Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma kokarin janye jikinta, amman ya hanata kan ta ya fara kokarin dagowa, yana dagowa takai tafukan hannunta ta rufe fuskarta.

Murmushi ya saki ya kai bakin sa yana mata rada a kunne, da sauri ta fara jujjuya kai tana rufe kunnen ta da hannayen ta, mikewa yayi yana kallon ta, ita kuwa fadawa tayi saman gadon tana rufe fuskar ta da filo, dan bata taba yadda Yaa Aliyu ne yai kissing nata ba, Yayan ta, wannan abun ya bata kunya.

"In dawo ne?"
Ya fada yana rakwafowa, da sauri ta girgiza kai, yana murmushi ya fita a dakin, ita kuwa kunya ta hanata ta fita a dakin tasan yanzu Aisha zata sata a gaba, Allah yaso da ya fita ba kowa a falo, dan Aisha kitchen ta shiga tana ganin fitar sa tai murmushi tana mai jin dadi ko ba komai tasan Yaa Aliyu zai maye gurbin Yaa Haidar a wajen Maryam dan shima ta ga yana son ta gashi yana da qaulities din da duk za a so mutum dashi. Sai da ta gama abinda zatai sannan ta nufi dakin da Maryam take, kwance ta same ta ta zauna tana fadin
"Bacci kike ne?"

Mikewa tayi tana kallon ta, Aisha tai murmushi tace
'Menene kike kallo nane?"
Mikewa tayi ta shige bandaki dan bata so Aisha ta sata a gaba, wanka tayo sannan ta fito Aisha ta bita da kallo, kai ta dauke ta fara shafa mai ta saka kaya ta kalle ta tace
"Kiran sallah dai ake kin zauna kin sani gaba kamar TV."

"Amarya Matar yaa Haidar."
Dan hararar ta tayi ta hau kan sallaya dan yin sallah, Aisha kuma ta shige bandaki dan dauro alwala.


*
Da dare, Aisha ta tafi sashen ta ita da Yaa Alkasim, Haidar ma ranar yana wajen Ummi, Ammi ta tafi sashen Abbi, ita kadai ce a dakin ta kwance ta kasa bacci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki, wani irin feeling take ji, dan in ta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaa Haidar tsigar jikin ta tashi take yi, tana cikin wannan halin, wayarta ta fara kara, dan tsaki ta saki dan bata san waye zai dame ta ba, har ta katse bata dauka ba wani kiran ya sake shigo, jin kiran ya isheta sai ta mika hannu ta dauko wayar ta saka a kunnen ta ba tare da ta duba me kiran ba.
"Bacci kike?"
Ya fada cikin muryar sa mai dadi da sanyi.

A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu, saboda wani sanyi da taji, kan tai magana yace
"Na kasa baccin ni amman ke kina ta baccin ki ko?"

Da kyar ta iya cewa
"Eh"
"Anya kuwa? Fada min gaskiya ba boye boye tsakanin mu uhmmm."

Ido ta lumshe tai shiru kawai, yace
"Ni gani tunanin ki ya hanani bacci ke kuma kina ta bacci ko? To hira na kira muyi."
“Hira Yaya nifa bacci zan yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka?"

Wani murmushi ya saki mai sauti yace
"Wannan lokacin yafi dadi ga ma'aurata Maryam."
Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce,
"Uhmm ki min hira wacce miji da mata suke yi ko na samu sassauci."

Shiru ta karayi, ya lumshe ido yace
“Maryam haka zamu yi da ke ko?”
Shirun ta karayi ya mike zaune yace
“Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Ammi ba za ta ki hanani ba."

Shiru tayi dan ta rasa me zata ce, wayar ya kashe tabi wayar da kallo, baki ta tabe ta mike ta cire kayan jikin ta da ta kasa cirewa tin dazu take juyi akan gado, doguwar riga ta saka iya gwiwa ta saka hula akan ta sannan ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito, dagowar da zata taga mutum tsaye a jikin kofa gaban ta ne ya yanke ya fadi, ta sunkuyar da kanta kasa. A hankali ya karaso sanye yake da kayan bacci wando da riga farare tas, wanda suke cotton masu laushi, karasawa yayi inda take tsaye yana binta da wani kallo, hannun sa na dama ya mika mata yace
“Zo mu yi hirar!”

