Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san komai nawa ba bansan kowa nawa ba!"

Ya karanta ya dago ya kalle ta sannan ya mika mata yace
"Kika ce sunan ki Maryam!"
"Eh Sunana Maryam Muhammad Jabeer!"
Ta rubuta masa, kai ya gyada yace
"Tayaya kika san sunan ki?"

"I didn't know!"
Ta bashi amsa a rubuce ya kalle ta yace
"Wa zaki iya tunawa a rayuwar ki!"

Hawaye ne ciki idon ta ta fara rubutu tace
" *Mijin Maryam* miji na kawai zan iya tunawa Yaa Haidar!"
"Where is he?"

"I just didn't know i only know Yaa Haidar as my husband and i loss him from their i can't recall any thing except My Ammi."
Kura mata ido yayi can ya dauke kansa yace
"Ummi na macece mai tausayi da son taimako i hope zaki zauna da ita tsakani da Allah kuma ba zaki cutar da ita ba!"

Kai ta gyada tai masa bayani da hannu kan cewa bazata cutar da ita ba. Ta gode kuma. Kai ya jingina da kujera yace
"Yanzu me yake damun ki?"

"Komai ciwo yake min bana jin dadin komai na rayuwa!"
Ta fada idon ta na cikowa da kwalla. Tausayin ta ne ya kama Aliyu yace
"How old are you?"

"Seventeen year old!"
Tai masa nuni da hannu.
Tausayin ta ya kara ji dan yarinya ce sosai ace tana cikin irin wannan rayuwar ga ciki ba miji and babu iyaye ko wani nata yanzu in da ba Ummi ce ta dauko ta bafa wane hali zata shiga.

Waya ya dauka yai magana da daya daga cikin nurses din sannan ya ajiye wayar ya cigaba da aiki a system din sa. Ba a jina ba akai knocking ya bada izinin shiga nurse ce ta shigo tace
"Gani Dr A.S"

Paper ya zara yai rubutu yace
"Gasu nan wadan nan test din nake so ai mata ina son result din yanzu, wanda ba zai samu yau ba ayi kokari a samar min su gobe."
Amsa tayi ta kalli Maryam dake kwance jikin table din nasa.

Kallon ta yayi yace
"Ko ba zaki iya bane a kawo kujera?"
Kai ta girgiza ta mike a hankali tana cije baki,ย  nurse din ta kama hannun ta suka fara tafiya a hankali. Da ido ya bisu har suka rufe kofar dakin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kan sa da jikin kujera.

Awar su biyu da fita suka dawo da Maryam direct kan gadon dakin ta wuce da ita dan ba karamin galabai ta tayi ba ga zazzabi ga yunwa ga ciwo. Kwanciya tayi, Aliyu yana kallon su sanna Nurse din ta karaso ta mika masa result din amsa yayi ya duba agogon hannun sa 3:52pm lokacin sallah la'asar yayi dan gashi can ana tada harama mikewa yayi ya fita a office din masallaci yaje bayan an idar da sallah ya dawo.

Wayar sa dake aljihun sa ta hau kara zarowa yayi ya tsaya kallon kiran har ya katse sannan ya bi kiran yana saka wayar a kunnen sa. Amsa sallamar yayi yace
"Ummi ta biyo 'yar ta!"
"Na kira dai naji ya jikin nata?"

"Da sauki Ummi tana office tana bacci yanzu zan koma!"
"Alright me ta ci kuwa dan yau bata ci komai ba!"

"Ba abinda taci bari naje na tambaye ta me zataci!"
"Ok please ka kular min da ita."

"Insha Allahu!"
"Allah maka albarka ya kiyaye ku!"

"Amin ya Hayyu ya Qayyum Ummi!"
Ta kashe wayar ya tura kofar office din tana kwance ya karasa bakin gadon yana kallon ta. Kai ya dauke yace
"Anyi sallah fa!"

Hannun ta da daura akan ta tai masa nuni da jiri take ji!. Nurse din dazu ya kira yace
"Take her in and perform abulution!"

