Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makaranta. Ranar lahadi tana zaune bayan ta tsefe kan ta, saloon take so taje a wanke mata dan tasan in ta koma makaranta ba lokaci ne da ita ba.

Saukowa tai daga bene sanye da doguwar riga abaya baka sai mayafin ta, da ta yafa tace
"Ummi zan tafi."
Ummi dake zaune ta dago tace
"To amman za ai miki kitson ko?"

Fuska ta bata tace
"Ummi wallahi zafi kitson."
"Sai kizo kina damuna da in miki calba ko?"

"Ummi itama da zafi fa kike min."
"Oh da zafi nake miki ko to ban sakewa."

Jikin Ummi ta kwanra tace
"A'ah Ummi kiyi hakuri wasa nake."

"Shikenan sai kin dawo, na miki transfer kudin."
Sumbatar Ummi tayi a kumatu tace
"Nagode Ummi Allah Kara budi."

Tai mata murmushi ta fita, tana fita ta nufi wajen motar su, Baba Anas ya karaso yana fadin
"Kin fito?"

Kai ta gyada tace
"Kayi hakuri na barka kana ta jira ko?"
"Ah ba komai Hajiya."

" 'yar ka dai Baba."
Yace
"To 'ya ta."


Ta budi baya ta shiga, wata mota ce ya faka a gefen su, Baba Anas ya shiga dai dai fitowar ta, da sauri Maryam ta dakatar da Baba Anas dake niyyar tada motar tace....





*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*



*Antty*
[10/23, 14:06] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 4

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*







Ta budi baya ta shiga, wata mota ce ya faka a gefen su, Baba Anas ya shiga dai dai fitowar ta, da sauri Maryam ta dakatar da Baba Anas dake niyyar tada motar tana fadin
"Baba Anas tsaya kaga Jawahir."

Ya dakatar da driving din yace
"Ban lura da ita ba."
"Ba komai."

Ta fada tana bude motar, Jawahir da har ta Isa bakin kofa tajiyo Maryam na kiran ta da sauri ta juyo, ganin Maryam ta dan hade rai tace
"Nifa ba wajen ki na zo ba."

"Ah haba Sister ta."
Kai ta dauke sukai ciki tace
"To me nayi ne wai."

Ummi dake ciki tace
"Baki tafi ba Daughter?"
Ganin Jawahir yasa tace
"Ah Jawahir ce sannu da zuwa."

Kan Jawahir a kasa ta karasa ciki tace
"Wallahi Ummi."
Ta karasa ta zauna a kasa tana gaishe da Ummi, Ummi ta amsa tace
"Koma sama ki zauna."

Ta mike ta koma Maryam ta kawo mata lemo da ruwa ta dan harare tace
"Nifa wajen Ummi nazo ba wajen ki ba."

Ummi tace
"Ai kuwa dai."
"Haba Ummi ki sa baki ai nayi niyyar zuwa fa ni ranar me ma ya faru?"
"Uhmm ke kika sani "

Ummi tace
"Ina Momyn taki!"
"Tana gida tace a gaishe ki."

Zama Maryam tayi tace
"Allah yayi ba zamuyi sabani ba."
"To Ina ruwa na ko munyi sabanin ma ai ba wajen ki na zo ba. Ina Haidar?"

"Yana wajen Yaa Aliyu."
Maryam ta bata amsa sannan ta kalli Jawahir tace
"Gobe sai school ko?"

Share ta tayi, Ummi ta basu waje, a haka dai sai da Maryam ta lallabata har ta sauko suna hirar su tace
"Ina zakine wai?"

"Gyaran Kai zani dan nasan aka koma ckul sai kuma Allah."
"Ai kuwa tashi muje nima ina so a min kitso na jima rabo na da kitso."

Ta mike sukaje suka fadawa Ummi sun fita. Jawahir ita tai driving nasu inda ake gyarawa Maryam kai sukaje akai musu wankin kai da kitso har da lalle Jawahir tasa akai musu ta biya kudin shida saura suka fito suka koma gida. Sallah kawai sukai Jawahir tace zata tafi Ummi tace ta tsaya taci abinci da kyar ta tsaya taci sannan sukai sallama.

