Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kai ga hassada ba zai kushe Maryam ba a wannan rana takalmi da jaka bakake tayi amfani dasu, fitowa sukai dan su Ummi duk sun riga da sun tafi.

Waya Maryam tayiwa Jawahir take fada mata an kwashe kowa suma yanzu suna hanya, compound suka fita dan ta kira driver ya kai su, suna fitowa gaban ta yai wata mummunar faduwa saboda hango Aliyu da tayi a compound din gida, Basma dake waya ta karaso tana fadin
"Waye zai kai mu?"

Kasa magana Maryam tayi, dan kallon Aliyu dake sanye da wando jeans baki da riga fara ta kama jikinshi yai kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran tashi kuwa kamar wacce aka dasa, ji tayi kamar ta juya sai kuma ta dake tunda bai ganta ba. Wata mota ce ta shigo compound din Basma tayi gaba, Aliyu taiwa magana sannan ta karasa wajen motar da ta shigo ta tsaya, gaba Maryam tayi zata wuce.

Wanda ya ke driving ne ya fito yana kallon Najwa, kofar da take ta mai zaman banza ma aka bude wani kyakyawan saurayi ne ya fito, gaisawa sukai da Basma, har Maryam zata shige Basma tace
"Sister meet Fauwaz."
Juyowa tayi ta dan kalle su, tace
"Sannun ku da zuwa."

Suka fara gaisawa dayan da yake abokin Fauwaz ya zuba mata ido, kai ta dauke ta kalli Aliyu wanda yayi wani kicin kicin da fuska kamar ba zata gaishe shi ba sai ta daure tace
"Ina yini?"

"Lafiya."
Ya amsa a ciki tare da mikawa Fauwaz hannu yana fadin
"Ashe kana gida."
Ya mikawa dayan hannu fuska a hade suka gaisa,

Gefe Maryam tayi, Aliyu ya nufi motar sa yana shiga ya fara dailing number wayar, wayar Maryam ce ta hau kara, kallon wayar tayi, ganin Aliyu yana kiran ta yasa ta dago tana kallon sa, kai ya dauke kamar bashi ke kiran ta ba, a hankali ta fara tafiya har ta karasa, batai magana ba yace
"Zagayo ki shigo."
Ba musu ta zagaya ta bude motar ta shiga,
"Kira Basma mu tafi."
Ya fada ba tare da ya kalle ta ba.

Waya ta dauka ta kira wayar Basma, karasowa tai Aliyu yace
"Shigo mu tafi."
Fuska ta shagwabe tace
"Please Yaya ka barni na tafi dasu kaga danni suka zo."

"Ku biyo motata."
Tace "Ok."

Ya tada mota ya fita, sukabi bayansu har hall din da ake bikin yai parking zata fita ya saka lock, juyowa tayi ta kalle sa, kai dauke yace
"Naga kamar kanki yana rawa ki kula, nasan Muhammad ya zo ko? Abokin Abdul ne bana so kinji ko?"

Kai ta dauke ba tare da tai magana ba, hannun ta ya kamo ta juyo da sauri dan wannan ne karo na farko da Aliyu ya taba ta ba cikin wani lalura ko taimako ba, wanda daga ita har sai da sukaji wani shock, bata gama mamaki ba taji ya matsa hannun ta da sauri ta runtsa ido tana fadin
"Da zafi fa Yaya."

Wani kallo ya watsa mata yace
"Ina miki magana kina dauken kai ni sa'an ki ne?"
"Nifa ba kai na dauke ba."

Hannun ta ya saki ta dago hannun tana kallon hannun har yai ja, ya kada mata yatsun hannun sa yace
"Ki kula."
Sannan yayi unlock din motar da sauri ta fice ya bita da kallo, wajen Basma ta karasa tace
"Ke wai yaushe Yaya ya dawo?"