Ta kama ta suka shiga bandakin tayi alwala suna fitowa ta shimfida mata sallaya ta zauna a zaune tai sallah. Bayan ta idar ya mike ya dawo gaban ta ya ajiye mata memo da pen yace
"Kina jin yunwa ne?"

Kai ta gyada masa yace
"Me kike so kici?"
Da hannu tai masa alamar da ba komai. Ya dan kalle ta ya dauke ido yace
"Ba abinda kike sha'awa?"

Kai ta gyada masa. Mikewa yayi ya koma kan kujera ya dauki folder da aka kawo da result na test da screening da akai duk ya duba sannan ya dauki waya yai typing sannan ya ajiye bayan minti na Messenger sa ya shigo da katuwar leda. Ajiye masa yayi. Aliyu yai godiya sannan ya hau rubutu bayan mintina ya dago ya mika masa yace
"Ka amso min a permarcy!"

Ya amsa ya juya ya fita. Bai jima ba ya dawo da leda guda ta magunguna da allurai ya bashi ya amsa ya kara godiya. Mikewa yayi a hankali ya dauki ledar magani da wacce ya shigo da ita dazu ya koma gaban Maryam da kan ta ke kasa.


Durkusawa yayi ya bude ledar farko ya ciro park uku daya shinkafa da miya ne, daya fried rice, daya tuwo ne miyar taushe sai ya fito da dayar ledar da suke dangin snack ne meat pie, cake, semosa, spring roll, da sauran su. Sai lemuka kala kala daban daban yace
"Ki zabi abinda zakici kinji!"

Dagowa tayi ta kalli gaban ta taga kayayyakin ba abinda ya bata sha'awa a ciki amman yadda cikin ta ke jin yunwa yasa ta dauki spoon ta dibi fried rice din tana kaiwa bakin ta, ta bata fuska kamar zatai kuka ya dan kalle ta ta gefen ido yace
"Mene ne?"

Kai ta girgiza sai ta dauki spoon din ta dibi rice and stew din, shima bata fuska tayi sai ta ajiye spoon din dan duk basuyi mata ba. Maltina ta dauka ta bude ta sha kadan ta ajiye tana mai da numfashi a hankali da sauri ta mike wanda batai aune ba ta zame kara kokarin mikewa take ta kasa yazo ya kamata yana fadin
"Mene ne?"

Kokarin mikewa take dan amai take ji amman ta kasa gane mai take nufi yasa ya dago ta suka shiga bandakin tana rike a hannun sa. Suna shiga ta shiga yin aman wanda dan abinda taci ta harar sai kuma kakarin da take tana yi yana shafa bayan ta har ta gama ya bata ruwa ta dauraye bakin ta sannan suka fito tana rike da hannun sa. Kan gado ta koma ta kwanta ya bita da kallo.




*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu xuwan yasa mu cika da kyau da imani.*

*Antty*




[11/19, 12:34] Maryam S Indabawa๐Ÿฅฐ: ๏ปฟ๐Ÿ’—๐Ÿ’— *MATAR HAIDAR* ๐Ÿ’—๐Ÿ’—
Page 43

By
*MARYAM S INDABAWA*

Hakuri da Juriyya Online โœ
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


*Wannan shafin naki ne, Zarah Muhmmad Sani Kibia (My Habibty) ina godiya, Allah ya bar kauna da zumunci Allah ya baki zuri'a masu albarka ya kara muku fahintar juna tsakanin ki da mijin ki Amin.*

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli kayan abincin da ba abinda ta taba, rufewa yayi ya koma ya dauki ledar maganin ya hada ruwan da zai saka mata ya hada allura da wacce ya zuba a ruwan ya saka mata. Tana bacci taji shigar allurar a hannun ta ya saka mata ruwa, bude ido hawaye na zubo mata dan zafin da taji yace
"Sannu!"
Ido ta lumshe tana ji yace
"Gyara na miki allura!"

Idon ta ne yai raurau dan tasan faman da suke da Yaa Haidar a gida ma kenan in bata da lafiya.
"Bafa da zafi zan miki ba!"
Ya fada yana kallon ta.

