Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dagowa tayi tana ganin sa bai magana ba kuma bai daina kallon ta ba karasowa tayi tana tsayawa ya shiga tare da bude dayan gefen yai mata nuni a hankali ta karasa ta shiga ta zauna motar ya tayar wannan yasa ta rufe kofar dan kada ta fadi in ya ja,

Sanyi da kamshi dake cikin motar su suka saka ta lumshe ido, cikin isa da jan aji ya tashi motar ba tare da ya dube ta ba cikin gwaninta ya fisgo motar da gudu sai da suka hau titin wayar ta, ta dauka ta saka a silent dan kar Muhammad ya kira, dagowar da zatai taga sun dauki hanyar gidan da ya kai ta jiya, tsoro ne ya kamata da fargaba kar fa ya hanata zuwa wajen yinin nan, amman bari taga gudun ruwan sa, har ciki suka shiga ya bude ya fita kamar jiya ya dawo ya bude mata kofa, kallon sa tayi tace
"Yaya wajen yini fa zani."

Kai ya girgiza yace
"Ba inda zaki dan nima ba zani ba, bana son hayani gwara kema ki saba da rashin son ta, bama wannan ba kina so kije maza suyi ta kallon ki a haka ko? Kinga yadda kakai kyau."
Kai ya girgiza, cike da damuwa take kallon sa tace
"Yaya nayi gayyata kuma wasu daga kawayen Najwa ni suka sani ba dadi."
Kallon ta kawai yake ta dago suka hada ido da sauri ta kawar da idon ta yace
"yunwa nake ji banci komai ba Unmi batai mana girki ba yau, mu shiga ki min abinci."

Kallon sa tayi ganin fuskar shi ba alamun wasa yasa tai kasa da kai tace
"Ayyah Yaya muje wajen anyi abinci sai na kawo maka."

Jingina yayi da motar sa tare da harde hannu a kirji yana kallon ta tace
"Kin taba ganin naci abincin waje bare na wajen biki?"
Shiru tayi yace
"Gwara ki sani bana cin abincin waje duk uzurin ki, sai kin min abinci kan kiyi abinda kike so."

Ya fada yana yin cikin gidan, tsayawa tayi a wajen kamar ta fasa kuka amman ba yadda zatayi tafi minti biyar tsaye ta rasa me zatayi taji wayar ta na vibrating dubawa tayi taga shine, kin dauka tayi amman sai ga wani kiran nasa nan, dauka tayi ta kai kunne yace
"Yunwa fa nake ji."
Yadda yai maganar sai da yasa tsigar jikin ta ta tashi.

Wayar ta kashe tace
"To ina ruwa na."
Sai kuma ta juya ta nufi cikin gidan, tana shiga baya falon farko na biyu ta nufa ta same shi kwance akan kujera yana kallo a TV kitchen ta nufa tana shiga ta dauki indomie ta dafa masa ta saka kifin gwangwani ta dafa wani kwan wani ta soya ta dauko ta kawo masa falo, a gabanshi ta jera komai ta koma ta zauna ya dube ta yace
"Me kika dafan?"

"Indomie."
"Ni bana cin indomie."
Ya fada yana tsure ta da ido, kai ta dauke ya janyo stool din yace
"Amman tinda kin dafa yaya zanyi?"

A ranta tace
"Kada kaci."
Ya bude kamshi ya daki hancin sa ya lumshe ido yace
"Zo mu ci."

kai kawai ta girgiza dai dai lokacin da taji vibration din wayar ta a cikin jakata ta ciro wayar har ta katse ta duba taga uban miss call ta duba su Jawahir ne da Muhammad da Basma dagowa tayi ta dube shi, sai abincin sa yake ci hankalin sa kwance, baki ta tabe tace
"Dan Allah yaya kai sauri suna jira na."

"Nai sauri muje ina?"
"Wajen bikin."

Dagowa yayi yace
"Amman ai nace baza a ba ko?"
"Yaya bikin fa Najwa ne."

"Bikin Najwa bikin ki ne?"
Shiru tayi ya cigaba da cin abincin shi sai da yayi dam sannan ya mike yai ciki.

