Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini, mu dai Allah raba mu dashi ace yaro sai kaji shi da hawan jini ai duniya ta zama abinda ta zama, ina fada miki ga ulcer yaro sai ya hau tsamurewa da kyar da addu'a da rokan Allah, Aliyu yake rayuwa amman da tini shima mun rasa, to fa shikenan tin lokacin ya canja ko magana bai fiya so ba yafi son ya kadai ta abinci kuwa kina ganin sa zandamemen nan sai Aisha ta saka shi a gaba da lallashi, da komai kamar jariri, ai ita dai Aisha yar albarka ce, ta iya riko, kinga yadda ta riki Aliyu kuwa ko uwar sa bata rike shi kamar yadda ta raine shi ba, ita dai tana son yara amman Allah bai bata zaunanne ba, kinga fa haka ta samo mana wani yaro Abubakar wanda na fada miki yana auren yar autata suna can Canada da ya'ya su har hudu, ai Aisha Allah ne kadai zai biya ta, ta kula da Aliyu da matar sa, ke yau suna gidan ta gobe suna gidan su basu da wajen zama tsayayye ita ke dawainiyya da su, ai kuwa itama taji mutuwar haka da rokan Allah fa aka fara samk kan sa, to kinji fa tin rasuwar matar sa ni ban 'kara ganin sa cikin nishadi ba sai haihuwar ki da yadda yake wa yaron ki, dan Allah da iyayen zasu dau tawa ai da an masa aure ko shima zai ga gudan jinin nasa ko? Ace yaro ya girna amman ba aure ga farouk nan ma yana koyi da dan uwan nashi."

Idon Maryam har yayi ja jin labarin Aliyu maikon kwallar dake kwarmin idon ta, ta saka hannu ta goge tana fadin
"Allah mata rahma. Ina rashin masoyi babban damuwa ce ni gani nan na rasa nawa na rasa iyaye na, na kasa sanin kowa nawa sai ku."

Maryam ta fada tana fashewa da kuka. Inna tace
"Haba yar nan ke kuwa kada kiyi kuka wani yazo ya zata wani abu nai miki dan Allah kiyi hakuri, ke kuwa kike da masu son ki, wallahi zan iya rantse miki da Allah ina jin ki tamkar jika ta dan haka ki bar kuka komai kike so ki fada min ni nai miki alkawarin kula dake da miki duk abinda nake so kinji?"

Kai ta gyada tace
"Ban taba haduwa da mutane masu karamci kamar ku ba kun min komai duk da baku sanni ba Allah ya saka muku da gidan aljanna nagode sosai da sosai."

"Ba komai yiwa kai ne kai kasan halin da naka zai fada a ciki? Ki daina kukan to."
Hawaye ta goge Inna ta cigaba da mata hira tana sata dariya har ta dan sake amman abun na damun ta dan labarin Aliyu ya taba mata zuciya.

Fura Inna ta dama musu har da madara da kwakwa Maryam ta saka afirij dan ta dan yi sanyi sannan ta fito tai alwala dan an tada sallah magariba sallah tayi tana zaune tana addu'a har akai isha'i sukai sallah sannan ta mike tace
"Inna zan tafi sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
Har ta kai kofa Inna tace
"Oh zo ki anshi furar ki."
Ta dauko jug Inna ta zuba mata da yawa sukai sallama. Ta fita, ta kusa zuwa sashen Ummi sai ga Farouk nan kallo daya yai mata ya gane tana da damuwa ba kamar dazu da ya ganta ba dan haka ya tsaya kallon ta can kuma yace
"Lafiya dai ko?"

Dagowa tayi dan ita bata san dashi ba. Kai ta dauke tace
"Ba komai."
"To sai da safe."

Suka bar wajen yai bangaren Inna ita kuma tai bangaren su. Tana shiga ta samu Ummi da Aliyu, Haidar a hannun Aliyu yana jijjiga shi, sama tayi Ummi da Aliyu suka bita da kallo Ummi tace
"Lafiya kuma?"

