Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da jefa shi a wani halin, daga baya dauko ta yai gaba daya suka dawo daki, sai da suka bata wajen awa kusan d'aya sannan ya sarara mata, Maryam kuwa taji maza ta lafe a jikin sa kawai tana maida nunfashin wuya. Sai da ya ji kwarin jikin sa ya mike ya shiga ya kara hada musu wani ruwan zafin tare suka shiga ya farai nata wanka wanda yana yi yana kara tattabe ta sai da tayi da gaske amman da sai an kara maimaitawa.

Da kansa ya shirya ta cikin wasu kananun kaya wanda siket din yake iya cinya sai rigar da iya kar ta cibiya, kallon ta ya tsaya, ta dauki hijab ta saka tana fadin
"Allah Yaya ba kyau, kalli agogo uku saura."

Murnushi ya saki yai k'asa da kansa, dan hakika yana son Maryam da kaunar ta in ta tashi ne ba zai taba barin ta ba, shiryawa yayi ya jasu sallah bayan sun idar ya dauke ta sukai falo, kayan kallo ya kunna musu ya zauna tare da manna ta da jikinsa, a haka aka kira shi ya fita bai jima ba ya dawo da kayan abincin su, da kan sa ya bata taci suka cigaba da kallon su tana jikin sa ya kanainaye ta hannunsa na yawo sassan jikinta. Haka suka wuni cur yana bata wata irin kulawa tamkar zai maidata cikin cikinsa, itako sai shagwab'a take zuba masa, yana nan nan da ita,

Weekend din ba abinda ya dinga sai kula da Maryam wacce zallar shagwaba take masa, komai shi yake mata abinci daga na safe har dare order yake da kayan motsa baki ba inda yake zuwa sai massalaci suna makale da juna cikin kwana biyun nan so, kauna da tausayin junan su ya ninku, shakuwar su ta kara daduwa duk yadda yake bukatar Maryam daurewa yayi dan yasan bai mata ta sauki ba, ta sha wahala sai dai ko ba komai yana rage zafi tinga zai yi romancing nata bata hanasa sam. Amman jikin ta yana fada mata, dan kirji ta in banda zafi na tsosa da matsa da suka sha ba abinda suke mata.


Bai so mai da ita ranar Monday ba amman ganin ranar Laraba zasu fara Waec yasa ya fara shirye shiryen kai ta amman a safiyyar ranar ba karamin wahala ya bawa Maryam ba dan dakyar take iya tafiya sai da ya kara gasa ta har yana fadin
"Baby ko dai sai gobe zaki tafi?"

Kafada ta make tana girgiza kai tace
"Yaya Exam kuma kar Ammi tazo tace min zatazo this week."
Ba dan yaso ba ya shiryata wajen sha biyu suka koma *MI College* wanda tana tafiya yana mata sannu ji yake kamar ya dauke ta ji yake kamar yai mata tafiyar., ita kuwa cinyoyin ta ne suke mata wani irin ciwo da kyar take takawa. Da su Aisha suka zo dan debar mata kaya sunga soyayya dan yadda Aliyu ya dingai mata itama tana kara shagwabe masa kamar zatai kuka ido da hanci suka saki suna kallon su, da zasu rabu kuwa har da hawaye ji take kamar ta bishi haka ya rumgume ta yana lallashin ta a school compound sosai sukai mamaki dan Yaa Aliyu bai rumgume ta amman sai suka dauki hakan amatsayin lallashin a haka suka rabu da kewar junan su.

Tin lokacin wata soyayya ta kara kullewa da shakuwa dan in suna waya jin muryar junan su kadai kan tayar musu da hankali in kuwa yazo principal ya bar musu office yai ta lugwiwitata, wanda irin haka zata ce
"Ba kyau ba."
Shi kuwa ya kanyi murmushi wani lokacin yace
"Ai matata ce."