Murmushi Basma tayi tace
"Uhmm tare muka dawo ni ban so ya biyo mu ba dan nasan ba zai barmu mu sake a bikin nan ba, dama yai zaman sa."
"Gaskiya."
Maryam ta fada wanda iya kar sa baki ne dan kasan zuciyar ta taji dadin ganin sa, suna tsaye motar su Najwa ta tsaya, Tasleem ce ta bude gidan baya ta fito sanye da wani ash kalar material dinkin fitat gown ya kamata sosai, ta saka hill takalmi, sai jaka a hannun ta sai yamutsa fuska take, Basma ce ta saki tsaki tana fadin
"Wai a haka take son Yaya ya so ta."

"Wanne Yayan?"
"Yaa Aliyu."
Basma ta bata amsa.

"Yaa Aliyu,....."
Maryam ta fada cike da mamaki tana kara bin Tasleem da kallo,
"Yes tinda Aunty Maryam ta rasu take son Yaa Aliyu ya aure ta, Kisan Yaya shi da fi'ili ba kowa ke burge shi ba, bare ita da bata da kamun kai duba fa ita a dole yar mai kudi acikin yan uwan ma sai ta nuna jiji da kai, zo mu tafi dan Allah."

Ta kama hannun Maryam zata bar wajen, wayar Maryam tai kara tana dubawa taga Najwa dagawa tayi taji tana fadin
"Ina kuma zaku, ku zo mana."

Ta juyo sai taga Tasleem tayi wajen motar Aliyu bude front seat tayi ta zauna, kai Maryam ta dauke su kai wajen Najwa tayi kyau sosai, tare suka shiga hall din. A can aka kama amarya aka cigaba da shagalin biki, lokacin da aka kira yan uwan amarya gaba daya su Anty Asiya, da su Maryam, Basma suka shiga fili suka dingai mata ruwan kudi kamar basu san zafin su ba.

Sai da aka kusan tashi sannan da abokan sa suka zo, tinda Muhammad yazo yake baza ido yaga ta ina zai ga Maryam, can gefe ya hango su ita da Basma, sai Fauwaz da abokin sa, karasawa yayi yai sallama suka amsa tare da gaisawa, Muhammad ya kalli Maryam yace
"Ranki ya dade minti biyu mana."

Basma ta kalla tace
"Ina zuwa."
Suka fita daga compound din Aliyu dake cikin mota ya hango su nan da nan ya hade fuaka yai kicin kicin, daman ransa ya baci, Tasleem dake waje tace
"Lafiya swt Yaya?"

Bai kula ta ba ya dauki waya ya kai kunne Maryam dake tsaye da Muhammad ta dauka ta kai kunnen ta, yace
"Ki kira Basma zan mai daku gida."

"Yaya ba fa a tashi ba kuma zamu tafi da su Ummi."
"Bana son magana kije ki kirata."

Ya kashe, Muhammad ta kalla, tace
"Zamu tafi."
"Bikin Najwan kuma tin yanzu?"

"To Yaya ne."
"Wanne Yayan? Farouk ko?"

"Yaa Aliyu."
"Ya dawo ne?"

Kai ta gyada tace
"Bari na kira Basman."
Ta koma ciki wajen su Basma taje ta same su ta kamo hannun ta suka matsa gefe tace
"Yaya yace kizo mu tafi."

"Tab tin yanzu?"
"Haka yace."

"Gaskiya ba zan iya ba kije kice baki ganni ba."
"To ni kadai a gida dan Allah."

"Ai ni gidan Sitti zan tafi ma wajen su Najwa."
Wayar Maryam ce tai kara tace
"Wayoo kinga ko yana kira."

Dauka tayi ta kai kunnen ta, tace
"Yaya ban ganta ba."
"To fito mu tafi."
Ya kashe wayar, Basma ta kalla kamar zatai kuka tace
"Kizo mu tafi."

Kafada ta make tace
"Kema kije kice masa a gidan Sitti zaki kwana."
"Ba sai zai barni ba."

"Ki gwada."
Ta juya ta nufi kofa, Muhammad ta hadu dashi yace
"Wai tafiyar zakiyi."

Kai ta gyada tace
"Ai zamu hadu gobe."
"Shikenan Baby take care."

