman shiru ya buga yafi sau biyar ba a amsa ba har ya juyo zai bar wajen sai kuma ya koma da ya kasa kunnen sa a jikin kofar nishin ta ya fara jiyowa sama sama da sauri ya saka hannu ya murda kofar dakin ya shiga a can gefe gado ya hango ta zaune tana fitar da wani irin numfashin wahala ta kan gadon ya dira ya karasa wajen ta yana fadin
"Maryam! Maryam!!"

Ina bata san ma me yake ba dan azabar ciwon da take ciki dago ta yai ya fita dakin da ita a haka suka sauka daga benen yana kwadawa Ummi kira. Ummi dake wake kayan da tai amfani dasu ta fito tana fadin
"Ah Dr daman baka tafi ba...."

Maganar tace ta tsaya lokacin da ta ganshi dauke da Maryam a hannun sa har ya kai kofar dakin. Da gudu tabi bayan sa ya saka Maryam a bayan mota sannan ya shiga wajen mai tuki. Ummi ta shiga wajen Maryam da sauri tana janyo ta jikin ta tare da mata sannu.

Yana yiwa motar key ya dannan wani uban horn wanda kan ya karasa har masu gadi sun bude masa kofa a guje ya fice a gidan cikin minti takwas suka karasa asibitn dan gudu yake kamar zai tashi sama. Suna shiga nurses din dake wajen suka karaso da gadon daura mara lafiya. Motar Ummi ta bude ta fito suka fito da Maryam suka daura ta akan gadon sannan sukai cikin asibitin da ita da gudu.

Labour room suka nufa da ita Ummi da Dr suka bi bayan su da sauri a bakin kofa Ummi ta tsaya Aliyu ya shiga yana kallon yadda Nurses din ke bata taimakon gaggawa. Daya daga cikin nurse din ya kalla yace
"Jeki ki kira min Dr Nusaiba ki fada mata yanzu yanzu dan akwai emergency aiki please."

"Ok Sir."
Ta fada ta fice daga dakin. Yana daga nesa yana kallon su. Ba ai minti uku ba sai ga Dr Nusaiba tare da nurse din da ya aika tana zuwa ta wuce kan Maryam tana dubata. Karasowa yai yace
"Haihuwa ce ko?"

"Eh Sir amman kuma lokacin ne bai yi kila amman daga yanzu zuwa ko da yaushe zata iya sauka."
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Ba dai wata matsala ko?"

"Babu insha Allahu."
"Alhamdulillah please Doctor ki kula da ita sosai."

"Insha Allahu."
Ya fita daga dakin Ummi ya sama tana safa da marwa daga wannan bangon zuwa dayan bangon. Da sauri ya karasa yana fadin
"Muje Ummi ki zauna insha Allahu yanzu zata sauka."

"A'ah Aliyu ba zan iya tafiya na bar ta a wannan halin ba."
Hannun ta ya janyo yace
"To taho ki zauna anan."

Ta zauna shima ya zauna yana fadin
"Bamu fadawa kowa a gida ba."
"Kira Abba na sanar masa kada ya tashi yaga ba kowa ma a gidan."

Nan Aliyu ya kira Abba da Mami ya fada musu sannan ya kashe wayar yana fadin
"Allah sauke ta lafiya."
"Amin ya Allah."

Dukkan su cikin tashin hankali suke suna zaune a wajen har karfe takwas amman shiru kasa zama yai ya mike ya shiga dakin ganin ta yai tana ta fama duk ta galabaita.

Karasawa yai bakin gadon yana mata tofi sai da ya gama ya dago yana kallon Dr Nusaiba da Dr Yasmeen yace
"Har yanzu ko?"
"Eh Wallahi amman ka kwantar da hankalin ka insha Allahu in less than 30 minute zata sauka."

"Allah ya yadda. Bari naje."
Ya fita ya samu Ummi tace
"Har yanzu ko?"

"Eh wallahi Ummi."
"Bani wayar ka na kira Mami nace a samo mata rubutun nan."

"Ummi rubutu kuma."
"Bani nace kai komai ba dai dai bane a wajen ka."

wayar ya mika mata nan ta fada mata abinda take so ba ai minti goma ba aka kawo musu rubutun da kan ta ta shiga ta bawa Maryam ta sha. Duk ta galabaita.



Abu kamar wasa har karfe biyu na rana Maryam na fama da nakuda daga ita har likitocin duk sun galabaita. Ummi kuwa duk ta tsorata. Ba wanda yafi Aliyu shiga wani hali dan gani yake abinda ya faru da matar sa shi ne yake shirin kara faruwa ya kasa tsaye ya kasa zaune ko yaje kan ta ba abinda yake iya aikatawa ga tausayin ta da a lokaci guda ta rame idanun ta duk sun kara fiffitowa ga ba baki sai nishi da hawaye dake zubowa kawai.

Hakika duk wanda yaga Maryam a halin da take ciki sai ya tausaya mata masu raguwar zuciya kuwa sai sun zubar mata da hawaye. Inna ma ta zo asibitin dan ta shiga wajen Ummi mai aikin take fada mata tana asibiti Maryam zata haihu cikin tashin hankali tace
"Tin yaushe kuma?"
"Nima da nazo wajen sha daya ba kowa duk suna asibiti."

"Ba zama ai."
Ta fice tana kwadawa Farouk kira lokacin dawowar sa kenan ya karaso yana fadin
"Haba Inna me ya faru? Wannan kira sai kace ana yaki."