Tin daga lokacin bai jin nauyin kowa zai ce shi matar sa kawai yake so a bashi duk abinda suke so bidi'a ne sam su Mami basa ganewa, a haka suka fara jarabawa ranar da suka fara ranar Ammi tazo daga kallo daya taga Maryam ta sauya ta kalle ta tace
"Daughter baki da lafiya ne?"

Gabanta ne ya fadi tana tsoron ba dai Ammi ta gane sunyi wani da Ya Haidar ba, kai ta girgiza Ammi tace
"Kar kisa damuwa fa akan jarabawar nan zaku ci da izinin Allah."
Haka ta dinga bata kwarin gwiwa tatafi.

Aliyu bai kwana uku bai zo ba kuma in har yazo daga shi har Maryam sai yanayin su ya canja ganin in har yazo tana kasa karatu tai ta kasala da shiga damuwa yasa ko yazo iyakar su school compound dan baya so yai mata abinda zai takura ta ta kasa sakewa wanda itama a lokacin ba abinda take so sai ta kasance da shi taji dumin jikin sa, taji yana lalube ta.

Suna tsaka da exam ta fara samun canji wanda da ta kwanta sai bacci ga yawan tashin zuciya ko tai ta tsurfa da zabar abinda zataci a har suka gama exam ta dawo gida aka fara shirin bikin su.```

Wanda ranar daurin auren su Aliyu ya rasu, ranar da take zaton burin su ya cika zasuje su sha soyayya su kula da juna amman sai gashi Allah ya dauke Aliyu, wanda daga nan kaddarar ta ta fara sai gashi ta bar gida da cikin Aliyu taje tai rayuwa a wani wajen da suka rike ta tamkar 'yar su suka bata duk wani gata da soyayya, suka rike ta da amana ita da danta shin me zataiwa wadan nan mutanen, wanda a karshe basu kyamace ta ba suce basu san d'an waye ba ko a ina tai ciki suka aura mata dansu da suka fiso shin ita dan me zatai butulci.

Ta sani tana son Yaa Haidar amman kuma ya zatayi Allah ya dauke shi ya kawo mata wani Yaa Haidar din sai a yanzu ta tuna abinda yake fada mata ko ya tafi wani zai zo ya kula da ita, zata kasance matar Haidar kuma Uwar Haidar.

Hawaye ta goge tuna yanzu fa ita matar aure ce, ta sani Yaa Haidar yafi karfin ta kuma bata isa ya sota ba amman tayi alkawarin zama dashi a haka tinda tata kalar kadaddar kenan Allah ya bata ikon cinyewa.

Wayar tace tai kara ta dauka tana duba screen din Yaa Haidar ta gani bata dauka har ta tsinke ya sake kira tana gab da tsunkewa takai kunnen ta murya a hankali wacce ta sha kuka tai sallama Aliyu dake kwance ya mike da sauri yana fadin
"Me ya samu muryar ki?"

"Ba komai."
"Fada min gaskiya kuka kikai ko?"
Ji tayi zuciyar ta tayi rauni bata san lokacin da kukan ya fito fili ba, kai ya dafe dan a duniya ba abinda ya tsana kamar kukan mace macen ma kuma matar sa.

A hankali yace
"Is ok bar kukan ki fada min menene? Auren mune bakya so ko? Kinsan na miki alkawari in har bakya so zan sauwake miki sai ki nemi wanda yake sonki kike son sa wanda ya fi cancanta dake."

A zuciyar ta ta ce
"Ba wanda ya camcanta dani sai kai, dole zan zauna dakai ko dan taimakon taka rayuwar kamar yadda ka taimaki tawa amman matsalar tayaya zan fara bayan baka so na."

"Ki bar kukan to."
Ya katse mata tunanin da take, shiru tayi yace
"Ki cire damuwar auren mu kinji?"
Kai ta gyada yace
"Alright ina Son dina."

