Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani, gwara shi Muhammad ta sani kishi ne Aliyu kuma tausayi ne da kulawar da yake mata, dan tsaki ta saki tace
"Suna sani ina yin karya."

"Hello!"
Ya fada tace
"Uhmm ina jin ka."

"Nace dawa kike waya?"
"Yaya ne yana koya min wani karatu ne."

"Uhmm Yaya a wannan lokacin yake koya miki karatu."
"Eh!"

Kawai ta fada a dan fusace wannan yasa yace
"To shikenan sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
Ta kashe wayar kawai. Kwanciyya tayi tana mai rufe idon ta kawai.


A cikin satin Abba ya kira Muhammad akan ya turo magabatan sa akan zancen auren su da Maryam, Muhammad ma da yake a shirye yake yana fadawa Dadyn sa, Dadyn sa yasa ya tambaya yaushe zasu zo suka saka rana, lokaci nayi suka shirya da Dadyn sa da yan uwansa biyu da aminin sa sukaje, sosai akai musu tarba sukace dan su yaga yarinya yana so in an basu dama zasu kawo kudin saka rana da komai na biki dan su haka suke yi, su Abbi suka yadda akan haka.

Bayan wata daya suka dawo da kudin saka rana da sadaki har da lefe suka saka wata uku masu zuwa wanda a lokacin su Maryam sun samu hutu suna komawa shekara daya zasuyi karatu sun gama gaba daya.

Bayan tafiyar su Ummi da Mami suka shiga ganin uban kayan da aka kawo kamar wanda za a bude shago dasu, kaya ne masu kyau da tsada ko akwati nan har da ruwan gold aka hada aka yi su, Lokacin da Mama ta gani ba karamin tashin hankali ta shiga ba, dan Mama irin matan nan ne masu bakin ciki ba sa son abu ya samu wani sai su kadai, Inna kuwa sai saka albarka take har da kuka na murna Maryam zata samu gidan hutu mai sonta, gwala gwale kuwa an saka mata har guda uku, banda zobe da awarwaro duk a ciki, bangaren Ummi aka mai da kayan su Anty Asiya, Najwa duk sun zo sun ga kaya.

Maryam ce zaune a dakin ta tana neman layin Jawahir tana fara ringing ta dauka ta kai kunnen ta Jawahir tace
"Ke albishirin ki?"

"Goro ya akai?"
"An kai kayan auren Yaa Khalifa fa, nan da wata uku muna da biki."

"Ah haba Masha Allah Allah sanya alheri ya bada zaman lafiya."
"Amin."

"Nima yau aka kawo lefe na fa."
"Me?"

"Abinda kika ji."
"Dan Allah da gaske kike ko wasa kike?"

"Wallahi da gaske nake."
"Lallai ma Maryam amman da waye wannan, ko da yake bama sai kin fada ma nasan yar gida za ai ni nasan shiyasa ma baki fadan ba dan kina ta boye boye ko? Allah Maryam baki kyauta min ba ace za a kawo kayan auren ki ban sani ba sai bayan an kawo."
"Kiyi hakuri daga zuwa tambaya fa su Abba sukace ayi komai a gama shine fa suka hado komai da komai ai ba yanzu bane bikin sai mun gama da asibiti."

Wayar kawai Jawahir ta kashe ta tafi wajen Momyn ta, tana daki ta shiga tace
"Momy kinsan me?"
"A'ah."

"Yau aka kai kayan auren Maryam fa."
"Wacce Maryam."

"Maryam dina amman Momy wai yanzu take fada min"
"To kiyi hakuri kila sha'afa tayi yanzu ba gashi ta fada miki ba."

"Bari naje gidan nasu."
"Ki gaishe da Ummin tata kice ina mata Allah sanya alheri."

Ta fita driver ne ya kai ta, tana shiga ta wuce dakin Maryam kwance ta same ta suna waya da Muhammad tana shiga ta katse wayar tana fadin
"Tuba nake."

Zama tayi tace
"Ai kya tuba tunda kin min laifi."
"Ai na fada miki uzuri na."

Baki ta tabe tace
"Ina kayan?"
"Suna dayan dakin kije ki gani."