Ta fita ta nufi motar Aliyu, tana bude front seat taga Tasleem zaune maida kofar tayi ta tsaya a waje, Aliyu ya kalli Tasleem yace
"Zamu tafi."

"Yaya nace zan biku."
"No kije kwa taho dasu Ummi."

"Swt bro..."
"Please Tasleem sauri nake."
Ba dan taso ba ta bude motar ta fito, Maryam ta kalla ta harara, Maryam ta tabe baki, bata shiga ba sai da ya kira ta, ta dauka takai kunne yace
"Bazaki shigo ba."

Baki ta turo ta bude motar ta shiga ya tada motar suka fice a wajen, maimakon suyi hanyar gida sai taga ya dauki hanyar asibiti, suna zuwa ya kashe motar yace
"Muje."

Ta bude ta fita, bayan sa tabi har suka isa office dinsa sannan ya bude suka shiga zama yayi yana duba wasu file, sannan ya mike ya fita, tana zaune a wajen har akai magariba tai sallah ita ce har bakwai babu shi har bakwai da rabi sannan ya dawo, kallon ta yayi yace
"Muje."


Kamar zatai kuka ta mike suka fita, daga nan gida sukai amman har lokacin su Ummi basu dawo ba, yana parking ta fice a motar tai cikin gida da kallo ya bita yana murnushin kasa kasa, masallaci ya tafi dan yaji an tada sallah, bayan ya dawo ya shiga gida ba kowa a gidan sai shi kai dai. A falo ya zauna ya fara neman layin ta, har tai wanka tayi sallah taji kiran wayar ta, ta dauka yace
"Kizo ki samen a kasa."

Ta mike ta fito ta karaso ta tsaya a gefe tace
"Gani."
"Zubo min abinci."

Dining ta nufa ta zubo masa abincin ta kawo zata bar wajen yace
"Zauna, "
Ta koma ta zauna, yana ci yana kallo har tara saura sannan su Ummi suka dawo, Ummi tace
"Ai ina ta neman ki Basma tace Yaya ya taho dake."

"Eh ni gidan Sitti zani."
"Ba inda zaki."
Ya fada yana barin wajen. Ummi ta kalla tace
"Dan Allah Ummi ki masa magana."

"To yanzu kije ki kwanta ko gobe ne kya kwana a can."
Kofa aka bude Tasmeen ta shigo tana tafiya da kyar ta zauna tace
"Ummi ana zan kwana."

"To shikenan."
Maryam ta mike tai sama, Ummi ta shiga kitchen, tana zaune har wajen goma a kasa Ummi ta sauko tace
"Tasleem ki shiga ki kwanta mana."

"To Ummi zan hawo."
"Ok ni dai na tafi, kya shiga dakin Maryam ko?"

"To Ummi."
Ta juya tai sama, kwanciyya tayi akan kujera tana kallo, around 11pm taji an bude kofa da sauri ta mike, tana kallon sa ta hau fari da ido, bai kalle ta ba ya dau hanyar dakin sa, tabbas da ya san zai same ta anan da ya wuce dakin sa na bangaren su,
"Swt Yaya."

Ta kira sa sanin halin ta sai tace zata bi sa yasa ya juyo ta mike ta karaso tana tafiya tana karairaya, kai ya dauke yace
"Menene?"

'Swt Yaya please ya kamata mu zauna mu tattauna mu cikawa iyayen mu burin su."
"Burin su kamar yaya?"

"Tinda Anty Maryam ta rasu, Yaya me zai hana ka auren tinda nima yar uwar kace, tin ina alkunya kana gani har na daina please kai ma ka ba da kai."
Fuska ya daure ya dago ya kalle ta yace
"Tinda kinsan da haka ai da ina bukatar ki da tin da na nuna to bana bukatar ki, in baki sani ba ki sani bakya cikin tsarin matan da nake so, ki haska rayuwar ki da ta Maryam ki gani, kije wajen Ummi ta fada miki irin matar da nake so in kina da irin qualites din to zan aure ki."