Kallon Haidar tayi dake bacci tace
"Bacci yake."
"Ok shi na kira daman muyi waya tinda bacci yake sai anjima ko?"

"A'ah Yaya...."
Sai tayi shiru yace
"Uhm mrenene?"

"Ya aikin?"
Ya dan saki murmushi yace
"Alhamdulillah."

Tai shiru yace
"Uhm shikenan?"
Kai ta gyada kawai jin shiru yace
"To shikenan sai anjima zan kira muyi waya da My Son."

"Toh."
Ta fada tana kashe wayar. Kwanciyya tayi tana lumshe ido, fuskar Yaa Aliyu ta bayyana kyakyawa mai nutsuwa da kwarjini wanda samun sa sai an tona mai ilimi both arabi and boko shin me zatayi yau in Yaa Haidar ya sake ta wa zai aure ta wanda take so a gida duk wanda zai aure ta sai ta hadu da kalubale wasu baza su ta'ba yadda cewa da aure ta haifi Haidar ba wasu ko sun yadda to tabbas zasu ce taje yawon duniya mafita daya ce shine ta hakura ta zauna da Yaa Haidar, ta sani tana kallon Yaa Haidar a matsayin Yayan ta duk da wasu lokutan takan manta wane irin feeling take ji game da shi, amman ta sani yana daga cikin irin mazan da take so da wadan nan tunanin bacci ya dauke ta.

Kiran sallah la'asar ya tashe ta a bacci ta samu Haidar kwance rike da waya a kunne yana fadin
"Abbi yaushe zaka zo?"

Ta mike ta shiga bandaki taji yana fadin
"Abbi, Adda ta tashi yanzu."
Kofar bandaki ya kalla yace
"Toilet ta shiga"

Ya sauka akan gadon yace
"Abbi an kiran Sallah zanje nayi Sallah a kusa a Abbin Adda, ka kira anjima bye."
Ya ajiye wayar ya fita dai dai fitowar Maryam ta dauki wayar tana fadin
"Ko tayaya aka kira ban ji ba."

Aliyu da bai kashe wayar ba yana jin ta, ta ajiye ta dauki Hijab ta saka ta tada sallah.

*
Kwanan su goma Abbi yasa Aliyu da su Ummi suzo dan aje Adamawa dasu gaba daya, har da Abba aka zo da Sitti da Innah da Yaa Farouk, bangaren biyu na gidan da ba kowa wanda sai su Yaa Alkasim sunzo suke sauka anan sai na Yaa Abdullah da bai aure ba anan aka sauke su, sunga kulawa sosai dan ba abinda ba a ajiye musu, tinda suka zo Maryam na wajen Ummi sai shagwaba take zuba mata dan har lokacin bata jin dadi gaba daya ta kasa sakewa ta kasa sabawa da sabuwar rayuwar ta ta yanzu kewar su Ummi ta dingayi dan haka da suka zo tana jikin Ummi, Ammi da Mami kuwa sosai sukaji dadi dan ganin su Ummi kadai ya sanya Maryam sakewa, tinda suka zo bata ga Yaa Aliyu ba kuma ance tare dashi suka zo, ko da yake shi a gidan su Mami ya sauka bangaren Yaa Haidar na da, Yaa Abubakar kuma suna boy quarters.

In Ammi taga yadda Maryam take sakewa a cikin su Sitti da su Ummi wani dadi take ji da nutsuwa ashe yar ta a cikin gata take sai taji hankalin ta ya kwanta sam bata da damuwa auren da akai mata ma da taga Yaa Aliyu sosai ta jinjina abin dan Aliyu namijin nunawa sa'a ne bama da Yaa Abubakar ya karai musu bayani waye Aliyu duk sai suka ji sanyi duk da basu san Muhammad ba amman hankalin su yafi kwanciyya da auren ta da Aliyu akan da Muhammad.