Jikinta na makyarkyata ta ce,
“Ni bacci nake ji”
“Tunda na kasa kema ba za ki yi ba”

“Yaya don Allah ka zo ka tafi, kada Ammi ta fito, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka. Cewa zatai ni nake kai kaina wajen maza.”
Dan murmushi yayi yace
"Ai da aure in ma kinbi."
Kafada ta make abin sai ya bashi dariya ma, Maryam kuwa gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto.

A tausashe ya ce,
“Zan tafi, but on one condition....”
Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata.

“I only want to kiss you again! matata don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!”



Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606




*Allah yai mana rahna, Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*

.

*Antty*
[12/9, 18:20] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 80

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Ido ta zaro tana mai girgiza kai kamar zatai kuka tace
"Ni dai dan Allah Yaya kayi hakuri Allah ba zan iya ba."
Mikewa yayi batai aune ba sai jin tayi ya dauke ta gaba dayan ta da sauri ta fara kokarin sauka amman yadda ya rumgume ta a kirjin sa yasa ta hakura sai hannun ta da ta zuro ta wuyan sa, tana fadin
"Dan Allah Yaya kayi hakuri ni wallahi kunya nake ji dan Allah ka sauke ni."

"In baki min shiru ba har dakin Ummi zamu a haka."
Take tai dif kamar ruwa ya cinye ta a haka suka shiga falon, Allah yaso ba kowa har wata ajiyar zuciya ta sauke zasu shiga dakin kenan Ummi ta fito daga kitchen basu ganta ba dan sun juya mata baya, ita ce ta gansu kai kawai ta girgiza tana mai addu'a Allah ya tabbatar da alherin sa yasa Aliyu yaso ta su zauna lafiya ya basu zuri'a ta gari.

Har bedroom ya shiga da ita ya ajiye ta, akan gado matsawa tayi karshen gado tana takurewa ya karasa wajen kofa ya saka key sannan ya shige bandaki, sai da ya dauki wajen minti ashirin sannan ya fito sanye da armless riga da three quarter sai zuba kamshi yake, kayan sun masa kyau, wajen ta ya karaso ya zauna a gefen ta ya dagata ya daura akan kafar sa, motsu motsu ta fara dan duk ta kasa sakewa, kanta ya dago yana kallonta, ido ta lumshe sai ga hawaye na zuba a idon ta, harshen sa yasa yana share mata su yanayi wasu na zubowa, a hankali yace
"Menene?"
"Dan Allah Yaya ka bari kar Inna taje taga bana nan tazo kuma taga bana nan."

"Naga matata ce."
"Dan Allah ka bari Yaya ai ban tare ba."

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Kin fiso na kwana ina fushi dake."
Jikin sa ta shige tana girgiza kai, yace
"To ki shiru ni ba abinda zan miki kawai ina son na kwana a jikin matata ok?"

Ido kawai ta lumshe ya kwantar da ita ya tashi ya kashe fitila tana ji ya hawo gadon ya jata jikin sa, rumgume ta kawai yayi yana cusa kan sa a wuyan ta a haka sukai baccin dan ya ga duk ta takura taki sakewa, sai asuba suka tashi, ya shiga bandaki, kan ya fito ta fice ta bar masa dakin, sama ta wuce da sauri ta shiga dakin Haidar karami acan tai wanka tai alwala tai sallah. Sai karfe bakwai ta fita ta gaishe da su Ummi sannan ta koma dakin Inna.

Rukayya ta sama tana ta baccin ta, Inna kuwa na kitchen tana ta hada kayan karyawa a falo ta zauna tana sauraron azkar din da ake yi a TV, idon ta a lumshe bataji shigowar sa ba sai kamshin turaren sa da taji tana bude idon ta ta ganshi durkushe a gaban ta, zama ta gyara tace
"Ina kwana Yaya?"

Ido ya lumshe ya bude a hankali yace
"Matar Haidar ta gudu ta bar mijin ta ko?"
Kai ta girgiza ya dan saki murmushi dai dai fitowar Inna da tray ta ajiye, tace
'Menene haka nake gani?"