"Ke fa?"
"Ni kunya nake ji wallahi."
Mikewa tayi ta fita acan ta samu su Ummi suka gaisa Ummi tace
"Sai kikaji an kawo kaya?"

"Ai yanzu na gamai mata Ummi bafa ta taba fada min ba."
"Ai abun ne yazo a haka ba mu zata haka da wuri za ai ba."

"Allah sanya alheri."
Jawahir ta matsa wajen kayan tana kalla tin daga akwatin nan taso ta shaida kayan amman ganin wannan lokacin su ake yayi yasa ta share kawai ta fara kallon kayan wasu ta sansu dan Momyn ta ita ta hada kayan wasu ita tayo order Muhammad ya gani yace yana son su amman sai ta share a haka ta gama gani ta koma wajen Maryam tace
"Wai waye wannan mai sa'ar?"

"Ki bari zan kirasa sai ku gaisa."
"Bana so sai yanzu."

"Nifa ba laifi na bane."
"Laifin waye?"

"Nashi ne."
"Hmmm."

Wayar Maryan tai kara ta dauka takai kunne ta mike ta fita, yace
"Ke da waye ne?"
"Jawahir ce tazo tana ta mita ban fada mata za a kawo kaya ba."

Dariya yayi yace
"Jawahir kenan jiya ta ishe ni da sai na kai ta wajen Antyn ta."
"Yanzu dai na fada mata anjima zaka zo sai ku gaisa ko?"

Dariya yayi yace
"Shikenan sai anjima zan biyo sai mu wuce gida tare."
"Shikenan."

Sai bayan magariba yazo suka fita dan a bakin gate ya ajiye motar, yana ganin su ya fito, ido Jawahir ta zaro tana zancen zuci kenan abokin Yaa Khalifa ne saurayin Maryam kenan tare zasuyi aure haba no wonder naga wasu kayan iri daya da nasa.

Karasowa yayi yace
"Lil sister."
Jawahir leke leke take tana son ta ga ta ina zataga saurayin Maryam, Muhammad yace
"Me kike nema ne?"

Kallon sa tayi tace
"Kai da wa kazo?"
"Ni kadai."

Ya fada yana maida kallon sa kan Maryam ya dan matsa gefen ta yace
"My wife!"
Ido Jawahir ta zaro, Maryam tai kasa da kai tace
"Ina yini?"

"Lafiya lou yasu Ummi da Haidar?"
"Kowa lafiya."

Ya kalli Jawahir da ta kasa magana sai kallon su take ya sakar mata murmushi yace
"Finally meet ur in-law Maryam."
Ya kalli Maryam yace
"You too meet your sister in-law Jawahir!"

"Please Yaya are u serious?"
"Yess!"

Wata rumguma taiwa Maryam tace
"Da gaske Sister?"
Kai ta gyada sai ta fada jikin Muhammad tace
"Amman Yaya naji dadi sosai kasan wacece kuwa Maryam wallahi ka dace Allah ya barku tare ya bada zaman lafiya amman kun dace da juna."

"Ni kadai nai dace?"
Dariya tayi tace
"Itama tayi dace amman ai ba zan yabe ka ba kar taga kamar dan d'an uwa nane ta gani da kanta."
Murmushi kawai Maryam take, Jawahir tace
"Amman Yaya tin yaushe kuke tare?"

Maryam ya kalla yace
"Tin kan na ganta a gida na santa."
Ido ta zaro tace
"Amman kuka dinga boye min ko? Sam ban taba ganewa ba kai Yaya? Ko da yake ita ce ma"

"A'ah ba ruwan princess, saboda ni na hanata fada miki nasan ki da surutu."
"Oh ko? Ai kuwa zakaga ina da surutu sai naje gida duk na fadawa kowa na gidan nan har Dady."

Maryam tace
"A'ah ni dai kiyi hakuri."
Dariya tayi tace
"Nasan wa kike jin kunya wallahi ita zan fara fadawa kai koma kiranta zanyi ne tin kan na koma gida."
Hararar ta Maryam tayi tace
"Ni zan shiga gida sai da safe."

