Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bace wacce take dan shi ya riga ya mutu shin ya zata dauki wannan abun in taji cewar Yaa Haidar ya mutu. Gefe kawai taja tana sakin kuka dan abin ita kanta ya bata tsoro.

Mutanen da jiya ke tare ya rumgume ta yana godiya da Allah ta zama matar da kowa ya shaida ashe ba rabon zama ashe farin cikin kenan. Duk soyayyar da sukewa juna shikenan ta kare ta mutu lallai duniya abar tsoro ce. Sai tsoron Allah ya dada kamata ta rufe ido kawai tana mai jin tausayin aminiyar tata. Haka suka kwana a zaune Maryam na kuka Aisha na kuka an rasa me rarrashin wani ma.

Suna zaune aka fara kiran sallah asuba, nafila Aisha ta tashi tayi dan Maryam ta kasa mikewa dan yadda kafafun ta sukai wani sanyi suna zaune sukaji an kira sallah asuba amman sam ta kasa tashi gashi tana son ta kara tada sallah. Sai da Yaya Fadima ta gama sannan ta kalli Maryam tace
"Bakya sallah ne?"

Hawaye ne ya zubo mata tace
"Na kasa tashi kafafu na kamar ba ajikina suke ba ki taimakan."
Mikewa Yaya Fadima tayi ta Kamata har bandaki ta raka ta, shigar ta kenan aka idar da sallah sannan aka sanar da jana'idar Aliyu da za ayi nan da karfe takwas na safe. Tana bandaki sam bata ji ba ta fito tana dafa bango dan har wani jiri take gani. Da sauri Aisha ta mike ta kamata ta tayar da sallah ta jima tana kan sallaya tana addu'a bayan ta gama tai azkar.

Agogo ta dago ta kalla taga karfe shida da rabi. Aisha ta kalla dake rike da carbi tace
"Ki kara kira min Yaa Alkasin naji ya jikin Yaa Haidar!"
Wayarta ta zaro ta fara neman layin Yaa Alkasim amman me a kashe take wayar. ajiyar zuciya ta sauke tace
"Kinji wayar tasa wai a kashe."

"Dan Allah kira min Yaya Fadima!"
Ta fada tana gyara zaman ta. Mikewa Aisha tayi ta nufi dakin Ammi. Anan ta samu Rukayya da Zarah suna ta kuka dan jin mutuwar tasu kenan da sauri suka fita dan tabbatar da cewa wane Yaa Haidar din, fada masu cewa shine yasa suka zauna suna ta kuka sun kasa tafiya wajen Maryam ma. A haka Aisha ta shiga ta same su Yaya Fadima na basu baki.

"Yaya Fadima kizo inji Maryam!"
Mikewa tayi tace
"Ince dai bata ji sanarwa nan ba?"

"Bataji ba so take a kira mata ma Yaa Alkasim taji ya jikin Yaa Haidar?"
Ta karasa maganar tana share hawayen idon ta.

"Muje!" Suka fita tare. Suna shiga suka jiyo sautin kukan ta, hannun ta rike da kan ta tana kukan.



*Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan kasa muyi kyakyawan karshe.*


*Amin.*

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 25

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*





Dafata Yaya Fadima tayi tace
"Dan Allah kibar kukan nan haka menene kuma ya faru?"

"Dan Allah kicewa Ammi akai ni wajen Yaa Haidar, in ba mai kaini ni zan tafi dan Allah ki rokar min ita."
"To naji! Ki bar kukan ko a haka zakije masa kina kuka ki dada tada masa hankali."

"Wai tayaya kuke son na daina kukan nan nifa ban san yana fitowa ba nakasa rike shi dan Allah kije ki mata magana."
Mikewa tayi tace
"Toh!"

Ta tafi dakin Ammi. Dawowar Ammi daga gidan Mamah kenan gidan da har ya fara cika da mutane ga na biki ga yan uwa, da makwabta. Mamah na zaune a gefen Aliyu sai addu'a take masa Abbah da Abbi da Alkasim da baya uhm bare Uhm uhm duk suna zaune. A cikin gida kuwa sai kuka ake. Zuwan Ammi ma dan Abbi yace tazo ta kira Maryam ne suyi sallama wannan yasa ta mike ta nufi gida shine suka hadu da Fadima.

