Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta nufi dakin Aliyu, ajiyewa tayi ta zauna tana fadin
"Ana sallama ne?"
"Eh gata nan sai kuka take sai kace akan ta aka fara aure."

Tai murnushi ta mike tace
"Bari naje Abban ku ya dawo."
Ta mike ta fita, da kan sa ya zuba mata abinci ya mika mata ta dauka zata ci ta kalle sa tace
"Kaima baka ci komai ba Yaya."

"Ke dai kici."
Fuska ta shagawabe kamar zatai kuka tace
"Please come and join me."

Ta saka masa spoon tare suka ci abincin a plate daya suna cikin ci Ummi ta shigo har suka gama sannan Maryam ta dauke kwanukan ta dawo tai masa sai da safe ta tafi.

Aliyu kuwa wanka yayi yazo ya kwanta dan yai bacci amman sam bacci yaki yazo sai tunanin da yake wanda ya haifar masa da zazzabi da ciwon kai, duk da halin da yake ciki haka ya mike yayo alwala akan sallaya ya kwana har asuba bai bacci ba sai da ya dawo daga masallaci yasha maganin bacci da kyar bacci ya dauke shi.


A bangaren Maryam ma haka bayan tai wanka ta kwana a kusa da Basma kasa baccin tai sai juyi da take wanda ganin zata bata lokaci ne a tunani ta mike ta tada sallah kwana tayi tana sallah da addu'a akan auren ta da rayuwar ta ta baya Allah ya dawo mata da komai wanda ta sha kuka kan asuba idon nan ya kumbura, fuskar ta tai jawur ga wani ciwon kai tana sallah asuba bacci ya dauke ta a wajen da tai sallah.



Karfe goma ta farka da wata matsananciyar faduwar gaba, mai gyara ce tazo dan haka nan aka hau mata wanda ya dauke su awa biyu sha biyu aka gama ta shiga tai wanka da ruwan turare ta fito ta turare mata jikin ta da kamshi mai dadi da sanyi, zama tayi mai make up tazo zatai mata kememe ta hana tace bata so, wani ubansun less fari tas aka dauko mata ta saka riga da zani ne sai farin mayafi wanda duk stones din su fari tai daurin ta normal amman sai tai kyau sai kyal-kyali take da ka kalle ta zaka san bata cikin nutsuwar ta, gefen gado ta koma ta zauna Jawahir ce ta shigo tana buda hadi da fadin
"Amarya ta ango."

Maryam ta dago ta kalle ta cikin wani yanayi mai wuyar fasallatawa, Jawahir ta karaso cike da damuwa tace
"Lafiya Sister me yake faruwa ne tin jiya naga yanayin ki ya canja dan Allah ki kwantar da hankalin ki yaya yana son ki muma muna son ki to damuwar menene su Ummi kuna tare na tabbata Yaya zai miki abinda kike so dan Allah ki saki ranki Yaya ta uwar Ya'yan Yaa Khalifa, Yayar Jawahir."

Najwa da Basma ne suka shigo suna fadin
"An gama shiryawa ne?"
Najwa tace
"Ah ya ba ai make up din ba?"

Basma tace
"Tace bata so."
"Amman saboda me Maryam?"

Kai kawai ta dauke dan ko magana ma bata so, Najwa ta mike tace
"Uhmm kinci abinci to?"
"Bata ci komai ba."
Basma ta fada.

Najwa tace
"Jeki ki debo mata ni bana son amarya da rashin cin abinci dan nima lokaci na ban zauna ba cin abinci ba."
Jawahir tace
"Miskilancin Amarya ya tashi yau ango zai sha fama."

Najwa tace
"Da ta shiga hannu zata sake."
Sukai dariya. Wayar Najwa ce tai kara ta kai kunnen ta tana fadin
"Hello Aisha."

Tai shiru tana sauraran ta can tace
"To shikenan zan turo miki ai nazata yau ma ba zaki iya fitowa ba."
Tai shiru sai tace
"To sai kinzo."