Fuska Aliyu ya hade ya koma ya zauna, baki Inna ta tabe tace
"Kazo zaka takurawa yar mutane me ya kawo ka sashe na da sassafen nan?"

"Wajen Matata nazo."
"To ba a sashe na ba tashi ka fitar min tinda ka zama marar kunya."

"Sai na ciyar da ita tukkuna Inna kawo na bata taci ta koshi sai kici sauran ta."
"Tinda Aisha ce ta girkan ba, Ja'iri."
Ta shiga ta fito da kayan ta shiga daki dan taso Rukayya tea ya hada mata mai kauri dan sosai yaiwa Inna ta'adin madara ya debi dankalin da ta suya da pepper soup ya zuba a bowl ya kalli Maryam yace
"Sauko kici."

"Dan Allah Yaya ka tafi ni zanci da kaina."
"Da yawa?"
Yai mata tambayar yana binta da wani kallo wanda yasa duk jikin ta yai sanyi. Kai ta gyada yace
"To shikenan."

Ya mike har ya kai kofa tace
"Yaya kai fa?"
"Ni me?"

"Abincin?"
Ta fada tana sunkuyar da kanta, yai murmushi yace
"To an damu in ci ne?"

Kai ta gyada, ya doshi kofar yana fadin
"In an damu naci azo a bani."
Murmushi kawai tayi Inna da Rukky suka fito, tare suka karya bayan sun gama suka shiga kitchen suka wanke kwanukan, suna kitchen suka jiyo sallamar Najwa tana fadin
"Amaryar Yaya."

Inna tace
"Wacce irin Amaryar Yaya, Antyn ki."
Maryam ta fito tana fadin
"Ai kuwa dai."

Suka zauna, tace
"Mutanen Kano, kinga yadda kikai kara kyau."
Rukky ce ta fito Najwa tace
"Wannan ce Rukky ko?"

Kai ta gyada suka gaisa tace
"Kinga tashi zaki muje a dan gyara ki ai amarya ba ta tafi ba dan lalle bare gyaran kai ba ko?"
Inna tace
"Yauwah yar gari, ga mijin nata naga ya zama bita zai zai."

Sukai murmushi, Maryam ta sunkuyar da kai, Najwa tace
'Bari naje wajen su Yaya Fadima ki shirya dan naji Ummi na fadin yau zaki tare gwara muje mu shirya da wuri ko?"
Ta mike ta fita, Maryam ta nufi sashen Ummi, wanka ta sake sannan ta saka doguwar riga tai rolling din mayafi ta fito falo, zasu fita kenan Yaa Aliyu ya shigo gidan da kallo ya bita zata shiga mota wani horn ya danna da yasa duk suka tsaya da abinda suke, bai fito ba ya kure ta da ido, Najwa tace
"Alhaji Yaya mulki, to kije kiji."

"Ai Yaya wallahi ya fiya rigima."
"Je ki dai jiran ki yake."

Kofa ta saki ta juya ta nufi wajen sa ta inda yake ta tsaya da yake tint ne yana ganin ta amman ita bata ganin sa, baki ta dan turo dan yaki sauke glass din, kofar dayan side din ya bude zagayawa tai ta shiga, zaune ta ganshi cikin shiga ta wandon jeans da riga orange kala tai masa kyau sai tashin kamshi yake, kallo ya kafe ta dashi, ta dago tace
"Yaya."

Zama ya gyara, baki ta dan kara turowa tace
"Yaya fita fa zamuyi na barsu suna jira na."
"Da izinin wa?"

Ya fada yana duba agogon azurfan dake hannun sa.
"Haba Yaya yau kadai fa."
"Me din?"

Kai tayi kasa dashi yace
"Kalli a yadda kika fito sai kace ba matar aure ba salon ki fita maza suna tsayar dake ko?"
"Haba dai Yaya ko a da bana tsayawa bare yanzu."

"Abinda bana so din kenan ai wani ya kallen min ke."
"To kayi hakuri."

"Ina ma zaku?"
"Uhmm Najwa ce ta matsa wai sai munje lalle."

"Kace ni za ai wa gyara."
Kai ta gyada yace
"Ok yanzu kije ki sako hijab da nikaf kinji?"

Kai ta gyada ta fita, ciki ta koma bata jima ba ta fito sanye da hijab da nikaf ta karaso tace
"Nayi?"
"Sosai ma kuwa."