Hannu ya daga alamar 'Waya sani.' Haidar ya kalla yaga yai bacci ya mikawa Ummi yace
"Ummi a kwantar dashi, daga nan kiji me yake damun ta?"

Amsar sa tayi tai sama. Dakin Maryam ta shiga taga bata ciki, motsi taji a toilet ta kwantar da Haidar tare da dauko masa kayan baccin sa ta saka masa ta lullube shi sannan tai masa addu'a zaman jiran fitowar ta tayi. Bata jima ba ta fito daure da towel da hijab a saman kan ta.

Ummi ta kalla ta dan saki murmushi ta nufi doruwa ta dauki kayan baccin ta, ta koma ta saka sannan ta fito hula ta saka akan ta ta nufi gadon tana fadin
"Ummi, Abba bai dawo bane?"

"Ya dawo menene?"
"Na ganki a zaune anan ne."

"To me zanje nai masa?"
Murmushi Maryam ta saki tace
"A'ah ba komai wai nace yaci abinci ne?"

"Yaci nasan yanzu ma ya kwata zauna muyi magana."
Zama tayi a gefen ta Ummi ta kamo hannun ta tace
"A duniya a halin yanzu baki da sama da Haidar to amman Haidar ba zai iya tambayar ki damuwar ki ba, ni din dai nice makusanciyar ki fiye da kowa a yanzu dan haka ki fada min me yake damun ki?"

"Ummi ba komai. Ni ba abinda yake damuna. Me zai damen ina dake?"
"Kin tabbata?"

Kai ta gyada tace
"To Allah ya dafa bari naje na kwanta kiyi addu'a sannan kiyiwa mai gidan nawa."
"To Ummi."


*Allah ya jikan mu ya sa muyi kyakyawan karshe. Amin*


*Antty*
[11/25, 11:27] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 56

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Bayan wata hudu.
Tsaye take a kitchen tana karasa miyar da ta daura, Ummi na gaban sink tana wanke kwanuka, gas din ta rage ta rufe miyar sannan ta tafi wajen Ummi tana fadin
"Ummi nace ki bari na karasa dan Allah!"

Ta dauki kwanon tana dauraye wa. Ummi tace
"Ai na kusa bari kawai na karasa."

Haka suka cigaba dayi Ummi na wankewa Maryam na daurayewa. A haka har suka gaba Maryam ta kwashe ta kai ma'ajiyar, Ummi kuma ta dauraye wajen.

Sallamar Aliyu suka jiyo suka amsa Ummi na fadin
"Mai gida ya dawo."

Ta fita Maryam ta karasa wajen miya ta kashe gas din ta zuba a flask sannan ta dauraye hannun ta. Fita tayi zuwa falo.

Haidar ta gano yana daddafa kujera yana tafiya tare da gwaranci. Aliyu na zaune ya jingina da kujera Ummi na kallon Haidar tana fadin
"Wato Haidar dai ya dage kan ya shekara sai ya taka."

Yana ganin Maryam ya fara daga mata hannu yana fadin
"Ammmmiii Mommmi Annnttti."
Karasowa tai ta dauke shi tana fadin
"Oyoyo yaron Ummi."

Ta dauke shi tare da kallo Aliyu da tin da ta haihu ya daina sakar mata duk wannan kulawar ya daina sai dai Haidar ita daga gaisuwa shikenan. A hankali tace
"Sannu da zuwa Yaa Aliyu!"

"Yauwah!"
Kawai ya fada ba tare da ya kalli inda take ba ya cigaba da danna wayar sa. Ummi dai bata tanka ba itama sai ta cigaba da kallon Haidar dake tai mata gwale gwale shi alallai labari yake bata ita kuma tana ta biye masa can Aliyu ya mike yai daki dukkan su da kallo suka bishi.

Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Zo nan Maryam!"
Mikewa tayi rike da Haidar suka karasa, Ummi tace
"Kada ki damu da halin yayan ki, haka yake wani irin miskili ne ba kasafai aka fi gane abinda yake so ba, amman zan fada miki Aliyu bai son rawar kai sam duk da nasan ke ba ruwan ki, yana son nutsatsen mutum kamar yadda kike bai son hayaniya dan haka please kar ki sa damuwa kinji?"