Yana fada ya shige daki, da kallo ta bishi tana jin wani irin zafi a zuciyar ta duk mazan da suke son ta taki ita kullum sai Aliyu amman shine yake mata haka, kan kujera ta koma ta zauna ta fara kuka, ranar a falo ta kwana ta kasa bacci sai kuka da take saboda da gaske take son Aliyu tunda Yayar ta ta mutu taji duk duniya ba wanda take so sai shi.





*Allah y jikan musulmai Allah kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin*



*Antty*
[11/27, 14:18] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 59

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


Da asuba da ya fito zai tafi masallaci ya ganta kwance akan kujera kai ya dauke ya fice kawai, Ummi ce ta sauko ta ganta sosai tai mamaki ta zauna tana tashin ta, ido ta bude wanda suka dan daga saboda kukan da ta sha. Ummi tace
"Me ya samu idon ki fuskar ki duk tai ja, idon ki ya kumbura."

Mutsuka idon ta take tace
'Ummi Yaya ne, Ummi wacce irin mace Yaya yake so?"
"Kije alwala kiyi sallah tukkunan."

Ta mike ta wuce sama wanka ta farayi sannan ta fito ta canja kaya, Maryam na zaune akan sallaya tana karatun Alkur'ani ta fito, ta tada sallah sannan ta koma kam gado ta kwanta.

Da safe Maryam na falo kwance akan kujera sanye da hijab har kasa, hannun ta daure da counter tana yin tasbihi, Ummi na kan two sitter, Tasleem ce ta fito sanye da dogon wando da riga karama kan ta ba dankwalli, ta zauna a kan hannun kujerar da Ummi take, Ummi ta kalle ta yace
"Abinci fa."

Cikin ta ta shafa tace
"Tukkuna Ummi ki fada min Ummi meyasa Yaya baya so na, wai wacce irin mata yake so?"
"Me ya kawo wannan to?"

"Shi yace na tambaya."
"Hmm Aliyu kenan, to shi Aliyu yana da wuyar sha'ani miskili ne bai son mutum mai surutu da rawar kai, yana son mace mai kamun kai da shiga ta mutunci duk kyale kyalen nan basa gaban sa fatan sa ya samu salihar mace, ai ke shaidace akan yar uwar ki ba ruwan ta ba sawa ba sakawa to dalilin da yasa ya so ta kenan kuma har yau yake kan son ta, kiyi kokari ki koyi wasu halaiyar nata in kina son Aliyu ya so ki."

"Ummi ai Yaya Maryam bata waye ba gaba daya tayi rayuwar waje amman kullum bata waye ba, da ba dan Yaa Aliyu ya aure ta ba da ina zaton ba mai auren ta a zamanin nan."
Ummi tace
"A haka kuma yaso ta yaki ki fa, ku kun dauki wayewa a zubar da mutunci ai zubar da mutunci mana, kalli fa yadda kika sauko kanki ba dan kwallin kuma ina tunanin acan ma zaki iya fita kusan haka, bayan a addini bai kamata wanda ba muharramin ki ba ya ganki a haka, bansan me yasa Yaya yake barin ku a haka ba, ga Maryam nan dai a gidan nan ko da mayafi ba zaki ganta ba kullum hijab amman ke kalli yadda kika sauko ba ruwanki wani ya ganki a haka wanda ba dai dai bane."

"Ummi Yaya ne fa."
"Yayan muharramin ki ne? Naga da aure a tsakanin ku."

Baki ta turo, Ummi tace
"Zagi na zaki?"
"Nifa Ummi a'ah ba abinda nace."

"Uhmm wallahi ki kula ace duk Yaya ya barku haka sai abinda kukayi, ko da yake laifin mahaifiyar taku ce tinda shi ba zama yake ba."
Fuska ta daure. Sallamar Aliyu ita tasa Ummi tayi shiru, suka amsa sallamar, a gefen Ummi ya zauna, Ummi ta kalle shi tace
"Ni sai naga duk ka rame Yaya bata kular min da kai ko?"