Ya dauki wayar sa ya danyi dane dane yace
"To sai kun dawo ko nazo na kaiki?"

"A'ah zamu tafi kawai."
Taji karar shigowar sako dubawa tayi sai taga kudi yai mata transfer, dagowa tai yace
"Aje ai lallen dasu sai anjima in mun hadu a gdan mu."
Ya fada yana kanne mata ido da sauri ta bar wajen ta nufi wajen su Najwa suka bar gidan.

Tin da sukaje ake gyara ta, aka gyara mata fata, kafar ta da hannu sannan aka gyara kanta akai mata lalle, sosai tai kyau fuskar ta ta kara wani kyau tai fresh.

Sai biyar da wani abu suka dawo, suna shigowa abinci sukaci Ummi tace ta shiga tai wanka, da kanta ta hada mata wani ruwan turare ta shiga tayi, tana fitowa ta bata wani turaren ta shafe jikin ta sannan ta turare jikin ta take wani kamshi mai dadi ya hau tashi a jikin ta.


*
Sai da tayi sallah sannan Ummi ta shigo ta kamata suka fita, mayafi ne rufe a kanta inda take sanye da wata farar atamfa da akai ado da ja da blue atamfar tai kyau ta yafa farin mayafi ta saka flat white shoe, duk inda ta gifta kamshi ne ke tashi, a haka suka karasa bangaren Inna, wacce tai mata bankwana da karai mata nasiha da saka mata albarka, wajen Mami aka kai ta itama tai mata nasiha sannan Mama ma tace
"Allah bada zaman lafiya."

Wanda daga Maryam har Ummi mamakin canjawar Maman suke, daga nan suka fito suka shiga wata hadadiyar mota wacce Yaa Farouk ke driving, gida ne babba mai kyau tun daga waje ga filawoyi sun fito ta saman katanga. Gidan sai kamshi yake tin daga compound zaka san gidan amarya ne dan yadda kamshi yake tashi, wanda tin safe su Yaya Ummulkairi ke aikin kintsa gidan dan sai da suka gyara jeren da akai dan an kwaso kayan duk kayan da aka kai gidan Muhammad, bangaren Maryam kawai aka zubawa kayan dan bangaren Aliyu akwai kayan sa dan dawowar sa a canja su, sai da suka wuce falo har biyu sannan aka dangana da ita ga dakin ta, wanda ba karamin kokari Ummi da Abba sukai ba, ba karamin kudi suka kashe mata ba yan uwan ta duk sunji dadin wannan soyayyar da su Ummi kewa yar tasu wannan yasa suka kara basu wani matsayi.

Daga nan aka wuce da ita dakint baccin, wanda sima ya hadu sosai, kanta a rufe yake tana hawaye har aka zaunar da ita a bakin gado. Yan uwan ta suka karai mata nasiha sannan sukai mata ban kwana suka tafi.

Bayan tafiyarsu daga ita sai su Rukky, Najwa, da Aisha wanda daga baya falo suka sauko dawo, wajen karfe takwas sukaji an bude gate, wanda sai gaban Maryam ya fadi, tsoro fargaba ya kamata yau gata a gidan auren ta a karo na biyu, waccan karan da ango bai shigo gidan nasa ba, wannan karon ma sai tsoro ya kamata kada abinda ya faru waccan karan ya sake faruwa, ido ta runtse tana jiran taji me zai faru.

Sallamar sa taji cikin muryar sa mai dadi da sanyi, Yaa Farouk biye dashi da Yaa Abubakar wanda yake aboki ga Yaa Aliyu, sai Yaa Alkasim amsawa sukai suka shiga, Yaa Farouk ya ajiye ledojin hannun sa, tana ji Yaa Haidar ya zauna a gefen ta, bayan sun gaisa Yaa Abubakar yai nasiha sosai sannan ya rufe da musu addua.

Tin sallamar Yaa Haidar bata karajin bakin sa ba, har sai da suka gama suka mike zasu tafi ya kalli Najwa yace
"Ina Abdul din?"

"Yaya a gida zan kwana ne."
"Ok sai Farouk ya ajiye ki ke da Rukayya, Alkasim kuma ya dauki Aisha, Abubakar kuma sai ka tafi gida kai tsaye dan ban rike ka ba kada Aunty tace ni na rike mata miji."