Tana ganin ta tace
"Daman wajen ki zani!"
"Meyafaru ba dai taji ba?"

"Bata ji ba dan so take kisa a kai ta wajen Yaa Haidar."
"Ikon Allah! Tayaya zan sanar mata ne. Bari naje dai."
Ta nufi dakin Yaya Fadima na bin ta a baya.

Tana shiga Maryam ta rarrafo wajen Ammi ta kama kafar ta tace
"Ammi dan Allah kada kice min A'ah!"
Kamo ta Ammi tayi tana boye hawayen idon ta tace
"Ba zance ba, taso muje!"


Ta kamota ta mike ta lafe a jikin Ammi dan yadda take ganin bibbiyu. Ammi ta kama ta tace
"Menene?"
"Jiri Ammi, biyu biyu nake gani Ammi!"

"To rufe idon ki kinji!"
Rufe idon tai Ammi ta lattafe ta suka fita a dakin. Suna fita Fadima da Aisha suka fashe da kuka. Fadima ce ta mike tace
"Taso muje."
Suka bi bayan su.

Har suka fita compound idon ta a rufe yake sai da suka kusa kofar gidan su Aliyu ta bude ido. Mutanen da ta gani ne ya bata tsoro tace
"Ammi me ya faru?"

"Ba komai."
"Waye zai kaini gun Yaa Haidar?"

"An sallamo shi fa yana gida "
"Ammi da gaske? Yaji sauki ko?"
Kai Ammi ta gyada tana kama ta suka shiga gidan yadda taga compound din a cike wasu na kuka wasu na jimami yasa gaban ta ya kara yankewa ya fadi. Tunanin ta ya gushe dan ta kasa gane mutanen menene suka zo musu haka. Sai kace jiya ranar bikin su da daurin auren su.

Kama ta tayi suka nufi bangaren Aliyu, yan tsakar gidan kuwa sai nuna ta suke da hannu suna fadin
"Ga matar tasa. Allah sarki!"

"Ai fa jiya jiya aka daura aure yau ba miji wannan wane irin tashin hankali ne."
Haka suke ta magana kala kala dai.

Suna shiga falon Aliyu gaban Maryam ya kara faduwa har sai da ta durkusa ta dafe kirjin ta. Ammi ta durkusa tace
"Menene?"
"Ammi kirjina, sai faduwa yake."

"Kina fadin Innalillahi wainna illahir rajiun kinji?"
Kai ta gyada ta fara ambaton haka a zuciyar ta. Ammi ta dago ta suka shiga. Abbah da Abbi ta fara gani sai Yaa Alkasim da Mamah daga kan da zatai ta gano Mutum kwance rufe da farin abu da sauri ta juya ta kamo hannun Ammi tana nuna mata abun hannunta na rawa bakin ta ma rawa yake ta kasa furta komai, sai nuna abun da take jikin ta na karkarwa.

Tin kafin Ammi tai magana ta sulale zata fadi kasa da sauri Ammi takamo ta tana fadin
"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Abbi ya mike da sauri yayo wajen su yana fadin
"Me ya faru?"

"Suma tayi ko?"
Ya dago ta ya karasa dakin da ita. Ammi ta dauko ruwa a firij ta shafa mata a fuska shiru bata farka ba, kara zuba mata tayi nan ma haka ruwan ta tuttula mata a kanta wannan yasa taja wata doguwar ajiyar zuciya wanda yasa kowa fadin
"Alhamdulillah!"

Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa bude idonta. Tsoro take ta bude za ta sake ganin abinda ta gani, wannan shi ake kira mummunan gani.
"Shin waye ma a kwance a cikin likafani?
Tai tambayar a zuciya da sauri ta bude ido dan gwara ta gama sanin wanene ta tabbata dai ba Yaa Haidar bane. Ina Yaa Haidar ba zai mutu ya barta ba.