Sai da yaji ana kiran sallah sannan ya fito ya fita anan tai sallah sai bayan ya idar ya kira ta a waya yace
"Fito mu tafi."
Ta fita suka shiga mota suka bar gidan ganin sun dauki hanyar wajen bikin yasa ta fara murna amman sai taga ya dauke hanya, ranar dai a haka suka yi ta yawo a gari har taran dare, kuka ne kawai Maryam bata yi ba dan haushi wai ace biki kamar na Najwa bata guri ai da takaici gashi ya amshe wayata ya kashe sai tara ya maida ta gidan Sitti shima da kyar dan da cewa yai gida zai kai ta sai da tai ta rokan sa sannan ya kai ta gidan Sitti.

Tana shiga ta wuce dakin Sitti ta fada gado tana sakin kukan da bata samu tayi shi ba, Najwa da Jawahir dake compound sukaga wucewar ta suka biyo ta da fada Najwa ta shigo amman ganin tana kuka sai ta sakko tana tambayata menene? cikin kuka takece mata Yaya ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani zuwa gurin yinin, Najwa tace
"Ba komai kila shima yana da dalili."

"Wanne dalili? shidai burin shi ya ga raina a bace."
Nan dai ta shiga lallashin ta sannan ta fita Jawahir ta kalle ta tace
"Wai Yayan nan ba son ki yake ba kuwa?"

"Kema zaki fara ko?"
"Allah naga takurar tai yawa."

Dan tsaki ta saki ta haye gado tana fadin
"Dan Allah Jawahir kada ki fara."
"To taso muci abinci yanzu Yaa Muhammad ya kawo."

Shiru tai mata Jawahir ta hau gadon ta juyo da ita yace
"To wai menene?"
"Yaya ne mana duk ya batan yau dina."

"To menene sis yanzu fushin zai dawo miki da lokacin ne?"
Kai ta girgiza, Jawahir tace
"To please forget about it, let continue celebrate the rest day."

Ta kamo hannun ta suka sauka kasa tace
"Bari na kira Basma."
Ta mike ta fita tare suka ci Basma da Najwa da Jawahir da Maryam, nama ne da wani hadin salad, bayan sun gama suka zauna hira sune har karfe biyu idon su biyu, sannan suka kwanta.

Washe gari aka daura auren su Najwa da Abdul, da safe, bayan anyi reception, suka karaso gidan Sitti, anan akai hutuna, Maryam na daki akwace wayar ta ta hau kara, tana dubawa taga Muhammad ne yace
"Ina kika buye ban ganki ba sai zuba ido nake."

"Ina daki kunzo ne?"
"Yes gamu a sitting room naga kowa ban dake."

"Uhmm."
Yace
"Common my dear zo inga kwalliyar ki ai mana picture kinji."

Yana fada ya kashe wayar ta mike ta dauki rigar ta da ta cire ta saka wata army green kalar shadda wacce tai mata kyau ta dada haskaka ta, red mayafi ta yafa a kafadar ta, ta saka wani flat red takalmi ta daura dankwalin ta ta nufi stting room tana shiga ya taso ya karaso waje ta, a bakin kofa ta tsaya ya durkusa a gaban ta ya zaro wani box a aljihun sa ya bude wani zuben gold ne mai tsada a ciki ya dago yana kallon ta yace
"Will you marry me?"

Kallon sa ta tsaya yi, ya sakar mata wani murmushi mai sanyi ido ta lumshe tana sakin murnushi tare da gyada masa kai, yan dakin ne suka hau tafi ya kamo hannun ta ya zura mata zoben ta dago hannun ta tana kallon zoben, ya mike ya karasa wajen ta nan aka hau daukar su pictures tare akai musu da amare da ango Jawahir na wajen Yaa Farouk bata san me akai ba, Hauwa kawar Najwa tace
"Wannan shine Yayan naku?"

Najwa tace
"A'ah abokin Abdul ne fa."
"Tab gaskiya shima yana son ta, ko Yaya za ayi?"

"Uhmm ita tace Yaa Aliyu ba son ta yake ba."
"Uhmm kinga banganshi ba ko? Amman duk wanda zai ji yadda yake mata wallahi yasan son ta yake."