Muhammad yace
"Ok sai munyi waya."
Ta kalli Maryam tace
"Bye."

Jawahir dake cike da mamaki na wai da gaske dai Yayan ta shi zai auri aminiyar ta, tace
"Ok bye."
Suka shige mota suka bar wajen.


Canada
A gajiye ya shigo gidan ya samu Mami da Basma na kallon waya, karasawa yai ya leka yace
"Me kuke kalla?"
Basma ta dago tace
"Yaya lefen Maryam aka kawo."

Cak ya tsaya, jin kamar bai ji mai tace ba yace
"Laifen wa?"
"Laifen Maryam."

"Wacce Maryam?"
"Ta Ummi mana."

Mami ya kalla dan samun karin bayani yace
"Mami da gaske ne wai?"
"Kai ta gyada tace
"Eh an kawo lefen Maryam yau an saka wata uku kaga lokacin ma kana can za ayi."

Bai kuma magana ba sai hanyar dakin sa da yayi, yana shiga ya zauna a gefen gado kansa ya dafe jin abun a bazata wai an kawo lefen Maryam wato aure zatayi kai ya dafe ya dauko wayar sa neman layin ta ya fara amman ba a dauka ba sai da ya kira sau uku amman ba a dauka ba wayar sa yai cilli da ita ya runtse idon sa.

Mikewa yayi ya cire kayan sa ya shiga yin wanka, yana fitowa ya haye gadon ya kwanta wani iri ya dinga ji a cikin zuciyar sa, daga baya ya tashi zauna yana jingina da gado, ido ya lumshe kawai yana tunanin wani abu, daga baya ya mirginawa ya kwanta wayar sa yaji tana kara da sauri ya tashi ya dauka yana dubawa ya zata zai ga Maryam ce amman sai yaga Ummi ce sai da ta kusan tsinkewa ya dauka ya kai kunnen sa yai sallama cikin sanyin murya.
"Lafiya Dr?"
"Ina yini Ummi?"

"Lafiya me yake damun ka?"
"Ba komai."

"Anya kuwa Dr?"
"Ba komai Ummi."
Yai maganar cikin jarumta dan bai so ta san halin da yake ciki.

"To shikenan na bugu na fada maka an kaso kayan Maryam ne."
"Ok."

"An saka wata uku."
Numfashi ya fesar mai zafi yace
"Allah kaimu lokacin."

"Amin."
"Ina Haidar?"

"Yana wajen Inna."
"Ok sai anjima kaina ciwo yake Ummi zan dan kwanta ne."

"Ni ai nasan akwai abinda yake damun ka kasha magani kaji."
'To."
Kawai ya fada ya kashe wayar, kan sa ya dafe yana kwanciyya ido ya rufe so yake ya runtsa amman ya kasa wani irin yake ji a zuciyar sa abinda bai taba ji ba kenan.


*
Maryam na shiga daki ta ga missed call din Yaa Aliyu, zama tayi tana dafe zuciyar ta dan tinda Muhammad ya turo iyayen sa take cike da wani fargaba ba kamar yau da aka kawo lefen ta gaba daya ji tayi ta rasa nutsuwar ta, fara neman layin nasa tayi amman har ta gama ringing bai dauka ba sai da ta kira sau uku amman bai dauka ba ajiye wayar tayi sai kuma ta dauka ta fara rubuta masa sako
"Yaya ina ka shiga haka? Naga missed call din ka na kira baka dauka ba. Ya kake ya aiki?"

Ta tura masa yana kwance yaga dukkan missed din nata amman bai dauka ba jin shigowar sakon ma yagani amman bai duba ba sai matsar da wayar da yayi, dan ya rasa hope me ma zai fada mata, me zaice mata, hakika ya fara sarewa, ranar kwana yayi bai bacci ba kan safe ya farka da wani ciwon kai, da zazzabi da kyar ya shirya ya fito, a falo ya samu Mami tana zaune ya durkusa ya gaishe ta, ta kalli shi tace
"Dr me yake damun ka ne?"

Ido ya lumshe ya mike yace
"Zani asibiti Mami bana jin dadi ne."
"To sannu Allah sauwake."