Ta kashe wayar tana kallon Maryam da take danna wayar ta wanda bata san me take dannawa ba dan bata jin dadi duk jikin ta wani iri yake mata ga damuwa da take ciki, ga faduwar gaba, Najwa tace
"Ina makwabciyya ta da nake baki labarin sun dawo daga Canada last month ita ce zata zo kinsa bata samu tazo kowanne event ba saboda tsohon ciki gareta bata jin dadi amman tace yau zata zo."

Wacce akewa maganar ma bata san anayi ba sai da Jawahir ta tabo ta, ta dago da sauri, Najwa tai dariya tana fadin
"Wai wannan har bakin ya mutu yau za a shiga hannun mazaje ai ke ki godewa Allah ma da saurayi ne, hmmm wallahi in da mai mata ne ko,? Ko irin su Yaa Aliyu da aka jima da rasa mata sai ya kusan kashe ki."

Dagowa Maryam tai idon ta cike da kwalla, Najwa tai saurin matsowa tana fadin
"Me ya faru Sister dan Allah ki kwantar da hankalin ki."
Ido ta lumshe kawai. Basma ce ta shigo hannun ta rike da tray ta ajiye a gaban Maryam tace
"Ummi tace ki shanye peper soup din nan tas."

Ture kayan tayi tana kokarin kwanciyya akan gado Najwa ta taro ta tana fadin
"Kisha ko tea ne da peper soup din, wallahi zaki wahala in kika ce ba zakici komai ba."

Ummi ce ta shigo tana fadin
"Ina Maryam din maza kici abincin nan kinji ko?"
Maryam ta kalle ta cike da damuwa Ummi tace
"Dauki kisha naza ina kallon ki."

Tea'n da Ummi ta hada mata mai kauri ta dauka ta sha jin dumin sa yasa ta shanye tas Ummi ta sata agaba ta sha peper soup sai da ta gama sannan ta fita, komawa tai ta kwanta, karfe daya tayo alwala ta tada sallah.


*
Bangaren Aliyu ma sai wajen sha biyu ya farka dan rabon sa da bacci yau kusan kwana uku in ya kwanta ko awa bayayi yana bacci sai tunani da kwana akan sallaya, jiki a mace ya mike ya shiga ya jima a bandaki ya fito ya zauna a gefen gado yana goge jikin sa mai ya shafa sannan ya mike ya taje gashin kansa. Wata sabuwar farar shadda ya saka wacce take kyalli ta warwali, yar ciki da babbar riga ce agogon azurfa ya saka ya murza bakar hula ya saka bakin takalmi hadi da feshe jikin sa da turare agogo ya kalla yaga daya saura, da sauri ya mike dan yana son ya samu hudubar juma'a,

Counter ya dauka tare da wayar sa da mukullin motar sa, fita yayi a dakin yana mai dannan counter din bakin sa na motsi alamar tasbihi yake yi, a haka ya fito falo wanda yai dai dai da fitowar Ummi daga bene har ya kai kofa tace
"Dr!"

Tsayawa yayi ya juyo yana amsawa, ta karaso tana fadin
"Na shiga yau wajen uku kana bacci kaci abinci?"
Agogo ya kalla yace
"Ummi in an sauko zanci bari naje kar na rasa sallah."

"Wanne masallacin zaka kasan dai yau za ai daurin auren Maryam."
"Ummi ai acan muke sallah."

"To adawo lafiya Allah kiyaye hanya."
"Amin."
Ya juya ya fita.


A bakin gate din masalacin suka hadu dasu Abbi bayan yai parking motar sa, ya karaso yana kallon su duk kansu basa cikin walwalar su, ya durkusa ya gaishe su, Abba yace
"Allah maka albarka."