Duk sukai murnushi ya mike ya tafi rakasu, tana ji suka fita aka rufe gate sannan ya shigo ya rufe kofar falon, kanta a kasa taji tafiyar sa, tana ji ya karaso inda take wanda kamshin sa ya cika mata hanci, ba tai aune ba taji ya bude mayafinta ya shigo da kansa ciki. Hannu yasa ya tallabo ta ta fado jikin sa, idonta rufe cike da kunya.

A hankali yake mata magana "Kinyi kyau Matar Haidar."
Sake runtse ido tayi tana jin wata irin kunyarsa tana karuwa a zuciyarta. Ya dago kanta tare da matso da bakinsa kusa da nata ga hancinsu yana gugar juna
"Ko na daukeki ne?"

A hankali ta bude ido suka sauka cikin nasa. Murmushi tayi masa wanda yaji gaba daya ta hargitsa masa lissafi. Hannun ta ya kamo ya dago ta, hannun ya kama suka fara tafiya har suka karasa dakin ta sannan ya sake ta yace
"Kiyi alwala kafin na dawo"

Da sauri tayi cikin bandakin ta dauro alwala, ya bita da kallo yana murmushi, bai jima ba ya dawo dakin, sanye da kayan bacci sky blue, riga da wando, sallaya ya dauka ya shimfida masu sannan ya nuna mata kan sallayar mikewa tayi ta tsaya a bayan sa ya tayar da sallah, lokacin da ta fara jin kira'ar sa ido kawai ta lumshe dan har tsigar jikin ta taji tana tashi, yadda yake karatun cikin tajwid yana bawa ko wacce harafi hakkin sa. Raka'a biyu suka yi sai shafai da wutri sannan ya shiga jero addu'a da larabci kamar bazai dena ba. Bayan ya kai karshe suka shafa ya dawo gabanta ya dafa kanta ya sake wata sannan ya tashi tare da kamo hannun ta, falo suka fita, ya dauko ledar da suka shigo da su, kitchen ya shiga ya dauko cup da plate bayan ya wanke ya fito.

"Yau komai yiwa amarya ake ko?"
Shiru tayi tai kasa da kan ta. Ya bude leda ya dauko wani park wanda snacks ne a ciki, meat pie, spring roll, samosa, cake ko wannen an masa column dinsa, sai wata leda da kaza ne a ciki ya dauko ya juye a plate, sai wani pack wanda kayan ciki ne aka musu wani gashi mai ruwa ruwa yaji kayan kamshi dai kamshi yake, sai kalolin lemo da madara da youghurt.

"Bismillah.'
Kai ta girgiza dan ji tayi duk a takure take, murmushi yayi, dago ta yayi daga inda take ya daura ta akan cinyar sa, ya dago kanta yana kallon ta yace
"Yanzu fa na zama mijin ki, sirrin ki majibancin alamuran ki, wanda zan kasance komai naki, bana son wannan kunyar ki ajiye ta gefe ki kula dani kawai, ina son kula ina son soyayya dan haka dole ki ajiye wannan kunyar kinji?"

Ta rausayar da kai gefe guda tana kokarin zillewa.
"Idan bazaki ci ba nima haka nake so kinga sai mu shige daki abun mu akwai abubuwa da yawa a gaban mu."

Baki ta turo tace
"Uhmm zanci mana yunwa nake ji."
"Good girl."

Ya janyo abubuwan tana kan cinyar sa ya dinga bata, sai da taci sosai dan bata wani ci abincin kirki ba tin safe da suka dawo ma lemo kadai ta sha ita ta shiga wanka da shirya.

Bayan sun gama ta mike dan kwashe abubuwan ya mike yace
"Yau ni zan komai."
"A'ah Yaya gani wane aiki zakai kuma."

Ta amsa ta nufi kitchen din wanda yake biye da ita a baya sauran abinda basuci ba ta saka a firij, juyowar da zatai sukai karo ya taro ta a haka suka fito tana jikin sa.

"Sai soyayya ko?"
Ya fada yana kallon idon ta, kanta ta kawar tace
"Nifa bacci nake ji Yaya bari na tafi daki na na kwanta."