"Kai ni rufe min baki, kazo ka kaini asibiti."
"Me yake faruwa?"

"Kaini dai kawai."
Kallon ta ya tsaya tace
"Mahaukaciya ka maidani ne ko? In ba zaka kai ni ba bari na kira Shehu da Suleimanu su kaini."

"A'ah Inna muje."
Yai gaba ya bude mata kofa, ta shiga ya rufe suka nufi asibiti. A can suka samu Mami da Ummi. Inna ta karasa tana fadin
"Ya jikin nata?"

"Tana ciki dai."
"Innalillahi Allah ka sauki yarinyar nan lafiya. Haihuwa yakin mata tana ina naganta."

"Inna kinsan basa bari a shiga dakin ai."
"Ni da kun bar ta a gida na amshi haihuwar ta ko me asibitin suka iya?"

Aliyu ne ya fito ya samu waje ya zauna tare da dafe kan sa. Ummi ta mike tana fadin
"Ya dai Dr?"
"Ummi har yanzu dai she is suffering."

"Allah ka dubi baiwar ka, ka saukaka mata wannan ciwo."
"Amin Ummi."

"Kada ka saka damuwa Aliyu zata sauka lafiya da izinin Allah."
"Allah ya yadda."

Farouk sai yaji zuciyar sa ta karye tausayin ta ya kamashi shima sai gashi yana addu'a Allah ya sauke ta lafiya. Suna zaune har akai la'asar Aliyu da Farouk suka tafi masallaci Ummi kuma sukai sallah a ofishin Aliyu. Suna idarwa suka koma kofar dakin basu jima ba sai ga Su Aliyu sun dawo. Suna zaune wajen biyar sai ga Abbi da Abba sun shigo.

Abba yace
"Wai har yanzu ba matsala kuwa Dr kasan ba a son doguwar nakudar nan."
"Abinda na ke tunani kenan Abba to daman da naji zaku zo nace in kunzo mayi maganar gwara a aikin sai ka sa hannu ko?"

"To ya kuka ce?"
Abba ya fada yana kallon su Abbi da Ummi. Hawayen Ummi ta goge tace
"Gwara ayin ko ta huta itama."

"To shikenan."
Aliyu ya shiga yaiwa Dr magana suka fara shirin aiki. Ya kawo wa Abba takarda Abba ya saka hannu wanda cikin rabin awa an gama shirye shiryen shiga aiki. Aliyu ne ya shiga dakin da Maryam take, har lokacin tana kwance ya karasa ta dago ta kalle shi cikin sarewa ta nuna masa waje tana masa alamar ya kirawa mata wani a waje. Ko bata fada ba yasan ba wanda zata bukaci gani a irin wannan lokacin sai Ummi dan haka da sauri ya fita ya kamo hannun Ummi suka shigo dakin. Ummi na ganin Maryam ta karasa da sauri ta kama hannun ta tana fadin
"Sannu 'Ya ta insha Allah za ai aikin nan lafiya da izinin Allah."

Kai Maryam ta fara girgizawa hawaye na fita a idon ta. Ummi tace
"Ki bar kuka kinji Maryama da yadda Allah zaki tashi kiyi rayuwa da yaron ki."

Nan ma kai ta girgiza ta kamo hannun Ummi ta daura aka cikin ta sannan ta kamo hannun Aliyu ta daura akan na Ummi tai nuni da ta basu abinda yake cikin su rike mata shi amana. Hawaye ne ya zubowa Ummi ta hau girgiza kai tana fadin
"Kema zaki rayuwa da dan ki insha Allahu."

Aliyu ta kalla wanda tashin hankalin da yake ciki har ya saka jijiyoyi kan sa sun fito rada rada dan shi halin da Maryam take ciki yana tino masa da halin da tashi matar ta shiga a baya. Juyawa yai ya fice a dakin ya wuce office dinsa kawai. Yana shiga ya hade kan sa da table din sa addu'a kawai yake a cikin ransa Allah ya sauki Maryam lafiya. Ummi ma da kuka ta fito suna tsaye aka fito da Maryam daga dakin akan gado suka nufi dakin da za ai aikin Maryam na ganin Ummi ta daga mata hannu tana mata bye bye abinda ya kara karyawa su Mami da Ummi zuciya kenan. Farouk kan sa dake wajen sai da hawaye ya ciko idon sa tausayi Maryam yaji sosai. Abba da Abbi ma sun mata addu'a Alah yasa ayi aiki lafiya.

Bakwai saura kwata suka farai mata aiki lokacin Abbi, Abba, Farouk da Aliyu suna masallaci duk da sun idar da sallah amman sun kasa fitowa daga Asibiti su Abba ko gida sun kasa tafiya. A cikin asibiti kuwa su Ummi, Mami da Inna bayan sunyi sallah Inna sai kuka take tana fadin
"Yarinyar kirki Allah yasa ayi a sa'a."
Ita kadai sai surutai take yi.

Suna masallaci aka kira isha'i suka gabatar sannan suka addu'a. Farouk ne ya fara fita a masallacin can inda dakin ya karasa su Ummi ya sama zaune a wajen. Bai jima ba Abba ya karaso wayar farouk ce ta hau kara yana dubawa yaga Mama ce kamar ba zai dauka ba sai ya dauka.
"Kana ina?"

"Ina asibiti Mama wana..."
"Kanwar uwar kace ko ta uban ka?"
Ta fada cikin fada.

Please Login or Register in order to submit comment