Kai ya amsa yana fadin
"Amin Abba."
"Kayi hakuri da duk abinda yazo maka a rayuwa wani abun alheri ne a rayuwa, sai daga baya za a gani, mu iyayen ka ne duk abinda zanuyi maka rashin so ba zai saka muyi maka ba sai dai son da muke maka Allah maka albarka."

Kasa gane maganganun su Abbi yayi, Abbi yace
"Mu shiga daga ciki."







*Allah ya jikan musulmai ya kyautata nanu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya. Allah yai mana rahma. Amin.*





*Antty*
[12/1, 18:00] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 67

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Suka shiga a gefen Abbi Aliyu yai sallah. Ana idar da sallah liman ya nemi shaidun madaura auren da za ayi, Abba da Abbi da Yayan su Ummi suka karasa wajen Liman, nan aka bada health status din amarya da ango Abba ne ya zaro kudi a aljihun sa ya ajiye a take aka daura aure.

Aliyu dake zaune a inda yake bai taba zaton sunan da yaji an kira na angon ba ana daura auren, haka ya dinga kallon Abba da Abbi ko kiftawa babu, Farouk ma cike da mamaki yake kallon su Abbi. Aliyu kuwa ko motsi ya kasa, can ya lumshe ido ya bude zuciyarsa na bugawa.

Abba ne ya karaso wajen ya sakar ma Aliyu murmushi yace
"Ina fatan ba zaka bani kunya ba. Allah ya taya ka riko."
Kasa gane inda zancen Abba, Aliyu yayi.....


*
Maryam ce kwance akan gado bayan ta idar da sallah counter ce a hannun ta tana dannawa tare da motsa bakin ta, idon ta a lumshe yake, Jawahir da Najwa na falo suna zazzaune, Basma ce kadai zaune a gefen gadon, kamar ance ta bude idon ta ya sauka akan agogon dakin su wanda ya nuna biyu da yan mintuna, bugawar zuciyar ta ce ta dadu tai saurin mai da idon ta, ta rufe tabbas tasan by this time an riga da an daura auren shikenan ta zama matar Muhammad Auwal, wani yanayi ta fada wanda ta kasa gane wane iri ne, mamakin ta daya zuwa biyu, shine na rashin ganin sakon Muhammad wanda tasan a duk halin da yake yai alkawarin shi zai fara shaida mata daurin auren su, to amman meyasa bai fada mata ba ko da yake dama fada ce tasa kawai tayaya yana cikin mutane zai samu damar sanar mata.

Guda taji ana yi a kasa wanda ya kara sawa faduwar gaban ta, dan har sai da ta dafe kirjin ta, ta runtsa idonta, tana karanto addu'a a ranta ko zata samu natsuwa daga bugawan da zuciyarta ke yi,

Daga masallaci gaba daya gida suka yo, Aliyu kasa tukin ma yayi gaba daya, Abba da Abbi na mota daya a haka suka shigo cikin compound din wanda yake cike da yan uwan su dan yadda suka dauki Maryam tamkar yar Ummin ce dan haka tai gayya abokan ta da yan uwa haka ma Mami, ga Hajiya Inna gasu Anty Asiya da Hanna kowa da tawagarsa, Mami ce ta fara hango su Abba daga ganin yanayin su ya nuna mata basa cikin nutsuwar su ba tin yanzu ba tin kafin su fita ma, tana ganin Aliyu ya fito a mota ya nufi bangaren Ummi, Abba yace
"Aliyu!"

Juyowa yayi yace
"Zo muje bangaren Abbin ku akwai maganar da zamuyi."
Suka juya suka nufi bangaren Abbi, da sauri Mami tabi bayan sa, a falon Abba da Abbi ne da Yayan su Mami zaune akan kujera sai Aliyu da Farouk dake kasa, Mami ce ta shigo da sallama a bakin ta, suka amsa ta karaso tana fadin
"Lafiya kuwa?"