Kasa-kasa take jin muryar su Mamah, Ammi suna fadin
"Tana numfashi."
Tofi taji ana mata a hankali ta bude idon ta. Abbi ta gani yana mata tofi. Idonta ta mayar kan gawar dake kwance sambal nuni tai musu da ita dan su fada mata waye a ciki amman duk suka gaza bata amsa.

A hankali ta mike zaune ta dafe kai dake barazanar rabewa gida biyu, kallon gawar ta karayi sannan ta mike tsaye Ammi ta kamo ta cire hannun Ammi tayi ta tafi gaban gawar a dai dai kan sa ta durkusa jikinta na rawa ido na zubar da hawaye ta mika hannu ta dage Likafanin.....

Fuskar Yaa Haidar ce wacce yake tai mata murmushi ta bayyana, bata san lokacin da zauna akasa ba ta tsurawa gawar ido ba abinda yake motsi a jikin ta har numfashin ta daukewa yayi cak idon ta na kafe akan sa kawai. Ammi ce ta gane ta shiga shock wannan yasa ta karasa kusa da ita da sauri tana zuwa ta taba ta ai take ta bingire a jikin Ammi.

Yaa Muhammad ne ya miko ruwan dazu dan a shafa mata amman ko gezau, har juye mata akai amman sam bata farka ba kuma ko alamun rai babu a jikin ta. Ammi ce tace
"Itama fa ta mutu!"

Da sauri Mamah ta karaso tana fadin
"Mun shiga uku, Yaa Allah kada ka jarabce mu da rasa yara biyu a lokaci daya Allah mun tuba in wani laifi mukai maka."

Abbi ne ya karaso ya duba kai ya girgiza yace
"Ai kuwa kamar itama ta rasu!"
Kuka Ammi da Mamah suka saka. Ammi ta rumgume gawar Maryam tana jijjigawa..........



~Please ku karata kasan nan~
*_Ban taba zato ba, ban zata haka ba*_

_Jiya naji dadi sosai dan ba a taba yin comment kamar jiya ba, daga facebook har whatsapp naga abinda akai ta tattaunawa shine MATAR HAIDAR abun ya bani nishadi duk da akwai taba zuciya, ba yau na fara rubutu ba, ba yau kuma in nayi wasu suke cewa sun daina karantawa ba dan ban musu yadda suke so ba, duk abinda kuka gani a littafin nan na rubuta shi sama da watanni bawai ko sama da haka kafin na rubutawa kuwa labarin yana kaina sama da shekara biyu sai a yanzu dai Allah yayi lokacin sa, ba dan nishadi kawai nake rubutu ba ina rubutu dan fadakarwa da zaburarwa so, ni akwai abinda nake son na isar am not after all this love in zakuyi duba irin wannan deep love din bai fiya kaiwa inda ake so ba, kuma ko a gaske muna son mutane Allah ke daukewa, masu cewa Maryam tayi wauta jarabawa ce Allah ya riga ya rubuta, mu bamu san irin wacce Allah zai jarabce mu da ita ba, fatan mu dai Allah ya bamu ikon cinye tamu kalar jarabawar, itama bamu san tukuwicin da Allah zai mata ba, kila Yaa Haidar ba alheri bane a gareta ba shiyasa ya dauke shi, kuma rabon wani a ko da yaushe yakan iya kisa dan haka kuyi shiru kawai ku dai...._


*Hakika naga kauna sosai Allahu ya bar zumunci, masu kuka kuyi hakuri mutuwa nasan ko ta wasa ce babu dadi nima nai kukan kuma duk lokacin da na karanta abun mutuwa yana kara kashen jiki da kara min imani wanda yake kara min kusanci ga Allah, abinda nake so daku kuma kenan. Allah jikan musulmai yasa muyi kyakyawa karshe yasa mu cika da kyau da imani*





*Maryam Suleiman*
*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 26

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



Yaa Muhammad ne yace
"Abbi aje asibiti dai a kara gwada ta."