Ya mike ya fita, a asibiti sai da aka saka masa ruwa da magunguna amman kamar dada masa ciwo ake. Sai yamma ya koma gida ba kowa a falo dakin sa ya koma ya kwanta kawai. Sai bayan goman dare Mami taga bai dawo ba ta leka taga motar sa a waje dakinsa ta shiga ta same shi kwance cikin bargo yana rawar sanyi da sauri ta karasa tana fadin
"Subhanallah Aliyu jikin ne?"
Ta karasa ta dafa sa zafi taji a jikinsa ta dauke hannu da sauri tace
"Innalillahi wainna illahir rajiun."
Ta mike ta fita da sauri mai gidan ta ta fadawa, ya shigo ya daga shi yana fadin
"Sannu Dr!"






*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan, Allah mana rahma. Amin.*



*Antty*
[11/29, 18:54] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 64

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Wayar sa ya dauka ya kira likita ba ajima ba likitan ya karaso, taimako ya bashi wanda nan da nan zazzabin ya sauka, bacci ya dauke shi, washe gari da ciwon kai ya tashi sai rashin karfin jikin sa. Wanka kawai yayi ya koma ya kwanta wajen karfe takwas Mami ta shigo dakin a gefen gado ta zauna ta taba jikin sa, ido ya lumshe yana me kokarin mikewa
"Yi kwanciyyar ka Aliyu."

Kwanciyya yayi yace
"Ina kwana Mami?"
"Lafiya lou Son ya jikin?"

"Alhamdulillah."
"Allah kara sauki."

"Amin Mami."
Fita tayi bata jima ba ta dawo da kayan abinci taimaka masa tayi ya zauna tana fadin
"Kaci abinci sai kasha maganin ko?"

"To Mami."
Ta fara bashi kadan yaci yasha magani ya koma ya kwanta, maganin da ya sha shi yai ta saka shi bacci dan ranar yini yayi yana bacci Ummi ta kira ma sai Mami ce ta amsa wayar tace yana bacci, sosai Mami ta kula da Aliyu, haka yai ta ciwo a daddafe a daddafe wanda lokaci kadan ya rame da yaje asibitin su akai masa check up likita yace ya rage tunani da damuwa.


Maryam ma ba karamin damuwa tayi da rashin kiran nasa ba, gashi Ummi tace mata bai da lafiya ko ta kira baya dauka wani lokaci ne ma Mami ke dauka ko tace yana bacci.


*
Zaune suke, Maryam sanye da Hijab har kasa, kanta a kasa sai murmushi take, Muhammad yace
"Oh dariya na baki, Yes I have been counting down since but kamar ba a tafiya fa."
Zaro ido tayi ta kallesa, yace
"Sure, ni daman a rage wallahi da yawa lokacin"

"Aa ba wani lokaci mai yawa."
Ya lumshe ido ya bude yace
"Wallahi da yawa Baby"

Maryam ta kallesa tace
"Kamar yau ne fa in muna raye"
"Toh Allah ya kai mu lafiya"

Tace "Ameen"
Yace "Promise me something please...."
Maryam tayi shiru tana kallonsa, yace "Ki min alkawarin baza ki yi betraying din soyayyata gare ki ba, and I am also promising u same, I will and will never leave u for any reason"

Lokaci daya jikin Maryam yayi sanyi tace
"Ae an riga an baka ni, so there is nothing to worry about"
yace "Sure an san ni, but I am afraid of ur cousins"

Da mamaki tace
"Cousins dina kuma? Again?"
Ya d'an yi murmushi yace "Yes kada su min fin karfi...."

