Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ya rumgume yana shafa bayan ta a hankali wanda jin ta a jikin sa yasa ya fara jin wani yanayi, abinda ya gani a cikin idon ta yake so ya gaskata, shin da gaske ne son sa yake gani a cikin idanun Maryam ko kuwa gizo abin yake masa, a hankali ya matsar da bakin sa saitin kunnen ta yana fadin
"To ya isa menene na kuka?"
"Ni ka daina cewa bana son ka Yaya."

"To kina son nawa ne?"
Shiru tayi yace
"Uhmm gashi nan, na sani bakya so na auren dole akai miki, duk da haka kina da chance na sanar da iyayen mu i will do you what u want and i will support you kinji."

Jikin ta ta janye dan da gaske maganar sa bata mata rai take cikin murya kuka take fadin
"Ko da bana son ka ba zan taba fadawa iyaye na ba, ko da bana son ka nayi alkawarin zama dakai na har abada, ko da ba zaka na kallo na a matsayin mata ba zan kasance a matsayin kanwar ka, amman ka daina cewa bana son ka, kun min abinda ba zan ta'ba kin ku ba, kun dauken a lokacin da baku san ko ni wacece ba, baku kyamacen ba har kuka fifitani a cikin yan uwan ku, a karshe aka aure min kai Yaya meyasa zan 'ki ka, wane aibu ne da kai da zan ki ka, bayan ni tin baku san wacece niba kuka soni kuka kaunacen Yaya in nace bana son ka nayi karya a duniya daga iyaye na a yanzu sai Ummi da kai nafi so da kauna."

A hankali ya tako gaban ta yace
"Wannan kaunar ta hallacin da mukai miki ce Maryam ba 'kauna ta auratayya kike min ba."
"Menene bambamcin ta, tinda duk 'kauna ce Yaya?"
Matsowa yayi dab da ita ya dago kanta yace
" 'Kauna da soyayya da sha'awa kuma wacce ita zata bamu damar sanin sirrin juna."

Ido tai saurin runtsewa jin yadda yake yawo dan idonsa a cikin nata, hannun sa dake rike da kanta ya saka yana shafa gefen fuskar ta wanda hakan ya fara haifar mata da wani iri a jikin ta so take ta kwace amman ta kasa, ta janye jiki ta juya zata bar dakin cikin zafin nama ya kamo hannun ta ya janyo ta da karfi ta fado jikin sa, hannun sa ya sa ya zagaye ta dan yasan yanzu zata ce zata gudu, ganin ba zata iya kwacewa ba yasa tayi kasa da kanta yace
"Kunyar kuma fa?"

Kai ta girgiza ya dago kanta wanda hakan yasa tai saurin runtsa idon ta ya saki murmushi yana fadin
"Ni dai dan Allah ki daina tsayawa da ko wanne namiji wallai baki ji yadda nake ji ba."

Kai ta gyada yace
"Ki min magana ba gyada kai ba."
"To Yaya ba zan kara ba."

"Allah miki albarka."
"Amin."

Ya sake ta ya juya zai fita har ya kai kofa tace
"Yaya!"
Juyowa yayi tace
"Please ka ban dama nai masa bayani a baya bai san ina da aure bane shiyasa."

Kallon ta ya tsaya yi ta langwabar da kai tace
"Nasan me nake Yaya nasan ba kyau tsayawa da wanda ba muharami na ba ka yadda dani Yaya ba zan wani abu ba dai dai ba."
"Ba komai."

Ya fada ya juya ta kara fadin "Yaya!"
Juyowa yayi sai tayi kasa da kanta dan ji tayi bata so ya tafi, ganin ta kasa magana yasa ya karaso ya zo daf da ita ya janyo ta jikin sa tare da dago kanta yace
"Fada min menene?"

Kai tayi kasa dashi yace
"Shikenan tinda na zama sirikin ni bari naje na kwanta."
Ya juya ta kamo hannun sa ya juyo sai ta fada jikin sa tana fashewa da kuka. Yace
"Menene kuma?"

"Yaya please ka yafe min, tinda na san ina da aure na cire kowa a raina, sai kokarin ganin na saka soyayyar ka nake."
Hannu ya saka yana shafa bayan ta yace
"To na shiga zuciyar taki?"

Shiru tayi ya dago kanta da hawaye ke kwance a fuskar ta yace
"Uhmm."
Ido ta lumshe ya saki murmushi yace
"To ni sakeni tinda ba zaki fada min ba."