Yaa Abdullah yace
"Akwai likitoci, a waje bari na kira wani."
Ya juya ya fita da sauri da daya daga cikin abokan Aliyu ne basu koma ba suka zo amsa jana'idar sa suka shigo Maryam ya dudduba sannan yace
"A kai ta asibiti dan tana cikin mayuwacin hali in ba a kula da ita ba zata iya karasawa."

Da sauri Yaa Muhammad ya dauke ta Ammi tabi bayan sa. A bakin bangaren Yaa Haidar su Aisha sukaga Yaa Muhammad ya fito da Maryam da sauri suka bi bayan sa Ammi ma ta fito mota daya suka shiga. Yaa Fadima na gaba Ammi da Aisha na baya rike da Maryam wacce take tamkar gawa.

Suna zuwa aka amshe ta aka wuce da ita emergency likitoci ne suka hadu dan ceto ranta wanda suka kwashe sama da awa takwas akan ta amman sam bata dawo haiyacin ta ba da taimakon oxygen dai sun samu tana numfashi amma daga nan ba abinda yake motsi a jikin ta.

Wanda asibiti zuwa wannan lokacin a cike yake dan wajen hudu na yamma lokacin har an sallaci Aliyu Haidar wanda ya samu hallartar mutane masu yawa aka kai shi gidan sa na gaskiya kowa sai addu'a yake masa dan Aliyu mutumin kirki ne bai taba fada da kowa ba kowa nasa ne dan haka kowa sai yabon sa yake.

Ammi, Yaya Fadima da Aisha sune suke asibitin tin safe basu koma gida ba. Yaya Zainab, Yaya Ummulkursum, Yaya Rabi da Hauwa duk sun zo. Haka nan Innah da su Anty Asibi, Anty Hauwa da sauran suma kowa yazo yaga halin da Maryam take, kowa yazo da kuka yake tafiya. Innah ce ta kasa tafiya itama dan halin da taga Maryam ya tsorata ta gani take itama kamar mutuwa zatai.

Suna zaune sukaji sallamar Mamah, da sauri Ammi ta mike tana fadin
"Da kanki Hajiya ai wandan da suka zo ma sun wadatar!"
Zama Mamah tayi tana goge hawaye tace
" *Matar Haidar* ce fa, dole na rike masa amanar ta ko da bashi da rai domin ba tin yau ba yake ban amanar ta dan da yana da rai da shine mutum na farko da zai kasance akan ta to bashi da rai dan haka ni zan kasance mata tamkar Haidar insha Allahu. Allah ya bata lafiya domin Ita kadai zan kalla na tina haidar ita mutane da yawa zasu kalla suyiwa Haidar addu'a dan za ace ga *Matar Haidar* wanda ranar daurin auren su ya rasu....."

Kasa karasawa tayi, saboda kuka. Innah ma kukan take tace
"Tabbas ko ba aure shakuwar Ali da Takwara abin duba ne dole ta shiga wani hali, Allah ya tashi kafadun ta shi kuma munyi rashi yaro mai hankali da nustuwa ga zumunci takanas kafa ya kafa yake zuwa ya gaishe ni, Allah ya jikan sa yasa can tafi nan Allah gafarta masa."

"Amin Amin! Amin Ya hayyu ya qayyum!"
Haka duk yan dakin suka amsa. Bayan mintina Ammi ta kalli Mamah tace
"Hajiya amman da kin koma gida saboda yan zuwa gaisuwa ko?"

"Hajiya Aliyu ya riga ya tafi addu'a ce kawai abinda zamuyi masa, Maryam ita ke bukatar mu yanzu dan Allah ku barni anjima na tafi ganin Maryam nasa naji tamkar Aliyu nake gani".
"Allahu Akbar! Lallai ku mutanen kwarai ne, Allah ya jikan Aliyu."
Innah ta fada. Suka amsa da Amin.


Sai dare da Abbi da Abbah suka zo sannan Mamah ta tafi aka tafi da Innah da Yaya Fadima dan Aisha sam taki tafiya itama sai kuka take iyayen ta dazu sun zo sunje gaisuwa suka biyo asibiti. sai bayan fitar su Abbi ya kalli Ammi yace
"Alkasim ma fa yana gida ana masa karin ruwa tinda muka kai Aliyu yake kuka ya suma yafi sau biyar ga zazzabi dake damun sa ga rashin bacci da abinci."