Kalaman Yaa Haidar kenan in zai mata allurar yace ba da zafi zai mata ba. Juyawa tayi ya dage hijab din ta doguwar ta bayyana ta ciki ya zura allura ya zira mata wata yar kara ta saki sai kuma ta fashe da kuka a zuciyar ta take kiran Ammi, Ammi nah! Yatsa ya saka yana mulmula wajen sannan ya mike a hankali ya koma wajen da yake zaune.

A hankali yasaka zuwan ruwan saboda yabi jikin ta sosai. Wannan yasa tin hudu har shida leda na biyu ko rabi bai yi ba. Wayar sa ya dauka ya kira Ummi. Ummi da ke hanyar komawa gida ta daga kira ta na fadin
"Ba dai kun dawo ba na nan ba?"

Maryam ya kalla sannan yace
"Aah muna asibiti ruwa nake kara mata daga wannan ya kare zamu taho sai bayan magariba."
Ya fada yana kallon agogon hannun sa dan lokacin shida har ta gota.
"Ya dai jikin nata?"

"Ummi da sauki!"
"To Allah kara sauki. Allah dawo daku lafiya."

"Amin!"
Ya kashe wayar ya shiga yai alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da akai isha'i. Nurse din da yasa ta kula da ita tana zaune ya shigo ta mike da sauri. Ya kalle ta yace
"Ta tashi ne?"

"A'ah!"
Ruwan ya kalla yaga saura kadan bai fi minti biyar ba zai kare. Zama yayi a kujera yana danna system din sa. Bayan minti hudu ya mike ya karaso wajen ya zare mata ruwan sannan ya koma ya cigaba da aikin sa.

Karfe takwas ya rufe system din sannan ya saka a jaka ya mike ya nufi bakin gadon nata.
"Maryam!"
Ya fada zuciyar na bugawa. A hankali ta motsa tana bude idon ta. Kai yai saurin kaudawa yace
"Tashi mu tafi ko?"

Kayan abincin gaba ta ta kalla ta zuro kafar ta kasa ta sauko ta zauna a gaban abincin tuwon da bata ci ba ta bude ta fara ci sai dai batai loma uku ba amai ya taso ta yunkura zata tashi ya rike ta yana fadin
"Ki daina tashi a gujen nan fa."

Kan ta kwace jikin ta ta dinga kwara aman anan wajen. Sai da ta gama ya daga ta suka shiga ta dauraye bakin ta sannan ya kira nurse yace a gyara office din a bawa messenger sa key.

Maryam yasa daya daga cikin nurse din ta kamo messenger sa ya dauki jakar system din sa da magunguna ya bi bayan Aliyu. Mota ya shiga ya zauna messenger ya bude gidan baya ya saka masa kayan nurse din suka karaso da Maryam ta bude dayan side din ta saka ta rufe mata kofa tace
"Allah kara sauki!"
Kai ta gyada Aliyu ya amsa da
"Amin ya Hayyu ya Qayyum!"

Sannan ya tada motar yana motsa bakin sa dake tasbihi a haka suka fuce daga asibitin yana driving cikin nutsuwa da sannu da sannu suka karasa gida. Yai horn mai gadi ya leko ya bude masa yana daga masa hannu da masa sannu da zuwa. Wajen da yake parking ya karasa yai parking sannan ya fito ya bude mata kofar mota ya kamo hannun ta, suka nufi sashen Ummi.

Yana karasawa bakin main falon Ummi ya jiyo muryar Inna na fadin
"To sai yaushe zasu dawo tin safe fa ta fita!"
"Inna nasan suna hanya!"

Bata rufe baki yai sallama. Ummi ta amsa tana mikewa da sauri ta karaso ta kama Maryam ta karasa da ita kan kujera ta kwanta. Ummi ta kalle ta tace
"Sannu!"

Ta juyo ta kalli Aliyu da har ya kusa kofar dakin sa. Yana shiga ya cire kayan sa ya shiga yai wanka ya saka three quarter wando da riga marar nauyi. Wayar sa ya dauka ya kai kunne yace
"Kaje mota ta ka daukon bag system dina da wata ledar magunguna ina part din Ummi!"
Ya kashe wayar yana duba sakon da ya shigo masa.