"Menene kuma dakin ki, dakin mu dai, ki sani ban yadda da wai dakin ki ko dakina ba komai nawa yanzu ya zama naki kamar yadda komai naki ya zama nawa dan haka daga wancan part din har wannan dukka dakin mune kin gane?"

Kai kawai ta gyada yace
"To yau a wanne zamu kwana?"
Inda aka fara kai ta ta nuna yace
"No zo muje can ki gani.



***
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga mama guyn sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono). Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji. Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata. Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606
***



*Allah mana rahma ya yafe mna, Allah yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*



*Antty*
[12/10, 13:41] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 81

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Hannunta ya kama suka tafi. Ni'imtaccen kamshi da sanyi ne suka doki hancinta. Ba karamin burge ta dakin yayi ba, suna shiga ya saki hannun ta ya shiga bandaki, gefen gado ta zauna yana fitowa ya nufi wardrobe din sa wasu kayan bacci ya fito dasu masu shege kyau akan gado ya ajiye. Dagata yayi yace
"Bari na shirya matata."

Kafada ta make, ganin ta kasa sakewa ya mika mata rigar yace
"Shikenan ki shirya bari na baki waje minti biyu."

Ya fada ya juya ya bar dakin. Rigar ta d'aga ta juya ta kara juyawa, da kyar dai ta saka, ta dauki mayafin ta ta rufe jikin ta.

Yana shigowa yai arba da ita, takure waje daya, dan murmushi ya saki tare da lumshe ido ya karasa ya rumgume ta, hawaye ne suka soma fita daga idon ta saboda tina irin wannan makamanciyyar ranar da ya shude wanda a lokacin baya ta kasance cikin zumudin tarbar Yaa Haidar sai dai Allah bai ba, ranar farin cikin su, a ranar ya koma ga mahallacin sa, hakika duk abinda ya faru da ita jarabawa ce kuma ta sani sau'ki ne a rayuwar ta, da hakan bai faru ba da bata san yadda zatai rayuwa ba Yaa Haidar ba, amman da ta bar gida taje wani waje tai rayuwa ta samu sassauci daga abinda take ji na rashin Yaa Haidar tin da gashi a yau har zuciyar ta ta aminta da wani ta bashi gurbin soyayyar ta, sai dai ta sani ba zata taba mantawa da Yaa Haidar ba kuma ba zata taba daina masa addua ba, take taji zuciyar ta na kara rauni na tuna abubuwa masu yawa, sosai Yaa Haidar ya rude da ganin halin da take ciki, tambayar ta ya hau yi amman sam ta kasa magana sai hawaye dake zuba a idon ta, wata irin rumgume yai mata wacce take nuna tsananin so da kulawa ga abinda ake so, kansa dake wuyanta yana shakar wani kamshi da ya rasa wane iri ne ya gama cika masa ciki, sai furzar sa yake, ya dago yana kai bakin sa dai dai kunnen ta ido ya bude a hankali numfashin na sauka a cikin kunnen nata wanda ya fara haifar mata da wani irin yanayi, ido ta lumshe, kan ya fara magana cikin kunnen nata a hankali yana fadin
"Kin tuna Aliyu ne? Addu'a ya kamata kiyi masa ba kuka ba. Kinji?"

Wani abu taji yana wayo a jikin ta, ido ta runtse hawaye na cigaba da zubowa, tabbas ta tuna Yaa Haidar amman kuma bai kamata a wannan lokacin ba a wannan yanayin da suke ciki, so take tai masa bayani amman ta kasa ta gaza motsa bakin ta ma bare ta fada masa wani abun, ganin yadda take kukan yasa ya kwantar da ita a saman gadon yace
"Am sorry i don't means to hurt you Baby, in barki ki ta begen Yaa Aliyun ko?"

Mikewa tayi ta fada jikin sa tana wani kuka mai tsuma zuciya da tada hankalin mai saurare. Dole tayi kuka a wannan rana ko taji sauki a ranta, a wacan karon taso taga wannan tsayin daren tare da Yaa Haidar sai dai Allah bai ba, duk burin Yaa Haidar na irin wannan daren Allah bai nufa zai gani ba,

Please Login or Register in order to submit comment