"To ni dai dukka ina son su, zan fi son ta da Yaa Aliyu dan indai da gaske Yaa Aliyu na son ta to tabbas ba son wasa yake ba dan ko matar sa da ta rasu hadasu akai amman ita kuma ace yana son ta after so many year of lossing his wife kai da naji dadi wallahi."

Tai murmushi tace
"Allah ya zaba mafi alheri ai Maryam abar so ce."
"Gaskiya ba ruwan ta gata da hakuri sosai."

"Uhmm Allah sarki."
Wajen su tayo suka gaisa da Hauwa dan bata san zuwan ta ba anan mazajen suka tafi suka bar yan mata suna yinin su. da daddare aka kai Najwa gidan Abdul

Suna zaune a dakin Najwa Muhammad ya kira ta, ba dan taso ba ta mike ta nufi bakin gate yana cikin mota layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace
"Ina yini"
yace
"Lafiya lau Baby."

"Masha Allah an gama biki lafiya Allah basu zaman lafiya"
tace
"Ameen"

yace
"Sauran namu ko?"
Fuska ta rufe da hannu, yace
"Eh mana dan kin nace sai kin gama karatun nan naki ne amman da nima kwanan nan zamuyi mu huta ko?"

Shiru tayi yace
'Ke za a bari yar zaman daki."
Ido ta zaro tace
"Da girma na."

Yai murmushi yace
'Gaskiya ke zaki sa musu ido su kasa sakewa ko?"
Tace
"Yaushe ango zai zo ne gida nake son tafiya."

"Ah haba tin yanzu ai sai anjima kar ki damu ni zan kai ki gida da kai na."
Shiru tayi tace
"To ni dai su Ummi na ciki bari na koma kar su zo tafiya su ganni waje da kai."

"Ke kuma gaki bafulatana ko?"
"Uhmm."
Yace
"Ban gaji da ganin ki ba."

"Uhmm please ba anjima zaka dawo ba."
"Kawai dai dan kince su Ummi zasu fito ne."

Motace tazo ta tsaya a wajen, ta juyo tana kallon motar, Gabanta ne ya fadi ta juya da sauri, Muhammad yace
"Kamar Yayan ku ko?"

Kai ta gyada tace
"Shine"




*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Allah mana rahma ya yafe mana. Amin*



*Antty*
[11/28, 13:42] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 62

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Aliyu tinda yai parking yake kallonsu, Muhammad yace
"Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa"
shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali yace
"Ko bakya so?"

Tayi murmushi tana girgiza kai yace
"Bakya son yan gidanku su san ni kenan?"
D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni zan shiga ciki dan nasan su Ummi yazo dauka"

"Ohk"
gate ta nufa tana satan kallon Aliyu da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Muhammad kuma ya nufi inda yake, sauke glass Aliyu yayi ya bude motar ganin Muhammad, ya fito yana kallon direct cikin ido, Muhammad ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Aliyu ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Muhammad yace
"I am Muhammad Auwal"

Aliyu ya gyada masa kai kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace
"Aliyu Suleiman."
Muhammad yace
"Masha Allah it's nice meeting you"

Aliyu yace
"Same"
Muhammad yace
"Alright zan koma, zamu rako ango sai da safe"

Aliyu yace
"Ohk."
Suka kara musabaha sannan ya juya ya tafi, cikin mota ya shiga ya zauna, su Ummi suka fito ya kalli Ummi yace
"Ummi Maryam fa?"

"Tana ciki sai abokan ango sunzo zasu kawo su."
Kallon Ummi yayi yace
"Why?"

"Ai ba sa bar ta ita kadai ba ko?"
"Ita da waye a ciki?"

"Ita da Basma ne."
"Ummi please suzo mu tafi kawai me zasuyi mata dare nayi kalli agogo fa tara saura, sai yaushe kuma zasu zo please Ummi."

"Shikenan."
Ta juya ta shiga. Tana zuwa ta same su a zaune tace
"Yayan ku yace ku taso mu tafi."