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah mungode maka Allah mungode maka Allah ka yafe mana ka jikan Aliyu ka tashi kafadun yaran nan!"
"Amin!"
Abbi da Aisha suka amsa. Daga haka ba abinda suke ce. Can sai ga Yaya Ummulkursum da Yaa Muhammad ya kawo ta dan ta kwana da Maryam amman Ammi tace suje kawai zata kwana. Aisha taki tafiya Ammi tace a barta.


Haka aka cigaba da zaman makokin Aliyu har kwana uku, har wannan lokacin Maryam bata farka ba, tana kwance yadda take likitoci sai kula da kai komo suke akan ta sai aikin karin ruwa da allurai. Alkasim ma har lokacin mutuwar bata sake shi ba, dan ya kasa cire abun ya rame ga ciwo na cin shi. Ya cire rayuwa da komai da kowa ko wayar sa tinda yasa a durowa bai kara bi ta kanta ba. Abokan su ana uku duk suka koma yan nesa. Aisha ma bata kwana a asibiti amman tin safe in tazo sai dare suke tafiya ita da Rukayya suma sun rame sun shiga damuwa sam basu da sukuni su kadai suka zauna a daki suyi ta kuka na tausayin kawar su da halin da take da wanda zata shiga in ta farka dan sun san bata gama jimamin rasuwar Yaa Haidar ba. Hakika suna tausayin ta suna tausayin kan su. Mamah ma kullum sai taje dubo Maryam Umma ce kadai bata taba zuwa ko addu'a bare sannu amman, kowa na gidan gaisuwa yaje ya dubo Maryam. Haka su Yaya Ummulkursum duk basu koma ba suna gida suma suna amsar gaisuwar Aliyu. A haka har akai sadakar bakwai akai addu'a aka bada sadaka aka tashi daga taron zaman makoki sai wandan da basa garin in sunzo sunji suke zuwa yiwa ahalin biyu gaisuwa dan duk wanda yasan Abbi yasan Aliyu dan in Ramadan yazo tare suke tafsir haka ko masallacin juma'a tare suke zuwa shiyasa Abbi yake ganin Aliyu shi zai gaje shi ashe ba nisan kwanan. Shi kan sa Abbi ba karamin jin mutuwar Aliyu yai ba yaro mai hankali nutsuwa, ladabi, ilimi ga kunya kullun sai yai masa addu'a.

Yau kwana Aliyu goma sha biyu da rasuwa. Ammi ce zaune da Mamah da Yaya Fadima da Yaa Alkasim da ko magana ya daina sai da kyar zakaji muryar sa sai Yaya Rabi'a da Yaya Hauwa matan Yaa Muhammad da Ibrahim sai Yaa Abdullah wanda shima duk yai sanyi ganin kanwar tasa a wannan halin kullum tana kwance tamkar gawa.

Suna zaune sukaga yatsan kafar ta ya fara motsi da sauri suka mike sai kuma suka ga ta motsa hannu sai kuma tari da ya sarke ta duk da oxygen dake makale da hancin ta. Da sauri Yaa Abdullah ya fita ya kira doctor da gudu suka karaso suka sa su Ammi fita sai da suka kwashi tsawon awa biyar sannan suka fito, Yaa Alkasim ne ya karasa yace
"Ya jikin nata?"
"Alhamdulillah ta dawo amman bata farka ba numfashin ta ya dawo dai dai kuma a ko wanne lokaci zata iya farkawa. Allah ya bata lafiya."

"Amin mungode!"
Suka koma dakin suna kallon ta. Lokacin yamma tayi amman gaba dayan su sun kasa tafiya so suke kawai Maryam ta farka akan idon su. Har Abbi da Abbah da sauran yan uwa aka fadawa cigaban da aka samu akan Maryam baku ga murna ba sai kace wanda akace ta tashi.