Murmushi Maryam ta kwakwalo dan sam bata son wannan canjin daga gareshi da safe da rana da dare sai ya dubata da lallashin ta me take so da matsa mata akan abu ko zuwa motsa jiki in tana damuwa yafi kowa damuwa amman yanzu ya canja bai damu da ita ba ko zasuyi kwana nawa bai ganta ba bai damu ba, sam bata son haka amman ya zatayi tinda haka yake zata daure ta daina damuwa insha Allahu. Dagowa tayi ta kalli Ummi tace
"Ba komai Ummi na jima da gane hakan."

"Yauwah Maryama."
Ta mike sukai sama ita da Haidar tana fadin
"Bari nai masa wanka kan ai magariba."



*
8:15pm
Dakin sa ta Shiga da sallama, ya amsa ta Shiga, yana zaune akan carpet gaban sa system Haidar na kan gado gaban sa biskit, alawa da chocolate.

"Ummi!"
Haidar ya fada yana mika mata wata alawa.
"A'ah Haidar kayan zakin nan ai sai ku."

Ta zauna tana fadin
"Shiyasa kake gudowa nan, dan sai abinda kake so kake yi ko?"

Aliyu ya kalli Haidar dake shan alawa, murmushi yayi ya juyo yace
"To Ummi ai gwara abarshi yai abinda yake so ko?"

"Hmmm wajen ka nazo Doctor."
Dagowa yayi yace
"To Ummi lafiya dai ko?"

"Yadda kakewa Maryam kasan bata da kowa sama damu a yanzu dan haka dole mu jata a jiki Dr dole mu sakar mata."
"Ummi ni kuma ke dai amman ni me zan mata kuma? Duk abinda take so ta fadan zan mata insha Allahu."

"Duk da haka nasan kai daman halin ka wani lokacin kana da wuyar sha'ani."
Haidar ne ya sauko ya gangaro yana son ya dauke shi, daukar sa yayi ya amshi chocolate din hannun sa ya bude masa sannan ya mika masa amsa yayi ya saka a bakin sa sai kuma ya fito da ita ya saka a bakin Aliyu ya gutsura ya mikawa Haidar yace
"Sha abinka."

Ummi ya dago ya kalla yace
"Ummi ni ina da shawara akan Maryam."
"Ina jin ka."

"Mai zai hana ta zana jarabawa daga nan mu sama mata addmision dan shine kadai gatan ta a duniya."
"Na jima da yin wannan shawarar amman ganin tana shayawar shiyasa na dakata."

"Haidar bai da matsala, kuma kinga an kusa zana weac ana ta registeration har anyi kan lokacin fara makaranta ta fara ko yaye shine tayi tinda kinga bai fiya damuwa da maman ba."
"To shikenan Allah taimaka yanzu ya za ayi?"

"Gobe zan turo a dauke ta aje ai mata komai."
"Shikenan Allah yayi albarka."

"Amin Ummi."
Ummi ta mike tace
"Haidar ko zamu tafi?"

Aliyu ya kamkame yana shigewa jikin sa. Ummi tace
"Zaka zo ka samen."
Ta fita.



Haka akai ciki hukuncin ubangiji akai mata registeration wanda Aliyu ya dauki mai mata lesson kan a fara exam wata daya da registeration suka fara exam sannan aka saka ta wata isilamiyya dake unguwar da taje akai mata interview komai ta wuce yan makarantar dan haka suka samu Aliyu sukai masa bayani kan cewa da za su same ta a matsayin malama zasuyi murna. Wannan yasa Aliyu ya sanar da Ummi, Ummi ta samu Maryam, Maryam tace ba matsala dan haka ta fara zuwa suka bata aji tana koyar wa.


*
Ranar da zata fara exam da safe Maryam ta fito daga dakin ta shirye cikin goggagun uniform din makarantar da zata zana jarabawa, sakowa tayi daga bene, kitchen ta shiga gun Ummi, Ummi dake juye ruwan shayi a flask ta juyo tace
"Yan makaranta an fito?"