Dan su Aliyu sun san Maryam sun kuma dauke ta tamkar 'yar cikin su basu nuna kyama ba yau ko Aliyu bai son Maryam ai ba zasu ce a kunce auren ba bare yadda yake son Aliyu ya dauke shi tamkar d'an sa da yadda yai dawainiyya da Maryam ma zai nuna akwai tausayi da shakuwa tsakanin su, wanda so yana farawa ne daga tausayawa juna dan haka sai Ammi ta samu nustuwa a yanzu bata da damuwa sai na ganin farin cikin yar tata kawai dan haka zata kara bata kwarin gwiwa akan ta zauna da mijin ta lafiya duk da tasan Maryam yarinya ce mai hakuri ladabi da biyayya.

*
Kwance take a jikin Sitti, Ummi na gefen kafar ta tana danna waya sukaji sallamar sa da sauri ta rufe idon ta, su Ummi suka amsa ya shigo ya zauna a gefen Ummi yana gaishe su, Inna tace
"Kai dai Aliyu tinda muka zo ban kara ganin ka ba."

Kallon ta yayi yace
"Ai Inna ke uzuri za a na miki dan wallahi kin gama tsufa kin fara rikicin tsufa."

Ummi tai murmushi yace
"To Ummi dazu fa na shigo kawai dai ita ce ina jin ta fara daina gane mutane."
"Kaniyar ka nace, ai ba wanda ba zan gane a cikin ku ba kiji fa Hadiza ina tsufan da zan kasa gane Ali ko na kasa gane kowa ai na gane kai, yaron da ni na raine shi a hannu na ya girma."

Maryam juyi tayi tana fuskantar Aliyu kamar mai bacci amman idon ta biyu ta kasan idon ta take kallon sa sanye yake da milk kalar boyel wanda tana gano singlet din sa. Kansa sanye da brown kalar hula ya kara kyau da haske kamshin sa ya cika dakin, yana lura da ita yadda gashin idon ta ke motsawa alamar idon ta biyu, kafar sa ya mike yana fadin
"To shikenan Hajiya Inna."

Sitti tana dariya tace
"Ai gwara tai maka dai."
"Ni dai na tuba ban shirya fada dake ba."

Ya kalli Ummi yace
"Ina Haidar ne?"
"Yanzu ya fita fa kila yayi can cikin gida yazo yaga yan uwa ai ba zama kasan Haidar da son mutane."

Kai ya gyada ya mike yana kallon Maryam dake kwance jikin Sitti yace
"Ita kuwa wannan baccin la'asar Ummi, kuma dan ta karya min mata gaskiya ta daina kwanciyya a jikin Sitti."

Baki ta dan turo, ya dan yi murmushi ya juya ya nufi kofa ta bude ido tana binsa da kallo yana kaiwa kofa ya juyo ido hudu sukai ya kanne mata ido daya yai, tai saurin rufe idon ta ya saki murmushi kawai ya fice.



*Allah ka yafe mana kai mana rahma, Allah yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*



*Antty*
[12/5, 13:30] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 75

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Washe gari da daddare wajen karfe tara ta fito daga bangaren Ammi zata wajen Ummi, tinda ya fito daga compound ya hango ta wannan yasa ya koma ciki da sauri ya buya a jikin flowers din dake wajen, ta karaso wajen ta shiga, hannu yasa ya janyo ta jikin sa baki ta bude zatai ihu yai saurin daura tafin hannun sa akan bakin ta yana fadin
"Ke kar ki taran mutane."

Ido ta zaro tana kallon sa kirjin ta na dukan uku uku, ta marairaice ta zame bakin ta tace
"To Yaya ba tsoratar dani kayi ba."

Ya dan harare ta yace
"Shine zaki min ihu to."
Baki ta dan turo, yana kallon ta yace
"Wato ke yanzu baki iya gaisuwa ba ko? In kinga mutane ma sai ki fara baccin karya ko?"