"Uhmm ba dan kaga na fara ba shine kake hukuntani."
Da sauri ya dago kanta yana kallon ta ji yake kamar ba ita tai magana ba yace
"What?"

Kanta ta tusa a cikin kirjin sa tana girgiza kai, kara matse ta yayi a jikin sa yana mai godiya da Allah da ya fara karkato masa da hankalin Maryam kansa,

Kansa ya shafa yana kallonta ya dago ta yana kallon ta sam baya gajiya da kallon Maryam ko kadan.
"Maryam kina sona?"
Jikin sa ta fada tana boye fuskar sa yai murmushi yace
"Any way, fada da fatar baki bata lokaci ne, later in kika shigo gida na baki san lokacin da zaki fadan ba, wanda before then ur reaction will say everything."

Sakin sa tayi da sauri ta juya masa baya, ya karasa yana fadin
"Oh kunya ko? Naga ke dai kika hanani tafiya ko? Na tafi to."

Ya fada yana juyawa yana tafiya yana juyowa, yana karasawa bakin kofa yace
" *Matar Haidar* "
Cak komai ya tsaya mata, abubuwa da yawa suka hau dawo mata, da gaske dai ta tabbata *Matar Haidar,* da gaskiyar Yaa Haidar da yace ko ya tafi zata kasance *Matar Haidar,* kasa juyowa tayi idon ta na kawo hawaye bana komai bane sai na godiya ga Allah, Yaa Aliyu da yake kallon ta shima wai abun ne ke masa yawo da gaske dai Maryam ce zata kasance matar sa, ya rasa Maryam wata Maryam din mai irin halin ta ta kara shigowa rayuwar sa, har ta kara zama matar sa ya kara zama Mijin Maryam kenan.

Ya juya ya fita ta fada saman gado tana mai lumshe idon ta, a falo suka hadu da Ammi zaune ita da Aisha wata kunya yaji ya rasa yaya zaiyi da kyar ya karasa ya gaishe da Ammi sannan ya fice yana sunne kai. Ahmad ya gani da Rukky suna ta hira ya wuce bangaren su Ummi yai musu sai da safe ya fito ya kara ganin su suka sallama ya fita.


Aisha na ganin fitar sa ta shiga dakin ganin Maryam a kwance ta daka mata duka tace
"Kin gama soyayya shine kika kwanta kina wani lumlumshe ido ki tashi ki bishi in bukatar sa kike mana."

Ido ta zaro tana fadin
"Ni ba zaki lalatani ba wallahi."
Ta mike tai bandaki bata jima ba ta fito daure da towel, Aisha tace
"Uhmm har wanka ya sakaki."

Kamar zatai kuka ta juyo tace
"Dan Allah ki bari ni wallahi ba ruwa na kunya nake ji."
"Zama ki ji kunya ne ke da idon ki yake fes tin ba yanzu ba."

"Allah ya sakan wancan lokacin duk yarinta ce ban san komai ba."
"Yanzu fa?"

Banza tai mata, Aisha tace
" 'Kya yi shiru ma kun gama tsots...."
"Wallahi ba abinda mukai magana fa mukai akan Yaa Ahmad."

'Me ya faru dashi?"
"Kinsan yazo ne wai yana so na."
"Ina? *Matar Haidar* ai sai Yaa Haidar din."

Baki Maryam ta tabe, Aisha tace
"Ni sai naga kamar bakya son sa."
"In ni ina son sa shi yana so na?"

"Ke macece tinda bai nuna rashin 'kin ki ba yana so kenan, ke zaki kara karkato da hankalin sa."
Rigar bacci ta saka tazo ta zauna tace
"Aisha nima fa ina son sa, ban kara sanin haka ba sai kwanan nan."

Nan ta bata labarin dukka rayuwar su, sai da ta gama Aisha ta saki buda tana fadin
"Malama shi fa yana son ki kema kawai ki bada kai bori ya hau, kin yi dace kin rasa Yaa Haidar kin samu wani Yaa Haidar din in their structure they look alike behavoiur din ne dai, but shima wannan naga da ya shigo hannu zaki saisaita shi dan shi naga yana da dan tsare gida ne ba kamar Yaa Haidar ba, amman ni dadin da naji shima yana son ki ga yadda yake son Haidar kinga kuwa ai ki godewa Allah."