Da kallo Inna tabi shi tana tabe baki tace
"Kai ka sani!"
Sannan ta dauko flask din da tazo dashi na faten dankali da tai mata da wake da alaiyahu da hanta ta zuba mata ta mikawa Ummi tace
"Bata taci kila haka ya barta ba abinda taci tin safe!"

Ummi ta amsa tace
"Tashi kici kinji maryam!"
Mikewa tayi ta amshi kwanon ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan so take ko zai dawo wani itama ya zauna a cikin ta sai da taci da yawa sannan taji yana son ya taso mata ajiye plate din tayi tana dafe kirji.

Inna tace
"Sannu aman ne?"
Kaita gyada tace
"Sannu!"
Ido ta runtse. Dai dai fitowar Aliyu kenan ya dinga kallon ta da plate din gaban ta. Karasowa yayi a hankali ya zo ya dauki plate din yana duba abinda ke ciki hannu ya saka ya dangwala ya kai bakin sa sannan ya tabe baki yace
"Mene ne kuma wannan?"

"Wallahi Allah ka fita hanya ta Aliyu ni dai ban saka da kai ba kuma ba kai naiwa ba ah toh!"
Ummi ta kalle shi ya dauke kai yace
"Taci ne?"

"Taci ina jin shi yake damun ta tinda taci amai take so tayi ma ta kasa."
Inna ya kalla yace
"Kinga kin kara mata wahala ko? Dame zata ji da ciwon ko da aman dake damun ta."

Mikewa Inna ta yi tace
"Ni dai ba ruwa na da kai balle ka sa min ciwon kai. Kai da ba a iya maka me taci tin safe ta ci wannan da yawa kai da zakai godiya zakai min fada. Ni dai ba dan kai nake ba dan uwarka nake kuma da tausayin yarinyar amman dan takai wallahi ba zan ba."
Ta fice tana mita. Ummi ya kalla. Ummi tace
"Menene aibun wannan din?"

"Ummi but ai damun ta yake!"
"To ta dawo dashi ne da ta zauna da yunwa fa? Me taci acan clinic din?"

"Na siyo mata komai amman ba abinda taci da tayi spoon daya sai amai."
"To kaga ai gwara wannan ya dan zauna ko?"

Da sauri ta mike zatai sama Aliyu ya kamo ta sukai toilet din falon nan tai ta amai sai da ta harar da duk abinda taci. Tana aman Farouk ya shigo jin kakarin amai duk ya daga masa zuciya ya bata fuska shi a lallai kyamkyami yake. Ummi na bakin kofa tana tai mata sannu.

Sai da ta gama Aliyu ya fito da ita. Kallon su Farouk ya tsaya yi da mamaki wace wannan kuma. Akan kujera ya kwantar da ita ya cire mata hijab. Juyowa yai ya kalli farouk da ya tsaya kamar statue. Hannu ya mika masa bag din maganin ya amsa ya balli wanda zata sha sannan ya mika mata ruwa. Fuska ta bata kamar zatai kuka yace
"No don't cry take it kinji zai sa ki rage jin ciwo."

Ta amsa Ummi ta fito ta nufi dining ta dauko lemon da Maryam ke so ta taho dashi ta kalli Farouk tace
"Ya kake tsaye kai kuma?"
Fuska ya yamutsa sannan ya ajiyewa Aliyu system yace
"Tafiya zanyi!"

"To!"
Ya juya ya fita yana tofar da yawu. Da kyar ta sha maganin sannan Ummi ta bata lemon da ta kusan shanye shi sannan ta koma ta kwanta take bacci ya dauke ta.

Ajiyar zuciya Ummi da Aliyu suka sauke sannan Ummi ta kalli Aliyu tace
"Kai me kaci?"
"Ba komai!"

"Gwara kaje kaci ko dare nayi!"
Mikewa yayi ya nufi dining yana fadin
"Abbah fa!"