Baki ta dan turo ta juya tace
"To ni yaushe na ganka tinda kuka zo ma ko nema na bakai ba sai ta yaron ka kake."
Tai magana hawaye na taruwa a idon ta ya zagayo gaban ta yana kallon yadda hawayen ya taru a idon ta, hannun ta ya kama suka karasa wani waje da yake da dakali suka zauna yace
"Yanzu ni dake waye me laifi?"

Da hannu ta nuna sa, yace
"To ni menene laifin nawa?"
"Gashi nan baka nemana ko son ganina bakayi ina ta murna zaku zo amman shine kai baka neman na."

Tai maganar tana sunkuyar da kanta dan bata san yadda akai ta fada masa ba kawai abin na ranta ne bata ji dadi ba ace wai yazo kwana biyu amman basu hadu ba bai kuma damu da neman ta ba, sai Haidar tare suke yini gaba daya fa sai jiyan nan ta ganshi ai dai ko kiranta yayi ashe saboda Haidar yake kiranta.

"To shikenan am sorry nayi laifi amman ke meyasa bazaki neman ba."
Ido ta dan zaro tace
"Mata ita ke zuwa wajen namiji?"

"Menene a ciki, naga yanzu kin zama matata."
Kai tayi kasa dashi yace
"Ko dan ni ba a so na, ai da Muhammad ne da zaki nemesa ko a waya ne, amman ni fada min tin da kuka zo Kano kin neman in bani na neme ki ba."

Baki ta dan turo tace
"Uhmm kai ma ai Haidar kake nema."
"Ohk naji na nemi Haidar amman ai ta wajen ki ko? Kuma sai mun gaisa in naso zan kira Aunty Nusy ta kira min shi ko Alkasim."

"Uhmm uhmm to kayi hakuri ni bansan me zan kira nace ba."
"Oh har gaisawa."

"Uhm uhmm to naji kayi hakuri."
Kamo hannun ta yayi ya juyo da ita yace
"To na hakura, yanzu gani kalle ni shikenan gani."

Ta dago ta dan kalle sa sai ta dauke kan ta, yace
"Oh har kin gama kallon nawa."
Mikewa tayi tace
"Uhmm ni wajen Sitti zani sai da safe."

Ta juya zata tafi ya kamo hannun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna kamshin turaren su na tashi, dagowa yai yana kallon ta, itama shi take kalla, Yaa Farouk ne ya shigo kamar ance ya juyo ya gansu baki ya saki yana kallon love wayar sa ya zaro ya fara snapping nasu picture hasken flash din shi yasa suka juyo a tare da sauri Aliyu ya sake ta yana hade rai ya kalli Farouk yace
"Menene haka?"

"Alhaji Yaa Hamma tuba nake soyayya na gani kuma abun yai kyau shiyasa na tsaya koya."
Ya fada yana murmushi Haidar ya karasa yana kama kunnen sa yace
"Gidan ku."

Da sauri Maryam ta bar wajen, Farouk ya hau ihu yana fadin
"Tuba nake Yaya, Dr Hamma."

Ya rankwashe shi ya amshi wayar yana kallon screem din picture din yayi kyau sosai, sun shagala kallon junan su ba karamin kyau sukai da dacewa da juna ba. Ya mika masa wayar yace
"Tafi ka ban waje."

"Allah kara girma da lafiya Yaya na."
Farouk ya fada yana dariya dan murmushi Haidar yai ya juyo wajen Maryam sai dai me? Ba kowa a wajen dube dube ya fara sai ya saki murmushi kenan ta gudu, fita yayi ya tafi kawai.


Tana shiga ta zauna a gefen Sitti tana fadin
"Bakuyi bacci ba?"
"Bamuyi ba daga ina kke?"

Yaa Farouk da ya shigo yace
"Daga soyayya take Sitti."
Maryam ta dago tana marairacewa tace
"Kai Yaa Farouk soyayya kuma dawa?"

"Da mijin ki Dr Hamma na."
Ido ta zaro tace
"A ina ka gamu tare."