Suna jikin motar ta Yaa Aliyu ya dawo da Haidar da gudu Haidar ya karaso yazo ya rumgume Jawahir yace
"Anty yaushe kika zo?"
"Na dade gashi har zan tafi."

Fuska ya bata tace
"Zan zo wata rana kaji."
Kai ya gyada ta dauke shi ta dago tana kallo Aliyu da yazo wucewa ya nuna bai ma san da su ba. Jawahir ta ce
"Ina yini?"

Bai jiyo ba ya amsa, ta sauke Haidar ta bude bayan mota ta dauko wata leda tace
"Gashi nan."
"Nagode Anty."

Ya amsa ya bi bayan Aliyu da gudu Maryam tace
"Ka daina gudun nan fa Haidar."

Juyowa Aliyu da ya kai kofa yayi ya tsaya ya karasa ya kama hannun sa sukai ciki. Baki Jawahir ta tabe tace
"Wannan Yayan naki ya fiya miskilanci da yawa."

"Hmmm shi haka yake da Yaa Farouk ne sai kin toshe kunnen ki."
Tai dariya tace
"Ni da ake boyen shi, wallahi Maryam ko ki fada ko kar ki fada yadda Yaa Farouk ke miki kadai ya nuna soyayya kuke "

Ido Maryam ta zaro tana dariya tace
"Yaa Farouk din tab kinga budurwar sa kuwa kyakyawa ga aji da ilimi."
Tsaki Jawahir ta saki tace
"Ta kai ki."

"Ta fini sosai da sosai."
Baki ta tabe tace
"Ba wacce zatafi Besty na."

Ta bude mota ta shiga tace
"Duk boye boyen ki fa wata rana zai fito fili Besty, ki gaishe shi in ya dawo ki fada masa kuma dole yabi ta waje na in yana son a so shi."

"Allah ya shirya ki Besty nagode sosai ki gaida Momy please Ina nan zuwa."
Baki ta tabe ta tada motar tace
"Ban ji ba."

Maryam tai dariya tace
"Zama kiji ne."
Ta matsa Jawahir ta ja motar ta bar wajen. Sai da taga fitar ta sannan ta koma ciki tana murmushi ita kadai.



A haka rayuwa ta dinga gangarawa cikin hukuncin Allah komai yana tafiya dai dai duk da wani abun dole yazo da kalubale a cikin sa kamar bangaren Maryam wanda karatun nasu sai suka ga kamar wahala aka kara masa a haka suke kokari wajen ganin komai suna fahimta, kulawar ta ga Yaa Farouk kuwa sai gaba da ta kara dan ya zamana ko da bai ganta ba zai kira ta, banda kyaututuka da yake yawan mata, ko bata sani ba in yaje shopping sai ya siyo mata kaya duk abinda ya burge shi yaji yana so zai daukarwa Maryam, haka nan yakan yawan aiko mata da kayan ciye ciye ko da basu hadu ba, ita da Aliyu kuwa daga gaisuwa shikenan dan wani lokacin sai tayi sati ma bata ganshi ba duk da zata jiyo muryar sa a falon sama ko kasa ko in tana kitchen zai fita ko makamantan sa, wani lokacin ne ma yakan aika Haidar ya kira ta ya bata wasu sakonnin amman wai hira da sakin fuska a tsakanin su duk babu duk da tana daukar haka a halin sa na miskilanci da na rayuwar da ya tsinci kansa na rashin masoyiyar sa, a haka lokaci ya dinga tafiya har ya kai su Maryam sun shiga level 200 kuma cikin hukuncin Allah da result din su ya fito gaba daya basu da matsala dan 4point ta baro ranar da ta sanar a gida Ummi tai murna sosai haka Yaa Farouk amman Yaa Aliyu sai cewa yayi
"Ki dai dage dan yanzu kika fara."