Mikewa tayi tace
"Yana sama bari naje!"
Ta tafi shi kuma ya zuba abinci kadan yaci ya ture ya 'kurawa Maryam dake bacci ido. Yafi awa daya a zaune Ummi ta sauko cikin shirin bacci ta tada Maryam sukai sama. Ta kalli Aliyu tace
"Zaman me kake ne?"

Mikewa yai yana shafa kai ya dauki jakar system yace
"Sai da safe!"
"Allah bamu alheri!"
Ya nufi dakin sa ya ajiye system ya zauna bakin gado yai shiru kawai.

Sai wajen daya ya kwanta karfe uku kuma ya tashi ya yafi masallaci. Acan suka hadu da Abba da Abbi har farouk duk acan suka baro shi sai bakwai ya koma gida. Ummi ya sama a falo tana gyara dining ya karasa ya durkusa a kasa yana fadin
"Barka da safiya Ummi!"

Ta shafa kan sa tace
"Ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah! Ya me jiki?"

"Da sauki! me yake damun ka?"
Kai ya girgiza yai kasa da kai. Tai murmushi tace
"Shikenan!"
Ya mike yace
"Yau ta tashi da zazzabin?"

"Eh tana can kwance!"
Sama ya nufa ya haye Abbah ya sama zaune a falo ya karasa ya durkusa suka kara gaisawa sannan ya mike ya nufi dakin da take. A bakin kofa ya tsaya ya kalle ta tana kwance cikin bargo. Juyowa yayi ya sauka ya koma dakin sa.

Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani dogon cofee wando mai layi layin milk ya saka milk riga mai dogon hannu ya shafa turare sannan ya nufi falo. Abbah da Ummi ya sama a dining ya karasa ya zauna. Ummi ta mike zatai serving nata yai saurin rike hannun ta yace
"Ummi zan zuba fa."

"Nasan hali kila kaki ci ne?"
"Zan ci Ummi, amman Maryam fa?"
Ya karashe fada da sunan ta a hankali.

"Kasan ba ci zatai ba."
"Ummi ban son rashin cin abincin nan matsala ne ga ita da kuma Babyn."

"Amman kasan ba yadda zamuyi ko?"
"Haka ne Ummi amman fa haka Maryam tayi suffering wanda sai da tai wata biyar ta fara cin abinci Ummi am affraid kar abinda ya same ta ya samu wannan ma."

"Insha Allah ba abinda zai same ta. Itama haka Allah yayi zata mutu da Babyn tayi shahada dan haka ka daina saka damuwa da tsoro nasan abinda ke damun ka kenan daman."
Kai yai kasa dashi ta hada masa tea din ta tura masa da abincin amsa yayi ya sha tea din ya dan cakuli abincin wanda tini Abbah ya fita.

Bayan ya gama ya bi Ummi kitchen yace
"Ummi am thinking of me zanwa yarinyar nan ta samu lafiya!"
"Ciwo ne fa Allah ya daura mata kuma a sannu zata warke, insha Allahu naka dai ka bata kulawa da addu'a."

"Allah bata lafiya to!"
"Amin amin!"

"Na daura ta akan maganin rashin maganar nan in ta kiyaye insha Allahu zata dawo mata since ba dashi aka haife ta ba ina ganin in ta fara maganar wani abun zai zo da sauki amman ace ba magana ga ciwo abun zai mata yawa"
"Allah saka da alheri kuma Allah bata lafiya ta tuna komai da iyayen ta shine farin ciki na."

"Nasa an bincika min ko lossing memory tayi but ba wani matsala a game da wannan Ummi what are you thinking?"
"Allahu a'alam!"

Mikewa yayi yace
"Let me go an greet Inna and Mami i will come back and check on her!"
"Ok!"
Ya fita.



Sashen Inna ya nufa a falo ya same ta tana ta goge goge wanda ba abinda take gogowa dan yadda wajen yake a gyare tsaf. Kai ya girgiza ya zauna akan kujera. Ta juyo tana fadin
"Wallahi daman nasan sai kai. Kai ne baka magana a fili sai a ciki in ba haka ba yanzu in nace bakai sallama ba sai ka rantse da Allah kayi muryar ma rowar ta kake kai kam ka shige su ban san tayaya kukai rayuwa da Maryam ba wallahi yarinyar nan tayi hakuri da rayuwa da kai Allah dai yai mata rahma amman nasan ka cutar da ita da yawa."