Bayan isha'i suna haramar tafiya dan Ammi tace su tafi suna hada kaya ana dan hira sama sama duk akan Aliyu ne da rasuwar sa. Wanda tin da suka fara maganar sa Maryam ta farka amman batai motsi ba tana jin duk abinda ake. Sai da Yaa Abdullah yace
"Munyi rashin Yaya mai son mu da kaunar mu. Allah ya jikan Yaa Haidar!"

Wannan ya tuno kuma ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba. Lallai ta rasa Yaa Haidar har abada. Ji tayi ina ma daga wannan kwanciyar itama mutuwar ta dauketa. Ya zata yi da rayuwarta ba tare dashi ba?

Hawaye ne ya zubo ta gefen idonta. Yaa Abdullah da ya karasa gefen gado dan dauko flask ya kalle ta sai yaga hawaye na bin gefen fuskar ta da sauri yace
"Ammi ta farfado."

Da sauri Mamah ta karasa gefen gadon tana fadin
"Alhamdulillah!"
Sai ta kamo hannun ta da ba a sawa karin ruwa ba, tace
"Ki bude idon ki Maryam kinji."

Yaa Abdullah yace
"Alhamdulillah kwana goma sha yau Allah ya dawo mana dake dan Allah ki bude idon ki Maryam!"

"Subhanallah! Innalillahi wainna illahir rajiun har kwana goma sha, Ta tabbatar ta rasa Yaa Haidar kenan. Garin yaya aka barta a kwance har ta kai yanzu ba'a bari ta sake ganinsa ba? Saboda me akai mata haka?"
Ta fada cikin zuciyar ta tana sake runtse idon ta, ji tayi gwara ta cigaba da kwanciyar har nata lokacin ya yi, amman tayaya zatai rayuwa ba Yaa Haidar.

Ammi da sai yanzu ta mike ta karaso ta kalleta da tausayawa kwalla ta cika mata ido, dan itama Maryam ba karamin tausayi ta bata tace
"kiyi hakuri Maryam Shima ba gaggawa yayi ba. Mu kuma da kike ganin mu a nan ba jinkiri muka yi ba. Duk mai rai yana da wa'adin da Allah Ya dibar masa na rayuwar duniya. Mutuwa nada daci amma babu abinda hakuri da tawakkali ya bari. Kiyi hakuri haka Allah ya tsara babu yadda zamuyi sai mu amshi jarabarwa mu muce Alhamdulillah!"

Maganganun Ammi suka sake saka mutanen dakin kuka. Dan daman kukan suke tinda suka ga Maryam taki bude idon ta sai mutuwar ta dawo musu sabuwa fil. Maryam kuwa duhun da take gani ido rufe ya fiye mata akan hasken da babu Yaa Haidar a cikinsa. Duk yadda aka rinka rarrashinta sam taki yarda ta bude idonta balle ta tashi zaune.

Suna haka suka ji sallamar Abbi. Amsawa sukai ya shigo yace
"Ya naga kuna kuka me kuma ya faru ta farka ne?"
Ammi tace
"Ta farka amman taki ta bude ido."

Abbi ya karasa gefen gadon ya kamo hannun ta dayan hannun ya daura akan ta yana shafawa, zuciyar kowa ta kara karyewa har Maryam dake kwance tana jin komai. Abbi cikin sanyin murya yace
"Mama nah kuka ba soyayya bane tsakaninki da Aliyu soyayyar shine kiyi masa addu'a da fatan samun rahmar Mahaliccinmu. Soyayyar da zaki nuna masa kenan addu'a. Da iliminki amma ace kin kasa karbar kaddara? Dukkanmu nan jiran lokaci muke yi. Ki daure ki tashi indai ba kina son ki nuna cewa kinfi karfin jarabta daga Allah ba."

Jin haka Maryam ta bude idonun ta da suka kumbura da kyar. Dishi dishi ta fara gani a hankali kuwa taga Abbi tsaye gefen ta dayan gefen Mamah da Ammi, can kuma Yayen ta kowa hawaye yake yi. Wani kuka ne ya kwace mata nan ta shiga yi suna taya ta. Abbi ne yai karfin halin rarrashin su wanda Maryam kuwa tini numfashin ta ya fara neman daukewa da sauri aka kira likita ya zo ya saka mata oxygen sannan yace
"A kula da abinda za a fada mata da zai sa ta shiga damuwa ko wani halin!"
Jiki ba dadi su Mamah suka tafi.