Yaya da take saukowa tace
"Allah yaso nazo da sai dai ai min sharri, wannan yaron naki dai yana da damuwa nayi nayi dashi ya fada min yaki, ko dan ni ba uwar sa bace, nasan ke ya fada miki, kullum bai cin abinci sai ya raba dare idon sa biyu sam bai hutawa ke daga kallo daya zaki gane yana da damuwa amman yaki ya fada kullum sai munyi fada dashi akan abinci sai kace wani yaro."

Ummi ta juyo tace
"Haba yaron kirki "
"Ummi nifa kewar ku nake kawai."

"Jika sai kace karamin yaro, Aliyu ka rage wannan kwulaficin naka ka girma fa in da ba dan kaddara ba ai kaima da yanzu kana da iyalai wanda zasu na maka haka amman kai kake yi, mufa tamu ta kusa karewa in kuma muka mutu fa shikenan zaka ce ka daina rayuwa ne? Dan Allah My Son kana ragewa kaji yaro na."
Kansa ya daura akan kafadar ta yace
"Ummi ba yanzu zaku tafi ku barni ba bana so Ummi dan Allah ki daina maganar nan, Maryam ta tafi ta barni so kike kema ki tafi ki barni?"

"Ba tafiya zanyi na barka ba, ina fada maka abinda ya dace ne kaji."
"To Ummi."

"Abinci fa meyasa bakaci."
"Ummi kinsan in ba girkin ki ba, ba wanda yake mun dadi "

Dakuwa Yaya tai masa tace
"Kaniyar ka, da kai na nake shiga na girka masa abinci amman yaron nan ko kallon sa bayayi sai ya mai dani karya nai ta fada sannan zai dan taba."

Dagowa Ummi tayi ta kalli Maryam da ke danna wayar ta suna chat da Muhammad tace
"Daughter kawo masa abinci yanzu."
Ajiye wayar tayi ta mike, Ummi tace
"Yau sai ka dawo da kibar da ka rage."

Yaya ya kalla yace
"Momy ki fada mata ai ina ci aiki ne fa kawai yasa na fada."
"Wane irin aiki ne wanna Son?"

Kai ya shafa, ya mike ya dauki wayar Maryam ba security yana dauka yaga suna magana akan dinner anjima da za ayi, wani murmushi ya saki, ya maida wayar ya ajiye, Maryam ta karaso ta ajiye ta dauki wayar ta tai sama.

Tasleem kuwa tana zaune sai bata fuska take, Yaya ce tace
"Ita kuma wannan fa?"
"Dan na mata fada ne."

"Akan me?"
"Kinsan su, su ya'yan turawa ne ina mamakin yadda su Basma basa wannan rayuwar dasu suke ko da yake a gidan nasu ma marigayiya batai ba amman wannan kingan ta ta dauki dabi'ar su gaba daya ita take yi kuma laifi uwar tasu ce ai."

"Uhmm Allah ya shirya shine take bata fuska dan an mata fada."
"Gashi nan dai sai cika take ba."

Aliyu ne ya dago ya kalle ta kai ya dauke yana tabe baki, yace
"Wannan shigar kuma fa? Ina dankwalin ki? Tashi kije ki saka hijab."

Mikewa tai tayi sama da sauri idon ta na kawo ruwan hawaye, Maryam ta sama kwance akan gado tana rike da waya a kunne sai murmushi take, zama tayi a gefen gado tana goge hawayen idon ta, can ta mike ta dauki wata after dress wacce ba abinda ba a gani a jikin ta sai dan mayafi da ta daura akanta, ta dauki jakar ta, ta fice a dakin da kallo Maryam ta bita tana tabe baki.

Tana sauka ta samu Aliyu na cin abincin sa hankali kwance, Ummi ce ta fara ganin ta tace
"Ina kuma zaki?"
"Gida zan koma."

"Dan an miki fada ke kin fi karfin ai miki fada kenan ko?"
Hawayen idon ta ta hau gogewa ta fashe da kuka tace
"To Momy ya zanyi? Me nayi?"