Da kallo ta bishi ya mike yai dakin sa. Ummi tai murmushi tace
"Haka ne ki dage dan yanzu kika fara karkiga point din ki, kuma ki tsaya wasa."
"To Ummi nagode."
Yaa Farouk kuwa sai wasa ta yake har da gift ya kawo mata na wata sarka mai kyau tai ta godiya kuwa.

A daki Ummi ta samu Yaa Aliyu ta zauna tace
"Son."
Ya juyo yana kallon ta, tace
"Son na rasa meyasa yanzu baka fadan damuwar ka."

Tasowa yai ya zauna kusa da ita yace
"Ummi akan wajen aiki ne."
"Me ya faru?"

"Ina karatun da nake ta naci su bar ni na tafi shekara uku baya?"
Kai Ummi ta gyada tace
"Eh."

"Ummi shi suke maganar wai suna so su tura ni yanzu."
"Ah Alhamdulillah menene na damuwa a ciki to?"

"Ummi a baya na so amman yanzu sam bana so, nafi son na zauna a gida daku ga Haidar."
Kallon sa Ummi tayi ta girgiza kai. Yace
"Kwata kwata bana so nai nesa da gida."

"To ya za ayi yanzu?"
"Zance musu su saka wani."

Kai ta girgiza tace
"Kada ka soma wannan wata dama takace da ka jima kana nema in har mune muna nan zakaje ka dawo ka same mu da izinin Allah, haka Haidar zamu kula dashi kamar kana nan dan haka ka daina cewa ba zaka ba wannan nasarar taka ce shekara nawa abun?"

"Baifi daya ba."
"Ah to kaga shekara daya kamar yau ne inda rai dan haka ina mai baka kwarin gwiwa akan kaje ka cika burin ka insha Allahu zaka samu nasara akan komai mu kuma muna nan muna jiran ka, Haba My Son yau kafara tafiye tafiye ina acan ka kare karatun ka na shekara biyar ka koma kai shekara biyu yanzu ne fa ka saba da zaman gidan ni dai nasan yaro na jarumi ne zaije kuma zai dawo mana da nasara da sa'a da izinin Allah."

"Insha Allahu Ummi but zanyi jewar ki Ummi."
Ya kwanta a cinyar ta ta shafa kansa tace
"Na sani my Son amman ai kace Japan zakaje kuma su Yaya suna can da Sitti."

Kai ya girgiza yace
"Sitti jira take kawai Najwa ta kare karatu su dawo tare."
"To kada ka damu muna tare da kai kaji."

Kai ya gyada ta shafa kansa tace
"Amman meyasa kake wa Maryam haka?"
"Me nayi ummi?"

"Tazo tana murna ka sace mata gwiwa."
Murmushi yayi yana mai lumshe ido kamar ba zai magana ba kuma sai yace
"Ummi wannan shine kalar yadda zan sa ta zabura ne, Ummi in tayi abu ba sai ana nuna tayi ba in aka nuna mata zata san tayi next ta iya dakushewa amman a yanzu abinda na fada mata zai na sa tana zabura ko dan ta bani kunya ni kuma bata san nasan tana kokari ba kuma kunyar da take so ta bani shi zai bamu abinda muke so dagamu har ita."

"Haidarrr....."
"Uhmm Ummi nah."

"Haidar."
Juyowa yai yana kallon ta, zatai magana aka kira sallah, wata ajiyar zuciya ya sauke wacce sai da Ummin ta bishi da kallo ya mike yace
"Bari nai alwala kada na makara."

Ya shige bandaki da sauri. Murmushi tayi tace
"Yaro man kaza, duk boye boyen ka dai watarana ka fito ka fada."
Ta mike ta fita a dakin.




***
Tafe suke a hanya za a kai ta makaranta wanda sauri takeyi dan exam din tara ce dasu gashi har takwas da rabi ta gota, suna cikin tafiya motar ta tsaya akan titi da sauri ta dago tace
"Lafiya Baba Anas?"