Mayafin Najwa ta bude tace
"Ummi dan Allah su bari su karaso."
Kai Ummi ta girgjza tace
"Me zasuyi miki, tinda sun gyara ko ina kuma ba abinda zasuyi miki kawai su taso nasan suma suna hanya dare yayi kiyi hakuri kinji."

Kuka Najwa ta saka Ummi ta kalli su Maryam tace
"Ku tashi mu tafi"
Suka mike suka ce
"Sister sai gobe."

Ko kula su batai ba tana kuka suka fita. Maryam na fita ta shige baya, Basma ta shiga gaba, sai da Ummi ta lallashi Najwa sannan suka fito suka tafi gida.




Bayan gama bikin Yaa Aliyu bai kuma damunta ba sam gaisuwa ke hada su, bayan biki da sati daya su Momy da Basma da Yaa Aliyu suka fara shirin tafiya.

Yau a gidan Sitti ta yini, dan tinda aka gama biki bataje ba da dare tana shirin tafiya sukaji sallamar Yaa Aliyu, ya shiga ya zauna suka gaisa da Sitti, Sitti tace
"Ai nazata zaka tafi baka zo mun gaisa ba."

"Haba dai Sitti, in banzo ba ai ba zan tafi ba kenan."
Tai murmushi tace
"Uhmm nayi mamakin zuwan ka bayan nasan kai baka fiya son taro ba amman kana wata kasa ka dawo."

"Akwai wani abu da nake so nayi ne Sitti kuma nayi kinga sai na koma."
"Sauran wata nawa ka dawo?"

"Nan da wata takwas."
"To ni dai fatana kana dawowa kai aure kaji."

Yai murmushi yace
"Sitti kenan. Bari na tafi."
"To dan nayi maganar aure ko, Maryam tana ciki tafiya zatai sai ku tafi tare ko?"

Ya mike ya fita, ta kira Maryam tace
"Kije ku tafi tare."
Tace
"Sitti sai da safe."

Tunda suka dau hanya ita da Yaa Aliyu ba wanda yayi magana can yace
"Gobe zamu koma."
"Allah ya tsare hanya."

'Me kike bukata?"
"Ba komai."

"Kin tabbata?"
Kai ta gyada, dai dai lokacin da ya shiga cikin gidan, ya dan saci kallon ta ya dauke kai, yace
"Sauran na tafi ki cigaba da kula samari."

Yana fada ya fice ta tabe baki ta fita tabi bayan sa. Washe gari suka tafi, Maryam da Basma har da kuka haka suka rabu.

Makaranta suka koma suka cigaba da daukar karatu satin Najwa uku suka shirya zuwa gidan ta da Jawahir.

Ranar asabar suka shirya zuwa wajen Najwa gida Jawahir tazo suka tafi sunga tarba wajen Najwa kamar tai musu me aka cika musu gaba da kayan abinci da na sha kala kala sai dare suka tafi.

Abu daya ta kasa ganewa game da Yaa Aliyu yadda ya canja mata gaba daya, yakan yawan kiran ta tare da mata tambayoyi akan rayuwar ta da karatun ta, tin tana dar dar dashi ganin ba fada yasa ta dan sake take iya fada masa duk abinda take ciki, sai dai in yana bugar cikin ta akan Muhammad ne take shiru, amman bini bini zai kira ta wani abun lokacin ma ya rasa me zai fada mata, amman wannan ya bashi damar kara sanin ta da sanin a halin da take ciki. Yasan lokacin da take karatu da zuwa makaranta da komai.

Zaune suke ita da Muhammad a harabar gidan su suna hira, bai yi awa daya da zuwa ba amman ta amsa wayar Aliyu yafi sau biyu, kallon ta yayi yace
"Wai da wa kike waya ne?"
"Yaya ne fa."

Fuskarsa cike da mamaki yace
"Wanne Yayan?"
Tace
"Yaa Aliyu."

Jingina yayi da kujera yace
"Wani lokacin ina jin tsoro Maryam."
"Tsoran me kuma?"

"Tsoron rasa ki."
Wani murmushi tayi tace
"Tayaya zaka rasa ni?"