"Oh duk fadan da akai miki ma baki san me kikai ba?"
Kuka ta kuma saki Aliyu ya mike ya fita a dakin gaba daya da kallo ta bishi, Ummi tace
"Ina zaki yanzu?"

"Gidan sitti zan koma."
"To kije driver ya kai ki, sai anjima in mun hadu."
Jakar ta taja ta fita a gidan. A waje ta same shi yana rike da waya a kunnen sa, tsayawa tai tana kallon sa, har ya gama ya juyo yana ganin ta ya hade fuska yace
"Yanzu nai miki magana akan shigar ki a haka kike son ki fita ko?"

Kallon kanta tayi tace
"To Yaya menene da wannan kayan?"
Kai ya dauke yace
"Muje na sauke ki."

Dadi taji ko ba komai zata kasance dashi, mota ya shiga ta shiga gefen su a hanya yace
"Tasleem abinda Ummi ke fada gaskiya ne dan haka ki kula."
"To Yaya zan gyara in munyi aure ma hijab zan na sakawa har kasa."

"Kiyi tin yanzu shine zan gane zaki ko ba zaki iya ba gaba."
"Yaya da zafi fa, ita wannan ta gidan naku da take saka hijab kullum bata jin zafi ne?"

"Kije ki tambaye ta."
"Kaga wani gani gani da take min."

"A'ah Tasleem Maryam bata da matsala kwata kwata, dan haka karkice haka kila ke kikai abinda take miki wani gani ganin."
"Yaya yanzu baka ganin laifin ta."
Dai dai zuwan su gida, ya kalle ta yace
"Sauka kije."

"To Yaya zaka zo anjima."
"May be."

"Please Yaya kazo"
"Ok."
Ta bude ta fita ta daga masa hannu tace
"Thank you dear."
Ya dauke kai ya tada motar ya bar wajen. Karfe takwas ta fito daga sashen su ba kowa a gidan tsit, compound ta fita ta duba taga motar da ita kadai ce a harabar gidan bata san motar ba dan haka ta tsaya daga nesa da motar to yanzu wa zai kai, wayar ta duba, dan Kiran Muhammad, dan daman yace zai kai ta tace a'ah to gwara yazo su tafin kawai.

Aliyu dake cikin mota sanye da wata brown kala shadda, ya saka hula kalar kayan har da glass agogon hannun sa na azurfa yana ganin zata kira wani ya danna horn da sauri ta dago tana kallon motar, horn aka kara dannawa wannan yasa ta karaso wajen motar, dan ita a tunanin ta Yaa Farouk ne gefen inda driver yake ta tsaya yana daga ciki ya sauke glass din motar sai da jikin ta yayi yarrr yanda ta ganshi yayi masifar kyau kyamshi ya kara fitowa tamkar shi yayi kanshi, da sauri ta sauke kan ta kasa, kofar motar ya bude yai mata nuni tare da fadin
"Shigo."

Jiki a sanyaye ta zagaya da kallo ya bita har ta shiga wani kamshi da sanyi taji a hankali ta lumshe idon ta, zama tayi ta rufe kofar ya tada motar ya bar wajen ba tare da yayi mata magana ba sai kira'ar sudais dake tashi a cikin motar, can wayarta ta soma ringing a jaka hannu ta saka ta ciro ta Ummi ce, dauka tayi takai kunnen ta Ummi tace
"Kina Ina?"

"Muna hanya."
"Ke da waye?"

Aliyu ta dan kalla ta dauke kai tace
"Yaya ne."
"Ok sai kun karaso."

Ummi ta kashe wayar, ya juyo ya dubeta, sannan ya dauke ido ya mai da kan titi yace
"Wanene?"
"Ummi ce."

Parking yayi a gefen titi ya dago yana kallon ta, dagowa tai idon su ya hadu waje daya kasa daina kallon juna sukai sai da suka dauki minti kusan uku sannan tai karfin halin janye idon ta, shi kuwa ido ya lumshe sannan ya kara kallon ta yace
"kinyi kyau sosai, wa yai miki kwalliya?"