"Hajiya Inna i just come to greet you not listen to dis you gist!"
"Kai ka sani! Me ma ya kawo ka waje na? Naga nace ba ruwa na da kai ko? Kaga ni bana son ma ina ganin ka wallahi tinda baka son gaskiya."

"Dan Allah Inna ki bari mu gaisa in tafi ni."
"Na hanaka gaishen ne?"

"Ina kwana?"
"Da ban kwana ba zaka ganni ne?"

Mikewa yayi ya nufi kofa tace
"Au yau ko na sa albarka ba zaka bani ba."
Hannu ya zura a aljihu ya zaro 3k ya ajiye mata sannan ya juya ya fita yana jin ta tana fadin
"Ko kai fa Allah yayi albarka ya tsare ka ya jikan Maryam!"

"Amin ya Hayyu ya Qayyum!"
Ya fada a zucya.

Sashen su yaje ya samu Mami a falo zata shiga sashen Abbi tare suka karasa. A kasa ya zauna ya gaishe da ita sannan ya gaishe da Abbi sukai masa nasiha sannan ya tafi sashen Ummi.



*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Amin"





*Antty*
[11/19, 12:34] Maryam S Indabawa๐Ÿฅฐ: ๏ปฟ๐Ÿ’—๐Ÿ’— *MATAR HAIDAR* ๐Ÿ’—๐Ÿ’—
Page 44

By
*MARYAM S INDABAWA*

Hakuri da Juriyya Online โœ
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


A sama ya same ta a dakin Maryam, ta taimakawa Maryam ta shirya tana zaune tana lallabata ta sha ko tea ne amman taki sai lemon da ta sha kawai. Shigowa yayi ya durkusa a gaban su. Ummi ta mike tana fadin
"Ina zuwa bari na kira office naji dan yau da kyar zan fita ban san wa zan barwa Maryam ba."

"Ba aikin da zakiyi ne?"
"Wallahi akwai wani case da aka kawon nake son na fara aiki akan sa amman ban san tayaya zan ba ina ganin ko na samo me kula da ita."

Zama yayi sannan yace
"For today u can go and do your work since i will not go any where!"
"Kai amman nagode kuwa Son kaga na samu nayi abu da yawa yau."

Ta juya ta fita. Ya juyo ya kalli Maryam da ta hade kan ta da gwiwoyin ta. Gyaran murya yayi yace
"Kinsan ba za dai ki zauna haka ba komai a cikin ki ba ko? Ko kina son ki rasa Babyn dake cikin ki?".

Da sauri ta dago tana kallon sa hannun ta akan cikin ta. Sai ta hau girgiza kan hawaye na zubo mata. Yace
"Fada min me kike so?"
Kai ta girgiza ya dauki cake din gaban ta ya mika mata. Amsa tayi ta kai bakin ta kadan ta gutsura ta tauna ya kalle ta yace
"Kara mana!"

Ta dago ta kalle shi, murmushi ya dan mata yace
"Kici kinji!"
Kara gutsura tayi dai dai lokacin da Ummi ta shigo cikin shirin ta na tafiya aiki. Ta kalle ta ta saki murmushi tace
"Tana ci kenan!"

"Eh tana dan ci."
Ya bata amsa, ta karasa wajen Maryam ta dafa ta tace,
"Daugther zan fita aiki but i will soon come back, ga Yayan ki nan he will take care of u if u need any thing else tell him. Allah baki lafiya!"

Hannun ta ta kama tai mata godiya sannan ta mike ta kalli Aliyu tace
"Son am going take care!"
"Insha Allah!"

Ya mike zai rakata tace
"No ka zauna wajen ta takarasa kaji!"
"Ok!"

Ta juya ta fita yana mata addu'a sannan ya kalli Maryam yace
"To ki dan sha Tea din!"
Idon ta ne ya ciko da kwalla. Yace
"Try it!"