Kai Abbi ya girgiza ya fada mata duk abinda ya faru, Zama Mami tayi cike da damuwa tana fadin
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Aliyu ta kalla wanda yake jingine da kujera ta kasa gane a wane hali yake amman tabbas yana cike da shock din abunda yaji. Abbi ya kalli Mami yace
"Kije ki kira Aisha da Maryam har da Inna da Sitti dan suji ko me yake faruwa."

Mami ta mike ta fita, Mama ce ta shigo kamar an jefo ta dan hankalin ta a matukar tashe yake bata son wannan auren ya tabbata taki jinin taga Maryam cikin jin dadin rayuwa dan haka ganin shigowar su Abbi ya sa tasan lallai da akwai damuwa, magana zatai Abbi ya daga mata hannu tare da nuna mata waje yace
"Zauna."

Zama tayi tana kallon yan dakin, ba a dauki mintina ba Ummi ta shigo dakin tare da Anty Nusaiba autar Inna, ba a jima ba sai ga Inna da Sitti nan sun shigo, cikin kaya iri daya wanda Aliyu ya dinka musu dan yin fitar biki.

Ummi ce ta kasa nutsuwa cike da damuwa dan har jikin ta wani irin tsuma yake ta kalli Abbi tace
"Meya faru ne Abbi?"

A hankali Abbi yace "Lafiya lau"
Ba tare da ya kalle ta ba, jikin ta ya kara sanyi, dakin yai shiru Inna da Sitti kuwa sai kallon su suke, can Inna tace
"Shanyar bata bushe bane Suleimanu?"

Mami ce ta shigo dakin rike da hannun Maryam da ta yafa mayafin ta akan ta, tafiya take kawai amman bata san inda take saka kafar ta ba a haka suka karaso parlon Abbi, ta zaunar da ita a gefenta.

Kan Maryam a kasa cike da fargaba wanda yasa gabanta sai faduwa yake, Abba ya bude wajen da addu'a sannan a hankali yace
"Babu amfanin tsaya jan zance ko wani boye boye, kuma ina son kowa a nan ya dau abinda ya faru yau a matsayin kaddara wanda aka ce ta riga fata, mu ma ba haka muka so ba, kowa ma ba haka ya so ba, sai dai kawai mu kara gode ma Allah don shi ya san dai dai, kuma duk abinda ya faru ga bawa mai kyau ko akasin sa kaddara ce daga Allah wanda in ka cinye wannan jarabawar Allah zai maka sakayyah da abu mai kyau a rayuwa, duk abinda ya faru da bawa mai kyau ko akasin sa ce ne Alhamdulillah Allah zai baka lada dauke ka amshi jarabawar kada kace kai kadai Allah ya daurawa abu kaza....."

Inna tace
"To Shehu jan ran yai yawa dan Allah ka daure ka fito ka fara fada mana me ya faru dan bakaji yadda ciki na ya murda min ba."
Abbi yace
"Akan zancen auren Maryam ne wanda a takaice dai babu zancen auren Maryam da Muhammad..."

A razane mutanen dakin suka dago suna kallon Abbi da yai maganar cike da razana da gigita bama Ummi da tafi kowa rudewa, Mama kuwa murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta kasa boye abinda ke ranta abinda yasa yan dakin basu gane me take ciki ba saboda damuwar da suke ciki ne.

Shiru dakin yayi kamar ruwa ya cinye su, baka jin komai sai numfashi da karar fanka da AC, Sitti ce tai karfin furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa Suleiman"

Yaya Shuaib babban dan Sitti yaya ga su Ummi yace
"To sai dai ayi hakuri, bamu taba zaton haka ba, komai ya samu bawa a duniya dama rubutattce ne, kuma babu wanda ya isa ya kauce ma kaddararsa, wannan yaro Muhammad dai Allah ya rubuta daman can ba mijin Maryam bane dan haka duk abinda ya faru sanadi ne, kullum addu'a mu Allah ya zaba mana mafi alheri to kila rashin alherin yasa haka, wanda kuma aka aura mata a yanzu muna fatan ya zama alheri a rayuwar ta."