Dan murmushi tayi tace
"Nagode."
Ya daga mata gira yace
"Wa yai mki kwalliyar?"

Ita a ganin ta ba wani kyau da tayi dan da kanta tayi kwalliyar yar kadan wanda ba karamin kyau tayin ba, kanta tai kasa dashi saboda jin idon sa akan ta tace
"Ni nayi."
"Oh daman kin iya?"

Kai ta gyada yace
"Amman bakya yi a gida why?"
Shiru tayi shima jin zai saki layi yace
"Tayi kyau."

Ya zuba mata ido ita kuwa kan ta a kasa ta kasa duban shi, numfashi ya ja sannan yace
"Maryam!"
Wani iri taji dan sai da tsigar jikin ta ta tashi, ta dago ta kalle shi da sauri ta dauke kanta, dan bata iya jurar kallon idon sa, wani abu take gani yana fitowa yana shiga nata wanda hakan ke haifar mata da mutuwar jiki, shiru yai kamar ba zai magana ba sai kuma yace
"Bayan tafiya ta kin shiga wani mawuyacin hali wanda ni kaina da bana nan na shiga makamancin sa, a dalilin rashin daukar shawara ta abin yaso ya taba miki rayuwar ki, in nine ke ba ruwa na da wani samari karatu na zan rika a gaba zaki samu masu son ki wanda kema a lokacin kin kama kasa amman a yanzu karatun shine ya dace da ki sa a gaba, kina zaune wani yazo zai tarwarsa miki rayuwa akan me? Me sonki na gaskiya ba zai taba barin ki ba ko tuhumar wani abu akan ki, yana da kyau ki nutsu ki gane mai sonki, da wanda kike so."

Hannun ta ya kamo wani iri taji waninshock wand ashima sai da yaji tsargawar sa, dan murazawa yayi sannan ya saki yace
"Dan Allah ba danni ba ki bar harkar wasu samari ki riki karatun ki, ki taimakawa Haidar, a gaba zaki samu mai son ki wanda baki taba tsammani ba amman ba yanzu ba kinji."

Mamakin Aliyu take saboda me yake hadata da Allah bayan rayuwar tace, shi bai aure ba itama kada tayi kenan anya ba aljanu ne dashi ba wanda basa son aure to aljanu mana. Hannun ta ya dago yace
"Yes nasan zaki ce ina ruwana da rayuwar ki amman ki sani rayuwar ki na da mahimmanci ga mutane da yawa ingantata zai bawa mutane da yawa farin ciki ki tsaya ki nutsu ki duba kinji little sister dita."

Baki ta turo yai murmushi yace
"Wato bakiji ba ko?"
Hannu ta daura akan bakin ta, yace
"Kin fiso ki ta tara maza suna zuwa su taso miki da son sanin wacece ke ko?"

Ji tayi zuciyar ta ta karye dan tabbas duk wanda ya ganta zai so ya mallake ta kuma tana yawan samun masoya amman ta ina zata fara sam bata fatan abun da ya faru akan ta da Muhammad ya kara faruwa bata fatan tarihin ta yai ta yawo ana mata wani kallo wanda bata san dai dalilin komai ba amman kuma tabbas duk abinda Aliyu yake ada gaskiya ne, amman tayaya zata na gujewa samarin dake kawo mata hari, tana lura da wanda suke tare da Fauwaz yadda yake ta shishige mata bata san ya akai ba sai kawai jin hawaye tayi na bin kumatunta tabbas tasani rayuwar ta abin tausayi ce shin ko ta auri Muhammad wane hali zata shiga a gidan sa, kada wata rana ai mata gori da ya zataji anya kuwa batai gangancin amsar soyayyar Muhammad ba, Aliyu ganin hawaye a idon ta ya hau lallashi amman ina kana dada tunzurata yayi, wannan yasa ya janyo ta jikin sa ya rumgume ta hadi da runtsa idon sa, dan abinda yaji a tare da shi, tana jin ta a jikin sa taji wani nutsuwa wanda bata san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba, take kukan nata ya dauke, so take ta bar

Please Login or Register in order to submit comment