"Bari na duba."
Ya fada ya fita dube dube ya fara ya dawo ya kunna amman taki tashi haka ya kara fita ya kara tattaba motar amman taki tashi, kara fita yayi Maryam ta fito kamar zatai kuka tana duba agogon hannun ta wanda ya nuna mata saura kwata, titi ta fara kalla amman kuma ba abin hawa dan titin ba a fiya samun motar haya ba.

"Baba motar taki ko?"
Ta fada tana matsawa wajen sa. Dagowa yai yace
"Wallahi Hajiya bansan me ya same ta ba lallai na yadda da akace karfen nasara bai da tabbas in banda haka lafiya fa muka fito amman ta tsaya Allah yasa ba nan kusa zaku shiga jarabawar ba."

Agogo ta kalla tace
"Kaga saura minti goma ma."
Ta fada kamar zatai kuka.
"To ko mota zan samar miki?"

"Baba ina kaga alamar mota anan?"
"Bari na duba can kasa layin sai a samo."
Ya rufe motar ya nufi titin da zai fitar dashi babban titi kai ya dafe tana duba agogo.

Tin da ya taho ya hange ta, yana karasowa yaga damuwar dake kwance karara akan fuskar ta, parking yai a tsallake ya fito ya karaso wajen ta cikin cool voice taji ance
"Are you okay"
Da sauri ta dago tana kallon waye, wani dogon matashi ne da bazai wuce thirty two ba (Dan ba zai wuce Yaa Farouk ba), yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakin spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baza a sa shi a jerin farare ba, damuwar da ya kara gani a saman fuskar ta kamar zatai kuka ne yasa yace
"Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss"

Cikin rawar murya tace
"Motar mu ce ta lalace kuma exam ce dani......"
Ta duba agogo ta yarfe hannu tace
"Kaga ko sauran minti biyar."

Ta kare maganar cikin shagwaba kamar zatai kuka, jin shiru yasa ta dago ta kalle shi, shima kallon ta yake dan haka ya saki wani murmushi yace
"Toh mu je in ajiye ki ga mota ta can"
Ya nuno mata motar kallon motar tayi har zatace to sai kuma taji tsoro ya kamata kar taje dan kidnapping ne dan haka sai ta noke, gane abinda take nufi yasa yai murmushi yace
"Am sorry daga gidan aboki na nake na amso wani abu shine na biyo ta nan tin daga nesa na gane kina cikin damuwa da bukatar taimako, shine nace bari naji ko zan iya taimaka miki to kuma naji zan iya shine, ni ba dan kidnapping ko yankan kai bane."

Fuska ta rufe da hannayen ta da suke masu kyau tana murmushi kasa kasa, wanda kallon hannun nata ya shagaltar dashi, shima murmushin yake yace
"Mu je to"
Ta girgiza kai tace "A'a"

Yace
"Ohk in samar maki abin hawa tinda baki yadda dani ba?"
"Ni ba haka bane ba kawai dai...."

Yai murmushi yace
"What?"
Zatai magana taji Baba Anas yazo yana haki dan gudu ma yayi yace
"Hajiya ban samu ba ya za ayi ko zaki zo mu karasa mu samu wani ya rage miki hanya."

Sai ya kalli wannan saurayin yace
"Sannu bawan Allah."
"Ina kwana Baba?"
"Lafiya lou."
"Nace tazo na kai ta taki gani take ko dan kidnapping ne ina jin."
Ya zaro wallet din sa ya ciro card din sa ya mikawa Baba sannan ya bashi number wayar sa yace
"In bata dawo gida ba ga abubuwa na."

"A'ah insha Allahu ma zata dawo gida kije Maryam kada ki rasa jarabawar."
Ta kalli Baba ya gyada mata kai. Mutumin ya tsallaka Maryam tace
"Baba ni tsoro nake ji."

"Kiyi addu'a 'yata Allah yana tare dake kinji?"
"To Baba nagode sai munyi waya."
Ya tsallakar da ita titi ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna Baba ya rufe mata ta daga masa hannu ya tayar da motar a guje dan har tara tayi suka fice a kan titin da gudu, tuki yake cikn sauri har suka karasa makarantar
"Wane hall zakuyi exam?"
Ya tambaya.