"Amman kuma fa yana da yan mata."
"Son su yake?"

Kai ta girgiza Aisha tace
"Ke zaki kara hanashi son nasu tinda yana son ki."
"Ki bar cewa yana sona Yaa Aliyun?"

"Yes."
"Uhmm."

Rukky ce ta shigo ta fada saman gadon tana fadin
"Shine kika gudu kika barni ko? Kin taho soyayya."
"Kada tayi?"
Aisha ta fada.

"Ah ni na isa na ce, Allah taimaka ni da so nake da kin sauke da wata shida itama ta sauke."
Filo Maryam ta jefa mata tace
"Sai dai mu sauke tare."

"Kamar ya?"
"Zan jira har ki aure sai mu samu tare mu haife tare."

"Kaji muguwar mata ko hutawa da cin amarci ban ba, a'ah na dai barki miki, ranar sunan ki na fara laulayin dai."
"Ah da wa zamu sha ne?"

"Tukkuna ni mazan ne tsoro suke bani ku dai kun dace Allah ya samu a danshin ku."
"Amin, Allah zai baki miji na gari insha Allah."

"Allah ya yadda."
Daga haka suka cigaba da hirar su har wajen sha biyu, wayar Maryam ita ta katse musu hirar ta janyo yana fadin
"Waye da wannan daren?"

Ta dauka sai taga number Yaa Haidar, dauka tayi ta kai kunnen ta tana yin sallama. Ya amsa cikin muryar sa mai dadin sauraro ido ta lumshe yace
"Baki bacci ba?"

Ido ta bude tace
"Eh muna hirar yaushe gamo."
"Jiyama haka kuka kwana kenan."

"Uhmm."
"Kina son ki ciwon kai?"

"A'ah to maza yanzu aje a kwanta gobe a karasa kinji?"
"To yaya sai da safe."

"Yauwah kije kiyi alwala ki kwanta tare da addu'a."
"Insha Allah gud nyt."

"Have a nice dream."
Ta kashe wayar.


*
Washe gari da yamma tana daki, sai ga kiran Yaa Ahmad nan dauka tayi cikin sanyin jiki, yace
"Nazo ne Matar Haidar, kizo muyi magana akan kawar ki."
" 'Kawata wacce?"

"Wacce kuwa banda Rukayya."
"Me ya faru?"

"Tin da ban samu matar Haidar ba ai sai na koma ga 'kawar Matar Haidar ko? kila wasu daga cikin halaiyar tasu ya zama iri daya."
"Kai amman naji dadi sosai. Ina zuwa gani nan."

Ta kashe wayar har ta mike kuma ta koma ta zauna, wayar ta ta dauka ta fara kiran layin Yaa Haidar, har ta katse ba a dauka ba zata kara kira sai ga kiran shi nan, dauka tayi ta kai kunne tare da sallama. Muryar sa mai sanyi ta daki kunnen ta, ido ta lumshe yace
"Ya kike?"
"Ina yini Yaya?"

"Lafiya lou."
"Uhmm Yaya daman.. Daman Yaa Ahmad ne yazo yace yana son ya ganni, shine nace bari na fada maka naje?"

"Me zai miki?"
"Akan maganar wai 'kawata ce."

"Maryam ki sa hijab kuma ban yadda da murmushi ba, minti biyar na baku yanzu zan fito."
"Nagode Yaya."

*Please Read*
_Dan Allah mai son abu a waje na, ko mai son min magana, da yayi sallama ya rubuta abinda yake so wanda ina gani in da hali na bashi amsa ba sai kayi sallama na baka amsa ba sannan a kara gaisuwa, sannan ace kuma za a fadi abinda ake so, please da kayi sallama da gaisuwa fadi abinda kake so kai tsaye, abubuwa da yawa in nace haka za ana tafiya abun da yawa ba za akai inda ake so ba daga haka kuma sai ace anyi wulakanci, bama yan facebook please ku gyara 😀 nagode_




Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono).
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji.
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606




*Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Allah ya yafe mana. Amin.*


*Antty*💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 78

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Dis page is ur Amina Yar'adua i really appreciate with all ur comment keep it up. I heart you Mamanah*


Ya kashe wayar tabi wayar da kallo sai ta mike, hijab ta saka har kasa sannan ta fice daga dakin, a compound ta same shi ta karasa tana fadin
"Ina yini Yaa Ahmad?"