Maryam ta kasa daina masa kallon sa da mamaki tace "Sau nawa zan ce maka su Yaa Aliyu Yayyena ne ba so na suke ba"
Muhammad ya girgiza kai yace
"I saw their reactions ranan, more especially wanda baya garin nan"

Maryam gabanta ya shiga faduwa, Muhammad yace
"They might not tell you now amma kada watarana su zo su ce suna sonki, ki mance alkawarin mu, kada ki min haka please Maryam..."
Cike da damuwa ya fadi haka, Maryam ta ji kamar ta fashe da kuka tace
"Ni ka daina cewa haka, ba wanda ke so na cikinsu duk yayyena ne su wallahi, ba komai tsakanin mu, sanin tarihi na bashi zai saka kana jin haka akan su ba, suna so na kamar yadda suke son yan uwan su, haka suke ga duk kannen su, shiyasa nima suke treating dina thesame, they are only disturb saboda kar naje inda za ai min gori ko na samu matsala."

yace "Toh Allah ya sa haka, amma ba sai kin min kuka ba gimbiyata, reminder ne"
Maryam ta boye fuskarta da Hijab, yayi murmushi yana kallonta, murya can kasa yace
"I love you."

"I do love u too."
Agogo ya kalla ya mike yace
"Am going My Happiness."

"Since now?
"Yes Ammi ta aiken so that is why."
Ta mike ta rakasa gate, ya juya yana kallonta kafin yace komai, a hankali tace "Thanks so much."


*
Bayan sati daya, wayarta dake hannu ta danna sannan ta kara a kunnen ta, Aliyu na kwance ya mike yana duba wayar, yana ganin sunan ta ya runtse idon sa yana tunani ya dauka ko kuwa yana son ya dauka baya son ya kara fama inda ke masa ciwo ba, har wayar ta katse yana tunanin, sai da wayar ta kara shigowa sannan ya dauka ya kai kunnen sa tare da yin sallama, amsawa tayi tana fadin
"Yaya ya jikin ka?"

Ido ya lumshe yace
"Alhamdulillah."
"Yaya me yake damun ka?"

"Ciwo ne daga Allah."
"To Yaya kana cin abinci?"

"Eh."
"Magani fa?"

"Eh."
"To Allah kara sauki."

"Amin ya makarantar?"
"Alhamdulillah."

"In Son dina?"
"Yana nan."

Sukai shiru a hankali tace
"Yaya ranan naga missed call din ka na kira baka dauka ba daman zan fada maka cewar an kawo....."
Tari ya fara da wata irin kwarewa yayi sai kace shine yake maganar nan ta hau masa sannu amman ina sai da ya ajiye wayar da kyar tarin ya tsaya ya koma ya kwanta yana dafe kirjin sa, yana mamakin kansa Bai san yaya zai ba, amman zai daure ya cire damuwar nan ya karasa abinda yazo yi ya koma gida shi kuma tashi kalar kaddarar sa ya rasa matar sa ga wata jarabawar Allah ya bashi ikon cinye jarabawar sa amman halin da yake ciki a yanzu yana ji a da bai shiga kamarsa ba, kwanciyya yayi sai kuma ya mike yana jingina da gado.

A haka ya dinga ciwon sa shi kadai yasan me yake damun sa Mami sai dai taga duk ya rame ya kara rage magana da walwala kuma in tai magana sai yace ba abinda yake damun sa har ta hakura ta saka masa ido. A haka ya cinye sauran lokacin sa ya fara shirin komawa, haka ya shiga kasuwa yayo wa su Maryam da Haidar tsaraba mai yawan gaske. A haka yai booking flight ya sanar da Ummi zuwan sa.

Maryam na zaune sukai waya da Aliyu duk da danna waya take amman gaba daya hankalin ta na kam wayar da Ummi keyi suna gamawa ta juya tana fadin
"Ummi Yaya ne zai dawo."

"Eh shine zai dawo jibi."
"Masha Allah. Allah kawo shi lafiya ya tsare. Amin."

Murna Maryam kasa boyuwa tayi sai dai can ta koma ta zauna tana fadin
"Ni kwana biyu yama daina kira na tinda yayi ciwon nan."

"Haka Mamin ku ke min complain ya daina walwala gaba daya."
"Uhmmm."

A satin Maryam ta gyarawa masa dakin sa, ta wanke ban dakin sa komai yakoma fess dashi. Ranar da zai dawo kitchen ta shiga ita ce girka wannan dafa wancan ita da Haidar sai murna suke suna gamawa ta shiga suka shirya ita da Haidar dan zuwa tarbar sa.