Fada masa tayi ya karasa yai parking ganin wajen ba kowa kuma alamar duk an shiga yasa ta bude motar da sauri bata tsaya fadin komai ba ta nufi hall din da gudu kallon ta ya tsaya yi, Jawahir dake corridor din hall din tana ta trying number Maryam ba a dauka ba ta kira Ummi tace ta fito amman suna hanya sam taki dauka tana ganin ta ta sauke wata ajiyar zuciya hannunta ta kama kawai sukai cikin hall din jaka suka ajiye suka karasa suka amshi booklet dan ba a raba exam question ba suka zauna. Sai da suka dauki awa uku suka fito.

Suna fitowa Jawahir ta kalli Maryam tace
"Me ya faru ne? Kikai latti."
"Mota ce ta lalace ga ba abin hawa, wannan yasa da kyar na samu wani ya kawo ni fa."

"Kai amman mungode masa Allah saka da alheri."
Sai da tai maganar Maryam ta mike da sauri ta fito tana duba wajen. Jawahir ta karaso tace
"Menene?"

"Ban masa godiya ba fa?"
Dariya Jawahir tayi tace
"Shine kika zo neman sa tsayawa jiran ki zai yi?"

"Ke kin fiya wasa wallahi."
Tace
"Bari na kira Baba naji ya motar an gyara."
Ta kira Baba yace an gyara ya jarabawar sannan ta kashe wayar suka koma karatu. Sai Yamma Baba yazo ya dauke ta suka koma gida.





****
Da wuri ta dawo daga makaranta, kasancewa yau juma'a kuma yau Abba zai dawo, jakarta ta ajiye a daki kawai ta fito ta shiga kitchen dan taya Ummi aikin tarbar Abba. Karfe daya saura suka gama komai, turare suka karayiwa falon suka kara hade gidan sannan duk suka wuce dakin su, Maryam ta shiga tai wanka ta fito ta shafa mai ta saka wata doguwar riga ash kala mai layi layin baki da fari, mayafin rigar ta yafa kan ta da yake a tsefe ta dago ta baya yayi kamar acuci maza tayi, turare ta shafa tai sallah, fita tayi ta isa dakin Ummi ta tadda Ummi na daurin dankwali, karasawa tai tana murmushi tace
"Ummi Amaryar Abba."

"Zanci kaniyar ki fa Daughter."
"To Ummi ni me nace?"
Ta amshi dankwalin tana fadin kawo na daura miki, ta amsa tai mata dauri mai kyau, Ummi ta karasa gaban mirrow ta kalli kanta tace
"Wannan daurin ai sai ku daughter."

"Ummi ki barshi wallahi har manya sunayi Kuma ke da ba fita zaki ba Abba fa zakiyiwa kwalliya."
Ji sukai an bude gate da sauri Maryam ta karasa ta bude taga motar Abba ta gani an shigo da ita labulen ta saki da sauri tace
"Abba ya dawo."

Ta fita da sauri yana fitowa tana karasawa ta durkusa tace
"Sannu da zuwa Abba."
Kamo ta yayi yace
"Yauwah My Daughter."

Ta amshi yar jakar sa da wata leda suka nufi cikin gidan, Yaa Farouk da Yaa Aliyu da dawowar su daga masallaci kenan suka biyo bayan su, a falo ya zauna Haidar ya haye cinyar sa, nan suka gaishe shi sannan suka mike suka fice falon Inna, Maryam da Haidar aka bari suna taiwa Abba surutu, duk da Haidar yafi cika dakin.

Tin kan Ummi ta karaso kamshin ta ya cika Abba, daga kai yayi yana kallon ta murmushi dauke a fuskar sa ta zauna tace
"Barka da zuwa Ranka ya dade."

"Barka da zuwa Madam ya gidan ya yara da kowa?"
"Alhamdulillah."
Ta mike ta isa firij din dakin ta dauko jug dake ciki ta zo ta tsiyaya masa lemon kwakwan da tayi a ciki, amsa yayi yace
"Nagode."