"Yayunki suna son rabani dake."
Dagowa tayi tace
"Kamar ya kenan?"

"Yadda na lura dukkan su son ki suke."
Da sauri ta dago tana girgiza kai dan bata son ana fadin haka, ita ta sani Aliyu tausayin ta yake kawai, Yaa Farouk kuma me yayi za a ce son ta yake bayan bai taba nuna mata ba in banda kyautatawa ita da Haidar me yake yi da za ace son ta yake.

"Ke ai ba zaki gani ba, bansan kuma saboda me ba?"
"Saboda na yadda dasu kuma na dauke su a matsayin yayye na kuma suma haka."

Wani murmushi yayi yace
"Shikenan ko a yanzu wani bai fada miki ba a gaba zaki gane tabbas son ki suke."
"Dan Allah kabar fadar haka a duk lokacin da aka fadan ana tada min da hankali."

"Akwai wanda ya taba fada miki kenan?"
Mikewa kawai tayi tace
"Zan shiga ciki ka gaida su Momy."

Tana fada tai ciki, cikin wani irin yanayi, dakin ta ta shiga ta zauna tare da dafe kanta tana so ta gano son da ake cewa Aliyu yana mata sam ta kasa gano shi dan in zata tuna sam Aliyu bai son zama a inda take a baya dai da tana da cikin Haidar ta dan samu kulawar sa amman tinda Haidar yazo duk kulawar ta koma kan sa wanda sai ta kwana nawa bata ganshi ba, kuma ina tana waje bai faya zama ba, takura mata da ya fara akan Muhammad ne yaso ya tada mata hankali akan son sanin asalin ta, wanda take ganin tausayin ta da fargabar kar ta fada wani hali ne yasa yake bata wannan kariyar to tayaya za a ce Yaya yana son ta, ai Aliyu yafi karfin ta tasan ruwa ba sa'an kwando bane ba takai matsayin da zai so ta ba sam ta girgiza kai, kiran sa ne ya shigo taki dauka amman sai da ya kira sau uku sannan ta dauka murya a sanyaye, ya amsa sallamar tare da tambayar ta me yake damun ta?

Ido ta lumshe tace
"Ba komai."
"A'ah Maryam muryar ki ta riga da ta fada tunanin me kike?"

"Tunanin rayuwa."
Ya dan ja numfashi yace
"yana da kyau amman kar a zurafafa."
"To."

"Ina Haidar?"
"Yana waje."

"Ke kina ina?"
"Ina daki."

"Ok sai anjima."
Ya kashe wayar, ta dafe kai tana mai ambaton sunan Allah, kawai dai kishin Muhammad ne yasa yake son yace son ta suke.

Haka next zuwan nasa da yazo Aliyu ya dinga kiran ta fuska ya hade yace
"Wai ke da waye ne?"
"Yaya ne fa."

Fuska ya kara hadewa yace
"Ranan na miki magana akan Yayan ki na sonki kin ki yadda to meyasa yake yawan kiran ki."

Wani kallo tai masa tace
"Shikenan kuma ba zamuyi waya da dan uwa na ba" "Bance ba amman abun yai yawa yau da muharamin ki ne wallahi ba zan damu ba amman ni ina tsoro kar na rasa ki."

"Kana kishi dai, yanzu kai dan yar uwar ka ta kira zan hanaka yin waya da ita ne? Ni kake dauren fuska dan ina waya da su, yaye nane, kuma dole ka amshe su a haka duk da ba ciki daya muke ba amman sun min abinda ko yaye na da muke uwa daga uba daya zasu yi min dan haka bana son wani abu ya shiga tsakanin ku, ba zan yadda su bata maka ba kaima kuma haka."
Ganin ranta ya baci sai ya lallabata a haka suka rabu.

Yau tin karfe biyar yake kiran ta amman wayar tana daki ita kuma tana tare da Muhammad da suke hira a compound din gidan ta bar wayar a daki ne dan tasan zai ta kiran ta ita kuma bata son ko da yaushe suna samun matsala da Muhammad akan wannan lamarin. Zaune suke suna hira cikin so da kaunar juna Muhammad yace
"Dear tinda yanzu kuna asibiti karatun ya ragu, nasan da kun dawo ba wani karatu zakuyi kamar na baya ba ki bani dama azo a fara shirye shiryen auren mu, wallahi na kosa naga kin tabbata tawa ina tsoron rasa ki."