Wayar sa ya nunowa Sitti Maryam ta mike da sauri ta warce wayar tana fadin
"Sharri zai mana Sitti."

Sitti na murmushi tace
"Ai Faruku bashi da dama."
"Sitti menene kuma Faruku ko dadi babu Farouk ake cewa fa."

"Dan nace Faruku da bance Umaru ba."
Daman ke da Inna haka kuke kuyi ta batawa mutane suna."

Inna dake gyangyadi ta bude ido tace
"Me nayi ake kira na."
Juyawa yayi yace
"Ni sai da safe."

Maryam ta mike tace
'Nima bari na tafi Yaya Faruku tsayani."
Juyowa yayi ya harare ta ta sunne kai tana fadin
"Sorry Yaya na."

Tare suka fita ta shiga sashen su shi kuma ya shiga bangaren Yaa Abdullah dan tare suke.

Kwanan su uku suka wuce Adamawa, Shigar yamma sukai nan aka hau tarbar su dan sun san da zuwan nasu Malam kuwa da yaga Maryam bakin sa yaki rufuwa, haka da yaga Haidar ya kamashi yana fadin
"Masha Allah, kamar su daya kuwa da mahaifin nasa, Allah masa rahma."

Masauki aka basu, dan kowa yaje ya huta aka cika su da kayan ci da sha kala kala, Maryam kuwa daman sakin shan fura ai ita tai ta dirka Haidar ma ita ya sha sai gashin nama da suka ci amman sunki cin abinci shi da Maryam sam.


*
Washe gari da safe, Malam ya kira meeting, domin kowa yana gidan Abbi da Yaa Usman ne kadai ba a garin ba to shima bayan su Abbi sunzo ya iso da iyalan sa. Bayan kowa ya hallara ne, Malam yayi godiya da Allah da ya dawo da Maryam lafiya tare da godiya ga su Ummi akan rikon da sukai wa Maryam.

A take ya umarci Maryam da ta basu labarin abunda ya faru da ita, da asalin cikin waye, Malam ya kalli Maryam dan ta fara, tai kasa da kai murya a sanyaye ta fadi komai da ta sani bayan ta gama ta mika masa wata jakar ta inda a ciki ne sadakin ta yake na sarkar gold din da Aliyu ya bayar da marriage certificate tare da wayar da akai vedion komai.

Malam ya dauka ya bawa Yaa Alkasim ya duba komai ya kunna wayar tare da nuna musu vedion wanda Malam yasa akai connecting nasa da TV dake dakin, wanda kowa yaga abinda akai kamar a lokacin a kai, wanda duk jikin mutanen dakin yai sanyi, Mami da Maryam kuwa kuka suke dan ganin Aliyu a vedion sai ya dawo musu da rasuwar sa sabuwa ganin sa yana motsi da murmushi da magana.