Saukowa take daga bene sanye da doguwar riga orange kala mai haske, tayi rolling kanta da mayafin rigar da aka sakawa stone coffe kala, sai tashin kamshi take waya ce kare a kunnen ta, falon ta sauko ta tadda Ummi ma a tsaye kallon Ummi tayi tace
"Ina Haidar din?"

"Ya fita."
"Muje to."
Suka fita, a harabar gidan suka same shi tsaye yana ganin su yace
"Ummi kuyi sauri."

Ummi tai murmushi, suka karasa wajen mota driver ya bude Haidar ya shiga gaba, Maryam da Ummi suka shiga baya motar suka tayar suka bar harabar gidan.

Suna isa Airport din taji gaban ta yai wata muguwar faduwa, da sauri ta daura hannu ta ta dafe kirjin ta, ta bude mota ta fita, a lokacin har jirgin su Aliyu ya sauka an fara saukowa, Haidar sai lekawa yake kamar ance ya daga kansa ya hango Aliyu tafe yana jan trolly dinsa, Sanye yake da bakin dogon wando da ornage kalar riga mai dogon hannu sai top baka, idon sa sanye da bakin glass, kafar sa cikin takalmin sa sau ciki, ya kara haske sai dai ya rame, Haidar dake rike da Ummi ya saki hannu Ummi ya kwasa a guje yana fadin
"Abbi! Abbi!"

Yadda Haidar ke kiran Abbi yaja hankalin mutane da yawa a ciki har da wata mata da miji da suma saukar su daga jirgin kenan, matar na da ciki sai mijin ta dake rike da hannun ta dayan hannun yana jan trolly, tsayawa kallon yaron sukai, da sauri Maryam ta dago ta hango Aliyu yana murmushi kafin ya durkusa ya bude masa hannu Haidar ya fada jikin sa yana fadin
"I miss you Abbi."

Rungume shi Aliyu ya karayi a jikin sa yana jin wani so da kaunar yaron na dada shigar sa,
"Miss you my Son!"

Sun jima a haka sannan Aliyu ya mike dashi suka nufi wajen Ummi, Maryam na ganin sa gaban ta ya kara yankewa ya fadi da sauri ta juya tana dafe kirjin ta, da kallo kawai ya bita ya karasa ya durkusa a gaban Ummi, Mata da mijin da suka kasa daina kallon Aliyu da Haidar ne suka sauke wata ajiyar zuciya, sannan suka kalli juna, Matar ce tace
"Honey kaga abinda na gani kuwa?"

"Na gani Baby."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Yaron yai kama da Yaa Haidar sosai."

Ajiyar zuciya mutumin ya sauke yace
"Ina ma Haidar ya bar baya, da tabbas ni zan maye masa gurbin mahaifin sa amman Allah baiyi ba."

Idon matar ne ya ciko da kwalla, mijin ya saka handkerchief ya goge mata yana fadin
"Ki musu addu'a kawai."
Hawaye ne ya zubo mata,
"Ko dai......"

"Ko dai me? Kila kamace, kina ganin yaron da uban suna kama suma, kawai dai kama ce."
Kai ta gyada tana goge hawayen dake zuba a idon ta, janye ta yayi suka bar wajen suka nufi inda su Aliyu suke, da suka karasa sai da suka kara kallon su Aliyu da Ummi ta dafa kansa tace
"My Son barka da zuwa."

"Yauwah Ummi da fatan na same ku lafiya."
"Alhamdulillah!"

Kai suka dauke, Maryam kuma jin gaban ta na tsanan ta faduwa ta dago da sauri, tana kallon mutanen wata irin juwa taji tana mata yawo aka, da sauri ta dafe kanta tana mai cigaba da kallon mutanen da suka nufi fita a wajen, Ummi ce ta juya taga Maryam a wani hali dafe da kai dayan hannun akan kirji da sauri ta karasa tana fadin
"Lafiya."

Hanyar da mutanen suka bi ta hau nunawa Ummi ta kalli wajen taga mutane na wucewa da sauri ta dawo da kallon ta gun Maryam wacce take kokarin zubewa a wajen da azama Aliyu ya taro ta yana fadin
"Daman bata da lafiya ne?"