Ya kurba tare da lumshe ido, Maryam ta mike Abba yace
"Shiga kitchen akwai sakon Inna ki mika mata."
"To Abba."

Ta fada tana kamo hannun Haidar, Ummi tace
"Ki tafi mata da abinci."

Duk da basa bawa Inna abinci dan tace ita da kan ta zatayi bata son jagwalgwalo amman in sunyi sakakke suna aika mata, abun ta dauka ta nufi sashen Inna, tana karasawa ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Aliyu ta gani zaune yana kallon Inna dake bada labari sai wani murmushi yake kasa kasa, da gudu Haidar ya dafe shi ya rumgume shi yace
"My Son."
Lafewa yai a jikin sa Aliyu ya shafa kan sa. Inna ta bawa sakon sannan ta juyo tai kofa, Inna tace
"Oh ba zama zaki ba?"

"Kaina ke ciwo Inna zanje na kwanta ne."
"To kisha magani kinji je ki kwanta ki huta"
Ta fita Inna ta daura mita
"Haba ba dole kai yai ciwo ba kullum sai an fita ga karatu ko da yaushe kai mu kam munji dadi amman mutanen yanzu wahala kawai suke sha haba mu a da muyi zaman mu a gida miji na kula da kai amman yanzu kaine yawo karatu kaine yawo aiki kullum kana tsaye kana tafe duk kullum kana a kare."

Aliyu dai bai tanka mata ba, Inna ta juyo ta kalle shi tace
"Dadi na da kai miskilanci ina maka magana ka share ni bana son irin haka wallahi Ali."
"To ni nasan dani kike Inna?"

"To zan ta magana ne ni kadai haba dan Allah sai kace mahaukaciya."
"Inna ai naga wani lokacin kina tabawa."

"In abu ya ishen ba na rasa wanda zan fadawa kuma yana cina a rai ba."
"To ni dai naji shikenan."
Ya dauki Haidar ya fita. Ta bishi da kallon sa tace
"Dan jakar uba."
Yana ji yai murmushi kawai bangaren su suka koma ya shiga daki ya dauko magani ya bawa Haidar yace
"Je ka kaiwa Antyn ka."

Da gudu Haidar yaje ya same ta har ta kwanta ya hau kan gado yace
"Adda."
Ido ta bude yace
"Gashi inji Abbi yace ki sha."

Amsa tayi ta ajiye tace
"Je kace na sha."
"Adda bafa ki sha ba."

"Zan sha jeka."
Ta fada tana tura sa ya fita ya koma wajen Aliyu ya same shi zaune Aliyu yace
"Tasha maganin?"

"No Abbi tace inje zata sha wai."
Mikewa yai ya nufi kitchen ya dauko ruwa sannan ya wuce dakin ta tana kwance taji knocking ta amsa masa, tana kwance akan gado gashin kanta duk ya barbazu, jin an shigo yasa ta dago ganin sa yasa da sauri ta ja mayafin ta tana rufe kan ta dan bata zata shi bane, ya karaso yana kallo ta yace
"Kan ne?"

Kai ta girgiza ya mika mata ruwan yace
"Sha maganin."
Fuska ta bata dan bata son magani yace
"Bazaki sha ba."

"Nifa kan ya daina ciwo."
"Duk da haka ki sha nace."
Ya fada tare da daure fuska dauka tayi ta balla ta amshi ruwan ta sha hannu ta daure a kirji tana yarfe hannu tace
"Wayoo Yaya kaji shi ko bai tafi ba."

Da sauri ya mike ya juya mata baya sai kuma yace
"Kara ruwa."
Yana fada ya fice ta kara shan ruwan ta koma ta kwanta ta kamar zatai kuka.



**
Washe gari da yake weekend ne kuma shine na last a month din kamar yadda ya saba duk ending month yana daukar su ita da Haidar ya kai su, su dibi abinda suke so, tana kwance a daki rike da waya suna chat da Jawahir Haidar ya shigo da sallama yace
"Adda kizo inji Abbi."
Mikewa tayi ta yafa mayafi tabi bayan sa, yana tsaye a falo yana daura agogo ta karasa yace
"Ki fito yanzu."