Cup din ta dauka ta kai bakin ta dumim tea din yasa ta kafa kai sai da tasha rabi sannan ta ajiye, kirji ta dafe yace
"No kar kiyi kinji!"
Kai ta gyada amman yadda take jin tashin zuciyar bata san lokacin da ta mike da sauri tayi bandaki ba. Da sauri yabi bayan ta.

Ummi na sauka ta samu Farouk zaune a falo. Kallon sa tayi tace
"Ah Farouk kai kadai zaune anan!"
Kai ya shafa yace
"Nazo wajen Hamma ne!"

Sama ta kalla tace
"Yana sama ai! Kaje ka same shi!" "Toh fita zakiyi?"

"Eh zani aiki ne!"
"Adawo lafiya Allah tsare."

"Amin!"
Ta juya ta fita shi kuma ya haye sama ya nufi dakin Ummi ya murda. Kakarin aman ta ya jiyo da sauri ya juya ya fita yana yamutsa fuska. Anan falon sama ya zauna yana pressing phone nasa.

Ganin ya kwashe wajen minti goma bai fito ba yasa ya nufi dakin. Ganin su yayi sun fito a toilet din Maryam na gaba Aliyu na bayan ta. Kan gado ta kwanta taja bargo ta rufa ya karaso cikin kulawa da tausayi yace
"Sannu!"
Kai ta gyada ya dago yana kallon Farouk dake tsaye fuska a yamutse dan Farouk ba dai kyamkyami ba.

"Kaje daki na ka daukon wata leda akan kujera!"
Da sauri ya juya bai jima ba ya dawo ya mika masa leda ya juya ya fita. Ruwa ya dauka a ciki ya hada ya saka mata nan take bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kwashe kwanukan wajen ya fita dakin

Farouk ya gani zaune ya kalle shi ya nufi stair da sauri Farouk ya karaso yana fadin
"Kawo big bro!"
Ya amsa ya sauka Aliyu yabi bayansa. Kitchen ya kai ya dawo ya sami Aliyu a kasa yace
"Hamma wai wacece wacan ne?"

Dagowa yai ya kalle shi sai yai sauri yai kasa da kansa yace
"Uhmm ina kwana Yaa Haidar!"
"Ka tashi lafiya?"

"Alhamdulillah!"
"Mukullin motar yana kan dressing mirrow!"
Yana fadar haka ya fara danne danne a waya.

"Nagode Allah kara bude!"
"Amin!"
Ya juya ya nufi dakin sa. Wayar sa ce tai kara ya dauka yace
"Ummi menene?"

"Anjima mai aiki zata zo shine nace bari na fada maka."
"Allah kawo ta lafiya."

"Ya me jikin?"
"Na saka mata ruwa bacci take yi!"
Ya fada ya mike ya nufi sama dai dai fitowar Farouk ya kalle shi ya fita kawai yana tunanin to wacece wannan yarinyar.

Bacci ya same ta take yi sauka yayi ya koma dakin sa ya fara aiki a system din sa. Har karfe sha biyu yajiyo ana knocking ya sauka ya ga mai aikin ce. Suka gaisa sannan ya bata hanya. Kitchen ta shiga tai wanke wanke ta gyarawa Ummi kayan miyan da ta saka ta dan basa mata girki iyakar su wanke wanke da sauran su. Aliyu na bude mata ya juya ya koma dakin lokacin ruwan ya kare ya zare mata ya sauka ya zauna a falo.

Yana zaune yajiyo sallamar Inna kai ya dafe ya amsa. Ta shigo ta zauna tana fadin
"Ina mahaifiyar taka?"

"Ta fita aiki!"
Mikewa tayi tai sama tace
"Ba wajen ka nazo ba ai da kake sha min kamshi!"

Ya bita da kallo sannan ya dauke kai. Maryam ta sama kwance amman idon ta biyu ta kalle ta tace
"Sannu Uwa ta ya jikin?"
Mikewa tayi tai mata alama da hannu ina kwana? Inna tace
"Lafiya ya jikin?"

Tai mata alama da da sauki. Tace
"To Allah kara

Please Login or Register in order to submit comment