Bayan an gama Malam ya dago ya kalli yan dakin yace
"Alhamdulillah duk da Muhammad yai min bayanin komai akan auren sirrin dasu Maryam sukai nasa ta bayyana komai saboda ku sani kuma ku tabbatar Maryam ba zina tayi ba da aure ta haifi yaron ta wanda ga shaida nan, Ahmad abokin Haidar ya kai Muhammad har wajen malamin kan Maryam tazo da wadan nan shaidu, dan haka ba abinda zamuce sai godiya ga Allah da ya tsare mana zuria daga aikata zina, sai dai akwai jan hankalin da zanyi ga kowa na nan wajen, wannan kaddara ce ga Maryam ya tashi jarabtar ta duk da tayi aure da Aliyu amman kasancewar bata bawa iyayen nata damar aurar da ita ba shiyasa bata samu abinda take so ba, kuma Allah ya nuna isharar sa, dan da Aliyu bai son ta bayan ya same ta zai iya watsi da ita amman da yake ba abin Allah wadai sukai ba sai soyayya ce ta dadu, to kunga yadda karshen su ya kasance duk da ba su sa'bawa Allah ba amman sa'bawa iyaye da rashin sanin su shine silar barin ta gida da shiga wata rayuwa wanda 'kaddarar auren Aliyu ita ce zan ce ta sa ta bar gida, jan hankalin da zanyi shine mu kasance masu bawa iyayen mu mahimmanci a komai, yau da Maryam da Aliyu sun sanar da iyaye akai musu aure da kan rasuwar Aliyu sun jima da zama a inuwa daya wacce ba zasu na jin shakar komai ba, haka nan da Muhammad ba zai fushi ya kori Maryam ba, amman da yake Allah ya k'addarta haka sai mu gode masa, amman ku sani ba kowa ne karshen sa zai zo irin nata ba naka zai iya fin nata in har kace zakai koyi da nata, kamar lokacin da ta bar gida zata iya cin karo da mutanen banza ko a 'ki taimaka mata shaidan yasa ta fada mummunar hanya amman Allah sai ya takaita wanda kila dan basu bi son zuciya wajen sa'ba masa ba ya hada ta da wadan nan bayin Allah to mu kiyaye shi Aliyu Allah masa rahma yasa ya huta.
To kunga barin ta gida ta samu kalubale da yawa wanda har auren ta aka fasa wanda ba abinda yafi wannan tashin hankali amman sai gashi wadan nan bayin Allah suka hada auren 'dansu da ita ba abinda zamuce sai godiya, Allah ya saka muku da gidan Allah, Maryam ke kuma Allah ya miki Albarka ya kiyaye gaba rayuwar Maryam ta zama izina garemu, Haidar ya rasu wani ya dawo ya maye gurbin sa a matsayin mijin ta Allah ya basu zaman lafiya ya raya Haidar karami yai muku albarka."

Duk dakin jikin su yai sanyi dan haka gaba daya suka hada baki wajen fadin
"Amin!"

Haka Malam ya kara musu nasiha mai ratsa jiki akan tsoron Allah da illar sa'bawa iyaye wanda su Maryam rashin sanar da iyaye ne kawai sukayi amman Allah ya nuna musu wanna isharar to wannan izna ce ga yan baya in tata tai kyau to ta wani ba dole ne tai kyan da tata tayi ba.


Bayan komai ya lafa ne aka yi liyafa anan babban falon Malam inda akaci aka sha anyi yanka raguna kaji da abubuwa sosai, suna tsaka da liyafa, Ahmad ya shigo tare da jagorancin d'aya daga cikin almajiran Malam, Yaa Alkasim ne ya mike suka karaso ya zauna, bayan an gama yace
"Ina Maryam din ne?"

Ciki Yaa Alkasim ya shiga bai jima ba sai gashi ya dawo dauke da Haidar, Ahmad na ganin Haidar sai da gaban sa ya fadi ya amshi yaron ya rumgume hawaye na zubowa a idon sa yace
"Masha Allah, burin Aliyu ya cika ya sunan ka boy?"

"Haidar!"
Haidar ya bashi amsa ya kara rumgume shi yace
"Masha Allah."


Hijab ne sanye a jikin ta, ta fito daidai lokacin da Ahmad ya d'ago kansa. Suna hada ido, idonta ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai.

Ya kura mata ido yana kallonta Maryam ta dad'a kyau ta zama cikakkiyar mace ba kamar shekarun baya ba. Ta karaso yace
"Maryam kece haka?"

Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. Ya dada zama cikakken mutum, a gefen Yaa Alkasim ta tsaya ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye, bayan sun gaisa tace
"Yaa Ahmad ai bazan ganeka ba"

Ya dan saki murmushi dan wani dadi yake ji, ji yake kamar ya rumgume ta dan farin ciki da dadi yau Maryam ta dawo gida cikin iyalan ta ga yaron su burin sa kenan ya kusa

Please Login or Register in order to submit comment