"Jarumi baya tsoro."
Ta fada tana murmushi kasa kasa, yace
"Haka ne amman akan ki dole ayi dan ke din abar aji tsoro ce dan nasan akwai masu son kawon farmaki."

"Hmmm to Allah zaba mana mafi alheri."
"Ki ban dama na turo gida a saka mana rana."

Dagowa tai ta kalle sa, ya sakar mata wani cool smile tai saurin yin kasa da ido, yace
"Eh saboda asan da gaske nake kar wani yazo yai min kwab daya."

"Aikin kenan kar a kwace maka ni, please ka rage kawo abu a ranka sannan akai na ka amshi kaddarar ka duk wacce zata zo mana."
"Zanyi kokari."

Bayan ya tafi ta koma daki ta samu missed call din Aliyu har guda biyar, zama tayi ta dafe kai ta fara tunanin me zata fada masa in ya kira, bata tsaida ma tsaya ba wayar ta, ta hau kara ta dauka ta kai kunnen ta, Yace
"Ina kika shiga?"

Yai tambayar Murya ba wasa, tace
"Muhammad ne yazo."
"Oh har yanzu kuna tare ko?"

Shiru tayi, sai kawai ya kashe wayar, wayar tabi da kallo tana jin ba dadi dan bata son bacin ransa kwata kwata bama yadda yake kyautata mata. Samun kan ta tayi da neman layin nasa, yana gani ta kira amman bai dauka ba, kara kira yayi sai da ta kusan tsinkewa sannan ta dauki wayar, yace
"Hello."

"Yaya dan Allah kayi hakuri."
"Uhmm da akai me?"

Shiru tayi can yace
"In baki da abin fada sai anjima."
Ya kashe wayar, ajiye wayar tayi tana mai lumshe idon ta, kwanciyya tayi akan gado, sai bayan isha'i ta sauka kasa, Ummi ta gani da Haidar suna zaune, zama tayi a gefen Ummi, Ummi ta kalle ta tace
"Me yake damun ki ne?"
Kai ta girgiza tace
"Ba komai."

Jingina tayi da jikin kujera tana mai lumshe ido. Haidar ya tashi ya dawo kusa da ita yace
"Adda kira min Abbi."
Ido ta bude ta mika masa wayar ta, amsa yayi ya fara dailing number Aliyu yana kwance yaga kira da sauri ya dauka dan shima so yake yaji muryar ta dan ya saba da jin muryar ta duk bayan wasu lokuta, wanda ya zame masa jiki, jin muryar Haidar yasa yace
"Ina Addan taka?"

"Gata nan."
Ya mika mata waya, ta amsa tana kaiwa kunnen ta,
"Shine baki kirani ba?"

"To Yaya ba na kira ka kashen waya ba."
"Shine kikai fushi."

"A'ah."
"To ni na fada miki bana son kina kula samari ko?"

Shiru tayi yace
"Uhmm."
"To Yaya ni yaya zanyi? Su Abba sun riga sun bashi dama yaya zanyi?"

"Ki daina bashi fuska."
"Hmmm to."

"Oh Hmmm ko? Ba zaki iya ba ko?"
"Nifa bance ba."

"Bani Haidar."
"To kayi hakuri."

Ta bashi wayar tana mikewa, fita tayi ta bar wajen Haidar yace
"Abbi ya aiki?"
"Alhamdulillah Son ya makaranta?"

"Alhamdulillah."
"Abbi naga wani abu da nake so ka kawon."

"A in ka ganshi?"
"A school dazu."

"To gobe in kunje kasa Baba Driver ya samar min picturen sai Adda ta turo maka kaji?"
"To Abbi nagode."

"Ummi fa?"
Mika mata wayar yayi ta amsa, Ummi tace
"Aliyu ya aikin?"

"Lafiya lou Ummi ina yini?"
"Lafiya yasu Yaya?"