Yai gaba Haidar yabi bayan sa, ita mema take bukata babu da ya barta ta zauna amman tasan ba kyale ta zai ba, to me kuma zata dauko a sama ta kalli kan ta kawai ta bi bayan su a haka a cikin mota ta same su ta zaune suka dauki hanya, suna zuwa suka shiga bata da abinda zasu dauka turare da mai ta dauka kawai sai chocolate da wasu ribom da ta gani, lokacin da a kaje biyan kudi Aliyu ya dinga mamaki dan abinda zata dauka baki ya tabe dan ya fara gajiya ace in ba shi ya dibar mata abu ba ita daga turare shikenan, gaba tayi dan ta riga su gaba tana tsaye jikin mota tana danne danne a wayar ta kamar ance ta ta dago taga wani tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana kallon saitinta ta cikin black glasses dake idonsa, mamaki ta fara shin ita yake kallo ko kuwa, baki ta tabe ta cigaba da abinda take dagowar da zatai taga ita yake kalla sosai, tunani ta tafiyi can ta dago sai taga ya cire glass din idonsa yana cigaba da kallonta da kyau, murmushi ta saki tunawa da a inda ta sanshi, dai dai kuma karasowar Aliyu ya bude booth aka saka kaya sannan ya juyo ganin bata shiga ba, wanda a lokacin ta daga kai tana kallon mutumin Aliyu yabi wajen da take bi da kallo wani abu yaji ya tokare shi ya karasa wajen ta yace
"Kinsan shine?"
Kai ta girgza da sauri ta bude mota ta shiga, ta dago tana kara kallon mutumin da bai fasa kallonta ba, Aliyu ya lura dan har yai reservse mutumin take kalla dan haka a guje yaja motar suka fice daga wajen.



Washe gari lahadi tin da tatashi taji yanayin jikin ta ya sauya, calendar ta duba ta zaro ido tana fadin
"Watakila gobe."
Gaban mudubi ta koma ta janyo tana dubawa ledar pad dinta, ta dauko taga saura daya komawa tai ta zauna sai kuma ta mike ta sauka kasa wajen Ummi zama tayi a kusa da ita tace
"Ummi ina son zan je supermarket in siya pad"
Ummi ta kalleta tace
"Naga jiya kuka je."

"Ummi na manta ban dauka ba."
Wanda fada kawai tayi dan in har da Aliyu zasu shopping kunyar dauka take a gaban sa wani lokacin ne ma shi da kan sa in zai karayo mata siyayya yake hadowa da ita to gashi tana tsammanin gobe yazo dole taje ta nemo ta kan yazo mata.

"Toh driver ya fita wa zai kaiki tinda ke kin ki, ki koyi mota ma."
"Ummi zani da kai na, kuma Yaa Farouk yace da munyi hutu zai koyan."

"Ya dai kamata Baba Anas ma ya huta da fitar safe ai."
Maryam ta mike tace
"Bana so magariba tayi min bari naje na shirya."

Ta haye sama, siket ne da t-shirt a jikin ta dan haka ta dauki katon hijab ta zura wanda ya saukar mata har kasa, sannan ta dauki purse da wayar ta ta fita, Ummi ta sama a falo tace
"Ummi na fito."
Waya ta dauka tai danne danne wanda wayar Maryam yai kara tace
"To sai kin dawo."

Maryam ta duba taga 5k Ummi ta tura mata ta rumgume ta tace
"Nagode Ummi."

Tunda Maryam ta fito Yaa Farouk dake jikin motar sa fita zai yi ko dawowa yayi oho dai yake hangen ta murmushi yake ta saki, ta nufo gate bama ta lura dashi ba lokacin Mama ta fito zata sashen Inna, Maryam ta durkusa tace
"Ina yini?"
Ko kallon

Please Login or Register in order to submit comment