Murmushi tayi tace
"Eh Ummi, nazo na karasa."
"A'ah bari ai na gama."
Ummi ta karasa ta mika mata flask din ta fita dashi dining Ummi ta fito da flask din da ta zuba dankali da kwan da ta suya. Maryam ta hada tea ta zuba dankalin ta ci.

Maryam na gamawa ta kai plate din da cup kitchen, ta dauraye ta samu Ummi a sama ta shiga ta dauki hijab din ta ta fito tace
"Ummi zan tafi."

Ummi dake aiki a system ta dago tace
"Ki duba gaban dressing mirror a daki na akwai duba daya ki dauka."
Dakin ta juya ta shiga ta dauko sannan ta fito tace
"Ummi sai na dawo"

Ummi tace
"Ohk Allah ya tsare kiyi addu'a kafin ki fita, driver na waje."
Fita tayi ta nufi can parking space din Farouk ta gani a jikin motar sa yana worming din ta, tinda ta fito yake bin ta da kallo har ta karaso, kai tai kasa dashi tace
"Ina kwana Yaa Farouk?"

"Kin tashi lafiya yau sai makaranta ko?"
Tai murmushi ta gyada kai."
Driver ne ya karaso ya gaishe da Farouk sannan ya kalli Maryam ya gaishe ta, amman sai taki amsawa ta gaishe shi. Farouk ne yace
"Bari na kai ta, kazo daukar ta."

"Ok ranka ya dade."
Ta kalli farouk zatai magana ya daura mata hannu a kan leben sa yace
"Shiiii!"
Tare da mata nuni da ta zagaya ta shiga. drivern ta kalla tace
"Yaa Aliyu ya baka time table din ai ko?"

"Eh ya bani dazu da zai fita."
"Yauwah sai kazo dauka ta."
Ta karasa ta shiga shima ya shiga ya fitar da mota.

Suna tafe a hanya yana dan jan ta da hira har suka karasa makarantar har cikin school din ya shiga da ita sannan yai parking ya zaro kudi a aljihun sa ya mika mata yana fadin
"Allah bada sa'a."

"Amin."
Ta amsa ba tare da ta amshi kudin hannun sa ba yace
"Ki amsa mana?"

Kai ta girgiza tace
"Ummi fa ta bani."
"Na Ummi daban nawa daban amshi kinji kanwata ba kyau maida hannun kyauta baya."
Amsa tayi da hannu biyu tace
"Nagode!"
Ta rufe kofar ta juya ta nufi wajen wasu dalibai da ta gani dan tambayar exam hall. Tana zuwa ta tambaya daya a cikin su tace
"Muma can zamuje muje."

Suka dunguma suka karasa karfe tara suka shiga kowa ya zauna a sit din sa tara da rabi aka fara raba booklet suka fara exam. Da yake da Biology ce awa biyu aka bayar karfe sha biyu har sun fito. Da motar gida tai tozali ta karasa wajen Driver na gani ya taso ya bude mata ta shiga suka kama hanyar gida.

Ummi na wajen aiki amman har ta gama girki dan haka tana komawa ruwa ta watsa tai alwala tai sallah lemo kadai ta sha ta rufe sashen su ta tafi bangaren Inna.

Inna na kitchen ta shiga jiyo muryar Maryam tace
"Gani nan shigo daga ciki."
Maryam ta karasa tana fadin
"Hajiya Inna me ake soya mana?"

Cincin take soyawa Maryam tai murmushi dan bata taba ganin tsohuwa kamar Inna wacce ta iya komai daga na zamani har na gargajiya ba abinda bata yi in tana sha'awa bata fiya son kayan shago ba da kanta take fi yin komai. Maryam tace
"Inna ina yini?"

"Lafiya lou yau ina kika shiga na jiki shiru naje bangaren na same shi a rufe."
"Ai yau muka fara jarabawa shiyasa."

"Ayyaho Allah ya bada sa'a."
Ta fada tana tsame ragowar cincin din ta zuba a collender tace
"Ina Haidar din shi kuma?"