"Suna lafiya."
"Masha Allah."

Ta mikawa Haidar, Haidar yace
"Abbi sauran kwana nawa?"
"Kusan three month fa Son da saura."

"Abbi i miss u."
"Miss u more Son. Kunje shopping dis month?"

"A'ah."
"To zan turo muku kudi Adda ta kai ka kayi shopping kayi wasa kaji?"

"To Abbi nagode."
"Ina Addan taka?"

Tana kitchen."
"Bata wayar."
Ya tafi kitchen ya bata wayar, amsa tayi ta kai kunne yace
"Uhmm me kike a kitchen?"

"Abinci zanci."
"Baki ci abincin rana ba ko?"

"Uhmm a'ah."
"Kina nan da rashin cin abincin ki ko? Shiyasa gaki nan kullum bakya gaba."

"Kai Yaya kaima fa ba son ci kake ba."
"Oh ni zaki kwaikwaya?"

"In kanwa ta kwaikwayi Yayan ta menene a ciki?"
"Hmmm zan kamaki ne, but seriously kina cin abinci kinji my dear."

Murmushi ta dan saki tace
"Ok Yaya."
"Kici abincin i will call u later."

"Alright."
Ta kashe wayar tana zubo abinci, falo ta dawo ta zauna tana cin abinci tana kallo, Ummi tace
"Me ya hadaki da Aliyun ne?"

"Akan Muhammad ne."
"Me Muhammad din yayi?"

"Ummi Yaya baya son ina kula samari wai kar abinda ya faru kwanaki ya kara faruwa kuma ni naga Muhammad din kawai nake kulawa."
"Hmmm Allah kyauta to, banda abinsa tinda Muhammad yasan komai ai shikenan wanin ne dai bama fata ya kara zuwa bare ai ta fada masa rayuwar ki, tin kana haduwa da mutanen kirki har kazo ka hadu da na banza."

"Ummi shiyasa nake tsoron mazan nan, wallahi basu da tabbas a haka ma sun nuna suna son ka sun wulakanta ka ina ga ba wani son ka suke ba, rayuwa dai ta baci kowa ba amana Allah yasa mudace."
"Amin. Shiyasa ban fiya son doguwar soyayya ba shima Muhammad zanyiwa Abbi magana ai masa magana in da gaske yake ya turo iyayen sa ayi komai a huta, kusan shekara kuna tare."

Kasa tayi da kanta, Ummi tace
"Ko bakya son sa."
Shiru tayi Ummi tai murmushi tace
"Shikenan."




*Allah kai mana rahma kasa muyi kyakyawan karshe amin."



*Antty*
[11/29, 18:54] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 63

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Ta mike ta kwashe kwanukan takai kitchen ta dawo ta wuce sama, har tayi shirin bacci Muhammad ya kira ta, dauka tayi tace
"Baka kwanta ba?"
"Yanzu zan kwanta nace bari na kira My happiness."

Murmushi ta dan saki, kira taji yana shigowa ta dauke taga Aliyu ne ido ta dan zaro tace
"Please bari na amsa wani call."

Ta kashe ta dauki ta Aliyu,
"Dawa kike waya?"
Ya tambaya,
"Uhmm uhmm da Jawahir ne."

"Me kuke fadi?"
"Yaya akan makarana wani aiki?"

"Wane aikin?"
Idon ta ne yai tsilli tsilli yace
"Uhmm ina jin ki."

Wani case ta lalubo ta fada masa yace
"Ganewa ne baki ba ko me?"
"Eh."

Bayani ya hau yi mata, tana ji sosai take ganewa, Muhammad ya kira yafi sau uku sai yaji call waiting sun dauki kusan awa daya sannan yace
"Ina fatan kin gane?"
Kai ta gyada yace
"To kije ki kwanta nasan dare yayi muku sai da safe."

"To Yaya nagode."
Ta kashe wayar, tana kashewa Muhammad na kiranta, dauka tayi yace
"Dawa kike waya?"

Shiru tayi tana mamakin wai meyasa suke mata haka ne kowa bai son tai waya da

Please Login or Register in order to submit comment