"Lafiya lou, ya gida ina My son?"
"Yana can wajen su Ummi ina jin."

Sukai shiru sai kuma ya dago ya dan kalle ta yace
"A baya naso na maye gurbin aboki na amman Allah bai nufa ba, Allah ya karasa kin tabbata a matar Haidar din ba abinda zance sai fatan alheri."

Kan ta a kasa tace
"Nagode Yaa Ahmad."
Yayi mata murmushi
"Babu wata godiya mata zaki bani kawai."

Itama tayi murmushin tace
"Wacece nai alkawarin ni kuma Insha Allahu."
Yai murmushi yace
"Shi nazo na fada miki amman ina neman wata afarma."

Kai ta gyada yace
"Ina so ki dauken tamkar Alkasim wanda in kina bukatar taimako ko wani abu direct zaki fada min ni kuma zan ji dadi fiye da yadda zaki zato, kuma ina son ana bani Haidar yana zuwa gidana hutu."

"Insha Allahu Yaa Ahmad, Haidar kuma d'an ka ne."
"Haka ne sai batu na biyu."

Kai ta gyada yace
" 'Kawar ki nake so Maryam, a jiya na fara jin wani abu game da ita, ta kwanta min itama tana da sanyin hali kamar naki, ina fatan zaki tayani mika kokon barata, a gida an damen da batun aure ina ta dojewa dan ina sa ran dawowar ki to yanzu kin dawo a matsayin Matar aure kin ga dole nima na nemi mata ko?"

"Haka ne Yaya duk da mun jima ba tare ba amman har yanzu Rukkaya na nan a yadda na san ta, tana da sanyin hali da hakuri, tabbas kun dace da juna ba tin yau ba nake maka sha'awar ta, ashe dai da rabon, Allah nagode maka, Yaa Alkasim ya auri Aisha kai kuma Rukayya, nice dai na rasa Yaa Haidar, ko da yake nima ban rasa shi ba tinda ga wani Yaa Haidar din."
Tai magana hawaye na taruwa a idon ta sai yaji tausayin ta kai ya dauke yace
"Zan tafi yaushe zaku koma?"

"Jibi!"
"Ok zan zo muyi sallama gobe, ki turon number Rukuyyan."
Kai ta gyada ta juya kenan Yaa Haidar ya karaso kusan cin karo sukai ta dago da sauri, idon ta dake cike da hawaye ta dago suna kallon juna, gefen sa tabi tayi cikin gida ya karasa wajen Yaa Ahmad suka gaisa yace
"Ai ban san da aure a tsakanin ku ba sai jiya, ina maka fatan alheri da fatan Allah ya kawo zuria ta gari, muna godiya da dawainiyya Allah saka da gidan aljanna."

"Amin Amin Ahmad."
Ya saki hannun sa yabi bayan Maryam dan duk hankalin sa na kan ta, yana shiga falo ba kowa dakin ta ya nufa direct, yana shiga ya same ta kwance akan gado ko hijab din ta bata cire ba, karasawa yayi ya zauna a gefen gadon yana dago ta gaba daya, a zabure ta dago ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya, a jikin sa ya matse ta yana fadin
"Menene?"

Kai ta hau girgizawa yace
"Fada min sirrin zuciyar ki."
Kin magana tayi, yasa hannun sa ya dago kanta, ta runtsa idon ta yace
"Ni dai na gaji wallahi dan Allah fada min abinda na jima ina gani a cikin idon ki."

Da sauri ta bude idon ta tana son taji me ya jima da gani a cikin su, ganin Maryam na son raina masa hankali yasa ya sake ta tare da fuskantar ta, hannun ta dukka biyun ya kamo ya rike ya dago fuskar ta ya saita da tashi yace
"Ki tsaya a haka."

Kallon sa take, ya kalle ta shima yace
"Akwai shekarun baya da zan tafi na fada miki komai akan ina karantar mutum, to saboda me ba zan karanci ma wacce nake so ba, a lokacin na so ki sanar dani sirrin zuciyar ki, amman kika ki, har kika yaudari yaron mutane, dan nasan ba son sa kike ba kin amshi shi ne kawai a rashi na, wanda naso nai wauta da na kasa fada miki sirrin zuciyata har wani yaso ya dauken ke, ni dake mun so muyi zurfin ciki, amman Allah ya kaddara cewa ke din Matar Haidar ce, in tambaye ki da kin aure shi yaya zakiyi da soyayya ta?"