"Ai Inna ni yau banga Haidar ba ma kwata kwata. Kila Yaa Aliyu ne ya fita da shi."
"Dan kar yazo waje na ya fice dashi to wane aikin kirki zai da yaro dan Allah."

"Nima dai ina mamakin ta yadda yake aiki da Haidar."
"Hmmm ai dan kar yazo min nan ne nima ban neme shi ba suje can su karata sai fa nai wata ban saka yaron nan a ido na ba ko zai zo gaishe ni bai zuwa dashi."

"To kiyi hakuri Inna zan kawo miki shi anjima."
"A'ah A'ah bar mishi tinda bai so yazo waje na."

Suka zauna suna hira har akai la'asar Maryam ta koma dan tasan Ummi ta dawo a lokacin ai kuwa ta dawo tana sama tana watsa ruwa dakin Ummi ta shiga rike da kudin da farouk ya bata. Ummi ta fito tace
"Yan makaranta an dawo?"

Kai ta gyada tana murmushi tace
"Sannu da zuwa."
"Yauwah ya makarantar da jarabawa?"

"Alhamdulillah."
"Ince tai sauki."
Murmushi ta saki tace
"Sosai Ummi."

"To Allah bada sa'a."
"Amin nagode."
Ta fada tana mko mata kudi
"Na menene?"

"Dazu Yaa Farouk ne ya kai ni shine ya ban wannan kudin."
"To angode."

"To Ummi ki amsa."
"A'ah ki ajiye a wajen ki."

"To ni ki ajiyen."
"To nawa ne?"

Kirgawa tayi ta fada mata tace
"Dubu biyar ne."
"Angode."
Ta amsa ta saka a cikin dorowa Maryam ta mike tace
"Me za a dafa?"

"A'ah ke da zaki karatu."
"Ummi gobe ba jarabawa ko da dare nayi."

"To kije kiyi abu mai sauki."
"To Ummi."
Ta juya ta fita. Ummi ta shirya ta sauka tare suka gama abincin suna gyara kitchen su Aliyu suka dawo. Da gudu Haidar ya rumgume Ummi ya sake ta yayo wajen Maryam ta dauke shi tana fadin
"Haidar."

Ya hau mata dariya ta dire shi tana fadin
"Na kusa daina daukar ka nauyi kake karawa wallahi."
Ummi tace
"Haidar din."

"Allah Ummi baki ji yadda ya kara nauyi ba."
Dariya Ummi tayi tace
"Dan dai baki saba ba amman da ace nacewa ne dashi da kullum yana goye a bayan ki fa."

"Ai nagodewa Allah."
Ummi ta dauki Haidar suka fice Maryam ta karasa aiki.

Aliyu ta sama a falo yace
"Ummi ya gidan?"
"Alhamdulillah ya aiki?"

"Alhamdulilah."
Yai shiru yana so ya tambayi ya exam kuma baya so can yace
"Ina Maryam ya jarabawar tata?"

"Bari ta fito ta fada maka."
"A'ah Ummi kema ai nasan ta fada miki...."

Sallamar Maryam ce ta sa yayi shiru ta shigo tace
"Ina yini Yaa Aliyu."
"Lafiya lou."

Tai hanyar sama. Ummi tace
"Zo ki fada masa ya jarabawar mana."
"Ummi alhamdulillah."

"To Allah bada sa'a."
Ya fada ta amsa da Amin itama ta haye sama.

Haka suka cigaba da jarabawar acan ta hadu da wata yarinya Jawahir yar minister ce tana son Maryam duk da Maryam bata sake da ita ba amman ita ta makale mata har number Ummi ta amsa a wajen Maryam dan suna gaisawa bini bini in ba exam kuwa ta kira ta su gaisa.