Kalaman Daddy ya sanyaya musu rai sai dai duk da haka suna cike da fargabar abinda zai faru, Abba yai gyaran murya.


Yesterday @11:00pm
"Jiya Muhammad yazo, wanda ina can bangare na aka zo aka fada min wai Muhammad yana nema na, gane wane Muhammad yasa nasan akwai abinda yake bukata dan haka na nufo wajen Yaya inda na same shi na sanar dashi zuwan Muhammad din, Farouk ya aika akan ya shigo dashi, inda suka shigo dakin tare, cikin nutsuwa ya karaso amman daga saman fuskar sa zaka gane yana cike da damuwa da tashin hankali, anan ya zauna yai kasa da kan sa.
Gaishe mu yayi cikin ladabi da biyayya muka amsa sai yai shiru Abbi ne yai karfin halin cewa
"Muhammad ina fatan lafiya?"

Kasa magana yayi kuma ya kasa dagowa ya kalle mu, wanda abin ya bamu mamaki daga ni har Yaya kallon sa muke cike da mamaki, kasa magana duk mukai sai daga baya nace
"Muhammad kai mana bayani."

"Bansan ta ina zan fara ba amman tabbas ina cikin tashin hankali kuma tabbas ku zaku ceto ni daga halin da nake ciki tinda iyaye na sun kasa, idon su ya rufe sun ki yadda dani da abinda naje musu."
Yai maganar yana sheshekar kuka, wanda ya saka mana fargaba dan bamu san akan menene ba.

Nine nayi karfin halin fadin
"To Muhammad yi min bayani mai ya faru?"
Nan yai min bayanin komai........


Kallon mamaki ni, Yaya da Farouk muka bisa dashi, duk muka kasa magana sai can Yaya yace
"Amman Muhammad meyasa tin farko da mukai maka bayani baka yiwa iyayen ka ba tin alokacin in suna da ja sai asan me ake ciki ba yanzu ba."

Kansa a kasa yace
"Banyi haka da wata manufa ba nayi hakan ne dan kara samar mata mutunci tinda ba wanda yasan ita din ba yar ku bace wanda in naje na fada ko a gida basu ce komai ba nasan yan uwa wasu zasu samu abin fada wanda abinda bana so kenan a saka min mata a damuwa dan nima da naso sanin ta shiga damuwa bare kuma taji a duniya duk da eh na yadda amman kasan ba kowa ne zai yadda ba, Yanzu ma ina da tabbaci wanda yasan Maryam shi yaje ya kai maganar gida dan na tabbata da ba dan haka ba su Ammi ba zasu yadda ba."

Yaya ne yace
"To yanzu me kake so muyi Muhammad kazo mana a kurarren lokaci kana gani gobe za a daura aure wanda bai kai nan da awa sha biyu ba."
"So nake kuje wajen Dady na ku bashi hakuri tare da masa bayani."

Kai na fara girgizawa ina fadin
"Wannan ba mafita bace Muhammad tayaya zamuje mu bashi hakuri kenan tallan ta muke masa ko? Yadda za a kara kin ganin yar mu da daraja in har mahaifin ka na son ka da son abinda kake so ya kamata yazo ya fara jin ba'asi wanda daga nan sai ya yanke hukunci amman gaskiya abinda kake nema ba zai taba faruwa ba kayi hakuri..."

Rarrafowa Muhammad yayi gabana yana mai rokata Allah da annabi akan muje wanda naki tanka masa domin ba zan iya yin wannan danyen aikin ba. Ganin yana ta wannan kukan ya bamu tausayi, Abbi ya dago Muhammad yace
"Ka daina kuka Muhammad zamu duba insha Allahu duk yadda ake ciki zakaji zuwa gobe."