Washe gari da safe asibiti ya cika da yan uwa da abokan arziki saboda anji cewar Maryam ta farka. Wanda kowa yake murna sai dai me har goma da wani abu bata tashi ba. Abbi da kan sa yaje wajen likita dan jin ko lafiya Maryam bata kara tashi ba. Tare suka zo ya kara auna ta sannan ya basu tabbacin zata tashi a ko wanne lokaci. Wannan ya dan kwantar musu da hankali.

Karfe daya mazan duk sun tafi masallaci sai matan da wasu ke sallah wasu na zaune jigum jigum. Aisha ce zaune a kan kujera gaban gadon, tana rike da waya tana dannawa akai akai tana kallon Maryam. A hankali ta bude idon ta, ta dinga bin dakin da kallo da sauri Aisha ta mike tana fadin
"Besty kin tashi?"

Juyowa tayi ta kurawa Aisha ido, ko me ta tuna sai kuma hawaye ta bude mata hannu da sauri Aisha ta karasa ta rumgume ta. Yaya Fadima da fitowar ta daga bandaki kenan ta karaso. Mamah ma da idar da sallah ta kenan ta tashi tana fadin
"Alhamdulillah sannu Maryam!"

Ido Maryam ta dago ta kalli Mamah wani kuka ne mai karfi ya kwace mata. Mamah ta karasa ta rumgume ta tana shafa kan ta hadi dabata baki. Lafewa tayi a jikin Mamah. Ammi ma bayan ta idar ta karaso tazo tai mata sannu matan Yayen ta da Yayyen ta da kannen Ammi dake waje duk suka shigo sukai nata sannu.

Su Abbi bayan an idar da sallah suka dawo suka samu dakin cike dan Maryam ta tashi. Likita aka kira ya kara duba ta bayan ya gama yace
"Me yake miki ciwo?"

Kallon sa kawai tayi ta nuna kirjin ta, dubata ya kara yace
"Ya yake miki ciwon?"
Yan dakin ta kalla amman ta kasa magana, Abbi ya karaso yace
"Mama nah fada masa ya yake miki ciwo!"

Da hannu tai masa alama. Doctor ya kalla yace
"Ka gane?"
Kai ya gyada. Abbi yace
"Amman meyasa ba magana?"



*Wasu na fadin basu gane ba, to daga FLASH BACK na tafi rayuwar Maryam ne kan tazo gidan su Ummi da Yaa Haidar (rayuwarta ta baya) wanda a gaba na tabbata zaku gane, ba wannan Aliyun miskili bane ya mutu, wata rayuwar Maryam ce kan tazo wannan rayuwar da fatan kun gane, sannan ku cigaba da bina sannu a hankali, zaku gane komai insha Allahu.*

*Allah ya jikan musulmai Allah yasa muyi kyakyawan karshe, Allah kyautata namu zuwan. Amin*




Maryam Suleiman
*Antty*


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 27

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



"Muje office!"
Doctor ya fada ya fita. Abbi da Yaa Muhammad suka bi bayan sa. Yan dakin kuwa sai murna suke suna mata sannu Maryam kuwa ba magana sai hawaye dake zuba a idon ta kawai.


Abbi ne zaune shida Yaa Muhammad sai Doctor dake duba file din Maryam. Mikewa yayi yace
"Ina zuwa!"
Sannan ya koma dakin ta. Sallamar su yayi dan su basu waje aka barta ita dashi sai wasu nurses sawa sukai ta mike tayi tafiya sannan suka sa tayi motsi da wasu part din jikin ta, bayan ta gama yace
"Yi min magana Maryam!"

Idon ta ne ya kara cikowa da hawaye sai ta girgiza kai alamar ba zata iya ba. Duk yadda yaso tayi bata iya

Please Login or Register in order to submit comment