*
Sati uku sukai suna jarabawa suka gama tayi jamb sai zaman jiran result. Haidar kuwa lokacin ya yaye kan sa sam ya daina shan nono sai kayan da Aliyu ke siyo masa ga tafiya ko ina yana iyawa dan a lokacin ya shiga shekara daya, yaron gwanin sha'awa ga farin jiki gashi duk abinda aka saka masa kyau yake masa ga fara'a ga kyau kamar shi yayi kansa. Maryam ma in yana bacci ta zuba masa ido ko in yai wani abu dan sosai yake kama da Abban sa. Shiyasa take jin wani son sa a zuciyar ta na daban.

Satin da suka gama jarabawa Ummi ta siya mata waya mai kyau da tsada ai kuwa Jawahir ta fara kira ta bata number sannan ta fita nunawa Inna. A falon Inna ta samu Farouk yana cin abinci ta shiga da murnar ta tana ganin sa tai kasa da kan ta ta karasa wajen Inna tana fadin
"Inna kinga wayar da Ummi ta siyon."

Amsa Inna tayi tana fadin
"Kai masha Allah. Allah yasa rai akaiwa."
"Amin."

Farouk ya dago yace
"Ni ba za a nuna min ha."
Mika masa tayi ya amsa yai danne danne sannan ya mika mata yace
"Allah sanya alheri bari na saka miki kati."

Sai jin karar shigowar sako tayi tana dubawa taga dubu biyar ya saka mata tace
"Nagode."
Sannan ta mike ta koma bangaren Ummi. Tana falo tana danne danne su Haidar suka dawo yayo wajen ta a guje yana fadin
"Oyoyo."
Ta rumgune shi tana fadin
"Zo ka taya ni murna Ummi ta sai mana waya."

Aliyu dai daki ya shige nan suka hau hotona ita da Haidar har Ummi ta sauko yayi wajen ta. Satin su daya da yin Jamb result ya fito ta samu 250 daman medicine ta cike ana haka wanda wata daya da gama exam shima ya fito tana da A guda biyar sai B guda hudu murna wajen Maryam kamar me? Ummi ma ta tayata murna sosai haka ta dauki dan ta tana ta juyi dashi.

Da dare Aliyu na zaune a falo Ummi ta shiga dakin Maryam lokacin Haidar yai Bacci Ummi tace
"Kin nunawa Yayan naki kuwa jarabawar?"
"A'ah Ummi."
"To kije ki nuna masa kinji."

"To Unmi."
Ta mike ta saka hijab akan kayan baccin ta sannan ta fice ta sauka kasa hannun ta rike da waya da takardar. Da sallama ta karasa ya amsa ta zauna a kasa tare da fadin
"Ina yini?"

"Lafiya lou."
Ya fada shiru tayi sai kuma ya mike zai bar wajen murya na rawa dan ganin ko kallon ta bai ba kuma yake kokarin mikewa tace
"Daman jarabawar muce ta fito shine na kawo maka."

Hannu ya mika, ta miko masa ya kalla yace
"Allah sanya alheri."
Yasa kai yai cikin dakin sa. Da kallo ta bishi wayar ta ce tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dan haka ta dauka tace
"Ya dai yan mata."

"kin dubo exam?"
"Na dubo A5 B4"

"Masha Allah nima yanzu aka dubo min amman ni da C."
"Masha Allah Allah sa albarka.".

"Amin dan Allah kice a kawo ki makarantar da na cike."
Murmushi Maryam tayi tace
"Sai yadda su Ummi suka ce."

"Ke dai bakya so mu hadu ko?"
"Bani da kawa ko daya sai ke kinga kuwa ai zan so mu hadu tare amman ban sani ba a jamb ai can aka cike in Allah yayi sai kiga nazo nan din?"
"To shikenan Allah yasa su kawo ki nan mu hade."
Tace
"Amin"
Aliyu ne ya fito ya shiga kitchen ya dauki abu tana falo suna waya da Jawahir har ya koma itama tai sama ta kwanta bayan ta tofe su da addu'a.

Basu san komai akan harkar karatun nata ba dan lokacin har an fara addmision har Maryam ta fitar da rai, Ummi kuma a lokacin tana busy dan akwai wani case dake hannun ta wanda bata zama kullum tana aiki akan sa duk da abin na ranta amman sai ta sha'afa in tana son ta tambaye shi.