Nan ya zube yana tai mana godiya sannan ya mike Farouk yabi bayan sa abakin kofa ya barsa ya koma daki wajen mu ya dawo shiru ya same mu ya zauna bayan mintina na sauki ajiyar zuciya ina mai furta
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Ita ka dai na dinga furtawa domin ita ce kawai ma fita kai na ya kulle abinda ake gudun dai gashi ya faru, amman tayaya gidan mace zasuje neman bikon mijin tin ba ai aure ba sam wannan ba abun yiyuwa bane,

Yaya ne yai karfin hali yace "Kaga Usman kada ka damu, haka Allah ya tsara kuma Alhamdulilalh, da abin yazo tin kan a daura aure nima ban ga dalilin da zamuje neman auren ba tinda mahaifin nasa yace a'ah zamu hada musu kayan auren su a mayar musu, Allah yasa haka ne mafi alheri."

Abba yai wani murmushin karfin hali yace
"Amin kuma ba zan taba basu auren Maryam ba tinda sun nuna su kananun mutane ne, suzo su fara bincika mana suji halaiyar ta, shin ko karuwanci aka kama ta tana yi ai yanzu bata yi amman bakuyi bincike ba kuzo ku yanke hukunci zasuyi danasani tabbas, ai Muhammad dan sune suje suyi masa yadda suke so nasan yana son Maryam duk halin da ya shiga na rashin ta su suka jiyo, amman tabbas ba zan basu auren 'ya ta."

Abba ya mike zai bar wajen Abbi yace
"Shehu."
Juyowa Abba yayi Abbi yace
"Kada ka fadawa kowa komai bari har zuwa gobe?"

"Yaya ai ya kamata a sanar da fasa daurin auren ko?"
Kai Abbi ya girgxa yace
"Mu bari goben dai."

Kallon sa Abba ya tsaya Abbi yace
"I mean it."
"Allah kaimu sai da safe."

Ya juya ya fita dan lokacin wajen sha biyun dare kenan. Farouk yana wajen but he is speechless, sai da Abbi ya kalli shi yace
"Farouk dare yayi jeka ka kwanta."

Mikewa yayi jiki a sabule yaiwa Abbi sallama ya tafi ya kwanta, kasa bacci shima yayi a daren dan yana tunanin tayaya zai nuna yana son Maryam a gobe a aura masa ita bayan abinda Mama ta fada dole ba zai bi Mama domin uwar sa tace matsawar yace yana son Maryam bata yafe ba sai ta tsine masa dan haka ko da son Maryam zai kashe shi ba zai furta ba yau in su Abbi sun bashi zai musu biyayya tinda shima uban sa ne. Kwana yayi addu'a akan Allah kawo mafita kada iyayen sa su zama kananun mutane bayan sunyi gayya.


Today @12pm
Cikin shiri Abba ya fito ya nufi sashen Abbi, sanye da farar shadda sabuwa kal yar ciki da babbar riga sai zuba kamshi yake zaune ya same shi shima cikin irin shigar sa yace
"Barka da asuba Yaya?"

"Barka ka dai ya muka ji da wannan alamarin?"
"Sai godiyar ubangiji jiya gaba daya na kasa runtsawa saboda wannan matsalar."

"Nima haka amman da fatan ka samo mana mafita?"
Numfashi Abba yaja yace
"Babu tunani wandan da suka zo daurin aure yaya za ayi dasu ga mata nan sai cigaba da shagulgula suke."

Abbi yace
"Kyale su suyi ni nayi wani tunani akan lamarin ban sani ba ko zaku yadda dashi?"
"Wane tunani ne?"

"Allah ya bamu yara maza dole a ciki zamu dauki wani mu aurawa Maryam ko dan ceto martabar ta nasan in ba haka ba zamuji kunya itama rayuwa ta zata kara gurbacewa nasani mai son ta tsakani da Allah zai iya auren ta a haka amman matsalar shine iyayen sa da yan uwa kamar yanzu dai Muhammad yana so iyayen basa so to bana son taje inda za a tsangwame ta sam."
"Haka ne amman kai Yaya yanzu a cikin Aliyu da Farouk wa kake ganin za a aurawa."