Idon ta lumshe yace
"Fada min."
"Yadda zakaji haka zanji koma naji fiye da nakan."

"Kinsan da cewa ina sonki?"
Kai ta sunkuyar ya saka hannun sa ya dago kan nata yace
"Kin sani?"

Kai ta girgiza yace
"Karya kike Maryam, yadda nake mu'amalantar ki kadai zaki kawo akwai wani abu a kasa, kawai dai ke sai kin wahalar dani ko?"

Fuska ta kawar tace
"Aah."
"Gashi nan, kinsa sai wahala nake, shakara fiye da bakwai ina dawainiyya da son ki, na sha wahala akan sonki."

"Meyasa kaki ka fada min?"
Ido ya lumshe yana fadin
"Ban gama yadda da so bane a baya na zata tausayi ne dan tin da na fara ganin ki wani abu ya darsu a zuciya ta, ba wata soyayya mukai da matata kan ta rasu ba kafin aure sai da mukai aure nake matukar son ta bansan haka son yake ba, kin bani wahala Maryam a ko da yaushe da sonki nake kwana dashi nake tashi."

"Kai Yaa Haidar amman kake guje min in nazo waje ka bar wajen ko makamantansu."
"Hmmm so kike kisan sirrin komai dai ko, to zan fada miki amman kema sai kin fada min naki sirrin zuciyar.
Na fara gujewa haduwa dake bayan kin haifi Haidar dan a lokacin ko ganin ki nayi kasa bacci nake, nai ta mafarkanki da wasu sigogi kike zuwar min na rasa kwanciyyar hankali, ki tadan bukata ki tadan hankali, sai nai kwana biyu bana cikin nutsuwa ta ba abinda nake so sai kasancewa dake, duk lokacin da muka samu body content ko na taba hannun ki ni kadai nasan halin da nake ciki wannan yasa nake gudarwa ganin ki, amman daga baya ba wanda yafi ni son ganin ki, har ta window nake labewa na hango ki daga bangaren Inna ko na biki can, ke shaidace akan zuwan da kikai gidan Sitti kasa jurewa nake ina miki wani irin so da bansan yawan sa ba, ban taba jin son abu kamar yadda nake son ki ba. Kece buri na kuma Alhamdulillah sai gashi na same ki."

"Ka kusa kai asara."
"Ko muyi dai gaba dayan mu, nayi shiru na mi'ka komai ga Allah ne nasan shi zai iya min kuma gashi yayi min."

Ido ta lumshe hawaye na zubo mata ya janyo ta ya rumgume wanda sukaji wani sanyi gaba dayan su, yace
"Ki bar kukan nan."

Ajiyar zuciya ta sauke yace
"Tin yaushe kika fara so na?"
Kai ta girgiza tana fadin
"Na zata ba son ka nake ba, na zata kawai dan kana kyautata min da Haidar ne, tabbas nayi soyayya da Yaa Muhammad amman gaba d'aya hankali na da tunani na suna wajen ka, sai dai kai na kasa gane inda ka dosa...."

Tai shiru, kanta ya dago tai saurin runtse idon ta, kallon kyakyawar fuskar ta ya tsaya yi, wacce take dauke da dogon siririn hancin ta, sai mayan idanu da madaidaicin bakin ta wanda yake pink kala, daura idon sa akan lips din ta yasa yaji wani iri a jikin sa ba abinda yake sha'awa sai yin kiss bai san lokacin da ya matsar da fuskar sa zuwa fuskar ta ba, batai aune ba sai jin numfashin sa mai kamshi tayi na dukan fuskar ta da sauri ta bude ido dai dai lokacin da ya bawa bakin ta wani kiss wanda Maryam ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da wacce ta manta da ita a rayuwar ta, abubuwa da yawa ke yawo a kwanyarta, zuciya da jikinta, Yaa Aliyu a wannan lokacin wanda shi kansa ya kasa sanin a ina yake, ya kasa daina sumbatar ta kuma ya kasa rabata da jikinsa.

Gaba daya sun manta a inda suke in banda kissing nata ba abinda yake, a hankali ta bude idon ta wanda ta hango Aisha na fita a dakin, wannan yasa ta tina a inda suke ta fara kokarin janye jikin ta amman sam Aliyu bai san ma tana yi ba, hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma kokarin janye jikinta, amman ya hanata kan ta ya fara kokarin dagowa, yana dagowa takai tafukan hannunta ta rufe fuskarta.