A haka ne Aliyu yai tai mata ciko ciko ba tare da sanin ta ba sai kiran ta da yayi kawai ya bata admission letter da kudin registration *Page 1/2*


~Flash back finish~


*Allah jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani Amin.*



*Antty*[11/26, 18:57] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 57

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



~Cigaban labari~


Da dare, Ummi, Abba da Maryam suna zaune a falo, Maryam na kwance akan three sitter an saka mata karin ruwa, bacci take sama-sama, sai Abba da Ummi dake magana akan zuwan Muhammad, wayar Abba ce tai kara Ummi ta mika masa ya amsa, wanda karar wayar yasa Maryam ta bude idon ta a hankali, sai kuma ta mai dasu ta rufe.

Abba ya dauki wayar yace
"Muhammad ka karaso to ka shigo mana."
Da sauri Maryam ta bude ido tana kallon Abba to wanne Muhammad din? Ido ta mayar ta rufe dan wani bacci ke son dibar ta dan har da allurar bacci akai mata saboda ta samu hutu da nutsuwa dan jinin ta har ya hau.

Ummi tace
"Ai bangaren Abbi zaku ko?"
"Eh bari na kira naji ya dawo?"

Sallama Muhammad yayi ya shigo, su Ummi suka amsa masa ya karaso ya durkusa ya gaishe da Ummi da Abba suka amsa Ummi tace
"Zauna mana."

Kan sa a kasa yace
"Ummi nan ma yayi."
Ya zauna a gefen carpet, Maryam ya saci kallo yaga yadda idon ta ke motsi alamar ba baccin take ba bude idon ne bata so, Ummi ya kalla saboda Abba na waya yace
"Ummi bata da lafiya ne?"

"Eh bata jin dadi."
"Allah sauwake."

"Amin mungode."
Abba ya gama waya yace
"Tashi muje."

Muhammad ya mike yabi bayan Abba, har cikin babban falon sa suka karasa, ya zauna akan carpet, Abbi yace
"Ah Muhammad yi zaman ka akan kujera."

"Nan ma ya isa."
Ya fada yana gaishe shi. Abbi ya amsa sannan yai gyaran murya, zai magana kenan Farouk ya shigo, ya gaishe da su Abbi sannan ya mikawa Muhammad hannu ba yabo ba fallasa suka gaisa, gyara zama yai shima akan carpet, Abbi yace
"Muhammad mun kira ka ne akan Maryam, hakika wani lokacin ina manta alakar mu da ita domin mun dauke ta tamkar yar cikin mu, zan iya ce maka tafi wasu ya'yan namu a wajen mu, yarinya ce mai ladabi da biyayya wacce take da addini da ilimi, mai son kyautatawa kowa bata da hayaniya bare fada tin zaman mu da ita a gidan nan na sama da shekara hudu ban taba jin wani yace tai masa abu na batanci ba sam, kullum cikin kyautatawa mutanen gidan nan take, duk wanda ya samu Maryam ya dace kuma ya samu babba rabo. Ba ina fada maka haka bane dan na yabeta ko in kara maka son ta ta yadda zaka kara kwadaituwa da ita ba, sai dan naga kai ma kana da hankali in har haka zata faru zamufi kowa jin dadi dan fatana kenan Maryam ta samu me rike ta tamkar tana hannun mu bana son tai maraicin komai da kowa."

Abbi ya dakata Muhammad kan sa na 'kasa sai yanzu ya gane cewa Maryam ba yar gidan nan ba kila yar kanin su ko wansu ce, kila iyayen ta ne suka mutu. Maganar Abba ce ta dawo da shi daga tunanin da yake,
"Mun tsinci Maryam shakara hudu da wani abu da suka wuce a garin Bauchi lokacin munje wani aiki da mai daki na akan hanyar mu ta dawowa muka bige ta wannan dalilin yasa muka kai ta asibiti, dole mu tsaya akan ta muga yanayin jikin ta wanda a dalilin haka muka kwana a asibitin duk

Please Login or Register in order to submit comment