"Zan so na aurawa Farouk ita."
Kallon sa Abba yayi yace
"Saboda me?"

"Yauwah Farouk yana da saukin kai da hakuri na tabbata zai rike ta da hakuri kuma naga yana kula da ita da tausayin ta."
"Haka ne saboda me ba za a bawa Aliyu ba?"

"Aliyu yana cike da damuwa har yanzu, bama wannan ba kasan Aliyu da zafin rai ga miskilaci ba kowa ne zai iya rayuwa dashi ba ina son inda Maryam ba za tai kuka ba."
"Amma Yaya kasan abinda muka guda shi zai faru in har Farouk ya auri Maryam kai kan ka shaida ne akan halaiyar Barira kana tunanin zata samu nutsuwar da muke so?
Aliyu mun isa dashi kuma burin mu yai aure in har muka bar wannan damar ban san kuma tayaya zamuyiwa Aliyu aure ba dan kullum bai da budurwa ko bai so Maryam akwai tausayi na sanin wacece ita kuma zasu taru su rufawa kansu asiri kuma Mami ba zata tsangwame ta ba zata cigaba da rike ta tamkar yar ta me kace Yaya?"

Kai Abbi ya jinjina yace
"Gaskiya ne amman Barira ai bata fi karfi na ba."
"Na sani amman hanyar lafiya abita da shekara Yaya muyi abinda ba zamu zo muna danasi ba ko? Ana cizon yatsa."

"Shikenan!"
Ya kalli agogo yace
"Daya tayi har da kwata tashi muje Allah yasa haka ne mafi alheri."

"Amin."
Suka mike suka fita akan idon Farouk wanda shima yabi bayan su, basu jima da fita ba Aliyu shima ya mara musu baya tare da sauran hadiman gidan dan duk a masallacin zasuyi sallah juma'a.



*
*Cigaban labarin*
3:15pm
Abba ne yace
"To wannan yasa muka daura auren Maryam da Aliyu."
Yana fadin haka, Abbi ya fiddo kudi a aljihunsa ya mika ma Abba. Abba ya amsa yace
"Ga sadakin Maryam 200k."
Gaba daya dakin kabbara aka dauka.

Aliyu da tinda yaji sanarwar auren ya kasa yadda da abinda aka ce yanzu Abba na maimaitawa ya sunkuyar da kansa yana mai tsabihi ga Allah.


*Am sorry for the late update, today am so busy*

*Allah yai mana rahma, Allah ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*




*Antty*
[12/1, 18:00] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 68

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Yesterday 10:00pm*
At Auwal House.
Abinda ya faru jiya bayan dawowar su daga dinner, wanda lokacin goman dare, yana shigowa gidan aka fada masa Dady na neman sa wannan yasa ya nufi bangaren mahafin nasa, zaune yaga Dad dinsa Ammin sa na safa da marwa wanda hakan ya nuna akwai wani abu da ya faru, da kallo suka bishi har ya shiga ya zauna.

Kansa a 'kansa yace
"Dad lafiya?"
Kan Dad yai magana Ammi ta hau fada
"Kana da hankali kuwa?"

Dagowa yayi ta koma ta zauna tace
"Ashe baka da hankali ace kana neman yarinyar da ba a sam asalin ta ba karuwa...."
Har tsakar kansa yaji wannan mummunar kalmar cikin damuwa ya dago ya kalli Ammi yace
"Ammi ba karuwa bace sam...."

"Rufe min baki, Khalifa in har ni na haife ka to ka sani ba kai ba waccan yarinyar ace har dan shege ne da ita amman kake son ta a haka? Shin asirce ka tayi, amman ka bani kunya to wallahi kaji na rantse ba

Please Login or Register in order to submit comment