Murmushi ya saki ya kai bakin sa yana mata rada a kunne, da sauri ta fara jujjuya kai tana rufe kunnen ta da hannayen ta, mikewa yayi yana kallon ta, ita kuwa fadawa tayi saman gadon tana rufe fuskar ta da filo, dan bata taba yadda Yaa Aliyu ne yai kissing nata ba, Yayan ta, wannan abun ya bata kunya.

"In dawo ne?"
Ya fada yana rakwafowa, da sauri ta girgiza kai, yana murmushi ya fita a dakin, ita kuwa kunya ta hanata ta fita a dakin tasan yanzu Aisha zata sata a gaba, Allah yaso da ya fita ba kowa a falo, dan Aisha kitchen ta shiga tana ganin fitar sa tai murmushi tana mai jin dadi ko ba komai tasan Yaa Aliyu zai maye gurbin Yaa Haidar a wajen Maryam dan shima ta ga yana son ta gashi yana da qaulities din da duk za a so mutum dashi. Sai da ta gama abinda zatai sannan ta nufi dakin da Maryam take, kwance ta same ta ta zauna tana fadin
"Bacci kike ne?"

Mikewa tayi tana kallon ta, Aisha tai murmushi tace
'Menene kike kallo nane?"
Mikewa tayi ta shige bandaki dan bata so Aisha ta sata a gaba, wanka tayo sannan ta fito Aisha ta bita da kallo, kai ta dauke ta fara shafa mai ta saka kaya ta kalle ta tace
"Kiran sallah dai ake kin zauna kin sani gaba kamar TV."

"Amarya Matar yaa Haidar."
Dan hararar ta tayi ta hau kan sallaya dan yin sallah, Aisha kuma ta shige bandaki dan dauro alwala.


*
Da dare, Aisha ta tafi sashen ta ita da Yaa Alkasim, Haidar ma ranar yana wajen Ummi, Ammi ta tafi sashen Abbi, ita kadai ce a dakin ta kwance ta kasa bacci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki, wani irin feeling take ji, dan in ta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaa Haidar tsigar jikin ta tashi take yi, tana cikin wannan halin, wayarta ta fara kara, dan tsaki ta saki dan bata san waye zai dame ta ba, har ta katse bata dauka ba wani kiran ya sake shigo, jin kiran ya isheta sai ta mika hannu ta dauko wayar ta saka a kunnen ta ba tare da ta duba me kiran ba.
"Bacci kike?"
Ya fada cikin muryar sa mai dadi da sanyi.

A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu, saboda wani sanyi da taji, kan tai magana yace
"Na kasa baccin ni amman ke kina ta baccin ki ko?"

Da kyar ta iya cewa
"Eh"
"Anya kuwa? Fada min gaskiya ba boye boye tsakanin mu uhmmm."

Ido ta lumshe tai shiru kawai, yace
"Ni gani tunanin ki ya hanani bacci ke kuma kina ta bacci ko? To hira na kira muyi."
“Hira Yaya nifa bacci zan yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka?"

Wani murmushi ya saki mai sauti yace
"Wannan lokacin yafi dadi ga ma'aurata Maryam."
Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce,
"Uhmm ki min hira wacce miji da mata suke yi ko na samu sassauci."

Shiru ta karayi, ya lumshe ido yace
“Maryam haka zamu yi da ke ko?”
Shirun ta karayi ya mike zaune yace
“Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Ammi ba za ta ki hanani ba."

Shiru tayi dan ta rasa me zata ce, wayar ya kashe tabi wayar da kallo, baki ta tabe ta mike ta cire kayan jikin ta da ta kasa cirewa tin dazu take juyi akan gado, doguwar riga ta saka iya gwiwa ta saka hula akan ta sannan ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito, dagowar da zata taga mutum tsaye a jikin kofa gaban ta ne ya yanke ya fadi, ta sunkuyar da kanta kasa. A hankali ya karaso sanye yake da kayan bacci wando da riga farare tas, wanda suke cotton masu laushi, karasawa yayi inda take tsaye yana binta da wani kallo, hannun sa na dama ya mika mata yace
“Zo mu yi hirar!”

Jikinta na makyarkyata ta ce,
“Ni bacci nake ji”
“Tunda na kasa kema ba za ki yi

Please Login or Register in order to submit comment