Kai Ummi ta girgiza daukar ta yayi cak, suka bar wajen a cikin mota ya kwantar da ita yana bata taimakon gaggawa, da kyar numfashin ta ya dawo sai kuma bacci da ya dauke ta, gida suka nufa suna shiga ya bude mota ya dauke ta sukai ciki, dakin sa dake kasa ya shga da ita ya ajiye ta akan gado, first aid box ya dauko yana dubata sannan ya dauki wayar sa ya fara neman layin Farouk.

Yana dauka yace
"Ga text nan na maka kai sauri ka kawon magungunan."
"To Hamma."
Ya kashe wayar, Ummi ya juyo ya kalla yace
"Ummi me yake damun Maryam?"

Zama tayi a gefen gadon tace
"Bata fada min ba, kamar yadda kai ma kaki ka fada min, Aliyu ka ganka kuwa? Kalli yadda ka rame Aliyu me yake damun ka dan....."

"Kar ki hadani da Allah Ummi, zan fada miki insha Allahu."
Kai ta girgiza tace
"Zurfin ciki ba inda zai kai ku, gwara ku fito, ku fadi abinda ke damun ku ko a taimaka muku."

Murmushi yayi ya mike yana fadin
"Bari nai wanka."
Ya dibi abinda zai bukata ya shiga bandaki, da shirinsa ya fito ya samu Ummi bata dakin sai Haidar, ya dauke shi suka fita yana tai masa surutu shekara daya kawai amman sai yaga yaron ya girma sosai, a falo suka zauna Ummi ta sauko tace
"Dr Abinci fa?"

"Ummi sai anjima bari naje wajen Hajiya Inna."
Ya fita rike da Haidar, bai jima da fita ba Farouk ya shigo rike da ledar magani, amsa Ummi tayi tace yana wajen Inna can ya tafi yai masa sannu da zuwa tare suka tafi wajen su Mami da Mama da ta amsa masa sallamar ba yabo ba fallasa.

Sai da akai isha'i suka dawo kuma har lokacin bacci Maryam take, da kyar Ummi ta matsa masa yaci abinci sannan ya koma daki, a yadda ya barta a haka yazo ya same ta, ya zauna a resting chair yana danne danne a waya, motsin ta yaji, ya kalle ta mikewa tai zaune tana kalle kallen dakin,
"Sannu."

Taji muryar sa da sauri ta juyo sai ta dauke kanta ya karaso ya zauna agefen ta yace
"Me yake damun ki?"
Kai ta girgiza ya kure ta da ido tai saurin yin kasa da kai yace
"Fada min."

"Yaya ba komai."
"Haba My Baby Sis tell me kinji."

Da sauri ta dago tana kallon sa shima ita yake kalla, ya rame sosai, kai ta dauke tace
"Yaya baka da lafiya ne?"
"Me kika gani?"

"Duk ka rame."
"Kema haka?"
Kai ta kas dashi ta dire kafar ta a kasa tana fadin
"Bari naje daki."

Kan yai magana ta fice, ya koma ya zauna yana jingina da kujera, daki ta shiga ta cire kayan ta tai wanka, tare da daura alwala, tana fitowa ta saka kaya ta hau yin salla sai da ta idar ta fara addu'a sannan ta dafe kanta, tunani ta fara me ya same ta haka? Kasa tuno komai tayi wannan yasa ta mike ta haye gado, tana kwanciyya ana bude dakin, ta dago tana kallon Ummi, ta shigo, mikewa tayi tana kallon ta, Ummi ta zauna a gefen gado, ta kamo hannun Maryam tace
"Me yake damunki Daughter?"

Kai ta hau girgizawa sai hawaye kuma, Ummi ta daura hannun ta akan fuskar Maryam tana goge mata hawayen dake kan fuskar ta, kai ta girgiza mata tace
"Ki daina kuka kinji daughter me yake damun ki fada min."

Ta bude baki zatai magana kenan aka bude dakin Aliyu ne ya shigo hannun sa rike da leda, ya mikawa Ummi yace
"Ummi taci abinci ta sha maganin nan kan gobe mu shiga

Please Login or Register in order to submit comment